Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 38

Sponsored Links

Mami na shiga parlor Sudais dake tsaye kusa da window din bedroom dinsa ya sauke curtain din ya bar jikin windan ya rungume hannayensa kamar me naxari, can kuma ya nufi study area dinsa ya ja kujera ya xauna, then… What’s Mami telling Musa? Ya kusa minti talatin xaune yana jiran ya ji fitar musa a gidan da mota domin kuwa hakan kadai xai sa ya cire wani xargin da yake a xuciyarsa, amma har kusan magrib shiru Musa bai fita ba, Sudais ya tabe baki ya mike ya tafi ya dauro alwala ya dawo ya xauna, lumshe ido yyi duk jikinsa yyi sanyi “Jiddah? Sure yasan ya so jiddah ba kadan ba a da can, but he just don’t knw what came over him all of a sudden yaji kawai ta fice masa a kai, gashi dai babu abinda tayi masa, ko don an takura sai yyi auren ne yake jin hakan, gaba daya ya ma rasa tunanin da xai yi a lkcn, toh shi yanxu ya xai yi da Khadijah da little babies dinta idan aka tilasta sa yin aure yanxu, bude ido yyi ya xauna da kyau yana naxarin idea din da ya xo masa, ya kama mata wani apartment din kenan? Shafa kansa yyi yana kara naxarin shawaran a ransa, jin xa a tada sllh ya mike ya nufi kofa ya fita dakin, ana idar da sllh ya dawo daki ya dau makullin motarsa ya fita, ce ma Mami dake parlor a xaune yyi sai ya dawo ba tare da ta kallesa ba tace “Allah ya kiyaye” yana shiga motarsa ya fita compound din bayan mai gadi ya bude masa gate, sai da ya kusa isa titi ya yaga musa ya danno kan mota xai fito gidan a guje ta madubinsa, Sudais ya hau kan titi driving slowly yana yana kallon musa dake can baya ta madubi, a hankali shi ma musan ke driving din, Sudais yyi murmushi ya kara gudun motar sai yaga shi ma ya kara, gidansu Yusuf ya nufa musa na biye da shi a baya har lkcn yana parking a waje ya fito ya ga musa nesa da shi a motar yyi kamar bai gansa ba ya shiga gidan, bai samu Yusuf a gida ba duk da ba gidan yyi niyyar xuwa ba, ya tsaya har suka d’an yi hira da mahaifiyar Yusuf sannan ya mata sallama ya wuce, gida ya koma yyi parking a waje ya fita ya shiga gidan, tare da mai gadi ya ga musa a xaune yana kallonsa yace “Same ni a waje musa” daga haka ya fita gate din, Musa ya mike ya bi bayansa sai dai fa ya tsorata, Sudais na kallonsa da kyau yace “Hajiya ce ta sa ka bi ni ka ga inda xa ni daxu?” in ina musa ya fara yi, Sudais ya daure fuska yace “Malam amsa min tambayata” gyada kai musa yyi yace “Kayi hakuri barrister umarnin da Hajiya ta bani kenan” Sudais yace “Ohk naga alama, this shud be ur 1st and last, ko da wasa ka kuskura ka sake bin bayana a mota I won’t take it likely with you” daga haka ya shiga gida ya bar sa tsaye gun. Sudais na shiga daki yayi dialing number jiddah, bayan ta dauka suka gaisa murya can kasa yace “Kina ji na jiddah?” Tace “Ina ji, ya su Mami?” Yace “They are fyn, ina son mu yi wata magana ne da ke, are you alone?” Tace “Yeah ni kadai ce, hope all is well” yace “Noo, Jiddah plss ki min wata alfarma don Allah” jin tayi shiru ya kwantar da murya yace “look jiddah am still yet to be settled, they are a lot of things I have not fixed right, beside ke ma fa ba wai kin gama karatun nan bane, why not ki gama nima nayi settling abubuwan dake gabana before any other thing, why the rush” ita dai tayi shiru tana saurararensa har ya gama, ta d’an yi murmushi tace “So what are you insinuating?” Ya lumshe idanuwansa ya bude a hankali yace “A kara daga bikin jiddah…” Tace “Uhm Aliyu kenan, ai ba wai na rasa manema bane kawai dai ina sonka ne fisabillah kamar yanda kai ma kake so na a baya, kuma idan baka manta ba kai ka damu ayi bikin nan a da, don kuma ka samu wata warce kake so bai kamata ka dinga yawo da hankalina da na magabata na ba, Ba damuwa xaka iya turowa a dau kayan ka, na hakura… Allah hada kowa da rabonsa na alkhairi” duk da jikin Sudais yyi sanyi sosai amma ya dake yace “Haka kika ce?” Tace “Ehh, ka turo a kwasa kayan ka” yace “Ohk” daga haka ya katse wayarsa, fadawa kan gado yyi ya lumshe ido thinking if he made the right decision, mikewa yyi ya sake kiranta sai da ya kusa katsewa ta dauka, yace “Then you do me the favour of telling ur mum ta kira Mamina ta sanar da ita, baxan iya kai ma Mami wannan xancen ba don xata yi tunanin ni ne na fasa…” Jiddah tace “Ohk” daga haka ta katse wayar, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya kwanta, Khadijah ce ta fado masa ya dau wayar ya shiga kiranta, ba a dau lkci ba ta daga cikin sanyin murya tayi masa sallama ya amsa yace “Babies din ne ke kuka haka?” Turo baki tayi ta kalli Mai sunansa dake tsala kuka tare da d’an uwansa tace “Toh Anty tana kitchen ban san me take ba” mikewa yyi xaune yace “ina yaran?” Tace “Ga su nan kan gado a kwance” shiru yyi ya ma rasa abinda xai ce mata, can ya katse wayarsa, Khadijah ta kalli wayar da sauri, jikinta yyi sanyi ta shiga kiransa kuma, har ya katse bai dauka ba, ajiye wayar tayi tana kallon yaran dake ta kuka, fashewa tayi da kuka tace “Toh ni ce na sa su kuka, ko me nayi masu?” Can karshen gado ta koma ta xauna tana hararansu, Mama Suwaiba na kitchen tana jin kukan yaran taki fitowa don lamarin Khadijah ya fara isarta, ya mutum xai haifi yara ya dinga masu abinda take yi, jin kukan yaran yyi yawa ta fito ta shiga dakin tana kallon khadijah tace “Ke kam baki da kirki gaskiya, kiyi hakuri hakan da na gaya maki, banda rashin hankali haka taki uwar ta maki, me yaran suka maki, kinsan baki son haihuwar kika dau cikinsu, kin xata hakkinsu xai bar ki? Yara ko kwana arba’in basu cika ba kika haramta masu nono, toh da haka ake haihuwa kam da ba ayi ba, ni tunda nake ban taba ganin uwa irin ki ba, na maki magana a matsayin wacce tayi jika dake, na maki magana a matsayin ‘ya na maki magana a matsayin ki na shugaba gare ni amma duk a banxa, toh wllh bari mijin naki ya dawo ta dalilin haka ma ni sai na bar maku gidan ku baxan iya ci gaba da xama ina ganin xaluncin nan ba, tun da uwata ta haifeni ban taba gani ko jin tarihin uwa irin ki ba, wannan kuma ya wuce yarinta tsabagaren iskanci ne, kilan idan na bar gidan kika ga babu mai daukarsu idan suna kuka ke xaki dauke kayan ki” daga haka mama suwaiba ta fita tana rike da yaran, hade kai da gwiwa Khadijah tayi tana kuka, Mama suwaiba na komawa parlor ta dau feedern su da ta hada masu tana jiran ganin fitowar Khadijah ta dauka ta je ta basu amma shiru, Su duka biyun ta hada tana ba abincin lkci daya duk tausayin su ya cikata, Sudais ne ya shigo parlorn, ko gaishesa bata yi ba tace “Yallabai dama ina jiran ganin dawowar ka” xaunawa yyi kan kujera yace “Toh gani mama” tace “Ina jin xan bar wannan aikin ku samu wata, ban jin xan iya ci gaba da xama gidan nan ina ganin abinda wancan yarinyar ke ma jariran nan, nayi mata magana a matsayin ta na shugaba gare ni, nayi a matsayin uwa gare ta, kai babu abinda ban ce mata ba a kan yaran nan, kwata kwata bata son su kamar a dole aka mata cikinsu, me yaran nan suka mata fisabillah, kai tun da kake ka taba jin uwa haka, yau ko da shegu ne yaran nan wllh basu cancanci abinda take masu ba, don haka baxan iya ba ni xan tafi kilan idan taga ba ni xata dinga masu abinda ya kamata” Sudais ya lumshe ido ya bude kafin ya mike ya wuce dakin da Khadijah take, dago kai tayi daga gwiwanta jin shigowarsa, wani kallo ya dinga mata kafin yace “Tashi ki je ki karbi yaranki, idan ma kashe su xa kiyi ki kashe su da hannunki” kin tashi tayi yyi mata wani tsawan da ya firgitata ta tashi a tsorace, tun da take bata taba ganinsa haka ba, kofa ta nufa da sauri ta fita, gun mama suwaiba ta tafi ta karbi yaron daya hawaye na sakko mata, tana ta tsaye yana hannunta, Mama suwaiba tace “Ki tafi ki kwantar shi ki dawo ki amshi wannan, in sha Allah tafiya ta xan yi baxan ci gaba da xama da mutum irin ki ba” a sanyaye ta je daki ta kwantar da shi, Bata yarda ta kalli sudais da ke ya tsaye ba ta koma ta dauko dayan, ta dawo ta ajiye sa kusa da d’an uwansa tana hawaye. Sudais na kallonta yace “Gobe xan baki kudin mota sai ki kai su gidan marayu ki bar su a can” ta kallesa da sauri tace “Da gaske?” Yace “Ehh” murmushi tayi tace “Toh nagode” Wani kallo kawai ya dinga mata yace “You are very heartless Amira, ki duba ki ga ni da na ajiye ki gidana na taba sanin ki?? Ban san ki ba ban san komai naki ba, I just saw you are helpless and I decided to help you… Amma yara su xauna wata tara cikinki ki haifesu sannan ace baki da makiya kamar su, just look at the helpless souls, me suka maki Amira? Me yasa kike shafa masu laifin ubansu?” Xaunawa tayi gefen gado bata ce komai ba, ya gyada kai yace “Na san maganin ki” daga haka ya fita dakin ya bar gidan gaba daya, turo baki tayi ta kwanta can nesa da yaran, a xuciyarta tace to ita ta iya rainansu ne, kawai su yi ta kuka kamar ana mintsilinsu baxa su yi shiru ba. As usual yau ma da daddare hangame baki Khadijah tayi tana bacci suka tashi suna kuka kamar ko da yaushe mama suwaiba ta xo ta kwashe su ta tafi dakinta tana girgixa kai. Washegari da safe Sudais ya dawo gidan, dubu Hamsin ya kawo ma mama suwaiba yace ta tafi kawai, duk da mama suwaiba ita ta fara bukatan hakan amma sai ta ji ba dadi, ta fara tausayin yaran, Sudais yace “kar ki damu mama idan taga babu kowa gidan xata dinga kula da abun ta, kiyi tafiyar ki kawai” Mama suwaiba tace “Toh shkkn, Allah yasa ta gane” Sudais yace “Ameen, amma mama kar ki tafi kina jin haushinta don Allah, ba laifinta bane but xata daina in sha Allah” shiru mama suwaiba ta yi shiru tana tunanin to ko dai iskokai gare ta, can tace “Toh shkkn, Allah ya shiryeta ya yaye mata abinda ke damunta, amma xa mu iya sallama da ita in roketa gafara idan na taba saba mata” Sudais yyi murmushi yace “Toh ki shiga ku yi sallaman mama” mama suwaiba ta shiga ta tada Khadijah nan tace mata xata tafi, Khadijah dake ta kallonta da mamaki tace “Ina xaki Anty?” Mama suwaiba tace “Kauyen mu mana” Khadijah ta xaro ido tace “Toh yaran fa?” Sakin baki mama suwaiba tayi tana kallonta a xuciyarta tace Lallai gaskiyarsa bata da lafiya, a fili kuwa tace “Toh anjima ai xan dawo” daga haka ta fita, suka yi sallama da Sudais bayan ta hada kayanta ta wuce cike da kewan Khadijah da yan biyun. Sudais ya dau yaran ya kai su can dakin da Khadijah take, har lkcn tana xaune, yana shigowa da damuwa tace “Toh wa xai dinga kula da yaran yanxu?” Yana mata wani kallo yace “Uwarsu” daga haka ya fita yana kallon wayarsa dake ring, ganin Mami ke kiransa ya d’an yi jim kafin ya daga, tace “Aliyu ka dawo gida yanxu ina neman ka” bata jira yace komai ba ta katse wayar ya koma dakin Khadijah yace “Xan je gida yanxu” kamar xata yi kuka tace “idan suka fara kuka fa? Ni ya xan yi?” Yace “Sai ku yi tare” daga haka ya fita ta fashe da kuka a hankali tana kallon yaran. Karfi Sha daya saura Sudais ya isa gida, bai yi mamakin ganin set din akwatunan da su Anty Maryam suka kai gidan su jiddah ba a parlor, ba Mami kadai ba yau har Abbansa na xaune parlor da kanninsa gaba daya, Kasa xaunawa yyi ya duka murya can kasa yana kallon kayan yace “Ga ni Mami” Mami tace “Kayan da kace dama su dawo da su ne suka kawo daxu shi yasa na kira ka, sai ka fada mana daga nan kuma ina xa a kai kayan?” Sudais ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, muryar Abbansa ya ji yana cewa “Aliyu duk shekaru na a garin nan kai ma ka taso kaga cewar lafiya nake xaune ban taba samun matsala da kowa ba, to ta dalilin ka ma baxan samu matsala da kowa ba domin kuwa kayi kadan, don haka kar ka sake xuwa min da xancen aure ko yanxu ko ba yanxu ba, dama idan ba dauko ma kai dala ba gamo ba ma har nawa kake Aliyu??” Abba ya kalli Mami da ta hade rai yace “Dubesa fa he is just 27 ne ko 28 ya ishe mutane aure gashi ya xo yana wawanci da sokwanci, ke kina ganin haka ma kisan baxa ayi abun kirki ba Idan aka masa auren, get out my frnd” Sudais ya sauke ajiyar xuciya a hankali ya mike ya bar wajen, Mami tace “Fadan kenan Abba?” Abba yace “Toh me xan ce masa, idan akwai wanda kika san xai yi aure soon kawai ki bada kayan gudunmawa, am nt in support of Aliyu getting married now, ya jira idan yayi 30” daga haka Abba ya mike ya bar parlon, murmushi kawai sudais yake shi kadai a daki, Anty Maryam ta shigo tace “Hankalin ka ya kwanta yanxu?” Da sauri yace “Wallahi Anty” Can nesa da Twins din khadijah ta xauna tana ta kallon yanda suke ta motsi, tsoronta daya ya xata yi da su idan suka fara kuka, kamar sun san tunanin da take taji daya ya fara kuka, Tashi tayi da sauri ta dau waya ta shiga kiran sudais, ya fito daga wanka kenan ya dau wayar ya katse ya kirata, kamar xata yi kuka tace “Wallahi gasu nan xasu fara” yace “Xa su fara me?” Tace “Kuka” murmushi yayi yana ci gaba da goge gashin kansa yace “Toh kiyi breastfeeding dinsu” xaro ido tayi tace “A’a ni dai madara Anty take basu” Yace “Toh sai ki basu madaran ai” hawaye ya cika idonta tace “Yaushe Anty xata dawo toh?” Yace “Ta tafi kenan ai” xaro ido tayi ta juya tana kallon yaran, kamar yasan abinda tayi yyi murmushi ya katse wayar ya fara shiryawa. Haka nan Khadijah ta dinga fama da yaran suna kuka tana kuka, gashi tana ta basu madaran basa sha, nan ko tun madarar safe da Mama suwaiba ta hada masu ne take basu, tun daga bakin kofa sudais ke jin kukan yaran ya shigo da sauri, tana ganinsa ta mike ta fashe da kuka tace “Ni dai don Allah ka tafi da su kar ka sake tafiya ka bar su” ko kallonta bai yi ba ya kwace feeder din hannunta bude baki yyi yana kallonta yace “Amira” tana goge idonta tace “Na’am” ya hade rai yace “Tunda kike kin taba shan shayi me sanyi, me yasa ke muguwa ce” kallonsa kawai ta tsaya yi, yyi tsaki ya dau dayan feeder din ma ya fita xuwa kitchen ya xubar da madarar ya xuba na xafi ya hada wani yyi diluting da ruwan gora ya dawo dakin, daukan little sudais yyi ya mika mata daya feeder yace “Ki dauki Muhd ki basa” ta turo baki ta karba ta dau yaran ta fara basa, tsit yaran suka yi gaba daya, bayan wani lkci ya juya yana kallon khadijah dake kallonsa, sauke idonta tayi da sauri, ya kwace feeder hannunta ganin a hancin d’an yaron ta saita yace “Kallon meye kike min xa ki xuba ma yaro madara a hanci” ta hade rai tace “Ai kai ma naga ka kalleni” shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya kwantar da little Sudais da har ya fara bacci ya karbi Muhd din hannunta a hankali yace “We will call him shureim” daga ido yyi yaga kallonsa take still, turo baki tayi ta dauke kai ta boye fuskarta jikin gado, yyi murmushi ya na ci gaba da ba shureim sauran madaran, har ya kwantar da yaron bata dago ba, ya tsura ma dogon gashinta ido dai dai lkcn da ta dago a hankali yyi saurin dauke kansa tace “Ae na kama ka”

Back to top button