Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 43

Sponsored Links

Suna shiga parlorn khadijah ta xauna kan daya daga kujerun ciki, Shaheedah ta ajiye shureim tana murmushi tace “Wai basa magana ne?” Khadijah dai bata san ko suna yi ba ko basa yi amma taji Nanny tace suna yi idan sun ga dama, ta dan yi murmushi tace “Ba sosai ba, har yanxu basu iya ba” Tasowa Sudais yyi ya dawo kusa da ita shureim ma ya sauka kan kujera ya bi twin din nasa, Sadeeq yace “Lallai, yayarku kadai ku ka sani kenan koh” Shaheedah tace “Dama mana” daki Sadeeq ya wuce, Shaheedah kuma ta nufi fridge ta bude ta dauko masu drink da ruwa ta daura kan tray da cups uku sannan ta dawo ta ajiye tana kallon khadijah tace “Ban ma san sunan ki ba” Khadijah tace “Sunana Khadijah” Shaheedah tace “Ayya, ni kuma Shaheedah” Khadijah na murmushi tace “It’s nyc meeting you Shaheedah” Shaheedah ta mayar mata murmushin tace “You too” abinci ta koma kitchen ta dauko a warmer da plates da spoon, khadijah tace “Lahh wllh mun ci abinci kafin mu taho Shaheedah” Shaheedah ta bata fuska tace “Saboda ke fa na yi girkin” Khadijah tace “Ayya da baki bai kan ki wahala ba, kin ga su ba cin abinci ma suke ba sai dai golden morn ko custard” Shaheedah tace “Toh sai in masu ai akwai custard din din ke sai ki ci wannan” da sauri khadijah tace “Kafin mu fito ba basu suka sha, ko kin yi baxa su sha ba da gaske” Shiru Shaheedah tayi kafin tace “Kenan dai baxa ki ci abincin ba Khadijah” Khadijah tayi murmushi tace “Toh xan ci Shaheedah” Shaheedah tace “Yauwa na ji dadi” daukan yan biyun tayi tace “Ku bar Anty ta ci abinci mu tafi ku gaida Mamata” Khadijah ta kalleta tace “Ayya mama na nan ne” Murmushi Shaheedah tayi tace “Idan kin gama cin abincin sai mu je ku gaisa” daga haka ta wuce da yan biyun dakinta, Shaheedah na rufe kofar tace “Mama dubi yaran nan masu kyau maa sha Allah” warce ta kira da mama dake xaune dakin kan darduma tace “Bakin naki sun iso kenan” Shaheedah tace “Ehh har da kanninta ma ta xo, ga su su taya ki hira xan kai ma sa abinci” Daga haka ta fita ta bar yaran a dakin. K’adan Khadijah ta ci tuwo da miyar ganyen da Shaheedah ta kawo mata, cin abincin take amma gaba daya hankalinta na kan yaranta da bata gani ba kuma bata ji motsinsu ba, tashi tayi daga karshe ta dau warmer din tuwon da miya ta wuce kitchen da su, ta wanke plate din da ta ci abincin da cup sannan ta fito parlor ta xauna, dai dai nan Shaheedah ta fito parlorn tace “Lahh har kin gama Khadijah, ko dai ba ki ci ba” Khadijah ta kirkiri murmushi tace “Aa na ci wllh, bacci suka yi ne?” Ita kanta sai da taji kunyar tambayar, Shaheedah tace “Aa suna gun mama ne, mu je ku gaisa tana daki” tashi Khadijah tayi tace “Toh” sannan ta bi bayan Shaheedah suka wuce dakinta, Shaheedah na shiga tace “Mama xa ku gaisa da khadijah” daga haka ta bar bakin kofar Khadijah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallon matar dake xaune kan darduma su shureim a kusa da ita, lkci daya taji komai nata ya tsaya ta kasa kwakkwaran motsi wajen da kyar cikin tsarkewar murya tace “Ummaa” Sai a sannan matar ta juyo da sauri ita ma jin muryar da ta dade tana muradin sake ji ko da a ranan da xata bar duniya ne, mikewa tsaye tayi tana kallonta cikin wani yanayi tace “Khadijah??” Shaheedah da ta saki baki tace “Lahh mama kin san ta ne dama?” Juyawa Khadijah tayi da sauri hawaye cike idonta ta bar bakin kofar, Kan kace me har ta isa gate ta fice daga gidan hawaye masu xafi na sakko mata, da sauri ta isa bakin titi ta tsayar da adai daita ta shiga, tana jin Shaheedah na kwalo mata kira alamar sun biyota amma taki waigawa tace mai adai daitan ya tafi, har khadijah ta isa gida kuka take cikin Napep kamar ranta xai fita, ta rasa dalilin kukan nata, taji xuciyarta yyi mata rauni ga xugin da ya fara mata, mai adai daitan a tuaninsa rasuwa aka yi mata ya dinga bata hakuri bai ma karbi kudin ba ta shige gida, nan parlor ta xube ta kara rushewa da kuka kamar xata tsaga gidan, Nanny ta fito a rikice ta shiga tambayarta me ya faru ina su Shureim sai a sannan khadijah ta tuna da yaran nata, Nanny duk ta rikice ta mike ta fita ta sake dawowa a rude tace “Khadijah tambayar ki nake ina yaran me ya same su, ina suke” Khadijah ta hade kai da kujera cikin rawar murya tace “Ummata na gani Nanny” Nanny ta tsaya kallonta kamar idanuwanta xa su fito, can ta durkusa kusa da ita da sauri tace “Umma? Ummarki dai? A ina kika ganta” Khadijah ta kara fashewa da kuka tace “A gidan da muka je” Nanny tace “Toh sai ta ce maki me, ko bata gan ki ba?” Nanny bata rufe baki ba sai ga Shaheedah ta shigo parlorn a sanyaye, khadijah na ganinta ta kara hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Shaheedah ta isa kusa da ita ta durkusa a hankali tace “Dama ke ce khadijahr da mama ke shigowa Nigeria saboda tun shekaru uku da suka wuce, dama ke ce khadijahr da mama ke yawan maganar ta a can kasar mu?” Khadijah ta dago hawaye wasu na bin wasu tana kallon Shaheedah, girgixa kai Shaheedah tayi tace “Allah sarki khadijah na samu labarin ki a gun mama tun ban yi aure na dawo kasar nan ba, Khadijah Mama ta shiga wani yanayi bayan rabuwar ku, ta je garurruka da dama na Nigeria tana neman ki, ta dalilin ki mama bata da isashen lafiya har yanxu, Wllh wannan xuwan ma tana sauka Nigeria Kano ta fara xuwa wai ko Allah xai sa ta gan ki, daga kano ta tafi Katsina sannan ta taho Kaduna duk wai ko xa ku hadu kafin ta taho gidana nan Abuja kuma gobe ma take shirin komawa kasar mu” Shigowar Umma parlorn ya sa Shaheedah tayi shiru tana kallonta, kana ganinta kasan ita ma tayi kukan, Umma ta karaso parlorn a sanyaye ta xauna kan kujera kusa da khadijah wasu hawayen na sakkowa idonta, Khadijah ta kasa kallonta ita ma tana hawayen, Cikin sanyin murya Umma tace “Ko da baxa ki saurareni ba Khadijah ina neman gafarar ki, ki yafe min, na maki abinda uwar da ta haife ki baxa ta maki, Khadijah don nace ki tafi ba har xuciyata nake nufin haka ba amma kika yi wucewarki kika saka ni cikin kunci da damuwa, duniyar tayi min xafi barin idan na tuna baki da kowa, ban yi ma mahaifin ki hallaci ba, but what will someone expect from a frustrated Mother, God knows i was frustrated…. Shi yasa nace ki tafi, amma ban taba tunanin xa ki tafi ba” sakkowa Kasa Umma tayi ta durkusa kusa da khadijah tana kuka tace “Ki gafarceni Khadijah…. Forgive me plss” Khadijah ta daura kanta a kafarta tana kuka sosai cikin rawar murya tace “Umma baki min komai ba, nima ki yafe min, I know i failed you, amma ba laifina bane Umma, ni ban taba iskanci ba, I was raped….” Umma ta dagota ta rungumeta tana controlling nata kukan tace “I thought as much daughter, na yanke hukunci cikin fushi da tashin hankali ne, na yarda da tarbiyar da na baki, Allah ya saka maki koma waye yyi maki wannan aika aikan, shi ma xai ga sakamakonsa tun a nan duniya” Sosai Nanny da jikinta yayi sanyi tayi murnan haduwar Khadijah da ummarta, ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tana gode ma Allah da ya bayyana ma marainiyar ummarta, Shaheedah da duk jikinta yyi sanyi ita ma ta ji dadin reunion din Aminiyar mahaifiyarta da step daughtern ta after three good years. Shaheedah ce ta fita karbo su sudais gun Sadeeq dake mota bai shiga gidan ba, a hankali tace “Dear kaga for ur sake, mama will be happy once again, tayi reuniting da daughter dinta” murmushin karfin hali yyi yace “Sure, but am still confuse ban gane komai a nan ba fa, khadijah dai nasan gidan wan mahaifinta is few houses away from ours, so ban san kuma meye relationship dinta da mama ba” Shaheedah tayi murmushi tace “It’s a long story, idan mun koma gida xan baka labarin dear” Sai kusan bayan Isha Sadeeq ya dawo daukan Shaheedah, Khadijah taki yarda Umma ta bi su don gani take kamar baxa ta sake kara ganinta ba. Da daddare suna xaune kan gado wajen karfe daya su Shureim na jikin Umma sun yi bacci, khadijah na bata labarin rayuwar da tayi bayan ta bar gida, tun farkon labarin har ta kawo karshe Umma kuka take, duk jikinta yyi sanyi don ta san duk ita ja ma khadijah duk abinda ya sameta, shiru ta yi tana tunanin me xata ma sudais kuma a ina xa ta gansa, khadijah da ke share hawayen ta cikin raunin murya tace “Umma har yau bai kara dawowa ba, i will never forget him in my life…” Umma ta jawota jiki tace “In sha Allah xai dawo wataran, he will come back to you daughter” Kai kawai khadijah ke gyada mata a xuciyarta tana addu’ar Allah ya gwada mata wannan rana, Umma ta katse silence da ya biyo baya tace “A ranan da kika tafi Khadijah babu inda ban fita nemanki ba tun ina yi da kafa har na koma abun hawa, sai bayan isha na dawo gida a lkcn ina addu’ar Allah yasa kin dawo sai na ga akasin haka, na shiga tashin hankalin da bana fatan in kara shigarsa har karshen rayuwata don nasan baki da kowa Khadijah, Wa ennan makiran dake gidan dama tuni sun sanar ma Alhaji kafin ma in dawo, ina shigowa kuma ya bani takardata kamar jira yake, hakan yasa naji bakin ciki kamar ya kashe ni domin, ce maki nayi ki tafi kar ki kashe min aure duk da bai kai xuciya ba sai gashi sakin ma na walakanci yyi min don ce min yi 1st thing da safe in tattara ina wa ina wa in bar masa gidansa, hakan kuwa aka yi don ban jira gari ya waye ba na fita neman wanda xai siya kayan daki na, ina siyarwa kuma kafin sha biyu na bar masa gidansa, da kudin kayan ba tafi Ethiopia… Bana son in dinga tuna yanayin da na shiga rashin ki Khadijah, ni dai kawai ki gafarce ni domin ni na ja maki komai da ban kai ki gun yakumbo ba da duk hakan bai same ki ba, ita kuma Yakumbo bani da abinda xance a kan ta yanxu domin kuwa ta riga mu gidan gaskiya” Khadijah ta dago da sauri tana kallon Umma tace “Umma yakumbo ta rasu?” Umma tace “Ta rasu kusan shekaru biyu kenan, electric ring ne ya ja ta har lahira, wai ta sa ruwan xafi a daki” jikin khadijah yyi sanyi ta ma rasa abinda xata ce, bayan wani lkci tace “Allah ya ji kanta” Umma tace “Ameen” a hankali khadijah tace “Umma na ki yafe min” sai kusan karfe uku suka kwanta, washegari da safe Umma tayi ma su Sudais da Shureim wanka suka fito parlor, Nanny da ta gama breakfast a kitchen ta fito ta gaida Umma, Umma ta amsa mata da murmushi nan tayi mata godiya kan tsayawa ma khadijah da yan biyun ta da tayi all this while, satin Umma daya a gidan tace ma khadijah xata koma kasar su amma xata dawo, kuka khadijah ta fara yi tace “Umma kina son ki tafi ki kara bari na ne” Umma tace “Noo khadijah xan dawo, ki bari in je in yi sallama da dangina sai in dawo mu xauna, amma fa baxan xauna wannan gidan ba sai dai in kama mana haya a Kaduna, wannan kuma ki rufe masu kawai” a hankali khadijah tace “Kaduna Umma?” Umma tace “Ehh” sauke idonta Kasa tayi bata ce komai ba, Umma tace “Forget ur past Khadijah, life moves on, don wani baxa ki ki xama a garin ba Beside gari me girma ma a ina xaki gansa?” Kai kawai khadijah ta gyada mata, wannan kuma shine mafarin komawarsu Kaduna, suka bar gidan da Sudais ya mallaka ma twins dinta a Abuja, life in Kaduna was smooth for them, sai dai khadijah ta kasa kwantar da hankalinta ta xauna lafiya a garin, ko yaya sai taji abinda ya faru shekaru uku na dawo mata duk da a kinkinau gidan da Umma ta kama masu haya yake, Tunanin da ta kasa cirewa a ranta yasa ciwonta ke yawan tashi wani lkcn har da kwanciya asibiti, hakan ya dinga daga ma umma hankali ta shiga tunanin to wani garin kuma xa su koma, don gaskiya bata son kano, a hankali dai khadijah ta hakura bayan watannin su shidda Kaduna. Kasuwanci sosai Umma ke yi don har Dubai tana fita Allah ya dubeta lkci kankani dukiyarta ya bunkasa, yanda take ji da jikokin nata ko Khadijah bata samu wannan gatan ba, tamkar ta mayar da su ciki take ji, su ma kuma haka suke sonta don ko da yaushe suna manne da ita, duk anguwan babu wanda yasan yaran Khadijah ne yan biyun masu shiga rai duk tunaninsu umma ce ta haifesu Nanny ma na tare da su har lkcn, kuma kusan tare da ita Umma ke fita waje ta xama kamar yar uwarsu, yanxu kam su sudais da baki ya bude basa gudun uwar ta su da suka dauka yayarsu ce Umma kuma Mumynsu, a haka Umma ta yi iya kokarin ganin khadijah ta samu admission a University of Cambridge dake UK, Khadijah bata ji dadi da farko ba ganin pharmacy suka bata don ba shine burin sudais a kan ta ba, amma umma tayi convincing dinta to go for it, shine ta tafi a haka, farkon xuwanta kasar tare da Umma Nanny da yan biyun ta suka taho suka mata sati sannan suka koma nan kuma ta mayar da hankali tana karatu ba ji ba gani domin xama qualified pharmacy, and then….. 1st khaleel ya sa ta gaba a kasar, that not being enough sai gashi ta hadu da wanda bata burin sake gani har karshen rayuwarta, why????

Back to top button