Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 20-21

Sponsored Links

Page2️⃣0️⃣&2️⃣1️⃣
Niii bazan iyya baka bashi ba true,

Habba jambosko ka duba dai pls insha Allah Zan biyaka,

Ok shikinan na nawa kake so?

Ni koh na nawa ma ka bani yanda kaga ya dace ,

Ok Zan baka na d’ari 300 Kai na d’ari 150 madam na150 kaga kudina 300 kenan ,

Nagode sosai,

No problem,

Maganin ya basa nata da nasa ya kamo hanyar gida…..

Nikam wanka nayi nayi Sallah na kwanta duk yanda Khadija tayi nacin naci abincin da ta dafa na Rana, na kasa itama tana gama aikace aikacen ta shigo d’aki,

Aunty’ya jikin dai?

“Da sauki Khadija”

Toh Allah ya k’ara sauki bara na tafi Aunty Koh kina da wani aiki da Zan Miki

“Khadija bani da aikin kome kije ki huta kema”,

Toh Aunty tace tana kokarin fita a d’akin

“Khadija ki dauki kula ki zuba abinci a ciki ki tafi dashi gida”

Toh Aunty,

Khadija kitchen ta shiga ta ibi abinci kamar yanda Aunty tace,ta kama hanyar waje zata fita,
a kofar gida suka haduwa da yayan ta zai shigo ,

Yaya baka da lfyn ma yawo kake,?

Khadija chemist naje fa na samo Mana magani Wai yaushe na fara Wasa da kene,

Hhh sorry toh ni Zan wuce yaya Allah ya yaye muku

Ameen Khadija ki gaida Goggo sannu da aiki

Toh Yaya zataji,

Cikin gidan ya wuce a hankali yake tafiya gaskiya mutuwar innon nan ta shiga jikin Yan gidan su yanzun gidan shuru,

Da sallama ya shigo d’akin , Assalamu alaikum,

amsa masa nayi “waalaikumu salam”

Ya jikin dai ?

“Da sauki”,

Toh ga magani nan Amma ya kamata ki samu kici abinci kafun Kisha,

“Wallahih banajin dadin bakina Sam”

Haka dai Zaki daure kinji

Toh nace ina mikewa fita nayi waje,

kitchen na shiga nad’au kulan da Khadija tace ta saka Mana abincin na bude,

Dafa dukan shinkafa da wake ne Kuma da D’an yawa ta dafa harda na dare kenan,iba nayi na zuzuba a plate guda biyu nasa shukali d’auka nayi a hankali ina taka kafata dake ciwo har yanzun,

na shiga d’akin aje abincin nayi na bude firij na siyaye ruwan randa danake zubawa a roba NASA a firij don yanzun Koh pure water bani da kudin saya bare drinks,

Ruwan na tseyaye a cup inda na jejjera a saman tire akan firij don irin haka,

Ruwan na iba na dawo na zauna tura masa nasa nayi hade da masa Bismillalahih,

Hannu Al’ameen ya saka ya fara cin abincin sa don shi Yana d’aya daga cikin irin mutanen nan da ciwo baya hanasu ci,

Nikam tsakura nayi na aje shukalin ruwan Randa Mai dumi na ibo nasha maganin dashe don ance ba’a Shan magani da ruwan sanyi na kwanta na barsa zaune yana cin abinci,

Harkin koshi kenan Sumayya?

“Nace maka bakina ba Dadi fa Amai zanyi wallahih Inna sake Kara Koh shukali D’aya ne”

Yana gama cin abincin ya mike ya tatara Kwanukan yakai kitchen dawowa yayi da ruwan Randa yasha maganin mikewa yayi zai sake fita,

“Ina zakaje Kuma”?

Zan D’an fitane ,

Zuwa Ina?

Zanje wajen sana’a ne,..

“A baka da lfyn zaka fita kaje ka zauna a Rana”,

In Rana ya Isa wajen bairona Ina komawa jikin shagon Haladu na zauna,

“Zirga zirgan fa magani fa kasha kadai bare itan Rana yadan fade kaji saukin jikin naka sai ka fita”

Ok toh yace ya lalube pillow ya jefa a kasan cafet ya kwanta,

Dukan mu bacci muka koma saboda maganin mura da mukasha,

Kiran la’asar shiya tashe mu Alhamdulillah daga ni harshe jikin mun yayi sauki,

Fita yayi Alwala ya wuce masallaci,,

Nima sallar nayi na wuce kitchen Jin zazzabina ya sauka sosai ruwa na daura a wuta yana zafi na surka a baf na zuba salt na tsoma kafata a ciki sosai na gasa kafar,naji dama dama

Kayan da Khadija ta wanke Mana na nade nakai whtdrp harda nasan TV na kunnan Ina kallo sosai na maida Hankali na akan TV don bani da aikin da zanyi kome Khadija tamin,

Al’ameen daga masallaci bairon mangoron sa ya wuce ya yaye buhun da yake rufewa,
cikin hukuncin Allah sai yayi cinikin dari,Jin ana Kiran mangariba yasa ya rufe,

Masallacin ya sake shiga ana idar da Sallah shagon jambosko ya wuce,sosai ya basa hakuri ya basa darin da yayi ciniki akan gobe in Allah ya kaimu zai basa sauran,

Ganin cika alkawarin Al’ameen yasa jambosko ya karbi D’arin,

Gida ya dawo lokacin Nima sosai naji saukin jikina Ina zaune a waje Kan darduma don yau d’auke NEPA sukayi daga Kiran mangari ba gashi sai zafi ake Kamar me,

Shigowa yayi Jin motsena akan dardumar shima lalubar dardumar yayi ya zauna a hankali,

“Daga tafiya sallah sai yanzun kuka idar kenan” na tambaye sa

Ah ah naje na bude Mangoro ne,

“Jikin yayi sauki.kenan”?

Alhamdulillah gaskiya nikam naji sauki bakiji muryana Yana fita ba Daman jambosko Kam indai ya hada ma mutun magani irin na kananun ciwo wukan nan haka ana Jin sauki cikin hukuncin ubangiji,

“Gaskiya ne Nima Alhamdulillah zazzabin ya sauka sosai,”

Allah ya kara sauwa kewa,

“Ameeeeeen bara na kawo maka abinci, kasan Khadija dafawa tayi da yawa Yar albarka”

Toh yace

Nikam tashi nayi na ibo Mana abincin kuma dukan mu ba laifi munci da yawa Koh nace naci da yawa don shikam baiji sauki bama ci yake abinsa,

Yau a waje Muka kwana dukan mu washe gari da karfin jiki Muka tashi Alhamdulillah Allah abin godiya,

Da safe da kaina na kimtsa kofa Amma bamuda abinci karyawa Koh sisi Bai kwana dashe ba fita yayi waje Koh Allah zai sa ya samo Mana na cefenen,

Al’ameen kam
duk buga bugansa Bai samu kome ba har karfe Tara Amma shuru ba Wanda ya Saya mangoro bare ya samu na cefene,

duk ya shiga damuwa sosai na rashin kudin da zai sayi kayan Miya sannna baison karban bashi a shagunan Yan unguwan don har sun saka Masa ido, duk da Daman ba basa bashin suke ba bare suce baya biya Amma har ya Kai idan suka gansa Yana tunkarar shagunansu sai sun Kama gulmar sa atunanin su yazo tambayan bashi,

*********
Ganin har 9:30 Bai dawo ba yasa na mike indomie na d’auka guda biyu, na soya Mana da Mai Koh albasa Babu bare tarugu,

Ina sauke indomie na juye Masa rabonsa a kula iban nawa nayi a plate na koma Kan darduma na zauna na Tasa indomie a gaba shukali nasa na iba a hankali Zan Kai baki bansan lokacin da wani irin kuka ya taso mini ba lallai duniya abin tsoro ne,tabbas duk rufin asirin da Allah ya maka tabbas zai jarrabeka don gwada imanin ka,

Ada Koh da sunan Wasa Ban taba tunanin akwai Randa xaizo nasha ruwan masu ruwa bama bare Wai ruwan rijiya, yau abinda nake ci Ada Koh Mai gadin mu yanacin Wanda yafi Wannan,

*********
Hawaye na share nakai indomie baki chusawa kawai bake Amma bawai don inajin dadin Saba don harma na gaji da indomie, taliya,shinkafa, macaron,i sukenan abinci a gidan nan tunda na aure yayan Khadija su nake ci,

Al’ameen Kam Yana zaune a kofar gidan har yanzun Sam ya kasa shiga ciki saboda baisan me zaice Mata ba,

Nikam Ina Gama cin abinci na tatara Kwanukan daidai lokacin aka kawo NEPA d’aki na shiga TV na kunna na kamo KungFu channel ana wani film Mai Dadi sosai na Bata hankali akai,ada Sam ban Damu da TV ba Amma yanzun karfe da yaji na zama Yar kallo
waya da laptop Kam duk na kashe su na aje,tunda Koh kudin data bani dashe Kuma bamai kirana,

Khadija ce take tahowa gidan yayanta tun daga nesa ta hangosa zaune a dakalin kofar gidan,

Assalamu alaikum yayana na kaina

Waalaikumu salam khadin Goggo kene ??

Eh Yaya Ina kwana?

Lafiya Alhamdulillah, khadija ya gida,?

Alhamdulillah,
ya jikinku da Aunty duka,?

Da sauki sosai wallahih khadija,

Allah ya Kara sauki

Ameen

Amma yaya yakake zaune a kofar gida Koh bazaka bude bane karfe 10:43 fa yanzun,Koh jikin baiyi kware bane

Lafiya klau khadija

Shuru kawai ta Masa Amma ita Karan kanta tasan akwai abinda ke damunsa boye Mata yake,

Toh Yaya bara na shiga ciki na kawowa Aunty kulanta ne,
Kuma na fad’a maka zanje Fulani Dance na auren Asma’u Inka Amince

Toh khadija a Ina ne za’a yi program in?

Yaya a Muri Hotel ne

Gaskiya khadija bana son kina zuwa ire iren wajajen bukukuwan shirmen nan ki dai bare Walima sai keje Mana?

Habba Yaya wallahih ba abinda zai faru kuma kasan yanzun ana saka Yan sanda a get bare auren Asma’u ba kowa za’a bare ya shiga ba,

Gaskiya khadija banason zuwa irin wannan program, Amma tunda kin nace Allah ya dawo dake lafiya,

Ah ah na fasa zuwa tunda baka so,ta fada amma fuskarta ba walwala don tanason zuwa Asma’u ce kawa ta farko data taba gayyatar ta biki Sam kawayen ta basason sakata a kawance saboda sunsan ba Anko zata Saya ba Amma Asma’u Bata damu ba a hakan ta gayyace ta ta shigo kawancen auren ta,

Ah ah khadija kije nasan Asma’u yarinyar kirkice duk da iyayen ta sai addu’a halinsu,

yauwa yayana na gode ,cikin farin ciki

Da yaushe za’aje Fulani Dance in?

Da yamma,

bani da kudin da Zan baki na machine khadija Amma in kin tashe tafiya ki biyo ta bakin titi taima nayi ciniki sai na baki,

Ka barshe Yaya jiya bayan na koma gida nama wasu yara kitso sun bani dari da hamsin zai isheni ,

Toh khadija muje ciki,

Shigowa sukayi da sallama karar TV yasa ban jisuba sai da ya shigo d’akin tukun na juyo “Ina ka shigane tun sassafe ga karyawan ka na zaune na Gama”

Sumayya ban samu na kayan Miya ba shiyasa ban dawo da wure ba,

“Allah yasa mu dace”kawai nace

Ameen, ya amsa a sanyaye

Ina kwana Aunty?

“Wai ni ba muryan khadija bane nakeji a waje”,

Nice Aunty

“Toh ki shigo mana”

Ah ah Aunty kula na kawo na aje a kitchen Zan wuce,

“Ai baki Isa ba daga zuwanki sai tafiya”

Kai Aunty kin manta nace Miki kawata zatayi aure,
ai yau za’a fara bikin auren,

“Wai su kawayen Amarya kenan toh da safen nan Zaki gidan sunne”?

Ah ah zanje na wanke Kaya nane nama Goggo girkin Rana zuwa yamma Zan wuce,

“Toh khadija ki kula da kanki kinje iyya kacinki wajen program Kuma 5:30 nayi ki kamo hanyar gida kinsan waje irin Wannan in dare ya fara akwai hatsari fa,”

Wallahih Aunty ni kwanaki ma haka naji lbr Wai ana tambe a wajen program har aka tsokawa Amarya wuka a ciki ta mutu,

“Toh ba kin gani ba khadija Allah ya tsare”

Ameen,tace tana kokarin juyawa,

“Yauwa khadija shiga kitchen akwai indomie a kula ki iba ”

Wallahih Aunty na koshe

Ganin Taki yarda ta iba yasa na barta ta tafi ni Kuma mikewa nayi na ibo Masa indomie kadan yaci,

don wallahih Sam baijin dadi a waye gari baida Koh sisi da zai Saya abun da zai baiwa Sumayya,

“Nikam Koh jikin ne”? na tambaye sa ganin sa a salube,

Ba kome yace Yana mikewa ni Zan fita me za’a Saya na Rana da dare,

” Duk abinda ka samu ka Saya daidai aljuhunkan”

Ba karamin Dadi yaji ba ganin Sam bata nuna Masa Koh a fuska ya Gaza riketa ba,
insha Allah Yana fatan zamansa da Sumayya ya d’aure,

**********
Har yamma cinikin dari biyu yayi,
saboda cika alkawari yasa Yana tashi daga bairon mangoron chemist ya wuce ya biya jambosko dari saura d’ari,

d’ayan D’arin Kuma ya sai Mana albasa da tarugu sai tunanin halinda Sumayya take kawai yake fama tun fitarsa da safe Bai samu kome ba sai da Allah ya Sosa wata baiwar Allah tazo tasai Mangoron dari biyun na,

Nikam ganin Bai dawo da Rana ba nasan Bai samo kome bane indomie d’anye na ci guda D’aya,

Sai goshin mangari ba Al’ameen ya dawo da cefene gonin tausayi Yana rike da laidar cefenen d’ayan hannun Kuma sandar sane,

karban kayan Miyan nayi na d’aura macaroni dafa duka,don yanzun mun zama masu cin dafa duka bamu da abinci sai she karfinsa baikai muci da Miya ba,

Wanka yayi ya d’aura Alwala ya wuce masallaci sallan mangariba Bai dawo ba Saida aka hada da isha’i

Vayan ya dawo mukaci abinci ya rufe kofar shashen mu muka shiga d’aki akan gado na kunna Tashar Arewa 24 ana kaddaran rayuwa na satin nan sosai nake dariyan Karam sosai ganin reaction nasa lokacin da saurayin preter ya shigo,

Al’ameen Yana zaune a Kan cafet ya kurawa TV ido kamar wani Mai kallo sai kyetkyet su yake,

Hala kinajin dadin kallon film in kenan?ya tambaye ni

“Sosai ma wallahi kasan me” Nima na tambaye sa

Cikin Jin Dadi ganin na fara sakin jiki dashe yace ah ah,

Dariya na sake sosai kamar ba abinda ke damuna”Wai karam Yana cewa sameer Wai kafadun saurayin d zaizo ganin preter, Wai kafad’arsa Kamar marikin Lena haka fa yayi da hannunsa lokacin da zai Fadi marikin lema” Ina kara sakin dariya,

Shikam sakake yayi Yana sauraranta abin sai mamaki yake basa irin dariyar da take innan,

“wallahih ni inason preter innan da Karam suna burgeni sai dai dukansu Basu ma San suna son juna ba Kuma Anya Wannan saurayin da yazo gidan su ba shine saurayin shalin ba kowa”?

Don me kike sonsa da preter in toh?

“Suna burgeni ne”,

Suwa kenan?

su biyun”

Harda namijin kenan?

Juyawa nayi cikin mamaki Ina kallonsa Wai me mutumin nan yake nufine Kam
Shuru na Masa

shima Jin tayi Shuru Bai sake magana ba,

Sai 11:7 na kashe TV kayan bacci nasa na kwanta

Jin tana bude whtdrp ya tabbatar Masa zata kwanta kenan yanzun, mikewa yayi ya dau pillow daidai lokacin yaji ta tana addu’an bacci kasa kasa,

Shima haurowa yayi bakin gadon,

Da mamaki nake kallonsa ban Gama Shan mamaki ba Saida Naga ya kwanta Yana lalube na

“Wai Kai malam tsaya me kake nufi ne Koh ruwa ake yanzun da zaka hauro wajen kwanciya na” nafada ina kallonsa da mamaki

Jin tambayar da ta Masa ya sakasa gane saitin da take,

A bazata kawai naji ya damko ni yana cewa

Eh ni yau……………..

*Gaisuwa na musamman gareku*
🍀 *Princess*
🍀 *Maman Ammar*
🍀 *Sakeenat*
🍀 *Faeexetion*
🍀 *Oum Abdullahi*
🍀 *Umme zariya*
*Naga comments naku na yaba sosai*

 

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

🍀 *Na tsunguno(habil)*
🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

Contact them vie
🪀08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense
[9/27, 4:10 PM] +234 806 983 1049: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
free book 🤧

Back to top button