Noor Al Hayat 14
By khaleesat Haiydar_đâđ»
14âŠ..
Tsayawa yyi yana kallonta ta shiga parlorn sannan shima ya shiga, kan kujera ta nufa ta xauna, ya karaso bayan ya kulle kofar ya ajiye ledan hannunsa kan center table, sannan ya shiga daki, jinginar da kai tayi da kujera tayi xurfi cikin tunanin da take taji yana kiranta, dagowa tayi da sauri ta gansa tsaye gefenta ya rungume hannunsa, a hankali yace âNa hada maki bathing water a bathroomâ sunkuyar da kai tayi, ta mike yana gaba ta bi bayansa xuwa dakin, towel ya dauko ya mika mata, ta karba murya can kasa tace âThank youâ ya juya ya fita dakin, da mouth wash na Listerine ta wanke bakinta, tayi wanka da shower gel, sai kusan bayan minti talatin ta fito daga bayin, bayan tayi ta tsayuwa bakin kofar bathroom din tana tunanin fitowa da towel, bbu kowa dakin sai Hijab dinta da ta gani kan gado, mamaki ya kama ta tayi ta kallon Hijab din, karasawa tayi ta dauka ta koma bathroom din, wanke kayan da ta cire tayi sannan ta sa hijab din ta fito da kayan da ta wanke a bucket, xaune ta gansa a parlor yana rike da remote, kallo daya yyi mata ya dauke kai har ta shigo parlorn, yace âWhy did u wash, u still under medicationâ bata ce komi ba, yace âNa bude maki kofarâŠ.â Tace âDa gaske?â Yace âEhh, ki tafi ki shiryaâ murya can kasa tace âNagodeâ sannan ta wuce tana rike da Hijab din. Sai da tayi sllh snn ta wanke masa towel din a bayinta ta fito ta shirya ta tafi shanya kayan da ta wanke da towel din nasa, kwanciya tayi daki bayan ta gama lkci daya bacci ya dauketa. A hankali ta bude ido jin kamar ana tashinta, ta mike da sauri tana kallon sa, yace âIâve been knocking and calling since, butâŠ. Taso mu je ki ci abinciâ ta girgixa kai tace âAm not hungry bacci nake jiâ yace âNoo, baki ci komai ba yau, kuma kinga xa ki sha magani, you have to take somethingâŠ.â Daga haka ya mike yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ta bi sa suka fita parlor, xuba mata abincin yyi ya mika mata ta karba ta fara ci, wayarsa yake ta dannawa har ta ajiye abincin tana yamutsa fuska tace âNa koshi faâ ya kalli abincin sannan ya dau ledan maganin ya ballar mata drugs din ya taso ya mika mata da goran ruwa ta karba, ta sha maganin tana kallon sa yace âAllah ya sauwakeâ bata iya ta ce komai ba, yace âTo ki je ki kwanta, sleep without thought plssâ ta gyada masa kai sannan ta tashi ta shiga daki. Bata tashi ba sai kusan biyu da rabi na rana, ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta sake kwanciya. Knocking kofar dakin taji ana yi cikin bacci, ta mike xaune ta sa hijab sannan ta bude kofar, yana tsaye bakin kofar, yace âHave u prayed zuhur?â Ta gyada masa kai, yace âAbinci faâ tace âI am not hungryâ ya girgixa kai yace âYou are, fito ga abinci na kawo maki sai ki sha maganiâ daga haka ya juya ya bar wajen, bin sa tayi, yana daga tsaye ya nuna mata abincin kan table, ta karasa ta dauka, tuwon shinkafa ne da miyar vegetable ta gani da ta bude, ta daga kai tana kallon sa, ya daga kafada yace âYea, a frnd of mine ce ta yiâŠâ Tace âKai baxa ka ci ba?â Ya girgixa kai da sauri yace âNoo I donât take heavy foods, I donât take swallowâ murmushi tayi ta dauke kai, ya shafa kai yace âSbda ke na karboâ tace âToh ngdâ yace âNo thanksâ plate taje ta dauko a kitchen ta debi abincin, shi dai har lkcn yana tsaye, ta kallesa a hankali tace âBaxa ka xauna baâ shiru ya dâan yi, sai kuma ya karaso ya xauna kan kujerar dake kallon nata yace âSo u careâ bata ce komai ba ita dai, a hankali ta dinga cin tuwon, duk lkcn da ta daga kai sai sun hada ido, daga karshe bata sake yrda ta dago ba har ta gama cin tuwon ta dau magani ta sha, sai a snn ta sake kallon sa taga kallonta yake still, hade rai tayi ta dauke kai, yyi murmushi yace âWho is Aliyu?â Kallon sa tayi da sauri, kamar yanda shi ma yake kallonta har lkcn, can ta tsuke fuska tace âBan gane baâ bai sake cewa komai, bayan kusan minti biyar yace âdonât pretend⊠Is he ur Husband?â xuciyarta na bugawa tace âNoooâ Yana mata wani kallo yace âUr Ex Husband?â Hade rai tayi sosai cike da masifa tace âNooooâ sai kuma ta mike tana masa wani kallo tace âI know nothing about what u are sayingâ ya dâan yi murmushi yace âYou passed out yesterday at the hospital with the name Aliyu in ur Mouthâ shiru tayi tana kallon sa a sanyaye, lkci daya hawaye ya cika idonta, can ta juya ta bar masa parlorn da sauri, kiran ta ya dinga yi har ta shige daki ta xauna kasa ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka, bin ta yyi cikin dakin, ya karaso gabanta ya durkusa a hankali yace âOhk, I am very sorry Khadijah, may be I shouldnât have say anything about that, but dole xan yi magana, Billah da xan ga Aliyun nan⊠Sai na sa ya dâan dani abin da kike ji, I guess he broke ur heart kuma yake kokarin dawowa rayuwar ki yanxu saboda may be selfish reason dinsa, he will regret that duk ranan da muka hadu face to faceâŠ. I vow!â ita dai bata ce masa komai ba sai kukan da take, duk jikinta yyi mugun sanyi, mikewa yyi ya fita dakin. Har dare khaleel bai shigo ba, tun da tayi magrib take hade abubuwan da tasan xa ta kai gida, don bata jin xata kara kwana a kasar, gaba daya xaman kasar da karatun ya fice mata a kai, hawaye kawai take duk jikinta a sanyaye, Sudais has always wanted her to be a doctor, ta xo ta samu kan ta a bangaren pharmacy, wanda a yanxu bata jin ma xata ci gaba, domin kuwa ta hakura da karatun, may be some other time she wil be d doctor Sudais wants her to be, to ko ta xama likitan ma what is that adding to her life, wanda take son yi dominsa ya tafi ya bar ta a lokacin ta fi bukatarsa a rayuwarta, baxa ta ce ya gujeta ba, but whatâs the difference? Kusan duk dayaâŠ. Ta share hawayen idonta ta fito parlor a sanyaye, tsaye tayi tana kallon Khaleel da shigowarsa knn a hankali ta sauke idonta kasa wasu sabbin hawayen na xubo mata, ya karaso kusa da ita yace âIna xa ki?â Ta juya masa baya tana kkrin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, a hankali yace âKhadijahâ cikin rawar murya tace âAm going back to Nigeriaâ ya juyo da ita ya xaunar gefen kujera yana kallonta, ya bar ta tayi kukan me isarta, ta hade kai da gwiwa tana sauke ajiyar xuciya, cikin sanyin murya yace âTell me about you Khadijahâ Ta dago tan kallon sa hawaye na sakko mata, sai dai kuma tayi ma kanta alkawarin bayan Sudais bbu wanda xai ji ita wacece, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, yace âI still donât deserve to know you koh?â Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen dake sakko mata, a ranta kuwa tunani take anya xata iya fadi ma Khaleel ita wacece kuwa, a hankali ta xamo kasa daga xaunen da take kan kujera, ya sakko kâasan shima yana kallon kwayar idanuwanta da suka rine, kife kanta tayi da kujera cikin sanyin murya tace âKa daina kallona da idon kaâ ya dâan yi jim sai kuma yace âWhy?â A hankli tace âBana son irin suâ murmushi yayi yace âDa gaskeâ taki cewa komai, a hankali yace âToh na daina kallon kiâ dagowa tayi suka kara hada ido tayi saurin mayar da kanta jikin kujera, dariya ta basa sai dai bai yi ba ya shafa kansa yana murmushi, murya can kasa yace âAm all ears Khadijahâ ta dago kanta tana wasa da dogayen yatsun ta tace âOhkâŠ..â Wayarsa ya da ya fara ring ya ciro aljihunsa, ta kalli screen din kamar yanda shi ma yake kallo, Jawaheer ne jikin screen din⊠Yyi silencing wayar ya ajiye a hankali, Tsura ma lallausan carpet din da suke xaune kai ido tayi ko kiftawa babu, cikin sanyayyan muryarta tace âI am an only child⊠I was raised from a very rich home, I was raised by only my Dad don kuwa ina da shekara uku kachal a duniya mahaifiyata ta rasuâŠ.â Dâan murmushi tayi wasu sabbin hawaye na taruwa idonta tana kallon Khaleel da ya kafeta da nasa idonâŠ.
Who is Khadijah?