Hausa NovelsHausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 19

Sponsored Links

💖🐝NAMIJIN ZUMA🐝PAID PAGE 19💖 *this book is only 1k 08101626484*

Tafiyar mintuna ashirin sukayi yayinda Aeezad bece da Zaks ga inda zasuje ba,shi kuma Zaks tsoro ya hanasa tambaya se sharara gudu yakeyi kawai a kan shantalelen ti-tin daze kaika kawo zuwa mando, har zuwa yanzu se kuka me sauti aunty nabeelah keyi, har yanzu dafe take da kuncinta ba karamin jin zafin marin tayi ba, a rayuwarta ba a taba touching jikinta taji zafinnnan dataji ba yanzu, hajiya Rafi’ah Tasha marinta yafi a kirga Kuma tanajin zafin sosai, Amma a duniyarta kaf ba a taba mata Marin da aka mata me zafi da rad’ad’i irin wanda Aeezad ya mata yau ba, tun daga saman fatar fuskarta takejin zafin marin har zuwa Cikin lungu da sakon zuciyarta, tunani-tunani kawai takeyi ina kuma ze kaita?. “Kagani kou? Takiyin shiru Kawai so takeyi in haukace, ga zafin abinda tamin ga zafin kukanta dake taba zuciyata…” Aeezad ya fadi bayan ya juya ya kalli Aunty nabeelah data hada Kai da guiwa se faman zuba kuka takeyi kmr karamar yarinya, bayan Aeezad ya kalleta kana ya dawo da dubansa kan Zaks din. “Kiyi hakuri Aunty nabeelah Dan Allah……” Cewar Zaks da bashi da yadda zeyi shida kansa yasan Aunty nabeelah ta maru iya maruwa, Amma yasan dole se Aeezad yayi nadamar marin dayayi mata gashi tin yanzu ma ya fara ganin alamar nadama a kan fuskar Aeezad din. “Gidan uban wa zaka kaini ne waikai ? Wa-wa kawai dakai se lulaka gudu kakeyi Dani a kan ti-ti kmr Wani Dan iska!’ ko an gaya maka ni Dan iska ne… sakarai kawai!” aeezad ya fadi Yana kallon Zaks daketa driving cikin zallar matsifa da bala’i Aeezad yayi mgnar. “Baka gayamin ina zamuje ba ai…” Zaks yayi mgnr cikin sanyi sbda ganin Aeezad na neman sauke masa bala’i daman aeezad matsifaffe ne ina maga yau da aka tabosa. “Baka da bakin dazaka tambayeni ina zaka kaimu Kai? Wa-wa kawai, ni zakama iskanci kaima, ko dankaga motarka nashiga aikin banza in bazaka kaini inda nakeso naje ba ka sauke mu nida ita se in goyata muje a kafa,!” aeezad ya fadi a zafafe kaf matsifarsa tadawo kan Zaks, Se tada jijiyoyin wuya yakeyi, gabaki daya baya hayyacinsa, duk kukan nabeelah ne ya kid’imasa ko ince yake kan kid’imasa shine yaketa bala’innan dabesan na meye ba. Zaks de shiru yayi ya masa uzuri domin ya kula bayin kansa bane duk baya hayyacinsa, Dan hk Sam Zaks bece komi ba yayi kwana ya dawo baya ya kalli Aeezad din daketa huci kmr zecinye kansa da matsifa. “Na juyu ina zamuje?” Zaks ya tambayesa cikin sanyi danshi ba mutum bane me fada ba kasafaima yake fushi ba. Aeezad ya masa banza kmr bejishi ba se kallon hanya yakeyi Yana cigaba da girgiza kafa kmr sarki a fadarsa, shi kadai yasan me yakeji a zuciyarsa,. “”Mu tsaya a Nan…” Aeezad ya fadi cikin zallar isa da mulki Hadi da kasaita ciki ciki ma yy mgnr kkr bayason Yi. Zaks ya kalli inda yace su tsaya yaga babban masallacin sultan bello ne. Cikin hanzari yayi packing a zuciyarsa Se tunani yakeyi meya kawosu masallaci, shifa yasha hotel ma aeezad din zece akaisu yasha a can zasu goge rainin. Zaks de mamaki ya cikasa Amma babu bakin tambaya sede yabi aeezad din da ido. Jin sun tsaya yasa aunty nabeelah dagowa ta kalli inda suka tsaya bakin masallaci Nan tashiga tunanin mezasuyi a Nan,, itafa tinda yasata a mota ta sadakar tasha Wani guri kebantacce ze kaita ya keta mata haddi sbda tasan shine abinda ya tsokare masa ido, tariga ta sadakar shiyasa taketa kukanta me dalilin a zuciyarta se Addu’ah takeyi Allah ya tseratar da ita daga sharrin Aeezad din. “Yanzu abinda yarinyar Nan tayi min ta kyauta Zaks?” Aeezad ya fadi Hadi da juyowa ya kalli Zaks da yayi packing motar ya tsaya Yana jiran cewar Gogan, Se Kuma yaji Yana wannaN maganar, Zaks ya amshe da “Inafa ta kyauta , ai kwata-kwata Mommynmu bata kyauta ba , sam-sam bata duba a wannan lamarinba…” Zaks ya fadi shi Lamarinma ya fara basa dariya. “kagani kou? Wai ace ni ina kwance gadon asibiti ita tana waje tana tad’i da namiji saboda ita ga macen ayu, mayyar maza,,, bafa sau daya ta fara ba, tayi first time na mata warning na dannewa raina, Amma seda ta kara yanzu ma, tayi fa yafi a kirga Ashe shi mutumin sbda ita yake zuwa ma asibitin tin Muna kano, Dan wulakanci yarinyar Nan ta cuceni wlhi Zaks Amma yau zan maganinta! Zanga gidan ubanwa zata kuma kula wani d’ana miji…” yadda yake mgnr kadai ya isa ya tabbatar maka da zuciyarsa na cike da bakin ciki da bacin Rai, aunty nabeelah dake baya tana jinsa , Abu Daya yafi Mata ciwo yadda yaketa cemata yarinya, abin na bata mamaki wai d’anda ta raina ne yake cemata yarinya, Gashi ya dawo yace mata mayyar maza. “Lallai lalacewata takai lalacewa…” Nabeelah ta fadi a ranta a zahiri kuwa wasu zafafan hawaye be suka wanke mata kunci sautin kukanma tini tadena sbda takaici ya hana kukan nata fidda sauti, ji takeyi kmr ta bude kofar ta fita Amma tana tsoron kar ya biyota ya sake marinta, Mari Daya kawai ya zuba mata Amma tini yasa tsoronsa a zuciyarta, a duniya nabeelah ta tsani ka taba mata lafiyar jiki, sannan tanada tsoro sosai duk tsoro ya kamata na Aeezad ko a mafarki akace mata Aeezad ze wanketa da mari zata misalta, gabaki daya jinta take kmr a mafarki har yanzu. “Kayi hakuri,dole se hakuri…” Cewar Zaks da yaketa kallon Aeezad wanda bayan ya gama zayyanowa Zaks maganganun ya koma yayi Shiru ya jingina bayansa da bayan kujerar yaci gaba da girgiza kawai shi kadai Kai kace girgizashi akeyi, Sbda tsabar jijjigar da yakeyi har Wani jijjiga ita kanta motar takeyi, ba a taba Bata masa Rai kmr yadda ta bata masa yau ba, tinda uwarsa ta haifesa be taba shiga bakin cikin Daya shiga yau ba kuma duk a kanta, shifa Sam ba haushinta yaji ba Kawai de ta bata masa raine,Amma yanzu haka Yana cikin nadamar marin da yayi mata, tinda yayi marinma yayi nadamar yinsa, Kawai de tinda yariga yayi ne ba yadda zeyi, Amma a zuciyarsa yayi nadama yafi a kirga. Seda suka kwashi 10mnt a Nan Tsaye kana Aeezad ya bude murfin mota ya fito cikin hanzari Zaks ya fito gudun kada yaki fitowa yayi lefi,. Bude gidan bayan Aeezad yayi yayinda Nabeelah ke zaune se faman kwallah takeyi ta dukar da Kai, kallo Daya ya mata yaji Wani irin tsumin tausayinta me zafi ya zuba a zuciyarsa, Nan take ya kuma nadamar marin da yayi mata, Amma sede yaga dukta nutsu da hakanan ne banza bazata taba yadda ya taho da ita suyi tafiyarnan a mota ba, da banza ne tini zata masa rashin mutumci kilama seta kuma marinsa. “Fito muje!” ya fadi cikin bada umarni, ta masa banza kmr bata jisa ba. “Ke bada ke nake mgna ba, ki fito nace mayyar maza, yau zan maganinki wlhi….” Aeezad ya fadi cikin tsawa Hadi da bacin Rai ji yakeyi kmr Yanzu yake ganinta da Alhaji sadi tsaye, Daya kalleta seyaji bacin ransa ya karu, ita Kam Kalmar dayace mata ta mayyar maza ba karamin bata mata Rai tayi ba, lefuffukansa gareta sunada yawa, Still ta masa banza taki fitowa kmr ma batasan da halittarsa ba.”wlhi in baki fito ba zan fiddoki da hannayena…” Cewar Aeezad, dayayi mgnr Yana kokarin rikota ta kwace jikinta Hadi da matsawa can cikin motar. Zaks dake tsaye Yana kallonsu da saurarensu yace “Aunty Kiyi hkri ki fito pls…” Nanma banza nabeelah ta musu, ran Aeezad ya kara baci daman yanada cikinta,ya shiga kokarin shiga ciki, ganin hakan yasata saurin fitowa gudun kar ya Kara mata Wani Marin har yanzu zafin na farko be saketaba. jawo hannunta yayi direct zuwa cikin masallacin. Ta kwace hannunya ya kuma kamowa ya rike gam, ta kallesa ta kasa cewa komi ya riga ya dasa mata tsoronsa a ruhinta , gani takeyi kmr in tai magana wani Marin ze kuma watsa mata. , zaks de na biye dasu, suka isa cikin farfajiyar masallacin Aeezad ya kalli agogon hannunsa yaga bakwai ta wuce gaf ake da sallah isha’i, ga cikin masallacin cike yake da mutane se wa’azi akeyi Ya kalli Zaks ba tare dayace komi ba ya saki hannunta ya nufa Cikin masallacin, nabeelah da Zaks suka bisa da ido, tunani nabeelah tashigayi meya kawosu masallaci, ba ita ba har Zaks idanuwa ya bishi dashi yayinda zuciyarsa ta tsunduma tunanin me sukazoyi masallaci kuma da Aunty nabeelah. Bayan Aeezad ya isa ga limamin ya karasa ya gaidasa kana ya masa maganganu kasa-kasa ba wanda yaji, sede limamin ya dauki uzuri wani ya hau yaci gaba da wa’azin,. Limamin wanda ke sanye da manyan Kaya na Alfarma babban mutum ne sosai, suka karaso inda nabeelah da Zaks suke tsaye,. Zaks ya bude baki ze gaida malamin Aeezad yayi hanzarin nuna nabeelah yana cewa “Yawwa malam gatanan, ka ganta nan muna kaunar juna kmr zamu kashe kanmu, iyayenmu sun hanamu Auren juna , sau bakwai ina mata ciki,…” Malam liman yace “Subhanallahi!” nabeelah ta zaro idanuwa waje a razane , ta kure Aeezad da ido, Jin irin bata mata sunan da yayi, nan ta daskare ta kasa mgna sbda mamaki, kallonsa takeyi kmr ba Aeezad dinta ba me hankali, se yanzu ta kara tabbatar da Aeezad dinnan bashi da hankali. Ba nabeelah ba hatta zaks seda ya zaro ido yabi Aeezad da kallo yana me mamakinsa, shi kansa Zaks ya fara tunanin soyayyar da Aeezad kema nabeelah ya fara taba masa hankali, rike baki Zaks yayi yana kallon Aeezad dayaci gaba da magana. “Zina zunubi ne me girma, shiyasa yanzu tayi istibra’i , Nima na tubarwa ubangiji Gashi iyayenmu sunki bari muyi Aure har yanzu, ni kuma in ban aure taba bazan iya hakura da ita ba, na riga nasaba da ita, bata da Aibu nima kuma banda Aibu gata nan de ka ganta malam liman duk muna kaunar juna nida ita, dan Allah ka taimakemu ka daura mana Aure yanzu yanzu nida ita in an fito sallar isha’i banso yau mu kwana tare ba tare da Aurenta a kaina ba, sbda dakinku daya gidanmu daya , gado daya muke kwana, kwara a mana Auren dan kar in afka mata yau hannun agogo yadawo sabo….” Aeezad ke mgnr ba kunya ba tsoron karyar da yake shimfid’awa yasan hakan ne zesa a muasa Aure da fitilarsa cikin sauki, ba tare da dogon bincike ba.

 

Yazata kaya ne?

 

Back to top button