Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 39-40

Sponsored Links

BOOK 1

Page 39-40💖

A hankali yake bata wani irin passionate kiss me tsayawa arai, ya dau dogon lokaci a haka kafun ya zare bakinsa cikin nata yana bin kyakkyawar fuskarta da kallo,rintse idanuwansa da suka fara kadawa yayi kafun ya furta “ what’s wrong with me”,cikin zuciyarsa ,be an karaba sai saukar lips dinta yaji cikin nasa,sosai itama take kissing din bakinsa kamar yadda yayi mata,tun lokacin da ta dora bakinta a kan nasa ya kasa motsi,sosai yake mamakinta gabaki d’aya ta kwance masa notukan kansa mamaki yake ta yadda ta iya wannan abun, a hankali ta zare bakinta cikin nasa tana bude idanuwanta,kyakkyawan murmushi ne ya bayyana kan kyakkyawar fuskarta da yasa dimples dinta lotsawa, bin dimples dinta yayi da kallo kafun ya sauke shi kan dan karamin bakinta da yayi jawur,”Nima na rama “ ta furta tana sakin dariyar da ya karawa fuskarta kyau da annuri,kamar wacce tayi wani babban abu harda yi masa kwalo ita a dole ta rama,yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafun ya gyara kwanciyarsa gefanta,ya dau kusan 3 minutes be ce komai ba kafun ya bude idanuwansa, a hankali ya furta” ko me akai miki se kin rama kenan ko”da sauri ta daga masa kai tana turo dan karamin bakinta ,kallan dan karamin bakin yayi kafun ya dauke idanuwansa “shiyasa dazu kikace a wajan dada zaki zauna kenan”, ya furta mata a hankali kamar Wanda aka sa dole, yanxu ma turo masa bakin tayi kafun ta furta “dady ta mareni fa kuma ta jimun ciwo”idanuwansa ya dan waro kadan” dagaske” ya furta, yanxu ma gyada masa kai tayi ,”oh shiyasa akace ba a sona kenan”, ya karasa zan can sa yana kauda kansa gefe,girgiza masa kai tayi cikin sauri ta furta” Aah ina sanka yanxu ai”,shareta yayi ba tare da ya tanka mata ba,matso da fuskarta tayi daidai tasa tare da furta “ina sanka fa dady”, juyar da fuskarsa ya karayi, itama kara matso da tatan tayi ita a dole sai ya kalleta, fahimtar hakan yasa king kara dauke fuskarsa, cikin murya kamar wacce zata saki kuka ta furta “Allah ina sanka dady”, yanxu ma shiru yayi mata Hakanan yau yake san yi mata magana,kuka ta fashe dashi ganin ya ki kulata, mikewa tayi zaune da niyar sauka daga kan gadon gabaki d’aya ,riko hannunta yayi ba tare da yace komai ba y jawo ta jikinsa , lafewa kuwa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya kafun ta dan dago ta kallesa “ dady ina sanka kaji” ta furta har yanxu bata dena kukan ba ,amaimakon ya bata amsa sai ya furta “bana san kuka”, share hawayen ta farayi kafun ta kara lafewa a jikinsa tana faman yin shesh sheka kadan kadan, be san lokacin da ya kai hannunsa baya ba yana shafa mata a hankali, kusan tsawan lokaci ya dauka yana mata haka kafun ya fara jin saukar nunfashin ta akan kirjinsa alamar bacci ya dauketa,gyara mata kwanciyarta yayi kafun ya kashe musu hasken dakin gabaki d’aya sea wata dum light da ya bari blue colour, a hankali ya karanto musu adduar kwanciya bacci kafun shima wani baccin ya daukeshi.

*********Wutace take tashi sosai a Wajan, duk ruwan da aka watsa mata sai wutar ta kara tashi kamar ana kara kunna ta,mika masa hannunsa yake yi ,a hankali yake furta “Akhie,Akhie”, so yake ya kwace jikinsa ya shiga cikin wutar ko xai ciro wanda yake ciki Amma sosai suka rikeshi,gabaki d’aya karfinsa yasa ya hankadasu suka fadi, da mugun gudun gaske ya nufa wutar kamar be san zafinta ba, wani irin tashi wutar tayi tare da tar watsewa a wajan,gabaki d’aya wajan ya dauki hayaki, a hankali yake furta “AKHIEE” kafun nunfashinsa ya dauke gabaki d’aya.

Mutsu mutsu ya fara yi da kansa da ya gama jikewa da zufa kamar Ac bata wura cikin dakin,sosai ya matse tayi dake jikinsa ,da yayi sanadiyyar farkarwa sabida irin matsar da yayi mata, har yanxu fuskarsa a kulle take, a hankali yake furta “Akhie” cikin fusgar nunfashi kamar Wanda nunfashinsa ke neman daukewa. Kura masa ido tahee tayi kafunta furta” dady da zafi”, kara matsetan yayi a jikinsa kafun ya furta”Akhie “da dan karfi tare da ware idanuwansa dasukayi mugun kadawa sukai ja,saurin mikewa zaune yayi yana mayar da ajiyar zuciya a hankali a hankali,duk abunda ya faru ashekarun baya shine yasake dawo masa cikin kwakwalwarsa da kullum yake tunawa,dan siririn diamond chain din hannun sa da baya cirewa ya kalla me harafin M&T,sosai ya zubawa chain din ido kamar mesan tunawani abu, nunfashinsa ne ya fara yin kasa kasa kamar me shirin daukewa gabaki d’aya,a hankali kirjinsa yake sama da kasa kamar me kokarin kasa controlling din nunfashin nasa, TAHEE data tashi zauna ne ta matso kusa dashi kamar me shirin yin kuka “dady”,be kulata ba har yanxu nunfashinsa kuma be dena kokarin kwacewa ba jijiyoyin kansa sun fito rudu Rudu duk da ba’a gani sabida Duhun dakin,bata san ya akai ba sai gani kawai tayi ta rungumeshi a jikinta tare da dora kansa akan cinyoyinta, sosai ya matse cikinta kamar Wanda akacewa za a kwace masa ita, ahankali ta fara shafa masa bayansa kamar yadda taga yana yi mata,nunfashinsa ne ya fara daidaita kafun a hankali wani baccin ya daukeshi a yadda yaken, kokarin janyeshi tayi, amma ya kara riketa gagam,lumshe idanuwanta tayi tare da jingina da jin gadon itama a haka bacci ya dauketa.

🫧🫧🫧🫧🫧

Kiran sallar asuba na farko ne ya tayar dashi da kyar ya iya bude idanuwansa da sukayi masa nauyi, kallan yadda ya kwanta yayi kafun ya sauke idanuwansa a kanta ,sosai ta bashi tausayi, a hankali ya daga jikinsa daga kan nata ,yasan da kyar in wuyanta be mata ciwoba,gyara mata kwanciyar yayi kafun ya mike ya shiga wani door , be wani jimaba ya futo sanye da farar jallabiya tare da nadin larabawa, sosai kamanninsa ya kara fito wa na sak larabawan sai faman tashin kamshi yake kamar ba asubahi ba, a hankali yake yin komai ,mafarkin da yayi na kara dawo masa,ganin ana kokarin tada sallah ne yasashi fita a dakin gabaki d’aya. Be dade da fita ba tahee ta farka daga baccin ta,sosai wuyanta yake mata ciwo da cinyoyinta,dubawa tayi taga king bayanan turbune fuska tayi kamar yana kallanta kafun ta mike taje tayo alwala, tana cikin yin sallar yashigo dakin,kan gadon ya koma kamar Wanda akasa dole sai faman ya tsina fuska yake sabida yadda kansa yake tsananin sara masa,kafin ta tashi daga kan sallayar har wani baccin ya fara fisgarsa, a hankali ta fara taku ita a dole karta tasheshi taje ta kwanta itama a hankali,duk abunda take yana kallanta motsawane kawai baze iya va,be dade ba wani saban baccin ya daukesu gabaki d’aya.

9:45am tahee ta soma mitsi mitsi da idanuwanta kafun ta budesu gabaki d’aya,gefen da yake ta juya wayar taga babu kowa, da sauri ta mike tare da nufar hanyar fita, har ta saka hannunta da niyar bud’e kofar ta tuna gargadinsa “kada ki kuskura ki kara fitowa nan baki yi wanka ba,kaxama “,shagwabe bakinta tayi kafun taje tayi wankan shaf shaf ko munti 10 batayi ba kafun ta shirya cikin wasu riga da wando na pakistan masu taushi da santsi,gashin kanta da ya zubo mata kar gadan bayanta tayi kiciniyar daurawa ganin ta kasane yasata daukar ribbon din tare da nufar falo, ba kowa a falo sai kamshin daddadan kamshi da yake tashi ne cike da sanyayyar kamshin ac, kofar fita daga part din ta nufa hannunta dauke da ribbon dinta ga gashinta da ya dauko mata har wajan kwankwasanta sai faman sheki yake dauka,Daidai ta sa hannu zata bude kofar taji an turo kofar da karfi.

Sanye take cikin wasu kananan kaya da basu dame jikinta sosai ba ,fuskarta Tasha uban makeup da bakin glass a idanta sai faman taunar cingum take, a yatsine take bin tahee da kallo irin kallon up and down dinnan, ta be bakinta tayi tare da kokarin shigowa ciki,wani irin kallo tahee ta jefa mata kafun ta furta”wacece ke”,daga hannu budurwar tayi tare da tsinkawa tahee mari a fuska”tanbayata kike wacece ni dan uwarki”. Tunda ta cinka mata marin tahee take dafe da kuncinta,kalmar uwarkice ta tsaya mata arai,itama batayi wata wata ba ta tsinkawa budurwar mari hagu da dama kafun ta dago idanuwanta a zuciye tana binta da kallo, cike da tsantsan mamaki budurwar take bin tahee da kallo itama hannunta dafe da kumatunta, dan ba kadan taji zafin marin ba”ni kika mara “ta furta kamar me shirin yin kuka ,banza tahee tayi da ita kafun ta juya tare da komawa ciki, tana cikin tafiyar taji anwani fusgota tare da hankadata, rufe idanuwanta tayi sosai ganin tana kokarin faduwa, a maimakon ta fadin sai taji an tarota,tare da saukan tagwayen maruka dafe kumatunta tayi ganin ba ita aka mara ba ,kafun ta bude idanuwan a tsorace,Wanda ta ganine yasata sakin ajiyar zuciya kafun ta kara rikeshi gagam.

Suman tsaye budurwar nan tayi jin saukar marin da ba a taba mata shiba a duba,hawayene sosai suka cika mata idanuwa kafun ta dago da idanuwanta ta kallesa,sosai ya kara yi mata kyau fiye da kullum da take hasashensa acikin zuciyarta, kalllansa take kamar wacce tasami abun kallo kafun ta soma magana“yanxu king akan wannan shegiyar da take muku wasan kwaikwayo da rayuwa zaka sa hannu ka maran”, kamar wacce tayi magana da dutse haka ya mayar da ita a wajan,ribbon din hannun tahee ya karba itama bai ce mata komai ba ya tufke mata gashin kafin ya ja hannunta suka bar wajan. Sakin baki tayi tana kallan abunda yake wa yarinyar da taji lokaci d’aya ta tsana ,abunda ko a mafarki in aka fada mata bazata taba yadda dashi ba ,wai yau shine yake taba mace ba ita ,ganin sun juya ne yasata bin bayansu tda kallo ganin irin wulakancin da king yayi mata a gaban kaskantacciyar da takewa kallan me aiki”kamar ni, Basma isma’il yar governor guda aka mara agaban wannan kaskantacciyar”,da karfi ta furta”impossible gaskiya bazai taba yiwuwa ba, dole ma mom kisan yadda zakiyi ayi auran mu da king cikin kankanin lokaci kafun nan kuma sai na gyarawa shedaniyar can zama” tana kammala zancanta tabar wajan cike da bacin rai.

Suna shiga daki ya saki hannunta kafun ya kalleta rai abace “ ba kyajin magana ko,kunnan kashine dake, baki isa a hanaki abuba” baki ta bude zatayi masa magana ya daga mata tsawar data firgitata har da ja baya kadan” shut up” ya kara daka mata tsawa “ daga yau in ina magana na kara gani kinsa mun baki, I will beat the hell in side you, stubborn girl” yana kammala zan cansa ya nufi kofa har zai futa ya dawo kallo d’aya yayi mata kafun ya furta “ idan na kuskura na kara ganin kafarki a waje zakiga abunda zai faru” ya karasa a zuciye tare da barin dakin. Sai a lokacin ta fashe da kuka ,gawani tsoran shi daya cika mata zuciya lokaci d’aya,sosai take yin kukan ga wuyanta dake mata ciwo ,a tsakar dakin ta kwanta har yanxu tana sakin kukan kamar wacce akace mata dadyn ta ne ya mutu, tafi tsawan mintuna 30 a kwance a wajan tun tanayin kukan da karfi har ya dena fitowa sai hawayen dake fito mata kadan kadan. Turo kofar dakin yayi hannunsa dauke da plate madaidaici, ajje plate din yayi a can center table din falon batare da ya kalletaba ya kara fita daga dakin, a hankali ta dago da kanta kan plate din da ya ajiye ,kafun ta kara sakin wani saban kukan muryarta har dushashewa take,gajiya da kwanciyar kasan tayi ta koma kan gado duk da tsananin yunwar da take ji, sanyi ta fara ji sosai shiyasa ta lulluba cikin bargon ko hangota ba a yi.

*****Direct yana fita daga dakin part din dada ya nufa ,hayaniyar da ya fara ji tana tashine yasa shi fasa shiga part din tare da nufar part din abeey. A shingide ya samesa kamar kullum sanye da fararan kaya yana karatun jarida , a hankali king ya karaso cikin falon kafun ya samu waje ya zauna, ya dau kusan mintuna uku be yi magana ba, shima abeey beyi maganar ba sai binsa da kallo da yake yi,sosai yake jin tausayin sa, ba abune me sauki ba zama da wacce tayi loosing memory ba har bata yadda da kowa sai kai,muryar king ce ta dawo dashi cikin tunanin da ya fada” abeey ina kwana” wani yalwataccen murmushi abeey ya saki,tun lokacin da akai Auran sai yanxu king ya shigo falon ,ya sani sarai fushi yake dashi, cikin farin ciki ya furta”ka tashi lapiya son”jinjina masa kai king yayi, kafun ya mike da niyar tashi,kalaman abeey ne suka ratsa kun nuwansa” am sorry son” tada sauri ya girgiza masa kai “ stop apologizing please abeey,ni bakaimun komai ba”.girgiza masa kai abeey yayi “ah ah son, nasan haryanxu kana fushi akan Auran da mukayi mata”,be karasa zan can nasa ba king ya girgiza kansa “abeey Ka dena wannan tunanin ,bazan taba fushi akan farin cikin kaba “kalaman king sosai yayi wa abeey dadi,besan lokacin da ya saki murmushi ba tare da furta”Allah yayi maka albarka son”,lumshe ido king yayi kafun ya furta Ameen a hankali,ya dan jima a Wajan abeey suna tattaunawa kafun yayi wa abeey sallama,yana fito wa daga part din suka ci karo da sha’aban, dan waro idanuwansa yayi kadan kafun ya tabe bakinsa “finally the Parrot is here “ ya furta cikin zuciyarsa.kyakkyawan saurayine chocolate colour fuskarsa cike take da murmushi, Wanda ya gani ne yasashi kara sakin wani murmushin kafun ya furta “my gee”dan hararansa king yayi kafun suyi hugging din juna, sosai saurayin yake sakin murmushi bayan sun rabu,”nayi missing dinka gee kamar ba gobe “ta’be baki king yayi kafun ya furta “ina Mahma take” sakin baki saurayin yayi yana bin king da kallo” yanxu gee sabida baka da mutumci nagama ce maka nayi kewarka shine kake tanbayata mahma,toh baza’a fada ba”,dafe kai king yayi kafun ya furta “oh my god sha’aban kafara samun ciwon kai, wai mema ya kawo ka”dariyar keta Wanda aka kira da sha’aban din ya saki kafun ya furta “nazo ganin amarsune, tunda kayi aure babu goran gayyata “ gajeran tsaki king yaja kafun ya furta “I don’t have your time “yanxu ma dariya sha’aban yasaki”dole ka fadi haka mana king tunda ka angwance kalli wani kyallin amarci da kake”Naushi king ya kai masa a kirji yana kaucewa , a hankali ya furta “parrot”,daga hannu sama sha’aban yayi kafun ya furta accepted,girgiza kai king kawai yayi tare da kama hanyar part dinsa ganin ankusa yin sallar azahar,shima sha’aban part din abeey ya shiga yana furtawa king sai yazo cin abincin amarya.

➰➰➰➰➰
Yana shiga part din nasa yaga bata falo sam ya manta da zancan yace mata kada ta fito a dakin, a gogon hannunsa ya duba 1:10pm, dakin da suka kwana ya nufa kai tsaye sai alokacin ya tuno da abunda ya faru,dafe goshin sa yayi kafun ya furta “ya salam “ yana shiga cikin dakin,yana shiga dakin da plate din da ya ajje mata na abinci ya fara cin karo ,yana nan yanda ya ajjesa da alamu ma ko tabashi ba aiba, cikin dakin ya karaso yana bin dakin da kallo dan ganin ta inda zata bullo, a saman gadon dakin idanuwansa ya sauka, sosai ta takure waje daya kamar me jin sanyi, cikin sauri ya karasa kan gadon kafun ya yaye bedsheet din,da sauri ta tashi zaune a firgice da alamu bancin nata be yi wani nisaba, tana ganinsa ta kara ja baya da sauri kamar wacce taga wani abun tsoratarwar,”me ya Hana ki cin abinci “ ya furta yana binta da idanu, a hankali ta furta “na koshi dady”kamar wacce aka sa dole,karasowa kan gadon yayi kafun ya dora hannunsa kan forehead din ta,zafin da ya jine yasashi saurin kallanta,ganin tana kokarin lumshe ido,”open your eyes “da Sauri kuwa ta bude idanuwan nata har yanxu tsoran nasa be fita a ranta ba, fita yayi daga dakin ba jimawa ya dawo hannunsa dauke da wani mug me shegen kyau, tea ne a ciki mea dumi sai faman tashin kamshi yake,mika mata yayi ba tare da ya kalletanba “shanyesa duka “baki ta bude zatai magana ya bita da rikitattun idanuwansa,da sauri ta kar ba ta farasha saura kadan ta kware,saida ta kammala sha ya kyaleta ,ganin yadda take sun kuyar da kaine yasa ta bashi tausayi duk da yasan ba lefin ta bane , a gefan gadan ya zauna kafun ya janyota jikinsa yana rungumeta,kuka kawai tahee ta fashe masa dashi ,tapping din bayanta yayi a hankali kafun ya dagota “kayi hakuri dady” ta furta a marairaice ,dogon hancinta yaja yana dan dungure mata kai, dariya ta fashe dashi kafin ta kara rungumeshin.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

YOLA

bakaramun ukubar rayuwa su taheer suke fuskanta ba, gashi sau daya ake basu abinci a rana sai biredin da ake jefo musu kamar wasu kaji, mutanan cikin dakin har yan rige rigen dauka suke sabida bakar azabar da suke fuskanta. Suna kwance a inda aka killacesu a ka bude kofar dakin,kowannansu rarra kubewa yayi gudun kar a gansu, mutane biyar mutumin ranar nan ya zaro, ciki har da taheer , bugun su mutuminnan ya fara kamar Wanda aka kaiko, kafun ya samu wani d’aki me shegen duhu ya kullesu a ciki, ko wannansu ba me motsin arziki aciki shash shekar d’aya daga cikin suce ta cika musu kunne a hankali taheer ya bude idanuwansa da sukai masa nauyi kafun ya soma magana “me yasa kake kuka”kara fashewa da kukan saurayin yayi kafun ya furta “gida nake so na koma” daya daga cikin sune ya amsa masa a wahale shima “muma dukan mu muna so mu koma gida amma ba yanda zamuyi, ni so nake na samo hanyar da zan futa daga wajan nan,mutanan nan basu da imani ko kadan,bamuyi musu komai ba suke cin zalin mu,kamar yadda sukai wa sauran muma ina tunanin siyar damu zasuyi”be karasa zan can nasa ba yaji an banko kofar, saurin gimtse bakinsa yayi, wani gabjejene ya shigo dakin ,yanxu ma jibgarsu yayi cikin mugunta da rashin imani kafun ya jefo musu guess’s guda uku da pure water guda biyu ,kamar Wanda suka shekara basu ci abinci ba haka suka samu guntuwar gurasar nan sunaci ,kalaman saurayin can ne yake ta faman kai kawo a zuciyar taheer,sosai kwadayin samun mafitar ta yanda zasu gudu ya shiga ransa shima ,babu Wanda ya kara magana a cikin su sabida yadda ko wannansu yake jan nunfashin azaba.

➰➰➰➰➰➰➰➰

BUNKURE

Acikin yan kwanakin nan sosai kaka ta bawa ta rame,duk lokacin da ta kwanta bacci mafarkin su oumma kawai take, tun abun baya tamun ta har ya soma damun ta,sosai ta shiga dana sanin abunda ta dinga yi musu alokacin baya , kusan kullum kenan yanxu sai ta leka dakinsu ko zata ga sun dawo, mutanan gidan ma ko wannansu ya fara shiga taitayinsa sabida wahalar baccin da suke samu cikin tare ,da yawa daga cikin su suka nutsu .

A ban garan su Dije kuwa liyafa ce ta karu, yanxu kwata kwata bintalo bata kwana a gidan sai dai tazo da safe tayi abunda zatayi ta bar gidan , wani lokacin ma kayan ta kawai zata iya ta har gidan, har yanxu kuma babu me daga mata yatsa sabida duk ta bawa boka sunayensu . Dije kuwa ko a jikinta halin da bintalo ta jefa kanta ,tunda tana kawo mata kudi,burin ta daman ta samu kudi,yanxu har wata kawa tayi me suna hajjo aunty, hajjo aunty makirar matace ,burinta kawai ace tafi wani, sun hadu da dije ne a wani biki ,shikenan suka kulla alaka mai karfi kamar wacce suka yi shekaru da dama tare , yanxu ko wana sirri na Dije ,hajjo aunty ta san dashi, itace kuma me bata shawara,yanxu itama hajjo ta fara sawa Dije kwadayin yawo kamar yadda take,a tunaninta ai shine kadai hanyar da samun kudi kafun su tura bintalo can burniii.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

LAGOS

8:30pm ya shigo cikin gidan , be nufi part din kowa ba sai na dada, babu kowa a cikin falon wani daki dake facing din na dada ya shiga,kamar yadda yayi hasashe kuwa tana kwance kan gado tana baccinta cikin kwanciyar hankali, kiss din da tayi masa a kumatu ne ya fado masa rai kafun ya kawar da zancen yana karasa shigowa cikin dakin , be jira komai ba dauketa kamar wanda ya dauki baby ya fito da ita, a maimakon ya fita daga part din dada wani corridor dake jiki ya nufa daga jikinsa wani dan adone a wajan ,adan wajan ya dan karkata kadan,take a Wajan jikin bangon ya tsaye wata kofa ta bayyana,shiga yayi ciki kafun ya kulle ta ciki, daga wajan kuwa kamar babu wata tsaga da ya taba yi a wajan, yar tafiya yayi kadan kafun ya bude daya daga cikin kofofi ukun da ke wajen, yanxun ma yar guntuwar tafiya yayi,kafun ya bude wata kofa,yana bude kofar kai tsaye bedroom din da suka kwana ne ya bayyana sai faman tashin kamshi dakin yake kamar kullum,kwantar da ita yayi kan bed din kafun ya warware mata veil din jikinta yana gyara mata kwanciyar . Sai da yayi Wanka kafun ya fito daga part din nasa , direct part din ammi ya nufa, koda ya isa part din ammi na kitchen sai faman aikace aikace suke,shigowar sa falon ne yasa ammey fito wa da yalwataccen murmushinta na kullum da ta saba, tana ganinshi ta bude masa hannayenta a hankali ya karasa wajan ta kafun yayi hugging dinta, cikin sanyayyar murya kamar bashi ba ya furta”nayi kewarki ammey “itama ammeyn cikin sanyin jiki ta furta “Nima nayi kewar ka sosai son,ya kake ya daughter na”gingina mata kai yayi kafun ya furta “all will be alright ammey,trust me zata ganeki soon” murmushi ammi ta saki tana ja masa hancinsa “ai na yadda da son dina ,shiyasa bani da wata damuwa”lumshe mata ido yayi yana budewa, kunun aya ta kawo masa tare da abinci, kunun ayan kawai ya sha sosai batare da yaci abinci ba,sun dau tsawan lokaci suna tare kafun yayi mata sai da safe.
Koda ya fita daga part din ammey part din ummey ya nufa,ko da ya shiga part din itama tana kokarin fitowa ne , ganin shine yasa ta koma,bayan gaisuwa babu wani abu da ya kara shiga tsakaninsu,Mikewa yayi da niyar tafiya yaji saukar muryan ummeyn sa”ya jikin daughter “ajiyar zuciya ya sauke kafun ya furta “Alhmdllh “,ummey bata kara cewa komai ba tsawan 2 minutes kafun ta furta ,”gobe UMAIMA zatazo” harbawa zuciyar sa taji jin umaima zata zo amma a fili babu alamun hakan a fuskarsa sai “Allah ya kawo ta lapiya “ da ya furta yana barin part din….

 

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK

ME BUKATAR GIDAN AUNTY COMPLETE YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.

Leave a Reply

Back to top button