Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 1

Sponsored Links

Waminal Hoob_* 1

PAID BOOK
Free page.

_Asmy b Aliyu_

A fusace ta nufi stairs da axamarsa ya cimmata gamida fisgota ta fada kan jikinsa,farar fuskarta ya kurawa ido.Wanda yana daya daga cikin Abunda yakeso ajikinta,haka Allah yayisa A rayuwarsa yana son farar Macce.lokaci daya ta fara Tara kwallah a idanunta,kara narke mata yayi .cikin fushi take kokarin fisge hannunta,daukarta yayi gaba dayanta ya nufi part dinsa daita,kafa yasa ya tura kofar dama a bude take bai direta koina ba sai akan farar soofa ,kokarin mikewa take .ya xuba mata blue Eye’s dinsa,Wanda yasan sune weakness dinta.Hannu ta saka ta koina tana kai masa duka take fadin”I hate you .”I hate you Aliyu waxeer!!””ta fada da dukkan karfinta hawaye na Rolling akan face dinta,Dora kanta tayi akan kafadarsa tana kara volume kukanta,Sam shi baya jure kukan macce ko kadan,ya tsani kuka…..
Ya rike kyawawan hannayenta yana murxawa a hankali ,cikin sanyi muryarsa yake fadin. “I miss you my girl,
” you did not tell me xaki xo ae.”ya fada yana Dan daga kafada gamida Dan buda kyawawan idanunsa,wata irin harara take yimasa da fararen idanunta Wanda suka fara canja kala.sau nawa Haidar?””Har sai yaushe xaka daina wahalar da xuciyana.”muna gari daya,na dawo Hutu ka kasa xuwa ka dubani.sai nice xan rika biyoka naku gidan,nice xan rika daga waya na kiraka nice mai xuwa hira gidan Ku.wannan wace irin soyayyace marar tsari.?”ta fada cikin sanyi murya,Dan karamin bakinta ya kaiwa kiss ya saki murmurshi gefen kumatunsa duka suka lotsa..fuskarta ya kara kaiwa kiss yana fadin”Am sorry my girl friend my one and only.”ke kinsan baxan shareki ba haka kurum ina busy ne kuma Bestyna ya shigo gari ,harara ta shiga watsa masa cikin shagwaba take fadin”Dama nasani ka fison Farhaan Shagari akaina,da karfi ya shiga fadin “Nooo kowa matsayinsa daban,duka ina sonku wlhi,ya fada yana Jan kumatun ta tamkar wata Bby haka ta rika turo masa kyakkyawan bakita.ya mikar daita tsaye yana fadin mu fita yawo yau tym dinki ne….

? ??
Baki sake Mami ke binsa da kallon takaici,kallonsa ya mayar kan daddy Wanda yaki yace komai.sai ma jarida da ya dauka gamida saka farin gilashinsa mai karawa idanunsa gani,salati Mami ta shiga xubawa tana fadin anya kuwa kanka daya Farhaan?”tayi maganar a mugun fusace,shuru yayi batare da ya kalli Mami ba…….Ya rabbi Allah yasa mafarki nake,Allah yasa ba gaskiyya bane Mami ta fada tana rufe idanunta Dan tabbatarwa,tana buda idanunta taga farhaan xaune agabanta.” Farhaan gobe ka shirya kayanka kabar kasar nan,
Wlhi baxaka kunyatani ba,shekarar ka talatin da biyu fah.”yayunka duka mata ne,kaine kawai nake dashi da xan jingina a kafadarsa nayi alfahari dashi a matsayin Namijin da ya fito daga cikin tsatsona,Farhaan ba yanxu nakeso kayi aure ba,,ka fahimta ina son ka xama wani Abu a rayuwarka,ina son ka kasance cikin manyyan attajiran da xaa rika gogawa dasu a kasar nan,me malami ya fada maka.”kasan dai halin dangin ubanka kou.”bawani kaunata sukeyi ba,kuma duka Rabin su a karkashin companyn mahaifinka suke aiki,,Allah kadai yasan cutar da ake yi masa.”idan ma Hajia Yasira taji baxata ji ddi ba,ji yarda take son kaxama surukinta ,nan ba da jimawa ba Idan Alh.Azzex Ali ya hau kujerar governor shi xaa tsayar da ixinin Allah.,Allah kadai yasan irin alkhairin da xamu samu.”ka mayi shuru da wannan maganar kar aji a waje ayi mana daria Dan Allah.”ya dago da idonsa da suka kada sukayi ja yana kallon maminsa yana mamakin ta yana karawa,
Akan wani ra’ayinta marar tushe…..kiyi min rai Mami,ya fada da wani yanayi a muryar sa gidan su noor sunce ta fiddo da miji Idan ba haka ba xasu aura mata duk Wanda sukaga dama.”su Aura mata mana me ake da gayyar talakkawa ,dama baka rabu da wannan matsiyaciyar yarinyar ba,,idan mafarki kake ka farka.tana nuna sa da yatsa cikin natsanin fushin da bai taba gani a idanunta ba take fadin”idan kana son kanka da lafia Farhaan shagari ,inhar ni na haifeka na dau cikin ka watanni Tara nayi nakudarsa,karka kara kawomin xancen yarinyyar nan,batayi Isar da xan hada jini daita ba.”Farhaan shagari tun daga kansa har yatsan kafarsa yake hada gumi duk da sanyin split dake ratsa falon,haka Mami ta tsallake sa cikin fushi tabar masa falon…Ya juya kan Alh.Omar shagari Wanda har lokacin yaki yace komai akan xancen……dajan duwawu ya karasa gaban mahaifinsa ya rike kafafun sa gagam,hawaye na xubar masa yake fadin”Daddy kayi min rai idan ban samu Noor ba mutuwa xanyi wlhi.”ka fahimtar da Mami hakan Dan Allah,shafa kansa daddy yayi yana fadin”kayi abunda mahaifiyarka keso Muhammad, nan shima daddy yabar masa falon,dafe Kansa yayi Wanda ke baraxanar yimasa ciwo,ya rasa waya’nne irin iyaye Allah yabasa masu akidar nasara……

???
Wani mugun kallo Aliyu kebin Farhaan dashi,Ahankali ya shiga girgixa kai yana sakin murmushin da shi kadai yasan ma’anar sa.da alamar bakada hankali Farhaan ka samu tabin kwakwalwa,
“Ni kake tunanin naje na auri yarinyyar da kake so har na tsawon shekara daya.”Aure ta kurane Farhaan Shagari ko kusa ban kawowa kaina Aure nan kusa ba,,kaima kaji xaka iyane yarinyya duk tabi ta wani shanyeka sai kace manyya.” Kama daina wannan maganar ko nayi fushin da ban taba yimaka irinsa ba,ya fada so pissed up yana hade rai,Farhaan ya lankwasa kai yana kallon Abokin nasa da idonsa da suka fada lokaci daya,
“Nasan nooryna bata cikin kalar matan da kakeso ,nasan ba ajinka bace,nasan baka sha’awar (BAKAR MACCE).”
Nasan ka nasan natsarinka Mr.Aliyu waxeer galadima.Abokin ka xakayiwa wannan alfarmar,da xarar na kammala masters dina xan dawo gareta muyi Aure.”Nasan karatuna shine burin Mami ni kuma burina na mallaki Noor,xan mallakawa Mami duk abunda takeso.”nima xata barni na Rayu da wacce nakeso,xan saka Noor makaranta bayan Auren Ku ina son Noor ta samu ilimi sosai,nasan baxaka ci amanata ba xaka kular min da Noor fiye da yarda xaka kula dani idan ina kusa.”girgixa kai Aliyu ya shigayi yana fadin ka haukace Farhaan wallahi ka haukace…!”

PAID BOOK
ASMY#??

Haske Writer’s Association #
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *_Waminal Hoob_* 2

PAID BOOK
Free page.

Back to top button