Auren Shehu Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 2 Page 1

Sponsored Links

Auren Shehu 2

Afuwan akan rashin cika alkwari, aiki ya min yawa, a yi min hakuri.

 

Nan Kawu Iliya ya bar Usman da Bello ba tare da yayi kokarin rarrashin su ba, yana cike da tsabagen takaicin dauke kafa da Usman yayi daga Rugar Shehu. Sun kai kusan minti talatin gaban kabarin Mahaifiyar su, Usman gani yake tamkar ita din ce zaune kusa da shi. Sai da sauran matasan Ruga su ka zo su ka ja shi suna mai bashi baki sannan ya hakura ya ta so su ka nufi cikin Rugar Shehu.

Tuni labarin dawowar Usman ya zaga lungu da sako na Rugar Shehu, har ya ga kai kunnan Baffa Mudi, hankalin sa tashe ya zo ganin shin da gaske Usman din ne dan kuwa bai taba tsammanin zai sake taka kafar sa a Rugar Shehu ba bayan kurciyar da ya masa, babban tashin hankalin sa be wuce kar Usman ya ce zai kwaci sarautar Rugar Shehu ba dan shi kan sa ya san jama’ar Rugar sun gaji da mulki irin na sa.

A dandalin shadi ya tarar da jama’a sun taru makil maza da mata, Yara da manya, mata da maza, masu kida na yi, haka masu tafi, tsuffin cikin su kuwa kuka biyu su ke, kukan dawowar Usman da kuma kukan rashin Iyar sa. Cike da tsana da faduwar gaba Baffa ya tsaya gefe ya na duban duk abubuwan da ke wakana, ganin yanda Usman ya ?ara girma ya zama cikakken matashi ma’abocin karfi da kwarjini, ga matasa zagaye da shi, sai koda shi su ke, su na masa kirari da fulatanci, fadi su ke

“Dan Shehu jikan Shehu, karen bana mai maganin zoman ba na, Shehu ya tafi, Shehu ya dawo!”

Ya sanya Baffa Mudi barin wajen a fusace, cikin ran sa ya na saka yanda zai dauki mataki akan dawowar Usman. Shi kuwa Usman gangan jikin sa ne kawai a wajan, zuciyar wacce ke cike da bakin cikin rashin Iyarsa tuni ta yi nisa wajan saka yanda za ta hukunta wacce ta ke da alhakin rashin ganawar sa da iyar sa na har abada, Amma ya kudiri niyar fara raba Rugar Shehu da ummul abasin dalilin da Iyar sa ta tilas ta masa barin Rugar a karan farko, wato Baffa Mudi.

Duk yanda ya so ya kadaice shi kadai yayi makokin Iyar sa abin gagarar, mutane ke ta kai kawo cikin sashen su domin masa maraba da kuma ta’aziya. Haka kuma kishiyoyin Iyasar sa Yagwalgwal da Duduwa su ka sako shi gaba da mitar barin Rugar Shehu da ya yi. Ba shi ya sami kan shi ba sai bayan ishi’i, ya na shirin shiga bukkan sa sai ga yan uwar Mahaifiyar sa sun zo. Yayar ta wacce ake kira da Huwaila, sai kuma kanwar ta mai suna Iyalle, da kuma matar shi Kawu Iliya Hansai.

Sune su ka sa Usman gaba da fadan barin gida da yayi shekara da shekaru babu ko waige, har Iyar sa ta fadi ta mutu. Usman ya kasa musu bayanin umarnin Iyar ta sa ne ya sanya shi barin Rugar dan kuwa har lokacin be yi niyar tonawa Baffa Mudi asiri ba. Jin su na rokan sa da ya kaunaci Allah ya karbi mulkin Rugar Shehu, a cewar Huwaila wasiyar da Iyar sa ta bar ma sa kenan, ya sa shi tambayar ko da wani abun da be sani ba ne?

Nan su ka bude ciki su ka bayyana masa mulkin zalinci da Baffa Mudi ya ke aikata mu su, tare da sana’ar da babban dan sa Tanko ya shiga na garkuwa da mutanen birni ana biyan shi kudi kafin ya sake su, Kuma duka ya na yi ne da sanin Baffa Mudi. Matukar ba so ya ke a maishe da duk matasan garin yan garkuwa da mutane ba, har gwamnati ta gane ta turo a ayi kan mai uwa da wabi toh lalle yayi wani abu.

Cikin bakin ciki da jimami su ka tafi su ka bar Usman, ba su dade da fita ba sai ga dattawan Rugar Sheshu su ma sun iso gare shi da irin bukatar da dangin Mahaifiyar shi su ka zo da shi, cewar su dan babu yanda za su yi ne da tuni sun bawa Muhammadu Bello sarautar Rugar Shehu, ya duba girman Allah ya fanshe su daga wannan ukuba da su ke ciki, Allah ne ya dube su ya dawo da shi.

Cike da girmamawa Usman ya sallame su tare da mu su alkawarin zai kwana da maganar cikin ran sa, in Sha Allah zai samar mu su mafita.

Sai da kafa ta dauke sannan Usman ya sami damar shiga dakin Mahaifiyar sa cikin faduwar gaba, gani ya ke kamar zai gan ta kwance bisa gadon karar ta. Har lokacin dakin cike ya ke da kayan ta kamar ta na raye. Duk yanda ya so daurewa kasawa yayi, Yana mai rungumar zanin Iyar ta sa hawaye ke fita daga idanun sa, haka ya zauna bakin gadon ta ya ci kukan sa ya koshi, be fita ba sai da ya daukarwa kan sa alkwari biyu, na farko shi ne tabbatar da cigaba da yancin Rugar Shehu ta hanyar karbar ta daga hannun Baffa Mudi kamar yanda Mahaifiyar sa ta bar masa wasiyya, na biyu kuma shi ne Zainab, ya yi alkawarin sai ta yi da na sanin zama silar rashin sake ganawa da mahaifiyar sa har abada, zai iya yafe komai amma ban da wannan.

Washegari tun kafin Usman ya je in da Baffa Mudi ya kafa fadansa dattawan Ruga su ka tada bukatar Baffa Mudi ya bawa mai mulki mulkin sa, dama ya kan yi ikirarin rashin Magajin Shehu ya sanya shi zama kan mulkin, toh Allah ya dawo da magajin Shehu.

Nan fa Baffa Mudi yayi kyememe ya ce be san zance ba, mulki ya rigada ya koma gidan sa, saboda haka be da wani magaji da ya wuce Tanko, in Sha Allah kuwa ko bayan ya mutu Tanko ne mai gadon Rugar Shehu. Nan fa aka hau kace na ce, masu goyan bayan Baffa Mudi na yi, haka kuma masu rantsewa sai ya sauka ba su fasa ba, ana cikin wannan yanayi ne Usman ya karaso.

Ganin sa gaban Baffa Mudi yayi mummunar faduwar, ga shi dai Usman din da ya sani ne, haka kuma tufar jikin sa ba ta sauya ba, rigar saki nan dai da kowa ke sakawa ne jikin sa, Amma wani irin cika ido da kwarjinin da Allah ya wa Usman sai ya zamewa Baffa Mudi tamkar Dodo, dan kuwa yanda ya ke shakkar Usman be ji shakkar Maihaifin Usman marigayiya Shehu ba. Usman be fasa gaishe shi cike da ladabi ba a matsayin sa na kanin mahaifin sa ba. Ba komai ne ya dagawa Baffa Mudi hankali ba sai jin furucin Usman na

“Baffa abubuwa da dama sun faru, wanda mun sani, ka sani, ka kuma san mun sani, wanda tonasu na nufin zubewar darajar ka a Rugar Shehu na har abada, haka ba ya cikin abin da na tanadar ma ka…..”

“Zancen banza zancen hofi!”

Baffa Mudi ya katse Usman cike da burin kunya, be gushe ba ya cigaba da fadin

” Kai Usman ni za ka zo ka nunawa bude idanu? Wai kai na birni idon ka ya bude ko? Nan ba kafa ka sa ka tsallake Rugar Shehun ba? Sai da ka ji labarin mun fara samin cigaba, shugaban kasa ya ce zai tallafawa fulani ta hanyar gina mana Ruga mai inganci, da asibitoci, da makarantu da kayan more rayuwa shi ne za ka wanko kafa ka dawo ko? Toh ko uban ka Tanko be isa ba…..”

“Baffa Mudi!!!!”

Usman ya daka masa tsawar da sai da ya sha ruwan jikin sa, a fusace Usman ya ce

“Kada ka yarda ka bari na take dan guntun girman da na ke ba ka! Mulki! Taimakon shugaban kasa da koma menene baya gaba na, cigabar Rugar Shehu shi ne gaba na…”

Ya tashi tsaye ya na mai duban dattawa da Kuma yan gari da ganin Usman ya sa su karasawa fadar Shehu. Cikin bada umarni Usman ya ce

“Ni Usman magajin Shehu ina mai sanar mu ku cewa ba na zo ne dan karbi sarautar Rugar Shehu ba, na zo ne ganin Iya ta, wacce Allah yayi ba za mu gana ba, duk da haka ba zan iya kau da kai daga gare ku ba bayan shekaru da dama, haka kuma ba zan ce kada ku bi Baffa Mudi ba, Amma ku sani ba a sarki biyu, dan haka idan har kuna so na kasance Shugaba gare ku sai mun canza sheka, ina mai umartar duk wanda ya ga zai iya zama karkashin jagoranci na da ya hade na shi ya nashi, kwanku da kwarkwatar ku, lokacin da Rugar Shehu za ta bar falgore yayi, za mu tasarwa barin falgore rana ita yau”

“Saboda da kai ne wa? Ka juyawa Rugar ta ka baya shekara da shekaru rana a tsaka ka zo ka na wani kurari? Sai mu ga wanda zai bika ai!”

Cewar wani dattijo wanda ke zaune kusa da shi ya kara da

“rabu da shi ya maishe da mutane sakarkaru, mutumin da be damu da uwar sa ba ina zai damu da mu?”

Wani ya ara ya yafa.

“Mu na biye da kai Shehu Usman, kafar ka kafar mu har illa mashaAllah!”

Cewar matasa da wasu daga cikin dattawan wanda su ka yi na’am da batun Usman. Da wanan rudani fadar Rugar Shehu ta watse, in da na jikin Baffa Mudi ke goyan bayan Shehu Mudi, duk da dai hankalin fiye da rabin jama’ar Rugar ya fi karkata ga bin Shehu Usman.

****

Maiduguri kuwa shirye shiryen auran Halitta da Sudais ne ya kankama duk da daurin aure kawai za a yi su tare. A nan cikin wannan hidimar Hajja Kilish ta nemi bukatar a bawa maneman Zinaru da Kori damar fitowa, idan sun shirya a hada auren gaba daya. Hakan kuwa ake yi Allah ya sa aka dace wanda ke neman Zinaru a shirye ya ke, na Kori ne dai ya turo iyayen sa amma tare da bukatar a dan ba shi lokaci be gama shirin sa ba.

Ganin kiri kiri za a aurar da yan uwan na ta biyu ga mazaje na gani na fada ne ya hana Zainab sukuni. Haka ta saka su Anty Sauda gaba da kuka, ta dena cin abinci ta dena walwala cewar ta da ta zauna da auren Usman gwara ta rasa ran ta. Ammy kuwa ta ce ba ita kadai ta haifa ba, idan mutuwar ta ce alkhairi gare su toh Allah ya sa a tafi a sa’a.

Duniya ta yi mata zafi, cikin kwana uku kacal ta rame ta fara lalacewa. Ganin haka Anty Sauda ta yanke hukuncin daukar mataki, gidan Malam ta je, ta saka Ammy gaba tare da Zainab, ta ce lalle ta kira gidan Kano ta ce Usman ya zo Maiduguri ta na san ganin sa.

Ammy na girgiza kai ta ce

“Ah ah ba zan kira shi ba fa, toh na kira shi ma akan me? Na fa fada mu ku wallahi babu yawu na cikin lamarin auren Yakura, gwara ma ta hakura ta zauna da mijin ta….”

“Na gaji da yin wannan maganar da ke Aleesha! Taurin kai gare ki kamar mutanan farko! Toh tantabara! Tunda masoyin ki ya daura ke kuma ba ki rabawa ko? Toh bari ki ga mu yi mai gaba daya, ni nan zan kira shi kuma sakin yarinyar nan ne sai yayi!”

Ammy na mai zuba mata idanu Anty Sauda ta kira numbar wayar da Malam ya aje bangaran masu gadi, wayar na kara ba a dauka ba, ta na shirin katsewa aka daga tare da yin sallama.

“Sunana Hajiya Sauda daga gidan Malam nan Maiduguri, ina son magana da Usman Maigadin”

Cewar Hajiya Sauda cikin dakiya. Shiru ne ya biyo baya daga bisani ta aje wayar ta na mai fadin

“Toh madallah, ke Yakura ai sai ki kwanatar da hankalin ki, Almajiri dai ya hade kayan sa yayi gaba, abin da abokin aikin sa ya sheda min kenan!”

“Yanzu haka ya tafi be sake ni ba? Toh wallahi ko da wasa kar a kara danganta ni da shi! Kada a sake cewa ina da aure….”

“Idan kuma ba haka ba fa?”

Cewar Ammy cikin tsawa, ta na mai nuna ta da yatsa ta ce

“Sai me za ki yi? As far as I’m concern Yakura ke matar aure ce ko kin ki ko kin so!”
Kuka Yakura ta saka wanda hakan ya sanya Anty Sauda fadin

“Sai ki kashe ta ki huta, ko kuwa ki janyo ta gudu ta bi duniya ayi biyu babu. Ke dena kuka na ce dai kun kusa komawa makaranta?”

Cikin muryar kuka ta ce

“Registration ma mu ke, na fadawa Ammy ko kudin registration din ma ba ta ba ni ba”

“Kudin registration dai? Ai kuwa a dangin uwar ki ba matsiyaci! Ki zo gida na ki karba gobe zan baki kudin registration da ma na kashewa”

“Waya ta ma ta lalace Anty Sauda”

Cewar Zainab cike da shagwaba.

“Toh kar ki damu sai a siyi wata ai, ki duba duk wacce ki ke so I got your back. Haka kuma ki hade na ki ya na ki ki koma makaranta, idan ma kin so kar ki halarci daurin auren gidan nan babu lalle ba tilas!”

Jin abin nema ya samu Zainab ta share hawayen ta tare da yiwa Anty Sauda godiya dan kuwa sai a sannan ta dan ji sanyi cikin ran ta, ta fice ta bar Anty Sauda da Ammy su na musayar magana kan ta, har sai da ran Anty Sauda ya baci sosai, cikin fushi su ka yi sallama ta tafi.

***

Washagari da sassafe Zainab ta nufi gidan Anty Sauda, Nan ta yi karin kumallo. Anty Sauda ta ba ta kudi masu yawan gaske domin registration da na kashewa har da na siyan wayar sanan ta kai ta super market ta mata siyayya sosai irin wanda Dady ya ke mata duk sanda za ta koma makaranta. Hatta tiket din jirgi Anty Sauda ce ta siya, Ammy ta sa mata idanu kawai. Wayewar gari Anty Sauda ta zo ta tisa ta gaba, Hajja Kilishi na fadin ba za ta jira a yi auren yan uwan ta ba? Anty Sauda ta ce
“idan lokaci yayi ta dawo, ai ba wani abu ba ne”

Ta yiwa kowa sallama amma ban da Halitta wacce dama idan ba dole ba magana ba ta hada su. Anty Sauda ce ta kai ta Airport, sai da ta tabbatar jirgin su ya tashi sannan ta juya gida.

Haka ma da jirgin su ya sauka birnin Yola Anty Sauda ta kira ta shedawa, Sai Anty Sauda ce ta sheda ma Ammy diyar ta ta sauka lafiya, ta kuma koma makaranta. Ammy da har ranta ba ta jin dadin halin da Zainab ke ciki ba addua ta yi, Allah ya shirya mata ita, ya sa ta gama makarantar nan lafiya ko Allah ya sa ta dawo gida gaba daya sai a san wani matsayi auren ta ya ke, idan kuma kafin nan Usman ya dawo a tura shi can makarantar ya je ya same ta.

***
A Rugar Shehu kuwa jama’ar Rugar na kan shiri na barin dajin falgore. Duk yanda Baffa Mudi ya buga surkullen shi jama’a ba su fasa shiri ba dan kuwa shiri su ke haikan, tare da taimakon Usman wanda cikin kankanin lokaci ya sami soyayyar jama’ar Rugar yara da manya. Iya kwanakin da ya rage mu su a kulli yaumin ya kan ziyarci kabarin Iyar sa, ya ke shafe awanni ya na hawaye ya na mata addua.

Ana sauran kwana daya su tafi aka kwana ana ruwan sama mai karfi a Rugar Shehu wanda ya hana kowa runtsawa, saboda tsoran rushewar gidagen su. Kusan awanni biyar aka dauka kafin ruwan ya tsaya, ruwa na tsayawa kenan ihu da kururruwar Bello ya kara?e Rugar Shehu.

Usman da sauri ya isa gare shi, ga mamakin sa sai ganin Bello yayi ya na birgima kasa yayinda wani irin bakin abu ke fita daga bakin sa.

“Innalillahi wainnailaihi rajiun!”

Cewar Usman yayinda ya tallabo Bello, be tsaya bata lokaci ba ya shiga karanto masa ayoyin rukiyya da ya koya wajan Malam dan ya tabbatar halin da Bello ya ke ciki ba zai wuce ko dai aikin sihiri ba ko kuma jinni. Sai da su ka kai kusan minti talatin cikin wannan hali, makota duk sun shigo suna tsaye bakin rumfar cike da al’ajabi, cikin su har da kawo Iliya. Bello ya saki nannauyar ajiyar zuciya sai kuma shiru jikin sa yayi sanyi tamkar matacce.

Ganin haka Usman ya rikici yayinda ya shiga jijjiga Bello ya na mai kiran sunan sa da karfi, jin haka Kawo Iliya ya shigo dakin da sauri ya na kokarin duba Bello ta hanyar saka kan sa bisa kirjin Bello. Cikin kaduwa Usman ya furta

“Shikenan Muhammadu Bello ma ya bi Iya! Muhammadu Bello ya tafi ya bar ni ni kadai Kawu Iliya….”

“Babu in da Muhammadu Bello ya tafi, a raye ya ke dan kuwa har yanzu zuciyar shi na harbawa”

Cewar Kawu Iliya ya na gyara kwanciyar Bello, be gushe ba ya kara da

“Kome aka yi Muhammadu ya shiga yanayi ko dai na sammu ko kuma makarin sammu da aka taba yi kan sa, zai fi kyau ka zauna nan tare da shi ka na masa tofi, in Sha Allah zai farfado cikin koshin lafiya”

Usman na mai kokarin saka zuciyar shi da ta amince akan bayanin da Kawu Iliya ya masa su ka yi sallama, Nan ya zauna tare da Bello ya na masa addua kamar yanda Kawu Iliya ya umarce shi, haka har ladanin Rugar Shehu ya kira sallar asuba Usman ya fita Sallah.

Bayan an idar da Sallah Usman ya dawo ya ji abin al’ajabin da ya zaci har ya koma ga mahallicin sa ba zai kara ji ba, wato muryar Bello da ta daki kunan shi ya na mai fadin

“Shehu……Shehu…..ka na jin murya ta kokwa dai a zuci na ke ma ka magana kamar yanda na saba?”

“Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu alaihi wasallam!”

Cewar Usman yayinda ya zube kasa ya na mai sujjada ga Allah. Ko da ya dago rungume Muhammadu Bello yayi, ya na hawayen murna ya ce

“Muhammadu Bello muryar ka na ji! Muhammadu Allah ya dawo ma ka da muryar ka! Ashe zan kara jin muryar ka? Ina ma Iya ta na raye Muhammad! Yau ga burin ta ya cika amma babu damar sanar mata”

Kamar yanda Usman ke hawayen murna haka shi ma Bello ya ke, fadi ya ke

“Zan sanarwa Iya, gari na haske zan je na sanar mata, zan yiwa Iya addua a zahiri ba a zuci ba, Zan yiwa Iya sallama, Allah ya sa za ta ji ni Shehu”

“Za ta ji ka Muhammadu Bello! Za ta ji ka da yardar Allah”

Cewar Usman cike da so da kaunar dan uwan na sa. Gari na wayewa labarin dawowar muryar Muhammadu Bello ya zagaye Rugar Shehu, labarin ne ya sanya Baffa Mudi ziyartar makabarta Rugar Shehu cike da tashin hankali domin neman amsar tambayar da ta addabi kwakkwalwar sa,

‘shin ya aka yi maganar Muhammadu Bello ta dawo alhalin yanda ya birne layar da ya masa asiri da shi tare da gawar ladan matukar ba tono gawar aka yi ba Muhammadu Bello ba zai sake magana a doran kasa ba’

Ile kuwa nan ya sami amsar tambayar, ashe daminace ta yi gyara a tsohuwar makabarta da ta dade da cika, ruwan da aka yi daren jiya ne yayi ambaliya makabarta har ya bude wasu daga cikin makwancin mamata, in ban da farin yadi babu abin da ke yawo.

“Lalle damina baki mugunta, na tabbata ruwan nan shi ya tono asirin da na rufe shekara da shekaru, matukar ban nemo layar nan na sa an sake rufe wani mamaci da shi ba toh fa asiri zai tonu!”

Cewar Baffa Mudi yayinda ya cire rawani ya aje gefe, sai gashi tsome tsome da shi cikin ruwa da cabi ya na neman laya. Yana cikin wannan yanayi ne Usman da Bello su ka karaso. Cikin kwalla kira Bello ya ce

“Kawu Mudi! Halan wannan ka ke nema?”

Ya daga masa layar da tun sassafe da su ka ziyarci kabarin Iyar su Bello ya tsinta, ruwan da aka yi ne ya korota makabartar su Iya. Ganin abin da ke hannun Bello da kuma yanda yanayin Usman ya canza gaba daya, dan yanda ya ke kallan sa tamkar aka ba shi wuka zai iya birma masa ya sa Baffa Mudi karasowa gaban su jiki sanyaye, gwiwowin su biyu ya durkusa gaban su tare da furta

“Na zalince ku, na ci amanar mahaifin ku, dan Allah ku yafe min kada ku tona min asiri! Duk abin da ku ke so ni me yi ne! Kai in har Shehuntakar Rugar nan ce ma ni na hakura na bar mu ku, Ni dai rufin asiri, kun ga dai ko ba komai ni kani ne gun Mahaifin ku, haka kuma ga iyali ga tsufa…”

“Ka san da haka ka aikta abubuwan da ka aikata?”

Cewar Usman cikin tsawa, be gushe ba ya kara da

“Ka cuce mu, ka cuci yar ka ta cikin ka ka cuci iyayen mu, Amma duka kan ka kafi cuta har ka na da bakin cewa a rufa ma ka asiri?”

“Dan Allah ba dan hali na ba! Ku tuna fa Allah na san rufin asiri! Ku rufa min asiri”

Cewar Baffa Mudi cikin rawar murya. Usman na duban sa ya ce

“In dai rufin asiri ne, za mu iya rufa ma ka, Amma da sharadi daya!”

“Koma menene sharadin na yarda! Zan bi!’

“Sharadin shi ne za mu bar wannan dajin, ba kuma zan hana masoyan ka zama da kai ba, Amma ko da wasa kada ka tako kafa ka zo in da mu ke! In ko ka kuskure ka biyo mu Baffa Mudi ko Kuma ka yi yunkurin lalata min tafiyar nan ta hanyar tsubbun da ka saba na lahira sai ya fi ka jin dadi!”

Baffa Mudi na mai jinjina kai ya ke fadi

“Na yarda Shehu adali, na yarda! Ka cika mai yafiya, in Sha Allah zan kiyaye sharadin ka”

Da haka ya tashi ya koma Rugar shehu cike da borin kunya. Usman kuwa wuta su ka sa suka kone layar da ke dauke da sunan Muhammadu Bello. Ranar wuni aka yi ana gayara makabarta, washagari da sassafe bayan Usman da Bello sun je sunyiwa Iyar su Sallama tare da addua, su ka tabbatar sun killace kabarin ta yanda ruwa ba zai taba tona shi ba, sannan su ka hada na su ya na su, kwansu da kwarkwatar su ka tasarwar barin dajin falgore. Baffa Mudi na ji ya na gani Usman ya kada duka Shanun da ya ke mallakin gidan Shehu be bar masa ko daya ba. Shanu ne masu yawa kwarai da gaske dan kuwa idan aka ce za a tsaya lissafa adadin su ace sharata ta ake. Haka kusan duka jama’ar Rugar Usman su ka bi, illa kalilan ne su ka tsaya tare da Baffa Mudi.

In da Rugar Shehu ke sauya sheka, gidan Malam kuwa auran su Halitta aka daura. Ba wani taro aka yi ba, auren kawai aka dora. Zainab ba ta halacci daurin auren ba bare ta kira amare ta mu su Allah ya sanya alkhairi. Babban bakin cikin ta shi ne tafiya Saudia da Sudais ya ke so yayi da Halitta a sakamakon aikin da ya samu a can. Zinaru kuwa a ranar aka mika ta dakin mijin ta.

Zainab sam ba ta canza zani ba, yanda ta ke rayuwa a da haka ta dora bayan ta koma makaranta, haka kuma ta sake bude saban account na Instagram bayan ta siyi dalleliyar wayar ta mai dauke da tambarin tufa ta cigaba da sharholiyar ta kamar yanda ta saba.

Satin su Usman da tawagar sa biyu suna yawo daga wannan dajin zuwa wannan dajin, su kutsa nan, su kutsa can, in da ya kamata a yada zango a yada cikin kokarin kare hakkin nomama ta hanyar kada shanun sa daga barin shiga gonaki, a haka har su ka iskewa wani daji arewa masogabashin kudu, dajin ya kasance mararraba tsakanin kudu da arewa.
Kasancewar dajin ya yalwatu da ‘ya’yan itatuwa, ga ruwa da yanayi mai kyau, haka kuma aikwai wadataccan fili tuni su ka yada zangon su na zama dirshen, kwanan su uku suna gine ginan bukka, haka kuma masu ilimin surkulle su ma su ka dukafa wajan kafe dajin, suna shiga lungu da sako sai da su ka kafe dajin kaf ya zame mu su tamakar gida hatta macijan dajin sai da su ka san da kafuwar Rugar Shehu.

Cikin watanni biyu Usman ya kafa daular sa, Shehuntakar sa ta ginu sosai musammam da Allah ya hore masa ilimin da ya koya daga wajan Malam. Ganin yanda ya habaka gashi babu mata ne ya sanya magidan ta da yawa yiwa Usman tayin matar aure daga cikin yan matan Rugar Shehu, musammam yanda kowacce da ta ke ji da kan ta ke da burin kasancewar mata wajen Shehu. Amma Usman kullun cikin ba su uzurin cewa zai karba, Amma akwai wata ajiya da ya ke da shi birnin Kano, matukar ba ajiyar nan ya dauko ba toh be shirya aure ba.

Bayan wata biyu da sati daya da kafuwar daular Rugar Shehu, Usman ya shirya tsaf da shirin zuwa dauko ajiyar sa, in da ya wakilta Muhammadu Bello ya kula da Rugar su kafin ya dawo.

Komawar shi Kano ya so ba shi wuya kasancewar ba da mota su ka shiga dajin su ba, tafiyar kasa ce su ka yi mikakkiya. Da kyar da taimakon Allah ya sami motar da ta kai shi Mambila, daga nan ya sami motar Taraba, a can ne ya sami na Kano direct.

Ganin Usman da kuma yanda ya canza ya kara kwarjini kamar wanda ya sha maganin kwarjini ba karamin mamaki su Isa su ka yi ba, musammam Jauro da ya kama kan sa dan shi kan sa ya san akwai bambamci tsakanin Usman din da da na yanzu, har da yanda Ammy ta karbe shi hannu bibbiyu. Ta dawo Kano ita da Falmat bayan sun fita takaba. Bakin ta ya ke jin labarin auran Halitta wacce a yanzu haka ta na can Saudiya tare da mijin ta. Yayi murna kwarai tare da mata addua. Amma ko da Ammy ta kawo maganar Zainab, ta na mai tambayar sa dalilin da ya sa ya tafi babu sallama sai cewa yayi

“A yi hakuri abin ne ya zo min a gaggawa, shi ya sa ma na dawo na gyara, ta na nan ne?

Ya tambaya ko Zainab ta na nan ne ba dan ya na so ya ji amsar da Ammy za ta ba shi ba, abu daya da ya sani shi ne ya zo tafiya da ita, ko ta nan ko bata nan kwana daya kacal ya ba ta za ta dawo ta same shi har in da ya ke.

Ammy ce ta masa bayanin Zainab din ta na makaranta, jami’ar da ta ke yi a Yola, Amma kada ya damu ai ta ma kusa fara jarabawa, kuma da ta dawo be fi watanni biyu zuwa uku za su kara su gama makarantar gaba daya ma

‘ai kuwa na ta makarantar ya kare daga gobe!’

Cewar Usman cikin ran sa, zahiri kuma cewa yayi

“babu komai ai kamar yau ne, Allah ya ba da sa’a”

BQ din nan dai da Malam ya basu nan aka sauke shi. Allah ya amsa adduar shi har lokacin akwai wasu daga cikin kayan Zainab, dan haka a daren ranar ya yanki daya daga cikin bakaken rugunan ta da ta bari a dakin, ya hada da wani ganyen turare da ya taho da shi daga Rugar Shehu. Sai da ya kulle dakin sannan ya hada garwashi ya ruru sosai yayi jajur, sannan ya dauki kyallen da ya yanka, ya hada da ganyen turare ya dora kan garwashin, yana murmushin mugunta ya ke duban yanda tufar ke konewa hayaki na ta shi, ya ce

“Kamar yanda tufar ki ke konewa haka zuciyar ki za ta na mi ki kuna matukar ba ki baro duk abin da ki ke kin zo gare ni ba Zainab, kamar yanda hayakin nan daya ke bin daya haka za ki bini duk in da na sa kafa….matata Abu”

***

Duk yanda Zainab ta so ta yi karatu daren ranar kasawa ta yi, ga shi ta na da jarabawar safiya. Washagari tun da asuba ta hado kayan ta, ba tare da ta nemi shawarar kowa ba ta na kallo kowa na shirin fita jarabawa amma ta tsallake ta dauki hanyar Kano a motar haya abin da ba ta taba shiga ba tun da ta fara karatu a Yola. Sai yamma likis ta isa Kano, wanda tun isowar ta jikin Usman ya bashi dan haka shi ma din ya fita kofar gida da shirin sa ba tare da ya bari su Jauro sun san da fitar shi ba. Be yi cakakken minti talatin da tsayuwa kofar gidan ba sai ga dan sahu ya zo ya tsaya gaban gidan Malam. Zainab ta fito sanye da bakar abaya, hannun ta rike da dan akwatin ta da ta debo kadan daga cikin kayan ta. Ta na sallamar dan sahu ta karasa gaban Usman ta tsaya, wanda tun saukowar ta ya tsura mata Ido cike da tsana. Wani farin mayafi da ya sha ado da kaloli irin na fulbe ya mika mata, Zainab ta sa hannu ta karba.

“Ki yafa shi yanzu”

Cewar Usman. Zainab ta amsa da toh sannan ta ware mayafin ta yafa.

“Sunan ki Abu….”

Cikin gasgatawa ta furta

“Sunana Abu…”

Usman ya kara da

“Ni mijin ki ne Shehu”

“Kai miji na ne, Shehu”

“Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu”

“Mu na hanyar komawa gida Rugar Shehu”

Zainab ta sake maimaitawa.

“Duk wanda ya mi ki magana a hanya kada ki tanka masa, matukar ba ni Shehu mijin ki ba ne ya baki umarni kin ji ko?”

Zainab ta na mai girgiza kai cike da ladabi ta furta

“Toh miji na Shehu…”

Kallan ta yayi sama da kasa ya gamsu da yanda mayafin da ta yafa ya dan ragewa rigar da ke sanye jikin ta kyau, cikin ran sa ya na mai neman yafiyar Ammy da Malam, ya ce da ita

“Biyo ni mu tafi!”

Babu musu Zainab ta bi bayan shi hanun ta rike da akwatin ta, ko waige ba ta yi ba bare ta tuna da gidan su ne nan ta bari.

Back to top button