Hausa NovelsHausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 46

Sponsored Links

46….

kafin a kira Assalatu Hajiya mommy ta nufo dakin domin ta tashi nabeelah Sbda ta daura girki da wuri, jiya mutane nata santin abincinta, Sam ma sauran abincin ba a Wani cicciba anficin Wanda nabeelah ta dafa. Ta kira sunanta, bayan ta shigo dakin ta tsaya a kanta,kwance nabeelah take tana kallon Saman dakin ita kadaice kwanciyar datake iyayi, bata ita wata kwanciya bayan wannan. Idanuwa Hajiya mommy ta tsure cikinta nabeelah dashi wanda ya bayyana, Amma se Hajiya mommy Tasha ko idonta ne, dukda taji Wani mummunar faduwar gaba, ta lumshe idanuwanta ta kara budewa a kan cikin nabeelah,. “toko tumbine?” Hajiya mommy ta tambayi kanta da kanta, haka kawai ta tsinci knta da fadawa duniyar tunanin da bata San kona menene ba. Tafi karfin 5mnt tsaye kan nabeelah wadda keta sheka bacci batasanma hajiya mommy ta shigo ba, kaf maaikatan dakin bacci sukeyi kusab su hudu kowacce da d’an gadanta me daukar kafita waya sha biyu, dakunan masu Aiki a gidan tafi daki ashirin Kuma ko wanne da masu Aiki a ciki kusan mutum hudu, shida na Maza shida na mata. Hannu takai ta daki nabeelah a kafada, da karfi, a firgice nabeelah ta tashi zaune idanuwanta suka sauka a kan hajiya mommy, cikin hanzari nabeelah ta kalli cikinta a ranta tayi Addu’ah Allah yasa de hajiya mommy bata gani ba…” “tashi kije Ki daura girki,,,” nabeelah tace Toh ta diro daga kan gadon tana kallon Agogon dakin taga karfe uku ne da Rabi na dare, ko hudu batayi ba, Sam baccin be isheta ba, ji tayi kmr Yanzu ta kwanta aka tasheta, Wani irin azababben ciwo taji kanta nayi, ga azabar ciwon ciki da taji Yana taso mata, ji take kmr ta koma ta kwanta, Amma dole ta lumshe idanuwanta ta bude, ta karfafa jikinta ta fice a dakin hajiya mommy nata binta da kallo haka kawai taji a ranta bata yadda da nabeelah ba, yayinda kiyayyarta ta yawaita a zuciyarta, a sukwane hajiya mommy ta biyota kiching din, se kawai nabeelah ta ganta kwatsam seda gabanta ya fadi, yaga de se binta take da kallo tako ina, zuciyar nabeelah na bugu zuciyar hajiya mommy na bugu, dukkaninsu ba a natse suke ba ba kmr ma nabeelah ita tasan dalilin rashin nutsuwarta ita Kuma hajiya mommy bata sani ba, itade kawai taji ta kasa nutsuwa. “Ai nagaya Miki abubuwan daza kiyi tin Jira kin fahimtar kou? Akwai komi a kitchen din kasa dazaki bukata,..” cewar hajiya mommy aunty Nabeelah tayi hanzarin amsawa da “toh…na fahimta…” Hajiya mommy ta shiga kare mata kallo, jikin Nabeelah ya fara Neman bari, kanta na kasa a ranta se Adduah takeyi zuciyarta nata fatt fatt fatt. Hajiya mommy ta juya xata fice a kitchen din se Kuma ta juyo ta sake kallon Nabeelah se kawai ta juya ta karasa ficewa a kitchen din haka kawai ta tsinci zuciyarta da saka da warwarar da batasan Kona meye ba a ranta de se tunani takeyi Kmr ciki tagani jikin nabeelah Kuma kamar tumbi,hakade Hajiya mommy tadinga saka da warwara. A ketchin din Nabeelah jiki ya mutu Se Kara adduah takeyi ta fara aikin tanayi tana layi kmr Yar maye, gashi ko Ina a jikinta azababben ciwo kawai yakeyi. Haka tadinga Ayyukan da kyar tanajin mararta kmr zata bude, inda ace da hali ma kwanciya zatayi , ji take kmr ta saka ihu, har akayi asubahi ta tsaya tayi sallar asubah, haka ta wuni tsaye yauma gashi cikinta ba komi se ruwa data sha, Aiko tanashan ruwan taji cikinta ya fara motsi, ada hatta tsorata, Dan haka ta dauki ayaba taci sosai Sbda tsoro takeji kar cikin ya dena motsi, a asibiti in taje awo doctor Maryam nace mata in ciki yadena motsi hanzari akeyi Azo asibiti wato da matsala, harga Allah batasan Wani Abu ya sameta koya samu d’an cikinta. Tukunya shida ta daura a wuta, tana Aikin ne da kyar, innah sadiya tazo ta tayata a tsorace take tayata gudun kar Hajiya mommy tazo ta ganu, sauran maaikatan nso su tayata Amma Suna tsoro. Haka suka gama aikin cikin temakon ubangiji, mutanen suka yawaita a gidan, hajiya mommy se shiga Ake ta alfarma ana fitowa it’s a dole matar Alhajin Allah. Nabeelah da wasu Wanda aka dakko Dan serving mutane suke ta serving mutane, hajiya mommy na bakin cikin nabeelah ta zauna, duk inda tayi seta bita da Ido, a ranta kawai bata yadda da ita ba,, nabeelah kanta a tsorace take ga uban ciwo jikinta nayi kafafuwanta sunyi Wani him, sun kumbure, Cikin jikinta yayi lakur saboda azabar yunwa SE a hnkli yake wutsil wutsil Daman a gida haka takeyi in taci abinci se ya hau motsi Sosai in tanajin yunwa se yayi lakur. DUk abubuwan da takeyi hankalinta na kan tunanin Aeezad ta tabbatar yanacan ya kusa hauka,ko seconds yayi beji taba zarewa yake neman yi, Ina maga wuni da kwana gashi Amma Kuma Wani wunin. Allah-allah nabeelah take ta bar gidan Amma Ina ranar ma Nan gidan ta kwana sbda bakin Basu watse ba wasu se jibi zasu watse Yan nesa kenan, wasu ma Yan kusan ne Amma Nan zasuyi sati daya sbda duk sun gama da mazajensu ba yadda zasuyi, itafa Hajiya mommy bata kawance da macen da namiji ya Isa da ita, sede tayi kawance da macen data isa da namiji. Daren Wannan ranar ita knta nabeelah gaza baccin tayi Sbda tunanin halin da mijinta yake ciki, ga ciwon ciki, gana baya, gana jiki Sbda azabar gajiya, duk de jikin ma ya mata ba dadih kmr ba nata ba.

A gidan Aunty hafsat Kam Aeezad nata kira, tin tana daukar tana masa karya, harta kashe wayar kawai Sbda ta rasa ma yazata ce dashi, harga Allah bazata iya gaya masa inda nabeelah take ba, Sbda tsoro, Se Yanzu take datasanima da gaya masa gaskiya tayi tin farko,tana kashe wayarta ya fara Kiran lambar big Hajiya, nanma Aunty hafsat ta dauki wayar ta kashe, big Hajiya se matsifa takeyi, da ace zata gane gidan rafi’ah da tini ta tafi, Sbda de kawai bazata gane bane gashi Kuma aunty hafsat taki kaita ko barinta ta fita ma taki,. haka suka wuni a falo jungum jungum, suna jiran dawowar nabeelah Amma Shiru har dare , gabaki daya se hankali ya kuma tashi, Daman 2days din takeyi in taje gidan ko 1day, Amma Yanzu se aunty hafsat ke gani kmr an gane cikin jikin Nabeelah ne,. Ranar ko part din baban Noor bata jeba, sede tace masa mgni zatasha ta kwanta kawai a part dinta. Nan falo suka kwana zaune, aunty hafsat ta rasa yazatayi tunaninta ya kasu kashi kashi. big Hajiya tasakota gaba da matsifa da bala’i, gani takeyi kamar lefin tane, se fadi takeyi “Meyasa Baki tasoni ba?ai da dakikaga zuwan rafi’ah ni dase ki tasoni Ina dai-dai da ita a Wannan Karan bazan daga mata kafa ba wallahi bazan bata fuska ba, daman insda cikinta,bata isa ba tayi kadan, ga dumbin rashin imani rafi’ah yarinya da ciki kusan wata takwas a wata takwas kadan ne babu, Nan a asibiti ko wahala ance ba aso tadingayin aikin whla,, saboda Allah fa, wlhi da lefinki hafsatu da lefinki, Allah yasani, Yanzu in mijinta yadawo miza ace dashi? Ubangiji ya Allah ka tsare cikin jikin yarinyar Nan…” Aunty hafsat sede ta rafka uban tagumi ta zubowa big Hajiya ido kawai ,ita kanta tayi nadamar ma bari nabeelah ta fita a gidan, tayi Dana Sani yafi sau dari, se Yanzu take tunanin daman cewa tayi nabeelah bata Nan tana garinsu, itade ubangiji ne kawai yasan ma a Wani hali take ciki yanzu, tashin hankalinta ma Aeezad kwara na big Hajiya DUk me saukin ne, ita yanzu big hajiya maganarta kawai ta cikin jikin Nabeelah ne,, ta tabbatar duk yanayin da suke ciki be kai kwatan yanayin da Aeezad yake ciki ba , shida ma be garin kenan, duk inda yake Aunty hafsat tasan hankalinsa yanacan a tashe,.

A bangaren Aeezad tinda ya kira Aunty hafsat yaji ta kashe waya hnklinsa ya tashi ya kira big hajiya itama bugu daya tayi aka kashe wayar, Nan take zuciyarsa ta Kuma tsinkewa, yashiga tunanin ko Wani Abu ne yasamu mommynsa, yayi innalillahi wa’inna ilaihirrajun yafi sau dubu, ji yake zuciyarsa na mugun bugu kmr zata fashe, a jikinsa yakeji Wani Abu yana faruwa da bangon zuciyarsa wato mommynsa , tunanin meya sameta da yayi yafi dubu? Kawai de ya fahimci dole Wani Abu ya samu mommynsa, aunty hafsat Kuma taki gaya masa, tabbas akwai abubuwan da take boye masa, shi komade mutuwa tayi ne mommy tasa? Se Kuma ya girgiza kai, yasan da mutuwata tayi dole ne a kirasa a gaya masa,. Ya kira wayar nabeelah data Aunty hafsat data big hajiya yafi sau dubu uku,. Wuraren karfe daya na dare ya fara tunanin barin garin zuwa garin katsina, Zaks ne ya dakatar dashi da kyar,ya dinga basa baki,, duk abubuwan dake faruwa Zaks na gefe, shine ya dinga kwantar masa da hankali kan ya bari giobe sesu kama hanyar zuwa katsina,. Gabaki daya Aeezad ya fita a hayyacinsa, Idanuwansa sunyi red sosai, ga uwar rama yayi, a lokaci kankani, tin randa bejita ba , har Yanzu ko ruwa be shiga cikinsa ba, bakinnan nasa yayi fari fattt, labbansa sun bushe rakayau idanuwansa sunyi narai-narai sun kankance Sbda damuwa, ji yakeyi kamar ya fashe da kuka,ya tabbar in Wani Abu ya samu mommynsa tabbas seya kusan mutuwa, shi da a taba masa mommy kwara shi a tabasa, da asa mommynsa kuka kwara shi asashi Kai inda halima a kashesa ko a nakasashi, duk ze dauka inde a kan mommy ne,.har bugun zuciyarsa ya chanza,haka ke kara bashi tabbacin Mahadin zuciyar tasa Bata cikin koshin lafiya. Be bar Kiran Aunty hafsat ba, da big hajiyar da lambar mommynsa, har safiya kamar yasamu aikinyi, haka ya kwana kira wlhi ko gajiya bayayi,Kuma amsar daya ce duk wayoyin kashe suke.washe gari tin adubah yaso subi fly suje katsina , sede an tashi da yanayin hazo, ta yadda jirgin sama bazeyu ya tashi ba,har wuraren karfe daya, Aeezad na Jira yaga ko hazon ze sauka Sbda bayajin ze iya bin mota zuwa katsina, gani yake kmr ze shekara a hanya basu isa ba. kawai jirgi yakeso yabi, duk lissafinsa ya kare Sbda baya hayyacinsa, ji yakeyi kmr ya kulle idanuwa ya bude ya gansa a gidan Aunty hafsat yaga meke faruwa da mommynsa. “Zaks aunty hafsat batamin adalciba…in Wani abu ne ya faru da mommyna,kwara a gayamin , kaga Yanzu fargaba na neman kasheni wlhi ji nake kmr zuciyata zata buga, mommy kawai nakeso nagani, wlhi inaso inga mommyna zaks, ko jinta nayi a waya baze wadatar Dani ba, so nakeyi kawai na ganta, mutuwa zanyi in Wani Abu ya samar min ita, wlhi har Aunty hafsat bazan bari ba in Wani Abu ya samu mommyna, saboda da gan-gan, ta kashe wayarta Kuma na tabbar tana sane, tinda harta amshi ta big Hajiya ta kashe again,,gaskiya akwai matsala! Akwai Wani Abu ba asone a gayamin kawai zaks,,Amma Ubangiji na Nan,insha Allahu mommyna tana Nan da Rai ita da babyna na cikinta…” Aeezad ya fadi da disasashiyar muryarsa wadda ta narke Sbda tashin hankali, da tsantsar fargaba, Ya kalli Zaks, wayarsa na hannunsa still se Kiran aunty hafsat yakeyi da lambar big Hajiyar data nabeelah shiru har yanzu, hankalinsa yafi na uban kowa tashi a ranar haka yake gani,. Cikin muryar kwantar da hankali Zaks yace “Karka damu Aeezad insha Allahu alkhairine, ka kwantar da hankalinka Dan Allah ..” murya kmr ze kuka ya amshe da “ta yaya zan kwantar da hankalina? Eheee ta yaya zan kwantar da hankalina? Kai kasan tashin hankalin da nake ciki kuwa? Wallahi kwara ace mutuwa nayi na huta da Wannan tashin hankalin da nake ciki for now…mommy fa? Mommyfa akace zaks ? Banganta ba, banjita ba, wlhi hauka cewa zanyi zaks!! Almost 3days yau banji mommy ba’ wallahi fashewa zuciyata zatayi zaks! Rayuwata na barazana Zaks! Ji nike kmr ruhina ze fita daga jikina!” aeezad ya karashe Yana Zamowa daga kan kujera ya zauna dabau kan tiles , Nan da Nan se wasu zafafan hawaye suka wanke masa kumatuna , ya kasae kwallah tinda abun ya faru se yau yasamu yayi. Kawai se bulbula hawaye keyi daga cikin idanuwansa. Zaks dashima yakejin kmr ya fashe da kuka,ya zamo kasan tiles din ya sharema Aeezad hawaye da rigar jikin zaka din ta shadda fara sol. “Wallahi mommy, ni mommy kawai, Zaks mommy kawai nasani a rayuwata, ji nakeyi yanzu kamar nayi hauka? Dan Allah ka dafemin zuciyata karta fashe…” Aeezad ya kara fadi still Yana kukan me tsuma zuciya kamar karamin yaro, duk yadda kakaiga rashin imani dole ka tausaya masa a yanayin da yake ciki a hslin yanzu . se uban bugu zuciyarsa keyi, ya kamo hannun Zaks ya daura a kan saitin zuciyar tasa,yayi dana sanin dawowarsa garin kano yafi a kirga, se yaji daman ma ajiye aikin yayi kawai da wannan tashin hankalin da yake ciki. Duk dakiya irin ta Zaks seda yayi kwallah shima Amma ya share, yashiga lallabar Aeezad da ban Baki cikin kalaman kwantar da hankalin,Amma Ina Sam beji yariga yayi nisa , yayi nisan da baya sauraren kira. Kawai zaks yace su tashi su hau car su kama hanyar zuwa garin katsina wuraren karfe daya da Rabi. Suka hayo mota dreva yajasu yayinda motocin sojoji takai mota ashirin suka kamo hanyar zuwa garin katsina, a motar ma Aeezad Se kwallah yakeyi Yana sambatun Kiran sunan mommy, shi inde a kan Aunty nabeelah ne bashi da dauriya ko kadan, karamin yaro ba koye ma yafisa hkri da juriya a kan mommy.

A bangaren nabeelah washe garima haka ta wuni tsaye gashi ba baccin kirki tayi ba, ga jamaah makis a gidan an taru a Falon hajiya mommy kawayenta ne kawai cike taf da Falon se Na’eema da kawarta khady suna cikin manyan mata, sunzo zasu tashi hajiya naja’atu tace “Aah yarana ku zauna Ayi hirar daku ai kuma kawayenmu ne, duk wacce keda diyya mata ai kawayenta ne,,,” nande suka zauna dasu aketa hiraraki Amma basa Sako baki sbda hirar tafi karfinsu, domin kuwa manyan mata sub fisu San mazajensu, Rabin hirarsu duk aKan mazajensu ne, tsofaffin mata ne marasa tarbiya Kuma marasa alkunya… Basu da girma Sena jikkunansu, manyan mata ne kowacce ta kama kasa,wato sun kama gidajen mazajensu sun rike gam se yadda sukayi da maza, saboda shige shige da azabar shaye-shayen magungunan mata (Ko a cikin dubu macen dake Shan maganin mata ta fita daban wallahi)
Na’eema ta fara fuskarta tasawar cikin nabeelah tin jiya ta fara fahimta Amma se tasha ko tumbine kmr yadda uwarta tayi tsamnanin hakan,. To yau da nabeelah na serving dinsu a breakfast seta kuma ganin de Abu kmr ciki, se kallon Nabeelah de takeyi wadda keta faman boye cikin jikinta, Amma Ina baze boyu ba saboda tsananin girnansa, duk wanda ya kalleta a natse dole ya fahimci akwai ciki jikinta. ita kanta hajiya mommy Sebin Nabeelah takeyi da idanuwa Kawai so takeyi ta gaskata zarginta, Amma de abu ne gashinan baro-baro.tinda naeema ta daura idanuwanta a kan Cikin jikin nabeelah taji hantar cikinta ta kad’a. bayan sun gama break, hajiya mommy ta nufa dakinta tana amsa waya, na’eema ta biyota dakin ta taddata zaune gefen gado tana wayar da bokanta a kan kasuwancinta sbda so takeyi ta kara bude Wani shagon,yanzu shagunanta sunfi biyar, na shida takeso ta bude. Naeema ta karaso bedside zata zauna uwar ta dakatar da ita da hannu sbda inta zauna mata a bedside tana iya lalata mata drower din side din, gashi gado na manyan kudade. na’eema ta fahimci me take nufi Dan haka ta zauna kasan carpet tana hade rai, ita ta rasa me uwarta ta maidata kawai Dan tayi kibarnan shikenan, ita Sam mafa bata ganin kibar tata, duk Wannan nonuwan nata Dake reto bata gani, nonuwa him bra sede tase ta manya-manyan mata irin manyan cups dinnan Kai kace katon kan mutum za asa, inta cire bra ta ajiye ko uwarta inta gani tsorata takeyi, itade tasan yarta nada nonuwa Amma ba kmr na yanzu ba da tayi year kibar ban. Allah-Allah na’eema tadingayi uwarta ta gama wayar ta shaida mata abinda tagani Amma Abu yakici yaki cinyewa,. Seda Ta jima tana wayar kana ta ajiye wayar, Kuma bata tsaya jiran cewar naeemar ba ta tashi ta nufa hanyar fita tana fadin “bari inje part din baban Aeezad…” Ta fice ba tare data tsaya jinn me na’eema zatace ba. Haka na’eema ta tashi ta fice a dakin, ta nufa part dinta da aka ware mata a gidan da tunani a ranta tayi wanka ta kwanta, kawai so takeyi ta tabbatar da dagaske cikine jikin nabeelah, domin itade idanuwanta ciki suka ganar mata. A bangaren nabeelah a tsorace take Sbda ta fahimci an fara Gane da ciki jikinta Aiko a tsorace take. Da yamma misalin karfe hudu da Rabi,falon Hajiya mommy cike yake taf da jamaah kaf kawayenta be yanzuma se na’eema, khady bata Nan tana gidanta tazo dazu da azahar zuwa karfe uku ta tafi. Nabeelah keta zirga zirga a Falon tana jide musu manyan tray cike da kayayyakin lambu na Motsa baki, wato kayan fruits nau’ila daban daban. Kusan seda ta kawo tray tara wannan ne na taran shine wanda ta ajiyesa a kan table din gaban Hajiya mommy wadda suke zaune gata ga Hajiya naja’atu, se na’eema hajiya mommy din akasa a tsakiya. Bayan nabeelah ta ajiye tray din a kan table din su hajiya mommy, tayi-tayi ta tashi Amma ta gaza tashi, saboda kafarta data makale , seda ta tsugunna sannan ta ajiye tray din, kafarta ta rike gam, tayi tayi ta tashi ta kasa. Hajiya mommy da na’eema da hajiya naja’atu suka zubo mata ido. “Lafiya kika zauna kinata kallonmu kmr kinsamu TV,,,,” hajiya mommy ta fadi tana kallon Nabeelah a wulakance. Na’eema ma ta kureta da ido, the more tana kallanta se taji zuciyarta na azabar bugu. “Kafata ce ta rike…” Nabeelah ta fadi a tsorace, sbda yadda hajiya mommy ta mata mgnr, zabura tayi ta mike da duk karfinta da kyar tasamu ta tashi tana Nishi da haki, ji tayi kmr an rike mata kafar ta-ta cikin hanzarin ta bar Falon. Na’eema da hajiya mommy suka kalli juna Sbda cikin dasuka gani baro baro a jikin nabeelah. Hajiya naja’atu ma ta gani tin shekara jiya datazo tagani, Amma we tayi shiru a tunaninta sun sani, ynzu ma tanaso tace Wani Abu Amma tayi shiru. Na’eema ce tace “Mommy naga Wani abu….” Ta fadi yayinda zuciyarta ke bugu, kowa hankalinsa na can suna kallan TV Kuma suna hira Dana kusa dasu, Hajiya naja’atu Kam idanuwanta na kan TV. Hajiya mommy da itama zuciyarta ke mugun harbawa, ta kalli na’eema tanaso tayi Mgna Amma ta kasa magana. Sede ta tsinci bakinta dacewa “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” Itace kalmar dataketa maimaitawa , Apple ne a cikin bakinta Amma ta kasa hadiyewa sede ta fiddosa waje, ta ajiye a gefen tray din. Dai dai Nabeelah ta dawo falon da Wani tray din ta ajiyesa a dayan table din Wanda shi kadai ya rage ba’a ajiye tray din a Kai ba. Zuciyar Nabeelah se bugu takeyi, bugun da bata tabajin irinsa ba ta juya zata bar falon, cikin hanzari hajiya mommy ta mike ta kawo mata hijjabinta ta baya cikin zafin nama. nan ta dakatar da ita sbda shakurewar datayima wuyanta data RIKO mata hijjabi har kakarin amai tashiga yi, nan take hankalinta ya kara tashi bugun zuciyarta ya kara yawaita, seda d’an cikinta yayi wata iriyar mummunar harbawa, ta cire hijjabin jikinta kawai sbda neman shidewa da takeyi ta zube kasan kafafuwanta cikin dimauta da tashin hankali mara misaltuwa, bata ma hayyacinta Sam sbda tashin hankali, takai hannu ta rufe cikin jikinta, shi kawai take ji. Nan idanuwan kowa na falon ya dawo kansu dan ganin meke faruwa. hajiya naja’atu tayi hanzarin cewa “hajiya meye haka zaki shakurewa mace meciki wuya? Kuma tsohon ciki bayan da kyar kake numfashi in kanada tsohon ciki , aise kisa numfashinta ya daukee….” Hajiya naja’au batasan mugunta ita Sam. . Juyowa tayi ta kalli naeema wadda tini itama ta mike tsaye, a tare ita da naeema suka kalli hajiya naja’atu suka hada baki gun cewa “Ciki?” Naeema seda ta dafe kirjinta sbda wani azababben bugu da yakeyi. “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!” Itace kalmar da nabeelah ta fadi a zuciyarta, ubangiji ne kawai yasan a wani Hali take ciki so takeyi tayi kuka ko zata samu nutsuwa a zuciyarta amma ta kasa, yaude asirinta ya gama tonuwa, d’an cikinta kuwa se azababben motsi yakeyi, motsin dabe taba irinsa ba se yau, in kasa ido har ta saman rigar jikinta zakaga harbawarsa, takai hannu ta RIKO kasan cikinta hadi da rintse ido, ta sadakar yau, daman jiya kwana tayi muggan mafarkai, ta RIKO cikin jikinta gam, a ranta Adduah takeyi Allah yasa kome ze faru ya tsaya a kanta kawai kar a taba mata ciki, yau ta tabbar har kasheta hajiya mommy na iyayi,. “Cikin shege! Haba biri yayi Kama da mutum, amma cikin shege a family din Alhaji Sunusi,, tabdijan!” Hajiya mommy ya fadi afirgice, zuciyarta na tsananta bugu, ta rasa dalilin dayasa takejin tashin hankali a kan cikin jikin yarinyar. Sbda tashin hankali Nabeelah taji kmr zuciyarta ta fito fili, se azabar bugu takeyi, ta rasa Ina zatasa rayuwarta taji dadih, ji takeyi kamar zuciyarta zata buga, se Adduah takeyi, ta rasa ma Wacce Adduah zatayi sbda tashin hankali tayi kasa da kanta, danma ubangiji ya rufa mata asiri, ta basu baya . Hajiya rafiah ta karasa ta juyo ta da ita ta yadda zata fuskanceta sosai ta tabbatar tabbas ciki ne a jikin yarinyar.ta kurama cikin jikinta ido , idanuwan nabeelah na kasa, jikinta se kakkarwa yakeyi ta tallabo cikinta ta rike sosai kmr za a kwace mata shi, ita cikin kawai takeji batajin ta kanta, abinka da zuciyar uwa, cikin se mugun harbawa yakeyi, hankalin nabeelah inyafi dubi seda ya tashi. A kallo uku hajiya mommy ta tabbatar da ciki ne a jikin nabeelah kuma tsoho, ta tabbatar kuma hafsat nada masaniya a kan cikin, koma menene da bakinta zata fadi sbda ba karamar azaba zata mata ba yau. Naeema ta matso daf da nabeelah nan ta kara ganin cikin baro-baro, ta kuma dafe kirji, tashin hankalin data Shiga baze misaltuba, ta kumajn tsanar nabeelah sosai, haka itama hajiya mommy nan take ta kumajin tsanar nabeelah sosai. Kowa de ya zubo ido amma Sam basu fahimci meke faruwa ba. “A gidan uban wa kika samo ciki? A gidan wa kika samo cikin shege? Yau se kinci uwarki da uban ubanki, yau sekin gayamin cikin waye wannan jikinki? Inmates hafsat ce ke Miki kawalanci yau duk senaji komi…” Hajiya mommy ta fadi cikin tsawa da karad’i. Jikin nabeelah ya kuma daukar rawa, ta kumayin kasa da kanta, hajiya mommy ta kuma tambayarta cikin tsawa “Cikin waye ga jikinki?” Nabeelah ta kasa mgna se azabar bugu da kirjinta keyi ta lumshe idanuwanta gam gam. “ bake ake tambaya ba dan ubanki! Ni daman na tsaneka wlhi, ne kaunarki ma bansansa,,, yau sekin gaya mana wani dan iskan ne ya miki ciki? Zakiyi magana kose jikinki ya gaya miki…” naeema ta fadi jikinta na tsuma, ji takeyi kmr tayi ball da ita da cikin jikinta, inda Hali ma Tana iya zama ajalin cikin jikinta, kawai taji ta tsani cikin sosai. Nabeelah tayi shiru ta kasa cewa komi kawai se kukan zuci takeyi,jikinta se kara rawa yakeyi.. hajiya rafi’ah a hasale tace “Dan ubanki uban wa ya miki ciki? Shegiya karuwar banza, daga yau zamanki ya kare a nan gidannan, zakiyi magana ko baza kiyi mgna ba yar iska ta kama ciken shege ta rike, dan kutmar ubanki ki gayamin uban wa ya miki cikinnan na jikinki?” Nabeelah ta girgiza Kai ta kasa mgna kawai se yanzu taji kwallah masu zafi sun wanke mata fuska,. Hajiya rafi’ah ta dagota da hannu daya ta wanketa da uban marirrika guda hudu, a Dukkanin kuncinanta biyu. Zafin Marin ya shigeta amma ta kara RIKO cikinta sosai ta fashe da wani irin kuka mara hawaye na zallar tashin hankali, se ihun haka kawai takeyi. “Uban wa ya miki ciki?” Hajiya mommy ta kuma tambayarta, still tana rike da bayan wuyanta ta riketa gam ta bayan wuyanta. “Bazaki gaya mana uban wa ya miki ciki ba?” Cewar naeema hajiya rafi’ah ta Ansha da “jeki ciromin wayar injin wallahi yau nice ajalinki da cikin jikinki, Nima ai ba kaunarki nake ba, dan kutmar ubanki yau zan kasheki na kashe banza na kashe hofi ba abinda aka isa Amin…” naeema ta nufa kitchen domin ta ciro bulalar jikin babban injin nika dake kitchen din kasa, ba bata lokaci ta ciro belt din jikin injin nika ta dawo falon, da zabgegen belt din. har lokacin hajiya rafi’ah na rike da wuyan nabeelah ta baya, naeema ta miko mata belt din injin ta amsa, ganin tana shirin zubawa nabeelah uban belt din yasa hajiya naja’atu saurin tasowa ta iso ta rike bulalar kowa ya kasa dktar da hajiya rafi’ah, se kallo kawai sukeyi se yanzu suka fahimci meke faruwa wato cikin shege yarinyar tayi? Dukkaninsu azabtar da yan aikinsu sukeyi dan haka se cewa sukeyi “Gaskiya hajiya Karki sassauta mata dan kutmar ubanta, shaggu masu aiki yan iska mayun mata, duk fatsikaine …” sune muggan kalaman daketa fitowa daga bakunan mutanen. “Karki daketa da wannan bulalar pls hajiya, kodan Albarkacin cikin jikinta…koda na shegen ne ki kyaleta pls, Karki kashe ta in kika kasheta Allah vaze barki ba, iya wuya karka dau hakkin wani kwarai tsakaninka da ubangiji inyaga dama ze iya yafe maka…” Cewar hajiya naja’atu data rike bulalar belt din hannun hajiya rafi’ah. Fisge bulalar hajiya rafiah tayi tana fadin “wani albarkaci Cikin shege ke garesa? Dan kutmar ubanta yau ita da cikin shegen duk nice ajalinsu, ko Alhaji sunusi inya shigo falonnnan be isa ya hanani na kashe yarinyar nan ba, tin fa Tana karama take gidannan, so kk ta Batawa gidan mijina suna? Tayi kadan dan bura ubanta,,,” hajiya mommy ta karasheta tana sakin nabeelah daga rikon datayi mata, ta turesa kasan tile din falon ta hankadata seda ta mirgina ta buge kanta da kujera, Sam nabeelah taki yadda cikinta ya bugu hkn ne yasa ta bugu a kai, nan take se goshinta ya kumbura sbda ta bugu sosai abinka da farar fata batasan whla. Hajiya rafiah ta daga bulalar ta fara shimfidama nabeelah a jikinta da karfi, zafin bulalar ya shiga nabeelah ya ratsata tako ina ta fasa ihu cikin fitar hayyaci tana me basu hakuri. Amma ina ai kmr Tana zuga ta, naeema ta jawo wayar wuta, tashiga zubawa nabeelah, yazamana su biyu ke bugunta da naeema da hajiya mommy,. Hajiya naja’atu de taga abu yafi karfinta taja gefee, tana tausaya wa nabeelah, yan falon de se zugawa sukeyi. Ita kam nabeelah dukta rikice se basu hakuri takeyi dukta rikice Gashi ta kasa motsawa ta gudu dagan inda take, se ihu takeyi kawai Tana kakkare cikinta, nan naeema tafi bugu, ita kam hajiya mommy tako ina kawai Kai mata dukan takeyi da karfinta tana dukanta tana Haki sbda da karfi take bugunta. “In har bazaki gaya mana wani shege ya miki cikin shege ba, sena zama ajalinki wannan cikin sede ki haifo shegen cikin naki a kabari..,” Cewar hajiya mommy. Yan falon se kara se zugawa yakeyi cikin sigar gulma, hajiya naja’atu ita kadai ce keta aikin bada hakuri taki daddara, ita de gaskiya da sauran imani jikinta. Nan da nan falon ya rikice da hayaniya tako ina. Hajiya naeema da hajiya mommy se aikin dukan nabeelah sukeyi wadda keta ihu har yanzu, tini jikinta ya rufe da azabar zafi sbda sun faffasa mata jiki tako ina, har fuskarta ta fashe se jini kawai ke fita a fuskarta da wasu sassa a jikinta , rigar jikinta me Haske ce, dukta baci da jini,farar fatar nan tata tayi red sosai ba karamin duka suke mata ba, a zuciyar nabeelah ta kudirta ko kasheta zasuyi bazata gaya musu waye uban cikin ba, sbda ta tabbar in sukaji, tabbas wuta kawai zasu hada su sata ciki.

Hayaniya Alhaji sunusi yaji wanda shigowarsa gidan kenan, ya fito daga mota yaji hayaniya tayi yawa, cikin hanzari ya nufo part din hajiya rafi’ah sbda ya fahimci hayaniyar bata lafiya bace, yana shigowa falon yaga abinda ke faruwa, kokarin dakatar da hajiya rafiah yayi amma taki dakatawa tayi ma kmr bata San ya shigo falon ba, shi Sam bema kula dawa ake dukanba balle ya kula da cikin jikinta. Kawai de yaji hajiya nata fadin “Sekin gayamin ubanwa ya miki cikin nan na jikinki?” Sune kalaman dake fitowa daga bakin hajiyar, nabeelah kam tin Tana ihu ana ji har muryarta ta disashe yazamana tana ihun amma bame ji. daman kwance take kasan tiles din se kara rirrike cikin jikinta takeyi, har yanzu duk azabar da takeji ta kasa sakin cikin jikinta. Duk yadda Alhaji sunusi yaso
Ya dakatar dasu abu yaci tura , yayi-yayi ma ta tsaya ta masa bayani amma ina, seda kyar naeema ta tsaya ta masa bayani se yanzu ne ya kallah yaga ashe nabeelah ce ga uban cikin yayi Totso a jikinta, naeema na gama masa bayani suka ci gaba da bugunta kmr wadda tayi musu wani mummunar kisan kai, Kai kace Ubangijine ya aikosu su daketa. Alhaji sunusi ya zubawa nabeelah ido cikin mamaki, shide dan bayadda zeyi ne amma a ransa yaji bayason dukan da Ake mata, dukda lefin datayi babba ne amma shi a ransa beji ya tsaneta ba,. Duk yadda yaso ya dakatar dasu abu yaci tura, yan falon de se kallonsa sukeyi daman duk sun San shi Mijin tace ne Sam basuyi mamakin danya Hana matarsa taki hanuwa ba a bainannassi. Hajiya rafiah bata taba bawa Alhaji sunusi rai ba kmr yau ganin yadda yayi-yayi ya hanata abinda takeyi ta masa bansa a karshe ma sede ta daka masa tsawa tace “Ba ruwanka kaji kou!! In bazaka iya gani ba ka fita!” Yaji zafin yadda ta masa hakan a gaban kawayenta, inda sabo yaci acee ya Saba Tasha masa hakan yafi a kirga a cikin mutane, ba kmr ma kawayenta, amma na yau ya masa zafi sosai.

 

 

Paid book ne 1k 08101626484

NAMIJIN ZUMA

Back to top button