Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 15

Sponsored Links

Book 2

*Episode 15*

Aryan Aunty Farida, zaune suke a palon Aunty farida suna hira

“Aryan gaskiya ban yar da ba awannan karon kam sai dai muje tare, dan ni gani nake kamar baku duba diyana da kyau ji nake kamar idan naje da kai na zan iya gane ta” chewar Aunty farida tayi maganar tana kare masa kallon kan sa na kasa ba tare da ya ɗago ba yace “no Aunty farida nima ba iya zuwa zan yi ba domin gaba ɗaya ji nake zuchiya ta na bugawa da karfi karfi na rasa me yasa tun dana kamo hanyar zuwa gidan nan naki gabana ke faɗuwa gaba ɗaya naji jikina ya mutu, na kira commitioner akan su kawo mana mutane gidan nan, kawai” “eyya sorry Allah ya sauwaka ya Allah kasa diyana ce awan nan karon, Aryan zanyi magana wayar sa ta fara ringing, chirota yayi daga aljihun sa, ganin sunan Shahram ne ya bayyasa akan screen ɗin yasa yayi saurin picking call ɗin,

“hello sir ga mutanen sun kariso” mikewa yayi da kyar yana faɗin “ok am coming” yana gama faɗin hakan ya katse kiran tare da ficewa daga palon, chikin sauri Aunty Farida ta haura masa ta ɗauko hijabi ta sanya ta bi bayan sa.

A harabar gidan Aryan ya tsaya tare da bawa sojojin sa umarni akan su shigo da mutanen, ba afi 2mins ba sai ga Shahram tare da wasu murane guda 2, dai dai lokacin Aunty farida ma ta fito ta kariso wajen nasu, chike da kwarin guiwa da sa ran zasuyi na sara Aunty farida ta fara magana “bayin Allah sannun ku” har suna haɗa baki wajen chewa yauwa hajjiya ina wuni? Batare da ta amsa gaisuwar ba tace “yanzu so muke ku kaimu in da mahaukachiyar yarinyar take, dan mu duba ita muke nema ko ba ita ba” shikam Aryan ido kawai yake bin su da shi ya kasa magana “hajjiya wlh tun lokacin da wani mai mota ya bugeta bamu sake ganin taba bamu sake jin ɗuriyar taba a takaice dai bamu san in da take ba, iya abun da muka sani shi ne lokachi da mai motar ya bugeta ya ɗauke ta ya sanya ta chikin motar sa, ina tsaye saman bene ina kallon sa har motar sa ta sauka daga kan titin layin ina kallon sa” Aunty farida zatayi magana Aryan ya riga ta da cewa “kun rike number motar ne? Motar wace iri ce? Shiru mutumin ya ɗan yi yana tunanin chan yace “gaskiya ban riƙe number motar ba ni dai na san motar baka che” tsaki Aryan yaja tare da bawa Shahram umarni akan ya sallami mutanen nan dan basu da anfani, chike da ɓachin rai ya juya ya nufi chikin gida da sauri Aunty Farida tabi bayan sa.

Saman doguwar kujera mai zaman mutun 3 ya zauna yana furzar da iska mai zafi daga bakin sa, gefen sa Aunty farida ta zauna chike da tausayin ɗan uwan na ta ta fara magana “kayi hakuri Aryan ba dare ba rana muna addu’a In Sha Allah diyana zata dawo garemu” shiru yayi dan ya kasa magana, karar shigowar sako wayar sane yasa ya ɗago tare da fitar da wayar yana sauke zazzafar ajiyar zuchiya, yasha ruwan mamaki lokacin da yaga wadda ya turo masa sakon, number Bgs ne ya turomasa sakon wani address, fita yayi daga wajen massage ya shiga contact ya fara kiran layin Bgs

Wayar tana ta ringing har sai da ta kusa katsewa tu kun nan Bgs yayi picking “Hello my blood Ykk? ya Uk? daga ɗayan ɓangaren Bgs yace “am fine what of U? “same here bro i saw Ur massage this address is for who? Shiru Bgs ya ɗanyi na yan sakanni kafin yace “am sorry tun jiya naso na turomaka ina busy ne akan batun kama su marwan da yan ta adda su kayi, alkhairin da na ɗauka maka akan ka bani 2daya zan nemo maka matar ka to shi ne na chika, address ɗin in da matar ka take ne” a’sukwane Aryan ya miƙe chike da farinchi yace “nasani na san zaka iya fiye da hakan, my blood 1 in million nasan ba dan busy da kake ba da ka ɗaɗe da nemo min ita, Allah ya maka albarka ya Allah yasa ka gama da duniya lfy daman nasan in ba kai ba ba wadda zai min wanan aiki chikin kankanin lokaci haka wai kasan me ma? Shiru Aryan yaji Bgs bai amsa ba chiro wayar yayi daga kunnen sa sai yaga ashe already Bgs ya katse kiran tun ɗazun farin ciki da zumuɗi ne yasa bai ma san lokacin da Bgs ya katse kiran ba

Hanyar fita palon ya nufa chikin sauri ya manta ma da Aunty farida suke zaune, muryar tane ta katse shi da chewa “Aryan lfy ni kabar ni a duhu me Prince ɗin ya tura maka? “Aunty farida ke kam ki jirani ina zuwa” ba tare da ya jira amsar taɓa ya fice daga palon, sauri sauri ya umarchi sojojin sa akan su shiga mota,

da gudu suka shehshege chikin motar, suka tayar, da wani mahaukachin gudu suka bar gidan, sai faɗa Aryan ke musu akan hanya akan su kara sauri, dan shi gani yake kamar idan bai yi sauri ba ahikenan zai rasa diyana, map na wayar sa ya buɗe ya shigar da address ɗin a wajen, da mamaki yake kallon waje basu da nisa da gidan Aunty farida, tunanin yake to anya wayan nan suna da hankali kuwa? ashe ma suna kusa? babu in da ba a baza hoton diyana a garinnan ba, zasuche basu gani bane, da bazasu kai ta police station ba,suka ajiyeta awajen su nan take yaji ransa yayi mugun ɓaci sosai amma da ya tuna yau zai ga diyanar sa sai ya ji ransa ta ɗanyi sanyi, daga ɗan nesa da gidan su Ahzan sukayi parking na motochin su, fitowa Abdol yayi ya buɗe wa Aryan chikin sauri Aryan ya fito yana kallon wayar sa, shiru ya ɗan yi yana so ya tantanche wani gidane gidan su Ahzan daga chikin gidajen layin, call ne ya shigo wayar sa, ganin kiran Bgs ne yasa ya ɗauki wayar da sauri.

“Hello my blood” daga ɗayan ɓangaren Bgs yace “ka kara gaba kaɗan gidan na gaban ka” murmushi kawai Aryan yayi dan yasan in dai Bgs na son yin abu tofa 30mins yayi yawa angama da wannan matsalar sai dai wata “Aryan kaje ba sai ka katse kiran ba ina ganin ka” “ok my blood” chike da jarunta Aryan ya fara taku, chikin sauri jibga jibgan sojojin sa suka diro daga saman nasu motocin suka bi bayan sa, hannu ya ɗaga musu alamar baya bukatar su bi sa, yana tafiya Bgs na faɗa masa in da zai bi, dai dai kofar gidan su Ahzan Bgs yace “nagama aiki na all the best my blood” yana gama faɗin hakan ya katse kiran juyowa Aryan yayi kallo ɗaya yayiwa gate ɗin gidan su Ahzan yaji ya tsani ganin gidan kwata kwata ƙarisawa bakin gate ɗin yayi chike da kyamar gidan yasa kafa ya taka gate ɗin a hankali dan ba zai iya sanya hannun sa a kazamin gate ɗin gidan nan ba

Da gudu mai gadin gidan su ya nufo wajen gate ɗin ya bude kofar, a tsorace mai gadin ya fara kallon Aryan from head to toe duk da Aryan ya rame sosai kallo ɗaya zaka masa kaga chikakken jarumin namiji ɗamtsen hannun sa kawai mai gadin yake kallo, kamar zasu fasa riga dan murɗewa da Chika, chike da tsoro Mai gadin yace “sannu ranka ya daɗe” kafa Aryan ya sanya ya shigo chikin gidan ba tare da yayi Magana ba, dan yana tabbacin diyana na chikin gidan nan, Bgs baya binchike akan abu sau biyu idan yayi binchike yace ga result tofa wannan result ɗin haka take babu tantama, idan kuma har diyana na chikin gidan nan tofa babu wanda zai rage a gidan nan bai ansa hukunchin ba.

A harabar gidan ya tsaya ya zura hannu a aljihun sa yana bin gidan da kallo kamar mai binchiken wani abun

da sauri mai gadin ya nufi chikin gida, jim kaɗan ya fito tare da Ahzan, kallon Aryan Ahzan yake kamar ya sanshi bin kirar jikin Aryan yayi da kallo duk tsawon da Ahzan yake da shi a kafaɗar Aryan ya tsaya “malam lfy ka shigo mana gida ba da izinin mu ba? chewar Ahzan yana magana a tsorache dan yadda ya kalli fiskan Aryan bai ga alamun annuri ba bai ga alamun wannan fuska ta san menen dariya ba” A wulakan che Aryan ya kalli Ahzan from head to toe, chike da jin haushi ya buɗe baki zai yi magana kenan sai ga hanan da Ummi sun fito, zasu shiga part ɗin su deen kallon Ummi kawai Aryan yake lokaci guda yani harshen sa ta masa nauyi tambayar kan sa yake wai shin gaskiya idon sa ke faɗa masa ne ko karya, runtse ido yayi da karfi ya furta “ke zo nan” a tare Hanan da Ummi suka juyo kallon Aryan Ummi take sosai ji take kamar ta sanshi ji take kamar ta taɓa ganin sa, chikin tsawa da tsoro Ahzan yace da su hanan “me ya fito da ku zaku wuche ku komane ko sai na same ku awajen” chikin sauri suka juya suka koma chikin gidan, chike da iyayi Ya juyo yana kallin Aryan “malam ka fice daga gidan nan tun ban kira yarana sun fitarmin da kai ba, daman ka karya doka ka shigo gidan mutane ba tare da izinin suba” shiru Aryan yayi yana tunanin hukunchin da ya dache da Ahzan

hannu Ahzan yasa yana kokarin ture Aryan akan ya fita daga gidan iya karfin sa ya sanya yana ture Aryan amma ina ko motsi Aryan bai yi ba.

gaba ɗaya ganin Ummi yasa jikin sa ya mutu baya son bugun mutun yanzu amma yazama dole Ahzan yaji kamshin lahira yanzu, damko wutar Ahzan Aryan yayi ya ɗaga shi sama yayi wurgi da shi gefe, wani ihun azaba Ahzan ya saki wadda yasa gaba ɗaya family Alhj Abbas fitowa da gudu, nan take Aryan yaji ransa yayi mugun bachi gadan gadan ya tinkari Ahzan kafar sa ta damko, ya ɗaga shi ya sake wurgi da shi gefe, wani wawan bugu ya kai masa a gefen chiki, kwata kwata Ahzan ya kasa ihu ma sai zazzare ido kawai yake kuka yaki fitowa, wani razannen ihu Mum Ahzan ta saki wadda ya sa Aryan ɗagowa ya kallin in da suke karaf idon sa ya sauka kan razanannen fuskan Ummi da ta kankame hanan hawaye na zuba daga idon ta, dafe kai yayi yana kallon ta baya son kukan da take, alama ya mata da hannu akan tazo kara kankame hanan tayi alamar tsoron sa take, shafa kan sa yayi da hannu ya chije lips nashi na kasa da karfi chike da jin haushi ya daka mata tsawa “zo nan nace” jikin ta har kerma yake ta kariso in da yake tsaye sai kuka take kasa kasa, daga ɗan baya kaɗan ta tsaya, hannu yasa ya fiskota ta faɗa kan faffadar kirjin sa rungumeta yayi sosai yana sauke nauyayyar ajiyar zuchiya gaba ɗaya jama’ar dake wajen, suka zuba masu ido, sai mutsu mutsu Ummi keyi ajikin sa yana kankame da ita da hannu ɗaya, yasa ɗayan hannu ya chiro wayar sa daga aljihu ya fara kiran layin Shahram, bugu ɗaya Shahram ya ɗaga “kuzo ku kwashe jamar dake chikin gidan nan dukka ku wuche dasu Kano, ku miƙasu ga D P O sai na dawo” yana gama faɗin hakan ya katse kiran, ya ɗan duƙa ya saɓi Ummi a kafaɗar sa, ya nufi gate ɗin gidan sai kuka Hanan take ta rungumi mum, duk iskanchin irin na Deen yau sai da ya nitsu kamar bashi awajen ya rungumi mum ɗin sa yana zare ido kamar an tare ɓera a tarko

Aryan na fita gidan rundunar jibga jibgan sojojin sa suka diro chikin gidan gaba ɗaya wayan da suke gidan suka tattare kowa dake chikin gidan har da mai gadi suka nufi airport suka wuche kano da su,

Gidan Aunty farida Aryan ya wuche da Ummi, Aunty farida na zaune a palo tayi shiru abun duniya ya ishe ta tunani take awani duniya diyana take yanzu.

Dauke da Ummi a saman kafaɗar sa ya shigo palon bakin sa ɗauke da sallama, chikin sauri Aunty Farida ta miƙe murya na rawa tace “diyana Aryan ina.. bata karisa maganar ba ta yake jiki zata faɗi da sauri Aryan ya tare ta, da hannu ɗaya ya sauke diyana daga saman kafaɗar sa ya rike Aunty farida da kyau ya kwantar da ita saman doguwar sofa dawo da kallon sa yayi kan Ummi dake tsaye tana zazzare blue eyes nata “ke ɗauko min ruwa a fridge” ya ƙarisa maganar tare da nuna mata in da fridge ɗin yake, ba musu ta nufi wajen ta ɗauko ruwan faro mai sanyi ta kawo masa ansa yayi ya buɗe bakin robar ruwam ya tarbo a hannun sa ya shafa ma Aunty farida a fuska, ajiyar zuchiya ta sauke tare da waro idon ta waje, mikewa yayi ya koma saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna ya sunkuyar da kan sa kasa, miƙewa zaune Aunty farida tayi chikin en ena tace “my diyana zo ki zauna kusa da ni mana, juyawa Ummi tayi tana neman ta ina diyanar take, ɗago kai Aryan yayi yana kallon ta, chikin sanyin murya yace “zo “yayi maganan yana mata alama da hannun sa, chike da tsoro ta karisa wajen sa hannun ta ya kama ya zaunar da ita kusa da shi chikin sanyin murya ya fara magana “me yasa kika tafi ki bar wajen da Aunty farida tace ku zauna ku jira ta? Me yasa baki sanar da wayan chan banzayen ke matar Kga bane? Shiru Ummi ta ɗanyi kamar mai tunani chan kuma tace “wacece kuma Aunty Farida? Ni ban san kuba dan Allah ka mai dani wajen Aunty Hanan tsoro nake ji” tana magana kamar zarayi kuka, zuba mata ido kawai Aryan yayi yana kallon ikon Allah yau diyana ce zata che bata san shi ba?

Masu karatu sai mun haɗu ranar Saturday idan Allah ya kaimu yau naje kunshi ne shi yasa baku samu long page ba

Jinjina da fatan alkhairin gare ku matanen duk karfin izzata paid group

Godiya da fatan alkhairin gare ku mutanen duk karfin izzata comments section group ina ganin comments naku ina godiya Allah ya bar zumunchi

Aisha baita jidda my mum
Aunty Asma’u
Aunty asmy
Sister shamsiya
Maman Amir
Maman Amira
Queen Haseena
Aunty Aisha
Aisha bello ashlady
Aisha gala dima
Baby Zahra
Sis Halima
Aunty kharima

Da duk sauran wayan da basu ji sunan su ba, ina miko sakon gaisuwa

Jinjina gareku the talent troupe writer’s fatan nasara garemu

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

Wannan page ɗin sadaukar wane gareki masoyiya Gidan Aunty ya Allah ya baki lfy Allah yasa kaffara ce

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin bDuk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Back to top button