Hausa NovelsHausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 37

Sponsored Links

smy Mom Aydah??: 37…

Wani irin kissing bakin nata yake zuciyarsa na wani irin harbawa,
Ya riketa sosai cikin jikinsa tamkar wanda za’ayi wa kwacenta sun fi minti goma a haka,dakyar ta samu ya cikata tana jin yarda bakin nata yake yimata wani zafi sabida irin tsosar da yayiwa bakin,lokaci daya hawaye suka cika idonta,tana jin wannan haushin tabatan da yakeyi ,taja da baya sosai haka sai da ta tabbata akwai spaces a tsakaninsu,
Ta share hawayen idanunta,tayi crossing hands dinta a kirji da serious Murya take fadin”xamuyi magana da kai Aliyu ,ina son kowace Amsa ka amsa min na baka zabi ka fadamin gaskiyya ko akasin hakan,wannan zaman haram din da muke banga Amfaninsa ba,
Ina maganar sakin da kayi min a baya ko ka manta dashi ,ko ka maida Auren mu batareda mun san da hakan ba dagani har Ammah,wannan sabon salon da ka dauko sam bana jin dadinsa bana gane komai cikin sa,nasan Auren mu na contract ne duka Bama son Junan mu akayi Auren ,ka datse Auren ne sabida dama can ba sona kake ba ko menene??”ko kuma ka hakura xaka xauna Dani a matsayin matar ka ta aure har abada koda baka sona har yanxu.”ko kuma ka fara sona nice ban san hakan ba kayi min bayani yarda xuciyata xata dauka dan Allah.”ta fada tana kallon cikin idanunsa,
Ya girgiza kai yana fadin”idan ina sonki wannan ba damuwar
Ki bane,haka idan na mayar da Aurenmu wannan bai shafeki ba,Abu daya na sani baki isa ki Auri wani ina raye ba.”wani murmushi mai ciwo tayi tana mamakin karfin zuciya irin na Aliyu da bakin sa baxai furta yana kaunarta ba koda sau daya ne tana son taji wannan kalmar,Hawaye na xubar mata take fa?in.”baxan iya zaman Aure da namijin da bbu soyayyata a xuciyarsa
ba ko ka?an ,na xabi na Barka Aliyu da naci gaba da zama dakai a matsayin miji,ya fisgota ya hade rai yana fa?in.”soyayyar da kike yimin fa??ya xakiyi da ita??wani sly smile ta saki hawaye masu zafi na saukar mata tana jin yarda xuciyarta nayi mata wani irin ciwo.ta kallesa ido cikin ido tana fa?in.”Ban taba sonka ba Aliyu waxeer kuma baxan fara yanxun ba,ka fita daga rayuwata dan Allah ka barni da xabin da Ammah tayi min .ya matseta sosai ransa yayi balain ?aci akan maganganun da ta yarfa masa,cikin ihu yake fa?in.”nima ban taba sonki ba,ina kare mutuncin kine kurum sabida Farhaan ,kin san matsayin Farhaan a wajena,so baxanyi sake da abunda ya barmin a matsayin amana ba,so kike nayi ta binki kamar wani sakarai haka kike so right.wani miskilin murmushi ya sakin yana fa?in.”baayi maccen da xanbi ba,idan haka kikeso na yarda na amince,
Daga yau baxan kara binki ba ,baxan kara shiga lamurranki ba,
Ta fisge kanta tana masa wani irin kallo A hankali ta juya da sauri tana kokarin fashewa da kuka a gabansa da gudu tabar cikin balcony din,tana saka hannayenta duka biyu tana rufe bakinta ,wani kuka mai ciwo taji yana taho mata…tsaye yayi yana kallonta yana sakin murmushin takaici,da gaske ta xabi ta Barsa da gaske noory bata sonsa???”kai kawai ke haukanka akanta,kaima ya kamata kabarta ko xaka samu sauqin abunda kake ji acikin xuciyarka,ka kyaleta ka fita daga Rayuwarta tayi Rayuwarta yarda takeso tamkar yarda ta fada maka.”wata zuciyar ta basa wannnan shawarar ya kamata ya dagawa nooryn kafa na kwana biyu yaga iya gudun ruwanta,sai ta maula take da rayuwarsa,yana Binta tana harbasa tamkar wani sakarai,ko Areefa mansoor da ya fada yana so da dukkan zuciya da ruhi bata tsayawa agabansa,ta gaya masa magana.shima a fusace ya juya Yabar cikin balcony din……
Hade Kai tayi da gwiwa ta shiga rera kuka mai sosa rai, addu’a take Allah ya rage mata son aliyu waxeer Koda Bai ciresa gaba daya ba acikin xuciyarta
,wata xuciya ta fada mata yanxu tunda kin san matsayinki na akan bai taba sonki ba,sai ki bude ido yanxu ki fuskanci Rayuwa ki nuna masa kema macce ce wanda dole za’ayi tattalinta a girmama soyayyarta,
Ta share hawayen idonta tana sakin wani irin murmushi mai ciwo,xata yi balain koyawa Aliyu waxeer hankali xata nuna masa itama macce ce tamkar kowa xata nuna masa darajarta a matsayinta na yah macce,damuwar Aliyu da ta sakawa ranta a wannan daren ta kwantar daita da wani irin xaxxabi wanda da kyar takai safe sai kuma wani irin amai,
Cikinta taji yana mata wani irin zafi,dakyar ta daga waya ta kira Ammah gamida fashe mata da wani irin kuka,Hankali tashe Ammah ta sameta a daki kusan karfe shidda da rabi na safe ,Ammah ta rikata a rikice tana fa?in.”kalmar innalillahi wainnah ilaihir raji’un,wani aman taji yanaxo mata ta saki Ammah ta nufi toilet da gudu ta shiga xuba amai,
Gaban Ammah na faduwa take bin kofar toilet din da kallo ta shiga ukku Allah yasa Noory ba ciki tayi ba,
Da sauri wata zuciyar ke fada mata ,babu ciki jikinta,Ammah na zaune kusan minti biyar sai ga nooryn ta fito,da sauri Ammah ta rikata ta zaunar daita gefen bed,tana yimata sannu da ina da ina ke maki ciwo??”cikina keyi min xafi da kuma xaxxabi,
Dakyar Ammah tace owk bari na kira Abdul-Hakeem yaxo kuje Asibiti,da haka Ammah tabar room din xuciyarta na wani irin tsalle tafi kowa shiga tashin hankali,kira daya ta yiwa Abdul-Hakeem waxeer ya daga yana gaisheta da ladabi,,,jin Muryar Ammah wani iri yake fa?in.are You owk Ammah??”dama Nooriyah ce babu lfy ko xaka fito yanxu muje Asibiti,cikin tashin hankali yake fadawa Ammah gayanan zuwa ,da haka ya katse kiran dama Jallabiyya ce ajikinsa mai guntun hannun tunda ya dawo Asubah bai cire ba,car key kawai ya dauka ya nufi gidan Ammah.kallonta kawai yake tana jikin Ammah kallo daya xakayi mata kasan tana jin jiki,bbu bata lokaci ya wuce dasu waxeer hospital ,da kansa ya dubata cikin office din Dr.ishaam tambayoyi ya shiga yimata tana bada amsa,ita dai Ammah ta kasa natsuwa,aka dibi jinin nooryn aka bata Gwajin fitsari.kusan minti Ashirin result ya fito,
Ya kalli Ammah xuciyarta na harbawa take kallon sa ya ware mata ido yana murmushi yana fa?in.”bafa Abunda kike tunani bane,ulcer ce tayi mata mugun kamu,wani irin ajiyar xuciya Ammah ta sauke,ya fadawa Ammah taci wani abu tukuna xai Bata injection ,ya saka mata drip sabida Aman da tayi duk ya tafi da karfin jikinta,
Waya Ammah Tayiwa Khaleel waxeer akan matarsa ta hado mata ruwan xafi yanxu ya kawo mata Asibitin waxeer.cikin minti talatin yazo da ruwan zafin dashi da laylah,itama gulma ta kawota jin ance Nooriyah ce ba lafiya har da egg ta soya Mata,da kanta ta shiga hada mata tea dakyar noory ta Sha Rabin cup Allura Hakeem ya shiga ha?awa,ta tsani allura dauriya kawai take a gabansa,ya ware mata ido yana fa?in.relax Mrs .Hakeem waxeer ,
Bbu xafi duk dauriyarta sai da ta saki karar azaba hawaye na xubar mata,ba’a dde da saka mata drip ba ta samu barci,kusan 12 na rana ya shigo gidan Ammah,fuskar nan tasa tamkar hadari,
Kallo yabi parlorn dashi kai tsaye stairs ya wuce ya nufi dakin Ammah ,knocking yayi a kofar dakin yaji shiru
Da haka ya tura kofar
Ya shiga sai dai shiru
Yaji ,kiran Ammah ya shigayi ,juyawa yayi yabar dakin ko kallon
Dakin noory bai yi ba,
Ya sauka zuwa dakin
Areefa mansoor tana
Ganin sa ta wani irin
Shagwabe fuska tana
Fa?in.”Gara da Allah ya jehoka gidan Aunty
Siddiqa xaka saukeni
Dan Allah,Ina Ammah???”tambayar da Aliyu yayi mata kenan,ta tabe Baki take fa?in”nima ga Nana nakeji sunje Asibiti waccan bakar Yarinyyar ce babu lfy,
Gabansa yaji yana bugawa dauriya kawai
Yake,ya juya xai bar room din da sauri ta riko hannunsa tana yimasa wani irin shegen kallo,muje ka saukeni gidan Aunty Siddiqa ya daga mata kai yayi gaba…….ganin irin mugun gudun da Aliyu waxeer yake da mota Areefa ta dafe cikin ta tana fa?in kashemu xakayi Aliyu??”ta fada muryarta na wani irin rawa ko kallonta baiyi ba,gudun da yake yi kan hanya yasa aka shiga xaginsa, bai isa ko’ina ba sai kofar gidan Aunty Siddiqa
Areefa na sauke numfashi ta kallesa a fusace take fa?in.”Are You mad??”lokaci daya ya shako Wuyanta ya xare Mata ido sosai kallonsa take da mugun shock
Abunda take gani cikin idanunsa a wannan lokacin baxai
Fadu ba,saboda ke ta gujeni saboda ke ta yanke duk wani relationship a tsakanin mu ,sabida ke xata ruguza xumuncin mu nida Hakeem waxeer,xaki fa?a min cikin ubanwa ne jikin ki ko sai na kasheki na kashe banxa,hawaye na xubar mata take girgixa masa kai cikin rawar murya take fa?in….”Kasheni xakayi Aliyu Kasheni xakayi nida yaron dake cikin cikina.”lokaci daya ya saketa ya bude Lock ya wani daka mata tsawa yana fadin.”fita!!!”da sauri ta fita cike da wani irin tsoransa, ya wani fisgi motar da kadan ya tafi da kafarta,a rikice ta shiga gidan Aunty Siddiqa bbu Abunda take saukewa sai wani irin numfashi ,kai tsaye bottle water ta dauko cikin fridge masu sanyi gaske,ta
Kafa sai da taji bbu komai ta sauke ,aunty Siddiqa da shigowarta kenan cikin kitchen din ta kalleta da mamaki tana fa?in.”Yaushe kika
shigo kin bani tsoro
Wlhi.”dabas ta xauna
Akan tales din kitchen
Ta fashe da wani irin
Kuka,cikin ihu take fadin”kin ga sha?ar da yayi min cikin mota kinga yarda yake yimin yana xare ido,
Yau da kadan Aliyu ya kasheni,Ni wallahi na gaji na gaji,baxan cigaba da hasarar kudina a banxa ba,ko uwarsa fa baki ga yarda ta maidani a gidan ba,bata shiga lamurrana,tamkar ba cikin Aliyu ke jikina ba.
Ta shiga nunawa aunty Siddiqa shakar da yayi mata a wuya
Har ya bayyana sabida kasancewar ta farar macce ita dai Aunty Siddiqa lokaci daya jikinta yayi sanyi,ta dagota suka koma parlor da mamaki take fa?in.”toke mekika yi masa ya hasala sa haka??”kin san asiri ba ko yaushe ake kwana aciki ba,cikin ihun tsawa Areefa ke fa?in.”kin san da haka kika kaini wurinsa ya cimin kudi a banxa,
Meyasa baki hanani xuba bora’ubata Ni kadai ba,shi yafi kowa sani na ,ko da asiri ko bbu asiri bai isa ya fiddani cikin rayuwarsa lokaci daya ba,Siddiqa ta kwantar da murya tana fa?in”baxa ayi haka ba pls ki kwantar da hankalin ki cikin ihu ta katse Siddiqa mansoor tana fa?in”in kwantar da hankalina fa kikace tayi maganar da ihun tsawa,Areefa ki natsu dan Allah Siddiqa mansoor tayi
Maganar tana kwantar da kai,shiru Areefa tayi hawaye na Rolling Akan face dinta,kina da kudi yanxu,wani kallo take yiwa Siddiqa mansoor nifa kudina baxasu kara tafia wajen wannan shegen malamin ba.
Karki ce haka kara mu koma mu fada masa aekin da yayi mana yana Rawa idan da taimakon da ya kamata yayi mana ba sai yayi mana ba,idan kuma baxaki koma ba kiyi ta zama a karo na biyu shegen duka xaiyi maki ya ha?a maki jini da majina,Areefa ta share hawayen idonta tas,tace akwai ki shirya yanxu muje dan wlhi hankali na baxai kwanta ba sai na koyawa Aliyu mugun hankali,sunyi sa’a suna isa yana shirin fita sai dai ya hakura ya gansu,Siddiqa ta shiga yiwa malam bayani,ya girgixa kai yana fa?in.”uwarsa a tsaye take tana yawan yin axkar shima da kika ga ya maki hakan
Xuciya ne dashi kuma uwarsa na tsaye akansa sai a hankali kin bata ransa da yawa yanxu xan baki wata laya,
Yau kiyi kokari ki dafa masa abinci sai ki tsoma layar sau ukku cikin abinci,in har yaci abincin nan sai yarda kika yi dashi,wannan karon baxan karbi kudin ki ba kije ki gwada wannan ban taba aeki baiyi kyau ba ,sai naki godia Siddiqa tayi masa a mota ta kwantar dakai tana fa?in “kiyi kokari kiyi masa abinci yau ki tabbata yaci abincin,
Har waxeer Mention Ta kaita kafin ta juya kan motar zuwa nata gidan,Ammah kadai ta tarar a parlor kallo daya tayi mata ta nufi dakinta,ko kallo bata ishi Ammah ba bayan
Magrib noory ta fito daga room dinta xuwa kasa Alhmdullh tun da aka saka mata drip taji sauki sai dai bata da karfin jiki Sosae,Ammah ta kalleta tana fadin”mekike so???meyasa baki kira ba a kawo maki ta xauna cikin soofas tana gaisheda Ammah take fadin.”bbu komai Ammah na gaji da kwanciya ne,sai da zasu sallar ishaai duka suka nufi sama,basu sauko ba sai kusan takwas da rabi,saboda zuwan Hakeem.da murmushi ya kalli noory ya mika mata manyyan ledojin hannunsa ta karba da ladabi tana fa?in.”nagode ya kalli Ammah yana fa?in.”Ammah yunwa nakeji mexan samu yau ,ummah tayi cimar da bana ci,Ammah tayi murmushi tana fa?in.”yau sinasir mukayi da stew na ganda da kunun aya kowa ya gaji da cin shinkafa,yayiwa Ammah salute murmushi Ammah ta saki tana Jan cheek’s dinsa gaba daya suka nufi dinning Hakeem waxeer ya jawa noory kujera,sai a idon Aliyu waxeer wanda shigowarsa kenan,dauke kansa yayi lokaci daya zuciyarsa na bugawa.
Ya kalli Amma suka gaisa ,ya mikawa Hakeem hannu sukayi musabaha,Hakeem ya lankwasa murya yana fa?in.”yau ina ka shiga ??bamu hadu ba,Aliyu ya shafa kansa yana wani daure face yake fa?in.”ina nan dama Areefa tana a kitchen tana soya Masa indomie tana jin ya shigo ta maxa ta xube indomi acikin plate ta saka masa fork ta nufi dinning area din ta wani daure fuska,kowa sai Binta yake da ido har ta karaso cikin parlorn hankalinsa na kan noory wacce tayi tamkar bata san da xamansa a wurin ba,ko kallonsa batayi ba.sai hirar ta take da
Hakeem waxeer da kuma Ammah,baby ga indomie na dafa maka.”ta fada tana dora plate din a gabansa,wani mugun kallo ya juya yana yimata kafin ya dauki plate din indomie ya juye Mata akae,wani irin tsalle ta saki gamida sakin ihu a fusace ya nufi hanyar barin parlorn da kallo Ammah ta bisa kafin ta maida kallonta kan
Areefa…..

_wallahi tallahi duk wacce ta karanta koda word daya na book din Nan batareda ta biyani hakkina ba baxan yafe mata ba,xata biya Ni a inda bata dashi…_

Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Back to top button