Auren Shehu Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 1 Page 3

Sponsored Links

AUREN SHEHU

3

Ta na zama bisa gado ta ?au wayarta ta kira abokin zuwa club din ta da ta ke kira Bobo, bugu daya ya daga tare da fa?in

“Zeee oh Zeee the slay mama the club mama, diyar Malam ta ki halin Malam! Ai ni na san baki fushi Zeeena…..”

“Eh en fa Bobo!”
Ta katse shi, ba ta gushe ba ta kara da

” Kar ka wani dame ni da dadin baki! Da ka san masifar da ka kusa jawo min jiya da ka ji tsoran ?aga waya ta!”

“Toh yanzu dai Allah ya baki hakuri, ko da ya ke tun da ki ka kira ni ma na san kin huce, wetin dey sup? Malam don commot?”

Cewar Bobo cikin muryar zolaya.
“Ehen na, him don go Maid, toh ya za a yi? Any happening tonight? Amma dan Allah kar ka kai ni club din talakawa, ka san I can’t stand them!”

Ta fada ta na mai yamutsa fuska. Dariyar kyeta ya saki, fadi ya ke

“Heheheheh Zeeena na da?e ban ga wanda ya ke kyamkyamin talauci kamar ki ba, babe don’t worry I got you, ki shirya 12 daidai ta yi mi ki gaban gate din ku, na san dai yau ba batun haurawa tunda Malam baya nan”

“Ba ka da matsala, su Isa ne ai wa’inan, in su ka sa shayi gaba har na wuce ma ba lalle su sani ba, sai ka zo”

Ta na maganar ne yayinda Usman ya fado mata rai, ta na mai adduar Allah ya mata katangar karfe da shi, su ka yi sallama da Bobo ta aje wayar.

***

Kamar yanda ta saba duk sanda ta san ta kulla harkallar ta, ana isha’i ta fara kukan ciwon kai, daga Ammy har Falmat babu wanda ya kawo wani abu cikin ran su, sai ma tararraya ta da su ka din ga yi, musammam ma Ammy. Halitta kuwa ko kallan in da take ba ta yi, dan cike fal ta ke da Zainab. Ammy ce ta bata magani ta sha, ta ce lalle ta je ta kwanta, amma Zainab ta ce ah ah, gwara ta zauna jikin su za ta fi jin dadi.

Sai da ta bari goma da rabi yayi sannan ta ce ciwan ya ci karfin ta, bari ta kwanta dan Allah kada wanda ya shigo ya tada ita, dan idan aka tada ita ba lallai ta iya komawa bacci ba, gashi kuma dama ciwon kai ta ke. Ana bin ta da sannu haka ta mu su sallama, ta koma daki ta yi kwanciyar ta har da kashe wuta.

Da ya ke uwa uwa ce wajen sha daya Ammy ta kasa hakuri, sai ga ta a dakin, ganin wutan a kashe ya sanya ta yin sanda zuwa ga gadon Zainab, wacce jin shigowar uwar ta saki jiki ta yi lum kamar mai bacci. Hannun ta dora bisa goshin Zainab ta na mai hamadala, fadi ta ke

“Alhamdulillah ta sami bacci”
Ta na mai jawo bargo ta dada rufe ta. Sai da ta karanta mata adduar bacci ta shefa jikin ta sannan ta juya ta fita.

Ta na fita Zainab ta yi zumbur ta mike, dan kuwa ta san babu mahalukin da zai sake shigo mata daki tunda har Ammy ta ga ta yi bacci, bari ma kuwa idan akwai wacce za ta iya shigo mata munafunci Halitta ce, ita kuma sun yi fada toh ta tabbatar hakan ta ya cimma ruwa.

Wankan ta tayi ta fito tsaf cikin wondan ta pencil Jean blue tare da yar karamar riga ja, ta faka gashin nan tsakiyar ka kai ka ce ba diyar musulmai ba ce. Ba ta damu da yin make up, dan irin su Zainab ake yiwa kirari da “black beauty better than gold always shining”. Tsadaddiyar powder mai sanya fuska sheki ta shafa, turaruka kuwa 212 sexy, escada magnetism, tare da Indian night Jasmine sai da su ka koka.
Gaban madubi ta tsaya ta na mai karkada kugu ta ke yiwa kan ta kirari

“Zeee oh Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Dadyn ta”

Sai da ta yi mai isar ta, ganin sha biyu ta kusa ta sanya hijabi har kasa, bayan ta gama gyara gado, ta saita fululluka kai kace mutum ne kwance ta sa bargo ta rufa mu su, takalmin ta mai tsinin gaske a hannun ta na mai sanda ta fito. Ganin wutan falon a kashe ta san kowa ya kwanta, sadaf sadaf ta zaga ta baya ta fice.

Isa kuwa da Jauro masu gadin gidan nan gaban gate su ke kwance bacci ya sace su dan yau ko karnukan gidan ba su sake ba. Kallo ?aya Zainab ta mu su ta ja tsaki tare da fadin

” Ji be su kwance kamar mushe! Idan ma sace gidan za a yi wato a yi tunda Dady bayanan, Allah ya kai mu gobe za ku yiwa Ammy bayani!”

Ba ta kara tsorata ba sai da ta ga gate din bude, wato ko sakata ma ba su sa ba! Har ta juya a fusace za ta tada su, sai ta tuna tana tayar da su shikenan asirin ta ya tonu, ta na mai adduar Allah ya kare su Ammy ta sa kafa ta fita, hakan yayi daidai da dalle ta da tocilit da aka yi, yanda hasken ya dalle idanun ta ya sanya runtse idanun ta na mai fadin

“Oh my God”

Tsaye ya ke ya na duban ta, suna hira da su Isa bacci ya kwashe su, dan haka ya dan fita waje mike kafa. Kusan mitunan shi ishirin waje gaban gate, dake unguwar ba mai hayaniya bace sosai kafar mutane ya dan dauke, jin wani ni’imataccen kamshi ya sanya shi dan waige waige tare da tunanin ko dai aljana mai turare ce ta bakunce yau, wanda fitowar ta ya gasgata masa da haka, dan kuwa dai da ya haske ta ganin ta ya ke tamkar aljanar ce tsaye gaban shi.

Ganin ba a da niyar daina haska ta ya sanya ta kare fuskar ta da tafin hannun ta, cike da nuna bacin rai ta ce

“Dalla Bobo dena haska ni kafin ka sa a kama mu! Kai fa iskancin ka yawa gare shi!”

Jin haka ya sanya shi kashe tocilan ba tare da ya iya furta komai ba, dan kuwa harshen sa ya sarke kamar wanda aka daure harshen cikin bakin sa. Bude idanun ta tayi tare da fadin

“Bobo…..”
Ganin wanda ke tsaye gaban ta sai da ta dan ja da baya, shi din nan dai Usman, sanye da rigar saka da rawani irin na buzaye, hannun sa na dama rike da sandar gora, dayan hannun kuma tocilan ne. Ta na shirin juyawa ta koma sai ga motar Bobo, ai kuwa kafin Usman ya ankare da gudun ta ta nufi motar, ganin haka Bobo ya tsaya ta shige ta na fadin

“Kai let’s get the hell out of here, ina tsoran Allah ina tsoran wannan dan boko haram din can!”

Back to top button