Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 11

Sponsored Links

Book 2

*Episode 11*

Maiduguri

misali karfe 1 na rana gaba ɗaya gidan ba kowa sai yarinyar da Ahzan ya buge da mota, hanan ta tafi school
Mum tana wajen aikin ta a babban hospital

zaune take a palon mum Ahzan tana chin pop corn, tana kallon film a chikin makekiyar Tv dake manne a bango.

jin motsin mutun a kantane yasa ta ɗago kai, kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta dan taga alamar bai yi kama da mutanen kirki ba, shiru tayi tana tunani anya wan nan ba shine yaya deen ɗin da Aunty hanan ta taɓa bata lbr ba kuwa, dama Aunty hanan tace min ɗan iskane ashe da gaske ne kaga wani gashi kamar shekan tsuntsu.

Chike da iskilancin deen yace “ke chika yaushe kika zo gidan nan? Baa faɗamin nazo na latsaki ba irin wan nan kaya ai sai ni, wai ma wacece ke? Waya kawo ki ko dai ke yar uwar wanchan matar ne? Shiru yarinyar tayi kamar ba da ita yake ba ta chigaba da chin pop corn nata “ke chika wai ba dake nake bane!? Ko kallon in da yake batayi ba, hannu ya kai zai taɓata chikin sauri ta mike tsaye tare da yar da roban pop corn ɗin chike da izza tace “wlh idan ka kuskura ka taɓani sai na sharara maka mari! “Wow kai kaji wata voice mai shegen daɗi, gaskiya ne ke barikiji tun da kika zo gidan mu tofa taɓaki ya zama dole, idan ma zaki saki jiki gwara ki saki jiki idan kuma kinki to zaki sha wahala “kai har ka isa ka bani wahala ni bari kaji mutumin kirki ma bana tsoran sa bare mutumin banza Allah kaɗai nake tsoro” wani wawan mari ya sakar mata a kuma wadda yasa ta fasa ihu kwashe kafafunta yayi ta faɗi kasa, chikin tsawa yace “ni zaki chewa ɗan iska to wlh yau sai kin gwammachi da baki zo gidan marigayi Alhaji Abbas ba” sake dungule hannu yayi zai kai mata bugu charaf Ahzan ya rike hannun sa ta baya chike da jin haushi ya wanka wa deen wani wawan mari chikin tsawa Ahzan yace “me ya kawo ka part ɗin nan!? Chike da rashin kunya deen ya fara magana “tambaya kake ko neman sani wai shin Ahzan ko ka manta Alhaji Abbas ne ya gina gidan nan ba kai ba to idan ka manta na tuna maka kuma kamar yadda kake ɗan shi nima haka nake ɗan shi har Alhaji Abbas ya bar duniya bai taɓa yiwa wani iyaka da shiga wani part a chikin gidan nan ba kuma koda yayi ma kasan dai ni bai isa ya hanani ba” afusache Ahzan ya sake ɗaga hannu zai mari deen chikin fushi deen ya rike hannun nashi yana girgiza kai “bari kaji Ahzan ko ɗazun da ka mare ni bansan zaka kawo marin bane shisaya har ka samun daman marin nawa, yanzu lokachin ka bugeni na barka ya wuce, dan ni ba yaro bane! Kwache hannun sa Ahzan yayi chikin fushi ya fara bugun deen, damko kafar sa yayi, yayi wurgi da shi, chiro belt nashi yayi ya fara bugun deen ɗin kamar Allah ne ya aiko sa, ihu deen yake yana faɗin “mugu azzalumi kawai dan kaga kafi karfi na ko to ai baka fi karfin Allah ba, duk zaluncin da zakamin wlh tarawa nake idan ya chika sai na rama, wani naushi Ahzan ya kai wa deen a baki dan yayi shiru amma ina yaki yin shiru, gaba ɗaya Ahzan ya fasawa deen baki sai jini ke zuba, da gudu yarinyar ta miƙe ta bar palon ta nufi ɗakin hanan tana kuka.

Sosai Ahzan ya bugi deen amma duk wan nan budu daa deen yasha hakan bai sa bakin sa tayi shiru ba daga karseh hakuri kawai Ahzan yayi ya kyalesa, ya juya ya bi bayan yarinyar, deen kuwa bajewa yayi a kasa awajen ya cigaba da ihun sa yana surutai.

Kwanche saman gadon hanan ya same ta tana kuka, saman drawer gefen gadon ya zauna a nitse ya fara magana “ya isa haka kukan kinji? Ɗago kai tayi tana ganin sa ta mike zaune tana goge hawayen “yaya Ahzan wai daman a gidan nan yaya deen yake kuma wai daman kanin kane, ni kullun idan Aunty hanan tana bani lbr sa, ina tunanin ko ba’a nan yake ba ban ma taɓa tunanin ɗan mum bane, yanzu gashi saboda ni ka da kesa a banza” tana magana tana shesshekar kuka “look ya isa haka deen kani na ne baban mu ɗaya amma ba mum che ta aife sa ba maman shi daban ina ga tun da kikazo gidan nan baki fita waje bane, amma da kin fita tsakar gida zakiga gate na shiga part nasu, daga gefen hagu, ki daina damuwa ba dan saboda ke na bugi deen ba kisani baa taɓa yin sati ban bugi deen ba na rufesa a station na bashi horo amma duk da haka a banza baya jin magana ga shaye shaye da bin abokan banza, idan na hukun tashi kullun sai mum nashi tayi ta faɗa bata son laifin sa ko kaɗan, dan haka babu ruwanki da shi idan ya shigo ya sameki a palo ki tashi ki koma ɗaki ki bar masa palon kinji ko? Gyaɗa masa kai tayi tare da faɗin “eh naji” “munyi magana da mum tun da har yanzu baki tuna sunan kiba zamu rinƙa kiranki da Ummi kinji” “to yaya Ahzan Nagode” “ki dai na min godiya kinji? ni yayan ki ne kuma kin chan chan chi na miki hakan, yanzu dai ya kamata ki shiga school kafin Allah yasa muga iyayenki ko? Da sauri ta mike zaune ta goge hawayen fuskarta ta fara murmushi “yaya Ahzan yanzu nima zan rinka sa uniform irin na Aunty Hanan? zan rinka zuwa in da take zuwa? Zan rinka rubutu a takarar da kamar yadda take? Kasa bata amsa ma yayi ya zuba mata ido kawai yana kallon yadda take murmushi chike da farinchiki, shi kanshi bai san lokacin da ya fara murmushi ba “yaya Ahzan yaushe zaka kai ni to? “Ranar Monday In Sha Allah” saukowa tayi daga gadon ta dawo gaban sa ta sungunna tace “Nagode yaya Ahzan” mikewa yayi ya nufi waje yana faɗin “ki dai na yimin godiya ni yayan ki ne mai kaunar ki dan Allah” yana gama faɗin hakan ya fice daga ɗakin, da murna Ummi ta mike ta koma kan gado tana ta farin ciki ta kwata ta lumshe ido kamar mai barchi

KANO

Kwanche Ammi take a saman gadon Abba ta tada kai da chinyar sa, tana wasa da yatsun hannun sa ɗaya, chikin nitsuwa Abba ke shafa gashin kanta da ɗayan hannun sa “Aisha an gama ginin gonan kun nan fa saura mu ɗauki ma aikata sai a kwaso dabbobi a zuba aduba abubuwa da ya kamata a kara awajen, amma wani suna ya kamata a sanyawa gidan gonan? Gyara kwanchiya Ammi tayi tana kallon face nashi da kyau ta fara magana “ni har ga Allah na barwa su hiyana rabon nawa gadon nariga da nayi kyauta da wadda zanyi sauran kuma a chigaba da kula musu da shi ka zaɓi duk sunan da ya dache ka sanyawa gidan gonar, amma ina neman wata alfarma, idan ba damuwa “wace alfarma che wan nan Aisha? ” Ina son idan anje ɗauko dabbobin nan a ɗauko har da bello dan bello ba mutunne na yarwa ba, ya mana halak chi ya chanchan chi muma mu kyautata masa, ina gidan da ka sayawa Ahmadu lokachin da mukayi mukayi ya dawo nan yaki to kabawa Bello gidan ya zauna da matar sa” “Aisha wan nan shawara ce mai kyau kinga daman yasan kan dabbobi sosai sai mu bashi aiki a gidan gonar yanayi duk wata muna biyan shi Albashi ko? “Eh hakane kaga yaransa zasu samu karatu zasuyi ilimi kuma zai sanya matar sa ma a makarantar tun da itama ba wani girmane da itaba kwata kwata bazata wuchi 18 to 19 years ba, shi kan shi Bellon ma bai wuchi 25 years ba zai iya shiga school ai” hakane kina da gaskiya Aisha Allah dai ya dafa mana zanyi magana da Aryan dan muga sunan da ya dache musawa gidan gonar.

“Yauwa niko ɗazun banga Aryan awajen breakfast ba naje part nashi baya nan na kira layin sa bata shiga” “Aryan fa baya nan ya tafi Maiduguri dan an kirashi jiya da daddare akoi wadda ya kalli diyana, shine yaje ya duba ko itace” zubur Ammi ta miƙe chike da farinchiki sai murmushin take tace “Allah yasa itace ko Aryan ya samu kwanchiyar hankali bawan Allah wlh kullun sai na tayashi da addu’a, duk lokacin da na tunashi sai nayi hawaye yana matikar Son diyana sosai gashi abun ya haɗe masa rasuwar Aiman batar diyana” Abba da ya lura yanayin Ammi ya fara sauyawa ta fara shiga bakin chiki da ta tuna diyana, sai ya matso kusa da ita chike da so da kauna ya rungumota tare da ɗago habarta yace “ai yadda nake son ki yafi yadda Aryan ke son diyana” hararan wasa ta wurga masa tana faɗin “gaskiya Aryan yana bala’i son diyana sosai” kara rungumota sosai Abba yayi yana kokarin mantar da ita maganar diyana dan yasan yanzu zata fara kuka, kwan chiya yayi da ita a jikin sa, yana shafa bayan ta a hankali, shiru sukayi har barchi ya ɗauketa.

UK

karfe 6pm hiyana ta farka a hankali ta waro idon ta, da kyar ta miƙe zaune a hankali chike da tsoro ta kai idonta kan katafaren gadon sa, ganin tayi Bgs baya nan chikin sauri ta fara jujjuya blue eyes nata tana duba ta ina zata gan shi, amma ina ko alamar sa babu a ɗakin mikewa tsaye tayi jiki ba kwari, tana son fita waje amma babu kayan sawa, a hankali ta taka ta fito palon su, ta rasa ya zatayi gashi daman da hijabi ɗaya tazo kuma ta yaga hijabin tana son ta shiga ɗakinta domin ta ɗauki kayan da ta chire ta mai da tun da bata da wani amma tana tsoro gani take kamar akoi wani machijin, tayi nisa chikin tunani sai ji tayi an taɓa ta firgigit ta ɗago ido ganin Amrat che yasa ta sauke ajiyar “Amrat jeki kawomin hijabin ki, in sanya ina su Aunty Zahra kuma? “Aunty Zahra suna palo yanzu muka dawo daga wajen shopping nima zanje na ajiyewa yaya Fahad kayan shine a ɗaki kizo muje palo kema kiga kayan da Aunty Zahra ta zaɓi miki” “to jeki kawomin hijabin ki tukun nan” to Amrat tache tare da wuchewa ta shiga ɗakin su Amrat na wuchewa sai ga Bgs, chikin sauri Hiyana ta sugunna kasa tace “ina wuni yaya prince” ko kallon in da take bai yiba ya wuche betroom nashi jim kaɗan ya fito ya fice waje, da alama wani abun ya ɗauko, tunani hiyana ta shigayi anya yaya prince zai iya sauyawa kuwa shi kwata kwata ma ba zaka taɓa gane in da ya dosaba baka gane daman shi bare hagun sa, mutunne kamar ba mutun ba, amma zanyi magana da Aunty Farida da kuma Ammi kila su karamin wani shawara amma gaskiya ina da babban aiki kuma da alama na dauki alkawarin da ba zan iya chikawa ba, tana duke a wajen har Amrat ta fito mata da hijabin ta.

“Aunty Hiyana ga hijabin” mikewa hiyana tayi ta ansa hijabin ta sanya iya guiwa hijabin Amrat ya tsaya mata tare suka jera zuwa palon kasa, nan suka samu Zahra da Lamrat sun baza kaya a gaba sai surutu suke, saman sofa mai zaman mutun 1 Hiyana ta zauna tare da ɗagawa Zahra gaisuwa, fiska ɗauke da fara Zahra ta amsa tare da faɗin “Aunty hiyana wayan chan trolley guda ukun nakine ki duba kayan idan akoi wani abun da kike bukata wadda baa sa a chiki ba yaya khalid yace ki faɗamin sai gobe mu koma wajen ki zaba da kan ki idan ma kayan gaba ɗaya basu miki ba sai muje gobe ki zabo da kanki.

Saukowa kasa karfet din Hiyana tayi batare da tayi magana ba ta fara bubbuɗe trolley tana duba kayan, gaba ɗaya trolley sai da ta buɗe su ta duba chike da jin haushi ta ɗaugo blue eyes nata tana kallon Zahra ta fara magana

“Aunty Zahra menene wan nan? Ai wan nan ba kaya bane shirme dai kuma naga babu hijabai da irin abayan nan da sauran manyan kaya na Musulunci a chiki sai dai shirmen irin kayan da diyana ke so” chike ta tsokana Zahra tace “Aunty hiyana yaya prince ne yace wa yaya khalid irin kayan da zai saya miki kenan kuma kada ki kuskura ki rinƙa sanya hijabi a chikin hidan nan dan nan ba gidan hijabi bane gidan kashe miji da love ne wai ma Aunty Hiyana ba Aunty farida ta hanaki sanya hijabi ba? Kina son in faɗa mata chewa baki jin maganar ta ko? “Aunty Zahra waye ya tsara miki maganar da zaki faɗamin haka? dan dai na san wan nan ba maganar ki bane sai dai idan wani ne ya tsaramiki “ni Aunty hiyana babu wan da ya tsaramin iya Gaskiya na faɗamiki” “naji iya gaskiya ne to amma Aunty Zahra me yasa kuke son haɗani da mutumin da baya ko san ganin fuskata? “Au yanzu Aunty Hiyana kin manta alkawarin da kikayiwa su yaya khalid ɗazun nan na chewa ki kayi fa kin ɗaura ɗamarar yaki da jiji da kan yaya prince? “Ban manta ba Aunty Zahra ina sane” “to ai saboda mu taya ki yaki da jiji da kan na shine yasa yaya Khalid yace in zaɓa miki irin kayan nan san nan yace ga waya na baki akoi sakon massage a chiki ki karanta” ta kari maganar tana mikowa hiyanar waya kiran i photo 14 promax, murmushi hiyana tayi tasa hannu ta ansa wayar tana faɗin “wow amma gaskiya wayar tayi kyau ki tayani yiwa yaya khalid godiya” “eh to yanzu dai ki duba massage ɗin dake chiki first” “aa Aunty Zahra zan duba amma sai na koma ɗaki yanzu bari na kwashe kayan na kai ɗaki tukun nan, dan bansan ganin waje a watse” shiru Zahra tayi bata sake magana ba miƙewa Hiyana tayi tare da ajiye wayar a hannun kujera ta fara kwashe kayan nata da ta watsa tana mayarwa chikin trolley

“Aunty Zahra yanzu da baku sayamin hijabi ba dame kuke son na rinƙa yin sallah? “To baki da hijabi ko nayin sallah ne daman? Ina wadda kika sanya da za mu zo” “ai shi na yaga dazun yanzu ko ɗaya babu” “to inaga sai dai ki rike na Amrat dake jikin kin nan dan a garin nan ba’a sayar da hijabi” shiru Hiyana tayi ta chigaba da kwashe kayan dan tasan karya Zahra ke mata akoi kasar da ba’a sai da hijabi ne amma bata son yin jayayya da maganar Zahra dan haka sai tayi shiru ta chigaba da kwashe kayan

Babban trolley ta fara za zuwa part nasu tana shiga ta tsaya turus a Palo tunani ta shiga yi aina zata ajiye kayan nata dan wlh ko kasheta za’ayi bazata koma ɗakin taba dan ita bata yarda da ɗakin ba gani take akoi wani snake ɗin a chiki, da taga ba abun da tunani zai kara mata idan ba zafin kai ba sai ta nufi bayan sofa mai zaman mutun 3 ta ajiye trolley haka ta kwaso sauran dukkan ta ajiye su a bayan sofa, buɗe trolley tayi ta ɗauki wasu riga da wando masu ɗan hankalin ta lallaɓa ta leka ɗakin yaya prince dan taga ko ya dawo bata sani ba, tana ganin baya chiki tayi sauri ta shige chikin ɗaki ta chire hijabi jikin ta sauri sauri ta sanya kayan data ɗuko tare da mai da masa towel nashi toilet ta fito da sauri har tana haɗawa da gudu

Sai da ta fito palo san nan ta sanya hijabin Amrat a jikin ta ta fice daga palon nasu ta sauka palon kasa

Tana zama saman sofa mai zaman mutun 1 su yaya khalid na shigowa shi da yaya Yusuf kusa da Zahra yaya Khalid ya zauna, shi kuma yaya Yusuf kusa da Lamrat ya zauna, chikin nitsuwa da girmama Hiyana ta gai dasu, da fara suka amsa mata tare da tambayar ta ya karfin jiki sunkuyar da kai kasa tayi tace “naji sauki”

“Amma sister kin kaiwa Bgs abin chi kuwa? Chewar khalid yayi maganar yana kallon ta “eh yaya Khalid tun kafin ku dawo wajen aiki naje na shirya masa abin chin sa a ɗaki amma bai Chiba, daman kuma nasan ba chiɗin zai yiba dan jiya ma da na kai masa bai Chi ba” chike da ɓachin rai Khalid ya miƙe ya nufi waje yana faɗin “ina zuwa, kai tsaye wajen hutawa dake gefen dama a chikin gidan Khalid ya nufa

Waje ne mai matikar kyau da tsaruwa kewaye yake da furanni masu kyau da tsada sai kamshi suke, daga tsakiyar wajen kuma wasu tsadaddun kujeru masu numbashine a wajen an sanya runfa mai kyau a dai dai saitin kujerun san nan aka kewaye kujerun da glass aka sanya karamin table a tsakiya, ga wasu yan kanan box glass masu kyau suna ɗauke da ruwa da wasu irin kifaye (fish) masu kyau sai yawo suke a chiki an kewaye wajen gaba ɗaya da box glass na kifin sai wasu tsadaddun fitilla masu bada haske mai tambarin Bgs, komai na wajen ɗauke yake da tambarin Bgs, kallo ɗaya zaka wa wajen kasan wajene na musamman kuma mai mallaki wajen mutun ne na musamman.

Zaune saman kujera yana latse latse a system dake kan chinyar sa Khalid ya iskoshi sanye yake chikin wando 3cuter da yar riga mara nauyi, chike da bachin rai khalid ya shigo wajen amma yanayin arba da face ɗin Bgs nan take yasha jinin jikin sa dan yaga babu alamar wasa a face nashi, jiki a mache ya zauna kusa da shi har yar shakewa voice nashi take ya fara magana

“Haba Bgs ba kamin alkawarin idan sister ta kawo maka abinchi zaka chi ba? Why yau baka chi ba? Shiru Bgs yayi kamar bai san da zaman mutun a kusa da shi ba, idan da sabo khalid ya saba yasan idan kayiwa Bgs magana wani lokaci ma yana ɗaukan 10mins kafin ya baka amsa idan sauri kake ma to sai dai ka tafi, dan wannan abun ya zamo masa jiki, wani lokaci sai ka chire rai da samun amsar Bgs tukun nan sai kuma kaji ya baka amsa wata zubin har sai ka manta da maganar da kayi masa ma, kafin ya baka amsa, to awan nan karon ma hakane sai da Khalid yayi zaman 15mins san

Batare da ya dogo idon sa daga kan system ɗin ba ya fara magana “ni fa Khalid ban maka alkawarin hakan ba kawai nache maka zanyi tunani ne, so naga ma no need nayi wani tunani dan nasan ba zan iya chin abun da yarinyar nan ta taɓa da hannun taɓa kyama take bani ban so, ɗazun ma dana che zanyi tunanin kawai dan naga kaji bachin rai sosai ne shiyasa na maka hakan dan ka sauko amma yanzu ka tashi ka bani waje dan nima raina a bache yake yanzu!! Ba musu khalid ya miƙe ya bar wajen dan ya lura tabbas Bgs na chikin bachin rai idan ya tsaya yache zai masa wani magana to zai iya sumar da shi awajen

Chikin gida ya koma kai tsaye ya wuche part nashi mikewa Zahra tayi ta bi bayan sa dan taga fiskar sa kamar babu annuri.

11pm Amrat che kadai zaune a palon kasa tana shan complex su Zahra sun tafi part nasu, a tare Fahad da Bgs suka shigo palon kai tsaye part nashi Bgs ya nufa, Fahad kuwa tsayuwa yayi yana kallon Amrat dake ta faman shan complex nata “ke me kike yi a nan har yanzu baki kwnata ba? “Naga baka dawo ba ne yaya Fahad kuma sai na fara jin yinwa shine na fito na haɗa complex, karisowa in da take yayi yasa hannu ya ansa cup din, debo complex ɗin yayi a spoon ya kai bakin sa ya sha zama yayi kusa da ita, ya fara shan complex ɗin sosai yana sha yana bata a baki gwanin sha’awa, a tare suka shanye complex ɗin bayan sun gamane ya ajiye cup ɗin a gefe, ya dawo da kallon sa kanta matso da fukarsa yayi kusa da tata har suna iya jiyo numfashi juna harchen sa ya kai kan ɗan karamin bakin ta la lashe ragowar madarar complex dake wajen, wani dogon numfashi Amrat taja tare da runtse ido kasa kasa yace “numfashi me kike ja kuma? Ko kinyi tunanin bakin naki zan sha ne? Girgiza masa kai tayi tana faɗin “aa” “to ai garama kiyi tunanin hakan dan yanzu kuwa zan fara shan kayana” buɗe baki Amrat tayi zatayi magana yayi saurin haɗe bakin su waje guda, sosai yake kissing nata chikin dabara ba tare da ya zame kabin sa daga nataba ya duke ta ya ɗorata kan chinyar sa tare da mikewa da ita ya nufi ɗakin su, yana shiga palon part nasu yachi karo da hiyana kwanche saman doguwar kujera tana barchi, ɗaure fuska sosai yayi a hankali ya zame bakin sa daga na Amrat tare da sauke ta kasa chike da bachin rai yace “Amrat jeki ɗaki ina zuwa, batare da ta lura da hiyana ba ta wuche ɗaki

Karisowa yayi wajen Hiyana yasa hannu ya ɗan bubbuga jikin kujerar yana kiran sunan ta, da kyar ta iya waro blue eyes nata waje sunyi jaa almar barchi bai ishe taba, “sister me ya kwantar dake a nan? Me yasa baki shiga ɗakin ki ba? Mikewa zaune Hiyana tayi chikin muryan barchi ta fara magana “yaya Fahad wlh ɗazun machiji na gani a ɗakina to na roki yaya prince ya chiremin shi amma har yanzu wlh tsoron ɗakin nake ji bazan iya shiga chiki ba” “machiji kuma!? a chikin gidan nan kai anya kin gani da kyau kuwa sister to wai ta yama za’ayi machiji ya shigo gidan nan har ɗaki” “wlh yaya Fahad na gani da kyau machijin gaskiyane, ka tambayi yaya prince kaji shi ya chire da kansa” “Gaskiya abun da abun mamaki a che snake a gidan nan amma dai ina zuwa” yana kai karshen maganar ya miƙe ya shiga ɗakin Bgs.

Gaban mirrow ya samu Bgs yana shafa mai da alama wanka yayi gefen gado Fahad ya zauna chike da jin haushin abun da Bgs yakeyi wa mutane ya fara magana “yaya prince dan Allah ka bar sister tazo ta kwana a ɗakin nan ko da saman kujera ne, dan tana tsoron ɗakin ta, kaji pls? Shiru yayi kamar bai san da shigowar Fahad dakin ba sai da ya gama shafa mai ɗin sa, ya feshe jikinsa da perfume masu bala’i kamshi da tsada, slowly ya juyo ya sauke idon sa a kan Fahad dake zaune ya zuba masa ido alamar yana jiran amsa “get out Fahad!! Ya furta cikin tsawa, mikewa Fahad yayi ba musu ya fice

yana fita bai bi ta kan hiyana ba dan bashi da wata amsa da zai bata wuchewa ɗakin sa kawai yayi.

Bgs kuwa dressing room nashi ya shiga jim kaɗan ya fito sanye da kayan barchi masu kyau da tsada farare tas masu laushi, saman gadon sa ya haye ya kwnata tare da jan kyakkyawa kuma lallausan blanket nashi zuwa kan chikinsa ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba dashi.

Ranan dai a palo hiyana ta kwana, ta takure waje guda kallo daya zaka mata ka gane ba karamin tsoron palon ta keji ba, shiyasa ta takure waje guda, fiskar ta duk hawaye a bushe…

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Back to top button