Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 36

Sponsored Links

Tashi sudais yyi daga karshe ya koma daki, ganin yanda ta dukunkune waje daya ya isa gadon a hankali yace “Are you cold” bata amsa ba don idonta a rufe suke, ya dauko duvet ya rufe ta da shi, murya can kasa tace ” thank you” ya tsaya yana kallonta don har sannan bata bude idon ba, juyawa yyi ya fita ya bar dakin ya tafi balcony ya xauna ya tsura ma motarsa dake parking space ido, tsoronsa daya mami hakan kuma yasa har lkcn xuciyarsa ke contemplating kan Khadijah, but is he that heartless after all, mikewa yyi daga karshe tunawa da yyi ko wanka bai yi ba gashi an kusa azahar, har ya kusa motarsa sai kuma ya tsaya, but can he go and leave her all alone here, bayan kusan minti biyu ya shiga gidan ya wuce bedroom ya ganta a kasa tana kakarin amai, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta fashe da kuka tana mai da numfashi, wayarsa ya fiddo a aljihunsa ya fita, bayan kusan minti sha biyar ya dawo dakin Yusuf na biye da shi a baya, bude ido tayi a hankali daga kwancen da take a kasa, Jin hannu a forehead dinta taga Dr Yusuf tsaye kanta sudais na daga gefensa, Dr Yusuf yace “Sorry, ya kike jin jikin ki…” Bata iya tace komai ba don ji tayi bakinta ya mata nauyi, yace “Me kike son ci yanxu?” Ta girgixa masa kai a hankali, ya kalli Sudais dake rungume da hannunsa yace “Try making a cup of tea with just milo for her pls” Sudais ya juya ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da cup din warm milo, Yusuf ne ya dinga forcing dinta ta shan tea din, cikin rawar murya hawaye na sakko mata tace “Wllh xai sa ni amai” Yusuf yace “Kadan xa ki sha” da ta kurbi kadan xata ajiye ta koma ta kwanta Yusuf xai hanata, sai da tayi rabin cup din sannan ya kyaleta ta ajiye ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya, bata san sanda karfi ya xo mata ba lkci daya ta tashi duk sai da ta kwarare shayin nan kasan tiles, Sudais dake tsaye ya juya a hankali, can ya sake juyowa, ganin yanda Yusuf ya tsaya kallonta ya duka yace “Tashi ki je bayi ki wanke bakin ki” dafa gado tayi ta mike tana ganin jiri ta shiga bayin, Sudais ya shiga gyara gun aman, komawa gefen gado Yusuf yyi ya xauna ya shiga hada drips da injections, kwanciya tayi bayan ta fito, sai da yyi mata alluran sannan ya sa mata ruwan drip din, tsabar xaxxabi bata ji xafin syringe ba a lkcn, ya lulluba ta da bargo suka fita shi da Sudais dake ta tsaye. Khadijah bata san irin baccin da tayi ba ta dai bude ido taga dim light ne a dakin alamar wai dare yyi ta kalli drip din hannunta taga kamar sabo ne, cike da karfin hali ta mike xaune, ta fi minti goma xaune aka bude kofar dakin, Sudais ya shigo ya kunna wuta yana kallonta yace “Kin tashi?” Kai ta gyada masa, ya karaso yace “How are you feeling now?” A hankali tace “Da sauki” Yace “what did you want to eat?” Murya can kasa tace “Sallah xanyi” yace “Sallah?” Ta gyada masa kai, ya kalli ruwan hannunta, karasowa yyi ya cire mata tube din jikin alluran yace “But be careful kar ruwa ya shiga ciki” ta gyada masa kai, kasa mikewa tsaye tayi da farko don gani take xata iya faduwa, yace “Baxa ki iya ba?” Da kyar ta mike cike da karfin hali ta shiga bayin, ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito, taga har ya shimfida mata darduma ya ajiye mata hijab ya fita, tun tana sllhn a tsaye har ta kasa ta fara yi a xaune, sai bayan da ta idar ya shigo dakin yana tsaye daga bakin kofa yace “Me xa ki ci?” Tayi shiru don a lkcn bbu abinda ke ranta bnda danwaken da Kyauta ta taba yi ranan a can gidan, ganin taki cewa komai ya karaso yace “Ki fadi abinda kike so xan je in siyo ynxu” ta kallesa kafin ta sauke idonta a hankali, yace “What did you want” murya can kasa tace “Danwake, amma tunda dare yyi kawai ka bar sa” tsaye yyi na d’an lkci kafin ya juya bai ce komai ba ya nufi kofa, har ya bude kofar xai fita ya juyo yace “But…. I don’t knw ur name” tana kallonsa a hankali tace “Khadijah….” Ganin yanda yake kallonta tace “Khadijah Muhammad” ya gyada kai yace “I will call you… Iman…. Cos you have the name of My mum” daga haka ya fita, ji gayi komai ya tsaya mata a lkcn, taji kamar ya fama mata wani ciwo ne a xuciyarta, har ya dawo kuma bata daina kukan da take ba kamar ranta xae fita, lkci daya hankalinsa ya tashi bayan ya ajiye warmer din danwaken, da damuwa yace “Me ya faru, why r u crying” cikin rawar murya tace “Don’t call me Iman plss don’t bana so” da mugun mamaki yake kallonta, can a hankali yace “Ohk I won’t” daga haka ya bude warmer din ya xuba mata danwaken a plate yana kallonta yace “Manja ko Man gyada?” Tayi shiru tana goge hawayen idonta, can a hankali tace “Man gyada” xuba mata yyi kadan, ya ajiye abincin da yajinsa a gabanta, bata iya ta ci da yajin ba, haka ta dinga ci gaya ko maggi bbu, gani take idan ta sa yajin xata yi amai, ba laifi ta ci me yawa, amma ta kasa shan ruwan da ya kawo mata, shi dai yana ta tsaye dakin yana danna waya lkci lkci yana kallonta, ganin bata sha ruwan ba yace “Why didn’t you drink d water” a hankali tace “amai, amma kila idan na sha mai xafi baxan yi ba,” wani kallo ya fara yi mata kafin ya tabe baki ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da ruwan dumi, cikin ikon Allah kuma bata yi aman ba da ta sha, sai da ya sa ta wanke baki snn ya maida mata drip din, tana kallonsa bata san lkcn da tace “Are you a doctor?” ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba yace “I am nt, but a lot of my frnds are” Komawa baya yyi bayan ya gama yace “Did you need anything, I mean anything?” Ta girgixa masa kai, xai yi magana wayarsa ta fara ring, ya dauka yana kallon screen din da sauri, gefen gado ya koma ya xauna ya daga ya kai kunne a hankali yace “Mami am on my way now, na tsaya yin wani abu ne, but nan da few minutes xan iso, Ki yi hakuri….” Sai bayan da ya mayar da wayar aljihu yace “Am going home now, anjima kadan Yusuf xai turo nurse da xa ta tsaya dake, she’s on her way now” a hankali Khadijah tace “Toh na gode” yace “No thanks” daga haka ya fita ya rufo mata kofar. Ko minti sha biyar bai yi da fita ba aka bude kofar dakin wata mata da baxata wuce 30 ba ta shigo dakin, ta karaso kusa da khadijah tace “Sannu ya jikin ki” ta gaisheta don ta gane ta tace da sauki, nurse din tace “Ba kya bukatar komai koh?” Khadijah ta gyada mata kai, tace “Toh ki kwanta kiyi bacci, Allah ya kara lfya” ba musu ta koma ta kwanta, nurse din ta juya ta fita, duk khadijah ta bude ido cikin dare sai ta ganta coincidentally ta shigo duba ruwan dake makale hannunta, duk da drip din kuma hakan bai hanata dinga jin xaxxabi sosai ba, sai kusan asuba ta cire mata drip din bayan ya kare, ta samu da kyar ta shiga bathroom, baki ta wanke tayi wanka ta dauro alwala ta fito, duk yanda ta so yin sllh a tsaye kasawa tayi don jiri ne ke dibanta sosai ga rawan sanyi da take, daga karshe tayi a xaune ta kwanta nan kan darduma, ji tayi ana tada ta ta bude ido da kyar taga nurse din ce, tace “Kin yi wanka ne?” Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace “Da ruwan sanyi?” Girgixa mata kai khadijah tayi tace “Akwai ruwan xafi a heater” nurse din tace “To tashi ki koma kan gado” da taimakonta khadijah ta koma kan gadon ta kwanta ta lullubeta ta fita. Takwas saura taji hannu forehead dinta ta bude ido da sauri, Dr Yusuf ta gani tsaye kanta yace “How are you feeling?” Ta tashi xaune tana gyara hijab dinta tace “Ina kwana” yace “Lafiya lau, ya jikin?” Ta sunkuyar da kai tace “Da sauki” ya kalli nurse din yace “She is having a running temperature” nurse din tace “Eh tun da tayi wanka da asuba” ya kalli khadijah yace “Da ruwan sanyi kika yi wankan?” Ta girgixa masa kai, ya kalli nurse din yace “Je ki bude mota akwai drips da injections da na taho da su daga clinic” tace “Ohk sir” daga haka ta fita, d’aga kai khadijah tayi taga kallonta yake, ya dauke idonsa yana girgixa kai ya nufi window ya dage curtains din yana kallon waje, bude kofa aka yi Sudais ya shigo da sallama, kananun kaya ne jikinsa lkci daya kamshin turarensa ya cika ko ina na dakin, a hankali cikin dubara ta toshe hancinta, Tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun Dr Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf yace “Ya su Mami” Sudais yace “They r ol fyn, amma daga clinic kake” Yusuf ya girgixa kai yace “No, yanxu dai xan je clinic din” Sudais yace “ohk how is she feeling now” kafin Yusuf yace komai ya nufo ta yana kallonta yace “Kin tashi lafiya?” Khadijah da har lkcn ta rufe hancinta tace “Ina kwana?” Yace “Lafiya lau, why are you uncomfortable” ta girgixa kai a hankali tana yamutse fuska tace “The perfume” kallon Yusuf yyi ya tabe baki, Nurse ta shigo da abinda Yusuf ya aiketa ta dauko, gaida sudais tayi ya amsa duk da sun gaisa a waje, Sudais ya maida dubansa kan Khadijah yace “Toh me xa ki ci” girgixa masa kai tayi tace “Bana jin yunwa yanxu” Yace “But you need to take something” shayi yasa Nurse ta hado mata mara xafi, ganin Cup din shayin kadai ya dinga tada mata xuciya har da hawayenta, hankali tashe tace “I said am nt hungry plss” Yusuf dai na tsaye kusa da window yana kallon su, Sudais ya karbi shayin ya hade rai ya mika mata yace “Collect it now, ina ruwan wani da rashin jin yunwar ki” Karba tayi ta runtse ido ta rike breath dinta ta kai baki amma ta ki sha, can ta bude ido a hankali tana kallon sa kamar xata yi kuka, taga yanda ya hade rai yana kallonta, kauda fuskarta tayi tace “Don Allah kayi hakuri Allah baxan iya sha ba amai xan yi” yace “Sha kiyi aman” bata ce komai ba kuma bata sha ba, ta kalli Yussuf taga ya rungume hannu yana kallon su kawai, Nurse din tace “Ki daure ki sha kin ji yan mata” runtse ido ta kara yi bata ce mata komai ba, wani tsawa da ya tsorata ta Sudais ya mata yace “Wa kike tunanin xaki dinga ba wahala” bata san lkcn da ta kai shayin baki ba ta kurba, sauka tayi daga kan gadon da sauri jin amai ya taho mata nurse din tayi saurin karban Cup din hannunta ta ajiye, ta shiga bayi tana amai, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta cire mata hijab ta wanke gun sannan suka fito tana rike da hannunta, bin su Sudais yyi da kallo har ta xaunar da khadijah gefen gado ta kwanta tana maida numfashi, Shi dai Yusuf har lkcn bai ce komai ba, ya karasa gun da nurse din ta ajiye ruwan drip din ya dauka ya fara hadawa, ita ya bar ma ta sa mata sannan ya kalli Sudais yace “Barrister…. I will be on my way now” Sudais ya bi bayansa suka fita. Xa a iya cewa kusan a gidan Sudais ya wuni ranan don da ya fita xai dawo, Nurse din kuma karfe sha biyu ta wuce, duk shigowar da xai yi daki kuma sai Khadijah ta farka daga baccin da take, wani lkcn ya mata sannu, wani lkcn kuma kawai ya juya ya fita. Tun bayan awaran da ta sa ya siyo mata ta samu ta ci kadan bata sake yarda ta ci komai ba don shi dinma damunta yake tayi gashi ta kasa yin aman, Karfe shidda saura ta bude ido jin budewar kofar, shi da Yusuf suka shigo, Yusuf ya mata ya jiki, ta gaishesa, Sudais na kallonta yace “I think Gobe xa mu je can Kaduna…” Sai a snn ta kallesa hnkli tace “Toh” Yusuf yace “Why nt ka bari ta fara samun Lafiya, she’s so sick” Sudais ya nufi kofa yace “Noo, she’s leaving tomorrow, for how long am I going to keep her here?” sai kuma ya juyo yace “Or is she going to stay here for ever? You knw presently I will be bringing a woman in here….” Daga haka ya fita, Yusuf ya bi sa da ido, can ya kalle Khadijah yace “What’s ur name?” A hankali tace “Khadijah” yace “Khadijah are you sure you are nt lying about ur self” hawaye ne ya cika idonta tana girgixa masa kai tace “To God who made me, I didnt lie.” Yau din ma nurse din ce ta kwana gidan tare da Khadijah, karfe bakwai da yan mintuna na safe sudais ya shigo gidan, parlor ya xauna bayan ya ajiye flask din hannunsa suka gaisa da nurse din yace “Don Allah ki sa ta shirya anytime soon xa mu kama hanya…” Ruwan xafi nurse din ta sa ma khadijah tayi wanka, ta fito bayan ta yi wankan tana rawan sanyi, nurse din ta ajiye mata daya daga kayan da sudais ya siyo mata dake cikin leda da lotion sannan ta fita, da kyar khadijah ta daure ta tashi ta shirya ta sa Hijab, sai sannan nurse din ta dawo tana kallonta tace “Ki fito yana jiran ki” daga haka ta fita khadijah ta mike a hankali ta bi bayanta, cup din kunun da sudais ya sa aka siyo mata nurse din ta dauka ta bata, amsa tayi tana kallon cikin cup din, can ta dago a hankali ta kalli sudais dake kallonta ta sauke idonta tace “Ina kwana?” Yace “How you feeling?” Ta gyada kai tace “Da sauki.” A hankali ta fara shan kunun tana tsoron kar tayi amai, cikin ikon Allah bata ji Aman ba, ta ajiye kusan Rabin cup tace ya isheta, mikewa yyi yace “Ina jiran ku a waje, you help me lock d door pls ga makulli a jiki” ya fadi hakan yana kallon nurse sannan ya juya ya fita, Khadijah ta bi sa da ido yana sanye cikin bakar suit da wando sai farar T-shirt da necktie banda kyalli bbu abinda cover shoe din kafarsa ke yi, nurse din ta kai flask da kunun cup din kitchen sannan ta fito tana kallon khadijah tace “Toh tashi muje” dafa kujera tayi ta mike nurse din na gaba ta bi bayanta har suka fita nurse din ta rufe kofar da makulli ta cire sannan ta tafi gun motarsa Khadijah na bin ta. Yana daga cikin motar ta mika masa ya karba yace “Shigo in rage maki hanya madam” nurse din tace “Toh” ita ta shiga gaban motar khadijah ta shiga baya, sai bayan sun fita gidan ya fito daga motar ya rufe gidan sannan ya koma ya ja motar suka bar layin, dai dai wani junction nurse din ta sauka tana masa godiya, kudin mota ta bata sannan ya ci gaba da tukinsa. Tun da suka fara tafiya khadijah ke jin xuciyarta ke tashi duk ta xama restless, yana lura da ita ta madubi bai dai ce komai ba, bayan wani lkci tace “Amai nake ji plss” yana kallonta ta madubi yace “Amai??” Toshe bakin ta yyi da hannunta da sauri, ya gangara gefen titi ta bude motar da sauri ta sauka ta dinga kwarara amai bakin hanyan, fitowa yyi ya tsaya jikin mota ya rungume hannu yana kallonta, ta gama Aman tana maida numfashi da kyar, bude front seat yyi ya dauko table water ya mika mata ta karba ta wanke bakin ta da fuskarta sannan ta mike kanta a kasa, ya nuna mata front seat yace “Shiga” a hankali ta karasa ta shiga ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga, kasa yyi mata da kujerar ya ci gaba da driving dinsa. Har suka yi nisa sosai a tafiyar bacci take, sudais dake kallonta lkci lkci ya gangara gefen titi yyi parking, suit din jikinsa ya cire ya rufa mata ganin sanyi take ji duk da bai kunna ac ba, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa. Sai da suka shigo traffic a kano ta farka, ya kalleta yace “Xa ki ci wani abu ne?” Da sauri ta girgixa masa kai, yace “Ko xa ki ci apple?” Shiru tayi tana kallon mai hawking apple dake tsaye gefen glass dinsa, ya dau suit dake jikinta ya cire kudi sannan ya mayar ya rufa mata ya sauke glass ya siya apples guda shidda ya ajiye kusa da ita, daya ta dauka ta kai baki a hankali gabanta na faduwa, taji bakin ta ba dadi ta dinga taunan Apple din a hankali tana tsoron kar ta ji amai, har ta ci rabi bata ji aman ba kafin su bar kano har ta cinye biyu daga nan kuma bacci ya dauketa. Khadijah bata sake farkawa ba sai da suka shigo garin kaduna kusan karfe uku, ganin ta tashi yace “Wani anguwa ne gidansu Aliyun yake?” A hankali tace “GRA” bai ce komai ba ya dinga driving a hankali sbda traffic, cikin minti ashirin suka shigo Gra, khadijah ta dinga yi masa kwatance har suka iso dai dai kofar gidansu Aliyu Sudais ya juya yana kallonta.

Back to top button