Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 4-5

Sponsored Links

Bismillahirrahmanir rahim……

Free page 4 and 5🦋

Bugun kofar da akai da Karfine ya katsemusu hirarsu, TAHEER ne ya mike da Niyar bude kofar amma oumma ta tsayar dashi, “dawo taheer bari na bude” fita oummansu tayi suma mimmikewa sukai tare da bin bayanta. Yan gidan ne cike taf a wajan kowa sai faman zabga masu Harara suke , mazan gidan kuwa duk Wanda yaga taheera sai ya kara kallanta sai mafan satar kallanta suke sabamin matan dake harararta.

“Munafukan Allah muna furcin me kuke kullawa, bayan kunsan akwai ayyuka a gabanku, shine dan muna furci da kinibibi kuka shige daki dake da ‘ya’yan ki masu kama da tattabaru” cewar wata da tafi kowa za’kewa a cikin su. Zuba wa sarautar Allah ido taheer da taheera sukai wai sune tattabaru hmm . Hakurin da suka ji oumma na bayarwa ne yasa suka maida hankalinsu kanta ,” kuyi hakuri Dije bansan akwai ragowar aiki ba shiyasa”.
Matar da aka kira da dije ce ta Dallawa oumma harara “ kyaji da munafurcin ki, inba munafurciba ba me kuke kullawa a daki ko sallan karuwancin da kika saba kike koya musu” baki taheer ya bude daniyar yin magana amma kallan da yaga oumma tayi masane ya hanashi hakan , sun kuyar da kanshi yayi yana taunar lebensa. Wata daga cikin mutanan gidan ce ta soma magana itama “ kinsan dangin Matsiyata ba abunda suka iya sai tsiya in ba karuwanci take koya musu ba me suke yi a dakin”, nan da nan mutanan gidan suka fara musu gori da hantara , suna ci musu mutunci , kowa nagidan da abunda yake fada a kansu, kaka ta bawace kawai bata wajan . TAHEE da tunda aka fadi kalmar karuwanci idanuwanta Suka faru da ha waye ga wani irin ja da sukai, ba abunda ke mata yawa sai kalmar karuwanci ko magan ganun da mutanan gidan suke bata ji, wata gigitacciyar kara ta saki da ya firgita kowa dake wajan hatta taheer da ke kusa da ita, hannunta ya so kamawa amma ta hankadashi , daya bayan daya ta soma bin mutanan gidan da tun lokacin da ta saki ihu sukai shiru da kallo, ba Wanda ne tsure ba da irin kallan da take musu, ida nuwanta ne suka sauka a kan dije dake faman zare idanuwa , a guje tayi ganta , suna ganin hakan kowa na gidan ya Watse dan ba karamun firgitasu tayi ba daga mazan har matan. Wani murmushi taheer ya saki daman yasan za Arina, a zuciyarsa sai faman Allah shikara yake musu. Dije dake kokarin shiga daki tahee ta cafko, riko tayi mata ba na wasa ba , Innalillahi wa inna ilaihi rajiuna Dije take ta faman fadi , fuskar ta tuni ta jike da gumi sai faman zare ido take , jama’a ku kawo mun a gaji shikenan ni fatalwa ta kamani, kukai kawai Dije take majina duk ta bata mata fuska. Ita kanta oumma Dije ta bata dariya kuma ta bata tausayi dan Tasan kome zatayi yanxu TAHEE bazata hakura un tayi mata ta Karfi kuma rashin lapiyar tane zea tashi. Taheer ma dake gefe sai faman kunshe dariyarsa yayi ganin yadda Dije ke faman fadin fatalwa ta kamata. Kallan d tahee tayi mata ne ya sata kunshe bakinta “nayi shiru , Wlh nayi shiru” , tana gama fatar hakan ta rike bakinta gam hawaye na fita, Kwale idanuwan ta TAHEE tayi a kanta , take a wajan Dije ta saki futsari dariyar da taheer yake rikewane ta fito wajan dan ba karamun dariya ta basu ba. Baki TAHEE ta bude da nufin cizonta, lokaci daya kuma ta zube a wajan. Tana faduwa kuwa Dije ta arta a guje duk da kibarta a haka ta ke kudin tana tsine TAHEE a zuciyarta.
Daukarta taheer yayi shi da oumma suka nufi daki da ita,” maza dakkomun maganinta “ cewar oumma , be dade ba ya fito dauke da roba a hannunta, ruwan adduar dake ciki oumma ta iba ta dan shash shafa mata a jikinta da fuskarta, nannauyar ajiyar zuciya ta saki , nun fashinanta na Daidai ta .
Har yanxu akwai ragowar murmushi akan fuskar taheer , hararar sa oumma tayi” kasan Kai kadai ne zaka iya temakonta, me yasa baka temake taba kabarta a hannu tahee”, wani murmushin taheer ya saki” oumma kinsa konayi kokarin temakonta Nima hadawa zatai dani, ranta ya baci sosai ko nine naje wajan ba ragamun zatai ba “, jinjina Kai oumma tayi Alamar gamsuwa da maganarsa, wata ko daddiyar dari biyu ta dakko tare da mika masa” ungo maza jeka siyo mana kwaki da kyada nasan in ta tashi zata dan ji yunwa , nan yadda ka kalli kowa ba ko kace zaka musu wani abu nasan halin ka sarai, saura kace kaima zaka rama, in naji sabanin hakan ranka zai baci” jinjina mata kai yayi tare da amsa mata, dan tabbas ba hakura yayi ba amma yanxu ba yadda zeyi dadinshi daya tahee ta rama.

Kasancewar basu da nida da me ka tin ba dadewa ya dawo , har lokacin tahee bata tashi daga baccin da take ba. Ajje Garin sukai sai da ta tashi sannan suka hada, har lokacin fuskarta a hade take , ba Wanda ya kulata a cikinsu har suka kammala cin abincin, maganin dazu oumma ta mikowa tahee , tana bata rai ta karbi maganin a haka ta shanyesa.

Kiran sallar da ake ne ya sasu mikewa tare da dauro alwala, lokacin ta saki fuskarta kamar ba Itace tagama tsorata Dije ba, sallah suka kabbara tare da bin jam’i, bayan sun idan ne sukayi shafa’i da wuturi, sannan ko wannansu ya biya wa oumma haddar alqur’ani cikin natsuwa. Bayan sun kammala ne oumma ta kara musu arba’una Hadith da ahlari, sai da ta tabbatar sun gane sanna suka zauna suka fara hirarsu irin tasu sai faman tsokanar oumma suke kamar wata kakarsu. Ganin 11 tawuce ne yasa oumma ta umarcesu da suje su kwanta.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰
Karfe 2 ya farka daga baccin da ya daukesa, a hankali ya fara karanta adduar tashi daga bacci cikin daddadar muryasa, sanna ya mike kamar bayasan taka kafafuwansa. Toilet ya nufa be dade ba yafito kyakkyawar fuskarsa dauke da ruwa da Alama alwala yayi, duk da kasancewar dare ne hakan be Hana takunsa na mazantaka canzawa ba, inda shinfidaddiyar farar daddumar take ya nufa tare da kabbara sallah cikin nutsuwarsa,ya dade yana nafilfilu sannan ya fara karatun alqur’ani mai girma a hankali cikin daddadar muryarsa ne ratsa zuciya kamar karya dena .sai da ya kammala suratul bakara gaba dayanta , sannan ya fara adduoi cikin harshen larabcin da ya zauna a bakinsa, ko wace harafi na futo wa .

4:2 shine abunda agogon wayarsa ya nuna masa, lumshe fararan idanuwansa yayi da suka fara canza kala tare da mikewa, inda system dinshi yake ya nufa , ya dade yana operating a kanta , kiran da ake na sallar asuba ne ya katse masa aikin da ya fara a system din nashi, ajjeta yayi gaba daya tare da gyara zamanshi kamar Wanda bazai tashi ba sai kuma ya mike tare da nufar hangar da zata sadashi da bathroom dinsa. Be dade ba ya fito cikin wasu kananan kaya white colour masu shegen kyau, damtsen hannunsa ya fito sosai , yayinda budaddiyar rigarsa me shape din v ya futo da kirjinsa kadan , sosai kayan sukai masa kyau , yalwataccen gashin Kansa masu sheki da san tsi sun kwanta luff tare da harneda da sajan fuskarsa, sosai kayan sukai wa kakkarfar surarsa kyau , ba abunda yake tashi sai kamshim imperial majesty .

Masallaci suka nufa shida zaki bayan An idarne kamar kullum ya umarci zaki ya bawa liman kudi yayi Sadaka,kamar yadda ya umarceshin haka yayi liman sai faman addua yake masa. Direct gida suka koma bayan an idar da sallah , part din dake tsakiya zaki yayi parking , king kuma ya shiga part din. Zaune yake cikin fararan kaya , dattijon arziki kenan, uban marayu, fari shima amma ba kamar king ba, kana ganinsa kaga bafullatani dattijo. Ciki ciki king yayi sallama tare da nufar inda mutumin yake , amsa sallamar mutumin yayi  tare da zuba masa kyawawan idanuwansa irin na king, kawar da Kai king yayi tare da zama a kasa wajan kafafuwan mutumin . Ya dau kusan 5 minutes zaune a wajan bece komai ba shima mutumin bai tanka masa ba har ynxu kuma bai dena kallan nasa ba. Dakyar ya iya bude bakin sa cikin daddadar muryasa kamar Wanda aka sa dole,” ina kwana abeey, ya karfin jiki”, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da amsa masa , lapiya son , jikina kuma nayi sauki ai, am getting much better now “. Dago da kaifafan idanuwansa yayi yana kallan mahaifin nasa , kawar da Kai abey yayi daga kallan king ya maida kan jaridar dake hannunsa . Sallamar da akaine ya Hana king magana , akan kujeran falan suka zauna, daya daga cikin sune ya fara magana” yaya barka da Safiya”, murmushi Abeey ya sakar masa “ katashi lapiya musaddiq”, amsa wa yayi da “lapiya Lou “, shima na kusa dashi gaishe shi yayi abeey ya amsa cikin kulawa. Kamar be san da mutane a falan ba,ya dau kusan mintuna yana juya yadda zai fara , kafun ya soma magana ciki ciki” ina.. kwana uncles “ daga haka be kara cewa komai ba, duk cikin su babu Wanda be san halinsa shiyasa basu damu ba Suka amsa masa cikin kulawa . Mikewa yayi tare da kallan abeey” take care” , jinjina masa kai abeey yayi, yana gama fadar hakan ya juya tare da barin part din, da kallo duk suka bishi suna kara jinjina miskilanci irin na king .

Yana komawa part dinsa , Wanka yayi cikin tsada sun suit dinsa black colour da suka fito da ainayin kalar fatar jikinsa , black hair din sa da ya hade da sajensa sai faman daukan sheki suke , hannunsa sanye yake cikin diamond watches , har yanxu fuskarsa a hade take karamun pink lips dinsa ya kara turuwa sosai , sosai kayan sukai masa kyau danshi din kyakkyawa ne da baki bazai iya fassara wa ba , yanxu ma ta elevator ya sakko kasa, ko kallan dining din da aka cika da kayan breakfast bayiba, zaki ne ya bude masa kofar falan shima fuskarsa a hade take sosai . Wasu irin tsadaddun motocine jere a wajan sai faman kyalli suke , wata farar Mercedes’ benz aka bude masa , basu tsaya ko ina ba sai wani babban part dake cikin gidan.
Cikin daya daga cikin kayataccen chairs din falon ya zauna , daddadan kamshin turarensa ya mamaye ko wana turare dake falon bakajin kamshin komai sai kamshin imperial majesty. Sanye take cikin wasu cotton din kaya  masu laushi da sanshi, idanta sanye da farin glass sai faman mita take ita kadai, ganin wanda ke falon ne yasata tabe baki, “ nifa Adena zuwa ana takuramin, ina dalili Ance kayi aure kaki sai kazo ka tare min a daki da sassafe fisabilillah “, kara tsuke fuskarsa king yayi cikin daddadar muryarsa ya gaisheta “ Dada ina kwana , ya karfin jiki”, sallallami wacce aka kira da dada tayi , “yanxu fisabilillahi saraki zautacciya kamayar dani da har kakemun ya jiki!”to wallahi bari kaji, lapiyar da nake da ita ko ubanka baba tunanin yana da ita , bai kula taba Samm , dada kuwa sai faman mita take yace mata ya jiki,mikewa tayi tare da shiga wata kofa bata dade ba ta fito dauke da wani glass cup , ajje sa tayi a gabansa “maza maza ka shanye furar da kazo ka ka tattara ka Barmin daki”, ko kallan furar da ta ajje beyi ba sai da ya Mula dan Kansa sannan ya fara sipping din furar a hankali, furar tayi masa dadi sosai amma a zahiri sai ka dauka dole akai masa yasha,ko rabin cup din be shaba ya ajjeta “pray for me” , inma zagina Kayi kai da Allah “purey (pray ) din kawai naji,”Allah ya tsare ka dan Jikalle , Allah ya kawo auranka jibi jibi” tsuke fuskar sa yayi jin adduar ta ta karshe , diamond watches dinsa ya kalla tare da nufar hanyar fita daga falan Daidai lokacin da abeey da uncles dinsa ke kokarin shigowa,cikin tsokana uncle salim ya soma magana “wato kazo kacinyewa yar tsohuwarmu  abinci kabarmu da kanzo ko”, duk murmushi suka saki yayinda fuskarsa take a haden ta har ynxu , wani murmushin abeey ya saki dan Sarai ya gane be san surutun da uncles din ke masa, uncle musaddiq ma sai faman dariyarsa yake ,sallama yayi musu tare da nufar part din mahaifiyarsa, bakowa a kantameman falon , direct dakin da yasan zai sameta ya nufa, knocking din kofar yayi, shiru ba’a amsa ba na kusan sakanni kafun ta bada izinin shigowa, cikin nutsuwarsa ya tura kofar dakin tana zaune cikin shigarta ta kullum, garage kyakkyawa irin asali da kyawun larabawa, doguwar jallabiya ce a jikinta red colour me shegen kyau da tsada , stone din jikin rigar sai faman kyalkyali yake, wata farar yarinyace a jikinta fara sol me kama da king kamar an tsaga kara, sallama yayi tare da karasa shigowa dakin, dagowa yarinyar tayi da sauri tare da nufarsa “AKHI!! ANA FI AINTIZARIK MUNDH ALBARIHA(yaya!! Tun jiya nake jiranka) ta karasa fada kamar zata saka kuka, lumshe mata idanunsa yayi tare da shafa fuskarsa da kyar ya furta “ana asf habibaty ( am sorry sweetheart), “hasanan akhi’usamihuk( okay brother , I forgive you).
Zoya !! Matar dake saune ta fada , cikin kinkina ta amsa mata “naam ummey”, ala yumkinuk an tahyiah lam ‘udadhirk min dhalik( bazaki gaishesaba , ban ja miki kunne ba) cewar ummey, kamar zatai kuka tace “ana asf ummey( kiyi hakuri ummey), sannan ta mayar da hankalin ta Kansa “ana asf akhi, sabah alkhaiyr( am sorry brother , ina kwana), girgiza Kai Kawai yayi dan har ta fara sa masa ciwon kai.

Cikin Yaren larabci ya gaishe da ummey, ba yabo ba fallasa ta amsa masa, bayan gaisuwa ba wanda ya kara magana sai zoya dake faman yi masa surutu, mikewa yayi tare da yi mata sallama , bin bayansa tayi da kallo har ya bar part din ka fun sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Tun daga entrance din falan ya fara jiyo hayaniya na tashi sama sama , yana shiga ya tarar dasu zazzaune a falon sai faman kwasan dariya suke, ammi na zaune tana kurban tea . Sallamar da yayine yasa falon yin shiru, kamar ba kowa  aciki  sai faman zare idanu suke , ganin sunyi shirune yasa ammi dago da idanuwanta, wanda ta ganine yasa ta sakin murmushi ,daman nasan za arina ta fada a zuciyarta, dukansu sak kowa sukai daga kan kujerar da suke , sai faman muzurai suke , cikin hada baki yan matan saka gaishesa” yaya king .. ina kwana”, kallan da yayi musune yasa hantar cikinsu kadawa, be amsa musu ba sai ma tanbayar da ya jefo musu, cikin husky voice dinsa “me ya hanaku zuwa makaranta”, ko waccensu tsure wa tayi suna kallan ammi ta gefan ido ko zata sa baki,ammi kuwa sharesu tayi, fingers din hannunsa ya daga musu “10 minutes only”, a guje ko waccensu ta bar part din dan sunsan ammi ce ta cecesu da bata wajan da Sunansu sorry. Suna barin part din ammi ta kalleshi, kaji da di daka tarwatsamun yaya , be amsa mata ba sai gaisuwar da yayi mata, itama bea dade ba  yabar part din. Cikin wasu irin slow motocinnan suka fara fita, duk inda ya wuce sai kaga ana saramasa, suna hawa kan titi motocin suka fara gudu, sir ina zamu cewar zaki, ya dau mintu biyu kamar bazai tankaba sai kuma ya bude bakinsa” company “.

➰➰➰➰➰➰➰➰
Manage please abubuwane suka dan shamun kai..

Comment and share ✍️🫶

💖the talent troupe 🔥

Writers of ……

Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Sarki sameer
Jini daya
Ya fita zakka…

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖GIDAN AUNTY💖

By mss LEE

💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

PAID BOOK

Leave a Reply

Back to top button