Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 75

Sponsored Links

Page 75

Kamar yadda ya saba ko yaushe bayan sallar asuba yana shigowa ya tabbatar da lafiyarta yauma haka

“Gidan hajiya nakeso naje yau” ta fadi masa bayan sun gama gaisawa

“Ba damuwa,jiya ban samu zuwa ba,ki shirya na fita dake idan zan fita anjima kadan” saita gyada kai,tana maida idanuwanta ta lumshesu,kwata kwata daga jiya zuwa yau batason zaman gidan.

Karfe goma na safe ta gama komai a bangarenta,ta gyarashi ta hada breakfast dan dai dai cikinta,ta kuma shirya cikin atamfa dinkin doguwar riga,tana zaune a falonta tana buga game a wayarta tana jiran fitowar abbas,hatta mayafinta yana gefe.

A nutse ya tura qofar falon,yana sanye da shadda butter color da aka tsarama wani lafiyayyen dinki me aji,a kanta idanunsa suka fara sauka,sai yayi tsaye riqe da handle din qofar yana kallonta idanuwansa suna lumshewa,tayi masa kyau har baisan iya yadda zai musalta ba,atamfar ta karbeta ainun,har ya gaza gane doguwar riga da kuma atamfa wanne ne yafi mata kyau,ya dan rufe idonsa yana shafar qirjinsa da hannunsa,yana jin tana sake saka kai sosai cikin zuciyarsa tana samun kyakkyawan mazauni,illa take masa a kowacce rana,kullum yaqi yake da zuciyarsa,yana ganin kamar ya fiya zaqewa da yawa,yanason canzata,yana son sake kawo kusancin da yafi wannan a tsakaninsu,baisan ta yadda komai zai zo ya kuma kasance ba.

Batasan da tsaiwarsa ba,saboda hankalinta yayi gaba a game din da takeyi,sai da qamshinsa ya fara kawowa hancinta ziyara,ta daga manyan idanuwanta a hankali,idanuwansu suka sarqe waje guda,siririn murmushi ya subuce mata,ta shagwabe fuska

“Ka tsoratani uncle” ta fada tana tura baki gaba,yabi dan qaramin bakinta da kallo,wanda yau yasha jambaki pink,hakan ya qarawa lips dinta color akan ainihin color dinsa.

Hannu ya saka ya yafitota yana jin jikinsa na mutuwa,ta miqe a hankali tana dubansa tare da takowa inda yake

“Uncleee…….na gama fa na dauko.mayafina?” Kasa amsa mata yayi har ta iso gabansa,yasa hannu a tausashe ya kamo qugunta janyota gabansa,suka zama very close sosai a tsakaninsu.

A tare suka lumshe idanu sannan suka bude,suka zubawa juna idanu kamar shiri,kowa da abinda jiki da zuciyarsa ke gaya masa,ya motsa labbansa da salon miskilancin nan nasa

“Kinyi kyau baby doll” murmushi ya kubce mata tana kallon manyan idanunsa da suka qara masa kyau a idanunta,kafin tace komai sautin muryar hafsat ta tunkarosu,da alama sassan take nufowa,tana ta hayagaga da mimi da nawwara,sai ka dauka wasu manyan ‘yammata ne.

Hannunta ta sanya da sauri ta zare hannayensa daga qugunta taja da baya,idamunsa a lumshe yana jinta,sai data matsa ta tsaya daga can baya sannan ya bude idon nasa fes a kanta yana kallonta

“Meye hakan?”

“Mommy” ta fada a tana yin narai narai da ido, kafin ya bata amsa hafsat din ta iso cikin saurinta kamar me shirin tashi sama,amma ganinsa a tsaye daga bakin qofa goye da hannayensa yana kallon ciki ya sauke mata duk wani fada da cin mutunci da tazo yiwa widad din nayin rana batazo tayi shara ba balle wanke wanke.

Ta gefansa ta raba ta shiga ciki,da widad din ta fara cin karo,wanda ke tsaye rataye da qaramar jaka a kafadarta tana qoqarin yane kanta da kyakkyawan mayafin daya dace da kayan jikinta.

Zuciyarta ce ta tsinke da irin kyan da yarinyar tayi,zuciyartata ta fara rawa,ta kuma fara ayyana mata tsaiwar da yayi widad din yake kallo,saita tsaya cak,ta fara raba kallonta tsakanin fuskokinsu su biyun,gabanta yana luguden faduwa.

Fes yake kallon widad din kansa tsaye ba tare daya nuna kara ko alkunyar wanzuwarta a wajen ba,abinda ya sake dimautata kenan,bakinta har rawa yakeyi sanda jefa musu tambaya kamar wasu ‘ya’yan cikinta

“Ina kuma zaku da safen nan…..naga har kun shirya” maganar ta ta tuna masa inda zasu,ya sauke hannayensa dake goye a qirjinsa yana daukar mimi da tafi kusa dashi ya juya zuwa waje yana cewa

“Ki sameni a mota,rana tana yi” da kallo hafsat din ta bishi har ya fice,saita dawo da dubanta ga widad,kamae zatayi kuka saboda wani malolon kishi daya riqe mata wuya

“Izinin wa kika nema da zaki shirya fita unguwa?kin fara rainani fa widad,ki shiga hankalinki” karon farko da taji maganar banbarakwai,tunda dai ita ce mata akayi ta tambayi abbas ne a duk sanda zata fita bawai hafsat ba,to amma tana jin shakkarta ba zata iya tsaiwa mata bayani ba,don batason fada ita sam a rayuwarta.

Hon din motarsa ya hana kowa a cikinsu magana,da wannan yake maka sign idan yana jiranka,duk da haka sai hafsat din ta kalli widad a gaggauce

“Ina zakuje?”

“Gidan hajiya”

“Shine kika saka wadan nan kayan?,bana gaya miki ki dinga killace kanki ba karki bari ya dinga ganin tsiraicinki?” Ta fafa gajiya da soki burutsun hafsat,ita kawai so take taga ta fita a gidan

“Aiba haram bane,tunda miji da mata ne ni dashi” ta amsa mata ba tare da kawo komai a zuciyarta ba,tunda dai tasan da wannan salon anty madeena tayi mata bayani.

Mummunar faduwar gaba ta saukar mata,yaushe yarinyar ta fara fahimtar kalmar MIJI da MATA?,lallai akwai qura,liqi yana shirin balle mata kenan,kasa ce mata komai tayi,saita juya kawai ya fita,widad din ta bita da kallo,akwai abubuwa da yawa.na mommy hafsat din dake bata mamaki,takowa tayi ta kulle sassan nata ta wuce zuwa motar tasa.

Ranar wuni tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga qarshe ta dauka waya ta kira anty ummee don ta labarta mata,kiran duniya wayar taqi tafiya,sai taji tana ds buqatar fita taje gidanta zaifi mata sauqi,wannan ya sanya ta yita kiran abbas ta gaya masa zata fita amma bai dauka ba,ashe yabar wayar cikin mota.

Ta kuwa cika tayi fam,zuciya ta dinga raya mata suna can suna holewarsa da yarinyar,lallai biri yayi kama da mutum,ba banza ba yarinyar ke iya kallon qwayar idanuwanta ba ta maida mata magana haka gatsal.

Ji tayi kamar ta rataya mayafi ta fice abinta,to amma tana shakkarsa,tasan ko zai dauki komai banda wannan,bazai lamunta ba,haka tana ji tana gani ta haqura da fitar,taci gaba da kiransa amma saita daina shiga ma daga qarshe.

Basu dawo ba sai dare,suna isowa kuma fa shige sassanta ta kulle abinta,abbas din ya bita da kallo, quruciya har yanzu taba dawainiya da ita ba ruwanta da zancan yau kwananta nw,baya mantawa akwai ranar da a gaban hafsat din ya zolayeta akan a sassansa zata kwana,kamar zata hadiyi zuciya haka hafsat taji amma ta dake tana tuna wasu daga cikin karatuttukan anty ummee,ta dake tana tayashi tsokanartata akan anan zata kwana, qarshe sulalewa tayi ya gudu abinta.

°°°°°°°Tun daga wannan ranar ya zamana fiye da rabin weekend dinta agidan hajiya takeyi,wani lokacin tun a hanya taje cewa ya wuce da ita,sai ya wuce gida bayan ya ajjiyeta,baya musu, saboda hakan shi kansa yana faranta masa rai,saboda yadda take nunawa hajiyan qauna da kulawa,ita kanta hajiyan hakan yana mata dadi,don duk sanda widad din tazo saita gaji da kala kalar girki,saiya zamana shi kansa zaiyiwu wuya baka sameshi a gidan ba,a nan zaici abincin rana har na dare,kai wani binma da safe yake fitowa da jallabiya yazo yaci breakfast ya koma hafsat din na bacci,idan taga bai nema abinci ba saita share taci gaba da sabgarta tana ganin sauqi ta samu.

Abu daya ke qonawa hafsan rai,yadda widad din ke guduwa tana barinta da tulin ayyukanta,tuni ungulu ta koma gidanta na gargajiya,qazanta sai wadda ta qaru,saboda gyaran weekend din data qwallafa rai akansa yanzu ba samuwa yake ba,idan widad ta shigo gidan sai daren da ana ya gobe zasu koma kaduna.

*_MAFARI RAYUWA DA SOYAYYA_*

Tun daga daren jiya daya daukota daga katsina gidan mahaifiyarta,har kawo yanzun da yake shigowa gidan jikinsa gaba daya baya jin dadinsa.

Ya jima a parking space bayan dawowarsa daga aiki,yana zaune cikin mota,shi bai shiga ba shi bai fita a motar ba,daga nan inda yake yana iya jiyo daddadan qamshin turaren wutarta daya zama tambarinta,qamshin da duk sanda zasu bar kaduna zuwa bauchi yake kewarsa,haqurinsa ya fara gazawa,yana dab da hanata weekend gidan hajiyan,tunda ko ba komai idan tana gida,iya qamshinta kawai na saukar masa da nutsuwa.

Cikin tattara qwarin gwiwar sa ya buda murfin motar ya fito,dai dai sanda ake qwala kiran sallar magariba a garin kadunan,sanye yake da uniform dinsa masu matuqar daraja da kuma qara masa kwarjini,yana iya hangen mai gadin gidan amma ya ratse yayi kaman bai ganshi ba,saboda yana jin kamae qafafuwansa ba zasu daukeshi ba.

Da sallam ya shiga parlor din,dai dai sanda take fitowa daga kitchen dauke da wani tray data jera lemon zobo da abarba data koya ta gwada,ya kuma bata ma’ana sosai har fiye da yadda ta zata.

Murmushi ne shimfide saman fuskartata,batasan dalilin da ya sanya kwata kwata batajin dadin gidan ba har sai sanda ya dawo,yayin da abbas din ya zube mata.manyan idanunsa yana kallonta,qafafunsa.na sakeyin laushi kamar bazasu iya daukarsa ba.

Sanye take da wata baqa wul din gown wadda kwata kwata tsahonta iyakarsa qasan gwiwarta,hannunta gajere ne don kana iya hangen hammatarta da kuma tundun qirjinta da cikar da suka fara yasa suke bayyana kansu.

Kanta babu komai sai lallausar sumarta baqa sidik mai laushi data yiwa kalba guda daya tak a kan nata,jelar ta sauka gadon bayanta taba reto,zata tsammaci relaxer ta sakawa kan nata.

Tray din ta ajjiye,saita fara takowa gabansa tana juyawa gaba da baya

“Uncle kalla ka gani,nayi kyau?,don Allah kwalliyata ba tayi kyau ba?” Ta fada bilhaqqi har cikin ranta tanason yace tayi kyau din,saboda ire iren kaya ne da mamarta mahaifiya ta hada mata su masu yawa da kyan gaske bayan ziyartarta da tayi,tsaraba tayi mata mara iyaka,don bata samu halartar bikinta ba,hasalima sai ana gobe daurin auren widad din ta sani,wannan yasa tayi fushi kwata kwata ta koma gefe,saidai zuwantan yasa tayi mata kyakkyawar tarba,ta kuma hada mata nau’in dukka wani kaya da tasan uwa zata yiwa diyarta,ta hada da nasiha mai kama da hannunka mai sanda

“Kar na sake jin sirrinku ya fito keda mijinki,idan ba haka ba zamu bata dake,kome ya umarceki kiyi kiyishi indai kinaso muci gaba da shiri” a duniya idan akwai abinda ta tsana wani yace sun b’ata,waninma mahaifiyarta da take mata wata irin qauna take jinta har ranta.

Bai ankara ba har ta iso gabansa,juyi daya tak tayi ta fada jikinsa,sai ta riqeshi tana dariya dariya

“Uncle…..ba kace wannan rigar ba zata yimin kyau ba?,shi yasa itama na gwada maka ka gani…..bakace komai ba” ta furta tana tsareshi da ido.

Tuni maqoshinsa ya bushe,ya tattaro yawu ya hadiye yana dan ja da baya

“You look so good baby doll” dan tsalle ta saki a jikinsa tana cewa

“Thank you uncle” cikin dabara yadan ja baya yana zare jikinsa saboda yadda yaji jikinsa ya fara dauka gaba daya,saita sake matsowa ba tare data lura da yanayin da gake ciki ba tana karbar jakar hannunsa

“Sannu da zuwa,na manta” ta fadi tana dariya sannan tayi gaba tana cewa

“Yau wani kalan abinci nayi maka,mommmy ce ta koyamin,tace irin abincinmu ne idan mun dawo nayi maka” duk maganar da takeyi yana tsaye cak yana kallon yadda qugunta yake juyawa ta cikin rigar,kusan rabin bayan rigar an debeshi,farar fata cikin baqar riga……abun ba qaramin qaawa yake bayarwa ba.

Kasa riqe kansa yayi,har jikinsa yake jin bazai iya jurewa ba,saiya ja baya a hankali ya fice daga falon salin alin,sai waiwayowa tayi taga wayam,mamaki ya cikata,tahau kiran sunansa tana leqawa dakinsa,har nata dakin zuwa kitchen bashi anan,saita koma saman kujera ta zauna tana hawaye,me yasa zaiyi mata haka?,ta gama wahalar shirya masa abincin kuma kawai saiya fita bai gaya mata ba?.

Tana qananun hawayenta ta miqe ta shiga daki itama ta daura alwalar sallar magariba ta tada sallar,tana sallar tana goge qwalla.
[3/17, 1:28 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button