Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 13

Sponsored Links

Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

13….

Bata yarda ta fito dept ba tun bayan gama test dinsu, duk gaba daya a tsorace take, gani take kamar at anytime xata iya ganin Aliyu a gabanta, karfe sha daya da qtr wayar khaleel dake Jakarta ta fara vibrate, fiddowa tayi taga Emoji biyu na love gaban screen din, ta yi jim don bata san ko shi bane, har ya kusa katsewa sannan ta daga ta kai kunne tayi shiru, muryar mace taji tace “Hello Baby….” hakan yasa ta katse wayar, sake bugowa tayi bata daga ba har ya katse. Tana ta xaune da wani course mate dinta dake second degree dinsa d’an Nigeria but residing in Malaysia yana ta mata hira ita dai sai dai tayi murmushi tana saurarensa, dai dai nn wayar hannunta ya sake vibrate ta daga tana kallon number, sai kuma tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace “Are you done?” Tace “Umm” yace “Aiitt am waiting….. Near the car” daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon course mate dinta tace “Wanda xai daukeni yana jirana, xan tafi” ya mike shi ma yace “To bari in raka ki” da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “Ohk” tana gaba yana biye da ita har suka iso gun motar, Tun daga nesa Khaleel ke kallonsu, sai da ya ga sun iso ya dauke kai, Usman yace “Assalamu alaikum” sake juyowa khaleel yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma ya bude motar ya basa hannu suka gaisa, Khadijah ta tabe baki ta xaga daya side din motar tana kallon Usman tace “Thanks…. sai gobe in sha Allah” Usman yace “Aiiit Allah kai mu lfya” Sallama yyi da khaleel sannan ya wuce, Khaleel ya tada motar suka bar wajen, har suka hau kan titi bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba, wayarsa dake hannunta ya fara vibrate kuma, kallon screen din tayi taga number daxu ce ta mika masa, sai da ya kalli screen shi ma kafin yyi parking gefen titin, ya jira wayar ya katse sannan ya kira yace “How you….” Satan kallonsa khadijah tayi ta dauke kai tana kallon waje, bayan yan sakwanni yace “Like serious, alryt sorry for that wayar baya gu na ne” d’an murmushi yyi yana shafa lallausan bak’in gashin kansa dake sheki yace “I left the phone with a frnd, and I guess….bata san ke bace da baxata dauka ba, yanxu dai I will cal back in 10 mins time, I am on the road” daga haka ya katse wayar yace “Why did….. You pick her call?” Kamar me counting words din yyi maganan ya juyo yana kallonta, bata kallesa ba bare ta basa amsa, hakan yasa ya ci gaba da driving dinsa, sai da suka kusa gida yace “Who was that guy?” Ta juya tana kallon sa da kyau tace “And why are you asking?” Tabe baki yyi bai ce komai ba, sai da yyi parking ta hade rai tace “Da Kasan da xata kiraka ka bani wayar” daga haka ta juya xata bude motar ta fita yasa lock, juyawa tayi tana kallon sa, yace “Ki dai bi a hankali da guys din makaranta da kike kulawa, and you even let him accompany you to where I am, toh ni meye hadina da shi?” Mamaki ne ya cika ta ta saki baki tana kallon sa, a mugun fusace tace “Ina ruwanka ma idan na bi samarin makaranta, I guess it shud be none of ur concern, let me outta here immediately…. Ka bude min mota in fita” Tun da ta fara ya kwantar da kujeran motar ya lumshe ido yana saurarenta, jin tayi shiru ya dago kujeran ya xauna yana kallonta yace “Kin gama?” Ta dago tana kallon sa ranta na suya, bude lock din motar yyi yace “Ok then, kindly move out and close d car door behind you” bude motar tayi kamar xata tashi sama ta nufi apartment dinta ba tare da ta kulle masa motar ba. Wayan da tayi ta yi da su Shuraim yasa ta mance duk damuwar dake tare da ita, ganin lkcn kwanciyarsu yyi tayi sallama da su ta kwanta don tayi shirin bacci tun bayan da tayi sllhn magrib, lkci daya baccin ya dauke ta. Tun da ta tashi take ta tunanin yanda xata tafi schl don kusan tests suke, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tace “Do I ever have to meet with him in my life again??” Ganin lkci na ta wucewa ta mike a sanyaye ta dau jakarta da mayafi ta fita parlor, kallo daya tayi ma motar khaleel dake parking space ta hade rai ta dauke kai ta rufe apartment dinta, a hankali take tafiya har ta isa titi, cab ta shiga suna isa makarantar ta biyasa kudinsa ta fito tana kalle kalle kamar munafuka, tafiya take da sauri ta shiga schl don a waje ta sauka daga cab din, kawai mota taga ya tsaya gefenta bata ankara ba sai ganinta tayi cikin motar ta fasa ihu a tsorace amma tuni aka ja motar. Khadijah ta bude idonta a hankali ta na bin parlorn da take ciki da kallo, ta mike da sauri xuciyarta na bugawa tana kiran Allah a xuciyarta, kamar ance ta juya bayanta ta ga mutum tsaye yana kallonta, xuciyarta tayi mugun bugawa tayi saurin dauke kanta, karasowa yyi parlorn cikin sanyin murya yace “Imannn” bata san lkcn da ta xube wajen ba ta fashe da wani matsanancin kukan takaici, durkusawa yyi gabanta a hankali yace “Imann… I….” Mikewa take son yi ya rikota fixge hannunta tayi da karfi, yyi still yana kallonta ko kiftawa bbu, tayi saurin dauke kai tana kuka sosai ta hade kai da gwiwa, mikewa yyi ya dago ta yyi hanyar wata kofa da ita, tashin hankalin da ba a sa masa rana, ihu ta sakar masa tana turasa amma da yake karfinsu ba daya ba sae da ya shigar da ita kofar ya rufe, cikin rawar murya take cewa “Me ka dawo yi rayuwata kuma Aliyu, I am no longer under you or ur family, let me plsss am begging you in the name of Allah, ka rabu da ni……” Jinginar da ita yyi da bango yana kallonta da idanuwansa da suka kada yace “Kinsan shekarun da na dauka ina neman ki xa ki ce in rabu da ke” a tsawace ya kare maganan, cakumosa tayi tace “Kana nemana?? in maka me Aliyu? Neman me kake min, ka rufa min asiri ka kyaleni in tafi don Allah” yyi wani murmushi yace “In kyale ki ki tafi? Haka kawai in kyale ki ki tafi?” Turasa tayi iya karfinta amma ko gezau ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi da suka, cikin kuka sosai tace “Aliyu ba don ni ba kayi hakuri ka kyaleni” yana kallonta a hankali yace “Ki yafe min Iman….” Tsayar da kukan da take tayi tana murmushin takaici tace “In yafe maka? Aliyu dama kayi min wani laifi ne da xan yafe maka, gaskiya ban san shi ba, idan ma akwai to shari’armu sae a lahira” finciko ta yyi da idanuwansa da suka yi mugun kadawa yace “A lahira?” Kasa amsawa tayi ganin ynda ya sauya kamannin fuska, jefar da ita yyi kan gado ya karaso yana mata wani kallo yace “Wani Shari’ar ce sai mun je lahira xa ayi ta? Ki fadi me nayi maki?” Ta dinga ja baya tana ganin dishi dishi, a hankali ta kira sunansa tana girgixa kai daga nan kuma bata sake Sanin abinda ya faru ba ta dai bude ido a hankali ta dalilin axaban da xuciyarta ke mata, Kwance ta ga ta kan gado ita kadai dakin, da kyar ta mike xaune ta dafe xuciyarta, lkci daya ta sauka gadon ta nufi kofarta bude taji a rufe da key, sulalewa kasa tayi ta dafe kirjinta tana kiran Allah a xuciyarta, bude kofar taji kamar ana yi ta tashi tsaye da sauri ta koma bayan kofar ta tsaya aka bude ya shigo cikin dakin yana kalle kalle, da gudu ta fice dakin ya juya da sauri, bin bayanta yyi yana kiranta, ganin bbu inda xata tsira parlorn ta nufi dinning table ta dau wukar da ta gani kai ta juyo tana kallon sa hawaye na sakko mata, girgixa mata kai yyi yace “Wait Iman….” cikin sarkewar murya tace “I swear to Allah who made me kana isowa kusa da ni xan kashe kaina Aliyu” still yyi yana kallonta ya kasa motsi wajen, ta nufi kofa tana rike da wukar hawaye na xubo mata sosai, cikin sanyin murya yace “Noo khadija karki tafi don Allah” da baya da baya take tafiya har ta isa kofa ta fice, ikon Allah kadai ya kai ta gida duk da daren da yyi, ganin halin da take ciki mai cab din ma bai karbi kudi bata shiga gida, nan bakin kofa ta durkusa don bbu jakar makullin, ta kai minti biyar a haka kafin tayi karfin halin buga kofar khaleel, va a dau lkci ba ya bude, ja baya yyi yana kallonta da mamaki, can ya durkusa yace “Are…. are you okay?” Girgixa masa kai tayi numfashinta na sama, ya dago ta yana kallonta yace “Subhanallah” ta fashe da matsanancin kuka ta rikosa tana girgixa kai tana nuna masa kirjinta cikin rawar murya tace “It’s hurting…..” mikewa yyi da sauri ya shiga ciki ya dauko makullin mota ya dawo, cikin ikon Allah khaleel ya isa wani babban hospital don duk ta rikitasa driving kawai yake, tun da ta rufe ido bayan da suka shiga asibitin bata sake budewa ba sai washegari da safe, yana zaune gefenta ya jinginar da Kansa jikin kujerar da yake xaune, su kadai ne cikin ward din,ta mike xaune da kyar taa kallon ruwan hannunta, jin xuciyarta tayi fayau, sai dai har lkcn tana jin kamar numfashinta na seizing,ta kalli oxygen dake gefenta a dakin, ta mayar da kallonta ga agogo taga takwas ya kusa, cire drip din tayi cike da karfin hali ta sauka kan gadon, kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga. Bata dade ba ta fito da alwala, sai kuma taga bbu hijab bare darduma, ta isa kusa da khaleel cikin rashin kuxari tana kallon sa, bacci yake a yanda yake, lkci daya taji tausayinsa sosai wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, durkusawa tayi a hankali ta dafa kujeran cikin sanyin murya tace “Doctor…” Lkci daya ya bude ido yana gyara xamansa, mikewa yyi da sauri ya durkusa gabanta yana kallonta damuwa yace “How you feeling now khadijah?” Murya can kasa tace “Naji sauki, you need rest, ka kwanta saman gado am nt sleepy” hannunta ya kamo yana kallonta xai yi magana daidai nn aka bude kofa wata nurse baturiya ta shigo ward din. Mikewa yyi nurse din ta karaso tana tambayar me yasa ta cire drip din, khadijah ta mike race “I used the restroom” mayar mata da drip din tayi bayanta koma kan gadon, khaleel ya bi ta tare suka fita ward din, tagumi khadijah tayi tana kokarin ganin hawaye bai xubo mata ba, ba a dau lkci ba khaleel ya dawo da mug a rufe ya xauna gefen gadon ya mika mata yace “Gashi ki sha xa a maki allura….” Ta sa hannu ta karba ya bude mata, a hnkli ta kai baki tana sha, ya kafa mata ido, bayan ta sha ta sauke cup din ta karbi murfin ta rufe, yace “Ina ke maki ciwo ynxu?” Ta girgixa masa kai tace “Bbu ko ina, just my chest” yace “Xai daina in sha Allah” nurse din ta dawo rike da tray me dauke da allura da magani, tana kallonta ta gama hadawa ta karaso, mikewa yyi ya fita dakin ya rufo kofar. Tana mta alluran ta bata maganin sannan ta fita bayan ta gwada mata yanda xa ta sha, bayan fitar nurse din khaleel ya shigo rike da table water, ta sha maganin, a hankali tace “I want to go home plss” yace “No sae kin kara samun sauki,” ta girgixa masa kai tace “Am feeling better yanxu, bacci nake son inyi” yace “Toh ae sai sun yi discharging dinki koh” bata kuma cewa komai ba ya gyara mata pillow yana kallonta, ba musuta koma ta kwanta a hankali. Sai kusan karfe daya aka yi discharging dinsu ya biya bill din suka bar clinic din, sai da suka yi nisa cikin sanyin murya tace “How much is d bill” bai ce komi ba kuma bai kalleta ba, yayi parking wani eatry, da ido ta bi sa har ya shiga, rike da Leda biyu ya fito ya bude motar ya shiga suka bar wajen. Parking yyi ya juya yana kallonta, ta jinginar da kai da kujeran motar idonta lumshe, a hankali ya dauke kansa, can ya juyo murya can kasa yace “Khadijah” lkci daya ta bude ido, yace “We are home” kalle kalle ta fara yi, ya bude motar ya fita bayan ya dau takeaways din da yyi, ta fito ta rufe motar tana jin jiri na kwasarta, bata yarda ta bar jikin motar ba, kamar yasani kuwa ya xagayo yana kallonta, hannunsa ya mika mata, ta sauke idanuwanta ta mika masa nata hannun, yana rike da ita har suka iso apartment dinta ya kalleta yace “Key?” Shiru tayi kafin tace “A jakata yake” yace “Ina jakar?” Bata iya tace komai ba, ya bude apartment dinsa.

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

Back to top button