Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 84-85

Sponsored Links

Page8⃣4⃣&8⃣5⃣
Mikewa Sukayi da sauri suka nufi kofar gidan, ba tare da wani tsoro ba suka zare sakatar, me zasu gani?bawan Allah nan ne aka d’ago rababe-rababe kamar kayan wanki, cikin hanzari suka bawa mutane biyu da suka d’agosa hanya suka shigo dashi cikin gidan, direct d’aki suka nufa dashi suka kwantar.

Al’ameen dake binsu a bayane ya tambaye su meya faru dashi?

Wani a cikin sune yake tsanar dashi wai ashe faduwa mutumin yayi a gidan da yake aiki, kafarsa ya karye shine aka kaisa asibiti aka d’aure kafar, amma yaki zaman asibiti wai sai dai a dawo dashi gida yayi jinya.

Allah ya kiyaye na gaba Su Al’ameen sukace suna komawa d’akin mutumin.

Kallon kafar da aka d’aure muhammad yayi, Sannu baba Allah ya kiyaye na gaba?

Amsa masa yayi da, Ameen Al’ameen.

Sannu baba, gidado da badaru sukace a tare, Amsa musu yayi a hankali, tashi Al’ameen yayi ya fita a d’akin, murhun inda ya gani na karfe d’an karami ga gaushi a ciki, nitsuwa yayi ya hura wutan ya d’aura butan shayi, atakaice dai shayi ya had’a a cikin butan ya had’a da kofi ya kaima mutumin, ba musu mutumin yasha kad’an, Al’ameen ya sake fita ya d’aura ruwan zafi, yana dumi ya d’auko a roba ya had’a da tsumma yazo ya gogewa mutumin jiki, ya shanja masa kaya, sosai mutumin yaji dadi yayita sama Muhammad Albarka.

Da dadare ma su gidado sun koma dakin su, yayinda Al’ameen ya kwanta da mutumin a d’akinsa tare, tsakar dare mutumin ya farka da taimakon muhammad yayi fitsari ya sake dawo dashi ya kwantar, a hankali mutumin ya kalli muhammad sai kuma ya bude baki ya fara magana, Allah ya dubi halinda zan shiga ya aiko mini ku muhammad, da ace yau babuku a gidan nan bansan halinda zan tsinci kaina ba, bani da kowa gashi ba Aure nake dashi ba bare yara.

Babu kome Baba fatan mudai Allah ya baka lafiya.

Ameen muhammad, Akwai wani taimako da nakeso kamin, in babu damuwa d’an nan?

Ba kome baba indai har baifi karfina ba, kuma bai sab’awa shariya ba, zan maka kome da kake bukata, kayi mana kome baba tunda ka bamu matsuguni a gidan ka.

Muhammad a gidan da nake aiki tsawon shekararu a gidan, tun lokacin da mahaifina ke aikin a matsayin da nake yau, ina binsa muje tare har Allah ya d’auki Ransa, ni na cigaba da aikin kamar shi, a yanzun bani da kowa ba uwa ba uba ba yara ni kad’a nake rayuwa ta a gidan nan, sai yanzun da Allah ya turo mini ku, in ba damuwa so nake muhammad kaje a matsayina, kaci gaba da aikin da nake har Allah yasa na samu Lafiya, kaga bazanso ace aikin da nake tsawon shekaru, yau a samu wani ya karbe mini ba, tunda ciwon bana kwana biyu koh uku na warke bane?sai nayi jinya mai tsawo.

Shuru muhammad yayi na d’an wani lokaci kafun yace, ba kome baba zanje nayi aikin har Allah ya baka lafiya, Amma wani irin aikine don ni baba banyi karatu mai zurfi ba?

Murmushin karfin hali mutumin yayi, bafa aikin da ya shafi ilimi bane, aikin gidan sarauta ne, kuma nine sarkin shayi na gidan.

Muhammad ne ya kalle sa da mamaki, Gidan sarauta kuma baba?

Eh d’an nan zakaje ka zauna a matsayina tun jiya na sanar dasu zaka fara zuwa aiki gobe.

Aini baba ban iyya dafa shayi irin naku ba, kadai ga yanda na had’a shayin d’azun baiyi irin wanda ka had’a mana ba.

Karka damu muhammad akwai wa’inda zan turaka wajen su, ‘yan gida nane suna taimaka mini wajen raraba shayi a gidan, Na sarki ne kawai nake kaiwa da kaina, kaima yanzun kaine zakana kai masa,sannan shayi kala uku ake, akwai na sarki shinasa dabanne, akwai na family akwai na bayi.

Baba anya zan iyya aikin nan kuwa, gidan sarauta fa kace?

Zaka iyya muhammad ka taimaka kaje kaji?

Shikenan Allah ya kaimu goben lafiya, Amma baba wazai nuna mini gidan, don ni bako ne , bansan ina ne gidan sarkin garin nan ba?

Karka damu muhammad akwai yaron makwantan mu gobe zan turaka gidan su saiya kaika.

Shuru muhammad yayi ya kwanta, Amma ya kasa bacci haka kawai yaji yana fargaban zuwa gidan kodon bai taba zuwa bane oho.

Washe gari muhammad ne yayi wa mutumin Alwala da ruwan zafi ya saita sa gabas, sukuma suka wuce masallaci.

Bayan sun dawo kamar jiya suka kimtsa gidan yau harda karyawa suka had’a mai kyau, bayan muhammad yayi wanka, baba kaya ya sakasa ya d’auka irin na buzaye, wando kato da rigansa mai aiki a gaba sai rawanin su, muhammad kasa nad’a rawanin yayi, Amma haka mutumin nan a bashi da lafiya saida ya nad’awa muhammad, rufe masa fuska yayi da rawanin babu abinda ake gani a fuskar sa sai kwayar idanunsa, sosai Al’ameen yayi mamaki harya kasa hakuri yayi magana, baba basai an rufe fuskar duka ba?

Ah ah muhammad ina son koh kaje gidan karka bude fuskar ka, ka barsa a haka, kuma kayi taka tsamtsam da kowa na gidan, karka yarda da kowa kayi abinda ya kaika ka dawo, ga wannan in kaje get sai kanuna, kafun a barka ka wuce ciki.

Karba muhammad yayi yana karanta abinda baba ya basa, get pass ne d’auke da rubutun larabci, a jiki saidai bai gane me aka rubuta ba, kasancewa yare aka rubuta da harufan Larabci sai hoton zaki a bayan get pass in, Muhammad fita yayi bayan yama su gidado bayanin inda zashi, sosai suke da Zuzuta karbar da kayan ta masa kamar buzun gaske, bayan ya fita a gidan, gidan makwancin su ya wuce ya masa bayani kamar yanda baban yace masa, had’asa da yaron sa mutumin yayi, ya rakasa gidan da baba ke aiki.

Tunda suka sauko a machine yakejin wani irin masifeffen bugun zuciya, ga wani irin fargaba dake cikin ransa ya rasa dalilin da yasa? ya tsinci kansa da tsoron zuwa gidan, tun daga nesa ya hango wani irin gini mai d’aukar hankali gini ne irin dogin nan masu masifar tsaho, ga wani fankamemen get fari mai d’auke da hoton zaki babba a jiki, gidane na Alfarma koh ince unguwa guda tun daga nesa zaka tambatar gidane na sarauta, masuji da mulki,yanda suke matsowa gidan haka bugun zuciyar Al’ameen ke kara yawaita, karasowa sukayi bakin get in, masu tsarone sanye da bakaken kaya hannunsu d’auke da manya manyan bindigogi cikin tsawa d’aya daga cikin su ya dakawa su muhammad da karfi cikin yare yake musu magana.

Daskarewa muhammad yayi jin yanda mutumin ya hayayyako musu kamar zaicisu d’anye, gashi sai yare yake shikuma baji yake ba, Allah yasa yaron da suka zo tare yana gun shiya musu bayanin zuwansu cikin yare tare da sanar dasu muhammad d’an uwan Sarkin shayi ne, zaizo ya karbe sa daidai yaji sauki.

Basu barsu sun shiga ba har saida Al’ameen ya nuna musu get pass da baba ya basa kafun suka barsu suka shiga ciki, mutuwar tsaye muhammad yayi lokacin da idanunsa suka sauka a compound na gidan, duniyace babba gida mai matukar girma, a haka suke taka tsakar gidan daidai sun iso tsakiyar gidan muhammad yaga gunkin zaki babba mai matukar girman gaske, An kawatashi a tsakar gidan a zaune kamar mai rai, wucewa wani shashe sukayi da yaron sai gasu a wani kayatancen falo mai masifar kyau da d’aukar hankali, kujerune na Alfarma a cikin su, zarce wa sukayi cikin wani kofa dake gefen falon, shidai muhammad idone nasa yake bin koh ina da kallo, har suka shiga cikin d’akin, wow shine abinda ya fitoh a bakin sa ganin wani irin kitcheen na Alfarma mai dauke da kayan Alatu na zamani, sai samari guda biyu dake kitchen in a tsaye suna aiki,jin motsen su muhammad da sallamar suce yasasu juyowa.

Amsa sallamar sukayi, bayan sun gaisa da yaron yake musu bayanin Al’ameen ne zai karbi, sarkin shayi harya warke, sannan sarkin shayi yace su koya masa had’a shayi, sannan shi zaina kaiwa sarki shayi kullum, duk da yare yaron ke musu bayani.

Muhammad kamfa ya shiga tsaka mai wuya don shi dai ba yare yake jiba, tayaya zai iyya zama da wa’innan mutane wai daman babu hausawa ne a nijar koh dai wannan garine baida hausawan oho?kuma gashi baba ya iyya hausa?

Yaron ne yajuya zai fita a kitchen in da sauri muhamamd ya bisa a baya, da mamaki yaron ya juyo ya kalli muhammad cikin mamaki yake tambayar sa yaya kuma zaina binsa?

Gaskiya nifa ban gane ba kowa a gidan nan sai yare yake mini, nifa baji nake ba.

Dariya yaron yayi karka damu kaji, wasu a cikin su suna ji sai dai in an ganka za’ayi tunanin koh kanajin yarene shiyasa wasu ke maka yare, Amma in suka maka magana kana musu hausa kaji zasu maka suma.

Toh nagode kawai muhammad yace, ya koma kitchen in, sosai suka sakasa aiki goge kofuna d’aura shayi saka wanshan ganye ah ah yi kaza sai kusan azahar, bayan sunyi sallah aka fara rabon shayi a gidan, shima wasu kofuna da buta na Alfarma masu shegen kyau da sheki ruwan Gold suka zuba shayin a butan, aka jera a karamin tire da shukali sai bolw na zuma, shima Golden colour da shukali biyu, mikama Al’ameen sukayi Hade da had’asa da wani a cikin ma’aikatan ya nuna masa flat na sarki.

Duk abinda Al’ameen kiyi tsananin bugun zuciyar sa nayi, har wa yanzun da suke nufar sashen sarki, hannunsa d’auke da tiren kayan shayin, suna isa kofar shiga falon, ma’aikacin ya koma ya bar muhammad tare da nuna masa kofar da hannu alamu dai nan zai shiga, yafi minutes 2 yana tsaye ya kasa shiga zuciyarsa na matukar buga wa da sauri-sauri, ganin wani bawa zai wuce yasa muhamamd saurin sa hannu ya murd’a kofar falon bakinsa d’auke da sallama, Amma bai shiga ciki ba a bakin kofar ya tsaya.

Amsa masa sallamar akayi saiga wata mata ta fitoh, sanye da kayan da bayin gidan ke sanyawa, hade da masa iso zuwa cikin falon, shigowa Al’ameen yayi yana bin bayanta har suka karaso cikin falon, falone babba mai girman gaske da kawatuwa irin falon nan na sarakuna, masu ji da lokacin su, wuce falon sukayi suka nufi wani kofa daban, nan ma falone Amma baikai wanda suka wuce girma ba Da kayatuwa, kara nausawa sukayi cikin wani kofar, saigasu a wajen shakatawa mai d’auke da shuke shuke na flowers mai ban sha’awa da kamshi, jefa kafa kawai muhammad yake don yayi matukar gajiya da tafiyar nan, da yake daman bai gama sauke gudun hijiran da sukayi ba, ga matsanan cin bugun zuciyrsa kiyi da karfi, lokacin da idanunsa suka sauka akan mutanen dake zaune su biyu cikin shiga na Alfarma wanda koh ba’a fad’a ba kasan sarkine tare da matarsa dake sanye da Alkimba mai masifar kyau da d’aukar ido, farace tas kyakkyawa da ita, yayinda sarkin ke sanye da rawanin buzaye a kansa ya rufe fuskar sa luf banda idanunsa babu abinda mutun zai hanga don koh kafar sa da hannunsa boye yake a cikin suturansa, shuru sarauniyar tayi ganin su Al’ameen da Alamu dai magana take da mijinta Da sallama a bakin su Al’ameen suka karaso inda suke, da sauri sarkin ya dafe daidai saitin zuciyarsa yana Ambatun sunan Allah a zuciyar sa, yayin da muhamamd suka tsunguna a kan gwuwuwinsu A hankali ya d’aura tiren akan table inda ke gabansu, hannunsa sai rawa yake wanda baisan dalilin hakan ba, tsiyaye shayin ya fara a kofi yana had’awa da zuma.

Sarauniya ita ta kula da halin da mijin ta ke ciki da sauri ta matso garesa Ranka ya dade lafiya meke faruwa zuciyar ce?

Shuru ya mata, itama bata damu ba don tasan halin mijin ta zata masa magana sau dubu ba Samun Amsa zatayi ba, yasha yarfata a gaban bayinta Amma tun yana damunta yanzun koh a jikinta, kara tambayar sa tayi zuciyar sa na ciwo ne?

Girgiza mata kai kawai yayi baiyi magana ba, jingina yayi da jikin kujeran da yake zaune akai ya lumshe ido yana maimaita innalilahi…..

Al’ameen na gama had’a shayin ya mike abinsa ya fita a lambun, sai a lokacin sarkin ya zare hannunsa daga kan kirjinsa yayinda idanunsa sunyi matukar kaduwa zuwa ja, sosai jikinsa ke rawa, ganin hakan yasa sarauniya mikewa da sauri ta fita a lambun ba’a jima ba saiga ta, ta dawo da wata tsohowar mata cikin shiga ta Alfarma kyakkyawa da ita fara, ta karaso garesa hannunta d’auke da magani, da saurin ta balla hade da karban kofin ruwan dake hannun sarauniya ta kafa masa a baki, ba musu ya karba yasha maganin, ka tashi ka koma ciki kaji?tsohowar tace

Girgiza mata kai kawai yayi vaiyi magana ba, Alamu dai yafison zaman nan in, ba musu daga matar tasa, har tsohowar suka basa waje don haka yake indai ta shine yafi kaunar a basa waje ya zauna shi kad’ai sau dubu akan ya zauna da mutane.

Al’ameen kam yana komawa kitchen in abinci aka kawo musu na rana, mai rai da lafiya harda kaji sukaci, zama sukayi a falon da kitchen in ke cikinsa suka kwanta a kan kujerun dake wajen alamu dai daman falon donsu akama,(ma’aikatan shayi) sai la’asar suka sake dafa sabon shaye wannan karon Al’ameen ne ya d’auka shi kad’an sa, ba tare da rakiyar jakadiya ba ya shigo falon, yarane zaune a tsakar falo su uku, biyu suna zaune a kasan cafet dake shimfid’e a tsakiyar falon, suna rubutu a takarda dukansu mata ne d’ayan zata kai shekara goma sha biyar, d’ayan kuma zata kai shekara Goma, Lokacin da yaran suka d’ago suka kallesa baisan lokacin da tiren shayin dake hannun sa ya tsubuce a hannunsa ba, a take kome ya tarwatse a wajen, suma yaran zare ido sukayi ganin barnan da muhammad ya musu a falo, d’aya yarinya ta ukun dake zaune akan kujera tana danna waya bazata wuce shekara 20 ba, ta mike cikin masifa da izza, kai wani irin wawane koh ince dolo kana da hankali kuwa zaka shigo mana falo kazo ka zubar da abu, sannan ka tsaya kana kallon mu, jira kake mu kwashe maka koh me?

Habba Nabila baikamata kima mutum babba kamar wannan irin zagin nan va, baikama taba gaskiya ki gyara halinki, d’aya daga cikin yaran da ke zaune a kasan cafet in tace ma nabilar.

Kinga muhibbat babu ruwan ki dani ki daina mini irin wannan abin da kike mini, niba sa’arki bace Amma na fahimci kina mini shishigi a lamurana be careful, takarasa maganar da barin falon tana hararan sa.

Muhibbat ce ta kallesa kaga malam tattara abinda ka fasan nan ka tafi store a baka wasu kayi sauri ka kawowa Abba shayi?duk da Turanci suke magana.

Muhammad kam mutuwar tsaye yayi yana kallon yarinyar, koh dai mafarki yake ne yarinyar kamar khadijar sa haka yake jin muryar ta, yanda khadija ke magana ba R haka ita ke magana, kaman ninta kome nata yana masa irin na yar uwarsa,duk da khadija na yarinya ya makance amma hakan bazai hanasa gane taba, a gaskiya abinnan ya basa mamaki matuka da kuma tsoro gasu su biyu masu tsananin kama da juna, koh yace masu kama dasu, jin ta sake masa magana cikin yanayin mamaki ya tsunguna ya kwashe fashashun kofunan ya fita a falon da sauri.

*****************
Sumayya fa yanzun ci yafi nada ga bacci babu aikin da take yanzun kome khadija kiyi in taga aikin yama khadija yawa saita, sata ta musu take Away kawai, don khadija na kokari ga zuwa school har yamma take dawowa ga aikin gida ga masu kitso, amma Alhmdulilah baza’ace aikin mai yawa ba tunda sharane kawai sai girkin abinda zasuci don yanzun cin sumayya yafi nada gashi cikin yayi girma sosai ya kara hurata, jiki tayi bana wasa ba kafafunta haka suka cika tim,An hanata cin gishiri ma A hospital yanzun ganin irin huruwar da tayi.

Yau weekend babu school khadija ce zaune a baranda tana ma mutane kitso, yayinda wasu ke zazzaune suna jiran layi yazo kansu, sumayya ce ta fito cikin shiga ta Alfarma zanine less da hijab nata mai hannu medium size, sai jakan sakalawa a kafad’a da waya a hannunta sosai tayi kyau, hannu tasa ta maida kofar falon ta rufe, “khadija lailar ta fitoh ne”?

Ah ah Aunty bata fitoh ba koh na dubo miki itane?

“Ah ah khadija ki bari kawai bara naje flat natan sai mu wuce”

Toh Aunty saikun dawo

Tana sauka a kan barandan tace”Yauwa khadija”

au na manta me zan dafa ne na rana?

“Kibari kawai khadija naga yau akwai layin kitso sosai in muka shiga kasuwa zanbi restaurant nai mana take Away”

Ok toh Aunty adawo lafiya

“Allah yasa khadija”wucewa compound in gidan tayi ta nufi sashen laila, harta haura dakalin d’akin ta saigata ta fitoh cikin shirin fita, ah ah sumayya harkin shiryane?

“Bazan shirya ba laila so fa nake mu dawo kafun Azahar don wannan zafin ranan ba lafiya bane”

Gaskiya kam bare ku masu ciki.

“Kinga laila don Allah ki shige muje bana son yawan tsayuwar nan habba”

Yi hakuri hajiya muje, kawai laila tace suka kama hanya da sumayya.

Kasuwa laila da sumayya sukaje da taimakon laila sukayi sayayyan kayan baby, dana haihuwa kama daga baf gadon yara kayan sawa feda kome daya dangance baby da sumayya wanda zatayi Amfani dashi lokacin haihuwa da bayan haihuwa ita da babyn ta duk sumayya ta saya, kaya niki niki haka suka zuba a Texi, har sun shiga mota sumayya ta hangi mai mangoro, take tunanin mijin ta daya zamo mata jiki ya fado mata, sai kuma taji tanason sha, hakuri ta baiwa mai motar ta sauka, da sauri ta nufi wajen mai mongoron bata saurare maganar da laila kece mata ba,tana kokarin bude jakar hannunta, gabaki d’aya hankalin ta na kan jakan, bata koh ganin gabanta.

Ji kawai tayi an bangajeta da karfi tayi baya tagal tagal zata fadi…………🍀🍀

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

Back to top button