Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 97

Sponsored Links

Page 97

“Sorry mommy…..bafa dake nake ba,da uncle dina,oh mijina,da mijina nake magana” widad din ta fada kanta tsaye,idanunta cikin na hafsat.

Wani abu mai nauyi hafsat din taji kamar an aza mata,kanta ya buga har tana jin wasu sautuka cikin kunnuwanta,ita widad din yau take kalla kai tsaye…..kuma kai tsaye,ido cikin ido take gayawa haka?,a gabanta take kiran abbas da mijinta?.

Kafin ta yanke abun yi har widad din ta soma qoqarin zame jakarta daga hannun abbas din,saidai yaqi cika mata,ganin yaqi cika matan saita juya ta fara takawa tana nufar sassanta,tana jin zuciyarta na mata qunci,batasan me yasa mommyn mimin keson shiga harkarta ba,bayan ita ko ganinta batason yi,batason su hada inuwa guda da ita, infact haushinta ma takeji,musamman lokuttan da zata gansu tare da uncle dinta.

Sanda hafsat din ta yunqura da nufin fita a motar tabi bayan widad din abbas yayi gaba,sai tayi mutuwar zaune tana binsa da kallo tare da son ganin inda zaiyi,zuciyarta na wani irin bugawa,tana fatar ba bayan widad din xaibi ba,yadda ta zata hakance ta faru,sassan widad din ya shige.

Tana shiga ta zare dankwalinta ta aje saman kujera,itama ta haye kujerar wayarta na hannunta tana ci gaba da chat dinta,duk da ranta a bace yake sosai amma batason tabar idanunta da suka tara hawaye su zubda qwalla.

Daga bakin qofa ya tsaya hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya zuba mata ido yana kallonta,qamshinsa ya sanyata gane ya shigo,ta daga kai sau daya ta kalleshi ta maida kanta ga chat dinta,qaramin murmushi yaso subuce masa,yana saurin karantarta fiye da kowacce mace a duniya,ya gane fushi takeyi amma batason nunawa,amma kuma shi bashi yayi laifin ba amma abun yana son qarewa a kansa,sai ya tako ya iso gabanta,ya zame a hankali ya duqa saman qafafunsa,ya riqe hannayenta da take chat din dasu yana duban qwayar idanunta

“Tashi mu tafi weedad……” Ya kira ainihin sunanta a tausashe,kawai tana daga kai suka hada ido dai kuka ya kufce mata,ya matse hannayenta gam cikin nasa yana jin wani abu na masa suka cikin zuciyarsa,bayason kuka sam,kukan ma kuma nata,bai hanata ba sai datayi kusa minti goma tana yi,sannan ta zare hannunta daga nashi ta dauki dankwalinta ta nufi bedroom dinta.

Binta yayi da kallo,bai taba zaton zata bisun ba,amma ga mamakinsa sai gata ta fito,ta wanke fuskarta fes ta sake shafa powder da lip gloss,ta zizarawa fararen idanuwanta kwalli

“Muje” ta fada fuskarta babu walwala,yi yayi kamar baiji ba amma idanunsa suna kanta,har zuwa sanda ta tako tazo dab dashi xata wuce sai ya matse mata hanya,ya kuma sanyata cikin jikinsa

“Bakya kyau da fushi baby doll,smile please” ya rada mata a kunne,a hankali murmushi ya kubce mata tana dan boye fuskarta.

Tuni ta gama cika ta batse,duk inda bacin rai yakai ranta yakai qololuwar zuwa wajen,sau biyu tana aika mimi tayi kiran daddynsu sai tace qofar na a rufe ne,gashi tashi yanzu wuya yake mata,har sai data yunqura zata fita taje da kanta ayi wadda za’a yi,sai gasu sun fito.

Sanda ta kalli fuskokinsu ji tayi qafafun ta sun riqe,haka abbas din zaiyi mata?,fuskar widad din kamar ma komai bai faru ba,ta shaqa iya shaqa,sai taji kamar numfashinta xai dauke,dole ta kauda kai daga kallonsu,wata zuciyar na bata shawarar ta fice a motar kawai tace ta fasa zuwa,amma sai wani sashen na zuciyarta ke gaya mata,idan tayi hakan ai kamar taci galaba a kanta kenan.

Fuska fs muryarta duka wasai tana tsokanar mimi daketa shirya beads masu dauke da alphabet nawwara na watsa mata,ta buda gidan bayan ta shige,taja yarinyar jikinta ta kama hannunta tana tayata saka beads din tare da warning nawwara cikin wasa kan kada ta sake ta taba musu.

Tsantsar baqinciki da bacin rai ya hana hafsat din magana har suka isa asibitin aka sauketa,taso bar musu yaran duka amma nawwara taqi sai mimi ce tabi widad din.

Abinda bata sani ba kwata kwata yara basa damun widad,hasalima ita din mayyar yara ce,ko hana mimi zuwa tayata kwana da takeyi hakan baya mata dadi kwata kwata,ita kadai tasan yadda taji,baya ga dan uban tsoron dake bibiyarta harda kewar yaran.

Kamar ko yaushe zama yayi a waje ya jirasu har aka gama,wannan karonma mimi ta samu albarkacin widad din,an wanke mata kan tsaf,yarinyar sai murna take tana shafa sumartata tana kallon widad

“Anty ashe da dadi” sarai widad ta fahimci me take nufi,tana nufin kanta yayi mata sawai,kuma ta tabbatar iska mai dadi yanzu tana shiga kan.

Tunda suka iso gidan,tun basu shiga ba gaba daya aka saukar mata da bacin rai da baqinciki,taji kamar ta cewa abbas don Allah kada ya shiga ya koma da ita,haka ta dinga qoqarin dannewa har ya saka kan motarsa cikin gidan.

Tana tsaye daga bakin window tana hangen komai dake faruwa cikin gidan,don haka tana hangen sanda ya ajjiyeta ya koma,ta jijjiga kai tana sakin labulen falon.

Da daren ranar ta dinga tsoron kada abinda ya faru xuwanta na qarshe bauchi ya sake maimaita kansa,idan ta runtse ido saita bude,ba motsin komai ko alamu na faruwar wani abu,daga baya tayi dukka addu’o’inta don haka ta samu relief sosai,saidai gidan gaba daya taji ta tsaneshi,tsananin tsana ta gasken gaske,a lokacin taji bata da wata buqata data wuce tabar gidan,bata da wata buqata data wuce ta ganta ba cikin gidan ba,haka ta dinga yawo tsakanin falonta zuwa bedroom,sai tayi kamar zata fita saita koma bakin qofa ta zauna ta fashe da kuka,kusan awa uku tana a wannan halin kafin daga bisani bacci yayi awon gaba da ita a nan bakin qofar a yashe a qasa.

*W A S H E G A R I*

Yadda parlor din yake fitar da sassanyan qamshi mai dadi,hakanan jikinta yake fidda nashi salon qamshin daban,girkinta ne ko ba girkinta ba,wannan duka bai dameta ba,kusan qamshi da tsafta sun zame mata gaado idan ana gadonsu,tun daga hannun ummu kawo yanzu.

Ita daya ce a parlor din,kwance cikin doguwar kujera mai cin mutum biyu,wani doguwar rigar material onion color ne a jikinta mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai sassalkar sumarta mai tsaho baqi da santsi data dameta cikin robber band,sai qyalli take saboda gyaran kan da taje shekaran jiya, hannunta wayarta ce,sunata hira da balkisa,bata jin dadin zaman ita daya,yau gaba daga ko dauriyarsa mimi ba,abinda bata sani ba hafsat dince ta hanata shigowa kwata kwata,ita kuwa koda wasa batayi gefan hafsat din ba,indai ba dalili bane ya hadasu a farfajiyar gidan,suna iya gama kwanakinsu duka basu hadu ba,hatta da gaisuwa da take zuwa mata a yanzun ta ajjiyeta gefe,idan sun hadu su gaisa,idan basu hadu ba fine,ta bawa bilkisa labari, bilkisan tana ta tsokanarta

“Sanda nace ki daina gani kikayi kamar sabo nayi ko?,yanzu fa?” Dariya kawai tayi,its har ga Allah zafin hafsat takeji,batason ma su faye haduwa,data gayawa balkisa dalili sai da tayi dariya sosai

“Anya widad,anya kuwa?,wannan zazzafar soyayya mai cike da kishin tsiya da akewa uncle?”

“Kishi kuma anty?”

“Qwarai da gaske” ta jima a ranar tana son gane banbanci tsakanin kishi da kuma abinda takeji akan hafsat din.

Sake gyara kwanciyarta tayi tana jin yadda gaba daya cikinta yake a cushe,duka cikin kwanakin nan bata jin dadin cikinta da jikinta sam,sai tajishi kamar a kushe,mararta babu dadi,amma saita danganta hakan da rashin zuwan period dinta da take saka ran ko yaushe zata iya ganinsa,tun tana lissafi da xuba ido harma ta share taci gaba da harkokinta hadi da cewa cikin ranta

“Wai meye ma don baizo ba zan damu?,nima na huta da takurarsa” har zata gayama abbas saita fasa,tana tsoron kada yace suje asibiti,daga nan ace sai anyi allura.

Tsayawa tayi da replying massage din da takeyi sanda sassanyan sound din data sama wayarta na musamman saboda shi ya shigo

“Baby uncle” shine sunan da tayi saving dashi, qaramin murmushi ya kubce mata saman fuskarta,bata gajiya da ganinsa,duk sanda zata bar kwana sassansa hafsat ta karba tana jin raunin zuciya sosai,tana jin kamar ta riqeshi ya barta tayita kwana,amma bata iya hakan.

Karbar jakarsa data gani daxun hafsat tayi ta kuma bishi sassansa ya fado mata a rai,saita tura baki sannan ta daga wayar a shagwabe tayi masa sallama.

Hannu yasa ya buda qaramar qofar dake jikin sashensa,wadda take bullo dashi zuwa parking lot na gidan,shi daya yake amfani da ita time to time,ya soma takawa a hankali yana fita daga sassan,sanye cikin wani yadin kaftan na maza,qafarsa sanye da lafiyayyen baqin half cover na maza qirar kamfanin aldo mai asalin kyau da tsada,kansa babu hula sai gyaran da yasha,komai nashi fes yana zuba qamshin nan nasa mai aji da daukan hankali.

Ya tabbata don hafsat bata nan ne,don bayan ta ajjiye masa abinci ta fita sashenta,kafin ta dawo ya shirya ya fito ko abincin bai tsaya ci ba,don gida zashi,akwai dan zama da zasuyi meeting shi da yayansa da yayyensa mata.

Idonsa ya lumshe,wani abu na tsarga masa sanda tayi masa sallama da shagwababbiyar muryarta,kwanaki biyun da zai cikashe a yau ba tare da ita ba sun masa mugun nisa,jinsu yake kamar shekaru biyu

“Kina ina baby?”

“Ina parlor”

“Okay,ki sameni ta qofar bayan part dina,fita zanyi”

“Okay sir” yadda ta fada cikin shagwaba da kuma salo na girmamawa dole yabar murmushi saman labbansa,ya zare wayar ya jingina da motarsa da ya saka sale ya wanketa kusan tun safe,idanunsa akan hanya yana jiran fitowarta.

Dakinta ta shiga tayi fitsarin daya cika mata mara,tana ta mamakin yawan fitsarin da takeyi yanzu akai akai,har ta gota madubinta ta dawo da baya,ta dauki turarenta ta sake fesawa sannan ta dawo parlor din ta zura slipper dinta ta fito ba tare data nema dankwali ba.

Tar harabar gidan take da wadataccen haske,wannan ne ya bashi damar hangota tun daga nesa,ya zuba mata idanu kamar ko yaushe yana kallonta,wani abu mai sanyi yana ratsa zuciyarsa,canji yake gani daga widad din da gasken gaske,murjewa takeyi tana sake ninka kyau da farinta

“Fatabarakallahu ahsanul khaliqin” ya samu kansa da furtawa yana shafa qirjinsa da hannunsa saitin zuciyarsa.

Dab dashi ta tsaya,ta langabe kai tana kallonsa, murmushi ya saki yana gyara tsaiwarsa,irin wannan kallon nata,duk sanda ya gani yasan zaisha rigima ne

“You look so good baby…..You look so cute,bansan yadda zan fasalta miki ba” dan murguda masa qaramin bakinta kadan tayi

“Duk ban yadda da wannan dadin bakin ba, kwalliyar ka kaima yau tayi yawa,ina zakaje?” Mamaki da dariya suka tuqeshi,yau itama zata rama kenan?,gefe daya kuma tana nufin kada ya fita yaje wajen wata?.

“Wajen hajajju zani ranki ya dade,na rantse babu inda zani daga nan” yadda ya rantse mata din yana daga hannuwansa sama alamun surrender ya bata dariya,ta tuntsire da dariya shima yana tayata,kafin daga bisani ya gyara tsaiwarsa yana dubanta

“Me zaki kaima yaa baraka na gudunmawa?” Fararen idanunta dake dimautar dashi ta juya sannan tace

“Na baka zabi,ko zabamin kome kaga ya dace,sai nakai din” folding hannayensa yayi yana kallonta, sosai ta bugeshi kimarta tana sake cika masa zuciya,sai ya tuna yadda sukayi da hafsat dazun da safe,kai tsaye ta nuna kudi zai bata,ya bata din kuma ta karba abinta,yasan halinta farin sani,bashi da tabbacin kuma zata kai abinda yakai kimar abinda ya batan,kansa ya jinjina ya buda baki zaiyi magana,saidai kafin yace komai hafsat ta bayyana a wajen from no where,daga shi har widad babu wanda yaga tahowarta bare isowarta wajen,tana isowa kuma babu inda ta nufa sai kan widad gadan gadan,batayi wata wata ba tasa hannu takai mata shaqa tana fadin

“Yau sai kinci ku******mar ubanki,zaki gane ke qaramar ‘yar iska ce” cikin sauri da kuma tsananin tsoro widad din ta kauce,saita sake kai mata cafka,dai dai sanda abbas yayo kanta yana daka mata tsawa

“Ke hafsa,meye haka?,kina da hankali kuwa?,me kike yi haka” ko sau daya bata nuna ma ta jishi ba bare ta dakatar da abinda take shirin aiwatarwa,burinta kawai ta cimma widad din ta ida nufinta,cikin wani irin zafin nama ya isa garesu ya kuma shiga tsakiya yana duban hafsat din cikin wani irin mummunar bacin rai da zaka jima baka ganshi kan fuskarsa ba.
[3/22, 8:25 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button