Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 6

Sponsored Links

Book 2

*Episode 6*

Saɗab saɗab Zahra take lallabawa kamar ɓarauniya ta shiga part ɗin Bgs sai waige waige take tana tafiya tana juyowa ta kalli bayan ta karaf sai ji tayi tayi karo da mutun chikin tsoro da tashin hankali ta ɗago kai ganin Aunty amarya ne tsaye a gaban ya sa ta sauke nauyayyar Ajiyar zuchiya tare da faɗin “ina wuni Aunty amarya “lfy lau Auta me ki ka zo yi a nan kuma kika bar ɗakin mijin ki? “Wajen Aunty hiyana nazo” jin Zahra ta ambaci sunan hiyana yasa Aunty amarya ta ɗaure fuska cheke da ɓachin rai tasa hannu tawa Zahra nuni da ɗakin Bgs dan mugunta tache hiyana na chikin nan” “to” kawai Zahra tace san nan ta wuche ta haye saman stair case ɗin ta nufi ɗakin yaya prince ɗin

Aunty Amarya kuma sai murmushin mugunta take ta nufi hanyar fita daga palon

A hankali Zahra ta tura kofar kamar wadda bata da gaskiya ta shiga yana tsaye gaban mirrow jikin sa sanye da kayan sojoji yana gyara lallausan kuma bakin gashin kan sa, jin anshigo masa ɗaki ne yasa ya ɗago green eyes nashi ta chikin mirrow yana kallon Zahra dake ta yan waige waige alamar bata ganshiba zuba mata ido yayi sosai
ya kalleta san nan ya kalli kanshi ba shakka Auta tana kama dani sosai, why nake kaunar Auta sosai har hakane? Yayi wa kansa yambayar da ba shi da amsar ta “zo nan ke!!”ya faɗa tare da juyowa yana kallon ta da kyau, chikin tsoro da tashin hankali Zahra ta karisa gaban sa ta sugun na kasa murya na rawa tace “ina wuni yaya prince” “me ya shigo dake part nan!!? banche karna kara ganin ku a nan ba!!? “Kayi hakuri wajen Aunty hiyana nazo, jin an ambaci sunan hiyana yasa ya ɗaure fuska sosai chikin tsawa yace “tashi ki fita ko nayi ball dake!!! Da gudu Zahra ta miƙe ta fito a bakin kofar ɗakin nasa ta waje ta tsaya tana tunanin ina ne ɗakin Hiyana dan ni dai gaskiya ba zan tafi ba har sai na ga hiyana ta

Tayi nisa chikin tunanin da take ne sai taji shesshekar kuka a ɗakin dake kusa da na Bgs kuma muryan Hiyana che ke wan nan kukan, chikin sauri ta tura kofar ɗakin ta shiga turus ta tsaya ganin hiyana a duke tali nill down ta daga hannu sama tana kuka ga zulaihat tsaye a kanta rike da bulala chike da bachin rai da fushi chikin tsawa Zahra tace “ke zulaihat me hakan!! Chike da izza zulaihat tace “ina ruwanki ko kimin shiru ki fita a ɗakin nan ko kuma in haɗa dake, karisowa chikin ɗakin Zahra tayi dai dai gaban hiyana taje tasa hannu ta ɗago ta tare da mai da ta kan gadon chikin fushi ta juyo ta zabgawa zulaihat wani wawan mari ta kwasa a guje tayi waje, a guje zulaihat ta bi bayan ta a dai dai tsakiyar palon kasa ta damko gashin Zahra ta baya da karfi ta ja ta baya wani ihu azaba Zahra ta saki hankaɗata kasa zulaihat tayi ta faɗi ta buge goshin ta a kasa wani razanannen kara ta saki gadan gadan zulaihat ta nufeta a zafafa ta ɗaga hannu zata kaiwa mata naushi a chiki, chak daji a damki hannun nata da karfi kafin ta ɗago taga wanene ya kwashe kafafunta ta faɗi kasa wani wawan mari ya wanke mata fuskar ta dashi wadda yasa gaba ɗaya ta daina gani, baiyi wata wata ba ya sa kasa yayi ball da ita ta tafi luuuu saboda tsantsin wajen ta bugu da jikin stair case wani ihun azaba ta saki lokachin guda kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa

Dawo da kallon sa kan Zahra yayi tare da miƙa mata hannu alamar ta kama hannun sa ta miƙe chike da tsoro da mamaki Zahra ta kama hannun sa jawota yayi ta faɗa kan faffadar kirjinsa da ɗan tsawa yace “ba nache ki bar part din nan ba me ya hana ki tafiya kuma wacece wanchan? Chikin shesshekar kuka Zahra tace “kayi hakuri yaya prince wlh ina son ganin Aunty hiyana che shiyasa amma yanzu zan tafi” ” wacece wan chan? “Yar uwan Aunty amarya che” “me ya kawota part nan har zata bugeki? Yayi Maganar tare da raba ta da jikin sa nan dai Zahra ta bashi labari yadda ta shigo ta samu abun da zulaihat kewa Hiyana, tsaki yaja tare da juyawa ya koma betroom na shi

Haurawa sama Zahra ma tayi ta koma ɗakin Hiyana suka bar zulaihat sume awajen

In da ta bar hiyana a wajen ta dawo ta same ta sai kuka take gefenta ta zauna chike da bachin rai tafara magana “yanzu Aunty Hiyana yar zulaihat ɗin nan zaki bari ta bugeki dame ta fiki eh? To wlh tun wuri idan zaki tashi ki dai na zama shiru shiru ki kwatar wa kan ki yanchi gwara ki tashi, wlh ki ajiye ustazan chinkin nan yanzu lokachin fafata yaki ne to bari kiji in faɗa miki ma zulaihat tazo gidan nan ne domin ta samu soyayyar yaya prince shiyasa na tsaneta ranan na shiga part ɗin Aunty amarya na jisu suna shawan yadda zasu bullowa yaya prince ita da Aunty amarya to kinga yanzu tashi zakiyi ki ɗaura ɗamarar yaki ki kwachi mijinki” chikin shesshekar kuka hiyana ta fara magana “Aunty Zahra ai Aunty amarya che tazo tache komai zulaihat ta sani in rin ka yi idan ban yiba sai ta kusan kashe ni shiyasa kuma Ni fa yaya prince ba sona yake ba ya tsane ni bai son gani na dan haka ba ruwana da shi nima, kuma ba wani yaki da zanyi a kansa” Zahra zatayi magana sukaji an buga kofar ɗakin

Da sauri Zahra ta miƙe ta nufi kofar tana faɗin “Allah yasa ba yaya prince bane dan yace na bar part din nan juyowa hiyana tayi ta zubawa kofar ɗakin blue eyes nata, chike da tsoro Zahra ta buɗe kofar ɗakin ganin yaya Khalid ne yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuchiya “my wife zo ki wuche kije ki ɗauki duk abun da kike bukata nan da 10mins jet ɗin yaya prince zai tashi zamu koma London ɗan leko da kansa ɗakin yayi chike da kulawa yache “hiyana tashi kema ki shirya yanzun nan muna palon Abba muna jiran ku yana gama faɗin hakan ya juya ya nufi hanyar fita

Juyowa Zahra tayi ta kallin Hiyana chike da farinchiki tace “to Aunty Hiyana yaki da su zulaihat ya kare kiyi sauri ki shirya “Aunty Zahra taya zan tafi ba tare dasu diyana ba? ina diyana na take? wani hali take chiki yanzu? shin tana raye ne? ko ta mutu? “Aunty Hiyana kiyi hakuri kisani Abba ba zai taɓa barin rayuwar diyana ya salwanta a ban za ba zasu nemota In Sha Allah yanzu dai ki tashi ki ɗauki abun da kike so kiyi sauri dan kinsan halin yaya prince baya son jira “to Aunty Zahra, da sauri Zahra ta bar wajen ta sauko kasa ta fice daga palon ta nufi part ɗin mijin ta sauri sauri Hiyana ta mike itama tafara shiri

Gaba ɗaya family sun haɗu a palo Abba ana jiran Hiyana da Lamrat da yaya Yusuf

Rike da hannu lamrat yaya Yusuf ya shigo gwanin ban sha’awa saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna tare da zaunar da Lamrat kusa dashi, sukayi shiru suna jiran Hiyana, sai kwaɓe fuska Bgs yake ba dan Ammi dake wajen ba da ba zai zauna ba

a hankali take takowa zuwa chikin palon tana sanye da hijabin ta har kasa fari tas ta sanya nikaf baki kusa da Ammi taje ta zauna gyaran murya Abba yayi ya fara magana “to ku bani hankalin ku gaba ɗayan ku, nitsuwa sukayi gaba ɗayan su suka zubawa Abba ido suna kallon sa banda Bgs daya sunkuyar da kai kasa chigaba da magana Abba yayi
“Safras ya bukachi da ku koma bakin Aikin ku yau to naji kuma na barɓi hakan amma ban da Aryan domin ya sanar dani ya bawa Aryan hutu zuwa lokacin da zamu gane diyana, tare da matan ku zaku koma kuma zaku tafi tare da Fahad saboda amrat dan idan kuka tafi da yan uwan ta bazata ji dadin zama ita kaɗai a nan ba, ba zan gaji da yimasu nashiha akan ku kula da hakkin marayun dake kanku ba kusani yanzu kune uwan su kune uban su basu san kowa a chan ba sai ku, ina haɗa ku da Allah karku bari yaran nan suyi kukan marai chi”

miƙewa Aryan yayi chikin dashewar murya yace “Abba ina ganin No need na zauna a wajen nan saura 30mins jirgi na ya tashi zuwa Maiduguri ya karisa maganar kamar zaiyi kuka, jiki ba kwari ya fice daga Palon, wani irin mugun tausayin Aryan ne ya dira a zuchiyoyin gaba ɗaya jama’ar dake Palon, shiru Abba yayi yama kasa chigaba da magana

Miƙewa tsaye Bgs yayi yace “Abba na wuche “aa Safras ka same a ɗaki zanyi magana da kai kafin ku wuche yana kai karshen maganar ya miƙe ya nufi betroom na shi bin bayan sa Bgs yayi

kutashi muje ko chewar Yusuf miƙewa sukayi a tare Yusuf ya riko hannun Lamrat Khalid ya riko hannun Zahra Ahmad da Fahad sukayi gaba Amrat ta rike hannun hiyana sukayi waje Umar da Haidar suka rufa musu baya, palon ya rage Ammi Ummi da kuma Aunty amarya

“wai ina zulaihat ne bata fito ba? chewar Ummi guntun tsaki Aunty amarya taja kafin tace “tana ɗakin ta mana kin san ita bata son hayani yane” shiru sukayi ba wanda ya sake magana

A harabar gidan jikin motochin da sojojin bgs suka jera musu domin tafiya Airport suka tsai tsaya suna jiran Bgs

Fitowa Bgs yayi Abba na biye da shi a baya yana musu fatan alkhairin, taku irin na jaruman maza bgs yake kallo ɗaya zaka yiwa face nashi ka fahimci yana chikin bachin rai sosai, sai wani huchi yake yana furzar da iska mai matukar zafi daga bakin sa, da gudu jibga jibgan sojojin sa sukayo wajen su bubbuɗe musu kofar motochin, bgs bai bi ta kan kowa ba ya shiga mota ya zauna Khalid Yusuf mota ɗaya suka shiga tare da matan su Motar da bgs ya shiga shi Fahad yaje ya shiga hiyana na rike da hannun Amrat sunyi shiru sun rasa wani mota zasu shiga

“Sister zo mushiga motan nan kinji? Chewar yaya Ahmad yayi maganar yana nunawa hiyana motar da zasu shiga ba musu hiyana ta bi bayan sa rike da hannun Amrat suka shiga mota ɗaya da yaya Ahmad, kwata kwata Abba bai ji dadin hakan ba amma baya son yayi magana dan yanzu ma da kyar ya shawo kan Bgs akan ya yarda hiyana ta rinƙa shirya masa abin chi idan sun koma London kuma da kyar ya lallaɓa shi akan karya rinƙa daka mata tsawa dan bawani koshin lafiya ne da itaba da zarar abu ya tsoratata sai suma shiyasa Abba ya lallaɓa bgs akan karya rinƙa mata tsawa.

Da gudun gaske motochin suka bar gidan kai tsaye Airport suka nufa, juyawa Abba yayi ya koma chikin gida chike da tunanin ya zaman Bgs da hiyana zai ka san che a London Amma yayi wa kansa alkawarin yimusu zuwan bazata nan da 2 week’s dan yaga meke tafiya

Karfe 2 dai dai katafaren haɗaɗɗen jet na Bgs wadda ke ɗauke da tambarin sunan sa kamar haka PRINCE SAFRAS ya ɗaga zuwa London United Kingdom

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu akoi chakwakiya fa shine yaya zaman hiyana da bgs a London? ina diyanan yaya Aryan take? Su Aunty amarya zasuyi nasara kuwa? Shin mutuwa zulaihat tayi ko suma? Inna habiba ta mutune ko suma tayi? Shin Aryan yana ganin diyana ku koma taɓata kenan? Yaya Aunty amarya zatayi idan ta samu lbr abun da bgs yayiwa zulaihat? To domin samun amshoshin ku ku chigaba da bibiyar princess teema Star lady 💃💃

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat….love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Back to top button