Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 4

Sponsored Links

By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

4……

Ta fi minti biyar a tsaye duk jikinta a mace, tunani daya ya xo xuciyarta a lokacin and that is ta bar apartment din ta koma gun Vanessa da xama gaba daya har ta samu wani gidan, ta juya ta kalli gas din kitchen din taga ya kashe, kamar mara laka ta fito parlor ta karasa kofa ta sa key, xaunawa tayi parlor har lkcn tana ganin abun kamar a mafarki, ita fa yanxu bata ga namijin da ya isa ya takura ma rayuwarta, ba ayi namijin nan ba ko waye shi kuwa, tunanin hakan yasa ta yi murmushin takaici hade da jan tsaki ta mike ta wuce daki, nan ma dai xaunawa tayi gefen gado ta kasa daina mamaki, kiss kuma? how dare him kiss her? Haka nan kawai yayi kissing dinta kuma ta kyalesa, hawaye ne ya cika idonta tuna hakan da tayi, ca tayi masa ita gantalalliya ce? Ko kuma xaman kanta take a k’asar? ta xamo kasa ta jinginar da kanta da gado xuciyarta na kuna, to yanxu wa xata kai ma kukanta a kasar nan, nobody in particular, Vanessa won’t take this as anything ko ta gaya mata ma dariya xata mata, Yusuf?? ji tayi ranta yyi wani mugun baci da ta tuna yaren da yyi mata, wai a hakan shi bahaushe ne ko kuwa Hausa kawai ya ji, abinda ta kasa ganewa kenan, ta kuma jan tsaki a xuciyarta tace ai sai dai kawai ya ji Hausan don in har dai shi Afuno ne he is nothing but a disgrace to Hausa and Hausa land as a whole, infact ta ma san ba bahaushe bane…. har kusan goma tana xaune kamar mara abun yi, xuciyarta dai ya kasa dawowa dai dai, ta Dade ranta bai baci ba irin na yau, can dai ta kuma jan tsaki for the countless time tace “Sai nayi maganinka kafin in bar gidan nan in sha Allah, you can’t just put ur filthy mouth in mine and go scot free….” daga haka ta mike ta shiga bathroom, wanka ta yi ta dauro alwala ta fito ta yi shafe shafenta ta xura doguwar Riga ta tada sallahn Isha, ko da ta idar ta shafe addu’o’in da tayi ta jawo wayarta don sau biyu ana kira tana sallan, Vanessa ce ke kiranta, ta shiga kiranta baya, Vanessa na dagawa tace “Hey love, you are still nt yet back” Khadijah ta kalli agogo a hankali tace “It’s late Vanessa, I will come over tomorrow” daga haka Vanessa tayi mata sai da safe ta katse wayar, sai a sannan taji ta fara jin yunwa, ta mike ta fita xuwa kitchen don duba girkinta na daxu, tsaye tayi ta kasa kunne jin kamar muryar mace a kitchen dinsa da yake ko ina was very silent, a hankali ta karasa jikin window ta kafa kunne, nan ko ta kara tabbatar da hakan, muryar mace take ji, ta rike ha6a da mamaki k’ana ta kyabe baki ta dau plate ta debi abincin da xata diba ta fita kitchen din, tana gama ci ta tafi daki ta hada gaba daya kayan sawanta a jaka biyu, tana shirin kwanciya wayarta yyi kara, ta dauka tana kallon screen din sannan ta xauna gefen gado ta daga kiran hade da sallama, a hankali tace “lafiya lau Umma ya gida” Daga daya bangaren warce ta kira da Umma tace “Alhmdllh, na ma yi tunanin kin kwanta, ya karatun” tace “Alhmdllh Umma, yanxu xan kwanta” Umma tace “Toh Allah ba mu alkhairi, a dai dinga kula sosai kinji” cikin sanyin murya tace “Toh Umma” daga haka suka yi sallama ta katse wayar, kwanciya tayi hade da rufe duk jikinta da duvet har lkcn ranta ba dadi. Tun da ta idar da sallan asuba bata koma ba kasancewar da safe take da lectures, ta yi wanka ta wanke bathroom dinta sannan ta fito xuwa kitchen don tsaftace sa shi ma, wanke duk utensils da ta 6ata jiya tayi sannan ta hada bin din gaba daya a kwandon da aka tanadar don haka, Hijab ta koma ta xura kan yar rigar jikinta ta dawo kitchen din ta bude kofar ciki ta fita don disposing sharan dustbin, still tayi ganinsa a wajen, ya ajiye weight din hannunsa tana ganin haka ta juya da gudu ta koma kitchen ta rufe kofar da makulli hannunta na rawa, tsaye yayi jikin window din kitchen dinta yace “Ga Beast ko monster koh?” Ko kallonsa bata yi ba, ta kashe fitilar kitchen din ta fita parlor ta yi banging kofar da karfi ta rufe. Yayi wani murmushi yana share xufar forehead dinsa, Komawar da ba ta yi kitchen din ba kenan har ta gama shirin makaranta, Abaya ne baki da mayafinsa sanye jikinta, duk da yunwar da take ji haka nan ta dau jakarta ta nufi kofa, a hankali ta murda makullin ta bude ta leka waje sannan ta fito tana karanto addu’a a xuciyarta, ta gama rufe kofar kenan, wata baturiya da baxata wuceta ba ta fito daga apartment dinsa, ba karamin faduwa gabanta yyi ba don a tunaninta shine, ‘yar riga ce iya cibi da wando jikin baturiyar sai yar karamar jaka da litattafai a hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba har ta sauka d’an stairs din dake wajen, taji yarinyar tace “Good morning” yi tayi kamar bata ji ta ba tayi wucewarta, taji yarinyar na cewa “Is she having difficulty in hearing?” sai a sannan Khadijah ta gane shi ma ya fito kenan, hakan yasa ta kara saurinta, taji yace “I think so” tuni ta fice daga gidan ta tsayar da cab ta hau ta gaya masa inda xa ta, ya ja cab din, a xuciyarta tace In sha Allah ma this is the end, ba lallai ma ta kwana gidan ba yau, don tana dawowa makaranta dama fiddo kayan ta xata yi ta yi wucewarta gidan Vanessa, but she promise before leaving xata koya masa lesson xata gwada masa cewar ba ko wace mace ce sha sha sha kamar sa ba, abinda ta lura da xaman k’asar shine gwara a hadaka da bature waje daya sau dubu a kan wanda ku ka fito k’asa daya. Xaune Khadijah take tare da Vanessa da wata course mate dinsu Angela, sai wata Maryam ‘yar Nigeria kamar ta amma kuma a nan UK aka haifeta, ko kadan Khadijah bata yarda sun saba da Maryam ba, hasalima gaisuwan kirki bai hadasu, ita kanta Maryam bata sake da ita ba, amma kilan hakan na da nasaba da cewar ba course daya suke ba, duk da haka dama can yarinyar bata ma Khadijah ba, ba wai tana da wani aibu bane ko wani abu, kawai she just don’t like her ta rasa dalili kuma, don so tari ma idan ta ganta sai taji faduwar gaba, sannan ganin ta na tuno mata da wani abu da ba ta son tunawa a rayuwarta gaba daya, yanxun ma su kadai suke hirar su, ita dai tana ta danna wayarta kanta a sunkuye, duk ta kagu Vanessa ta tashi su tafi, dama can Angela ba kawarta bace, don she is too lousy to be kept as friend, d’an gaisuwar da suke ma da ita ta dalilin course dinsu daya ne, gajiya tayi daga karshe ta mike ganin Vanessa bata da niyyar tashi da halshan turanci tace mata xata je can gidanta ta dau kayan da xata dauka sai su hadu a can gida, Wato gidan Vanessa din, Vanessa tace to sai sun hadu, daga haka ta fara tafiya, Angela tace “See yahh tomorrow Pretty” sunan da wasu ke kiranta da shi kenan a makarantar, Juyawa Khadijah tayi ta kirkiri murmushi tace “Sure” daga haka tayi wucewarta Maryam ta bi ta da kallo. Karfe biyu da yan mintuna ta isa gida, ta fito ta ba mai cab kudinsa, a hankali take jin faduwar gaba har ta shiga ciki tana kallon parking lot ta ga bbu motarsa, ajiyar xuciya ta sauke ta nufi flat dinta da sauri don ta yi abinda ya kawota ta bar gidan, da d’an mamaki take kallon farar matar dake tsaye b’akin apartment dinsa matar na rike da wata kyakkyawar yarinya kamar ta, lkci daya kuma tana kuma danna wayar hannunta, Khadijah bata sake kallonta ba ta shiga kokarin bude apartment dinta, a hankali matar tace “Hi” sai a sannan ta juyo ta kalli matar, ita dai matar ga ta kamar fulani kamar kuma balarabiya, idanuwanta kuma kamar na neighbor dinta, Khadijah ta dauke kai tace “Hello” matar tace “Plss Dr Ayman, will he be back anytime soon?” Khadijah ta mata wani kallo a takaice tace “I don’t knw” Matar tace “Really? And I have being Calling but I can’t reach him” Khadijah da har ta bude kofar ta tace “Hard luck” daga haka ta shiga ciki sai kuma ta juyo suka hada ido da cute babyn hannun matar, kasa rufe kofar tayi a hankali tace “Or you go come back, may be later” matar tace “Am from a far place, and he knws I will be here” Khadijah ta rasa abinda xata ce, can dai ta dauke kai ta juya ba don ranta ya so ba kuma don tausayin babyn hannun matar tace “If it’s ohk… u can come in and wait him” daga haka ta shiga parlor matar tace “Alryt Thank you” ta shigo parlorn ta xauna, Khadijah ta bude fridge ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye mata, matar ta d’an yi murmushi tace “I am fatima Ayman” kallonta Khadijah tayi na yan sakwanni kafin tace “Am Khadijah Muhd” Matar da ta kira kanta da fatima tace “Ohh that’s nyc, from which country?” Khadijah tace “Nigeria” d’an buda ido fatima tayi tace “Tribe” Khadijah tace “Hausa Fulani” Fatima tace “Waow ashe Hausa ce ke sister” Khadijah ta kalleta tayi murmushi tace “Ehh” Fatima tace “Allah sarki, amma naji dadin haduwa da ‘yar uwata daga Nigeria, na xo nan last 3 weeks but kamar baki nan” Khadijah tace “Eh naje gida ne” Fatima tace “Maa sha Allah, tare da mai gidana muke ya xo wani aiki a nan shine nace ya ajiye ni kawai mu gaisa da yayana tunda yau xa mu koma, kuma fa na sanar da shi yayan nawa xan xo amma dubi yanda ya shanya ni a waje” murmushi kawai Khadijah tayi ta amshi babyn hannun ta tana kallonta tace “Ya sunanta?” Fatima tace “Iman….” Lkci daya murmushin dake fuskar Khadijah yyi fading jikinta yayi sanyi……

*Haske writers association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

Back to top button