Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 55

Sponsored Links

Bude mata motar Aliyu yayi yana kallonta, ta ki kallonsa tana dai tsaye kamar me contemplating ta shiga ko kar ya shiga, a hankali ta karasa gun motar daga karshe ta shiga ya rufe, sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar. Sai da suka hau saman titi yace “Wani anguwar kike?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Tun da Maryam ta gaya maka gidanmu daya da Dr Ayman nasan ai baxata rasa gaya maka address da house number ba” Murmushi kawai Aliyu yyi yana ci gaba da driving dinsa bai ce komai ba, sai da suka iso street din ya kalleta yace “I only know the street….” ta fada masa number din gidan, yana isa dai dai gidan yayi parking yana dubanta yace “Wani schl din Shureim ke xuwa Iman?” Sai a sannan ta kallesa tace “I don’t think I have to tell you” Yana shafa kansa yace “It isn’t an offense ai Iman” ta bude motar ta fita tace “Thanks for the ride” murmushi kawai yayi ta wuce ciki ya bi ta da kallo, tabe baki Khadijah tayi ganin babu motar khaleel a garage ta fiddo makullinta cikin jaka ta bude kofar ta shiga ciki, wanka tayi sannan tayi sllh ta canxa kaya ta fito parlor, xaunawa tayi tana tunanin abinda xata girka, can ya mike ta wuce kitchen din, shinkafa da miya tayi deciding tayi sanin Shureim na son sa sosai, tana parboiling shinkafa taji shigowar motar khaleel gidan, da gudu ta fita parlor ta isa gun kofa ta sa makulli sanann ta koma kitchen ta ci gaba da abinda take, bell taji an danna, ta hade rai ta tura kofar kitchen din, ba a sake dannawa ba sai ringing din wayarta dake parlor ta ji, ta bude kofar ta fita ta dau wayar tana kallon screen din, ganin khaleel ke kiranta da har xata ajiye sai kuma ta daga ta kai kunne ta ki cewa komai, yace “Bacci kike ne?” Tace “What about that?” Yace “Ohk, naga takalman ki kin bari a waje, and ki fito ku gaisa da jawahir” Wani kallo tayi kamar yana gabanta tace “For what?” A hankali yace “Am waiting Khadijah….” daga haka ya katse wayar, mamaki ne ya cikata, a kan wani dalili xa ta gaisa da jawahir, tsaki tayi xata ajiye wayar text ya shigo nasa, ya budewa tayi tana kallon content din, “Plsss” abinda ya turo mata kenan, ta turo baki sai kuma ta harari kofar, a hankali ta isa gun kofar ta bude, tsaye ta gansa shi da jawahir din, suna hada ido jawahir tace “Sannu Khadijah ya gida?” Khadijah ta kirkiri murmushi tace “Lafiya lau, fatan kin xo lafiya” Jawahir tace “Alhmdllh, ya hakuri?” A hankali Khadijah tace “Alhmdllh nagode” kallonta kawai khaleel yake, Jawahir tace “Dama Dr yace in taho in maki gaisuwa ne” Khadijah tace “Ayya nagode, baxa ki shigo ba” khaleel na kallon jawahir yace “Shiga sai kiyi sllh” jawahir tace “Toh bari in yi” daga haka ta shiga parlorn Khadijah, ba tare da Khadijah ta kallesa ba ta rufe kofarta fuska daure, murmushi kawai khaleel yyi yana kallon kofar. Jawahir na kan darduma xaune parlorn Khadijah ta kawo mata abinci a plate, jawahir tace “Ayya na ci abinci Khadijah, am not hungry” Khadija tace “Haba ki ci ko kadan ne” Jawahir tace “Da gaske bana jin yunwa ki bar sa kawai” juyawa kawai Khadijah tayi rike da abincin ta koma kitchen, tana fitowa jawahir ta mike tace “Toh nagode bari in je” Khadijah tace “Welcm” daga haka ta fita, tana ji ta bude apartment din khaleel ta shiga, tabe baki Khadijah tayi, ta ja tsaki ta wuce daki, mayafinta ta dauko ganin Shureim ya kusa tashi a schl, tana fita apartment dinta ta sa makulli ta nufi waje, cab ta samu ya kai ta har makarantar, Rungume ta Shureim yayi bayan ya fito daga cikin makarantar yana kallonta yace “Anty me yasa uncle bai xo ba” Khadijah ta hade rai tace “Don’t ask me that again” daga haka ta kama hannunsa suka shiga cab din, suna isa gida ta biya mai cab din ta wuce ciki tana rike da hannunsa, sai kallon kofar khaleel take ta tabe baki ta bude kofarta ta shiga parlor da Shureim, makulli ta sa ma kofar, ta Shiga bedroom da shi ta cire masa uniform, tayi masa wanka ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi sanan ta sa yayi sllh, suka fito, a plate daya ta xuba masu abincin, tana ci a hankali tana kallonsa, muryarsa taji yace “Anty yaushe Sudais xai dawo? Umma tace min after one month, kuma ai one month yayi ai koh?” Khadijah ta sauke idonta daga kallonsa tana ci gaba da cin abincinta tace “Nima ban sani ba, sai dai anjima idan Umma ta kira ka tambayeta” ya langwabar da kai yace “Ohk” kallon wayarta dake ring tayi taga sabon number ke kiranta, ta dauka ya kai kunne, muryar Aliyu taji yace “Iman” a hankali tace “Na’am” yace “Fito ki amshi sakon Shureim din” kallon Shureim tayi tace “Ohk” daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon Shureim tace “Mu je ka rakani Shureim” ya tashi ta dauko plate ta rufe abincin, ta dau tissue ta goge masa bakinsa sannan ta dauko masa takalmansa ya sa suka fita, ba dai dai kofar gidan yayi parking ba, Khadijah na rike da hannun Shureim ta tsallaka xuwa side din da yake, daga cikin motar Aliyu ke kallonsu ko kiftawa babu har suka iso dai dai inda yayi parking, a hankali ya bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace “Uncle ka kai ni wajen mama plss” Aliyu ya dago kansa yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace “Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka” Shureim yace “Uncle plss ka tafi da ni” Aliyu ya kalli Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace “Thanks for coming out Khadijah” Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace “Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais…” Aliyu ya wara ido yace “Da gaske?” Yace “Yes uncle” ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace “Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu” Khadijah bata ce komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace “Ko xa ki raka mu?” Girgixa kai tayi tace “No way” daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike da makulin motarsa, ganinta yace “Let me go pick Shureim, na sha’afa wllh” a takaice tace “You don’t worry na dauko sa, Ni ban sha’afa ba” daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace “Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da mum dinsa a cafteria a schl” Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace “Kin tuna warce muka gani a cafteria jiya?” Deejah ta xaro ido tace “Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??” Maryam tace “Yauwa ita” da mamaki Deejah tace “Kar ki ce min ita ta haifi yaron nan?” Maryam tayi dariya tace “Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu” lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace “Allah sarki” Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace “but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa” Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace “Ke kuma meye haka? me ya faru?” A fusace ta fara magana tace “Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired” Maryam ta xauna kusa da ita tace “Toh fah, me kuma ya hada ku?” Mikewa Jawahir tayi rai bace tace “Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole…. Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan nata ne but now I am totally confuse….”
Deejah ta kamo hannunta a hankali tace “Kilan it’s not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?” Kamar xata yi kuka tace “Anty da kyar fa take amsa min magana idan na mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka” Deejah ta sauke ajiyar xuciya tace “But ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya” Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba, tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi, Deejah na kallonta tace “Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?” Maryam ta bude ido tace “A’a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu tare ba ko a schl” Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta ba Shureim, Maryam na kallonsu tace “Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba” Aliyu ya kalleta yace “Aa” Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake gabanta tace “Ka gaida mumy ka ji boy?” Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace “Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki” Murmushi Hajiya Mariya tayi tana shafa kansa tace “Toh ka gayar min da Anty son” Aliyu ta kalla tace “Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni” Aliyu yyi yar dariya yace “Ai Antyn nan sai a hankali ba xuwa xata yi ba” a hankali Hajiya Mariya tace “Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan” murmushi kawai Aliyu yyi bai ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace “Toh bari in mayar da shi mum, it’s getting late” Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo ganin sak mahaifinsa yana daga mata hannu, mikewa Maryam tayi ta bi bayansu, sai da suka fita waje ta kamo hannun Shureim ta durkusa tana gyara masa hular sweater dinsa tace “Darling ni baxa kace min bye bye ba” Dariya yayi yana kallonta ya daga mata hannu yace “Byee” mikewa tayi tana murmushi ta daga masa hannun ita ma sannan ta ce ma Aliyu sai ya dawo ta juya ta koma ciki, Aliyu ya sa Shureim mota sannan ya xaga ya Shiga ya tada motar ya nufi gida da shi, sai da suka kusa isa gidan ya juya yana kallonsa yace “Wani school kake xuwa Boy?” Shureim ya fada masa sunan makarantar, yace “Did you like the schl?” Gyada masa kai Shureim yayi, Aliyu yyi parking dai dai gidan yana kallonsa a hankali yace “Anty ce ta kai ka schl din?” Shureim yace “A’a uncle dina ne ya kai ni” Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba, can ya dauko wayarsa ya shiga kiran Khadijah, Tana xaune parlor tana karatu kiran ya shigo wayarta, tana ganin number ta gane ta daga ta kai kunne, Aliyu yace “ki d’an fito ki dau Shureim” Katse wayar tayi ta mike ta shiga daki ta sa hijab ta fito, kamar mai tausayin kasa take tafiya har ta isa inda motar Aliyu yake, fitowa yyi daga motar ya xagaya ya bude side din Shureim ya sauko da shi, Khadijah ta karaso ta kama hannun yaronta ba tare da ta kalli Aliyu ba tace “Sai da safe” Riko Hijab dinta yayi yana kallonta, ta juya suna hada ido gabanta ya fadi tayi saurin sunkuyar da kanta, murya can kasa yace “Sai da safe kuma? baki amshi sakon sa ba” Bata ce komai ba ya saketa ya bude bayan motar ya dauko babban leda ya dau ledan da Hajiya Mariya ta ba Shureim ya sa a ciki da ledan da yayi masa shopping duk ya hada su waje daya ya mika mata, karba tayi yace “Xa ki iya” Bata ce komai ba ta kama hannun Shureim ta fara tafiya, ya bi su da kallo, Shureim ya juya yana daga masa hannu, murmushi yayi ya daga masa hannun shi ma a sanyaye har suka wuce ciki. Manyan sweaters da head warmer ke cikin ledar da Aliyu ya bata na Shureim sai kaya kala hudu, ta bude daya ledan taga chocolates, biscuits sweets da dai abubuwan ci na yara, ta bude ledan da Hajiya Mariya ta basa taga lotions masu tsada da turare, tabe baki tayi ta mike ta wuce ciki da kayan, sai da ta ajiye kayan inda ya kamata a daki sannan ta fito da ledan chocolates din parlor, turus ta tsaya ganin khaleel xaune parlorn, ta dinga bin parlorn da kallo ganin bata ga Shureim ba, Mikewa khaleel yayi yana kallonta, sake ledan hannunta tayi ta juya da sauri xata koma ciki yace “Khadijah” tsayawa tayi amma ta ki juyowa, kawai ganinsa tayi gabanta yana kallonta, tayi saurin juyo masa baya, a hankali yace “Gaya min me na maki?” Ta turo baki tace “Toh ni na ce ka min wani abu ne?” D’an murmushi yayi yace “Saboda Aliyu kika canxa min Khadijah?” Shiru tayi ta rasa ma abinda xata ce masa, lkci daya jikinta yayi sanyi, jin shi ma bai ce komai ba ta juyo a hankali tana kallonsa, hawaye ya cika idonta tace “Me yasa xan canxa maka saboda Aliyu?” A sanyaye yace “Nima ban sani ba Khadijah” hawaye idonta ya xubo tace “Ko dai kai ne ka canxa min saboda budurwar ka” tana fadin haka ta fashe da kuka, kallonta ya dinga yi shi ma jikinsa yayi sanyi, da wani expression fuskarsa yace “Why? Why will I change because of Jawahir?” tana hararensa cikin kuka tace “Toh nima me yasa xan canxa saboda Aliyu?” Ya lumshe ido ya bude a hankali yana kallonta, rasa abin fadi yayi, har ransa yake jin kukanta, ya bude hannayensa cikin sanyin murya yace “Can… I console you?” Make kafada tayi ta juya masa baya, ya lumshe idanuwansa a hankali ya rungumota, cikin sanyayyan muryar sa yace “You know I love you Khadijah, and… I want you to be the mother of my kids, i want to marry you Khadijah, but you met me with Jawahir, I was with her before you, kin ga baxan mata walakanci ba saboda ke, jawahir na da saukin kai sosai, she don’t have problem, and I don’t want to betray her… Beside ita daban a rai na haka ke ma, Give me a chance to show you how much I love you plss Khadijah” kasa cewa komai Khadijah tayi, duk gaba daya jikinta yayi sanyi, jin tayi shiru ya juyo da ita a hankali yana kallonta, Bata yarda sun hada ido ba ta sulale nan kasa ta xauna, dukawa yayi gabanta yana kallonta murya can kasa yace “Say something plss Khadijah… Nace Ina son auren ki baki ce komai ba” Ta hade kai da gwiwa jin hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace “But Barrister Sudais….” Sai kuma ta fashe da kuka, ya dago kanta gabansa na faduwa, da kyar ya iya cewa “what about him Khadijah?” Tace “He proposed before you…” Shiru yayi yana kallonta ko kiftawa babu, a sanyaye tace “He said he want to marry me, and you know I can’t tell him no Doctor, aure ma bai isa na biyasa abinda ya min a rayuwa ba, he deserves more than that from me, though nasan 6 years back I will confess I was in love with him, but yanxu I only respect him as someone that brought light to my life after my Lord, sai gashi ya dawo yace yana son aure na, baxan iya cewa bana son Sudais ba, baxan iya cewa baxan auresa ba, but I am afraid of his wife” shi dai khaleel bai ce komai ba, kana ganinsa kasan jikinsa yayi sanyi sosai, mikewa yayi a hankali bayan few seconds yace “Ohk then, Khadijah, Allah yasa hakan yafi alkhairi, wishing you all the best” daga haka ya juya xai fita ta tashi da sauri hawaye na sakko mata tace “But I know I love you so much Dr, bayan Sudais you are the next in my life, da ba don kai ba da ban san abinda xai sameni ba few months back, you made me lively once more in life, may be….” sai da ya isa bakin kofa ya juyo yana kallonta ya katse ta yace “Forget I did that to you Khadijah” daga haka ya fita, ta bi sa da ido xuciyarta na bugawa.

Back to top button