Hausa NovelsMatan Ko Mazan Book 1

Matan Ko Mazan Book 1 Page 8

Sponsored Links

EPISODE 8️⃣
Adan birkice direba ya gangara zuwa gefen hanya yayi parking yin yanda Nura yabuga ihu, Nura yana murmushi sosai kaman wanda yaci lottery yakalli su Musa da duk suke kallonshi asankare irin ikon Allah din nan yace “kufita mana” dasauri Musa yace “ohhh Allah kana gwadamin halin Nura yau kaine haka kake rawan jiki kaman wani sabon shiga? Shekaran ka nawa yanzu kana buga odafere”? Kwashewa da dariya Engineer yayi yace “kai wlh dan iska ne Musa, mekuma Odafere” yakalli Nura yace “dan Allah kayakuri mutafi Nura, mukoma Abuja this one week Musa ya loda maka maganin basir kaga system dinka yayi refreshing afitar da toxins din ciki, sabon ruwa yazo yataru a buhu” dasauri Musa yace “itama bakasan da Gwaggon nata tace abarta abinda za’a mata ba kenan duk dadin kane fa, gyaramaka ita za’ayi fa, kuma ma ai da kunya kawani koma saikace wani saurayi, kawa Allah ka rungumi letter nan yarage maka zafi mutafi kai direba tada mota next week fa karenka zakaci ba babbaka” tada motan direba yayi badan yasoba yahakura cus yasan gaskiya suke fadi, koda suka shiga Abuja gidan engineer yaje yaci abinci yayi knack sukasha hira wuraren 11 yabaro gidan yakama hanya suwa gudanshi yakira Ummi amman wayanta akashe maybe ba chaji baiso yakira wayan Meena kuma around 11:30 yashigo gidan, yana bude kofan falon yasan Ummi bata gidan yau kaman ba falon da Ummi ta gyara dazu da safe ba.

Dakin gabaki daya a hargitse, school uniform din su Aman na nan falon da jakunkunan su da safa, dinning hargitse da plates ga ragowan abinci indomie yagani da egg is as if yaran basuci ba gadai cups na tea da ragowan slice bread da alamun abinda sukaci kenan, kitchen yaleka daganan dinning just indomie da Hadiza ta dafa tajuya kitchen din up side down kaman ba kitchen din daya shiga ya zauna aciki bane harya sha shayi rannan da Ummi ba, ijiyan zuciya yasauke yadawo falo da kanshi ya duka ya tattare kayansu na school sannan yabude baga nasu yaciro books nasu sunada homework ba’ayiba and wlh dudda Ummi is uneducated she manage ta koya musu homework duba ayyukan su nada yayi da Ummi ke tayasu duk sunci to menene ma amfanin auren Mai ilimi tunda bazata iya yima yaranta homework ba, kwasan komi yayi yawuce sama yakai kayan kowa dakinsu yana kallon yaran da ba’a musu wanka ba normal kayane ajikinsu bana bacci ba da Ummi tasaba saka musu, shiru yayi yanzu haka yaran nan zasuyi rayuwa, shi karan kanshi bazai iya kwatanta yanda yakeson yaranshi ba bazai dauki rashin kulan nan ba da rashin basu abincin nan ba ko kin musu homework ko uniform ma sabida yasan sunada wani set dazasu saka gobe ne amman what’s all this dakinshi yatashi yatafi yaje yayi wanka.

 

Da asuba as usual yafito harzai wuce yasauka kasa saikuma yajuyo dan yayadata tama yaran nan abincin school ta shiryasu gaban dakinta yaje tareda bude kofan yashiga ya kunna wutan dakin, bauu dakin yayi haske yatsine fuska Hadiza dake lafiyayyen bacci tayi jin haske, tadan bude idanunta kadan ganin Nura yasa cikin muryan bacci tace “Nuri am off salat ka tafiyan ka masallaci basaika tasheni ba” yana daga wajen yace “get up fix something for the kids and get them ready for school sannan basuyi home task nasuba, and arrange the house yayi datti gidan” wani kalan ware idanunta Hadiza tayi tasss takalli sama saikuma ta tashi zaune da sauri ta kakkalli gefe da gefenta dan she wanna be sure cewa bada ita Nuri yake ba ganin bakowa adakin yasa tanuna kanta da sauri tana kallonshi cikeda mamaki tace “Nuri ni kake bama order haka kake lissafo ma ayyuka haka?” Duk yanda taso kasa rike dariyan datakeji tayi tadan kyalkyala dariya tana nuna kanta tace “wait are u mistaking me for Ummi ne or wat dakake lissafo mini abubuwan da zanyi, idanunka gizo suke maka ne Nuri? Nayi kama da yar aikin mu ne? Wait ma kai what happen da u can’t do all of this abubuwan nan daka fadi are you not mahaifinsu? Can’t u cook for them? Can’t you bathe them and get them ready for school? Bazaka iya musu homework nasu ba? Who said shirya yara, basu abinci, getting them ready for school da gyaran gida responsibility mata ne kadai?” Babu wasa kan fuskan Nura yace “ki tabbatar kin tashi kin soma aikin dana fadi kafin nadawo gidan nan daga mosque” yana maganan yajuya yafita daga dakin mamaki yasa Hadiza tama kasa zama tashi tayi dasauri tasauko daga kan gado tafito daga dakin tabiyoshi abaya tace “Nuri ni kake commanding like that are you for real? Kalleni fa” tanuna kanta tana sanye dawasu arnaye kayan bacci tace “do I look like a house help? Listen fa Nuri lemme tell u something ko Allah yasan ni ba housewife bace, I have a business danake managing, I contacted agency masu kawo yan aiki babu wasu akasa za’a nemo mini, idanma zaka zauna and be attending to this children reschedule work naka do it tunda Ummi tatafi garinsu dankai ur company is big kaine CEO kanada manager dazasu iya managing komi niko banda manager, I manage everything about business dina nikadai banda sales girls danake dashi dake attending to customers namu but I do komi dakaina dan haka Nuri attend to ur kids, babu inda aka rubuta a musulunci cewa dolen dole mama ce zata dingama yara komi yaran nan na me and you get them, gaskiya I don’t have that tim…..” ganin Nuri yabude kofa yafita yasa Hadiza ta tsaya turus da mamaki, Nuri just walk out on her tanamai magana irin baida lokacin ta wow! Tana kallon kofan kirjinta na tafarfasa, da tayi niyan ko falon ne tadan tattare suyi sharing work din amman wlh tafasa tayaya zaiki girmamata ita ta girmamashi, wani disrespect ne hakan? Wannan sabon confidence din da Nuri yake mata kodan sabida yaga yasaketa tadawo gidan da next day ne yasa yake mata Iskanci haka, ta inama zata fara all this ayyuka Allah ma yasan bazata iyaba wlh, rabon datayi aikin gida harta manta to tariga tawuce wannan level din nayin aiki dakanta agidanta Allah ma yasani, idan tayi aiki agidan mijinta menene banbancin gidan ubanta da gidan mijinta? Kana gidan iyaye ne u must work, abaka umarni kabi, but your husband house suppose to be your paradise that’s the beauty of aure, kiyi duk yanda kikaga dama agidanki, kici karenki ba babbaka, tanada kudi mijinta nada kudi maisa zata tsaya da kanta tana all this silly household chores? No Nuri u can’t subject to into doing abinda zuciyana baiso yayi, itama shegiyan yarinyar nan akan wani dalili zata sakani in this tight spot, that stupid Ummi datawani tafi shegen kauyensu wai wajen kakanta, juyowa Hadiza tayi tarike waist nata tabi falon da kallo yanda yayi datti ga kwanukan abinci tsaki da ragowan food a dinning tayi tai ihuuu. “Wayyyooooo, Goddddd! A ina zan sami yar aiki yaune ni Hadiza? Ohhhh I can’t do this, how can I start doing this chores haba dan Allah, ai abin kunya ne, niba yar aiki bace ba I can’t do this wlh, ni nama manta yaya ake girki ma, indomie nan koni nakasa ci dana dafa jiya ewww, yuck” ta yatsine fuska, komawa sama tayi dakinta tawuce bayi abinta.

Dawowa gidan yayi around 7 yanda yabar falon haka yazo yasami falon sama yawuce Aman yagani da Amal duk sun zauna anan falon sama sunyi zugum kaman marasa lafiya, ganin babansu dasauri suka tashi sukai wajenshi Aman yace “Dady where’s Anty Ummi”? Amal kuma sai kawai tafashe da kuka tace “Daddy ina Anty Ummi tun jiya banganta ba she’s not in her room” tausayin yaran yaji dasauri yadauki Amal yakama hannun Aman yawuce dakin Amal yarufo kofa yace “Anty Ummi taje garinsu amman zata dawo next week I promise” dasauri Aman yace “daddy ka kaimu wajenta” shiru yayi yana kallon yaran saikuma yaga sun fashemai da kuka dukansu biyun atare dasauri yashiga lallashin su wayanshi yaciro yayi dialing number Ummi yana addu’a Allah sa akunne, kafinma wayan yayi ringin Aman ya karbi wayan yahau kan gadon Amali itama Amal tahau gadon kusa da Aman ta zauna wayan na ringing daya biyu Ummi tadauka cikin sweet voice nata data wani lankwasa ganin number mijinta tace “hello” atare yaran sukace “Anty Ummi” saikuma suka fashe da kuka atare, cikin kuka Aman yace “why did u go to kauye baki gayamana ba”? Amali tace “bakince zakije damu duk randa zaki kauyeba” Ummi jitayi zuciyanta ya tsinke dasauri cikin dabara tace “Aman wait one by one” a cartoon nasu ta koyi kalman, cikin kuka suma yaran sukace “one by one” ahankali tace “Aman daina kuka bari nafara magana da Amal” gyadamata kai yayi kaman yana gabanta cikeda lallashi Ummi jin yanda Amal ke kuka sosai tace “Amalily na, Amalily Dadynta, Yarinyar datafi duka yaran duniya kyau, ga gashi, gata yar fara, baturiya, balarabiya, Princess Amal Nura Wambai ammatana” wani kalan murmushi Amal tayi tana turo baki da saida abin yasa Nura yasaki baki yana kallon ikon Allah yarinyar dake kukane yanzun nan hartai murmushi sabida taji kirari ana cemata Ammata wai tafi duka yaran duniya kyau, gyara zama yayi yana kallonsu cikeda so. Ummi tace “banson Mudi yagane mini ke ne saisa ban gayamiki ba nazo amman zan dawo next week zan kawo miki goruba da aduwa da hanjin ligidi” dasauri Amal tace “tuwon madara fa”? Dariya Ummi tayi tace “harda tuwon madara Amal dina” wani ihu tayi tana tafi Ummi tace “tom jeki brush ba Aman wayan” bawa Aman wayan tayi tasauka dagudu tawuce bayi Ummi tace “takawanka lafiya d’a guda kuma daya tilo ga Baban shi, Mr Aman gogan zamani, matashin saurayi, dogo, yaro ga ilimi ga tausayi, yaron dayafi kowani yaro jin magana da hakuri kaman Baban shi, Amanu Aman babban yaya ga Amalily, haba ama Anty Ummi hakuri mana eh Yaya Aman” dan turobaki Aman yayi yana murmushi sosai yana juya idanu looking super cute ahankali yace “to nayi amman idan kinzo zaki mini Oumu Oumu mai cheese a tsakiya” dasauri Ummi tace “zanyi” murmushi yamata yace “bye bari naje nai brush” yana maganan yabawa babanshi waya yatafi bayinshi cire wayan Nura yayi daga Speaker yakai kunnenshi yadan lumshe idanu yace “nikuma mezan samu nida nafi kowa yin hakuri”? Dan murmushi Ummi tayi cikin wata narkakkiyan murya tace “barka da safiya Baban Aman da Amalily mijin Ummi kuma, ina kwana My Noor” wlh ko baitabajin sanyin dayakeji irin wannan dayakeji ba da gaisuwan nan datamai sai kawai yaji kanshi na kumbura, ahankali yace “Alhamdulillah ya darenki? Yasu Gwaggo? Meya sami wayanki jiya akashe” “Kowa lafiya lau, ba chaji ne, ya jikin Hajiya kuma yau zakuje asibiti?” Gyadamata kai yayi yace “eh zanje nakaita taga Dr” murmushi tayi tace “tom bari na barka kaduba Amal nasan wasa da ruwa take yanzu haka” dudda baiso ba haka yace “to zan kiraki anjima, kema kije kiyi breakfast, agaida mutanen gida” to katse wayan yayi yatashi yawuce bayin Amal shiyama yaran wanka ya shiryasu yadauki akwatin su yazuba musu kaya aciki komi dasuke bukata, yajawo suka fito falo Hadiza na zaune afalo taci uban gayu tasaka hill takada ma kanta tea tanaci da bread kadai anan kan kujera ganinsu duka da akwati yasa tace “ina zaka kaisu naga akwatinan su”? Batare daya kalleta ba yace “inda za’a kulamin dasu tunda bakida lokacin su” kofa yayi tabisu da kallo yaron ko kallonta basuyi ba, saikuma ta tabe baki ita adadinta ma atleast yau zatai zamanta ashigo without tunani su, amota ya lodasu straight gidan Baffan shi yayi dan Hajiya tacema yakawo su nan dan da ita ya tsaya yayi magana awaje kafin ya shigo gidan, akwai kananun yara agidan, anan sukaci abinci aka zuba musu abinci a lunch bag nasu dakanshi yakaisu makaranta sannan yabada addres na gidan kan anan zaa dinga zuwa daukansu sannan yadawo yakai Hajiya hospital.
***

Kusan 2min Meena tayi adakin da Ummi take zaune ga roban farfesun zabo agabanta bama ta taba ba tayi nisa sosai tana tunani, dan ijiyan zuciya Meena tasauke ta duka ahankali ta ijiye kofin madaran shanu mai zafi dake dauke da magani da Gwaggo tabata takawoma Ummi ta ijiye agabanta sannan ta taba Ummi tace “Ummi” firgigit Ummi takalleta tace “Na’am sorry banjikibane Meena” Meena dake kallonta tace “tunanin me kikeyi haka Ummi? Kinsan sau nawa ina kiran sunanki baki jiba tunanin me kikeyi haka?” Dan shiru Ummi tayi takasa magana hakan yasa Meena tazauna da kyau agabanta tana kallonta tace “meke damunki Ummi?” Yanda Meena ta tsareta da idanu yasa ahankali tace “Meena bansan yaya zan kalli Anty ba, bansan yaya duniya zata kalleni ba nazo aiki na aurema mata miji, kawai jinayi banajin dadin dan kaman nayi cin amana ne, wani kalan rashin jin dadi nakeji azuciyana da damuwa dadai wani iri” ahankali Meena tace “shi ake kira da guilt” ahankali Ummi tace “inajin shi guilt din azuciyana sosai wlh” ganin yanda Ummi tayi yasa ahankali Meena takama hannunta tace “Ummi tsaya kiji abu na farko danake so nafada miki shine Matar mutum kabarinsa, inhar Allah yarubuta wane ko wance matarka ce saika aureta ko ana k’ak’a” hannunta Meena tasaki tace “nasan yanda za’a kalli abin amman bakida laifin komi a case din nan” dan shiru Meena tayi saikuma ta nisa tace “Ummi kinga Yaya Nura bantaba ganin namiji Mai kirki da bala’in hakuri da rashin magana irinshi ba, tun yana yaro haka yake, baida hayaniya, baida rigima, baida fada, dukanmu kanninshi mata ne dukanmu mun taso shike kula da mu, ya wanke mana kaya, har yau ina tuna yanda yake wankemin kashi da ina yarinya yamin wanka ya goyani, ba karamin taimakawa Hajiya da rainanmu yayi ba cus tun ina yar yarinya babanmu yarabu da Hajiya sai Ya Nura yazame mana uba, wannan dabi’un nashi na sanyi da hakuri yasa Hadiza ta matukar rainashi” Meena tasake sauke ijiyan zuciya tace “nasan kalolin dumbin tunanin dakike azuciyanki Ummi irin yaya zakiyi kiyi zaman kishiya da Anty Hadiza, bari kiji aure is not about how beautiful you are, ba kyau, boko, kudi dawasu ado da kyalekyalen duniya bane aure ba dan duk zasu iya karewa, hali shine aure, halinki amatsayinki na mata zaisa mijinki yaji yana bala’in sonki da girmamaki haka kuma shi wannan halin shi zaka mijinki yaji kin siremai yakuma gaji dake, and duba ga abinda ni nagani da idanuna Ummi halinki da dabi’unki yasa Yaya Nura yakamu da sonki kaman yanda aranan damuka shigo Abuja muma mukaji muna sonki” Meena takai hannunta saman kan kafadan Ummi tace “ki cigaba da halinki abinda ake cewa da turenci keep being you Ummi, the caring sweet and soft Ummi mai kulawa da kowa, ki tsarkake zuciyanki ki shiga gidan Ya Nura da zuciya daya kiyi zaman aurenki kada ki bari wata ta zageki ko taci miki mutunci dagake har ita duk zamanshi kuke, wannan kunyan ki ijiyeshi agefe Ummi kinfini sanin abubuwan da Ya Nura baya samu wajen matarshi ke kibashi dan kin zauna agidan dasu, sannan namiki alkawari zan baki wasu abubuwa karatun classes na matan aure da M shakur keyi da hausa dan kowa yagane ki karanta sannan zan biyamiki kudi ki shiga classes din kokuma ma zan biyata ko nawa zata chajeni tamiki private erotic hausa class dantanayi ma wayanda basason group, ki koyi abubuwa ki ijiye kunyan nan ki farantama mijinki sama da yanda yar birni wayayya ma zata iya, ke ba budurwa bane kin Riga kin wuce level din nan, ba wani kwana kwana ki shayar da Yayana dadi da kwanciyan hankali and kiso mijinki sama da komi is not a crime kinji” Gyadamata kai Ummi tayi ahankali tanajin wani kalan kwarin guiwa Meena takai hannunta ta share mata dan guntun hawayen daya zubo tace “maza saki jiki kiyi walwala kisha magungunan ki da kyau ana miki gyaran jiki dan ki mantar da Yayana damuwanshi kuma ba kunya ehe kinajina” akunyace Ummi na murmushi ta sunnar da kanta dariya itama Meena tayi tanason kunyan Ummi ta tashi tafita, kofin Ymmi tadauka tafara sha saikuma ta kalli wayanta kewanshi kawai taji tanayi wlh ahankali tadauki wayan dailing numbershi tayi Kunya kuma saiyasa ta katse dasauri daga aurensu jiya dazu kuma yakirata dasafe saitayi ta damunshi ijiye wayan tayi agefenta dasauri tadauki cup din zata sha wayanta yahau ringing dasauri takalli wayan ganin shine yasa takai wayan kunnenta asanyaye tace “ina yini” cikin murya kaman batasaba yace “lafiya lau Ummi na kewana kikayi kikemin flashing”? Rufe fuskanta tayi kaman yana wajen baki tabude zatace a’a murya ciki ciki tace “eh” dasauri tazaro idanu taredakai hannunta ta rufe bakinta saikuma da karfi tace “wayyoo Allah ni a’a fa zance nace eh” hahahha Nura ya kyalkyala dariya wani kalan dadi yaji bana wasaba yanda she’s missing him din nan, cikeda so yace “kada kidamu nakusan zuwa na daukeki nima nagaji wlh kewan Hajiya Ummi nake sosai” adan kunyace cikeda son abar maganan tace “kaci abincin rana? Kun dawo daga asibitin da Hajiya ya jikinta”? Dan shiru yayi ko Allah yasan yanason yanda take tambayan jikin mahaifiyanshi da yanda take tambayan yaci abinci cikeda so yace “naci abinci tareda Hajiya Ummi, munje asibiti taga duka tests nata sun fito Dr yabata magani zatasha na 2weeks saimu kara komawa” dan ijiyan zuciya Ummi tasauke tace “Alhamdulillah Hajiya zata warke kaman ba itaba in sha Allah tayi ta tafiya da kanta batare da taimakon wani ba, akwai wani mai da Gwaggo tabani dana gayamata wai tadinga shafawa akafan zasuyi sauki” murmushi yayi yace “bari naduba jirgi nazo na amsa” dan zaro idanu Ummi tayi tace “aikin fa”? Yana murmushi yace “zan ijiyeshi agefe nazo naga matata wai nazo na amsan ma Hajiya maganin ta” kyalkyacewa da dariya Ummi tayi dayasa yayi shiru yana sauraran dariyanta dakema kunnuwanshi dadi kaman busan algaita, ahankali yace “ina sonki Ummi, Nura na sonki” akunyace ta sunnar da kanta tana boye kanta acikin guiwanta tana dariya kasa kasa hakan yasa murya chan kasa yace “bazaki gayamin kina sona ba? Maimaita abinda kika fadamini a wasikar nan” lankawshemai kai tayi saikuma ta kwanta anan kasan dakin datake ciki ta lumshe idanu kawai shitake gani cikeda shauki dakuma sautin wake dawani irin taushashiyan murya tace “banjin zugar kawaye a soyayya kaina dauka, ka sharemini hawaye, kasa nadaina kuka, indai ina araye Sam bana gudun ka, Allahu ya kiyaye banison waninka, kaine dai daya, acikin zuciya, mai sakani dariya sannu masoyinaaaaaaaaa” “Ummiiiiii haka kika iya wakan soyayya”? Cewan Gwaggo datagama jin komi, dasauri Ummi tace “wayyo Gwaggooo” ta katse wayan tana boye fuskanta bakaramin kunya taji ba ganin Gwaggo na jinta sai dariya take tana kwalama su Shatu da Meena kira suzo wakan soyayya Ummi takewa mijinta.

 

Wallahi Nura ko at this point jiyake bazai iya ba, dudda yau anci kwana biyu kaman sati bazai juyoba haka yakeji baiso yayi abin kunya ne shiba yaroba saisa kawai yake daure wa but Ummi zata kasheshi da soyayya, watttt!!! Ba’a tabamai wakaba tun zamanin yana secondary school daya fara soyayya da all this classmate yan aji but just look at wakan soyayyan data raira mishi ga muryanta kona mawaki baijin yakai na Ummi dadi ba, tashi yaji kanshi nayi yana kumbura, abu yaji an bugamai akai hakan yasa yabude idanunshi Musa ne yashigo office din dawata katuwan jaka a hannunshi yace “waikai mehaka saikace wani saurayi sai shafa kirji kake karike waya gam a kunne kaman wanda akema wahayi, ka lumshe idanu kana cikin kogin soyayya, dalla taso kazo nan nazo na shirya abokina” Musa yayi maganan yana zama kan dogon kujeran dake cikin office din yashigan hada mishi some magunguna yace “yauwa wai ban tambayeka ba ina zaka ijiye Ummi ne? Zaka rabamusu gidane”? Girgixamai kai yayi yace “a’a bazan so yarana su taso gida daban daban ba inaso yarana su taso kansu a hade, babban gidan nan nawa nasa an fara gyaranshi kowa da flat dinta nan da 2month za’a gama aikin tass, before then anan gidana zamu zauna dakina zan cire komi naciki nayi magana dawata interior decor gobe zatazo tadauki measurement jibi za’a kawo komi, and inaso nakara siyan wani gida a Adamawa, inaso idan na daukota daga kauyensu mu zauna anan muyi hornymoon and again yarana su Aman sunaso suje kauye to irin duk ranan da zamuzo munada gida agari kagane” Musa daya bashi kofi yace “nagane but Hadiza fa kasan kar kwankwamnata su tashi ta taba Ummi fa” wani kallo yama Musa yace “duk randa tai kuskuren tabamin mata saitaga other side of me” murmushi Musa yayi yace “shegge nawa tun yanzu kafara rawan jiki haka bare kuma kasha kindirmo” bugamai filo Nura yayi yana murmushi Musa yace “Nura kalleni nan, auren nan auren hutu ne da shakatawa dakuma more rayuwanka, Allah yabaka dukiya, yabaka yara, me kake nema banda jin dadi? Matarka taki kwantar maka da hankali tunda yanzu Allah yabaka Ummi enjoy your life da yarinya danya abinka, fresh yarinyar ni irinsu Ummi I still consider them virgins wlh, to tun suna yara akai auren nan, she’s semi virgin, gata da natsuwa ga kirki, she can cook, gata she’s not expose duk inda ka juya yarinyar nan zata juyun maka meyafi haka dadi? Enjoy your self abokina our 50’s can never be boring duk wacce tace bazatai corporating ba ajiyesu kadauko wacce zata bada hadinkai kaji dadi, kagama amarci dai tukunna nima kauyen nan zan shiga na dallo amarya ita wanchan tajika farantin nata tasha tunda ta tsufa dan wlh ni ban tsufaba ina mahaukacin son farantin nan, cheers to enjoying our 50’s Nura” cheers sukayi suna buga cups na magungunan basir sha suna dariyan keta, Musa yace “wayyoo kindirmo, Nura kawa Allah kagama amarci muje kauyen nan nima na zaba na dirja, mai manyan kindirmo zan dauka” murmushi Nura yayi shima he can’t wait yasha nashi kindirmon.
***

Tun ranan Wednesday Nura yashigo Adamawa, wani gida yasaya mai kyau duplex awani anguwan yan gayu da sunan Ummi yasai gidan, yashiga gyare siyo furnitures da sauransu ranan Friday gidan komi yagama haduwa dudda up and down dayakeyi baitaba missing shan maganin basir dinshi for a day ba, da kyar ya iya yayi bacci ranan Friday din nan ranan Saturday 11 yana kofar gidansu Ummi yasha wani jumper na ash yadi yasaka bakin shade da hula da takalmi yayi kyau kaman balarabe shiga cikin gidan yayi ya gaisa da matan dasuka cika gidan yabiya wasu kudaden daukan amarya da akace yabiya sannan yafito yashiga bayan jeep din dayazo dashi dan da direba yazo chan saiga Ummi an fito da ita wani alkyabba tasaka da atampa dan Nura yaturama Meena kudin tashiga cikin garin Adamawa tasayo komi, da kanta tama Ummi black and red henna takuma mata kitso Ummi harwani kyalli take abayan mota aka sakata itakuma Meena tashiga gaba, direba yaja motan, saida suka danyi nisa atafiya kaman daga sama Ummi taji yajawota ahankali yasata ajikinshi wani irin kunya taji dan akwai direba da Meena amotan kasa kwace kanta tayi tai kaman yar jaririya ajikinshi tana shakan cool kamshin turarenshi, hannunta yakarba yana kallon lallen ahankali yace “Auta wayama matana zane mai kyau haka”? Dasauri Meena tajuyo ganin yanda ya rungumo Ummi yasa tajuya dasauri tace “Yaya nine namata harda kitso ma” dasauri yace “aaah lallai Auta tai abin arziki mu bata tukuici ko baby” yayi maganan yana leka fuskan Ummi dake cikin alkyabba, gyadamai kai tayi akunyace, hannu yasa yadauki wata Prada purse dake sude na kofan motan yabude yaciro bandir daya na 1k yace “amsa Meena mun gode” cikeda dadi tace “laaaa Yaya thank you” gidan Ummi suka fara zuwa suka shiga ciki gidan yayi kyau zama Meena tayi afalo shikuma yana rikeda hannun Ummi sukaje sama daki uku ne asaman master bedroom yabude yashiga ciki da ita yana maida kofan ga mamakinta daukanta yayi chak atsorace tace “wayyoo Gwaggo” murmushi yayi yasa hannunshi ya jaye hulan alkyabban yana kallon fuskanta da black skin nata ke sheki sosai lumshe idanu yayi ya zaunar da ita kan gado tareda zama yana facing nata akunyace ta sunnar da kanta kasa, murmushi yamata yakai hannayenshi yabude boturan alkyabban yacire shi daga jikinta ya ijiye a gefe yana kallon kayan jikinta yaune first day dayake ganinta da atampa fitted daidai jikinta wanda duk aikin Meena ne ita tadauki measurement nata ta shigo birni dashi atampan yamata kyau, ahankali yakai bakinshi kan kumatunta yasakin mata peck. “Muah!” Wani yirrr Ummi taji dasauri ta runtse idanunta, batare daya cire bakinshi daga jikin kumatun ba yace “kinyi kyau sosai Zainab, kinyi kyau” idanunta alumshe itama cikin whispering tace “kaima kayi kyau bantaba ganin abu mai kyau irinka ba Noor” fuskanshi yakawo saitin nata yadaura hancinshi kan nata yana kallon dogayen gashin idanunta dan idanunta a kulle suke yace “kalleni, bude idanunki ki kalleni ki gayamini inada kyau Ummi” ahankali kaman mai tsoro Ummi tabude idanunta tahada da nashi idanunshi sun kankance kadan suna mata wani kallo da all she sees irin usulin soyayya aciki, gently tadaga hannunta daya takai saman kuncinshi wani kalan lumshe idanu Nura yayi sabida sanyin dayaji a hannnunta yakai hannunshi daya ya daura saman hannun dayaji yana rawa kaman zata dauke daga saman fuskan nashi yace “wayyooo Allah na” yabude idanunshi ahankali yadaura kan nata yace “Ummi kin iya shagaltar da namiji, wlh kina daburtamin lissafi” lumshe idanu tayi tabude su tadaura akanshi tareda huramai a very light breeze daga bakinta tace “huuuuuuhhh” ahankali ya lumshe idanunshi wani natsuwa na shiganshi yasake danne hannunta dake kan kuncinshi gam, with a vet light yet naked voice Ummi tace “tsarki ya tabbata ga Allah ubangijina, ubangijinka, Ubangijin talikai, ubangijin daya busa mana numfashi, ubangijin daya hallitoni yakuma halittoka ya halitto kowa, idanun Ummi basu taba ganin namiji da komi nashi kyau ne dashi kaman ka ba My Noor, idanunka farare fat masu asirtaccen kyau da mai baiwa irina kadai ke iya gani, fuskanka ka kyanshi zai iya sanyaya zuciyan mugu daya kawo maka hari, lafuzan ka yafi zuma zaki dakuma dadi, muryanka kaman ana busa sarewa, sarewan ma wacce ake samota abishiyan dake kan dutsen kufaina wacce take fitowa sau daya a shekaru dari, halikan gabaki daya yafi duk wani abu da Ummi tasani aduniyan mai kyau, gemun nan naka akullum saina tunashi dan shine abu na farko dake fara sanar dani zakamin murmushi” wani kalan murmushi Nura yayi yadaura bakinshi saman nata batare dayay kissing nata ba dasauri ta lumshe idanunta murya chan kasa yace “bakina kuma da kanshi zai sanar dake abinda yakeyi” soft sensual kiss yafara mata jikinshi na dan rawa kaman this is the first time yafara kiss in his life, almost 2min yayi ahaka sannan yasaki lips nata taredakai fuskanshi saman kirjinta ya kwantar tareda cuddling nata ahankali yana lumshe idanu feeling tudun chest nata kafin ahankali yakai hannunshi yaciro wayanshi, cikin muryanshi da baya fita sosai yace “wlh bazan iya kai Meena airport bari nakira direban nan yakaita”.

Assalam Alaykum Ladies.
This littafi ina yinshi ne dan gwadawa mata da maza some kuskure nasu, how to overcome major issues dake kashe aure and how to do and undo things a aure, I wanna ask something at this point. Kunason Erotic scene? Na koyamuku how to spice it up a bedroom? Kunason namuku erotic scene ko nabarshi??? I go with what majority want.
Thank u
M Shakur ✍🏻
[9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫 MATAN?? Ko MAZAN!??💫

 

✍🏻M SHAKUR

Back to top button