Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 87

Sponsored Links

Page 87

Wayar anty ummee ta sake kira cikin mugun rudani da tashin hankali tafara gaya mata yadda ake ciki,ita kanta abun ya bata mamaki sosai

“Wannan maganar bata waya bace,ki daure ki cinye komai kiyi masa duk abinda yakeso,zuwa jibi in sha Allah zamu dawo daga bikin ‘yar yayar babansu khadija(mijinta),gaata in sha Allah da wurwuri zaki ganni,idan ban samu fita bama zan miki magana saiki shigo mu hadu.

Wannan maganar ta tayar da hankalin hafsat din sosai,ganin jibi take tayi mata mugu mugun nisa

“Don Allah ki katse bikin nan anty ummee,kizo mu samu mafita,ina cikin mugu yanayi,ji nake zuciyata ba zata iya dauka ba,kamar zata fashe nakejinta”

“Indai bakiyi juriyar dana gaya miki ba kikace zakibi son zuciyarki to komai zai lalace miki ne” abinda tace da ita kenan.

Tayita kwatanta yadda zata fuskanceshi da fuskar komai ba komai ba amma ta kasa,kwata kwata zuciyarta bata da irin wannan juriyar da jarumtar irin ta anty ummee din,ta gama cusguna ma rayuwarta kuma tayi masa abinda yakeso?,babu abinda idanunta ke hango mata sai sanda suke fitowa daga dakin,yau hannun abbas dinta ne cikin na wata macen?,turakarsa da duk duniya ita kadai tasan kalarta yau sai ga wata mitsitsiyar yarinya ta fito daga ciki?,wa yasan ma me suka aikata suka ajiye mata yarinya a falo?.

Duk yadda ta juya ta kasa aiwatar da komai,kawai saita kulle kanta a dakin ita kadai,saqa da warwara ba irin wadda batayi ba akan yadda zata bullowa al’amarin,kota kan yaranta ba ma bata bi,suma yaran dawowar widad yasa basu sake nemanta ba,suna can wajenta,wadda bayan ta gama hada masa tea din ta koma yin wanka ta wuce dasu,ta sake yiwa nawwaran ma wanka,don ita kanta ba cikakkiyar tsafta a jikinta.

Zamansa a sassan nasa sai zuciyarsa ta kasa jurewa rashin ganin gilmawarta,ta saba masa da qamshinta,girkinta da a yanzu duk duniya babu girkin da yakejin taste dinsa idan ka dauke na hajiyarsa bayan nata,ya dinga qoqarin danne xuciyarsa,don a qa’ida awannin na hafsat ne,bayason kuma ya fara sabawa jiki da zuciyarsa da aikata wani abu da zai jagoranceshi ga zamowa kasashen namiji mara adalci,dole yayi wanka ya shirya ya biya ta sashenta don a qalla cikin su biyun ya kamata wata a ciki tasan inda zashi kada a nemeshi,hafsat ya dace ya soma fadawa,amma yaci alwashin bazai shiga sashenta ba,zai mata horon da zata sake shiga hankalinta.

Tana tsakiyar su mimi din suna assignment,ta dora abinci a kitchen,gown ce a jikinta na chiffon material butter color da zanen green flowers qananu

“Zan fita amma bazan dade ba zan dawo” ya furta jikinsa na amsawa,don daga inda yake tsayen yana iya jiyo qamshinta mai dadi,ga kuma qamshin da sashen kansa yakeyi wanda ya cukude da qamshin girkinta.

Marairaice fuska tayi tana kallonsa da farare sol din idanuwanta

“Uncle…..don Allah kada ka dade” murmushi ya subuce masa, ya jinjina kai yana kallo labbanta

“In sha Allah” kusan a tare sukayi masa a dawo lafiya,har ya isa bakin qofa yaji bazai iya wucewa ba,ta gama kashe masa jiki,yana qishirwar lausasan labban nan nata,sai yadan waiwayo ya mata sign din tazo.

Miqewa tayi tana sakin murmushi,tana kaiwa bakin qofar ya jawota cikin labule yadda yaran ba zasu iya hangosu ba,baiyi wata wata ba ya mannata da qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,ya dago fuskarta yana dubanta,idanunsu suka sarqe waje daya,sai suka hau yiwa juna kallon kallo,cikin zafin nama ya hade bakinsu waje daya.

Da qyar yayi controlling din kansa,ya zareta daga jikinsa yana sake kissing goshinta

“Allah yayi miki albarka,take care” ya fada yana ficewa a hankali,sai ta kasa motsawa ta bishi da kallo,yayin da wani lafiyayyen murmushi ya dinga fita daga fuskarsa,yana ji a jikinsa kallonsa take,wannan dalilin ya hanashi waiwayo,don ya bata damar kallon nasa sosai yadda ranta yakeso,ya hangi wasu abubuwa sosai daga zuciyarta,wanda ba lallai ita din ta fahimci shigarsa rayuwarta ba.

Sai data daidaita kanta sannan ta koma cikin yaran tana tana labbanta da yatsunta, batasan me yasa duk sanda yayi mata irin wannan abun take tsintar kanta a wani yanayi ba

“Kema kin zama yar iska ko?” Ta tambayi kanta da kanta,sai ta bushe da dariya ita kadai,har yaran suna kallonta dukansu,mimi ta tambaya

“Mene ne anty” dan zubawa yarinyar ido tayi har yanxu murmushin dake saman fuskar ta bai bace ba,sai ta kama kumatunta

“Babu komai mimi,kawai inason daddy uncle….” Ta furta maganar ba tare data shirya ba.

Farinciki ya kama yarinyar,ta washe bakinta tana dariya

“Shima yace yana sonki” ido ta fidda

“Yaushe?”

” rannan dinnan” murmushi ta kuma saki,tana juya maganar yarinyar a ranta,saita miqa mata pencil din sukaci gaba da rubutun,zuciyarta wasai cike da tunaninsa,abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba akan wani halitta.

Dole saboda yunwar cikinta ta fito ta shiga kitchen,ta fara tunanin me ma zata dafa musu?taja tsaki yafi a qirga,ta rasa dame zata fara,saita matsa ta window gaban window din kitchen din nata ta zugeshi saboda iska ta shigo.

Tana gama budewar iska me dadi mai hade da wani hadadden qamshin abinci ya cika mata ciki,ta hadiyi yawu da kyau tana tunanin ta inda qamshi kala kala yau yake cika mata gida,tabi wajen da kallo tana qaramin nazari,sai ganinta ya tuqe a sassan widad.

Gabanta yadan fadi,kada ya zamana yarinyar ke girkin dake bada irin wannan aroma din,kai ta kada,ko jikinta kunne ne ba zata yadda da haka ba,yarinyar da aka kawo ko ruwan zafi bata iya dafawa ba,yaushe akayi dare har garin zai waye ta iya girki haka?.

Tun tana aikin tana basarwa har ta gaza,sai ta ajjiye abinda takeyi ta juyo ta baro sassan nata ta doshi sashen widad din,tana kusantar part din iska da kums hancinta suna tabbatar mata daga can ne qamshin abincin ke fitowa,sai tayi tsaye daga bakin qofa yatsanta a baki,ya akayi haka ta faru?,bata da abinda zatayi,dole haka ta juya ta koma gwiwa a sanyaye,amma kuma ta cika da mamaki tare dason gano yadda akayi haka ta faru.

Tana girkin amma gaba daya tunani ya cika mata kanta,ranta a jagule yake,bata qaunar ganin wani ci gaba sauyi ko walwalar rayuwa daga yarinyar gaba daya.

Sallama taji da muryar mimi,a mamakance ta waiwayo tana kallon yarinyar

“Mommy kizo inji daddy”

“Ke…..waye ya koya miki sallama?” Daria ta saki cikin jin dadi

“Anty amarya ce,tace duk inda za’a shiga sai anyi sallama,ba kyau shiga guri idan ba’a yi sallama ba” haushi takaici da kuma baqinciki suka cikata,wanne irin sanabe ne haka za’a fito mata dashi akan diyarta,sai taha qwafa

“Shi kuma me zanyi masa,har ya gama fushin nasa ne?” Ta fada tana kallon yarinyar kamar itace zata bata amsa,ita dai batace komai ba,sai taja tsaki ta kashe gas din ta fito zuwa dakin baqi da tace yana can.

Tunda tayi sallama taga kawunta gabanta yayi mummunar faduwa,saboda tasan cewa lallai ruwa baya tsami banza,ta saci kallon abbas dake zaune daura da kawun nata suna taba hira,wadda duka akan abinda ya shafi security na qasa ne,baiko dubi sashenta ba,haka ta daga kai ta isa ga kawun nata ta zube tana gaidashi kanta a qasa.

Shuru tayi ta nutsu sosai kamar da gaske tana sauraron kawun nata sanda yake mata fadan tsafta,iya abinda yafi abbas din yakai qorafinta akai kenan,amma ji take gaba daya ya gama tozartata ya wulaqantata,hausawa sukance wai wanzami bayason jarfa.

“Nifa kawu kawai baya ganin qoqarina ne,amma ai inayin duk abinda naga zan iya bakin gwargwado”

“Oh…..qarya yake miki kenan?,nace qarya yake miki,to ko ni da nake namiji ai gashi ina gani” ya fada yana nuna dakin baqin da ya hada qura sosai,sai kawai ta saki kukan takaici,kawun ya qara da cewa

“Duk qoqarin da abbas yakeyi babu wanda bai san dashi ba,don bai taba kawo qararki ba tsahon zamanku tare sai yau,kuma bazai taba tiwuwa ace shekarun duka da kuka kwashe ke dashi baki taba yi masa laifi ba,saidai kece d baki gani”

“Nima kawu ai yana yimin”

“Rufen baki,me ya hanaki ki fada” ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,yayi mata fada sosai ya kuma tursasata ta bashi haquri.

Kamar wadda aka cusawa tsumma a baki kanta a qasa haka ta furta kayi haquri,gaba daya ma abun sai ya jishi banbarakwai,don zaiyi mugun mugun wahala kaji kalmar ban haquri daga bakinta,daga qarshe dukansu kawun ya hadasu yayi musu nasiha sannan ya wuce gida,abbas ya fita ya rakashi har bakin mota sannan yayi masa alkhairi,duk da cewa da qyar ya karba.

Daya dawo tana ta kumbure kumburenta sai ya watsar yayi kaman bai gani ba,ya tattara ya fita sallah,bai kuma dawo ba sai bayan isha’i,don ya tsaya ya saurari karatun da ake a masallacin duk bayan sallan isha’i zuwa qarfe tara na dare.

Silk sleeping dress ce a jikinta baby pink mai gajeran hannun net,duka tsahonta iya qaurinta yake,ta lullube kanta da wata qaramar hular net mahadin kayan,ta cusa duka gashinta aciki,idan kayi mata kallon farko saika dauka batasan ko zo na kasheka da hausa ba,dakin babu wadatar haske sosai,sai na screen din wayarta dake hannunta.

Gaba daya bata jin dadin chart din da takeyi,zuciyarta duka babu dadi,wani irin kewarsa ce take taba zuciyarta a hankali,tun dazu daya shigo yace zai fita bata kuma ganinsa ba,kuma dazun taji shigowar motarsa,taji mimi tana masa oyoyo,amma bai shigo ya sake ganinta ba?,wani abune da bata saba dashi ba,duka sai taji qirjinta da zuciyarta sun quntata,wayar ma ta fita a kanta,ta maidata gefa ta ajjiye tana zamewa ta kwanta,idanunta suna hada ruwan hawaye.

A gajiye yake jinsa,don haka ya nufi sashen widad yayi mata sai da safe,ya murda qofar ya jita a kulle

“Sarkin tsoro” ya fadi yana sakin murmushi,ya saka nasa key din ya bude ya shiga.

Falon nata neat kamar ba’a zauna ba,qamshinsan nan yana nan,amma akwai qarancin haske,da alama ta gama shirin kwanciya.

Lumshe idonta tayi sanda taji sallamarsa,sai taji wani abu da ya tokare mata a qirji yana sauka,ta bude idonta tana amsa masa sallamar,dai dai sanda ya shigo dakin,ya saka hannu ya kunna fitilar haske ya gauraye ko ina.

A kanta idanunsa suka fara sauka,suna hada ido sai taji zuciyarta ta karye,ta sake narkewa tana jin idanunta suna tsatstsafo da hawaye

“Bakiyi bacci ba?” Ya tambayeta yana takowa inda take,maimakon ta amsa masa saita cusa kanta cikin pillow tana sakin kuka,yaji a jikinsa kukan take,saboda haka ya tako da sauri ya iso inda take

“Wuud(qauna/soyayya,sunan da ya kuma fara kiranta dashi kenan)” sake cusa kanta a pillow din tayi,sai ya haura gadon gaba daya,ya birkitota jikinsa yana leqen fuskarta

“Me ya faru?,kuka?” Gaba daya ta saki kukanta,ta kuma qanqameshi tana saka kanta a qirjinsa,cikin narkakkiyar muryar kukan tace

“Ba kaine ba?”

“Nine?,nayi me?” Ya fada tana fidda idanunsa

“Tunda ka fita baka sake shigowa ba kayi tafiyarka,kuma daka dawo ka shiga wajen mommyn mimi ni kuma sai yanzu ka shigo,bayan ma a can zaka kwana”

“Kishi?!” Ya fada a zuciyarsa yana zaro idanunsa waje,wani lafiyayyen murmushi kwance saman fuskarsa,maganarta dai dai take da albishir a gareshi na rainon da yakewa zuciyarta ya fara kaiwa ga gaci,albishir ne a gareshi na zai fara tarbar sabuwar rayuwar daya raina,sabuwar zuciya da jaririyar soyayyar data fara ginuwa.

Rungumeta yayi gaba daya a jikinsa,cikin taushi da laushin harshe ya fara gaya mata wasu kalamai da suka sata jin kunya,tun tana ya bari yana qi har kunya ta sakata ta shige jikinsa gaba daya,sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya sakata ta kwanta,ya rufeta da duvet da kyau,ya saita mata sanyin ac dana fanka guri daya,ya kuma rufe mata dukka windows dinta dama sashen gaba daya.

Tana jinsa yana fita kamar tace masa ya dawo,to amma ta samu dakiyar zuciya tunda ya gaya mata goben a nan zai kwana,ta rufe idonta tana sake bawa kanta qwarin gwiwa,duk da zuciyar dai babu dadi.
[3/19, 5:44 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button