Hausa NovelsMatan Ko Mazan Book 1

Matan Ko Mazan Book 1 Page 38

Sponsored Links

38
Dan kallonta Hajiya tayi ganin yanda kanta ke kasa yasa tace “tashi ki dauko ruwa da drink a fridge ki debo duk abinda kikeso a kitchen ni kadaine Meena batanan” girgizama Hajiya kai Hadiza tayi baki tabude zatai magana saita kasa Hajiya duk tana lurada ita amman tai shiru ta maida kanta kan tv, cikin wata kalan murya dake breaking Hadiza tace “Hajiya bansan ta ina zan faraba, yau kalamai sunyi karanci abakina dazan hada nabaki hakuri bisa kuskuren danamiki abaya” yadanyi shiru sabida muryanta was shaking sosai tace “Hajiya nasan nayi abubuwa da dama dasukasa kika tsaneni harda su Ya Aisha ma I called all of them dan nabasu hakuri harda Meena babu wanda yadauki wayana I understand no one wants me, Hajiya dan girman Allah dan darajan Allah Hajiya kiyakuri ki yafemin kuyafemin dukanku gabaki daya Haji…….” Sai kawai kuka ya kufcemata Hajiya tai shiru tazuba mata idanu dukta lalace kaman ba Hadiza ba, tabama Hajiya tausayi dan she’s a mother babu abinda kecin mutum kaman guilt din yama wasu laifi basu yafemai ba dan gyaran murya tayi anatse dan ba kwana kwana tace “stop crying Hadiza ya isa Allah ya yafemana Hadiza gabaki daya wlh har raina nayafe miki, su Aisha baki musu komi ba wayan nan, Nura ma inamai tabbatar miki shima ya yafemiki” Hajiya tadanyi shiru tana kallonta har ranta din tayafemata tace “amman Hadiza bazan miki karyaba banma d’ana sha’awan aurenki har abada!” Dasauri Hadiza yadago rinannyn idanunta tana kallon Hajiya data gyadamata kai tace “Mun yafe miki kuma bamu rikeki araiba, an riga an zama daya yanzu Hadiza kin haifamana yara so har lahira ana tare, amman dai babu zancen aure tsakaninki da d’ana yanda kikeson Aman da Amal yanda kikasan darajan su ki kasan zafin haihuwansu haka nasan na nawa dan, koda kin chanza hali Hadiza wasu tabon basa goguwa dan haka kitashi kije amman idan zancen yafiyane wlh tallahi mun yafemiki, yaranki kuma idan sukai Hutu zaa dinga kawo miki su idan kinason ki gansu call me ko wani cikinmu za’a kawo miki su” hade hannayenta Hadiza tayi dagudu zuciyanta har mata yakeyi kaman zai katse tazo gaban Hajiya tana kuka sosai tace “Hajiya ki rufamin asiri, Hajiya Nura kadai nakeso arayuwana dashi kadai zan iya zaman aure” Dasauri Hajiya tace “d’ana yahakura dake Hadiza, please mubar maganan nan tashi kitafi akwai mutane a tsakar gidan nan kar aji muryanshi a shigo adauka wani abune tashi kitafi” Hajiya tai maganan tana dafa kujera tana yunkurin tashi kama kafan Hajiya Hadiza tayi tace “Hajiya kiji tausayina ki kalleni amatsayin yarki” Dasauri Hajiya ta nuna Hadiza da hannu tace “kul! Karki sake ki kwatanta yarana dake sabida nabasu tarbiyan da sunsan banbancin matsayin namiji da mace! Kap yarana mata mazajensu ne jagororin su! Yarana bazasu taba yima mazajensu kazafi ba har abada wlh inaaaa! Basasu taba yima masajensu tabon dahar abada bazai bar sunan su ba! You have no idea kotun da shairin dakikama Nura yayi affecting nashi da business nashi kinsan investors nawa ya rasa? Sakenmini kafa!” Hajiya tamata tsawa dan batason tuna abubuwan da Nura yagayamata ya sameshi daya koma Abuja kwanakin baya, ahankali Hadiza tasaki kadan Hajiya idanunta sunyi jazur Hajiya tace “wallahi na yafe miki Hadiza kinji namiki rantsuwa hakama Nura ai ko darajan yaranki yakai mu yafemiki amman I will tell you this to your face dan bazan miki karyaba ko in yaudareki ko amafarki, ko amafarki Hadiza banama d’ana kwadayin ki kuma, sai anjima” Hajiya tawuce dakinta ahankali tareda maido kofa tarufe.
Hadiza tai kuka tai kuka awajen na. Harta godema Allah takai almost 30min sannan ta tashi da kyar tawuce ta tafi bata damu da mutanen dake tsakar gidan ba haka tawuce, Hajiya tadade gaban dakin tanajin kukan Hadiza dake tabata kafin ahankali takoma bakin gado ta zauna tai shiru saida taji tafiyan Hadizan sannan tasauke ijiyan zuciya wayanta tadauka ahankali tai dialing number Nura.

Ringing daya ya katse yakirata back ya gaidata cikin tattausan muryan irin conversation na d’a da mahaifiyarsa Hajiya tace “yanzu Hadiza tabar gidan nan” dan shiru Nura yayi baice komiba, ahankali Hajiya tace “tazo tabani hakuri kan komi dayafaru tama kira su Aisha wai tabasu hakuri amman duk basu dauka ba, Nura duk ta lalace” “umm” was the only thing daya fito daga bakin Nura dan shiru Hajiya tayi sai chan tace “Son I know nidakai we had this conversation before, nasan abubuwan da Hadiza tamaka hurt me deeply, and I support you dakace bazaka kara zaman aure da ita ba but I looked into her eyes today Nura I saw sincere nadama, wlh danasani ne cike tap a idanunta, koda naji haushi ina fushi da ita the decision is still yours Nura, kanason Hadiza ko baka sonta yanzu tell me the truth Nurudeen” dan shiru Nura yayi tareda lumshe idanunshi ya jinginar da kanshi jikin kujeran office din, kaman bazaiyi magana ba ahankali yace “I will always love Hadiza Hajiya, but har cikin raina nahakura da ita kaman yanda na fadamiki ranan, nabude new chapter in my life, na yafemata, I’ve moved on, bazan iya cigaba da zama da itaba anytime na kalleta I will remember itane the first person data taba zagina kala kala aduniya, the first matan data chakumeni, tamin kazafi tamin kotu, akwai somethings aduniya dahar kamutu kanaso but u will never get them sabida wasu dalilai I think Hadiza is just one, Hajiya inason Hadiza sabida bani nadaurama kaina son ba Allah ne shi kadai zai iya cire mini, but nahakura da ita har abada, please Hajiya kada ki karamin maganan ta”
Ijiyan zuciya Hajiya tasauke tace “shikenan Nura, remember this kome kakeso I will always support you, all I want is inganka living peacefully and happily” anatse yace “Ummi is giving me that Hajiya, Ummi is the biggest gift in my life, yarinyar nan is just God sent, Hajiya she loves me unconditionally, duk abinda nakeso itama tanaso, she loves my children, zan biyamana aikin hajjin bana ma dukanmu mutafi harda ke Hajiya” murmushi tayi tace “Allah ya amsa, Allah yakaimu lokacin, Allah yabata yara itama” ahankali Nura yace “Ameen” cikeda so Hajiya tace “cigaba da aikin ka bari nadan kwanta” sallama sukayi daidai wayan Nuran na ringing yaga Baby dasauri ya dauka muryan Ummi yaji tana magana da kyar tana numfashi kaman wacce take kokawa tai numfashin da kyar tace “Da…….dyn Amal……” dip yaji shiru ga wayan na connecting dasauri ya mike yana “Baby, Ummi, Ummi” key mota kawai yadauka dasauri yashiga kiranta but ba’a dagawa 15mij yakaishi gidanshi yatafi side din Ummi aguje, yana bude kofa wani kamshin turaren wuta ya daki hancinshi, falon fess fess an gyara, sama yawuce yabude dakinta bata ciki shima agyare dakinshi yawuce kwance yaganta akan tile ga mop ga roban mop dudda ba ruwa akasa amman kaman zamiyewa tayi tafadi, tana nishi da kyar a sandare, dawani kalan gudu yayi wajen yadagota kadan kadan idanunta ke budewa arude yace “Ummi, what happen to you my baby?” Kallonshi takeyi but takasa magana sai hawaye dake bin gefen idanunta arude yashiga duddubata ganin kafafunta basa moving harta yatsunta ma, kawai ta sassandare kaman ice block yasa yaji gabanshi yadan fadi sai kawai yadauketa da sauri yakai mota yaja sai hospital aka shiga da ita ciki kusan 1hr yayi zaune Dr yafito suka wuce office nashi, Dr yabama Nura hannu yace “let’s start da good news your wife is 3month pregnant” dasauri Nura ya kalli Dr jikinshi har rawa rawa yake da mugun mugun mamaki yace “Dr wasa kakemin ne ko da gaske kake Ummi is pregnant”? Dr ya gyadamai kai yana murmushi hannu biyu Nura yadaura kan fuskanshi yace “Alhamdulillah, Alhamdulilah, Ya Allah thank you, Ya Allah nagode maka” he is seriously happy kaman zaiyi kuka, chan ya kalli Dr dake kallonshi yace “what’s the bad news Dr”? yayi maganan gabanshi na faduwa dum dum dum, ijiyan zuciya Dr yasauke yace “matarka is suffering from a very very rare disease, though bansan past medical history nata ba kota taba haihuwa” dasauri Nura yace “ta tabayi sort of sha she lost the baby at 6month hartai fama da yoyon fitsari” Dr yace “wow this information will go a long way it will help with investigation din dazamu mata” Dasauri Nura kirjinshi na dukan uku uku yace “to what’s wrong with my wife Dr? Lafiyanta kalau fa natafi office kaman faduwa tayi tana moping” ahankali Dr yace “I don’t think faduwa tayi datana moping, I mean she slipped and fall due to the watery ground I don’t think that’s the case here, your wife is suffering from HYPOKALEMIC PARALYSIS!” Wani kalan mikewa tsaye Nura yayi the only abinda ya gane a kalman is paralysis wato paralyze shiba science student bane amman kawai jikinshi saiyahau rawa kaman ba namiji ba da sauri Dr yatashi tareda kamashi yace “Alhaji Nura calm down is not abinda kake tunani zauna dan Allah calm down” idan kaga idanun Nura zaka tsorata yace “tell me Dr meya sami Ummi banni kawai ahakan am fine, tell me” yafadi maganan a hargitse, ahankali Dr yace “hypokalemic paralysis during pregnancy condition ne da bai cıka kama mata masu ciki ba, ba lallai nata yazama genetic ba sabida ciki yakawo mata halan, saimun gama investigation zamuyi ruling out”

but amman condition din dake sanya numbness, weakness na muscles, nata akafane yanzu haka two legs dinta are paralyze which zamu fara treatment immediately once result are out, yawancin abinda ke jawowa mata masu ciki condition din nan is low pottasuim level, paralysis ba abu mai kyau bane gabaki dayanta wajen mai ciki, so just pray for her to get through this inba hakaba gabaki dayan 9month pregnancy dinnan a wheelchair zata yishi dan she will not be able to use her legs, sabida ko zatai amfani da kafan maybe tafara tafiya bazatasan lokacin da kawai kafafun zasuyi sanyi su daina aiki ba, hopefully bazaiyi spreading zuwa hannuwanta ba for now she can’t feel her legs, maybe kuma ciwon is related to abinda yasameta a first child nata so contact the hospital din dasukai managing nata lokacin su bamu medical history nata, it will help alot sabida musan menene complications datai having a first pregnancy dinta” baya Nura yayi dasauri Dr ya tareshi, ijiyan zuciya yasauke yashiga tattaba kujera kaman makaho yazauna akai da nata ya buga tagumi, ahankali yace “agida ta haihu, magungunan datasha ma alokacin na gida ne bana hospital ba, ba’a kaita hospital ba alokacin, Dr kall…….” Nura yayi shiru idanunshi sun cika da hawaye saikuma yakai duka hannayenshi biyu yakama hannun Dr yace “Dr you see that woman Ummi, my Ummi” yanuna kanshi yace “she’s all I got, she takes care of me, my mother, my kids my entire family, Ummi is just like my back born” yayi shiruuu saikuma yasaki hannun Dr yaki hannayenshi kan idanunshi yace “bantaba ganin a selfless human like Ummi ba, her heart is filled with love, peace and harmony, she loves kowa da zuciya daya, she don’t have a Mom nor Dad, itane first born, tanada 2 sisters, her grandmother look up to her, her sisters look up to her, my kids look up to her, my Mom and even me, ko sauro banso ya ciji Ummi sabida mutumce ita mai kashemana sauro idan yazo zai cijemu, how can I be here ina kallon Ummi tana paralyze eh Doctor”? Nura yayi maganan yana zaro handky da sauri daga aljihun shi, yakai kan idanunshi dasauri ya goge yace “Dr please help me, I don’t know do everything, idanma akwai hospital that are specialize in managing condition nata ko a outside Nigeria ne am willing to take her there I can’t stand watching Ummi na in pains, I can’t!” Nura yayi maganan gwanin ban tausayi.💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣9️⃣

LABARIN FEMINIZM IS COMING TO AN END, CHAPTER2 IS AN ENTIRE DIFFERENT STORY ABOUT CHEATING🧡 KINDLY MAKE YOUR PAYMENT NA 1k and chat me up by clicking on this link;
wa.me/+2347012181461

You can make payment 1k here 👇🏼

3107021073 Aisha Muhammad first bank
KO

6353995766 M Shakur world Moniepoint
Send evidence of payment I will add you to chapter 2 group.

Back to top button