Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 31

Sponsored Links

*NOOR-AL-HAYAT* ✨

Da safe har su siyama suka tafi makaranta Anty khadijah bata sakko ba kamar yanda ta saba, tun bayan da ta kori kyauta da asuba take fitowa amma yau shiru, Khadijah ta taya mumy suka yi breakfast tun asuba sannan ta kwashi wanke wanke ta tafi tana yi duk da ba ita ce da yi ba baby ce, amma ganin tana bacci take taya ta, Mumy kuma ta wuce bedroom dinta, yanxu kam khadijah ta saba bata jika jikinta idan tana wanke wanke, ta gama wanke plates din gaba daya ta shigo kitchen tana ajiye ko wanne a maxauninsa, d’an dukawa tayi ta dalilin cikinta dake ciwo tun cikin dare, ta rasa irin ciwon cikin, Aliyu ya shigo da shirin fita office, tana ganin sa ta mike da sauri, yace “What’s wrong?” Murmushi tayi tace “Good morning” yace “I asked what’s wrong with you” tace “Ba komai, kawai cikina ke min ciwo amma yana sauki” yace “Since when?” Tana ci gaba da ajiye plates din hannunta tace “Da na tashi daxu” Yace “Ohk xan ajiye maki magani a bedroom, idan kin yi breakfast sai ki sha” tace “Toh nagode, in yi maka cup din coffee?” Yace “Ohk thanks” daga haka ya juya ya koma parlor, ta dau cup ta yi making masa coffee a ciki sannan ta fita ta kai masa, ya amsa yana kallonta yace “Nagode” murmushi tayi ta juya ta koma kitchen. Ita kadai ce kwance dakin banda juye juye babu abinda take, baby ta shigo daukan system dinta ganinta haka ta isa gabanta da sauri tace “Iman, what’s wrong are u okay” mikewa xaune khadijah tayi jin xuciyarta na tashi ta wuce bayi da sauri, amma ta kasa aman, sanin Mumy bata nan baby ta tafi dakin Anty khadijah dake parlor da yar ta suna kallo suna yin lunch din da mumy tayi kafin ta fita aiki, wayarta baby ta dauka tayi dialing number Aliyu da sauri, sosai Aliyu yayi mamakin ganin number Small mun dinsa, can dai ya dauka hade da sallama, Baby tace “Yayanmu it’s me baby, Iman ce bata da lafiya, she is even vomiting gashi mumy bata nan, nobody is at home sai Anty khadijah” Yace “Toh gani xan xo yanxu” katse wayar yyi, tayi deleting kiran a log sannan ta ajiye wayar ta fita da sauri ta koma dakinsu, Aliyu ya bar duk abinda yake cikin few minutes sai gashi ya dawo, hawaye kawai khadijah take da ya tambayeta inda ke mata ciwo, Anty khadijah na ganin ya shigo gidan ta hayo sama kamar me neman abu iklima na biye da ita, kamar dai daxu yanxu ma magani ya bata, sannan ya kira mumy ya sanar da ita bata da lafiya xa su tafi clinic ya dubata, Mumy dai tayi mamakin yanda aka yi ya sani har ya dawo shi da yake gun aiki, amma dai kawai tace masa toh, Hijab khadijah ta sa ta bi sa suka fita, Baby tace “yayanmu xan iya bin ku” ya kalleta yace “Clinic din?” Da sauri tace “Aa yi hakuri” murmushi yyi sanin tun tana yar karama take tsoron asibiti dama, suna isa asibitin office dinsa ya wuce direct da khadijah, sai dai ba shi ya dubata ba wani likitan ne daban ya dubata yasa aka mata series of tests, nan ya mata allura aka bata drugs, tun da aka yi alluran dama take kuka, Aliyu ya nuna mata gadon duba masu ciki yace “Kwanta can kiyi kukan da yawa” ba musu ta kwanta ta ci gaba da kukan nata a haka har bacci ya dauketa. Sai kusan la’asar ya tada ta, ta bude ido a hankali sannan ta mike xaune yace “How you feeling now?” Bata ce komai ba, yace “Toh taso kiyi alwala” ba musu ta mike, bayan ta gama sallah suka fita office din, Eatry ya kai ta ya siya mata abinci sannan ya mai da ta gida. Bayan kwana biyu, Aliyu na tsaye kitchen yana mamakin wa kuma ke shan coffee a gidan bayan shi, cos ya sami powder din ba yanda yake ajiye sa ba, hada coffee din yyi ya fita kitchen din, duk da shirin fita office da yyi komawa bedroom dinsa yyi ya kwanta bayan ya gama shan coffee din jin kansa na juya masa, Mumy ta gama shirin tafiya gun aikinta ganin bai fita ba tun safe ta shiga dakinsa, kwance ta samesa idonsa a rufe, tace “Abuturrab” ya bude ido da sauri tace “Are you okay” yace “Sure I am fine, it’s just headache anjima xan tafi aikin” Mumy tace “Toh Allah ya sauwake, sai ka sha magani, ni na tafi” yayi mata Allah ya tsare sannan ta fita, Anty khadijah dake xaune parlor tayi ma Mumy Allah ya kiyaye, Mumy tace “Ameen” sannan ta fita. Mumy na fita Anty khadijah ta shiga kitchen ta daura tea pot a kan gas, ta dau Lipton da kayan kamshi kamar dai yanda ake dafa ruwan shayi ta xuba a tea pot din, kulle kofar kitchen din tayi ta ciro wani kulli da ta tusa cikin bra dinta ta bude ta juye gaba daya garin ciki a tea pot din sannan ta rufe, bata bar kitchen din ba sai da ya tafasa sosai sai kamshi ruwan lipton din yake, sannan ta juye a karamar flask bayan tayi shifter din shaft din garin, ta kashe gas ta wanke tea pot din ta kife ta dau babban flask din gidan ta bude ta tuttule ruwan Lipton dake ciki a sink ta rufe ta ajiye sannan ta bar kitchen din ta koma parlor ta xauna. Karfe sha biyu saura Anty khadijah ta sa su baby da iklima su shirya wai xa su rakata, ba don ran baby ya so ba ta tafi dakinta shiryawa don tasan masifa xata yi ta masu a duk inda xa su, Bayan baby ta sa Hijab dinta ta kalli Khadijah da ke gyara mata kayanta da ta sassauke ta ajiye saman gado tace “Don’t worry fa Iman, ni ma kawai wahala nasan xan je mu yi, following Anty khadijah is always one of my worst night mare… beside Yayanmu is at home ai yana bacci, he will keep you company, you won’t be that lonely” khadijah tayi murmushi tace “Alright bye” daga haka baby ta fita, Anty khadijah na fitowa dakinta ta bude kofar dakin Aliyu a hankali dai dai lkcn da ya bude idonsa suka yi ido hudu, fuskewa tayi ta daure fuska ta shiga dakin ta tafi gaban madubinsa ta dau turarrukansa ta dinga fesawa irin shi ya kawo ta din nan, sannan ta fice daga dakin ta rufe masa kofa. baby ta ba handbag dinta da makullin motar tace “Gashi ku je ku jirani a mota da Iklima saura ku yi damben da ku ka saba kafin in fito” baby sai da taje ta fara yi ma yayanta sallama a dakinsa sannan ta sauka kasa, tana sauka Anty khadijah ta bude dakin babyn tana kallon khadijah dake ta gyaran kaya ta hade rai tace “Idan kin ga dama, kina gama gyaran kayan ki tafi ki kai ma Aliyu abinci don bai yi breakfast ba, ruwan Lipton din sa na nan a karamin flask na Babban flask ya kare” Khadijah tace “Toh Anty” ta maka mata harara tace “Kya nemi Antyn ki dai” daga haka ta juya ta fita ta rufe kofar. Khadijah na ji suka fita gidan a mota, ta ci gaba da gyaran da take a hankali har ta gama sannan ta fita, kitchen ta wuce don debar ma Ya Aliyu breakfast kamar yanda Anty khadijah ta ce mata, tsaye tayi inda karamin flask din yake ta kai hannu kan cabinet din kitchen din ta dangwalo wani garin magani da ta gani a xube wajen, ta dinga kallon bak’in maganin can ta tafi sink ta wanke hannunta, ta dawo ta dau napkin din kitchen din ta share wajen ta wanke napkin din a sink sannan ta shanya ta gama daura masa kayan break din a tray da karamin flask din ta fita xuwa dakinsa, kwance ta samesa idonsa biyu, ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace “Yayanmu ga breakfast din ka, in hada maka shayin” ya girgixa mata kai yace “Noo don’t worry xan yi da kai na, ke ba ki bi su ba?” Khadijah ta girgixa kai tace “A’a…” Shiru ya d’an yi sai kuma can yace “Toh ki je sanusi ya kai ki saloon kiyi gyaran gashin ki” turo baki tayi ta make kafada tace “A’a ni gashina bai yi datti ba Yayanmu, kuma on Sunday mumy ta kai mu ai” yace “Toh me ma ya hanaku xuwa islamiyya?” Ta wara ido tana murmushi tace “Ka mance yau Thursday” ya lumshe ido ya bude yace “Toh tashi ki tafi” mikewa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, bayan tafiyarta da kusan minti goma ya mike xaune a hankali yana son daurewa ya bar gidan ya tafi clinic, gaba daya ya rasa gane me ke damunsa, it seems he is sick, cup ya dauka ya debi ruwan Lipton dake flask kadan, sannan ya xuba madara da cube biyu na sugar ko bin ta kan Milo bai yi ba ya juya shayin da spoon ya ajiye ya huce, mikewa yayi ya shiga bathroom ya sake wanka sannan ya fito, ya dau wani kayan da xai sa ya ajiye saman gado ya xauna bakin gadon ya dau cup din shayin da ya riga ya huce ya kai baki ba tare da ya bi ta kan dankali da kwai dake rufe a plate ba…. Yana gama shanye shayin ya ajiye cup din. Kallon cup din kawai Aliyu yake bayan few minutes wondering is this really a tea he drank, cos even the taste… komawa yayi ya kwanta saman gado bayan kusan minti biyar ya rufe ido sosai, He just can’t imagine what is ringing all over is head a lkcn, ya sake mikewa xaune da sauri trying hard to control his self daga urge din da xuciyarsa ke masa, loudly xuciyarsa na bugawa sosai yace “Not… Iman” ya kai hannu da nufin sa kayansa ya bar gidan gaba daya amma ya kasa, komawa yayi kan gado yyi cike da karfin hali ya kwanta, jin sanyi na shigarsa ya rufa da duvet, dai dai nan aka bude kofar dakin ya juya da sauri, khadijah ce ta shigo rike da leda karami tace “Yayanmu ga shi sanusi yace in baka aiken da kayi masa daxu, naga drugs ne dama baka da lafiya ne?” Kin cewa komai yyi ya rufe ido kamar mai bacci, ta isa kusa da shi ta durkusa tace “Toh ka ta shi kasha Yayanmu” tana fadin haka ta fiddo duk maganin tana duba prescription amma bata ga ni ba, guda daddaya ta cire gaba daya hudun ta dau table water da ta gani dakin ta dawo gefensa tace “Ka tashi kasha Yayanmu” ya bude idonsa da ya kada yace “Ajiye ki fita” bai taba mata magana yanda yyi mata ba a lkcn amma a tunaninta ko rashin lafiyan ne, kamar xata yi kuka tace “Toh ka fara sha don Allah Yayanmu” lkci daya ya ji kamar an cire gaba daya sympathy dake tare da shi, Ya mike kamar wani xaki ya fixgota cikin tsawa yace “I said leave Iman” hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, cikin rawar murya tace “Ohk” daga haka ta ajiye masa magungunan cikin leda ta ajiye ruwan ma ta mike, da sauri ya jawota ta fado jikinsa ta xaro ido a tsorace tace “Yayanmu” ya rungumeta gam hade da lumshe ido muryarsa na rawa yace “I don’t want this to happen Iman, I….” Kasa ci gaba yayi jikinsa ya dau rawa, yasan he have tried for that long, the urge… He just don’t understand it, it’s unbearable…. It’s different. Aliyu never gave her a chance to raise any alarm duk da kokarin yin hakan da ta dinga yi, kai kana ganinta kasan bata taba tsorata da shiga tashin hankali irin na moment din ba, gashi yyi depriving dinta damar rokonsa ta kuma yi masa tuni da cewa ita marainiya ce ko xai ji tausayinta, domin kuwa ya rufe bakin ta, and that was how everything happened, tana ji tana gani Aliyu ya raba ta da pride dinta, daga nan da ta rufe ido bata sake budewa ba sai bayan wasu mintuna. Kwance ta ganta dakin baby an rufeta da duvet, ta dinga bin dakin da kallo a hankali kamar me son tuna wani abun, ta runtse ido ta dalilin sara mata da taji kanta ke yi sosai, bude ido tayi da sauri kuma a tsorace don a lkcn komai ya dawo mata, xata mike xaune taji wani xafi gaba daya jikinta, kara ta saki ba tare da ta shirya yin hakan ba duk jikinta na rawa tana kiran Ummanta, dai dai nan aka bude dakin, bata san lkcn da wani karfi ya xo mata ba tayi ignoring axaban da take ji ta mike a gigice tana neman sauka kan gadon cikin tashin hankali take cewa “Don Allah yaya Aliyu kayi hakuri ina rokan ka, wlh mutuwa xan yi, kar ka xo don Allah” ya isa har gabanta yana kallonta da idanuwansa da suka yi ja xata gudu ya rikota ya xaunar da ita gefen gado shi ma ya xauna ba tare da ya bari sun hada ido ba muryarsa na rawa yace “Don Allah ki yafe min Iman, sure I cheat you, but…” Kasa ci gaba yyi ya sake hannunta ya rike kansa da yyi masa nauyi hawaye na xuba idonsa, ita ma kukan take a raunane tana son tashi wajen amma ta kasa, sauka yyi kan gadon ya durkusa kan kneels dinsa hawaye na xuba idonsa ya daura kan sa kan kafarta trying hard to speak yace “Ki dubi girman Allah ki yafe min Khadijah, I didn’t do that intentionally, forgive me plss, I don’t knw wat came over me, ba halina bane Iman, don Allah ki yafe bi….” Kuka kawai khadijah take tana ja baya jikinta na rawa, cikin sarkewar murya tace “Na ji, amma ka tafi don Allah ina rokon ka, please go” ya fi minti biyar durkushe gabanta kansa a duke har lkcn hawaye ya ki tsaya masa, ya ji duk ya tsani kansa, of all people why Iman, cike da karfin hali ya mike ya fita dakin. Khadijah ta fada kan gado ta dinga kuka, tun bayan rasuwar Abbanta sai a lokacin ta ji ba ta son duniyar gaba daya, xuciyarta ya karaya taji ita ma da Allah ya dau ranta a lkcn ta huta. Bacci me nauyi ne ya dauketa afterward, bata tashi farkawa ba sai da su baby suka dawo misalin karfe biyar na yamma, ta dinga kallon baby da ta tasheta da idanuwanta da suka kumbura sosai, baby ta ja baya da mamaki tace “Iman, what’s wrong did you cried?” Hannu ta kai jikinta ta ji yyi mugun xafi, ta fita da sauri don kusan tare suka shigo gidan da Mumy, dakin ya Aliyu ta fara shiga ta ga baya nan, sannan ta sauka downstairs don har lkcn mumy da Anty khadijah ba su hauro sama ba, Anty khadijah duk ta gaji da xancen da mumy ke mata ta kagu ta wuce sama don kin xama ma ta yi a parlorn tana tsaye, da damuwa baby tace “Mumy kamar khadijah bata da lafiya….” Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tana kallonta tace “Me ya sameta?” Mumy kanta sai da ta kalli Anty khadijah, can Anty khadijah ta ankare ta tabe baki tace “Abun ka da xuciyar musulunci ban da haka ina ruwana, a kan yarinyar da ake min gori a gidan nan dubi yanda na xabura don ba ta da lafiya kamar iklima ce ba lafiya” mumy na kallon baby tace “Me ya sameta” baby tace “Nima ban sani ba, her eyes are swollen kuma jikinta yayi xafi sosai” mikewa Mumy tayi ta wuce sama, sai da Anty khadijah ta shiga kitchen ta dau flask din da ta xuba ruwa taji an diba sannan tayi murmushi ta bi bayan mumy da sauri, Cire bargon Mumy tayi tana kallon khadijah, ita kanta sai da ta tayi mamakin irin xafin da jikinta yyi ga wani shivering da take idanuwanta sun kumbura, Anty khadijah dake ta kallonta ta shimfida damuwa karara fuskarta tace “Me ya same ki haka” khadijah bata iya tace komai ba sai rawa da jikinta yake, Fita Anty khadijah tayi ta nufi dakin Aliyu da sauri ta bude, ganin baya dakin ta shiga don kara tabbatar da cewa ba xanin gadon da ta gani dakin bane daxu da ta shigo sannan ta fita daga dakin, Mumy ta kalli baby tace “Dauko min wayata” Da sauri baby ta fita sai ga ta ta dawo da wayar, Mumy ta shiga kiran Aliyu, yana gidansa kwance for the 1st time tun da Daddy yyi furnishing masa gidan, idonsa a lumshe suke ya bude a hankali jin karan wayarsa ya dinga kallon kiran ganin Mumy ce har ya katse, sake bugowa aka yi, yayi karfin halin mikewa don xaxxabi ne sosai jikinsa, ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga cikin sanyin murya yyi mata sallama, da damuwa Mumy tace “Aliyu where are you, Khadijah bata da lafiya sosai, ka taho yanxu idan ya kama ku tafi asibiti ne sai ku wuce” Da farko rasa abinda xai ce ma Mumy yayi lkci daya hawaye ya cika idonsa, har sai da tace “Hello Abuturrab, are you there?” Yyi karfin halin gyada kai yace “Xan taho yanxu Mumy” daga haka ya katse wayar ya ajiye ya rike kansa hawaye na sakko mishi.

Back to top button