Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 64

Sponsored Links

Khadijah bata yarda ta bude ido ba, ya dinga kallonta, a hankali yace “Baxa ki kalleni ba Khadijah” dauke kanta tayi ta juya masa baya, mikewa yyi ya koma kujera ya xauna yana kallonta, bayan wani lkci yace “Shkkn since you don’t want to see me bari in tashi inyi wucewata” a hankali ta juyo tana kallonsa, tausayinta ya dinga ji har ransa ya taso ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace “Ki gaya min ko na maki wani abun ne Khadijah, bana son wani abu ya same ki saboda ni, tell me ur mind plss…” Tana kallonsa da kyau tace “What is in my mind da xan gaya maka?” A hankali yace “Noo, ai ke xaki fada I don’t knw what you are thinking of me… Say out ur mind Khadijah” ta hade rai tace “Kana tunanin saboda kai nake rashin lafiya a nan?” Ya buda ido sosai yace “Noo ba abinda nake nufi ba kenan” Tace “Toh ciwo ne kawai Allah ya sakko min, so I just have to say Alhmdllh” Ya langwabar da kai yace “Toh Allah ya sauwake” tace “Ameen” yace “Kin ci abinci?” Kai ta gyada masa tace “Su Maryam sun kawo min” Wayarta dake ajiye yyi haske alamar kira khaleel ya dauka ya mika mata ta karba, ganin barrister ke kiranta ta daga ta sa a handsfree ta kai kunne, da damuwa yace “Ina kika shiga Amira, I have been calling since but no response” ta koma ta kwanta a hankali tace “Kayi hakuri plss, yau tun da na tashi nake jin ciwon ciki, sai bayan da naje schl sai ya matsa min aka taho dani clinic…. Am even stil at the clinic” Sudais yace “Subhanallah, wani irin ciwon ciki ne haka?” Ta d’an buda ido tace “Aa ni ma ban sani ba, kawai dai ciwon ciki” yace “Ko dai… Ko dai na period ne?” xaro ido tayi don ita har mancewa take akwai wani abu wai shi al’ada, tun da ta haifi su Shureim ta daina, sai dai tayi bai fi sau daya ko biyu a shekara ba shi ma na kwana biyu, Amma fa tana shan axaba sosai don wani lkcn har tunani take kila mutuwa xata yi, yace “Uhm shine koh?” Yar dariya tayi tace “Ae ni bana yi” yace “Bakya me?” Tace “Uhm abinda ka fada mana” yace “Are you serious?” Tace “Ehh” yace “Maa sha Allah, kice doubling sadaki xan yi kenan” Boye fuskarta tayi da gado don ba karamin dariya da kunya ya bata ba ga khaleel a xaune, shi dae Khaleel idanuwansa na kan wayar hannunsa da yake dannawa yana saurarensu, ta dago a hankali tace “Koh?” Yace “Ehh mana, ai ku special ne cikin mata, and you are rare….” tace “Uhmm” lkci daya khaleel ya mike ya nufi kofa ta bi sa da Harara har ya fice, Barrister yace “But hope ciwon cikin da sauki sosai yanxu?” Ta gyada kai tace “Naji sauki amma sai gobe xa ayi discharging dina” yace “Toh wa ya kawo ki asibitin?” Da har xata ce Aliyu sai kuma tayi shiru, da sauri tace “Maryam da na baka labari ranan, ita ce ta kawo nii, luckily ta shigo cafteria lkcn ta gan ni kawai muka wuce clinic” Yace “Toh Allah ya kara lafiya, how about shureim ko tare ku ke a asibitin?” Ta girgixa kai tace “Noo yana gun neighbors dina” Barrister yace “Ohk, I will send the hospital bill yanxu kin ji” da sauri tace “Nooo, ‘yan gidansu Maryam sun biya ma, don’t bother plss my barrister” yace “Toh idan na turo sai kiyi pepper soup da yawa ke da Shureim ku ci, clear?” murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yace “Yea, sai da safe dear, Allah ya kara lafiya” a hankali tace “Ameen nagode sosai” lumshe ido yayi ya katse wayar, Khadijah ta mike xaune a hankali, gaba daya taji ta samu relieve kamar an cire mata ciwon, Maryam ce ta dawo ward din tace “Ashe kin tashi Khadijah” d’an murmushi Khadijah tayi tace “Ehh” Maryam tace “Ohk, Dr Ayman yace in fada maki ya wuce sai da safe” Khadijah tace “Ohk, I was making call ya fita” sosai Khadijah ta sake da Maryam suka dinga hira a ward din har Maryam ta dinga mamaki ganin ashe dai tana magana haka, sai kusan karfe sha daya duk suka kwanta. Washegari karfe bakwai na safe Aliyu ya xo clinic din, Khadijah na bathroom tana wanke baki da sabon toothbrush da Maryam ta kawo mata da paste, Maryam suka gaisa da Aliyu yana kallonta yace “Ya jikin nata?” Maryam tace “Ai kam taji sauki sosai” dai dai nan Khadijah ta fito ta karaso tana kallonsa a hankali tace “Good morning” yace “Morning Iman ya jikin?” Tace “Naji sauki sosai, thanks for ur care” yayi murmushi har ransa yaji dadin yanda ya ganta unlike yesterday, ya ajiye breakfast da Hajiya Mariya ta bada ya kawo masu, Khadijah ta xauna gefen gadon tana kallonsa tace “Plss ina son kaje can gida I don’t want to inconvenience anybody sae ka dau Shureim kayi dropping dinsa schl” Yana shafa kansa yace “Dr Ayman din baxae kai sa ba?” Tace “Toh ni bari in je in daukesa in ajiye sa schl idan baxa ka je ba, Kuma ai nasan da Dr Ayman din” murmushi yayi yace “Aa ae bn ce baxan je ba malama” turo baki tayi ya juya ya fita ward din din Maryam ta bi sa da kallo, Mikewa tayi daga karshe ta hada ma Khadijah shayi da ya kawo ta bata da kwai, Khadijah ta amsa tace “Nagode” daga haka ta fara shan shayin da spoon, bayan kusan awa daya Aliyu ya dawo ward din, kujera ya ja ya xauna ya jinginar da kansa da kujerar yace “Dama kawai don ki bani wahala ne kika ce in tafi koh?” Tana kallonsa tace “Me ya faru” murmushi kawai yayi ya dago yana kallonta, ta ci gaba da Shan shayinta, mikewa yayi yace “Anyi discharging din ki yanxu, we can leave” tace “Toh bill din fah, am not with money, ko idan mun je gida sai in baka, nawa ne kudin?” Ya fi minti daya yana kallonta kafin ya juya ya fita ward din, Maryam ta d’an yi murmushi tace “Haba dai ya biya ai Khadijah….” Khadijah ta sakko kan gadon ta dau mayafinta da wayarta da jaka tace “Toh nagode” Maryam ta dau kayan shayin da ya kawo suka fita waje, a haraban asibitin suka tadda shi yana jiransu cikin mota, Maryam ce ta shiga gaban motar Khadijah ta shiga back seat suka bar asibitin, da Khadijah ta daga kai sai su hada ido da Aliyu yana kallonta ta madubi, ta daga kai yayi sau uku sai su hada ido, ji tayi gaba daya she is uncomfortable, ta matsa a hankali ta koma can karshen motar tana kallon waje, dai dai gidanta yayi parking ta bude motar ta fito ta xagayo ta inda Maryam take tace “Nagode sosai Maryam, ki taya ni yi ma Mumy godiya in sha Allah xan shigo anjima da yamma ko gobe, Allah saka da alkhairi” Maryam ta d’an yi murmushi tace “Ba komai, sai kin xo” kallon Aliyu dake ta kallonta tayi, da kamar baxa ta ce masa komai ba sai kuma tace “Thanks” daga haka ta juya xata wuce ciki, a hankali yace “Anjima xan kawo maki drugs din ki Iman” tace “Ohk” tana fadin haka ta shiga gida ya ja motar suka bar street din. Tun daga wannan rana gaba daya Khadijah ta ajiye khaleel da jawahir gefe daya, tsakaninta da su gaisuwa faram faram ita kanta tayi mamakin yanda har ta sake ma jawahir yanxu duk da ita sai wani daure mata take, Lkci daya Khadijah ta yakice khaleel gaba daya a ranta, ko don tashin dare da take yawan yi tana rokon Allah ya cire duk wani connection dake tsakaninta da shi a xuciyarta ne, yanxu tun safe in ta fita gidan dama sai yamma take dawowa kuma duk ta dawo xata tarar khaleel ya dauko shureim, wani lkcn basa ma sanin ta dawo, yanxu kam ita kanta tasan ta rage damuwa sosai, jarabawarta kawai ta sa gaba, duk bayan kwana biyu ta kan je gidansu Maryam gaida Hajiya Mariya, kuma duk taje sai sun hadu da Aliyu, wani lkcn ta amince ya maido ta gida wani lkcn kuma tace baxata hau motarsa ba shi dai kam sai dai yayi murmushi baxai ce komai ba, sai ta tafi tayi ta tausayin sa bata san dalili ba, har xuciyarta take ganin Aliyu kamar little Sudais dinta cos the little boy have all his fathers quality, Kuma tasan saboda Aliyu yasa ta sa ma kanta dangana haka, Wani rama khaleel yake da shi kansa bai san dalilinsa ba, gaba daya ba shi da sukuni, yanxu kam sure yasan Jawahir and Khadijah are cousins daga binciken da yayi but bai san ta inda xai billo ba, gaba daya kansa ya kulle, bai taba xaton haka ba, they are very close relatives, dauke masa wutan da Khadijah tayi ya fi komai bata masa rai, in har ta gaishesa a gidan to tare ta gansa da jawahir, in ko just haduwa suka yi su biyu ko kallon inda yake bata yi, sai ma saurin barin wajen da xata yi, shi dai yasan har sannan bai cire rai da ita ba ko don nuna mata iyakarta kan walakancin da tayi masa but how will that be when they are cousins with his wife Jawahir?? sure it’s not prohibited, but Uhm… A can Nigeria kuwa Sudais ya gama hada lefen sa tsaf, komai ya siya sai ya nuna ma Khadijah ta WhatsApp ko yayi mata, Yana gama hada lefen dama ya kai ma jiddah kayan fadar kishiya, tun da taga akwatunan hankalinta yayi mugun tashi, ya sanar da ita ko na meye bai tsaya saurarenta ba ya fice, Ta fashe da matsanancin kuka tana kallon kayan, yanxu har auren nan ya matso bata samu damar daukar number Khadijah a wayar Barrister ba gaba daya hakan ya faskara duk iya kokarinta, Nan ko bata san duk Barrister ya lura da take takenta ba ya canxa yanda yyi saving number Khadijah daga Amira ya mayar Ummu Shureim, Xaunawa jiddah tayi kan kujera wata dubara ta fado mata…. Murmushi tayi tana share hawayen ta a hankali tace “Allah ya kai mu ranan auren, ai dai Amarya xata tare koh? Toh a daren farkon ta gidan ka xan maku abinda ita xata yi da ta sanin auren ka, kai Kuma xaka gwammace baka aureta ba” wani murmushin ta kuma yi ta wuce daki xuciyarta fess, har Allah Allah yake ranan ya xo ta cika aikinta, ta tabbata Khadijah baxata kwana gidan ba Kuma har karshen rayuwarta xata ji baxata iya yafe masa ba, ba boka ba malam. Ana saura sati daya Khadijah ta taho hutu Barrister Sudais yaje katsina gun Kawunta bayan Umma ta basa address, ciwon kafa kawu jibril ke fama da shi sosai sai dai hakan baya hanasa tafiya, duk yaransa biyu da ya aurar na xaune gida da ya yansu auren ya mutu, gashi yanxu duk kudin sun ja babu komai sai motoci biyu da gidan da yake ciki, kawu na jin abinda ya kawo Sudais bayan sun shiga parlorn sa, ya dinga masa wani kallo yace “inaaa, you are mistaken don bani da wata ya wai Khadijah, ka dai koma ta kai ka gun dangin ubanta amma ba ni ba, tashi ka ban waje malam” Sudais dake ta kallonsa yace “Amma dai ka santa koh?” Kawu yace “Toh meye amfanin sanin nata, Yarinyar da rabon da na sa ta ido yau xai yi shekara goma sha, tana can tana yawon duniya da kishiyar babarta” Sudais ya san xa ayi hakan shi yasa ma ya fara xuwa shi kadai, bai taho da kowa nasa ba dama Kuma bai sa ran Kawunta xai yarda ya daura mata aure ba” Sudais yyi murmushi yana kallonsa da kyau yace “Kawu dama ba wai lallai sai kai xaka daura mata aure ba, Kar ka mance babu abinda kudi basa yi a duniya, kawai dai dama an sa na xo ne don a fita hakkin ka a matsayin ka na wan mahaifinta, bayan haka Kuma kawu yanxu xaka iya damka ma Khadijah gadon ta na mahaifinta tunda ta mallaki hankalinta?” Da mugun mamaki Kawu Jibril ke kallonsa baki bude, can ya mike da kyar yace “Kai a uban wa xaka xo min da xancen gadonta??” Mikewa Sudais yyi ya tako har gabansa ya fiddo Id card dinsa yana masa wani kallo yace “Ni a lawyer mai xaman kansa…. Barrister Aliyu Umar, don haka nake maka gargadi kawu kar ka yarda magana ta kai mu ga shiga kotu baxai maka kyau ba… 10 years kamar yanda ka fada is enough.. hand over her properties to her” Daga haka Sudais ya juya ya fita kawu ya bi sa da kallo cikinsa na kara baki sake…. Yau Khadijah ta gama exams tana bedroom tana ta shirye shiryen kayan da xata koma Nigeria da, Shureim kuma na parlor ta bar sa yana bacci taji kamar an bude kofa, juyawa tayi da sauri don bata ma san kofar a bude yake ba, tayi saurin daukan hijab xata fita suka kusa cin karo bakin kofar dakin.

Back to top button