Hausa NovelsHausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 35

Sponsored Links

Asmy Mom Aydah??: 35

Washegari kusan karfe shidda da rabi na safe suka shigo parlorn Ammah,ya kalli Khaleel waxeer yana fadin”Yaya naje nayi mata sallama dan Allah,wani kallo Khaleel waxeer yake yiwa Aliyu,cike da jin haushinsa yake fa?in”ka dai je kayiwa uwar danka sallama,meye ha?in ka da nooryn yanxu,
Shaye da toka yake kallon Khaleel waxeer,
Dukan ku baxaku gane ba,Ni dai dan Allah ba dan halina ba,kasani ko kallon karshe xanyi mata, Khaleel waxeer ya hade rai yake fa?in”wai meke damun kanka Aliyu daga jia xuwa yanxu ka ambaci mutuwa babu adadi,idan kan gannin nooryn kake fa?amin wannan kalmar na amince ka shiga minti ukku kacal ka fito idan Ammah ta kamaka bbu ruwana baxan ceceka ba wlhi.”Khaleel waxeer ya fada yana nufar upstairs da sauri Aliyu ya cimmasa suka jera tare yana fadin,xan shiga dakin Ammah na jira .karka batamin lokaci da haka Khaleel ya tsaya kofar dakin Ammah ya fara knocking a hankali,shima Aliyu dakin nooryn ya nufa addu’a kurum Yake Allah yasa babu key jikin kofar,yana murdawa ya jita a kulle,zuciyarsa yaji tana yimasa nauyi,
Knocking ya shigayi a hankali ,tana zaune kan sallaya taji ana buga kofar,bata yi tunanin komai ba tama dauka Ammah ce taje ta cire key din gamida buda kofar,ta xare ido sosai tana kallonsa kokari rufe kofar take .ya saka karfi ya rike kofar da shanyanyun idanunsa,ma su cike da wata irin soyayyarta mai tsayawa arai Yake Binta da kalo tana sanye da Hijab har kasar mai kalar blue Black wanda yayi mata kyau,sakar masa kofar tayi ya shigo yaje ya sakawa kofar toilet key ya cire key din ya dawo ya xauna yana kallonta,dan Allah ba danni ba kixo ki xauna xamuyi magana mai muhimmanci Nooriyah,jin ya hadata da Allah ta shigo cikin dakin ta xauna acikin doguwar soofa ?in dake cikin Dakin ta wani hade rai,ya saki murmushin gefen baki yana fa?in”Madam Noory yau babu gaisuwa??bata tankasa ba bata ko kalli inda yake ba,dan samun kanta tayi da wani irin jin haushinsa,Allah -Allah take ya gama abunda ya kawosa ya bata wuri kar Ammah ta rutsasu,ganin Aliyu waxeer tayi durkushe a gabanta ya tankwashe kafafunta ,gamida kama hannayenta duka biyu.”da sanyin murya yake fadin har yau fushin dai bai kare ba??Ya fada yana kallonta,kokarin xare hannunta take cikin nasa.Ya girgiza mata kai yana fa?in”banda yau wife.”ban da wannan ranar,ya fada da wata irin murya wacce bai taba yi mata magana daita ba,ta dago tana kallonsa cikin shaddar filtex mai cliff ajikin hannun rigar,yayi mata wani irin kyau fuskarsa sai ta kara yimata wani irin haske,ta Turo baki gamida dauke kanta akansa,ka fadi abunda xaka fada dan Allah kabar min daki kar Ammah taxo ta samemu A haka…….”ki yafemin da dukkan laifin da na aekata maki da Wanda na sani da wanda ban sani ba,xanyi tafia ban sani ba xan dawo ko baxan dawo ba.”ya kai hannunsa akan shafaffen cikinta yana fa?in”kin ki bari na aje ajiyata a wannan shafaffen cikin naki,
Ta Runtse ido ita ko kadan bata son wannan maganganun nasa ,suna mugun kashe mata jiki ya saki hannun ya mike tsaye yana kallonta yana fa?in.”xan tafi pls kiyi min Addu’a a duk inda kike,xuciyata a kullum tana tare dake ta mike tsaye tana jin hawaye na cika idonta,ya russuna ya subbaci bakin ta hancinta goshinta,kafin ya jawota duka yayi mata rumfa cikin jikinsa.tana jin yarda zuciyarsa ke wani irin bugawa da sauri da sauri,sunfi minti biyu a haka kafin ya xare jikinsa cikin nata ya juya Yabar dakin da sassarfa ko waiwaye hankalinta ya tashi gabanta yayi wata irin bugawar da bata taba jin hakan ba,
Zama tayi acikin soofa tare da dafe kirjinta,
Jin take tamkar ta fadawa Aliyu kar yayi tafian nan bata jin natsuwa bata jin dai-dai acikin wannan tafiar,hawaye taji suna cika idonta lokaci daya,cikin soofa ta saka kanta ta fashe da kukan da batasan dalilinsa ba,da sallama ya shiga dakin Ammah Khaleel waxeer yayi masa wani kallo,da sauri Aliyu ya hade hannunsa wuri ?aya yana dan sakin murmushi,xama yayi yana gaisheda Ammah ta amsa tana fa?in”har kayi shirin tafiar kenan?”ya dago kansa yana kallon Ammah ,kafin yace yanxu xan tafi Ammah ki yafemin kuma kiyi min addu’a dan Allah ,duk da nasan Addu’arki na tare dani a duk inda na taka kafa,Ammah tace Allah ya tsare hanya
Karin kumallo fah?”
Ya shafa kansa yana fa?in,idan na isa xanyi nasha bakin shayi kin san idan xanyi tafia bana so naci Abinci mai nauyi,Ammah ta hararesa tana fa?in”toh naji Bature murmushi yayi wa Ammah, Khaleel waxeer ya rakasa har jikin mota ya basa hug side Yana Fa?in”ka kula da kanka dan Allah banda gudu da mota nasan halinka,
Ya daga kai yana murmushi yana fa?in”ka kular min da noory tamkar yarda xaka kula da kanka ,
Shigewa mota yayi sai da Khaleel yaga fitarsa shima ya dauki motarsa ya fita,sunyi waya da laylah ta fada masa sai zuwa 2 xata baro Abuja ta jirgi xata dawo,a yinin ranar daki tayi ta kwanciya
Ko abincin Rana bata shiga taya Ammah ba,itama Ammah bata takura taba,ta xata ma har yau ciwon kan ne.sai dai Ammah bata sani ba kewar Aliyu waxeer ta saka ta A gaba tunda ya tafi ko wanka ta Kasayi tana ta kwanciya a daki,
Sai da xa tayi sallar axxahar ta lallaba tayi wanka,koda na gama sallar samun kaina nayi da daga hannayena sama ina yiwa Aliyu addu’ar tsari da fatan nasara a duk inda ya taka kafafunsa,wata irin kewarsa naji ina yi wacce ke kokarin Kashe min jiki gaba daya,lambarsa na kurawa ido wacce na dde da yin blocking dinsa,bisa bin umurnin Ammah,xuciyata na yimin wani iri nake fadin ki yafemin Ammah ina so na kirasa ina son naji ya Isa lafia ko sau daya ne…….tayi magana da wata irin murya da haka ta bude lambarsa tayi dialling lambarsa ,sai dai bata shiga dayan lambarsa ta kira ta glo itama haka,a sanyaye ta sauke wayar,tana jin wani abu na dukan xuciyarta ,powder ta murxawa fuskarta kar Ammah ta gano tayi kuka,kasa ta sauka bata jin cin abinci,
Fridge din Ammah ta bude ta dauko robar Rufaida yoghurt Wanda suke cike da fridge kasancewar Ammah na yawan son fura,da wuya Ammah taci abinci tana shiga kitchen ne sabida masu aeki da kuma bakin da takan yi ,sabida Ammah mutunniyar jama’a ce tamkar wata yar siyasa haka mata ke cika gidanta sabida kawai taimakonta da jin kai ga tallakawa.
Cup cake din da Ammah tayi da dare ta ha?a dashi anan cikin kitchen ta xauna tana ci,anan Ammah ta sameta da mamakin take kallon ta haka tana kallon Ramar da tayi ,
Lokaci daya gaban Ammah ya fadi”ko dai noory tunanin Aliyu ya maidata haka karfa taje garin gyara a rasa ido,tun kafin aje inda takeso akae .nooryn ta fara gaxawa.Ammah ta harde hannu akan kirjinta ta dan hade rai,
Da serious Murya take fadin”wai nikam noory ki fadamin meye damuwarki naga sai wani kashin wuya kike axawa babu gairi bbu dalili.”idan ma Aurenki da Aliyu ne yake saka ki wannan Ramar kara ki farfa?o ki dawo hankalin ki,dama can Aliyu bawai yana sonki bane,taimakonki yayi kuma wanda akanyi auren domin sa ya riga mu cikawa ba sai ki sakawa kanki salama ba.Ammah ta fada cike da jin haushin nooryn,bar mata kitchen din tayi
Hawaye na xubar mata tabi kofar da kallo,taya xata fahimtar da Ammah bayin kanta bane,Allah ya dora Mata son Aliyu,a kullum tana kokarin ciresa a ranta sai dai ta kasa,tafian nan da yayi shi yafi daga mata hankali koda bata kula Aliyu ba a matsayin miji,ya kamata ta kulasa sabida gatan da yayi mata ita da danginta,
Jin tayi furar da cup cake din da take marmarin ci duka sun fice mata arai sabida maganganun Ammah,
Gashi ita ba wata abokiya gareta ba wacce xatayi sharing damuwarta daita,Kabir ne da suka tashi gida daya namiji ne duk yarda xatayi masa bayani baxai fahimci haka ba,sai kuma Aunty Ramlah waxeer ,daga Ammah sai ita a matsayin da ta basu na sunan uwa.toh ta kirata ta fada mata Ammah tayi mata iyaka da Aliyu ko yaya??”baxata iya wannan gangancin ba,tana cikin matsala sosai bari ta kira Aunty Ramlah waxeer ,kiran ta tayi Ammah ta dde tana ring Bata dauka ba
Kara kiran tayi cikin sa’a aka dauka.tare da fa?in”Aunty noory…..!”Inteesar ta fada da Muryar jin dadi ,wato yar Aunty Ramlah ta farko,kokarin dai-daita kanta tayi tana fa?in”intee ya kike ya makaranta,lfy lau Alhmdullh ina Yaya Aliyu?”yana lfy,
“Mum tana wanka idan ta fito xan fada mata,nima na shigo dakinta duba wani Abu na tarar da wayar na Ringing godia tayi mata tana fa?in”xata kira idan ta fito,kusan minti goma sha biyar ta kara kiran ,Aunty Ramlah tace kina ta kira ina wanka,yanxu ma ina kokarin kira kika kira.”ya gida yasu Ammah,noory ta amsa da suna lfy.”da haka kuma nooryn tayi shiru hawaye na xubo mata tana saka bayan hannunta tana sharewa,da mamaki Aunty Ramlah ke fa?in”hellow Nooriyah kina jina kuwa,eh ina jinki Aunty,Jin yanayin muryarta tasan da matsala,tace ya naji muryarki wani iri?lokaci daya noory ta fashe da kukan da ta kasa rikesa,haka Aunty Ramlah ta ta sauraren kukan nata bata katseta ba ,har tayi kukanta mai isarta ,cikin sanyi murya Aunty Ramlah ta kira sunan ta,bata yi magana ba sai dai tana jin Aunty Ramlah din,nasan Aliyu ne damuwarki kou.”nasan ko baki fada ba shine,dan Allah ki sassauta wa xuciyarki kiyi hakuri mubi Ammah yarda takeso,bafa cewa akayi ba idan babu Aliyu baxaki iya rayuwa ba,,na fiki sanin wacece Ammah,tunda har kika ga Ammah ta shiga tsakaninku keda Aliyu abu mai girma ne ya sata aekata hakan,
Kiyi ta addu’a kinji ina nan shigowa acikin kwanakkin nan. da sai wani sati xan taho xan jira Inteesar ta karasa jarabawar da take rubutawa Ammah saboda ke xan shigo cikin satin nan idan ta gama tabiyo jirgi ta taho,Amma dan Allah ki saki ranki kin ji.”Ammah tana nan tana yimaki tanadin wani Babban goro,wanda xaki rungumi Ammah kina daria da farin cikin samun miji mai nagarta kamarsa,Tana girgiza kai aranta take fadin”babu wani babban goro a duniar nan sai Aliyu waxeer ,amma a fili batace komai ba tayi sallama da Aunty Ramlah ta sauke wayar,yinin ranar Ammah bata shiga sabgarta ba ta gano Ammah fushi tayi daita sai taji duk babu ddi,,da yammah ta shige kitchen hada abincin dare Wanda Ammah tana zaune a cikin parlor tana aeki da laptop dinta ko kallo bata isheta ba ,haka ta kokarta tayi abincin dare a lokacin ta kira wayar Aliyu yafi sau talatin a kashe,
Bayan magrib Khaleel waxeer ya shigo gidan yana fadin,Ammah wayoyin Aliyu duka basa shiga munyi waya dashi lokacin da ya isa Abuja,tun daga lokacin ban kara samun wayarsa ba,ya fada min jirgin karfe shidda xai bi zuwa uk……”Ammah tace maybe baya da caji,
Laylah ta gaisheda Ammah ,Ammah ta karba tana fadin ya hanya yasu mamanta,
Ta fada mata lfiar su kalau,sai ga Areefa mansoor ta fito riga da wando ne ajikin ta wanda sun kamata ,
Kanta babu dan kwali,kallo daya Khaleel waxeer yayi mata Yabar parlorn,.
Da murmushi Areefa ta karaso tana fadin”sai yanxu kika iso?”da yanxu naje shirin tafia gidan ki sai naji Muryar mijinki a parlor, murmushi Laylah ta kirkiro ganin kallon da Ammah keyi masu,yasa laylah duk ta tsargu Areefa ta kalli Ammah tana fa?in .”Ammah kunyi waya da Aliyu duka lambobin shi a kashe,
Allah yasa lafia,dai-dai lokacin nooryn ta fito daga kitchen kallo daya tayi masu ta nufi hanyar stairs suka bita da kallo , Areefa mansoor ta tabe Baki tana fa?in.”kawata mu koma daki mana,sai da laylah ta kalli Ammah taga gaba daya hankalinta baya kansu tabi laylah dakinta, Areefa mansoor ta bude baki tana fa?in”ke ya naganki haka tamkar kina tsoron Ammah,
Ji yarda kike mata wani ladabi yaushe kika canja laylah??”
Laylah ta juya ido tana fa?in.”mekike so nayi so kike na rika yimata rashin kunya ko yaya.”
Ae ba haka ake kwantar da kai ba Areefa ,ina lallabawa da Aure na so kike auren ya mutu na rasa inda xanje??An fadamaki samun miji irin Khaleel waxeer yana da sauqi ne,
Kin san yarda kuwa Khaleel ke son mahaifiyarsa,kema da kina jin shawarana da kin kwantar da Kanki kinbi Ammah so da kafa ko a munafurci ne kuwa,ni baki ga son munafurci nake nuna mata ba da ladabi,ae ba a sake da uwar miji ko baka so ba kullum kake nunawa ba,ta karkashi akebi,laylah ta xauna cikin soofa ta kalli Areefa tana fa?in”bani labari nasha,ita kuma wannan shashar metake a gidan Ammah har yanxu ,bata koma gidan su bane??”an sha jan miya anki Abar waxeer family.Areefa ta kalli laylah tana fa?in”mu dawo baya da xancen mu,mubar wannan daga baya mayi dan karamar alhaki ce a wajena.”mekike fada na kwanta nayiwa Ammah biyayya??’ke yaushe kika fara yimata biyayya ,amma yanxu kika ko yeta kou.?”nina fada maki bana biyayya sama-sama ina yi mana,baki san waye Khaleel bane ,duk yarda xan fada maki shi baxaki gane ba Areefa aeni yanxu na danyi hankali yanxu haka so nake na samu ciki.wani kallo Areefa Tayiwa laylah ta tabe Baki tana fa?in Ni kuma baxan iya kwantar da kai ba kamar yarda naga kuna yimata sai kace wata sarauniya,ae nima ba a zaune nake hakan nan ba,ke mubar ma wannan maganar dan Allah duk kin batamin mood Dina ,yarda Yarinyyar nan xata bar waxeer family nake tunani laylah tace in dai ta wannan tsinanniyar ne xan taimaka maki na tsaneta wlhi!!”Amma fa kafin tabar waxeer family sai mun sha fama ,dan wani irin so suke yimata tamkar yarda suke yiwa Aliyu.
Hanya daya kawai ce xamuyi wannan aekin,yan daba xamu turo anan gidan mu fada masu kamanninta,su yaga shegiya suyi mata cin kaca da wannan budurcin nata ,dan Aliyu waxeer har yau bai karbi wannan budurcin ba,abu na farko da Aliyu xai fara haukacewa dashi wannan budurcin da aka karba,nasan halinsa nasan zafin kishin sa zai yi wuya ya kara ko kallon inda take,haka da kansa zai fitar da ita cikin waxeer Family,bana son ta mutu yanxu,
Bana tunanin mutuwarta nan kusa sai ta gama wulakanta ,taga dan dake jikina ya fito Muna renonsa tareda Aliyu bayan Auren mu ,ko wannan kawai zai saka xuciyarta ta buga.toh ya kika ga shawarar tawa laylah ta juya ido tana fa?in.”dadina dake akwai hangen nesa,
To amma wani hanzari ba gudu ba tayaya zasu shigo cikin irin wannan gidan,in dai ba wasa da rayuwar su suke sonyi ba.”Daria Areefa tayi tana fadin dadina dake wani lokacin banxan tunani gareki,an gaya maki hakanan suke zaune a banxa suma fa suna aeki da bokaye ,sai dai aekin su akwai kashe kudi sosai amma akwai biyan bukata ,
Plan Dina yanxu shine bana son komai da gaggawa zuwa jibi nake son ayi wannan aekin,naji ddin da Aliyu baya kasar zai iya bata shirin mu duka,plan Dina na biyu .,akwai wani abu da xan sakawa Ammah cikin ruwan shanta wanda zai bugar daita ta kama barci komai ihun da Nooriyah xatayi baxata jiba,yan aekin Ammah dama suna boys Quarters wannan
Aekin yaran da xasuyi mana aekin ne,da sun kallesu ko yatsan su baxasu koma dagawa ba,har su gama abunda xasuyi su fita daga cikin gidan.sai Khaleel waxeer mijinki nasan xai bamu matsala ,duk Rintsi karki barsa yaxo gidan Ammah duk yarda xakiyi ki kasance da mijinki a wannan daren,ki nuna masa soyayya mai tsayawa arai haka ki tabbatar wayoyinsa kin kashe su har taki wayar karki bari,ki fada masa kin shirya haihuwa yanxu nasan xai haukace da jin wannan xancen ,Abu na karshe xan baki wani maganin mata mai suna tafi xindir hajiata da safe sai kibani labari…..”shewa laylah tayi tana jinjinawa makircin Areefa ,da sauri ta rufe baki tana fadin bari nayi shiru kar wani yaji,kai har namatsu jibi yaxo,hirar su suka cigaba dayi cike da nishadi har bayan sallar ishaai suna zaune a dakin Areefa cikin su babu wanda yayi tunanin yin sallah,sai da sukaji hayaniya a parlor suka fita , Khaleel waxeer ne yake fa?in”yanxu aka nuna a labarai Ammah jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa uk ya fadi”kalmar da ta fito ta shiga cikin kunnuwan Noory kenan tana kitchen tana ha?awa Ammah fruit salad acikin bowl ta saki bowl din a rude ta fito hawaye na wanke mata fuska tana jin kafafunta na mata wani irin nauyi,
Dabas Ammah ta xauna acikin soofa itama da nata hawayen a fuska xuciyarta na tsanananin bugawa.da wani irin karfi tamkar xata fita sabida tashin hankali…

*Karki karanta min book idan baki biya ba idan kika karanta ban yafe ba..*!

Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Team#WM
ASMY#??
Team#NooryAli forever#??

masu neman maganin gyaran breast sadidan kumatso kuzo nazo muku d bull-bull breast powder nasamo muku hadadden maganin gyaran nono wanda muka hadashi d tsirrai d saiwoyi domin y’an uwa mata

Maganinmu sadidan ne bashi d side effects yana aiki cikin 1week y’ar uwa kinga result maganinmu guarantee ne yana ciko d breast suyi bul-bul nono koya Kai silifas tamushewa inshallah zaki ga canji maganinmu 3k ne muna garin kano muna tura sako kowane state da yardar Allah 08063114606
[9/15, 6:11 PM]

Back to top button