Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 32

Sponsored Links

BOOK 1 📕

Page 32💖

Sanye take cikin wasu baka’ken kaya ba’a ganin ko ina na fuskarta hatta kwayar idanuwanta ta kulle su da bakin glass,magana take da wani da shima ba a iya ganin fuskarsa cikin wani yare mara dadin ji, wata yar karamar leda ya mika mata ,cikin ta wani farin abune aciki,tana ganin abun da ya bata ta kyalkyale da dariya kafun ta soma magana “tabbas a wannan karan burin mu na daf da cika, tunda munyi nasarar juyawa yarinyar kwakwalwa,ta Hakane zamuyi anfani da ita muka she wancan tsinannan ,burinmu na cika sai mu dora mata lefi,tabbas wannan karan za a jubda Jini”,babbakewa da dariya mutumin yayi kafun ya soma magana,”tsawan shekaru na dauka ina jiran wannan lokacin, da dukiyar NAHYAN zata dawo hannuna,kina tunanin zanyi sake da wannan damar,basu kadai ba,duk Wanda yayi kokarin rutsemun ginin da na dade ina gidawa babu abunda zai hana muga bayinsa,kamar yadda muka ga bayan mohammad”lokaci d’aya suka babbake da dariya tare da zuya harshen su zuwa wani yare da baba ganewa.

🫧🫧🫧🫧🫧

Karfe 6:30am ya turo kofar dakin a hankali,tun futar dayi dazu be kara dawowa ba,a takure ya hangota kansaman gadon ta takure jikinta,ba a hango komai nata sai fuskar ta dake a ya mutse,a hankali ya fara taku tare da nufar bakin gadon ,gabaki d’aya dakin tashin kamshin imperial majesty yake,sosai kayan jikinsa sukai masa kyau,sanye yace cikin wani red suit me shegen kyau, fuskarsa sanye yake cikin wani bakin glass da baka iya hango kwayar idanuwansa,sosai glass yin yayi wa fuskarsa kyau musamman dan karamin pink lips dinsa da ya kara fito da ainahin sajan sa,gashin kasansa sai kyalli take kamar kullum kara mata yawa ake,kallan diamond watches dinsa yayi kafun ya mayar da kallansa kan fuskarta da take baccin ta har yanxu ,sabanin dazu yanxu harda dan turo dan karamin bakin ta duk da bacci take, guntun tsaki yaja kafun ya taba pillow da kanta yake,motsa fuskarta tayi tana kara cono bakinta gaba,wani tsakin ya kara ja yana dafe goshinsa da ke Sara masa, kara taba pillown yayi ganin bata motsa bane a hankali ya furta “ke”, nan ma bata motsan ba ,da dan karfi ya daki pillow din a bazata ta mike da niyar guduwa, dan karamin tsaki yaja yana furta “matsoraciya kawai “ cikin kasan makoshinsa,kafun ya kalleta,”baki iya sallah bane,komai sai an koya miki” ya furta yana kara tsuke fuskarsa , shiru kawai tayi tana faman rarraba ido kafun ta turo karamin bakinta, “dady” ya furta da shakakkiyar muryarta,kallan yadda tayi maganar yayi kafun ya furta “momy”shima yana harararta,dariya ta kyalkyale dashi,be bari ta kara magana ba ya furta je kiyo alwala, gyada masa kai kawai tayi,sosai ta gane kofar da zata kai ta toilet,baka kara cewa komai ba ta mike tsaye dukda kasan cewar bariga a jikinta haka ta mike ,tana nufar kofar, saurin kawar da kansa yayi da ka kallanta ,yana ganin ta shige kofar shima ya fita daga dakin.

*****tun da ta shiga toilet din tsayawa kawai tayi tana bin ban dakin da kallo kafun ta dafe kanta da taji ya fara mata ciwon, sosai ta tsaya kallan bandakin ,cikin karan bani ta nufi wani glass dake kewaye da ban dakin, tsayawa tayi tana zubawa wajan idanu “toh shi dady yasan nan wani dakin ne shine zaice mun nazo”har ta juya daniyar komawa sea taji tana jin fitsari,kallan Inda zatayi futsarin ta fara dubawa,har ta tsugunna sai kuma ta tashi,kallan toilet tayi kamar me san tuno wani abu,kafun ta karasa wajan a hankali ,bakin tight dinta tacire jin ta fara yin futsarin,amai makon fitsarin kuma sai ga Jini, a firgice ta saki kara cikin razana ganin Jinin da tayi “dady ,dady” ta ke furtawa cikin birkicewa, cikin sauri ta nufi kofar fita daga ban dakin, Daidai ta taba hannun kofar toilet da niyar fita kanta ya sara mata,Kallan kafar tata tayi kafun kuma ta koma cikin bandakin,kamar tasan yadda ake anfani da kayan toilet din,sosai kuwa ta wanke jikinta har da zarcewa da yin Wanka da kayan wankan toilet din,kamar wacce ake controlling dinta, ban dakin sai faman tashin kamshi yake,komai a nutse take yi bayan ta kammala wankan harda gyara ban dakin duk da babu abunda tayi, fito wa tayi daga toilet din tana bin wajan da kallo, trolley din da king ya shigo da ita jiya ta tsaya bi da kallo, kafun ta karasa wajanta,budewa tayi a hankali tana bun jerarrun kayan dake cikin jakar,tsayawa kallansu tayi sosai kafun ta dakko wata doguwar riga baka sai digo digon ja dake jikinta, kara kallan jakan tayi,kafun ta sa hannu ta dauki wata jaka a ciki, bude cikin jakar tayi inners ne a cikin jakar sai pad shima,pant da bra ta dauka har zata kulle jakar sai kuma ta dauki pad din guda d’aya ,tare da Mayar da trolley din ta rufe kamar yadda ta ganta, a nutse ta saka pad dinta da pant, a wannan lokacin har bra dinta ta saka kafun ta kalli rigar dake gefenta,murmushi ta saki da har dimples dinta na dama da hagu na lobawa kafun ta saka rigar, bakaramun kyau rigar tayi wa jikinta ba musamman da ta kasance fara sai kayan suka haskata kasan tuwar kalan kayan ne ja da baki, hips dinta sosai ya fito cikin rigar jikinta ,yalwataccen gashin kanta da ya sakko har gadon bayanta me shegen cikowa ta kama da niyar tufkewa amma ta kasa,sosai ta fara kiciniyar yadda zata kamashi,ganin ta kasane yasa ta dakko gyalan kayanta daniyar barin dakin, taku d’aya biyu tayi kanta ya sara mata,tsayawa tayi tana bin inda take da kallo , tunani ta shigayi kafun ta turo dan karamin bakinta”to ni ya naganni a nan ba nashiga can ba” ta karasa zan can nata tana nuna kofar toilet ,sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan jikin ta , wayo manyan idanuwanta tayi tana bun jikinta da kallo, kafun ta kai hannu ta shafa kamar me tsoran shafawa, cikin Sauri ta dauke hannunta,”ko dady ne yamun wayo ,yasamun kayannan “ tunanin hakan yasa ta saki murmushi, cikin sauri ta karasa kofar fita daga dakin gashin kanta duk ya rufe mata fuska, bude komar datai ba wuya ta hango dadin nata na kokarin kai wani kyakkyawan cup bakinsa ,a guje ta nufi inda yake tana sakin gyalan hannunta,Daidai zai kai cup din bakinsa ta saki kara “dady”,dan juyo da idanuwansa yayi yana kokarin Shan coffee dinsa ta daka tsalle tare da bare kofin hannunsa,hawaye duk ya bata fuskarta cikin rawar murya ta furta “dady karkasha ,ansa guba “…..

(Tofa😳).

🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰➰➰➰

AMRAH

Karfe 4:30 ta farka tana ya mutse fuskarta , dafe goshinta tayi tana ware yan mitsi mitsin idanuwanta kafun ta waresu gabaki d’aya ,bin dakin ta farayi da kallo kafun ta motsa jikinta da niyar tashi, zafin da taji a kasantane yasata koma tare da bin jikinta da kallo,da kyar ta tashi zaune tana faman damshe bakinta sabida zafin da take ji a kasan ta, kallan yadda take babu kaya tayi kafun taja dogon tsaki tana mikewa tsaye ,kofar dakin ta sawa key kafun ta koma ta zauna,tana danasanin kiransa da tayi a waya ,”amma in kasan wata ai bata san wata ba” ta furta tare da nufar wardrobe dinta, wata fincinar riga ta dauka tare da sawa a jikin ta sai faman wale kafa take, kwalbar magungunan da tasha ta dauka tare da mayar dasu ma’ajiyarsu data boyesu,tunanin yadda zata kawar da tahee ta fara,ko tunanin gari be gama waye ba ,batayi ba ta dauki wayar ta tare da danna wata number ,kusan missed called uku har yanxu ba a daga ba ,wani dogon tsaki taja kafun ta kara kiran wayar, ringing biyu aka daga wayar,nishin da ta fara jiyowa cikin wayar ne yasata sakin tsaki dakashe wayar tata tana jefata kan gado duk tsikar jikinta ya tashi,sosai ta fara juyi saman gadon jarabarta na tashi, ga wani tsanan tahee dake kara ruruwa a cikin zuciyarta”a wannan karan da kaina zanje wajan boka ,bana bukatar te makon kowa” a haka ta cigaba da tunanin yadda Zata cika burinta batare da kowa ya farga da ita ba .

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

KANO

“Assalamu alaikum “ zahra ta shigo dakin tana dukar da kai,amsa mata oumma tayi tana sakin mata murmushi,itama zahra murmushin ta saki tana kallan oumma,”oumma daman breakfast aka gama ke kadai muke jira yanxu “, kallanta oumma tayi kamar bazata ce komai ba sai ta mike ,daman sanye take cikin hijab dinta, zahra na ganin hakan ta saki a jiyar zujiya , ta dauka oumma bazata biyo taba kamar yadda Khaleed ya fada mata,da sauri ta bude kofar dakin tana nunawa oumma hanya har suka karaso babban falon, Khaleed na ganinta shima ya mike,kwalo zahra ta sakar masa tana mika masa hannu “yaya my gift”,dan hararar ta Khaleed yayi kije kafun ya soma magana “kije dakina ki dauka” tsalle ta daka har da juyi tana dariya,kallan oumma Khaleed yayi tare da hararar zahra”kin tsaya shiririta kirbar mana oumma a tsaye “ da Sauri zahra ta juya Wajan oumma “ kiyi hakuri oumma”, shima Khaleed kallanta yayi ,tare da nuna mata hanyar dining “oumma kiyi hakuri mun barki a tsaye “murmushi kawai ta sakar masa itama tana tuno su taheern dinta , basu kara cewa komai ba suka nufi dinning din gabaki d’aya ,har yar rigan rigan Wanda zaiyi serving din oumma ake ,saida suka gama cika mata gabanta da kayan abinci har saida ta dakatar dasu , a hankali zahra tayi serving din Khaleed shima kafin su fara cin abincin, har sun kusa kammalawa breakfast Dinsu sai ga dady yafito, da sauri zahra ta zaro ido tana mike wa “dadyy “ta furta da niyar nufar inda yake ,nuni yayi mata data koma ta zauna kafun ya karaso wajan shima ,cikin zoyala ya soma magana “wato har kun fara mantawa dani” dariya suka saki banda oumma data kura wa abincin gabanta ido, a hankali ta bude bakinta tare da gaishesa, kallo daya yayi mata tare da amsawa shima zama yayi zahra tayi serving dinsa,shine ya soma tashi tare da musu sallama , mikewa Khaleed yayi shima dady ya komar dashi”ku kammala cin abin cinki, akwai meeting din da zani, auta me kikeso na taho miki dashi”girgiza masa kai zahra tayi “any dady”gyada mata kai kawai yayi tare da barin wajan ,yana jiyo yadda take faman furta “ Allah ya tsare dady,love you more “girgiza kai yayi yana sakin murmushi kafun ya bar falon. Suma suna kammala cin abincin falo suka dawo, suka fara hira da oumma wannan karan sunki barinta ta koma har saida ta fara sake musu suna hira,sallah ne kawai ke tayar dasu da oumma ta idar dasu kara zuwa su dakko ta , ko gajiya da hiran basayi.

🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰➰➰

BUNKURE

zaune Dije suke a daki ita da bintalo sai faman irgan kudi suke ,kallan Dije bintalo tayi cikin ya tsine,”wai ke dije wace Irin mutum ce me shegen san kudi,yanxu kudin ma bazaki barni na irgaba Haba ki canza Hali da wannan shegen san kudin naki”batare da dije ta damu da bakar maganar da bintalo ta saba fada mata ba ta wangale bakinta” Haba yar albarka ta ,Kema kinsan da kudin nan nake so ki koma gidan gayunnan “dan ta bile baki bintalo tayi kafun ta kammala irga kudinta tana mikewa,”ni yanxu bani da wannan lokaci,ki jira nagama cin duniyata sai ayi wannan maganar”ta karashe zancan ta tana jefawa Dije dubu biyar “ga wannan “ da Sauri Dije ta wawuri kudin tare da zurasu cikin zaninta,tsaki bintalo taja tana daukar wayar ta da ake kira,ganin me kiran ne yasa ta sakin murmushi “hajjaju barka da dare”daga daya ban garan banji me aka ceba sai dariyar da bintalo ta saki tana furta “baki da matsala hajjaju ganinan tafe”tana kammala zancanta ta kashe wayar tare da wawurar mayafinta tana barin dakin,ko damuwa da fadawa Dije inda zata bayi ba ta Sakai ta bar gidan.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Tun bayan data Barar masa da coffee din hannunsa bai motsaba,kafun ya dago da idanuwansa a zuciye yana kallanta “how dare you”, kura masa ido tahee tayi tana kallansa har yanxu da sauran hawaye a fuskarta da gashin kanta ya rufe fuskar,daga hannu yayi da niyar tsinka mata mari a bazata yaji ta rungumesa tana sakin saban kuka,kasa motsi king yayi ba ‘a jin karar komai sai karar sautin kukan ta dake tashi,a hankali ta soma magana cikin shashsheka “dady karkasha kaji, suna so sukashe mu ni banaso ka mutu kaji”,yanxun kam ko kwakkwaran motsi king be yi ba ,tunani ya fara “Anya buguwar da yarinyar nan tayi be taba mata hankali ba”,’ban’bareta yayi daga jikinsa yana hade ransa,langwabar masa dakai tahee tayi tana tuna dan karamin bakinta, bin wajan da ta zubar da coffee din yayi kafin ya maida hankalinsa kanta,”me ke damunki “,girgiza masa kai Kawai tayi alamun itama bata sani ba ,sai alokacin idanuwansa ya sauka kan kayan jikinta, sosai kayan sukai mata kyau musamman dogon gashin da ya gani a kanta,duk da ne gama yadda da gashin kanta bane ,a hankali ya fara taku tare matso ta,ganin yanda ya hade fuskarsa yasa ta tsorata,tare da cuno bakinta, itama baya ta fara ja kamar yadda taga yana matsowa ,bata san lokacin da suka jingida da jikin bango ba,hannunsa daya king ya sa tare da dafe jikin bango ,sosai yayi mata runfa ko ganinta ba a yi sosai,dan sunkuyo da fuskarsa yayi dai dai kan tata….

Mss Lee 💖
07041879581

💖💖The talent troupe writers 💖💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK

Mai bukatar complete din gidan aunty yayi mun magana ta wannan number 07041879581.

MASOYIYA WANNAN PAGE DINKI NE 💖💖💖💖I heart you so much 💖.

BARKAN KU DA SALLAH , hope anyi sallah lapiya, ina mika sakon jinjinawa ga al’ummar musulmai baki daya .

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

Kuma ban barku a baya ba …
💖💖masoyiya ta (duk karfin izzata )
Aunty sadiya (Jini daya )
Maman sayyid (ya fita zakka )
Auta( baby)
Maman twins (sarki sameer )
Memerh (ubana ne ko kishiyata)

Dukan ku ina Kaunar ku lodi lodi 💖🫶,Allah ya kara hada kawunanmu (Ameen)

Leave a Reply

Back to top button