Hausa NovelsMatan Ko Mazan Book 1

Matan Ko Mazan Book 1 Page 31

Sponsored Links

31
Waiwaye baya kadan!
5:00 daidai jirgin su Hadiza ya sauka a kano, fitowa tayi ahankali gabanta sai faduwa yake da maganan Baba, hakanan ta tare taxi 5k yakaita harchan Dakata dan anan gidan su yake, wani madaidaicin gidane yanada gate haka baki, gidan daidai na rufin asiri, sauka tayi tabiya kudi tajuyo gabanta still na bugawa tabude gate tashiga gidansu, kayan dakinta data fara gani a tsakar gidan yasa kawai taji wani irin chills na sanyi na shiga jikinta kawai ta tsaya chak tana kallon kayan, wani abu taji ya tsaya mata awuya amman ta daure ta danne tadauke idanunta dagakan kayan tafara tafiya compund nasu nada fadi gawata hadaddiyar Camry golden dake pake a compound din, babban flat ne guda daya agidan sai bq tabaya daga labule akayi aka fito Rabi ce rikeda kwano a hannunta ganin Hadiza yasa tace “Anty Hadiza, Mama Anty Hadiza ta iso” ijiye kwanon tayi da gudu tai wajen Hadiza sai kawai ta rungumeta tace “Anty Hadizaaaa” fitowa Hafsa tayi da gudu da babynta ma a hannunta amman ta ijiyeta tazo da gudu sai kawai suka rungumeta, Hadiza jitayi jikinta yamata wani kalan sanyi kafafunta kawai sukahau tankwashewa da kansu daidai Anty Jams da Mama nafitowa daga dakin, kallo daya Mama tamata tace “ku shigo da ita daki” kakkamata sukayi Hadiza takalli Maman nata dake mata kallo irin kallon haushinta takeji sosai din nan tace “kin sami abinda kikeso ai shikenan, ga gidan ubanki nan saiki zauna, ku wuce ku kaita ciki nace” Mama tai maganan with so much annoyance Anty Jams tayi shiru tana kallon Hadizan wacce idanunta kadai zaka kalla ta baka tausayi dan sunyi zuru zuru ta wajigu, wlh dudda tana fushi da Hadizan amman tabata tausayi matuka kaman tamata kuka, wucewa da ita ciki sukayi zama tayi a falon Rabi ta kawo mata ruwa da gudu kadan tasha kawai ta ijiye Mama da ranta ke masifar abace dan ba dadi auren yarka ya mutu wlh babu, balle kuma auren da kasan diyar naka ne at fault sai bakın cikin yazaman maka guda biyu, gana mutuwar aure, gana yar cikin nakane taja, no mother wish for mutuwan auren diyarta.
Sallama akayi wani magidancin mutum Ustaz sosai fa yana sanye da babban kaya da hula akanshi mai rawani yashigo gidan da wani mai kama dashi wanda zaka gane kaninshi ne, shiga falon sukayi Hadiza tasauke kanta kasa dasauri ahankali tace “ina wuni Baba” wucewa Baba yayi ya zauna kaninshi a gefenshi ya zubama Hadiza idanu kana ganinshi kasan yanada dan zafi irin ba mutum mai sanyi bane, babu wani bata lokaci ya nuna tundaga kan Jamila, Mama har zuwa kan Hafsatu yace “dago kanki ki kalli yan uwan ki kinsan mesa dukansu ke gidan nan yau”? Kasa dago kanta Hadiza tayi gabanta na faduwa sosai dan tana shakkan mahaifinta matuka tace “a’a Baba” cikin tsananin fada yace “sabida dukansu harda mahaifiyanki sukasa hannu suka tayaki kashe auren ki! Akanme kina gidan mijinki shekara da shekaru dabi’un banza kike zubawa banda labari?” Yayi maganan da fushi yana daga murya kowa ya sauke kanshi kasa cikinsu yace “akan me? Uhn uhn uhmmm Amadu kwanakin baya da diyar nan tai rashin lafiya cemin akayi rashin lafiya ne kawai, mijinta yace duk suje abujan yaturawa Jamila kudin jirgi sabida ciwon zuciya likitoci sunce tana bukatan yan uwan ta abinda aka gayamini ke nan, anyi haka ko ba’ayi haka ba”? Baba ya tambayi Mama data gyadamai jiki asanyaye, Baba da ranshi ke tafarfasa yace “saida sakon bawan Allahn nan Nura ya shigo wayana yace Baba namaka laifi na mari Hadiza abisa kuskuren fushi dakuma zafin zuciya wanda nai nadaman hakan, ta shigar dani kotu anbi mata hakkinta, Baba kayakuri na saki Hadiza saki nabiyu yau, yoo banmasan sanda akai na dayan ba, amman Mahaifiyarta da Yayarta da kannenta sunsan komi sukai shiru suna kallona saida na sami Maman na titsiyeta take gayamini gashi, gashi, gashi, ai yanzu gatanan tadawo gida kun huta”? Yayi maganan yana kallon Maman Hadiza yana bubbuga kafa akasa yana tafarfasa yana nuna musu Hadiza da hannu. Cikeda tsantsan adama da danasani Maman tace “Malam kayakuri, na amince namaka laifi, amman ka fahimce ni, iyaye maza sunada zafi barinma kai saisa zaka gani yawanci iyaye mata kan boye laifin yaransu daga mahaifan su gudun bacin rai da fushi, sa’an nan na dauka fadan damuke mata dani da Jamila zataji ta dauka basai ka shigo zancen ba, kaga kuma ada bahaka Hadizan takema komawanta jarababben shedanin garin nan ne yasa taje tahadu da shedanun ciki itama ta rikida tazama daya, amman kayakuri Malam, na dauki kuskure na hakan bazata kara faruwa ba, kayakuri Malam” “hakuri bayan kun kaso mata auren?” Baba yayi ihu yana hargowa dayasa Maman Hadiza ta runtse ido cikeda jin dacin maganan shi, Baba yace “Amadu Allah shaidane kaima shaidane yarana nabasu tarbiyan boko da islamiyya, dukkan su nan har ita Hadizan babu wacce batai sauka ba, nabasu tarbiya, sunsan Al,Qur’an, Tajweed, Tafseer, Ahalari, bulugul maram, umdatul Ahkam, zuhudu, fikihu, not to mention others, kai ni nan dakaina saida na zauna na koyar da yaran nan kap dinsu littafin siffofin mar’atul saliha, na killace su nakuma tabbatar da na aura musu mazaje nagari amman mahaifiyar su kullum boye mini zancen yarana take” Maman Hadiza tace “Malam kayakuri” dan shiru Baba yayi saikuma ya kalli Hadiza yace “kalleni ke kuma dan kaniyanki” ahankali Hadiza tadago kanta gabanta nafaduwa dum dum dum sosai takalli Baba, da hannu ya nuna kanshi yace “tunda na haifeki kin taba ganin Mahaifiyarki tamin ihu?” Girgizamai kai Hadiza tayi ahankali, cikin tsananin fada da kumfan baki Baba yace “kintaba ganin ta gasamin magana koko kin taba ganin ta rainamin wayau, ke kin taba ganin Mamanku tace nine zan muku girki yau ko na shiryaku zuwa makaranta koko kintaba ganin ta zauna tace ita tagaji da aikace aikacen gidana yau nine zanyi bani amsa” Baba yabuga hannun kujera, girgizamai kai Hadiza tayi, cikin wani kalan fushi Baba na kallon Hadizan dake girgizamai kai yawani zabura yatashi daga kan kujera kaman zai daketa yace “kin taba ganin mahaifiyarku ta daukowa Gwaggo yan sanda kafin ta rasu”? Tashi Hadiza tayi da gudu tawuce bayan Mama tariketa gam jikinta narawa gani take kaman dukanta zaiyi, akwai wani kalan haiba da kwarjini da mahaifinsu kedashi kodanshi Malami ne oho, amman baki isa ki kalli idanun Baba kiyi hayagaga agabanshi ba, babansu baida wasa ko kadan, sun taso shiba uba mai wasa da yaranshi bane saisa tsoronshi ke jikinsu tun suna yara, tsakaninsu dashi yakoya musu karatu yabasu abinda suke bukata but irin wasan nan kaman yanda Nura keyi dasu Amali ina Baban su baya wannan at all.

Dasauri Amadu yakama Baba yace “Yaya dan Allah kayakuri kaga Hadiza ba yarinya bace dazaka daka ba, magana kadaima ya isheta” ture Amadu Baba yayi yace “Amadu kasan hukuncin wanda yaci mutuncin iyaye kuwa? Matan nan ina kwanakin baya kafin taje Abujan saida nidakai mukaje har gidanta muka maidata, Hadiza matan dake ciwo kusan kowa yasani hawan jini da ciwon sugar sun sata gaba, ke har Mahaifiyanki da Jamila suma sunje sun gaidata, amman kika zagi Matar nan, kuma sabida rashin da’a kice bazata sauna gidanki ba, sannan ki dauko mata yansanda, tunda muka haifoki mun taba tsinemiki ko muntaba miki bakine dan wannan dabi’un tsinannun yara kikeyi wayanda iyayensu suka yafesu su shiga duniya su adddabi jama’a, muntaba tsine miki ne Hadiza”? Hawaye ne suka fito daga idanun Hadiza masu zafi. Maganganun Baba na mugun tabata dudda bawai tsinuwa yake mata ba but yanda yaketa tsinuwa kalman sun tsinemata ne har cikin kwanyanta takejin kalman, Baba ya fizge kanshi yanuna Amadu yace “ka kara rikeni saina kwada maka mari” yazo wajen Mama kawai ya fizgo Hadiza daga bayanta dasauri daga Mama harsu Anty Jams zasu saka baki Baba yace “Wlh babu ruwanku, duk Wanda yace tak sainayi mummunar sabamai” yarike hannayen Hadiza gam takasa kwacewa ido cikin ido dan abinda tama Hajiya ya girgizashi da aka fadamai yau, yace “Hadiza kin isa, kinkai matsayin yau, kawai so nake ki nunamin kin isan, da karfin ikonki da mulkinki dan haka yima ni ubanki duka” yakama hannayen Hadiza yakai saman fuskanshi zai mari kanshi da hannunta, da gudu Hadiza ta dunkule hannunta tawani kalan fashe da kukan da tuntuni take rikewa tace “Babaaa” cikin tsananin fushi Baba yace “Wlh, wlh, kinji na rantse miki saikin dakeni yau dan abinda kikama mahaifiyar mijinki yamafi dukan nan dazakimini ni mahaifinki girma Khadija, yafishi sau dubun dubara, uwa zaki daukoma yan sanda, ki kirata dakikiya, matan nan ta girmeni ni mahaifinki amman comfortably kika zageta, sannan saida kikasa tafita tabar gidan dan da ta tsuganna ta haifo, mareni! Dakeni nace me kike jira yimin duka” yanda Hadiza ke kuka ta dunkule hannunta gangam taki bude palm din kar Baba ya mari kanshi saiya baka mamaki, Baba yace “ai wlh baki isaba kinyi abinda yafi wannan yanzu kuma kice bazaki iya dukana ba, I said beat me” azuciye Baba yakai dunkulallen hannun Hadizan ya buga afuskanshi da hannun da kyau fa bawai duka kadan ba, wani kalan ihuuu Hadiza ta tsandala arazane irin tayi wani babban tabooo dinnan ta daki mahaifinta ta fizge hannunta dagana Baba daya sassauta rikon yana kallon reaction mata ta tsugunna da gudu tana wani kalan kuka tana goge hannayenta da gudu ajikinta irin ka rude din nan kayi laifi da hannunka kana purifying nasu immediately, Baba ya tsaya chak yana kallonta idanunshi sunyi jaaaa cikin wani kalan murya mai sanyi kaman kankara yace “how do you feel yanzu dakika dakeni ni mahaifinki? How Khadija”? Yayi tambayan kaman kankara, kasa magana Hadiza tayi sai goge hannun take tana kuka abun yay shaking nata ainun, Baba ya jinjina kai ya nuna kofa yace “Khadija kinma that poor old sick woman abinda yafi dukan nan dakikamin just now, cus ni mahaifinki just a physical punch kikamin but ita kin mata emotional, mental and even physical one din” yayi shiru sai kawai ya juya yakoma kan kujera ya zauna tareda daura hannayenshi akan fuskanshi jikin kowa yayi sanyi har ita Hadizan ganin mahaifinta na kuka, kowa was just cold a falon, fadan Baba ya taba jikin kowa, Hadiza jitayi kaman Allah yarigama ya jefata a wutan jahannama wannan kukan da dukan datama mahaifinta.
Yadan dade ahaka kafin yazare hannunshi ya goge idanunshi tass dasukai ja yace “kaico! Wallahi Billahi duk wanda ya wulakanta iyaye baya samin karshe mai kyau! Khadija yau na zubar da hawaye akanki sabida nariga na sani ne tabbas sai anwa diyata, diyar cikina abinda tayi ma wasu kama tudini tudan Hadiza!” Har wani shock Hadiza taji ajikinta maganan Baba ya shigeta, Baba yace “ana wani zamani da mata da yawa basason iyayen mazajen dasuke aure sun tsanesu, sun maidasu kaman wasu makiyansu, shi soyayya ba dole bane amman kyautatawa da sauke hakki dole ne! Yau koda bakason wani kada ka cutarda shi, da Hajiya bata haifa Nura ba dazaki sami Nura ki aura?” Baba yamata tambayan tasauke kanta kasa ahankali, shiru yayi yace “Khadijahh Annabi SAW yace Man tashabbaha bi qaumin fahuwa minhum, that whoever imitates others, he will be from amongst them duk wanda yaso wasu to yana tare dasu, kinje Abuja kin kaunaci dabi’un da mutanen dakika samu awajen sunayi to ranan gobe kiyama tare Allah zai tadaku” Baba yayi shiru yana kallonta chan yace “aure bautane, Allah yafadi acikin Al Qur’ani mai girma;
“وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ”

“Wama Khalaqtul Jinna Wal Insa Illa liya`a buduun, And I have not created the jinn and mankind except that they should worship Me, Ban halicci mutum da Aljan ba saidan su bauta mini. Hadiza part of bautan Allah shine aure amman kikai auren but bakiyiba, kikaje kinama ma mijinki abubuwa daban daban”
Baba yasakeyin shiru kafin yace “Nura mutum ne, dan idan nine matana ta zagi Gwaggo na kota dauko mata dan sanda basaki daya zan mataba aurena da ita har abada mungama na hakura, kinsan waye iyaye? Kinsan girman iyaye da darajan su? Fushin Allah yana daga cikin fushin iyaye hakama yardansa, idan iyayenka suka yarda dakai Allah ma ya yarda dakai, Aljanna Nura na karkashin kafan iyayenshi, bakiso ya rabu da su lafiya? Sabida kin tsani mahaifiyarshi karya kawota gidanki? Karya nema mata magani who are you?” Baba yasake shiru yace “mari ba kyau ba kyau ba kyau! Ke kinma bawan Allahn nan kuskuren dayafi na mari bai miki ba, kuma ya yafemiki, zaman aure zomu zauna zomu sabane, kowa na kuskure a duniya, akanme bazaki iya yafemai kuskure dayan nan ba tak! Kika makashi akotu kin riga kinma sunanshi tabo har karshen duniya!”
Baba yasake shiru na kusan 5min Chan yace “Abu biyu zuwa uku zan gayamiki, abinda kikayi kunya bazai taba barina na nemo Nura na muku sulhu ba bani acikin zancen nan idan yazo Alhamdulilah idan baizo bama Alhamdulillah!” Baba yayi shiru chan yace “abu nabiyu shine idan ada kin kada ganyenki kin tashi sama kin baza reshe bada sanina ba yanzu na shigo lamarin nakuma san meke faruwa bazan taba barinki ki koma Abuja ba saidai idan mijinki ne yazo ya daukeki daga gidan nan nawa ya maidaki!” Dasauri Hadiza takalli Baba dan business dinta kawai take tunani yace “daga rana irin tayau ko gaban gate na gidan nan bazaki kara zuwa ba idan kinga kin fita daga gidan to kin gama idda ne!” Hadiza takara kallon Baba gabanta na faduwa yace “kin riga kin nunama duniya gabaki daya bakida tarbiya, iyayenki basu koyamik, sannan ke gantalalla ve kuma tijararriya ba? To remember this shi karatu is never too late duk girmanka kuwa dan haka zaman gidan nan tarbiya ni mahaifinki zan koya miki da kaina! Dakaina Hadiza dan har mahaifiyar ku ban yarda da itaba yanzu” Baba ya sauke ijiyan zuciya yace “kinga duka abubuwan da bakiyi agidan mijinki ba starting from gobe dasafe kin farashi kennan!” yanda kirjin Hadiza ke bugawa zaka sauka gangan ne ake bugawa aciki, Baba yace “girki na safe, na rana dana dare na kanki, sharan tsakar gidan nan da gyaran gida, wankin kayan mahaifiyarki nawama sa’a kikaci wanki da guga nake bayarwa, wanke wanke da wankin bayi, bayan haka kullum ni da ke ina dawowa daga sallan asubar kullum ranan duniya zan karantan dake littatafai daga Alifu ba’un zan fara miki dan naga kaman kin sami memory loss duka kwakwalwanki ya shafe, komi da kika iya da yabace Allah yasama kin iya karanta fatiha yanzu” Baba yayi maganan da kakkausan murya sannan ya nuna Hadiza da yatsa yana kada kafa strictly yace “kinga dokokin nan dana shimfidamiki idan kika karya daidai da guda acikin su na sallamaki daga yaran dana haifa kenan aduniya” azuciye Baba ya tashi yana gyara Babban Riga shi yace “Amadu tashi mutafi masallaci” baima jiran Amadun ba yafice ranshi abace, Hadiza tafashe dawani kalan kuka sosai mai tsuma jiki, Anty Jams ba karamin dadin hukuncin baba taji ba shine daidai da Hadiza dan tana ganin ma maybe taurin kan Baba Hadizan ta dauko, ai zaici kaniyanta yanzu juyawa tayi kawai tace “Mama natafi gobe zanzo kuma ku wuce kutafi” tama su Rabi’a magana kozata lallashi Hadiza not today let her feel the gravity of mistake datai commiting tukunna before tamata magana but tabata tausayi kuka takeji but bataso tayi yanzu saita fita tashiga mota she pity her sister sosai.

I cried for Hadiza today😭
But ya kukaga hukuncin mahaifinta???
Yayi daidai ko yayi tsauri??
https://vm.tiktok.com/ZMjpou6Ex/💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣2️⃣
Kuna neman AFFORDABLE KAYAN BACCI DA BREZIYU, hohohooo gafa Qawxars nan💃 ku riketa gam gam and thank me later🥰

Are you looking for where to get affordable and quality sleepwear and underwear from the uk? Look no further @qawxarscollection got you covered we have alluring and beautiful bras padded and non padded, matching sets, sleep dresses, pj’s, & gift packages. What are you waiting for? Check us out on Instagram https://instagram.com/qawxarscollection?igshid=OGQ5ZDc2ODk2ZA==
Or click to send a dm
wa.me/+2348032022128

 

Back to top button