Hausa NovelsHausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 47

Sponsored Links

47…..

Ba karamin gudu Aeezad yasa dreva dinsa ke shararawa ba a kan shantalelen ti-tin daga Kano zuwa katsina,. Duka motocin tawagarsa kawai gudu sukeyi a kan Ti-Ti. gabaki daya Aeezad Gani yakeyi ma Kmr basa sauri, yakagu yaga mommynsa, gashi zuciyarsa nata azalzalarsa a kanta, a jikinsa yaji kawai Wani Abu na samunta, ji yayi har jikinsa da komi na jikinsa ciwo yake masa, zuciyarsa se uban Zababbaka takeyi ya rasa dalilin hakan, cikin mummunan baccin Rai ya tsinci kansa mara misaltuwa, kawai kuka yakeso yayi sbda yaji sassaucin matsifar dake zuciyarsa a kanta, ji yakeyi daga zuciyarsa zuwa gangar jikinsa zafi rakayau Kmr ana zuba masa rushi. “Ya hayyu ya kayyum,,,!” itace kalmar data fito daga bakinsa se Nishi yakeyi shi kadai yasan a Wani hali yake ciki. Zaks dake gefensa se Aikin kwantar masa da hankali yakeyi Yana fada masa kalamai masu sanyi Amma Ina be saurarensa sema yaji ya cika masa kunne Yana Neman hada masa tunaninsa biyu, shi Kuma yafi bukatar yayi tunani guda daya Rak a halin da yake ciki wato tunanin mommynsa shine ne abincin ruhinsa. Dasuka fara shigowa katsina suka tadda uban hold of, Aeezad ji yakeyi kmr ya sauka ya taka Zuwa gidan Aunty hafsat, harya fara kokarin sauka zaks ya rikesa da kyar ya hkra., sojojinsu suka sauka suka tsayar da kowa su suka wuce.
Karfe biyar dai-dai motocinsu sukayi packing a farfajiyar gidan Aunty hafsat, a tafkeken packing space din dake gidan.
Big hajiya da Aunty hafsat dasuke zaune jingum jingum a falon har yanzu ba Wanda yasawa cikinsa abinci har kwara big hajiya tasamu tasha tea, duk matsifar baccinta, yanzu baccin ya xamar ma big hajiya sede barawo. aunty hafsat taji karar shigowar motoci Cikin gidan, a matukar razane ta mike , ta lega Nan taga fitowar AEEEZAD daga mota, Daman tin kafin ta leka jikinta ya bata shine. “na bani yauni nashiga uku! Ina zansa rayuwata!” itace kalmar data fito daga bakin aunty hafsat yayinda zanin atamfar dake cikinta ke niyar faduwa ta rikosa da kyar, daura zaninma ta kasa seda kyar se fama takeyi ta daurasa Amma Yana subucewa Sbda tashin hnkli , inside zuciyarta se azabar lugude kawai takeyi,ta tabbatar in Aeezad yazo bega Aunty nabeelah ba ita ze bawa lefi, big hajiya ta bata lefi ma Ina maga uban gayyar. “Meya faru kk fadin kin shiga uku? Me kika gano? Ko wani Abun ne yasamu Cikin jikin yarinyar?” big hajiya dake zaune ta mike tsaye cikib tashin hankali take jeroma hafsat tambayoyin. “Aee…..za…d….ne,,,ya,,,da,,,wo”” aunty hafsat ta Fadi bakinta na rawa, ta cire dankwalin atamfa dake kanta ta ajiye kasa, azabar zafi da tiriri kawai taji brain dinta nayi, ta rasa Ina zatasa rayuwarta se Fadi takeyi ta bani, Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un Kam ta fadeta yafi a kirga, bata kai wata take daukat wata. Big hajiya a ranta taji dadin dawowar Aeezad, waNi farin ciki ya lullubeta, Daman kashe wuta seda ruwa, in ruwan beyi ba a Kasheta da wuta, Wani lokaci lalaman baya kashe bala’i, wuta seda wuta. Aunty hafsat na daga tsaye cikin mummunar fargaba da tashin hankali, big hajiya ma na tsaye,. Ya turo kofar falon da karfi kmr ze cireta, seda Aunty hafsat ta Kuma tsorata taci uwa zuciyarta zata buga, Nan take Wani zazzabi ya lullubeta, ta kama rawar d’ari, ko a iya Haka tashiga Azaba zazzabin da takeji bata taba jin irinsa ba se Yau. ya Sako kafafuwansa Wanda suke sanye da farin cilifas irin na Yan hutu, Sam ma besan silifas bane a kafarsa, a mota ya cire takalmin Daya sako, ya Saka slifas din ba tare ma Daya Sani ba. Zaks ke biye Dashi a baya. Idanuwansa suka sauka a kan Aunty hafsat, da big Hajiya dasuke tsaitsaye, tini ya hango uban rawar da jikin Aunty hafsat keyi, a fuskokinsu ya fahimci ba lafiya ga gidan yayi Wani silent kmr gidan mutuwa TV a kashe. “Ina mommy? Meya samu mommyna? A Wani hali momnyna take ciki? Meyasa kika kashe wayarki maman noor? Meyasa kika koma kika kashe wayar big hajiya Kuma ta mommy ma a kashe? Dan girman Allah Ayi gaggawan gayamin a Wani hali farin cikina na duniya take ciki Dan Allah na rokeku? Mommy na cikin wani hali inaji a zuciyata…a gayamin meya sameta? Ina take inaso in ganta? Jikina na bani bata gidannan ko ta gudu ne zuwa kasarsu? Dan Allah a gayamin” Aeezad ya jefo musu wannan tambayoyin masu rikita zuciyar Aunty hafsat, Hadi da magiya. , Nan take zuciyar Aunty hafsat tayi Wani mummunan bugu,. “Wayyoh na bani
Na mutu yau ni hafsat!” ta fadi a zuciyarta. Big hajiya ce ta kwashe Labarin komi ta gaya masa. Wani jiri luuuuuuuu ya nemi daukar gogan,seda Zaks ya rikosa, ya hadiye Wani yawu me mugun daci da kauri daga bakinsa zuwa cikinsa. ya tsurawa aunty hafsat idanuwa, ita kanta na kasa Daman tini. Cikin shauting da karadi da matsifa da tijara Aeezad ya fara cewa “Ni Zaki munafunta? Sannan kika kashe wayarki kika dawo kika kashe ta hajiya mommy? Wallahi kin zalinceni kin munafunceni, meyasa tin lokacin Baki kirani kin gayaminba, meyasa ba a gayaminba,Wani irin iskanci ne wannan, kika kashemin waya sbda Ke munafukata ce?!!!! Wlhi se kinyi nadamar dole zakiga another side of me, baruwana dake jininace, wlhi senayi maganinki!!!!! Kinci amanata, mena miki? Wlhi in Wani Abu yasamu mommyna bazan yafe miki ba, bana yafiya a kan lamarin mommyna!!!!…” ya karashe kmr ze rufeta da duka seda kaf falon suka amsa da kalaman sa, Nan take kwallah suka wanke masa fuska, itama aunty hafsat kwallah tashigayi kalaman kaninta gareta sun matukar Yi mata zafi me tsanani. cikin kuka tace “Ka gafarceni blood , nasan zaka ga kmr na munafunceka, Ina Neman Afuwarka tsoro ne ya hanani Kiran k….” Kafin ta karasa kawai taji saukar Mari a fuskarta, seda ta zube kasa sbda azabar marin dataji ya shigeta shiga me tsanani, Yana Shirin kara Kai mata Wani irin duka harda dunkule hannu cikin zafin nama, big hajiya na shirin zuwa ta rikosa sede tasan bazata iya ba, Zaks yayi hanzarin ya rikosa Yana fadin “Sir kayi hkri dan Allah kasawa zuciyarsa salama, yanzu kamata yayi mu nufa inda Mommy take domin muga ya lafiyarta take…” Zaks ya jashi zuwa kofar fita a Falon sbda inya barsa Yana iya sumar da Aunty hafsat, domin Zuciyarsa a zafafe take, se turiri yakeyi shi kadai. se uban turiri kawai yakeyi, kmr ze hadiye zuciya ya mutu sbda axabar zafin zuciyarsa haka yakeji. Dai-dai suna Shirin ficewa a Falon Aeezad ya juyo ya kalli Aunty hafsat daketa faman kwallah ta dafe kunci yace “Allah ya isa wallahi bazan taba yafe miki ba!” suka fice a falon,big hajiya ta biyosu Daman sanye take da hijjabi. Wannan kalmar Daya fadi mata ta Allah ya isa ba karamin kara dagawa Aunty hafsat hankali tayi ba,Nan take tashiga tashin hankali, ta fuskanci kamar ma Aeezad Yana ganin da hadin bakinta hajiya mommy tazo ta tafi da nabeelah gidanta, Wani irin kuka ya subucewa Aunty hafsat, ita datasan wannan tashin hankalin zata gani wlhi da bata bar nabeelah taje gidan ba, kwara suyi bala’in daza suyi da ita, tasan de baze Kai bala’in data shiga ba yau ita da Dan uwanta, Kuma tasan waye Dan uwanta, Sam bashi da sauki, bashi da saukin fushi Amma fa in ransa ya baci da mutum to ya barshi kenan har abadan.

Suka isa bakin mota, Zaks ne ya sanar da sauran motocin gidansu Aeezad zasuje. Zaks ya budewa Aeezad murfin mota yashiga Jiri kawai ke kwasarsa, a zuciyarsa ji yakeyi kmr ma mommy Ta rasu. Bayan Aeezad ya shiga motar, Zaks ya xagaya yashiga other side site din kusa da AEEEZAD, ganin haka yasa big hajiya saurin shigewa gaban motar ita Kuma, dreva yaja motar suka ficd a gidan Aeezad ya kalli Zaks “Shikenan mommy ta mutu,,,wlhi in suka gane cikin dake jikinta nawa Ne kashemin ita zasuyi.. a zuciyata inajin Wani Abu na faruwa da mommyna wlhi naji a raina Wani Abu ya sameta…Wlhi in Wani Abu ya samu mommyna duk wanda yakeda sa hannu a ciki, wallahi sena zamo ajalinsa ko wanene!!!.” Aeezad ya karashe Hadi da fashewa da kuka ya hade kansa da guiwa se kuka yakeyi me tsuma zuciya. Zaks yanata basa hkri kmr yadda de ya saba,. Big hajiya ta kada Baki tace ” in Wani Abu ya samu jinina dake jikinta Nima bazan yadda ba…” Cikin matsifa tayi mgnr. Sam aeezad ma besan ta biyosuba seda tayi magana yaji,. Ba Wani nisa tsakani sosai gashi Aeezad Se Azalzalawa yakeyi kan suyi sauri, ba bata lokaci suka isa gidan hajiya mommy, a jere akayi packing motocin tin kafin a gama packing Aeezad ya fito daga cikin motar, dai-dai motar Hajiya naja’atu ta fita a gidan, Saboda Kiran da mijinta yayi Mata na Yana Airport ya dawo daga Lagos gashima ya kusa zuwa gida, Daman Kuma bata gaya masa bata gida ba, Dan haka ta tattare ta fice daga gidan, Amma taso ta tsaya tadinga bawa hajiya mommy hakuri ko Allah zesa taji ta sassauta bugun da takewa yarinyar, sun shafe awa Daya Suna bugun yarinyar tin tana ihu harta dena, Amma Sam ba tausayi azuciyarsu, hajiya naja’atu batasan rashin imanin kawarta ya wuce tunaninta ba se yau, a hanya tadinga Kiran sauran kawayensu da Basu samu zuwa ba ta shaida musu duk abinda ke faruwa a gidan hajiya mommy nande suka sata a fai-fai,Daman kawayen bariki ba amana.

Direct Aeezad ya nufa falon hajiya mommy Zaks na biye dashi da big hajiya Amma sede Aeezad ya d’an musu nisa. Tinda ya nufo falon yake Jiyo zuciyarsa ba tsananta bugu Hadi da lugude, be tabajin irin bugun zuciyar da yake jiba yanzu,, Wani irin hayaniya yaji Yana tashi daga cikin falon nata, Dan haka cikin hanzari ya nufa falon nata, dai-dai ya Sako kafaduwa da Kai da jiki dai-dai saukar belt da bulalalar hannun na’eema data hajiya mommy a jikin Aunty Nabeelah, se zufa sukeyi su kansu sun gaji da dukan nata,ba inda basu fasa mata ba a jikinta, har fuskarta jini yakeyi tako ina sun fasa mata fuska, ba inda bulala bata samu ba a fuskarta, idanuwanta ta rufesu gam, ji takeyi kamar zata mutu, se kukan zuci Kawai takeyi Wanda yafi kukan Ido zafi, har yanzu ta kaMa ta kame cikinta gam ta kakkaresa da hannayenta, GAF take dajin fitar hayyaci wato sumewa. Idanuwan Aeezad Sukayi tozali da wannan matsifar, yayinda bawanda yaga shigowarsa falon sbda hankalin kowa na kan dukan da akema nabeelah falon ya rikice da zagin nabeelah gashi taf falon yake cike da bil’adama,ga Alhaji sunusi tsaye ba yadda zeyi.”zaki gayamin waye ya Miki ciki ko semun karasa kasheki zuwa lahira….” Aeezad da zuciyarsa da idanuwansa ke kan aunty nabeelah dake yashe kasan tiles tako ina jinine a jikinta, kwallarsa suka yawaita cikin zallar tausayinta, zuciyarsa ta Kuma shiga halarar kuna, yasan duk shine sanadin sata a wannan matsifar, Daman yasan za a rina. “cikina ne…..!!” Ya fadi da karfi, yayin da a guje ya karaso ya janyeta daga dukan da suke mata, ya rungumeta a jikinsa Yana kallon uban shedar bulala a jikinta inda ya d’an bude sbda hatta rigar jikinta ta fara yagewa, tinda ya shigo falon taji sbda kamshin turarensa Daya cika mata hanci, ko a yaya in har zataji kamshin turarensa seta gane. Toh fa, Nan kallo yadawo kan Aeezad da nabeelah, hajiya mommy Kam mutuwar tsaye tayi, na’eema ma haka tinda yace cikinsa ne suka dago Ido suka kallesa duk se mutuwar jikkuna tasamesu a lokaci kankani, gani sukeyi kmr a mafarki,jamaah suka hau kus-kus, sbda ba Wanda be gane Aeezad din ba mijin naeema kowa ya sanshi a cikinsu. Hatta Alhaji sunusi Yayi mutuwar razana jin abinda d’ansa yace daga bayyanarsa. “cikinka kmr ya? Ni ban fahimta ba, Wani irin sakarai ne Kai zaka danganta cikin shege jikin Yar Aiki kaskantaccita da kanka,,,,” cewar hajiya mommy, dai-dai big hajiya da zaks suka shigo falon, a guje big hajiya ta karaso inda take ganin Aeezad rungume da nabeelah, tini jinin jikinta ya gama shafarsa a jikin kayan jikinsa sbda rungumar dayayi mata Yana kuka kmr ransa ze fita, cikin zallar azabar tausayinta. Zaks de seyaja gefe ya tsaya shima Yana kallan abinda ya faru gasu hajiya mommy tsaitsaye da na’eema da bulala a hannu dagani su sukayi wannan aikin ko ba a gaya maka ba. Yaya de take ne?cikin jikinta de Wani Abu be samesa ba kou?” cewar big hajiya, Nan kowa ya kara dimauta a zallar damuwa da tashin hankali. Hmmm seda na’eema ta zauna dabau a kasa sbda azabar tashin hnkli da kishi tana fadin “hajiya Mommy ban fahimta ba? Ki tambayesu me suke nufi? Bazan lamunta ganin mijina rungume da mazinaciya me cikin shege a jikinta ba bazan lamunta b….” Aeezad Daya dago red eyes dinsa ya kalli na’eema ya dawo ya kalli mommy ya katse na’eema cikin tsawa da kunar zuciya a ransa yanaji ko kashesu yayi duk baze fita daga mummunan bakin cikin dasuka dasa masa ba a zuciya, wata iriyar tsanar na’eema da hajiya mommy tana ratsasa, a halin da yake ciki Yana iya kashesu su duka,Kai duk Yan falon ma Yana iya kashesu, dabadan bakin duniya ba, da har ubansa dake cikin falon yana iya cinna masa wuta, Sam baya hayyacinsa For now. “kar wadda ta kara shegantamin ciki, duk wadda ta kara shegantamin cikin keda uwarki, zan ninka muku azaba kan azabar dazan muku, bana yafiya Kuma bana afuwa A kan mommyna, Kuma matata, matatace ta sunnah, Aurenta nakeyi, cikin jikinta cikinane, ni namata shi, ga shaidojina Nan…” Ya karashe Hadi da nuna big hajiya da zaks. Big hajiya tayi hanzarin amshewa da “Tabbas kuwa cikinnan na sunnah ne, kada Yar bakar macen data Kuma shegantamin cikin jika na, in ba haka ba duk se na hadaku na kwashi babbar bura ubaku, ba kmr make rafi’ah Yar gidan laure me fura da no-no, kina zaton yadda kike shegiya Ubanki yayima uwarki cikin shege a ti-ti haka jikana yake? To kinyi kuskure, nayima yarana tarbiya kuma Suma sunma nasu, mu ba sauran bokaye bane,, tsakanina dake rafi’ah sede in biki da Allah ya isa, tsinuwata gareki bazata kare ba, koda an dannaki a wutar jahannama,abinda kkyi na raba uwa da d’anta a tunaninki Zaki gama da duniya lafiya? To knyi kuskure…” Big hajiya ta karashe tana kwallah. Tabdijan rigiji gabji! Halin da hajiya mommy da na’eema suka shiga baze misaltuba tini belt din hannun hajiya mommy ya subuce ya fadi kasa, ta juya ta kalli dumbin jamaah dake falon wanda suketa kus-kus, hajiya mommy ta juya ta kalli alhaji sunusi Wanda kansa ke kasa. bala’i biyu kenan gana big hajiya dana Aeezad, komi nafilah ne a kn na Aeezad. . Na’eema kawai seta fasa Wani irin uban ihu Hadi da kuka kmr ranta ze fita. Cikin tsawa da matsifar tashin hnkli ita fa har yanzu hajiya mommy bata fahimta ba, kanta ya kwance. “karya kakeyi ba matar ka bace,sbda bamu da labarin aurenka, ga ubanka can tsaye,besan kayi aure ba, wannan cikin na jikinta cikin shege ne, can kwartayenta suka mata, Yar iska karuwa, kana danganta kanka da karuwa, da Kuma Cikin jikinta na shege, ita kanta shegiya ce mara asali, fatsika, sekin gayamin waye yau ya Miki cikinnan…” Ta karashe Hadi da tsugunnawa zata dauko belt din Daya fadi daga hannunta, kawai daurewa takeyi Amma tashin hnkli da take cikin ya isa, har bata gani sosai, tazama kmr mahaukaciya, sbda ta fuskanci akwai gaskiya a lamarin, sannan tasan Aeezad baya karya komin zafin gaskiya haka yake furtata, a kalamansa ba wasa a ciki. Ta daga bulalar zata saukewa nabeelah, Kafin bulalar takai jikin nabeelah, aeezAd ya rike bulalar ya ajiye nabeelah ya tashi tsaye, ya watsawa hajiya mommy Wani irin lafiyeyyen marirrika a kuncinanta duka biyu, seda falon yayi amsa kuwwar marin, ji kake fassssssssssssssssssssss! Fassssssssssssssssssssss!! Nan fa kowa ya dawo hayyacinsa Alhaji sunusi na gani yanaso ya dakatar Amma ya kasa, ji yayi duk jikinsa ya rike ya kasa katafus, Abu de Kmr a film ko a Hausa novels. Nan take Hajiya mommy tajiyo kukan karnika a kunnuwanta abun ya wuce tajiyo kukan tsintsaye, axabar zafin marin ya isa, kukan karnika kawai ke mata amsa kuwwa a kunnuwanta sbda tsabagen azabar marin daya gigitata, ya rudata, ya kid’imata, hakoranta na gefe da gefe suka ya dauka ji kake kauuuuuuuuu!! Nan take taji faduwar hakoranta hudu, sbda azabar zafin marin dayayi mata, seda hakoranta biyu-biyu suka fita daga gefe da gefen bakinta Kuma duka turame ne suka fita. Falon fa ya kuma rikicewa da gulmar siriki ya mammari uwar matarsa a gaban jama’ah. Na’eema ta tashi tsaye cikin zafin nama dai-dai Aeezad nacewa “Kar wadda ta Kara shegantamin ciki, saboda cikina ni nayisa da kaina Kuma banyi saa seda shari’ah musulunci ta aminta nayisa…wannan Marin Dana miki hajiya mommy somin tafi ne, ki jira sauran azabata keda yarki da duk wata halitta dake falonnan, bana yafiya a kan mommyna, sbda ban taba San wata halitta kmr ita ba, duk wanda ya tabamin ita wlhi sena tabasa ko waye shi…” Toh fa Nan take kowa yasha jinin jikinsa, tunaninsu ko binsu zeyi da mari, Aiko da Nan take dole wata ta fadi ta mutu. Na’eema ta karaso ta cakumi wuyan Aeezad tana fadin “Wallahi baka Isa ba, kaidin banza dazaka mararmin uwa a gabana, waye Kai? A Kan wannan karuwar banzar zaka mararmin uwa, anje an debo cikin waje an mako maka asiri zakace cikinka ne, wallahi baka Isa ba,harda cewa ka aureta, waye Kai? Wanene Kai? Kaidin banza, wallahi bazaka iya hadani da wata ba, baka isa ka hadani da wata ba, watanma kaskantacciya me’aikinku, tsohuwar guzuma, wlhi kadawo hayyacinka ita ta raineka, ta girmeka, wlhi tsohuwar guzumace, karuwa ce, haihuwar karuwai, ta haifeka Wlhi…” Na’eema ta karashe Hadi da yaga masa rigar jikinta keeeetttt, har kasa seda ta yage masa riga kmr mahaukaciya, azababben kishi na addabarta,. “A haka nake santa,,,a haka nace se ita har abadan, kece banza a banza mommy ta wuce banza a idanuwana, tafiki komi ta fiki hakuri Dani, ta fiki juriya dani, ta fiki dadih, ta fiki test , ta fiki tsafta, banza jaka, sakarai, wawiya mara imani keda uwarki,!” Aeezad ya fadi Yana kokarin cire hannunsa daga cikinsa Amma Ina se cireta yakeyi tana Kuma dawowa, bakin cikin dayasa mata na kalamansa na Yanzu yafi mata komi zafi, ba kmr ma kalmar dayace ta fita dadih! Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Ba ita ba harta uwarta seda ta girgiza, ji sukeyi Daman mutuwa sukayi da ganin wannan bakar ranar ganin tozarci a idon jama’arhta an nuna mata ita ba komi bace, har siriki ya dauki hannu ya mareta, Kuma mijinta na kallo be dakatar ba a gaban mutanen da take nuna musu ita se yadda tayi da mijinta Amma Wannan matsifar ta faru a idonsu, Sam hajiya mommy bataso akayi shuka a idon makwarwa ba, gashi tin farko Da abun ya fara faruwa tini hajiya safiya kawar mommy ta danna video recording a wayarta cikin dabara takema komi video. Nanfa na’eema ta rikice kishi ya rufe mata Ido ta kama yagar Aeezad da kumba tana zaginsa ta uwa ta uba, kawai Aeezad ya barta ne tayi haukarta, ta d’and’ani azabarsa me sauki sannan ta jira sauran zuwar azabarsa garesu. Bayan ya gaji da haukarta da zagin da take masa ta uwa ta uba, har Kiran sunan uwarsa tayi na haihuwa karara ta danna mata mugun ashariya. Zagin datayima uwarsa wadda ke kwance a kabari ya hasalasa, ya dunkule hannu yakai mata Wani irin naushi nan take ya sameta a dai-dai saitin Ido idanonta ya kama zubda jini, kan kace kwabo idon nata ya kumbura Yayi suntum, ta rikesa ta fasa kara sbda ji takeyi kmr ya fasa mata kwayar ido, nanko azaba ce kawai, kashin kwayar idon ya buga Kuma ya bugu kiris ya rage ya karye, Nan take na’eema ta zube sumammita, hajiya mommy dataja da baya gudun kar ya kuma marinta ta kama Baki ta rike,. Tana ganin yarta ta zube a sume hankali tashe, ta karaso kan na’eema tana Fadin “Shikenan ya kashemin y’a Daya tilo ..nashiga uku zafin asiri yasa ya kashemin y’ata….Wayyohhhh ni na bani! Na shiga uku ni rafi’atu!!!! ” Hajiya mommy ta kama ihu ga jini nata zubowa daga bakinta, tini turamen hakoran nata dasuka fita Suka fado kasa, hankalin hajiya mommy ya Kuma tashi ganin sanadin Marin da Yayi mata ya cire mata turame har hudu na hakoran bakinta. “Wlhi kadan kuka gani….” Aeezad ya fadi cikin zafin Rai in Yana wannan mood din bame tinkararsa,fuskarnan bakikirin ya sunkuci mommy A kafata Big hajiya ta biyosa Zaks ya biyosa suka fice a falon a kan idon hajiya mommy wadda itama takejin kmr ta hadiye zuciya ta mutu, bakin cikin dasuke ciki ya isa.

Aeezad yasa nabeelah a mota, Zaks yashiga gidan gaba, big hajiya tashiga gidan baya ta rike nabeelah wadda takejin komi bata Suma ba Amma azabar da takeji a jikinta ta shahara, cikinta se murd’awa yakeyi, sbda dayasara a motar be shiga ba,se big hajiya de ta riketa, se addah takeyi Allah yasa de cikin jikin yarinyar Yana cikin koshin lafiya, ita tin daganin cikinnan tasan da wuya in Rai Daya ne a cikinsa. Aeezad ya iso inda securities suke,kowa ya nutsu ganin halin da yake ciki bana wasa bane. Babbansu a ciki ya iso inda Aeezad yake Tin kafin shi ya iso inda yake, domin tin daga nesa ya fahimci gunsa ze iso. Ya kame masa cikin girmamawa. fuska ba walwala Aeezad yace “duk Wata wadda ke cikin falon hajiya mommy banaso a barsu su fita a gidannan, da hajiya mommy da na’eema, duk a kwasosu asasu a bayan motar, kar asasu cikin mota, a bayan budaddiyar motar Nan za asasu, aje a kullesu a dakin duhu, kar abasu ci kar a Basu sha, harse sadda nazo….bance Kuma a ragawa kowa cikinsu ba, duk daki Daya nakeso a cunkusasu…” Yana gama fadar hakan ya juya ya nufa car dinsa ba tare Daya jira cewar Ayuba ba, domin uwarni ya Basu ba shawara ba. Yana shiga Motar drevansa Wanda shima yake sanye da kayan sojoji yaja suka fice a gidan aeezad ya kamo Mommy Daga jikin big hajiya ya rungumeta sosai jikinsa yana kwallar, yayinda kwallarsa suka sauka a kan fuskarta. “Ina sanki mommy, Kiyi hkri nasan ni nasaki a wannan wahalar, sbda ni aka Miki izayarnan, Ina tare dake wlhi har abadan zanci gaba dasanki mommy, koda kuwa ruhin jikina baya tattare dani, wlhi Ina sanki har lahira zanta sanki har abadan mommy!” ya karshe zazzafan kalamansa Hadi da Kai mata kiss a kunci, murmushi ta masa, Hakan ya bashi tabbacin tana jinsa kawai ta jigata ne, ya daura hannunsa akan cikinta, yayinda yakejin kaunarta Dana cikin jikin na Kara shigarsa. Direct Wani babban private hospital dreva ya nufa dasu.

A gidan gimbiya hajiya mommy kuwa. tini sojoji kusan su arba’in suka nufa cikin gidan, har yanzu hajiya mommy nata ihu tana zage-zage, dataga Aeezad ya fita., Se aikin jijjiga sumammiyar yarta takeyi, Alhaji sunusi de har yanzu bece komi ba abun ya daure masa kai Yana Shirin ficewa a Falon sojojin suka Danno Kai cikin falon,. Dole ya koma ciki. Mutan dake ciken falon na ganin sojoji sun shigo falon dayawa duk suka mike tsaye, Nan wasu suka fara Shirin ficewa Amma sojojin suka dakatar dasu, sukace su wuce su sasu a mota sbda Aeezad yace a kulle kaf halittar dake falon. Nanfa mata suka saka ihu,. A fari sunyi ma sojojin musu Amma dasukaga bindigo tini suka shige gaba aka sasu a bayan motar kmr barayi, duk suka saka kukan ba wadda batayi nadamar zuwanta gidan ba, se Allah ya isa sukema hajiya mommy wadda ita tasasu a matsifar Nan. “nashiga uku ni na bani yanzu mexan cewa mijina!!’. Suna kalaman dasuketa yawo a bakunan mata datawa dasuke gurin. Hajiya mommy da akaxo SATA a mota ta kama zage zage, ayuba yasa mata bindiga yace “Am sorry hajiya dole asaku a mota…” Alhaji sunusi dake tsaye ya dakatar dasu daga tasa ketar ta gaba, suka basa hkri sukace ba daga su bane, umarnine daga sama wato aeezad. Alhaji sunusi yana Gani kiri-kiri hajiya mommy da wata cikin kawayenta suka kama Naeema domin su sata a mota, da kyar matar ta yadda ta kama Naeema se harara take aikowa hajiya mommy,, ita batasanma tanayi ba tashin hankalinta ya isa, wai duk a kan me aiki ne Aeezad ya musu Wannan cin mutuncin. Inata tuna Wannan zuciyarta na kuna ruhinta na zafi,again Kuma ga yarta a sume tayi-tayi su kaisu ma asibiti, Amma Ina Basu bi ta kanta ba, Wani irin ihuuuuuu hajiya mommy tayi kmr mahaukaciya har sau uku, dai-dai an fito dasu waje haka aka hau ti-ti dasu kowa na kallansu kmr barayi, direct aka nufa barrack din sojoji, aka zubasu a daki daya, wato dakin duhu, Wani daki ne me uban duhu baka ganin haske ko kadan, aka kullesu gam suna ihu suna komi,kmr wasu karnika, Kai ko Kare aka kulle an zalincesa, kafin asasu Kuma seda aka amshe bags dinsu da phones dinsu,ranar de sunga Bono, hajiya mommy tayi kuka tayi kuka kmr zararriya ta zama kmr mahaukaciya, Abu kmr a mafarki, kawayenta nata gaggasa mata maganganu da aka zubasu a dakin, se zaginta sukeyi, ga yarta sume kmr ma bata da rau.

This book is 1k 08101626484

 

NAMIJIN ZUMA

 

Back to top button