Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 28-29

Sponsored Links

Page 2️⃣8️⃣&2️⃣9️⃣
Khadija ce a zube a kasa cikin ruwan cab’alin rijiya,salame na ruwan cikin ta,ta hakikance sai jibganta take

Sake hannun yayan khadija nayi Da wani irin gudu nayi Kan salame,don na fahimci Yan gidan nan in har baka koma irinsu ba zasu kasheka,yarinya sa’ar khadija Amma khadija ta sake jiki tana dukanta Koh martani Bata mayarwa sai k’okarin Kare kanta,kafun na Isa ba zatoh ba tsammani sai kawai Naga Iro ya kwashe salame da kafa daga Kan khadija yayi ball da ita sai da ta zube a Gefen rijiya bakin ta ya sare simintin rijiya,kafun kace me tuni ya rufe salame da duka sai a lokacin Yan gidan suka firfito,Abu kamar Wasa fad’a ya zama babba,don fadan yanzun Kam mutane sunkai biyar suke dambe,kama khadija nayi wance tunda Iro yayi ball da salame take gefe tana kuka duk jikinta sai rawa yake, “khadija tashi mu shiga kofata sannu”

Mikewa tayi a hankali,suka nufi kofar shashensu

Al’ameen Kam Yana tsaya Kamar andasa sa don baya gane kome tsabar yanda surutai da koke koke ke tashi a tsakar gidan,sai raba ido yake kawai

Muna zuwa saitin inda yake hannu kawai nasa na Kama NASA Muka shiga cikin kofar tare,
Sake hannunsa nayi,
Ruwa na iba na Kai Mata band’aki na Kama hannunta muka shiga, kanta na wanke Mata kafun na fita na barta tayi wanka
Kaya na makala Mata a jikin kofar band’akin,
Tana fitowa.

D’aki Muka shiga zaunar da ita nayi da sauri na d’auko D’an kwalina na d’aura Mata akanta dake ta zubar da jini”khadija meya hadaku meya faru?

Wallahih Aunty Ina fitowa kofarki kawai nazo wuce gindin rijiya,Daman salame na iban ruwa kawai ta kwashi kafafuna na zube shine tahau kaina tana dukana,kallifa Aunty ta fasamin Kai,ta fad’a tana Kara karfin kukanta

“Kiye Shuru khadija,share hawayen ki yanzun za’a bi Miki hakkinki wallahih in sunsan wata Basu San wata ba” nace Ina duba inda na aje wayata

In Raina dubune yau ya baci na gaji da bala’in Yan gidan nan da Talaucin da muke ciki zamuji Koh da tashin hankali’wayana na d’auka tunawa da nayi,da wani school mate nawa lokacin da na shiga jami’a shi Kuma Yana final year insa,yanzun police ne yana da babban mukami a hukuma, muna mutunci sosai kamar yan uwa danayi aure ne dai bamu sake magana dashi ba.

Me zakiye Sumayya? Al’ameen dake zaune a kujira yayi tagumi ya tambaye ta

“Mataki Zan d’auka”

Wani irin mataki?

Akwai Wanda Zan Kira wallahih Koh tantama banayi daga gidan nan direct sai prison Koh station bazata shiga ba Kuma sai naso za’a bada belin ta”.

Wa Zaki Kira?

“Wani friend Ina ne”

Toh wallahih ba’a gidan nan ba

“Ban gane ba’a gidan nan ba kenan kana nufin abarsu suci bulus kenan kaga yanda suka fasawa yarinya Kai kace a barsu”

Ina dai kanwata aka fasawa Kuma nace bana bukatar ki d’auki mataki

“Ok nuna mini kake khadija ba kanwata ba koh”fine shikenan gaka ga Yan gidan naku,Daman nice bare”nace Ina aje wayata na fita waje sosai maganar Al’ameen tamin zafi Wai kanwarsa Kuma yace baya bukatar mataki,watoh ba ruwana kenan a maganar

Al’ameen Kam harga Allah Bai Fad’a,don wani abuba kawai ya fad’ane don ta janye maganar rufe salame,baisan maganar zai Mata zafi harta fassarasa wani iri ba

Khadija Kam sosai taji Bata kyauta ba a sanadin ta ma’aurata sun samu sabani,mikewa tayi ta fita waje,
wajen da Sumayya ke zaune ta karasa

Aunty bara naje kasuwar

“Khadija Wai kina nufin kudin nan na hannunki”?
Ni na d’auka ma Koh kin yasar dashine tuntuni”

Ah ah Aunty Daman a bakin zanina na soke Kuma Allah ya taimakeni Bai fad’ ba

“Ok kibar zuwa cefenen”nace Ina karban kudin hannunta

Ah ah Aunty maganar Yan lallen fa,don Allah Aunty karki fasa lallen nan,Akan abinda ya faru.

“Ah ah khadija rike 1k innan kije chemist a Miki dressed in wajen Naga har yanzun jini Bai tsaya ba”

Toh Aunty na gode tace tana mikewa zata fita

Khadija tsaya muje na rakaki, Sumayya ki kawo cefenen Inna rakata chemist sai na wuce kasuwar, Al’ameen yace

Kala bance Masa ba don haushin sa nakeji sosai,hakurin sa yayi yawa shiyasa ake cutar sa kullum

Aunty Yaya na magana Wai zaije kasuwan,

“Ka barshi kawai gobe Zan aiki Yan lallen suje kasuwa su sai mini abin hadin”

Toh Aunty ki basa kudin cefenen sai ya sayo muku,ya iyya zuwa kasuwa, khadija tace cikin rashin Jin Dadi ganin yanda na Had’awa yayanta fuska

“Ungo”na Mika Masa 6k

Matsowa yayi Yana lalube ya karbi kudin a hannuna

Me da me Zan Saya?

“Ka tamabaye khadija na Mata lissafi ”

Ok yace cikin sanyin jiki don wallahih Bai d’auka maganar zatayi zafi haka ba

Suna kokarin fita Asma’u na shigowa da kawayen ta,suka gaisa da Al’ameen kafun suka shigo,khadija kuma suka fita

Shimfid’a musu darduma nayi,suka zazzauna

Tashi nayi naje na chanja kaya,na manna Gam a faranti,na kwaba lalle,Muka fara

Khadija ta dawo lokacin kusan karfe 10
“khadija ki shige d’aki kije ki kwanta Naga an kawo NEPA ki huta kinji”nace Mata Ina kallon kanta da aka mannawa plaster

Toh Aunty tace tana shigewa d’akin, kwanciya tayi a kujira,banci ya d’auke ta

Al’ameen Kam kasuwa ya wuce yaje yayi sayayan kayan abinci,Amma Sam yau Baya cikin walwala tunda suka D’an samu sabani da Sumayya,don shi Sam bayason yayi abinda zai bawa wani haushi harya kullace sa abin damunsa yake

Yan matan sunata Hira,inama Amarya lalle,saiga Al’ameen ya dawo da laidodi a hannunsa na sayayyan kasuwa,mikewa nayi na karbi laidan gudun kar na tozartashi a gaban su,kitchen na shiga da laidodin shima bayana yabi

Yan Mata Kam sai ido suke bin MAKAHO da MATARSA suna mamaki

Muna shiga kitchen in,na aje laidodin

Sumayya Naga Yan sana’ar sunzo Koh Zaki kawo na girka Mana abincin? in yaso

“Kai bazaka fita bane”?

Zan fita Amma sai bayan azahar

“Toh ka iyya girkine? koh da wani idon zaka girka Mana abinci muci”?

Eh na iyya girki,sai ki jera mini Abubuwan da Zan girka Zan iyya

“Bana bukata”nace Ina Shirin fita

Jin Amsar da ta Bashi ya tabbatar har yanzun haushi takeji,hannu yasa a hankali ya rikota Jin zata fita a kitchen in

“Ka sakeni”nace ba Wasa a muryata

Sumayya kiye hakuri in abinda na fada Bai Miki Dadi ba

“Ka sakeni nace maka”

Am sorry

“Ka sakeni”

Baki hakura ba?

“Ka sakeni”

Toh innaki fa,ba Matata na rike ba

“Matar ka ai da Ina da wannan matsayin da gaske da bazaka nuna mini banda matsayi agun khadija ba”

Amma ba nace kiye hakuri ba,yace Yana jawota jikinsa

“Nima ai bance maka naji haushi ba”

Amma gashe sai fushi kike

Haka dai Kai kake gani,nikam sakeni Rana yayi bamu karasa lalle ba

Bana gani sai dai ji

“Oho maka dai”

Mana dai,ba ni kadai ba

“Toh sakeni Mana”,nace Ina banbare jikina a nasa

Sumayya abinda yasa Kika ga naki ki d’auki mataki,da hukuma toh a gidan nan Babu Mai tsoron station Koh prison don ba bako bane agunsu, bare ya saka musu tsoro don kinsa an rufe salame,wata fitinar kika kunna,zaman gidan nan sai ya gagare mu

“Kai kake tsoron fitina bani ba’ akan gaskiya na Koh Ina zanje”

In Miki girkin?yace Yana kauda maganar

“Ka bare Zan girka”

Toh shikinan,yace Yana saketa,

Tsayawa nayi ya rigani fita a kitchen in,
Ya Kama hanyar kofar fita a shashen mu

Nima fita nayi,”am please bara na d’aura Abinci, Rana yayi sai nazo mu karasa”

Aunty bara na d’aura miki,wata Yan Mata a cikinsu tace

“Ah ah ki bare kawai”nace Ina tunanin karfa Bata iyya girki ba ta Bata mini kaji a banza

Kai Aunty Koh dai kina tunanin ban iyya girki bane?

Ba haka bane,Daman Ina tunanin karna takura Miki ne,Amma tunda kina sonyi shikenan,ki tuka semo laida babban duka,

Kitchen ta shiga
ni Kuma d’aki na shiga naje na leka khadija har lokacin bacci take

Sai azahar na kammala lallen Amarya,na tashe khadija mukayi sallah abincin da farida kawai Amarya ta girka na zubawa yayan Khadija nasa, na zuba na Daren mu, sauran na zuba ma kawayen, na ibawa Amarya na zuba Mana da khadija,sosai Tuwon yayi Dadi,bamu Gama ciba aka turo yara da kulolin Abinci daga gidansu Amarya shinkafa muka dad’a,
yaran na baiwa na yayan Khadija su Kai masa

Ganin da sauran lokaci yasa nama farida lalle (wance tamin girki)

Sai la’asar Asma’u tayi wanka sosai na zuba Mata light make-up tayi kyau Kamar me,ganin kawayen nata d’aukar ta hoto yasa Nima na fitar da wayata,na d’ad’auki hotonan lallen ta da kwalliyar da na Mata duk da hoto nason gida Mai kyau Amma wanka na gyara hoto ma ba gida kawai ba

************
Bayan tafiyar Amarya da kawayen ta, wanke wanke nayi na share kofar don yayi kaca kace,kowa yasan gidan Mai lalle in ta Tara customers,yanda yake baci

Wanka nayi,donna gaji sosai yau innan,vest nasa na d’aura zani don ba kowa a kofar nawa khadija ma ta tafi gida,don yau ba zuwa program Kai ya fashe

Bayan sallar mangariba ya dawo Kamar kullum wanka yayi mukaci Tuwon da farida ta dafa Mana da rana

Bayan sallan isha’i yau Koh jiran ya dawo masallaci banyi ba na kwanta don gabaki d’aya bacci nakeji ba kad’an ba ga gajiya sosai.

Yana dawowa ya tarar tayi bacci shima gadon ya hau don tabbas yau yasan ta gaji,tabata yayi yaji alamun bacci take,a hankali ya cire mata vest in jikinta daga ita sai wandon bacci,shima kayansa ya cire dagashi sai guntun wando a hankali ya rumgumeta,kome a hankali yake gudun karya ta tashi,sosai yaji wani irin yanayi Mai matukar shauki a tare dashe,amam haka yake dannewa,har bacci ya dauke sa

Misalin karfe 3 na asuba kamar a mafarki naji ana tattaba min kirji da sauri na bude ido,tashi nayi na zauna jina ba riga,sake taba jikina nayi don na tabbatar Aiko da gasken bani da riga,

“Wai meyasa kwana biyun nan ka chanja ne kanamin abinda ranka yake so”?

Mutum da halaliyarsa, ya Bata Amsa Kamar Wanda tama Dole

“Ka tashi mini a wajen kwanciya”

Ina kenan?

“Gado”

Naki, gaskiya yanzun bazanna kwana ni kadai ba alhalin Ina da mata.

“Don Allah nikam ka tashi, kaga yanzun ma Banga rigata ba ga d’akin duhu”

Saiki kwana haka

“Akan wani dalili Zan kwana ba riga,Kuma karka sake ciremin riga in Ina bacci banaso”

Inna cire fa?

“Au tamabaya ma kake sai me?

Eh tambaya nayi

“ka Dameni sai surutu kake sani tsakar dare”

Wani dare ai na yau ya wuce sai dai na gobe

“Ka tashi nace”

Naki

“sauka zanyi na bar maka d’akin ma in baka sauka ba”

Toh na hanaki ne

Mikewa nayi na sauka akan gadon nayi hanyar kofa Koh riga ban dashi,

Ba riga Zaki fita waje?

“Ai baka fini ido ba”nace Ina kokarin bude d’aki, kawai ji nayi y………..

*Aye manage in page bani da charge*

 

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

🍀 *Na tsunguno(habil)*
🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

Contact them vie
🪀08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
free book 🤧

Back to top button