Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 90

Sponsored Links

Page 90

Tun kafin su qarasa gaban motar tasa idanuwanta akan widad,a lokacin bata kula dasu ba,sai da suka kusa da ita,iska ta fara debo mata qamshinsa,saita lumshe idanunta tana sauraren bugun zuciyarta tare da dakon isowarss,qamshin nasa na daya daga cikin ababen da ko a bacci zata iya tantancesu.

Data waiwaya sai ta gansu su biyu,haka kawai taji ba dadi,saita dauke kanta ta dauki wayarta kafin su qaraso ta fara dannawa,hakan ya bawa Hafsat daman qare mata kallo da kyau,wani bahagon kishi na dukanta

“Kada fa dan hakkin data raina yazo ya tsone mata ido” ta fadawa kanta da kanta sanda take qarewa gefan fuskar widad din dake kwance da wani gashi mai santsi

“Anya kuwa batayi kuskure ba data gaza rabasu tun a farkon tafiya?” Ta sake tambayar kanta,da qyar ta hadiye wani abu mai tauri,taja ta tsaya kafin su qarasa tana yin magana da abbas din

“Kasan dai akwai ragowar kwanaki na akanka” dubanta ya danyi, mamaki ma take bashi idan tana zancan kwana,kamar ta wani bashi muhimmanci,ya furzar da iska daga bakinsa

“Na gaya miki amma uzuri ne ya taso ko?” Kai kawai ta gyada tana maida dubanta ga widad daya hakimce a gaban mota,zuwa yanzun ta zura earpiece a kunnenta ma.

Mintunan agogon wayarta take ta kalla tana lissafa mintunan da sukayi a tsaye shida ita,tanata qoqarin danne abinda yake taso mata harta gaza,ta daga fararen idanunta masu girma,ta sake sauke glass din motar,a shagwabe ta kira sunanshi

“Uncle……don Allah ka taho mu tafi……naaaa gajji”

“Kambu” Wasu tagawayen duka qirjin hafsat yayi,sautin muryar widad din sai ya zame mata kamar saukar ruwan dalma a kunnenta,yayin da ta fusgi hankalin abbas sosai,har dai daya sauke wata qaramar ajiyar zuciya da hafsat din ta jiyota har tsakiyar kanta,wannan ya sabbaba mata maida dubanta kansa cikin sauri ba tare data shirya ba.

Wani irin kallo da ita daya ta sanshi cikin idanunsa ta hanga kwance cikin idanuwan nasa yana yiwa widad din shi,wani malolon abu ya tokareta,dukka juriyar da takeson gwadawa ta gushe

“To uwarmu,saiki saurara mana,ko sallamarma bazamuyi ba?” Ta fada da madaukakin sauti tana duban widad din da wani irin kallo,kallo daya widad din tayi mata ta dage glass din motar,gab da zata kammala rufewar ta daga yatsunta tayi masa sign na i love you,hafsat din bata gane me ake nufi da hakan ba,taga dai ya saki siririn murmushi,sannan ya maida dubansa ga hafsat din da takejin kamar ta taka zuwa gaban motar ta fusgo yarinyar.

Cikin nutsuwa ya miqa mata tattausan hannunsa alamun musabaha,wannan kusan dabi’arsu ce shida widad,sai tabi hannun da kallo

“Amma dai kasan ni ba namiji bace ai” murmushin da bai shirya ba ya qwace masa,ya manta ba widad bace,sai ya matsa gabanta kadan yayi kissing goshinta yaja baya yana mata sallama,yayin da widad daga cikin motar tana hangesu,saita tura baki gaba tana jin haushin abinda yayi mata.

Har abbas din ya shiga motar ya tayar hafsat tana tsaye tana kallonsu,sai da suka fice daga gidan sannan ta koma sassanta da sauri kamar zata tashi sama,yau tabbas dole ta hadu da anty ummee,koda ba anty ummeen ba dole ta nema abokin shawara,tana jin alamu da qamshin lalacewar komai anan kusa idan bata sake daura damara ba,ta gaji da wanna pretending din,gwara ta fito sak a mutum ko zatafi qwatar ‘yancinta tare da nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace,ba kuma sa’ar yinta bace ita.

Juyawa yayi yadan kalleta kadan jin tayi shuru,tunda ya shigo motar batace komai ba,sai yaga titi kawai take kalla,ya motsa kadan ya saka tafin hannunsa cikin nata ya riqe da kyau cikin taushi

“Ba dai shikenan ba,kin hanani zama ko?” Daman jira takeyi,saita turo baki

“Bayan harda kiss dina ka yiwa mummyn mimi” sosai dariya ta kamashi,ya dan daki sitiyarin motar yana dan dubanta

“Wato kiss din ma naki ne…..wai…..yaushe kika koyi qorafi haka ne babyn uncle?” Fuska ta hade bata ce komai ba,ya sake sakin murmushi

“Yaushe kika koyi kishi ne baby?,Ita kiss dinki nayi mata,ke kuma uncle din kika dauke gaba daya,ba shikenan an raba ba?” Murmushi tadan saki ta jijjiga kai

“Good,yanzu bani labari,me dame za’a yimin idan mun koms,kinsan nayi missing dinki…..nayi missing abun nan…..” Ya fada ba tare daya qarasa ba,saita juya tana kallonsa,girarsa daya ya dage mata tare da kashe mata ido,abun ya bata kunya sosai,sai ta rufe fuskarta da hannuwanta tana dariya,shima ya tayata dariyar idanunsa na kallon titi.

Ko wanka bata tsaya yi ba,saboda tana ganin kamar zai bata mata lokaci ne kawai,ta canza kaya ta canzawa nawwara pampers,ta kada kan yaran ta zubasu a motarta suka wuce gidansu.

Kallonta kawai mamanta takeyi sanda take gaya mata duk irin abubuwan da suke faruwa

“Amma su uwa sun ha’inceni,keda duk da wadan nan matsalolin cikin gidanki amma kike zaune haka kina amfani da gurguwar shawarar ummee?,don ta kai mata ke lallai ne takai mikin?,bari na kira hajiya shuwa naji wanne malamin zata hadaki dashi” ta cire wayarta dake kusa da ita a chargy ta soma neman number din.

Kamar hafsat tace abarsa,duk ds yadda matsalar take damunta,amma dai sai ta kanne tana sauraren mamar tata sanda suke gaisawa da hajiya shuwa din.

Tana zaune tana sauraren umman nata tana yiwa hajiya shuwa bayani,bayan ta gama suka shiga tattanawa,kusan minti talatin sannan sukayi sallama,ta dubi hafsat

“Baki da wata matsala,itama kanta fadan zaman da kikeyi takeyi,tace yanzu ai ba’a zama,kada kiga wai yarinya qarama,idan batayi ba magabatanta zasuyi mata,bare sadakar yalla?,ai sai addu’a kawai,shu’umai ne” kai ta jinjina tana jin abun yana damunta har cikin zuciyarta

“Yanzu kudi kawai zaki fito dasu,sai mu saka rana mu sameta,tunda baya gari ma komai zaizo da sauqi”

“Kudi kaman nawa?” Ta tambaya tana duban umman nata

“Daga dai dubu dari zuwa sama”

“Za’a kaiwa malamin?” Hafsat ta tambaya tana dan riqe da habarta

“Eh,har miliyoyi ma ai kashewa akeyi,ita ranar biyan buqata rai ai ba’a bakin komai yake ba” janye hannunta tayi tana gyara zamanta,itakam bata jin ko naira dubu goma zata iya fitarwa,kudin da take fadi tashin tarawa rana daya ta wafci wani abun a ciki ta fara kaiwa wani suna raba dai dai,koma ya fita ci

“Shikenan umma,ki bari idan na shirya sai ayi mata magana sai muje” wani kallo uwar ta watsa mata,dama tuni labarin yadda ta baci da son abun duniya yake zuwa mata

“Kudin ne ba zaki iya fitarwa ba kenan?,ko a jikinsa ba zaki tarasu ba hafsatu?,gwara ki zauna da damuwarki kenan?” Kai ta girgiza

“Ni ba haka bane umma,kawai dai matsalar batayi girman da zan kashe wadan nan kudaden ba,mu bari kawai anty ummee din tazo nasan tabbas akwai mafita daga wajenta,basai an kashe komai ba” haushi takaici da baqinciki suka cika umman,saita dauke kanta gefe tana cewa

“To ai shikenan,sai kici gaba da zama har sai sanda matsalar ta girmama ta zama babbar”.

***********Tunda suka koma ta tattara ta watsar da batun mommy hafsat din ta shiga sabgoginta,sosai ta maida hankalinta ga karatunta koyon girke girke online da kuma practical classes da akeyi cikin garin kadunan.

Cikin lokaci qalilan ta zama expert,hannunta ya sake fadawa,ta kuma qware da kalolin abinci masu dama.

Zamu iya cewa batason so ba,amma tana jin wani abu mai qarfi akan uncle din nata,wanda inda da cikakken wayo kai tsaye zata fahimci soyayyarsa ce ta fara kafa kanta a zuciyarta,sam bata iya wuni guda cikin nutsuwarta muddin baga ganshi ba,kowanne lokaci burinta shine tayi abinda zaice

“That’s my baby…..ma sha Allah baby wannan yayi……baby doll inason abu kaza,babyn uncle wannan yayi dadi ko yayi kyau” wannan ya sanya ta sake zagewa da dukan iyawarta ta haddace abinda tasan yafiso yafi muradi,gefe guda anty deena da anty madeena harda hajja sun zage sosai suna wayar mata da kai dai dai gwargwado.

Ta gefan abbas kuwa abun har baya faduwa,wani irin wawan kamu soyayyar widad tayi masa,ta yadda shi kansa yake mamakin kansa,zuciyarsa ta koma sabuwa,tamkar bai taba qaunar wata halitta ba cikin rayuwarsa,yarinyar ta tafi da dukka zuciyarsa,ta kuma shiga rayuwarsa fiye da kima,har bayason wani abu da zai kawo su nisanci juna,duk da yana fama da shagwabrta sakalci da kuma wauta amma hakan sai ya zame masa kamar wani abun debe kewa,ya kuma zame mata ado,kasancewar bai saba ganin wannan ba.

A koda yaushe hafsatun na masa magana ne a tsaitsaye,tana kuma nuna masa ita din me wayo ce,bata da lokacin shagwaba ko karya murya,kamar yadda take ganin bai kamata ace mutum yana da wani choice a rayuwarsa ba na tsafta abinci turare sutura da sauransu ba,banbancin ra’ayi me girma da kuma tarin yawa ne a tsakaninsu.

Sabanin widad,da komai nata nashi ne,komai zatayi tana duba zai burge uncle?, uncle zaiji dadi?,hatta da shopping tana yinsa ne base on his choice,komai ta dauka saita tambaya cikin shagwabar nan tata

“Uncle yayi?” Wani lokaci yace baiyi ba,wani lokaci kuma ya barta da zabinta,ya zuwa yanzu bayajin akwai wani abu da zai iya shiga tsakaninsa da widad din,ta shiga rayuwarsa fiye da kima,ta samu gurbi a zuciyarsa sama da yadda kowa yake hange.

Tun daga wancan ranar ta rage binsa weeknd bauchi kwata kwata,koda ta bishi ma raba kwanan take tsakanin gidan hajiyan da kuma gidansu,dukkansu shi da hajiyan da suka fuskanci hakan yafi samar mata da nutsuwa sai suka rabu da ita.

Hafsat na gama kwananta baya iya jurewa,haka zai je gidan hajiyan da kansa yayita raragefen daukarta saboda kunyar hajiyan,abinka da uwa,takan bishi da murmushi ne kawai sannan ta sanya widad din shiryawa ta kuma bishi,a yanzun duk duniya tafi kowa samun farincikin canjin da abbas din ya samu,idan ka kalleshi da kyau zaka fahimci hakan,don har wata murjewa yayi,yayi ‘yar qiba,ba shakka ko ta iya fannin abinci kawai dole rayuwarsa ta sauya,saboda shi din mutum ne da baya wasa da cikinsa,sai Allah yasa widad din bata da wani fatinciki itin ta ganta cikin kitchen tana sarrafa wani sabon abu da basu saba ci ko basu taba ci ba,koda yaushe hajiyan godewa Allah takeyi da sauyin da abbas din ya samu,nutsuwa sosai tazo masa,duka matsalolin hafsat ma sai suka rahe damunsa,tunda ko ba komai akeai gefen da yake samun nutsuwa gamsuwa da kwanciyar hankali,inda widad din yakeso takai wanda bata qarasa kaiwa ba yanata qoqarin horar da abarsa cikin soyyaya qauna kulawa da kuma nutsuwa.

Gefe daya hafsat din itama bata sake tayar da zancan ba,saboda anty ummee ta kwabeta kan ta barta haka,kada a fahimci takunta,saidai akwai sabbin hanyoyin da zasu sake dubawa.

_wannan kenan_

*Masu karatu muje zuwa,akwai sinqi sinqin CAKWAKIYA a gaba*[3/20, 8:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button