Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 24-25

Sponsored Links

BOOK 1

Free page 24 and 25 🦋

“Tabbas yanxune ya kamata mu cika kudirin mu”,cewar d’aya daga cikin su me sanye da jajayan kaya a jikinta, gabaki d’ayan su maida hankalin su sukai kan daya daga cikinsu wacce take kishingide tun d’azu bata motsaba, tashi tsaye tayi tana kurban wani dan abu cikin wani Kofi me kayatarwa,duk da ba a iya ganin ko wacece cikin kausashshiyar murya ta soma magana rai a bace “bazan taba laminta ba , ginin da na soma tunda dad’ewa babu wani hamshakin daya isa ya rushe munshi”,duk hada baki suwai wajan cewa “tabbas maganar ki gaskiya ce abar kauna “,suka gamawa suka fara surutunsu cikin wani yare kafin su had’a kofunansu waje d’aya alamaun cheers .

******
KANO

Kasantuwar akwai tazara tsakanin UMC da nasarawa hakan yasa saida suka danyi doguwar tafiya kafun su karaso Layin nasu, Kai tsaye daya daga cikin manyan gidajen dake Layin khaleed ya nufa,yayinda Alhaji kabeer yake zaune a dayan side din, zahra da oumma suna baya,tun bayan shigarta motar ta dukar dakanta kasa ,lokaci zuwa lokaci tana share hawayen da ke taran mata a ido, duk akan idon Alhaji kabeer da lokaci zuwa lokaci ya kan kalleta ta mudi bi, itama zahra nagefe ta zuba tagumi sosai take jin tausayin oumma da labarin ta, “ya kamannin taheer da taheeran suke “,tunda yan biyu ne zanzo naga kamanninsu nasan za’ayi kyawawa musamman yadda oummansu take da kyawu itama kamar wata balarabiya, tunanin da ke yi mata yawo akai kenan har su ka karaso gidan bata sani ba, horn khaleed yayi wani katan soja dake ganin gate din gidan ya bude tare da sara musu, babban gida ne Wanda ya hadu iya haduwa da kayan alatu komai na more rayuwa akwai a gidan, parking khaleed yayi a parking space,tare da futo wa ya bude wa mahaifinsa kofa,itama zahran futowa tayi har lokacin oumma kanta na sunkuye batasan an tsaya ba sai da zahra ta tabata,dago da kyawawan idanuwanta da suka sauya tayi tare da sakar wa zahra guntun murmushi,”nagode “,murmushi zahra tayi mata tare da bude mata kofar, fitowa oumma tayi tana bin katan gidan da kallo kafun ta sunkuyar da kanta ganin ta hada ido da Wanda yace mata sunansa Alhaji kabeer,murmushin manya Alhaji kabeer ya saki kafun yace “Bismillah “ya karasa da nufar inda zai sadashi da cikin gidan,”oumma Bismillah “ cewar khaleed da ke gefen ta ,saurin dago da idanuwanta tayi jin sunan da ya kirata da shi kafun ta soma tafiya cikin sanyin jiki zahra na binsu a baya, a cikin kyataccan falon gidan suka tsaya,sosai falon ya hadu iya haduwa, ba wani tarkacene aciki ba amma sosai ya hadu,kallan zahra Alhaji kabeer yayi “daughter kaita masauki ta dan huta” sosai zahra ta murmusa “to dady”kafun ta dauki magun mugun oumma ,kallan oumma tayi haryanxu da murmushin nan akan fuskarta” oumma bari na kaiki dakin da zaki hutu”,itama oumma dan murmushi ta sakarmata tana jinjina karamci irin na mutanan gidan duk da kallo daya zaka musu kasan masu arziki ne amma basu wulakanta taba.

Wani dan corridor suka mi’ka kadan ya Kawosu wasu ‘kofofi dake kallan na junansu,kofar karshe zahra ta bude mata , babban d’a kine a wajan,gadone me fadi sai wardrobe ,komai na set d’in gado a kwai a dakin brown colour , murmushi zahra ta sakar mata “oumma Bismillah “ jinjina mata kai oumma tayi , a sanyaye ta furta “nagode”.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Sanye take cikin maroon d’in abaya A shape,kayan sosai ya fito da shape din jikinta, cikakken gashin kanta ya fito sosai ta gefe gefen kanta da ya kwanta,kwance take kan 3 sitter din falon ammi tana bacci cikin kwanciyar hankali, zoya ce ta shigo falon itama cikin shigar ta sa’banin tahee ita kananan kayane a jikinta bink colour Riga da wando, kanta sanye da pink din hula itama gashin go shin ta sosai ya fito, gashin d’awisun da ta zo nunawa tahee take ta faman wasa dashi harta nufa hanyar dakin taheen sai kuma ta jiyo ganin ta kwance tana bacci, saurin rufe bakinta tayi tana dariya kasa kasa kafun ta salallabo a hankali ta nufi inda taheen take, gashin d’awisun ta dauka ta somayiwa tahee tafiyar tsutsa a tafin kafarta, motsa kafan kadan tahee tayi kafun ta gyara wanciyarta, kara sa mata gashin zoya tayi nan ma motsa kafar tata tayi a hankali tana ya mutsa fuska,ganin hakan yasa zoya cigaba da sa mata d’awisun, cikin sauri tahee ta farka har dan kwalinta na zamewa, sosai zoya ta fashe da dariya ganin yadda tahee ta ‘bata fuskarta, itama tahee ganin zoya yasa ta mike da niyar kamota,sauri kaucewa zoya tayi tana dariya, ganin hakan yasa tahee binta da sauri, gudu zoya ta sa tana dariya tare da komawa bayan kujera, ganin hakan yasa tahee binta da gudu har dankwalin kanta ya faduwa kasa, bata damu da faduwar da yayi ba ta cigaba da bin zoya da niyar kamota ,itama zoyan ta ki bari ta kamota sai zillewa take tana mata dariya, ganin hakan yasa tahee sakin duk karfin ta ta biyo zoya da ta nufi hanyar fita da gudu gashin kanta sai faman lilo yake a bayanta, karan da tayi da abune yasata yin baya baya kamar zata fadi , batasan lokacin da ta fado kansa ba,sai daddad’an kamshin da ya cika mata hanci , da sauri ta wayo idanuwanta waje “na shiga uku ni tahee, kullum sai kinyi lefi”, saurin sunkuyar da kanta kasa tayi  tare da soma wasa da yan yatsunka, dai dai ta bude baki da niyar yin magana taji an capko dogon gashin kanta me shegen sanshi da daukar ido, tanbayar da ya jefo Matane yasata zare ido “ are you a non-Muslim da zakiyi Karin gashi a kanki” ya karasa zancen nasa da sauke idanuwanka kan gashin nata, sosai sukai masa dadin a tafin hannu musamman yadda suke kyalli amma a zahiri sai kara hade fuskarsa da yayi, “ni ban kara komai ba” ta fada muryarta na rawa rawa kamar me tsoran wani abu, kara damke kan nata yayi a hannunsa da karfi,sosai taji zafin yadda ya damki gashin nata ,bata san lokacin da dora hannunta kan nasa ba tana rintse idanuwanta, hawaye ne suka fara zubo mata cikin rawar murya ta soma magana “ka..kayi hakuri”, pink lips dinta dake motsawa a hankali ya zubawa idanuwa kusan minti daya ganin tana kokarin bude idanuwan yayi sauri hankad’a ta tafadi a kasa, amaimakon yashiga cikin falon sai ya bar falon gabaki daya, bin bayansa da kallo tahee tayi tana hararar iska ,”arrogant kawai “ta fada cikin sauri kafun ta toshe bakin ta gudun kar wani yaji, mikewa tayi a hankali “ke kuma zan kamakii, sabida kisan halin kayanki shiyasa kika gudu ni kuma aka Huce akai na thank god be ganki ba”ta karasa maganar tana sakin murmushi kasa kasa tare da shafa gashin kanta “wai gashin doki”wani murmushin ta saki tunano kalamansa, lokaci d’aya kuma duk fara’ar fuskarta ta dauke tuno oumma da taheer da tayi, yau kusan sati biyu basuyi waya ba, tunanin hakan yasa ta fara tunanin yadda zata yi Waja da su wajan ammi.

4:30 ammi ce ta shigo falon bakin ta dauke da sallama , har yanxu murmushin fuskarta be ‘boyuba, kallan tahee da ke zaune ita kadai tayi, “sorry daughter na barki ke kadai “, itama murmushi tahee ta sakar mata “sannu da zuwa ammi”saida ta zauna tukun na ta amsa mata, mikewa tahee tayi da nufar kitchen bata dade ba ta fito dauke da kara min tray, lemone a ciki masu sanyi gefe guda kuma kayan fruit ne cikin wa ni dan bwol, glass cup din dake kai tahee ta dauka da niyar zuba mata kunun ayar ammi tayi saurin Girgiza mata kai “no daughter ban dade da Shan ruwana ba , bani fruit din nasha “, bata ce komai ba ta ajje cup din tare da miko mata fruit din “nagode “shine abunda tace, murmushi tahee ta sakar mata batare da ta ce komai ba , kallan ta ammi tayi sau daya kafun ta dauki banana , sai da ta kammala cin bananar kafun ta dauki wayanta, dan danne danne tayi kafun ta dora wayan a kunne ,kusan sau uku tana hakan kafun ta kalli tahee, “yau 3 days ina gwada number yaya amma bata shiga, kiyi hakuri zan kara gwada zuwa anjima sai ku gaisa nasan kinyi kewarsu “sauke ajiyar zuciya tahee tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi dan tunda tazo ammi take kyautata mata kamar yar cikin da ta haifa, kauda maganar tayi ta hanyar sa wata jiran, sun dade suna hiran su cikin raha lokaci  zuwa lokaci ammi na kara wayarta a kunne , kiran sallahn magariba ne ya tayar dasu ,ita ta nufi sama tahee Kuma ta nufi dakin ta, tun jiya take jin wani iri kamar period dinta zaizo, koda tayo alwala sai da ta duba tukunna kafun ta fito, sallahr magariba tayi bata tashi a Wajan ba har saida tayi sallahr isha bayan karatun alkuranin datayi, yau akan daddumar bacci ya dauke ta lokacin da take karatun azkar dinta.

Karfe 6:10am na safe tahee ta farka sabida ciwon maran da ta soma , sosai kafarta ta dama take mata ciwo, ban daki ta shiga domin gyara jikin ta ganin har yanxu period din be zo bane yasata yin sallah, kafarta sai faman ciwo take , asabe ce ta kwankwasa kofar daman shigo tahee ta bata sai faman yatsina fuska take, breakfast ta kawo mata yau ko hirar da suke batai ba bayan ta amsa tayi kwanciyar ta , fita asabe tayi bayan ta mata sallama tana mamakin ta, ganin ta fitane yasa tahee mikewa tare da nufar abincin, kadan tashi ta tashi aguje ta nufi ban daki, duk abunda taci saida ta amayo dashi, jikinta sosai yake mata ciwo, wanka tayi da kyar tare da saka dogon hijabi Sabida sanyin da ta keji,ko da ta fito falo bata tarar da kowa ba , ganin hakan yasa itama bata zauna ba ta nufi part din dada, tunda ta doshi hanyar zuciyar ta ke tsinkewa bata san dalilin hakan ba, ta dora kafar da niyar shiga kenan taji kukan ammi” BA’ASAN INDA SUKE BA  ,DAGA ITA HAR TAHEER DIN ANNE MESU AN RASA ABUNKURE  “ kalaman da suka shiga kunnanta kenan, bata san lokacin da ta kwalla kara da karfin gaske ba , kafarta da ke step na biyar ya gurde ta fado kasa Tim kanta ya bugu da jikin step din, sosai Jini ya barke mata akasan ta , kanta da ya buguma sosai yake zubar da jini , da gudun gaske sukayo kanta , tun lokacin da ta saki karar nan, ganin tahee Baje a kasan yasa hankulansu kara tashi kowa fatan da yake Allah yasa bataji me ake tattaunawa ba, wani saban kuka ammi ta saki, kaka ma ganin halin da tahee take yasata sakin nata kukan “shikenan ta faru ta kare”abunda dada ke fadan fada kenan , ummey da abeey sukai dauriyar dagowa, ganin yadda jikinta yasaki ne yasa dada sakin wani kukan” wai ina sadaukine ba bokan turai bane yazo ya dubamana amanar Allah”kallan abey dada tayi cikin fada fada ta soma magana me kuke jirane ku kira sadauki ya dubata duk kunbi kun tsare ta da itanuwa “ ta kara zancen nata da kallon su uncle salim da suka karaso suda iyalansu, sosai hankalin yan gidan ya tashi, “amma dada me zea hana a tafi asibiti kawai tunda nasan ba za a rasa king acan va” kwallar da ta zubo mata  ta share maza zayed dauketa mu tafi asibitin kuma sai ku biyo bayan mu “da Sauri ammi ta mike ganin harsun nufi mota, baya ummey tashiga sai dada da tahee dake tsakiyarsu ba alamun rai , yayin da gaban motan kuma dr zayed ne da kansa zai tuka motar ammi na gefan sa, da gudun gaske suka bar gidan ganin haka yasa motoci biyu na sojoji bin bayansu, suma sauran yan gidan shiga mota sukai da bin bayansu sojoji ne take musu, aunty kawai aka bari datace ta zata taso amrah sai su taho tare, ba Wanda yace mata kala har suka taho asibitin.

Koda su dada suka shigo asibitin da gudu sojojin nan suka zagayesu kowa duk Wanda yazo wucewa sai ya kallesu, kara dialing number king abey yayi akaro na ba adadi, yanxu ma kara kiran yayi not rechable Daidai lokacin da wasu manyan likitocin asibitin suka karaso da gadon daukar mara lapiya , inda take abeey ya nuna musu, daya daga cikin doctor dinne ya bude motar da niyar dakko ta, Daidai lokacin da motar king ta sharo da gudun gaske,Kai tsaye inda su abey suke zaki ya nufa, suna ganinsa suka sauke a jiyar zuciya yau da kanshi ya bude kofar ya fito tare da nufarsu,ganin su gabaki d’aya a wajan ne yasa ya maida hankali kan abeey” what happen “ ya fada a kasalance, kasa yi masa magana sukai sai bayan Botar da suke nuna masa , a hankali ya bude kofar wacce ya ganine yasa shi dan ja baya kafun cikin azama ya shige cikin kotar, ganin yadda jikinta ya baci da jinine yasashi rintse ido kafin ya dauke ka kamar yar baby a jikinsa , ko gadon da aka dakko be kalla ba ya nufa da ita ciki cikin sassafa, kowa na wajan binsa da kallo yayi amma ba bakin magana hatta ma’aikatan wajan kowa sai satar kallonsa suke, sau daya ya kalli doctor din gefansa , “doctor halima” yana gama fadar Hakan ya shige lifter tare da barin yan gidan , direct office dinsa ya nufa da ita duk jikinsa shima ya baci, cikin few minutes sai ga wata doctor mace tazo lokacin da yake mata dressing din ciwon kan nata, sau daya ya kalleta be ce mata komai ba ya dauki tahee yanxun ma cikin sassarfa ya nufi wani door da ita, itama ma doctor haliman cikin Sauri tabi bayansa bayan ta kirawo wasu nurse, duk ragowar likitoci tsayawa sukai suna tsoran shiga theatre din ganin be nemesu ba kowa ya koma gaban aikinshi, kusan hour daya da rabi ya fito daga cikin theater din, kallansa abeey yayi cikin damuwa “ yaya jikin nata “ duk zuba masa ido yan gidan sukai suna jiran amsarta sa “ sai ta farka tukunna” ya karashe zancan nasa da kallon ammi da yake jin kukanta har zuciya, muryar abeey ce ta Katse masa tunaninsa” zamu iya shiga” jin jina masa kai king Kawai yayi sabida ciwon kan da yake ji, wani baban daki aka kaisu inda aka kwantar da ita, sosai Wajan yake da girma kamar ba asibiti ba, kwance take kan gadon sanye da kayan marasa lapiya , kanta nannade da bandage sai drip din da aka sa mata, sosai fuskarta tayi fiyau da ita ga wani kyau data kara jikin ta kamar babu Jini a jiki, ko wannansu kallanta yake cikin tausaya wa hatta summy da bata santa saida ta zubar mata da hawaye, sun dade zaune a asibitin har wjan 2 na rana kafun abeey ya bada umarnin su koma gida yayi saura daga dada sai ummey saishi ,uncle Saleem da uncle musaddiq kuma suka tafi tare dasu, shima abeey office din king ya nufa cikin rashin sa’a ya tarar da office din a kulle, ganin ana kiraye Kirayen sallane Ysa abeey ya nufi masallaci koda aka idar da sallan be koma ciki ba sai da yayi la’asar. Koda ya koma cikin tashin hankali ya samesu ganin yadda tahee ta cire drip din hannunta sai kuka take , duk Wanda yayi yun kurin tabata sai ta buga masa wani abu, gabaki d’aya doctor din tsaya wa sukai suka su ammi kuka suka saka ganin halin da take ciki, zuyawa yayi da niyar kiran king sai gashi yashigo cikin wata shigar daban,bin dakin yayi da kallo ganin yadda ya baci, daya daga cikin nurse dince ta nufi tahee da niyar rigeta bayan ta ga Shigowar king , bata Ankara ba tahee ta buga mata abu ka , kara ta saki tana ja da baya , kuka tahee ta saka “karku tabani, su wanane ku, kumaini wajan dady na” sukenan kalaman da take, umarni king ya bawa doctors din su fice da ido kafun a hankali cikin takunsa ya nufi wajan gadon, cikin rufewar ido tahee ta dauki abu daniyar kwala masa sai kuma ta tsaya da kukan da take ta fara dariya kamar wata zautacciya, be ankara ba sai ji yayi ta rungumesa “daddy na “ shine kadai abunda tace tare da kudun dune king da ko motsi yakasa bayan rungumesan da tayi.

Comment and share 😌✍️
Mss Lee 💖

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK

MESAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581.

Leave a Reply

Back to top button