Duk KarfinIzzata Book 2Hausa NovelsHausa Novels

Duk Karfin Izzata Book 2 Page 21

Sponsored Links

Book 2

Page 21

____da sauri hiyana ta koma palo ta ɗauko wayar ta lokacin da ta dawo ɗakin zaune a bakin gado ta same sa gaba ɗayan kunyar sa take ji yanzu gaban shi tazo ta tsugunna tare da miƙa masa watar tana faɗin “yaya Prince gata” batare da ya kalleta ba yace “sim ɗin zaki chire ki bani” zaro ido waje tayi sai yanzu ta fahimci me yake son yi wato bayaso tayi waya dasu diyana ko,shiru tayi ta kasa ko da motsi dan gaskiya tun da diyana ta dawo bazata iya kwana ɗaya basuyi waya ba,ita yanzu ya zatayi, ganin tayi shiru bata chire sim ɗin bane ya sanya ya ɗago kai ya kalle ta yayi niyar yi mata tsawa amma sai ya fasa saboda tausayin ta dayaji musamman daya ga face nata yadda ya sauya lokacin guda kasa kasa da sanyin murya yace “chiro sim ɗin ki bani idan kina son magana da su sai ki kirasu ta wayata”sunkuyar da kanta tayi kasa kafin tace “dan Allah yaya Prince kayi hakuri ka barmin kaga kai wani lokaci baka dawowa da wuri kuma kullun da rana muna waya da Aunty farida da Ammi” kawar da kansa yayi daga kallon ta ya ɗaure fuska sosai ya fara magana “ba dan su Aunty farida zan ansa sim naki ba nasan ko nace karki kira yar uwar ki sai kin kirata kuma idan kikayi haka ba ke kaɗai ba kuna gefa Aryan chikin tashin hankali da damuwa sister ki bata da lfy idan taji Voice naki tana kara birkichewa Aryan kema nan ki zauna kiyi ta kuka mara amfani addu’a zaki mata dan haka bani sim ɗin,duk lokacin da kike son magana da su Aunty farida ki furta afili kina son yin magana da su duk in da nake zan jiki ko nayi ni sa zan sanya a haɗaki da su” jikin ta har bari yake wajen chire sim ɗin kamar zatayi kuka haka ta chiro ta miƙa masa chikin sanyi murya tace “to yaya Prince ina son ganin Aunty farida da Ammi wlh ina kewar fuskar su” shiru ya ɗan yi kafin ya mata nuni da hannun sa akan ta zaun na gefen sa a saman gadon ba tare da yayi magana ba,chikin sauri ta koma saman gadon ta zauna kusa da shi

remote ya ɗauko daga bedside drawer ya kunna makekiyar Tv dake chikin ɗaki tana sai tin gadon sa, Cameras da ban da ban ne a jikin Tv tafiya yake kai tsaye ya shiga Cameran gida zai wuce idon sa ya sauka kan wata tsohuwar Camera na ɗakin da Ahmad ya kwanta rashin lfy bai san ma ta ya akayi ta shiga Cameran ba, tsaki yaja yana kokarin fita dai dai idon sa ya sauka lokacin da hiyana ta fara yiwa Ahmad addu’a da tsawar da taji da duk wani abu da ya faru a ɗakin, dakatawa yayi ya fasa fita ya chigaba da kallon ita kan ta hiyana waro ido waje tayi ta chigaba da kallo dan ita kwata kwata tama manta da yaya Ahmad ya taɓayin wani chiwo a rayuwar sa tun daga farko har karshen yanar da Ahmad ya warke sai da suka kalla a tare

nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke lokacin da suka kammala kallo satar kallon ta yayi ta kasar ido yayin da itama take satar kallon sa tana jiran taji me zai che, shiru yayi yana tunani idan dai hakane zuchiyar yarinyar nan take bai kamata naki ansar ta a matsayin sister na ba,tabbas ko dan taimakon ɗan uwana da tayi ya kamata itama na fara tausayin ta na ɗauke ta kamar Zahra Auta, da wanna tunani ya fita Cameran ɗakin Ahmad ya shiga na gidan Aunty farida tare da ɗaukar wayar sa ya kira layin Aunty farida

lokacin da kiran Bgs ya shigo wayar Aunty farida tana bedroom, nata Camera kuma a iya palo Bgs ya sanya shiya sa ya kirata domin ta fito palo, zubur Aunty farida ta miƙe tsaye lokacin da ta ga sunan mai kiran ta dogon numfashi ta ja tare da sauke ajiyar a fili tace “yau kuma an tuna da ni kenan yau kuma ko meya sanya Prince ya kirani ko dai ya hakura ya sauko ya chireni a blacklist ɗin ne,jiki na rawa ta ɗauki kiran tare da manna wayar a kunne tana faɗin “hello” ba tare daya amsa ba yace “ki fito palo” yana gama faɗin hakan ya katse kiran, chikin zafin nama ta nufi palo jikin ta har bari yake ita duk tunanin ta yazo gidan tane dan bata taɓa tunanin akoi Camera a gidan na ta ba

pitowa palo tayi amma bataga kowa ba zama tayi saman sofa tana jiran taji me zai faru kuma gaba, massage ne ya shigo wayar ta tana dubawa ta ga Bgs ne ya turo mata, “kunna cameran system naki” abun da aka rubuta a sakon massage ɗin kenan tunani ta shigayi anya Safras lafiyan sa kuwa anya bai sha wani abun ba kuwa? Mutun ne kamar wani aljani bai da aiki sai bawa mutane umarni kamar shi ya haifesu to idan nace ba zan kunna cameran bafa dan iskanci tun yaushe bamuyi waya da shi ba amma ko ya tambayi ya nake, wani tunanin ne ya sake faɗo mata to idan abu mai mahimmanci zai nuna mata fa ai gara ta kunna cameran dan tasan shi dai Safras baya chewa ayi abu haka kawai sai da dalili, tuna hakan yasa ta miƙe chikin sauri ta karisa wajen table ɗin tsakiyar palon ta ɗauko system ɗin duk abun da take Bgs da hiyana suna kallon ta tana kunna system ɗin ta shiga Camera tana shiga Bgs yayi connecting nasu,

Aunty farida bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba ganin Bgs da hiyana zaune waje guda saman gado ɗaya kawar da kai gefe Bgs yayi yana faɗin “ya Junior? Ba karamin haushi Aunty farida taji ba wato ma ba zai gaishe ta ba sai ya wani kawar da kai yama faɗin ya Junior wai shin yaushe Safras zai chan za ne shikan a rayuwar sa, hiyana ce ta katse ta da chewa “Aunty farida ina wuni dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan hiyana lokacin guda ta saki wani Cool murmushi tana son suyi gulma da hiyana amma ba hali tana so ta tambayeta ya akayi suke tare waje ɗaya da Bgs bayan ada tasan ko fuskar hiyana bai san gani amma duk ba daman yin haka dan yana zaune ya chiro wayar sa yana latsawa duk da hankali sa na kan wayar sa yana jin duk abun da suke sosai hiyana da Aunty farida ke zuba hira suna dariya kamar wasu kawaye kwata kwata hiyana ta manta ma Bgs na jinsu ta saki jiki sai zuba hira suke sai da ya gaji sun chika masa kunne dan shi ba mai son surutu bane chikin sauri ya ɗauki remote yayi disconnecting da Aunty farida ko sallama bai bari sun yi ba

wajen Ammi ya shiga ya ha ɗasu da Tv palon ta dan a iya palo kawai yake sanyawa matan Camera kannan sa maza ne yake samu su har bedroom na su

Ammi na zaune a palo tana shan fura ga Tv a kunne tana kallon News, kamar daga sama taga kallon ya ɗauke sai ganin hiyana da Bgs tayi zaune a bakin gado,tasha ruwan mamaki amma sai ta ɓoye mamakin nata chikin farinchiki kamar bakin ta ba zai rufu ba tace “my hiyana a ɗo jam (my hiyana kina lfy)? “Lfy lau Ammi ina wuni? Ammi dai tama kasa yin wani dogon magana gaba ɗaya farinciki da murna ganin hiyana ya sanya harshen ta yayi nauyi “Ammi ya su yaya Haidar? Hiyana ta sake jefo mata tambaya
Sai lokacin Ammi ta samu damar chewa “my hiyana yaya jiffina oɗo wanna ma ko haɗi ko? to owala wanna ma dai dai a yacha am (my hiyana yayan ki ya sauko yana miki abun da ya dace ko idan fa baya miki ko yana miki wani abun da baki so to ki sanar da ni karki ɓoyemin kin ji) Ammi tayi magana chikin harshen fullanci ne dan bata son Bgs yaji me suke faɗe satar kallon sa hiyana tayi ta kasan ido dan ita dai tasan Bgs na jin fullaci ta taɓa jin sa yana magana da harshen fullanci a waya ko kallon in da suke bai yi ba latsa waya kawai yake kai kace kwata kwata baya jin me suke faɗe, jiki a mace hiyana tace chikin harshen fullanci “babu abun da yake min Ammi sai kyautatawa” sosai suka sha hira Ammi sai kawo mata zanchen Bgs take da fullanci hiyana na kakkauchewa dan karya mata hukunci

Daya ji hiran Ammi fa ba mai karewa bane sai ya kashe Tv nasu gaba ɗaya yana jan tsaki su mata basu da wata matsala a rayuwar su idan sun haɗu dai sai suyi ta magana ba hutawa, chikin sanɗa hiyana ta miƙe tana son ta zame ta gudu dan tasan duk abun da Ammi ta faɗa yaji kuma yanzu zai iya mata wani abun akan hakan duk abun da take yana kallon ta ta wutsiyar ido sai da ya barta ta kai bakin kofar fita chikin harshen fullanci yace “waru haɗo (zonan)” turus ta tsaya zuchiyar ta na dukan uku uku dan daman tasan yaji kuma tun da yaji ba zai kyaleta ba mutun kamar wani aljani ko waye ya koya masa fullanci ohon masa ko aina ya koya oho gashi fullanci nasa ma har yafi nasu hiyana fita,

jiki a mace ta koma ta tsugunna a kasa tana faɗin “damin ɗo (gani nan) kamar bai san da zaman ta awajen ba yayi shiru ya chigaba da latse latsen wayar sa tun hiyana na sa ran zai yi magana har ta chire rai kwatsam sai taji sexy Voice nashi ya daki dodon kunnen chikin harshen fullanci “or daman kin che wa Ammi ina miki wani abun kenan ko? To me nake miki faɗa min naji” girgiza kai ta farayi tana faɗin “aa yaya Prince wlh ba abun da kake min” wani mugun kallo ya jefa mata da manya manyan green eyes nashi nan wadda ya sanya ta haɗiyar yawun wahala da kyar

“baki che mata komai ba baza tace na rage muguntar dana ke miki ba ko? Daman ina miki mugun ta kenan ko? to faɗa naji wani mugun tan nake miki? Sunkuyar da kai kasa tayi chikin sanyin murya tace “kayi hakuri ba zan sake ba na tuba dan Allah karka hukun tani nayi alkhari ba zan sake ba” dogon tsaki yaja bai sake magana ba yayi shiru itama shiru tayi tana tsugunne almost 30mins suka kwashe suna zaune a wajen ko kallon in da take bai sake ba hiyana ji take kamar zata faɗi dan ta gaji da tsuguno tana tsoron ta tashi dan yanzu ma bata san hukuncin da zai mata ba,karta kara laifi saman laifi sai da suka kara 10mins a haka sanan Bgs ya miƙe ba tare da yabi ta kan taba ya fice daga ɗakin yana fita ta zauna dirshan awajen tayi zaman yan bori tana mai da numfashi

30mins da tafiyar Bgs sai gashi ya dawo chikin sauri tana zaune yarda ya fita ya barta ta shiga duniyar tunanin meke damun diyana saxy Voice nashi ne ya daki dodon kunnen ta “ke zonan!” da sauri ta miƙe ta karisa wajen sa saman gadon ya haye ya zauna a tsakiya tare da nuna mata gefen sa akan ta zauna, system na shi dake saman bedside drawer ɗayan side ɗin ya ɗauko ya kunna system ɗin sauri sauri ya na yi yina tambayar ta

“wani magani kika bawa Ahmad? Satar kallon sa tayi ta kasan ido kafin tace “ruwa addu’a” chak ya tsaya da latsa system ɗin ya juyo yana kallon ta dan shi a tunanin sa wani maganin gargajiya ta bawa Ahmad “ok to ya kamata ki sanya sister ki a addu’a domin itama kusan chiwon ta ɗaya da Ahmad” na rai na rai tayi da ido chike da tausayin diyana ta fara magana “to dan Allah yaya Prince kasa a mai da ni gida sai na mata addu’a kaji? “Ki mata addu’a daga nan ko ina take zai same ta”yana kai karshen maganar ya miƙe ya fice daga ɗakin yana jiyo sassanyar Voice nata tana faɗin “Allah ya tsare a dawo lfy” a chikin zuciya ya amsa addu’ar yayi ficewar sa, gyara kwanciyar ta tayi saman gadon tana kallon sama kamar mai tunanin wani abu,ko me ta tuna sai kuma ta miƙe da sauri ta shiga toilet ta ɗauro alwala tazo ta fara sallah a sujadar farko tayiwa diyana addu’a sosai da sosai tana addu’a tana hawaye sharshar ta daɗe awajen tana jerawa Allah kirari tana rokon sa daya bawa diyana lfy bayan ta gama ta made daddumar ta koma saman gado ta kwanta

KANO

Abba Aryan da wani Babban malami ne zaune a palon Abba suna tattaunawa akan abubuwan dasu suke faruwa a gidan lbr Abba ya fara bawa malamin tun farkon chiwon Ahmad da duk wasu abubuwan da suka faru a gidan har izuwa yau,dogon numfashi malam ya ja lokacin da ya gama jin bayanan Abba chikin nitsuwa da girma ya fara magana

“gaskiya kunyi sakaci tun farko kun riƙe boko sosai kun yasan da addini da aladu duk waɗan nan abubuwa da suka faru a gidan nan ba komai bane face sihiri da tsubbace tsubbace yanzu dai ku kawomin marasa lfy bari afara yimusu addu’oe idan na gama sai abasu ruwan rubutun Alkur’ani mai girma” kasa kasa Abba ya sachi kallon Aryan dan yasan mawuyacin abune Aryan ya yarda dan su kwata kwata basa son abun gargajiya, komai nasu da ya shafi rashin lfy sai dai likita tun farko su sukaki a kira malami yayiwa Ahmad addu’a,gaba ɗaya su suka sanje gidan gargajiya izuwa gidan boko basa yarda da duk wani abu na gargaji da aladu,shiru palon yayi dan Abba bai san me zai ce ba “Ranka ya daɗe akawomin marasa lfy” malam ya mai mai ta maganar sa, kallon Aryan Abba yayi face to face yace “Aryan ka kawo diyana” miƙewa Aryan yayi ya nufi kofar fita har ya kai bakin kofa ya dakata da tafiyar ba tare da ya juyo ba yace “bana bukatar duk ire iren waɗan nan abubuwan Abba ni ban yarda da shan ruwan rubutu da sauran su ba ni Abba kasan ban son irin haka da kai na zan nemawa matata lfy ta hanyar da nake ganin ya fi ye min” yana gama faɗin hakan ya fice daga palon, ajiyar zuchiya Abba ya sauke daman ya san haka zata faru dan dukka yayan sa basu yarda da gargajiya ba a kan boko suka tashi kuma a hakan suke tafiya har yanzu

Kallon Abba malam yayi ya lura Abba ya shiga damuwa sosai chikin ni tsuwa ya fara magana “Ranka ya daɗe karka damu in dai irin yayan nan naka ne mun saba haɗuwa da ireren su yanzu dai zan sanya a kawo maka ruwan addu’a sai ka san yadda zakayi ka baiwa ita yarinyar” sunkuyar da kai Abba yayi dan kwata kwata bai ji daɗi ba ache ya sa a kira masa babban malami kamar wanna Aryan ya masa irin wanna chin fuska haka abun sam bai yi ba

dafa kafaɗar Abba malam yayi yace “karka damu yanzu dai kuyi taka tsan tsan domin masu bin ku da wanan asiri asiri da tsuɓɓace tsuɓaɓan nan dama masu bin family ka da sharri suna tare da kai makusan tan kane yanzu kasan yadda zakayi ka bawa duk family ka ruwan addu’ar nan da zan aiko ma,domin da alama makiyin ku na kusa sosai da ku sanan zan aiko maka da turaren ayi hayaki dukka gidan nan dan na san koda an bawa yarinyar addu’ar ita ta warke zaa iya sake yima wani asirin sai ku shirya” malama na gama magana ya miƙe ya nufi hanyar fita, kasa tashi Abba yayi yaje ya raka malam tunani ya shigayi makiyin mu na tare damu to wanene ke mana wanna abun? gaba ɗaya Abba yayi iya tunanin sa a gidan sa dai bai ga wan da zai iya aika ta wanna abun ba sai dai in daga wajen,jiki ba kwari ya miƙe ya shige bedroom na shi

UK

4pm

Sun gama shiryawa gaba ɗayan su suna zaune a babban palon kasa suna jiran hiyana zasu tafi wajen shakatawa sai murna su Zahra keyi yau yaya Khalid zai kai su yawo,gaba ɗayan su sun shirya chikin dogayen riga sai dai rigar ta kama su sosai Zahra da lamrat sun sanya ɗan karamin hijabi baki a kansu ita kuwa amrat ɗan karamin mayafi ta sanya yaya Ahmad sai tsokanan su yake yana dariya sunyi kyau da su abun su kamar ka sache su ka gudu da su dan kyau wajen 10mins suna zaune suna jiran hiyana shiru shiru tsaki Fahad yaja kafin yace “amrat je ki kira sister tazo mu wuce” da sauri Zahra ta miƙe tana faɗin “bari naje na kirata” bata jira amsar su ba ta haura sama.

Zaune a bakin gado ta isko hiyana ta gama shiryawa chikin wandon jeans baki crazy,da yar t-shirt fara mai laushi rigar tana da ɗan dogon hannu amma bai kai karshen hannun taba ta ɗaure gashin kanta a tsakiyar kai
sai chika take tana batsewa,kallo ɗaya Zahra ta mata ta fahimci abun da ya hanata fitowa dariyar mugunta ta guntse chike da iya shege da tsoka Zahra tace
“Aunty Hiyana yaya Khalid yace karki kuskura ki kara 1mins baki fitoba in kika kara tafiya zamuyi mu barki” wani mugun kallo ta wurgawa Zahra ji take kamar ta shako ta mata duka,ganin haka ya sa Zahra ta kariso chikin ɗakin ta chire hijabin jikin ta ta sanya mata ta kamo hannun ta suka nufi kofar fita,binjikin ta da kallo hiyana tayi kwata kwata hijabi a iya kirji ya tsaya mata bata san ya zatayi ba bazata iya fita gidan nan da wanan shigar ba gashi kuma tana mutuwar son fita dan ta gaji da zaman gida,runtse ido tayi ta rasa ya zatayi ahaka Zahra ta jata har palo, Khalid na ganin su suka miƙe a tare suna faɗin “muje ko? da sauri Zahra ta koma ɗaki ta ɗauko wani hijabin ta sanya ta dawo palo

Jerawa sukayi kowa ya rike hannun matar sa hiyana da yaya Ahmad suka gero daga ƙarshe suna fita harabar gidan dai dai lokacin motocin Bgs ya danno kai chikin gidan, tsayawa su Khalid sukayi suna jiran fitowar sa su gaisa

Jibga jibgan sojojin sa ne suka fara dirowa kasa daga saman nasu motocin ɗaya daga chikin su ya buɗe wa Bgs kofar motar ɗayan kuma ya buɗewa Abdol ya fito,jeruwa sojojin sukayi suka fara sara masa bai bi ta kan kowa ba ya nufi chikin gida ko kallon in da su Khalid suke bai yi ba ya wuce su

har ya kai bakin kofar shiga palo ya dakata ba tare da ya juyo ba yace “ke zo ki haɗamin fruits da Black tea” yana gama faɗin hakan ya wuce chiki, hiyana kamar zata yi kuka haka ta juya ta koma chikin gidan

Kallon su Yusuf Khalid yayi yace “muje ko” “aa yaya Khalid mu ɗan jira sister mana” chewar Yusuf murmushi Khalid yayi kafin yace “baza tazo ba muje kawai” “kamar yaya baza ta zo ba kuma” Ahmad ya tanbaya yana tsare Khalid da ido,

“Auta kuje wajen mota ku jiramu” chewar Khalid ba musu Zahra lamrat amrat suka wuche suka nufi wajen motocin suka tsaya

murmushi Fahad yayi ya fara magana “daga jiya zuwa yau na lura da wani abu tsakanin yaya Prince da sister, amma ba zan iya fassara menene ba mu dai je zuwa” tsaki Khalid yaja kafin yace “ai tun ranar dana sanya snake a toilet na sister, na fara sanya yakinin akan Bgs zai sauya dole idan suka koma kwana ɗaki ɗaya, sai dai ba yanzu ba sai alluran jikin sa ta sake sa daman 2 weeks alluran ke ɗauka ina ga ayanzu ya kai 10 days da yiwa kansa allura wlh duk ranar da alluran nan ta sake sa zai fara sha’awar sister daga sha’awa kuma sai soyayya ta biyo baya” dogon salati Fahad yayi kafin yace “amma yaya Khalid ka iya shirya kitinurmura daman kai ka sanya snake a toilet na sister?” dariya Khalid yayi kafin yace “ai ba a iya nan na tsaya ba ma nayi abubuwa dayawa sai dai ba zan faɗa muku ba wlh sister tana bani tausayi gashi Auren ta da Bgs babu saki to kunga tun da babu saki dolene a matsayin mu na wayan da suka san wanene Bgs mu tsaya tsayin daka mu taimaka mata dan ta samu fatinciki ni dai yanzu na ɗaura ɗamarar yaki da Bgs wlh ko jiya naso zuba masa magani chikin abinci amma dana tuna wanene Bgs sai na fasa dan idan na kuskura na zuba masa magani yasha tofa inaga zamu iya ɗaukar gawar sister dan bazata iya ɗaukar Bgs a yanzu ba tayi kankanta sai gaba” Yusuf ne ya ansa zanchen da chewa “ni nasan dole Bgs zai fara son sister sai dai matsalar bai san me so ba bai iya so ba,bazai taɓa gane yana son taba dan bai taɓa mu’amala da wata mace ba idan ba iyayen mu ba ko Aunty mardiya bai taba zama yayi magana da ita ba kunga ko ya fara son sister ba zai taɓa gane yana son taba” “kabar wanna maganar Yusuf duk na riga na gama shiri a kan haka yanzu ma na gama shiryawa sister yadda zata masa idan alluran nashi ya sake sa,bazan iya fuskantar sister na faɗa mata baki da baki ba shi ya sanya na rubuta mata massage a waya lokacin da na sai musu waya yanzu dai lokacin kawai zaku jira nan da two days dole Bgs ya fara sha’awar sister dole kuma ya fara kula ta bashi da zaɓi dan ba zan taɓa bari ya sake yiwa kansa allura ba,dani da Aryan mun gama shirya masa kitimurmura ta yadda ba zai sake yiwa kansa allura ba” chewar Khalid ya karisa maganar tare da kama hanyar tafiya “laaaa yaya Khalid wato kai da yaya Aryan kuna munafurtan yaya Prince ko?to sai na faɗa masa” chewar Fahad yayi maganar chikin raha “amma ni ina ganin kamar mujira sister dan wlh naga alamar tana san zuwa sosai kuma daman dole zata so zuwa zama waje ɗaya fa takurace” chewar yaya Ahmad, juyowa Khalid yayi ya dakata da tafiyar da yake yace “sister fa baza taje ba idan kun lura ba Black tea ko fruits yake son shaba kawai shigar da tayi zamu tafi ne bai masa ba lokacin da ya fito daga motar sa wlh ina kallon sa kallon ta yake ta kasan ido kayan jikin tane bai masa ta fita da su ba shi ya sanya, kuma dai wani lokaci sai ku rinka yin abu kamar baku san shi ba komai da Bgs zai chi a duniyar nan to da time na shi kai bama abun chi ba komai da zai aikata yana da lokacin yin sa baya barin wani lokacin ya shiga na wani yanzu fa karfe 5 ake nema ba zai chi wani abuba sai 12 dare kun san Bgs da bala’i kishi ko ku da kuke yan uwan sa ma yaya bare sister da yanzu tauraron ta zai fara haskawa a zuciyar sa” yana kai karshen maganar chikin raha da tsokana tare da wuche ya nufi wajen su Zahra chikin sauri su Yusuf suka bi bayan sa suna dariya,chikin motocin su suka shiga kowa da matar sa ya zauna yaya Ahmad shi kaɗai,a tare motocin suka fita gidan

A ɓangaren hiyana kuwa tana komawa chikin gida kitchen ta nufa ta shirya masa abun da ya bukata ta ɗauka ta nufi part na su zaune saman sofa a chikin bedroom ta same sa, ya jingina kan sa yana kallon sama chikin nitsuwa ta tako zuwa wajen saman table ta ajiye masa try ɗin ta dawo gabansa ta tsugunna ta fara chire masa ta kalmar kafar sa tana faɗin “sannu da dawowa ya Aiki” bai amsa mata ba kuma bai sauko da kansa ba yana kallon sama, chire masa ta kalmi tayi tare da safa ta ɗauka ta wuce ta ajiye wajen da ya dace, ta dawo tana kokarin tsugunnawa yayi saurin ɗaga mata hannu tare da nuna mata kusa da shi akan ta zauna ba musu ta zauna ba tare da ya kalle taba yace “ya sunan mahaifiyar ku? “Sunan ta Fateema amma yan garin mu suna che mata Ummi dan sunan kakan mune wadda ta haifi baban mu…ba ta karisa maganar ba ya ɗaga mata hannu yana faɗin “iya sunan ta na tambaya ban nemi wani karin bayani ba”shiru ta ɗan yi na yan mintoci kafin tace “yaya Prince in tafi? Sai lokacin ya sauko da kallon sa kanta ya tsare ta da ido tare da ɗaga mata gera ɗaya alamar ki tafi ina, narai narai tayi da fuska chikin dakiyar zuchiya tace “yaya Khalid ne zai kai mu yawo shakawata kuma suna jirana” ta kai karshen maganar kamar zatayi kuka “ba zakije ba” yana kai karshen maganar ya mai da kansa ya jingina yana kallon sama,ji take kamar ta shake sa dan haushi ta gaji da zaman gidan nan,ta gama tsarawa yau zata fita,shiru ta zauna da kamar zatayi kuka amma sai ta danne dan tayiwa kanta alkawari ba zata sake bari yaya Prince yaga kukan taba,da ta tuno ranar Monday zasu fara zuwa school sai tayi murmushi ko ba komai ranar Monday zata fita ai

“Yaya Prince ga tea ɗin fa zai yi sanyi” ta faɗa tana satar kallon sa,shiru yayi na ɗan lokacin kafin yace “ɗauka ki sha” “ni bana shan tea” ta bashi amsa chike da tsoron me zai biyo baya, wani mugun kallo ya gefa mata wadda ya sata ɗaukan cup ɗin tea ɗin ta fara sha tana ɓata fuska dan Black tea ɗin ko sugar babu a cikinta sai lemun tsami miƙewa yayi yama faɗin “ki fitarmin da kayan sawa” ya kai karshen maganar yana shigewa toilet

Yana shiga toilet tayi saurin ajiye cup ɗin tana goge bakin ta tare da fito da harshen ta waje tana gogewa dressing room nashi ta shiga kayan sa ta fara bi da kallo a shesshirye suƙe wajen wandon jeans daban wajen t-shirt daban wajen suit daban wajen takalmi agogo daban kowanne wajen sa daban tasha ruwan mamaki lokacin da idonta ya sauka kan kayan hausawa ashe yaya Prince yana da kayan hausawa gasu dayawa ma hannun ta har rawa yake wajen fito masa da jumpa da wando na wata dakakkiyar shadda mai bala’i tsada da kyau fari tas, chikin sauri ta zaɓo masa farar takalma da dangareren agogon diamond ta fito ta ajiye masa saman gado ta ta koma saman sofa ta zauna.

After 45mins

Ya fito ɗaure da towel a kugun sa kallo ɗaya yayiwa kayan da ta ajiye masa a saman gado ya kawar da kansa kai tsaye ya wuche gaban mirrow ya fara gyara gashin kansa duk abun da yake tana zaune tana satar kallon sa bayan ya gama gyara lallausan bakin gashin kan sa ne ya shafa body lotion nashi masu kamshi da tsada sanna ya wuce dressing room nashi jim kaɗan ya fito shirye chikin wando 3quarter fari da singlet fari tas ya ɗauki laptop nashi dake saman table ba tare da ya kalli in da take ba ya fice daga ɗakin

jiki ba kwati ta miƙe tazo ta kwashe kayan da ta fiddo masa da su ta mai da dressing room ɗin ta fito ta wuce wajen hutawar sa na chikin ɗaki

Gaisuwa da jinjina gareku yan Duk Karfin Izzata paid group Allah ya bar zumunci ina muku fatan alkhari ina matikar miko godiya gareku masu min comments ina magana ne akan yan duk karfin izzata comments section group ina jin daɗin comments naku ina godiya da muku fatan alkhari, masumin addu’oe ina godiya sosai Allah ya saka muku da gidan aljan na, wayan da basa min comments kuma ina gaishe ku Allah ya barmu tare ina kaunar ku love u all lodi lodi

💋Duk Karfin Izzata 💋

 

💖The Talent Troupe Writer’s 💖

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

💋I Hate you masoyiya gidan Aunty lodi lodi💋

💋Aunty sadeeya ina kaunar ki lodi lodi💋

💋Mum sayyid ke kam naki kaunar na daban ne love u lodi lodi 💋

Back to top button