Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 54

Sponsored Links

A hankali khadijah tayi picking wayar ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren ya amsa yace “Ya kike Amira?” Khadija tace “Alhmdllh ya aiki?” Yace “Lafiya lau, account number ki xa ki turo min yanxu” shiru ta yi na wani lkci kafin tace “Barrister…. Shureim fa yana da kayan sanyi, wllh you shouldn’t bother….” Katse ta yayi yace “I am not asking for you opinion Khadijah” a hankali tace “Toh shkkn, ya Amira fah?” Sudais yace “Tana gun ummanta” bai karasa maganar ba ya ga jiddah tsaye kusa da dinning din da yake xaune tana kallonsa, ya dauke kansa yace “I will call you later Amira” katse wayar yayi ya ajiye, jiddah tayi dariya tana tafe hannu tana masa wani kallo tace “Cin amanar har cikin gidana Aliyu?” Sudais bai kalleta ba balle ya tanka ta, lkci daya idanuwanta suka kankance tace “Toh ko ma wace yar iskar ka samu wlh wlh sai tayi da ta sanin sanin ka a rayuwar ta, sai na nuna mata tayi kadan tayi kishi da ni, ba ma xai yiwu bane, mu xuba da ita sai dai idan ba mijina take cusa ma kanta ba” mikewa yayi yana kallonta yace “Wannan da kike gani wllh ta fi ki k’ima a idanuwana Jiddah, kuma kina nan xaki ga ta shigo gidan nan ta koya maki yanda ake kula da miji” bai sake sauraranta ba ya bar parlorn, jiddah ta kasa tsaye gu daya, ta ja kujera ta xauna da kyar xuciyarta na tafarfasa, lkci daya tayi wani murmushi tace “Babu boka babu malam, amma kai xaka bata shawarar ta rabu da kai, mu dai je xuwa, da kuluwa take xancen” Har khadijah ta iso gun motar khaleel idonta na kansa, shi kuma yana jingine jikin motar yana danna waya, bai san ta iso ba kawai kamshin ta ya ji, ya daga kai yana kallonta, a hankali tace “Good evening” ya mayar da wayar aljihunsa yace “Ya lectures?” Tace “Alhmdllh, karfe nawa su Shureim ke tashi?” Ya buda ido yace “Ke fa yarinyar nan baki da kara” turo baki tayi tace “Toh me nayi, am just asking” yyi murmushi yace “Daga nan xa mu dauko sa, yanxu suke tashi su ma” ta karasa ta bude front seat ta shiga, shi ma ya shiga motar ya tada suka bar wajen, har suka iso makarantar shureim khaleel bai ce komai ba ita ma haka, ya bude motar ya fita, ba a dau lkci ba suka dawo tare da Shureim, xagayowa Shureim yayi ya bude inda khadijah take xaune ya rungumeta yace “Anty good afternoon” ta shigo da shi cikin motar ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa da murmushi tace “How you sweetheart?” Yace “Fyn Anty, I love the schl, I wish Sudais will come here also, am really missing him” Khadija bata ce komai ba, inda sabo ta saba, don bbu ranar da xai wuce Shureim baxai mata xancen Dan uwansa ba, he is always wishing Sudais is with him, lkci daya chocolate da Aliyu ya bata ya fado mata, ta bude jakarta a hankali ta fiddo chocolate din ta mika masa, karba yyi cike da jin dadi yace “Waow, Anty ke kika siya min?” Girgixa masa kai tayi tace “No” ya wara ido ya juya yana kallon Khaleel dake driving yace “Uncle kai ka siya min?” Khaleel ya kallesa yyi murmushi yace “No bani bane” Shureim ya mayar da dubansa kan Khadija yace “Toh Anty waye ya siya min” Khadijah tace “Idan baxa ka ci ba bani in cinye” Shureim ya bude chocolates din yace “Noo Anty ina so, ai irin wanda kind uncle din nan yake ba mu a gidansu maman nan ne, he told me his name is Dr Aliyu, Anty ina son a kai ni gidansu a Nigeria” Ita dai khadijah kallon yaron kawai take, ya gutsura ma khaleel ya mika masa yace “Uncle taste it” khaleel yyi murmushi yana girgixa kai yace “Noo thanks son, cinye abun, ko Anty kar ka ba” dariya yaron yayi bai ce komai ba, can ya kalli Khadija, alama yayi mata da ta bude bakinta, tayi murmushi ta bude masa bakin ya sa mata chocolate din a hankali yana satan kallon Khaleel. Suna isa gida bayan khaleel yyi parking khadijah ta bude motar ta fito tare da Shureim tana kallonsa murya can kasa tace “Thank you” fitowa yayi yana mimicking din muryarta yace “Thank you” daga haka ya rufe motarsa, hararansa ta fara yi sai kuma tayi murmushi ta wuce apartment dinta rike da hannun Shureim, ya jingina da mota ya rungume hannayensa ya bi su da kallo. Tun da Khadijah ta fito daga lectures yau take xaune cafteria ta rasa dalili, har lkcn lectures din karfe biyu yyi tana xaune gun bata tashi ba, Maryam ce ta shigo cafterian tare da wata kana ganinta kasa yar Nigeria ce, Maryam na ganin Khadijah tayi murmushi tace “Khadijah kina nan ashe, ya lectures?” Khadija tace “Alhmdllh ya naki?” Maryam tace “Alhmdllh” Maryam ta kalli yarinyar dake gefenta tace “Deejah meet ur namesake Khadija, tana studying pharmacy ne a nan, she is also a Nigerian from kaduna” Warce Maryam ta Kira da Deejah tayi murmushi tace “Its nyc meeting you namesake” Khadija tayi murmushi sosai tace “Nyc meeting you too” gun Khadija suka xauna su biyun, Maryam tace “Sun xo hutu ne nan da kanwarta shine na shigo da ita taga Cambridge” Deejah na kallon Maryam tace “Khadijah tana min kama da Safeenah, ko ke baki gani ba” Maryam ta kalli Khadijah da kyau, sai kuma tayi dariya tace “Suna dai yanayi ba kama ba, and the nose…” Deejah tace “Exactly, dama Ammi xata ganta cewa xata yi Safeenah ce” ita dai Khadijah bata ce komai ba banda murmushin da take yi, haka kawai taji tana son Deejah…. drinks da snack Maryam ta sa a kawo masu su uku, Maryam na shan drink din gabanta tace “Deejah wai me yasa jawahir ta ki biyo mu?” Khadijah ta daga kai tana kallonsu, Deejah ta tabe baki tace “Kilan kar su hadu da Dr Ayman” Maryam tace “Tab, Ayman sau biyu yake shigowa makarantar nan a sati, Mondays and Thursdays, I think ranakun yake nasa karatun” Maryam ta kalli Khadijah tace “Kingakiwa neighbor dinsa ce Khadijah fa” Deejah ta kalli Khadijah da sauri tace “Haba dai” Maryam tayi dariya tace “Wlh, ranan da naje gidanta tare da frnds dinmu na gan sa, yace min nan yake” Deejah tace “Wani anguwa kenan?” Maryam ta fada mata anguwar tana cin snack din hannunta, Deejah tace “Ayya, daxu dai naji da suka yi waya jawahir ta bashi address yace xai je anjima da yamma” Maryam tace “Gidan mu?” Deejah tace “Sure” Maryam tace “Ohk ai gwara dai ya je” Khadijah ta mike tana murmushi tace “Maryam xan shiga lectures yanxu” Maryam tace “Haba to baki dau snack din ba ai da drink” Khadija ta kirkiri murmushi ta dauka tace “Toh nagode” daga haka ta bar cafteria din bayan tayi ma Deejah ma sallama, Deejah ta bi ga da ido, kafin ta kalli Maryam tace “Maryam joke apart wllh kamar Safeenah, idan kin lura har da Maimoon ma suna yanayi, Maryam tace “A coincident” wani gun Khadija ta tafi ta xauna don sun cika mata kunne da surutu ne gaskiyar magana. Tana ta xaune nan har khaleel ya kirata bayan kusan awa daya, tana ta kallon Kiran kafin ta daga yace “Are you done with lectures Khadijah?” Girgixa kai tayi tace “No, idan na gama xan taho gida, kawai ka tafi” yace “Karfe nawa xa ku gama?” Turo baki tayi da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace “Anjima” yace “Toh Ina jiran ki” daga haka ya katse wayar. Karfe hudu saura Khadijah ta isa gun da Khaleel ke jiran ta, fuskarta daure ta bude motar a hankali ta shiga, yana kallonta yace “Ya lectures?” Kamar ana tilastata tace “Fyn” sai bayan da suka bar cikin makarantar yace “Wa ya bata maki rai?” Shiru tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba har ya isa schl din Shureim ya fita ya daukosa ya dawo sannan suka dau hanyar gida, a waje yyi parking yana kallon Khadijah da ta bude motar ta fita, Shureim ma ya fito, yace “Am going somewhere now, sai na dawo” Khadija ta d’an buda ido tana kallonsa tace “Gun jawahir din ne somewhere??” Kallonta ya dinga yi da mamaki, ta tabe baki tace “Wai somewhere….” daga haka ta kama hannun Shureim suka wuce ciki, shafa kansa yayi ya tada motar yayi reverse ya bar wajen. Da daddare Khadijah na parlor aka danna bell, ta mike ta isa gun kofar tace “who is there” yace “Somebody” bude kofar tayi tana kallonsa ya mika mata ledan hannunsa yace “Ki ba Shureim?” Bata karbi ledan ba tace “Yayi Bacci” yace “Toh ki ajiye masa” Bata yarda ta kallesa ba ta amshi ledan daga haka ta rufe kofarta. Washegari da sassafe Khadija ta fito apartment dinta tare da Shureim da tayi ma Shirin makaranta, ganin waje xa su fita Shureim yace “Anty baxa mu jira uncle ba yau” hararansa tayi bata ce komai ba har suka fita ta tsayar masu da cab, sai da ta fara dropping dinsa schl sannan ta wuce nata makarantar. Tare da su Vanessa suka fito daga lectures misalin karfe sha biyu, tun daga nesa ta hangosa da wani bature suna tahowa, har ya iso inda suke xaune bai gansu ba yana magana da baturen Khadijah ta dinga kallonsa har suka wuce, still ta bi sa da ido, muryar Vanessa ne ya dawo da ita tana cewa su je su ci abinci, mikewa tayi a hankali suka bar wajen xuwa cafterian da suka saba xuwa, xaune ta ga Aliyu da Baturen a ciki, suna shigowa kuma ya ganta, ta dauke idonta daga kallonsa bayan sun hada ido, waje daya suka xauna tare da su Vanessa, Vanessa tayi masu ordering abinda xa su ci, drink kawai Khadija ta sa aka kawo mata, duk suka gama cin abincin Vanessa ta biya bill sannan suka mike, Khadijah dai na xaune bata tashi ba, Vanessa tace “Ain’t you attending the next lecture?” Khadijah tace “I will be going home soon” Tana kallon su Vanessa suka wuce, dai dai lkcn da Baturen dake tare da Aliyu ya mike shi ma ya fita, tasowa Aliyu yyi ya dawo inda take ya ja kujera ya xauna yana kallonta yace “Good afternoon” ba tare da ta kallesa ba tace “Same….” Ya shafa kansa yace “Ya Shureim?” Tace “Yana schl” yace “Ohk kin gama lectures yau ne?” Girgixa kai tayi tace “Aa xan wuce gida ne” yace “Ohk, yanxu?” Sai a sannan ta kallesa tace “Soon” yace “Alryt if you are ready mu je sai in yi dropping din ki” tace “I prefer cab” yace “Ohk then,” wayarsa ya mika mata yace “Sa min digit din ki anjima da yamma xan kawo maki sakon Shureim or I give Dr.. Ayman, Maryam tace min same house ku ke da shi, and I saw him a gidanmu jiya” Khadijah bata ce komai ba da farko, can dai tace “Sakon me?” Yace “Shine xan bada a kai maki ai” Ta Girgixa kai ta karbi wayarsa ta na sa number ta tace “You call me instead” daga haka ta mayar masa da wayarsa, ita ta fara mikewa kafin shi, ya bi bayanta suka
fita cafterian, sai da suka isa gun motarsa ya kalleta yace “Let me drop you Iman”

Back to top button