Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 42-43

Sponsored Links

Page 4️⃣2️⃣&4️⃣3️⃣
Aishan ADARA ne kwance Bata motse, cikin sauri Al’ameen ya Isa gareta yana kuka,don zuwa yanzun sun fara sanin ciwon kansu daga shi har Salim in,rungumar mahaifiyar sa yayi Yana kuka,don Allah Mami karki tafi ki barmu mami karki tafi ki barmu wayyo mamin mu yace Yana fashewa da kuka Salim Kam tsabar tashin hankali ciwon sa ne ya tashi,da sauri likitoti suka Kira baban Aisha dake waje a zaune yazo ya fitar da Al’ameen shi Kuma Salim Nurse suka d’aukesa zuwa wani gadon.

Sumayya dake kwance a kirjin Al’ameen kukane ya k’wace Mata hannu tasa ta Kara rungumar sa tana kuka,shikam gabaki d’aya jijiyoyin kansa sun mike sosai, kallo D’aya mutum zai Masa yasan ran maza ya tsogalu.

Kafun ya Kara bude baki, ji kawai sukaye kuka na tashi a bakin kofar d’akin su da sauri Sumayya ta mike hade da kamo hannun Al’ameen suka fitoh wajen tare

Khadija ce duke tana kuka fuskarta harta kumbura Alamu dai ta Dade tanayinsa kasa kasa sune dai basuji ba.

Yaya Daman gidan ADARA ba dangin mahaifin mu bane? Shiyasa suka nuna Mana launin fata,khadija ke tambayar yayan ta

Ah ah khadija ba saboda haka bane suke wulakanta mu dama can haka kaddarar Rayuwar mu take, kishare hawayen ki maza ki tafi gida

Ni wallahih Yaya inason Jin karashin labarin mu don Allah Yaya kaga ba Wanda ya taba ban Tarihin iyayen mu kullum na tambaye ka Koh Goggo sai kuce mu Marayu ne.

Al’ameen nada niyar magana Sumayya ta regasa”gaskiya ne khadija tayi girman da zata San abubuwanda suka shafeta especially irin wa’innan Tarihin”

Shikenan naji ana Kiran azahar bara nayi sallah Kuma kuyi Inna dawo saimu d’aura daga inda na tsaya,yace Yana Mai laluben buta

Da sauri Sumayya ta nufi butar dake zaune a Gefen baranda ta Mika Masa.

Alwala sukayi Sumayya kudi ta baiwa Al’ameen 1k in zai shigo gida yasai musu doya soyayye a bakin titi na 500

Ba musu ya karba ya fita
Bayan an idar da sallah Al’ameen doya yasai musu suka ci su ukun, duka a plate d’aya bayan Sumayya ta matsa musu don har lokacin khadija kuka take Kamar yau Abubuwan da suka shige ya faru.

Khadija inkin San kuka zakiyi toh Zaki bar gidan nan Banga amfanin kina kuka Kuma kice na cigaba da baki labarin ba kije ki samu wani damuwanne Koh me? Al’ameen ya fad’a ransa a bace,don shima dauriyane kawai

“Don Allah yayan khadija kayi Hakuri mutuwar iyaye Koh shikara d’arine zafine da shi”

Kayi hakuri Yaya,khadija tace tana share hawayen ta

Dukansu Basuci wani abin kirki ba Al’ameen Kam doya yanka biyu kawai yace khadija Kam ma tanaci Amai tayi saboda yanda take ajiyar zuciya

Bayan sun wanke hannunsu Al’ameen ya cigaba……..
Bayan mutuwar Aisha Alhaji ubangari yaso d’aukar su Al’ameen ya rike, Amma baban Aisha ya murza ido yace ba dashi ba Koh kudi ubangari ya baiwa su Al’ameen sai an mayar Masa da kayansa sosai abubuwa suka ma ubangari yawa don yanzun Koh fita zainab Bata iyyawa,tana fita ana nunata .

Khadija Kam, kanwar Aisha aka bawa wance ta h Bata jima da haihuwa ba ta shayar da khadija, Amma khadija Taki karban nono Sam sai madara,ganin Amina Bata taba haihuwa ba yasa baba karban khadija ya Baiwa Amina Amana.

Al’ameen sunyi matukar kewar iyayensu Wanda Salim yafi saka abin a ransa shiyasa kullum cikin ciwo yake don yanzun dai Al’ameen wani abokin babane ya ajesa a shagonsa Yana sayar Masa da kayan marmari duk Rana Yana biyansa,da wannan yake Tarawa su had’a da baba akai Salim asibiti

Duk da wannan d’awainiyar Salim Bai hanasu karatu ba a hakan Alameda yake zuwa makarantan gwannati Dayake lokacin duniya sanyi kalau ba kamar yanzun ba da ake kashiwa makarantan gwannati kudi.

Relationship insu da kamila ba abinda ya ragu kullum saiya rakata gida kafun ya nufi unguwan su sosai Abu kamar Wasa shakuwarsu ta Kara karfin sosai saidai kamila Bata taba zuwa unguwan dasu Al’ameen suka koma ba shine dai Mai zuwa gunta,

Ubangari Kam zaman jalingo ya gagaresa don lafiyarsa Dana zainab sai a hankali don yanzun saita kwana ta wuni Bata cewa kome makarantar ma yanzun Bata zuwa sosai rayuwa ta musu kunci,ganin Halinda suke ciki, yasa matar ubangari Kiran Yan uwansa ta sanar dasu abinda ke faruwa,

Aiko a yanda suka tarar da ubangari da zainab don har an dakatar dashi agun aiki ganin Halinda yake ciki yasa Yan uwansa Saida gidan da suke ciki suka tatttarasu dashi da yaran NASA suka koma garinsu,Daman aikine ya kawo ubangari jalingo, Wannan kenan.

Khadija taci gaba da samun kulawa Awajen Amina Alhamdulillah yarinya ta fara girma ga wayo sai daifa Sam Bata da jiki Yar firet da ita kyakkyawa sosai don Kamar ta da Yusuf ne sak shiyasa ita da Al’ameen Koh baka sansuba ka gansu kaga jini d’aya Daman Salim ne baki a cikin su don da Aisha yake Kama.

Zaman su a gidan Adara Bai sauya musu hali ba, da yake abin a jininsu yake sanyi Hali da hakuri Amma fa Salim akwai zuciya mundin aka Bata Masa Rai in fa baisamu ya Rama ba saiya kwanta ciwo.

Bayan wasu shekaru mahaifin Aisha dai ya kwanta ciwon kafa Wanda Koh kofar gida baya iyya fita Sai an Taimaka masa,
don haka Abubuwa sun ma Al’ameen yawa ga kudin maganin Salim ga D’an abinda yake D’an kaima Yar kanwarsa khadija ga zaman shago ga zuwa makaranta ga soyayyar kamila wanda yake jinta har ransa.

Haka baban Aisha yayita fama da ciwo har Allah ya d’auke ransa Wanda kafun ya mutu Saida ya jaddada wa yaransa Koh bayan ransa Bai yarda Yusuf da Salim Subar gidan nan Adalilinsu ba d’akinsa da yake ya bar musu halak malak, baya cikin gado, Wannan shine kalmarsa ta karshe Kuma itace sukecin Albarkacinta har yanzun suna cikin gidan ADARA.

Bayan mutuwar baban Aisha rayuwa fa ta zamo ma su Al’ameen wani iri Sam a gidan Adara Babu Mai taimaka musu Koda ta abinda zasuci ne,Dole tasa Salim shima ya fad’a Tashar marmari Yana ma wasu jiran Kaya suna biyansa,saisu had’a da kudin Al’ameen su fidda na asibiti su fidda na abinci su fidda Wanda zasu baiwa Amina ta rage d’awainiyar khadija,hakan yasa Al’ameen aje karatunsa don ko yaje makarantan baya fahimtar kome tsabar damuwa,

Ganin ya aje karatunsa Salim ma yaki zuwa makaranta ba yanda baiyi dashi ba Amma yake ganin Al’ameen ya matsa Masa yasa sa cewa Al’ameen,Yaya moha Koh naje makaranta asaran kudi zakayi tayi Kaine yafi cancanta Kayi karatu Koh don kanwarmu ta samu rayuwa Mai inganci

Jin Amsar da Salim ya basa Saida Hankali Al’ameen ya tashe cikin damuwa yace Masa,salim ban gane ba kana nufin Kai Babu Amfanin karatun nakane, ka sani Koh Kaine Mai rabon Tallafawa Khadijan?

Ah ah Yaya Kaine ya dace Kaye karatu don Allah badon niba Yaya ka koma makaranta nikam bazanje ba karatun ya isheni haka ya karasa maganar da kuka

Rungumar sa Al’ameen yaye shima sai yaji hawaye nabin fuskarsa don yanzun sosai sukayi wayo girma ya fara zuwa musu Kuma labarin abinda ya faru ya riskesu,sosai suka kullace zainab a ransu Kuma har abada bazasu manta da fuskarta ba.

Haka ba yanda Al’ameen ya iyya ya koma makaranta don lokacin ma ya Shiga SSS class yayinda khadija ta Kai shiga primary school da Taimakon Goggo Amina aka sakata

Soyayya Kam tsakanin kamila da Al’ameen tayi girma don har abin yakai ga iyayensu sunsan kome,don kamila Kam Amfara zama Yan Mata kowa yazo da sunan soyayya haka zata koresa itakam fa sai Al’ameen,sosai mahaifyarta ta tsani wannan mu’amalar Al’ameen da kamila ganin ba’a San Asalin ubansa ba haka zuriyan maman sa Yan Ta’adane,gashi baida wani kakkauran sana’a Koh inda zaisaka kamila,Amma haka kamila ta nace sai shi,
duk yanda zata zugata Koh fad’a Mata abinda ya dace kamila bataji Bata gani itafa sai Al’ameen.

Hakan yasa baban kamila Kiran Al’ameen don ya yaba da Tarbiyan sa ga nutsuwa, yace Masa zai basa kamila Amma ya dage yayi karatu in waec nashi yayi kyau,ya d’auki d’awainiyar karasunsa harya kammala shi Kuma ya Masa Alkawarin xai basa kamila.

Jin hakan sosai muhammad ya Kara dagewa da neman na kansa da Kuma karatunsa don sosai yanzun yake son kamila

Shekaru sunja lokaci ya tafi rayuwa nata juyawa yau Dadi gobe Akatsen sa,hakan take a wajen su Al’ameen

Ranar 3/8/2009 ranar da Al’ameen bazai taba mantawa dashi ba,yau ne suka kammala waec nasu gabaki d’aya makaranta kowa ka gani farin ciki ne d’auke a fuskarsa wasu Kam har kukan rabuwa da juna suke, don irin Wannan ranane Inka rabu da wani har abada bazaka Kara ganinsa ba

Haka take a wajen Al’ameen ranar farin cikinsa ne ya kammala karatunsa na secondary sai Kuma jiran result,farin cikinsa harda hawaye ganin yau ya Gama jarabawa Amma bayada Wanda zai zauna ya nuna Masa farin ciki Kamar yanda sauran daliban iyayensu ke Basu kyaututuka da walima na murnar Ranar

A hankali yake tafiya jikinsa sanye da uniform na makaranta Yana tafiya Yana tunane tunane rayuwa don a lokacin sun girma shi yanada shekara 18 Salim 15 Khadija 6

Ji kawai yayi wata mota Tasha gabansa kafun ya Ankara ma har sun Wasa Masa wani abu Bai Kara tuna Koh sanin inda yake ba sai bayan sati D’aya

D’aya bude ido ya jisa a asibiti Amma baya ganin kome sai duhu,Wanda yake zaune dashi shine Wanda ya tsintosa a bayan gari wajen kauyensu ya fitoh gona kenan yaga wasu sunzo sun yarda Al’ameen a cikin ciyaye,shine ya daukosa ya kawosa hospital da vajin jikin uniform NASA aka gane makarantarsu har labari yaje gidan Adara Amma Amina ne kawai da Salim suka zo asibitin Kuma suke kokarin jinyansa da taimakon mutumin da ya tsintosa,

Al’ameen sosai ya Shiga damuwa Daya waye gari baya gani gashi Doctor’s sunyi iyya binciken su Amma basuga ciwo ba shi Karan kansa Al’ameen bayajin kome a cikin idon nasa

Haka tun Yana kuka harya sadakar ya karbe kaddararsa,bayan makantarsa abin mamaki Koh da kamila ta samu labari batazo Koh duba Al’ameen ba sai abokansa na makaranta dana unguwan sune sukazozzo don ganewa idanunsu shin da gaske ne labarin da sukaji Al’ameen ya makance

shine da kansa Yakama Salim ya Masa jagora zuwa gidansu kamila Amma Koh ganinta basu samuyi ba duk abokansa yanzun basa son Koh zama waje d’aya tare dashi kowa gudunsa yake

Bayan waec ya fitoh Salim ne ya karbo Masa result,ya samu 9credit sosai Al’ameen ya rungume result nasa a kirji Yana hawaye,yaci buri akan result nan yayi karatu har bacci bayayi,Ashe ba rabon zaiga abinda ya samu ma da idanunsa sai an duba an fad’a Masa.

Rayuwa fa Tama su Al’ameen zafi don abinda zasuci ma ya zamo musu aiki sai salim ya fita ya nema kafun su samu gashi yanzun an sallame Al’ameen a shagon da yake zama don ganin baida ido duk yanda yaso su taimake sa zai iyya ciniki koda ba idone abin ya gagara

Bayan wata D’aya da makantar Al’ameen yaje gidansu kamila yafi kafa goma Amma kullum sai ace Masa Batanan,Wasa Wasa jikin Salim ya Tashi don ba’a je ganin likita ba har wata ya wuce,ganin ciwo yaci karfin Salim ga bamai taimakonsu, yasa Al’ameen neman taimakon yaran unguwa suka kaisa asibiti

Likita yace Masa wannan karon aiki za’a ma Salim gashe kudi masu yawane,sosai hankalinsa ya Tashi ga rashin ido gashi basuda abinda zasu Kama su sayar sai sarkanda mahaifinsa ya bar Masa Wanda shi kad’aine abinda yake gani a matsayen Abu Mai girma da muhimmaci a Rayuwansa Wanda zai buga kirji yace Awajen iyayensa ya gada,Amma baikai Dan uwansa ba muhimmaci ba.

Haka ya d’auki sarkan yakai kasuwa don a Saya Amma masu sarka sukace bazasu Saya ba gudun karsu sayi abin sata bare sarka Mai shaki Kamar Wannan Basu taba ganin sarka Mai zubinsa ba

Duk inda Al’ameen yasan zai samu a taimaka Masa yaje Amma babu Wanda yayi yunkurin taimakon sa har gidansu kamila yaje Amma Koh sauraron sa mahaifinta baiyi ba

Karshe dai Koran su akayi a asibiti ganin Basu da Koh sisi kullum Kuma kudin gado karuwa yake,dawowar Salim gida ciwo ya Kara Tashi gadan gadan,haka Al’ameen yanaji Yana gani jikin Salim na tsanani Amma Babu yanda zaiyi haka yake fama ga rashin ido

Yauma Kamar kullum suna kwance a d’akinsu Wanda kakansu ya mutu ya barmusu tun 1:00 na dare jikin Salim ya tashi ko rimtsawa Basu samu sunyi ba dukansu biyu Al’ameen na zaune Salim ya kwantar da kansa akan cinyar D’an uwansa sosai yake Aman jini Al’ameen Kam sai kuka yake Yana Kara tallafar Kan D’an uwansa Jin Aman da Salim keyi Yana karnin jini yasaka yatsansa ya lakuto Aman tsuntsunawa yayi tabbas jinine ba Wai ba,
ai da gudu ya fita tsakar gidan Yana kuka Yana bubuga musu kofa Amma ba Wanda ya taimaka Masa Asalima zaginsa suke,insun bude kofar,da gudu yayi waje.

gidan makwancinsu ya shiga Yana kuka ya ringa buga masu kofa,mutumin na budewa yaga Al’ameen ne,hakika yau yaji tausayin yaran da gudu ya Kama Al’ameen sukaye cikin gidan Jin Al’ameen nace Masa Salim na Aman jini

Suna isowa zuwa lokacin salim kam jiki yayi tsamare sosai haka mutumin ya cicibesa Al’ameen na binsa a baya sai tuntube yake Yana buga kafarsa saboda rashin sandar jagora Koh D’an jagora

A haka suka fitoh kofar gidan, aje Salim mutumin yayi yace bara ya d’auko machine su kaisa hospital

Mutumin na shiga gidansa Salim ya ringa Kiran sunan Al’ameen Yana tari jini nabin Gefen bakinsa,Yaya Muhammad !!Yaya muhammad zuciya na, zuciya na na ciwo Yaya kamin fifita zafi nakeji a jikina Yaya bana ganinka Yaya zansha ruwa kishi nakeji
gabaki d’aya Al’ameen ya rude iyya rudewa da gudu ya ruga yayi randar masallaci saboda rashin jagora, ya hadu da pol ji kake Gauu ya buga goshinsa jini ya balle Masa duk irin azabar da yaji hakan baisa ya kasa tashi ba haka ya mike a daddafe yayi randar masallaci dumbulo ruwa yayi Yana kuka Yana sauri ya karaso kusa da Salim tsungunawa yayi ya d’ago kansa jikinsa na rawa Jin Salim ya daina kakarin Amai gashi kansa yayi nauyi daker ya d’agasa ya d’aura akan cinyarsa lalubar bakin salim yayi ya kafa Masa mod’an Amma Ina ruwa baya tafiya sai bin Gefen bakin yake Yana zuba,dagajin haka Al’ameen ya k’wala Kara

Yayi daidai da lokacin mutumin ya fitoh da machine da sauri ya karaso gunsu Jin ihun Al’ameen

Yana zuwa cikin hanzari ya haska su idonsa ya sauka akan Salim kwance ido ya kafe a sama jiki a sake Wanda Koh ba’a fad’a ba yasan lokacin Salim ne yayi Innalilahih wainnailaihir rajuun kalmarda ta fitoh a bakinsa kenan

Aiko Wannan kalmar ita ta Kara tabbatar wa Al’ameen lallai ya rasa kaninsa, a karo na uku Yana rasa mutanen da sukafi soyowa a ransa, farin cikinsa,duka a gabansa suka Amsa Kiran mahalincin su(Allah Kasa mu cika da imani,muyi kyakkyawan karshe)

Ji kawai mutumin yayi Al’ameen ya Fad’i timmmmmm………….

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

🍀 *Na tsunguno(habil)*
🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

Contact them vie
🪀08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
free book 🤧

Back to top button