Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 19

Sponsored Links

BOOK 1

بسم الله الرحمن الرحيم 💖💖………

Free Page 19 🦋

A hankali yake bude kyawawan idanuwansa da suka kada sukai ja, dafe goshinsa da ke tsananin sara masa yayi tare da mikewa zaune , bin dakin yake da kallo ta ko ina kafun ya dawo dashi kan hannunsa me ciwo, abubuwan da suka faru dazu ne suke dawo masa, sosai jijiyoyin kansa suka kara mikewa , ganin yana kokarin sawa kan sa wani ciwan kai ya mike tare da shiga toilet,ko kayan jikinsa be cire ba haka ya sakar wa kansu ruwan sanyi, sai faman sakin ajiyar zuciya yake, ya dade tsaye cikin ruwan kafun ya fito daga cikin toilet din , gashin kansa da ke faman d’igar da ruwa ya taba kafin yashiga wata door dake degensa , kusan awa daya da yan mintuna ya fito cikin sabuwar shigarsa, ash din Riga ce a jikinsa sai farin wandon da yasa, cikin sa sai faman tashin daddadan kamshin turaren sa yake, duk da yana yin da yake ciki ba karamin kyau yayi ba musamman gashin kansa da se faman kyalli yake , hatta ciwon hannunsa ya sake masa dressing kafin ya dauki wayoyinsa ya bar dakin , a kofar part din sa ya tarar da zaki sai faman kai kawo yake , Wanda ya ganine yasashi sakin ajiyar zuciya tun dazu yake tunanin ya koma ya duba sa amma yana shakkar shiga, ganin ya fito da kansa yasashi ajiyar zuciya , sau daya king ya kallesa tare da dauke kansa yana lumshe ido, wata hadaddiyar Ferrari la ferrari ya dakko sai faman kyalli take, ganin hakan yasa bodyguards dinsa matsowa, hannu daya kawai ya daga musu tare da nufar motar da zaki yayi Parking, cikin sauri daya daga cikin bodyguard dinnan ya bude masa kofar, bai ce komai ba sai shigewa dayayi, bayan ya kulle kofar sara masa sukai gabaki Dayan su kafun zaki ya tayar da motar tare da barin gidan gabaki daya , lokaci zuwa lokaci yakan dago idanuwansa ya kalli king da tun shigowarsa motar kansa yake a sunkuye kwata kwata ransa ba dadi , ya dago da niyar kara kallan sa yaci saukar muryarsa a bazata “ what happened “, ya gane me king ya ke nufi, be bata lokaci ba ya zayyane masa tun shigowarsa dakin har fitarsa saidai ya boye masa shakesan da yayi duk da yasan zai iya gane hakan.kara lumshe idanuwansa yayi sosai yake jin zuciyarsa wani irin amma a zahiri ko gezau bayayi har suka karasa katafaran asibitin Al_nahyan .

➰➰➰➰➰

Bata dau dogon lokaci ba , sai gata sun dawo ita da bintalo da sai faman ja mata Allah ya isa take a haka har suka kusa zuwa inda bukkar bokannan yake kafun tayi shiru, sai faman zare ido dake , dan ba karamun azaba Tasha ba a hannunsa, yana ganinsu ya fara babbaka dariya take da sudar baki kamar wani maye, jikinsa sai faman tashin wari yake .kara babbakewa da dariya yayi “kinsa mu duniya kamar yadda kuke so, burikanku zasu cika kamar yadda nayi muku alkawari, ayukanki da akai miki na baya bazasu taba fito wa fili ba hhhhhh” ya karasa tare da sakin sautin dariya Mara dadin ji,nannauyar ajiyar zuciya Dije ta sauke tana jin wani farincin na ratsata ta ko ina, bintalo na gefe jin ta take kowama zata iya takawa , sai faman washe baki take, kallansu bokan nan yayi tare da jefowa Dije wani magani, “ga wannan maganin kije ki zuba musu a duk inda kika san zasu taka, kada ki kuskura ki dawo nan wajen batare da kin cika aikin nan va,maza ki tafi”saurin daukar maganin Dije tayi sai faman Godiya take masa, tashi sukai da niyar tafiya ita da bintalo ya dakatar dasu”ke kadai zaki tafi, ita anan zaki barta sai kin dawo sai ku tafi a tare , Inba haka ba aikin da kuka fara zai karasa rugujewa da zarar kun isa wajan”, ko karin rike Mata hannu bintalo take bokannan ya daka masu tsawa” ku bace mun da gani “,hakuri Dije ta shiga bashi, bata tsaya sauraran bintalo ba tabar wajan ko tsoron halin da zata shiga batayi,tana fita bokan nan ya daka tsawa” zonan “ , jiki na rawa bintalo ta nufeshi, har kwalla ta fara tsoran ta karyace ze kuma tabata , bata karasa zancan nata ba taji razananniyar muryarsa” zauna anan “, inda ya nuna matane yasata sakin kuka , tsawar da ya daka matane yasa ba shiri ta zauna akan cinyarsa da ya bude,matseta yayi sosai a jikinsa yana shin shinarta, daga nan komai ya canza salo, sosai bintalo Tasha wuya a wajansa, ihu kawai take dan ji tayi azabar da taji yanxu yafi na wancan lokacin , kuka kawai take amma ko kezau bokannan beba sai da ya tabbatar ya biya bukatarsa sannan yayi jifa da ita har lokacin Dije bata dawo ba , ganin hakan yasa bintalo daukar hijabinta tare da rugawa a wuje sai a hanya tasaka hijabin sai faman tsine wa Dije take .

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Zazzaune mutanan gida suke duka a falon dada , king ne kawai babu, zoya na gefan tahee yau sai faman hira take mata ita da ihsan , yan matan ma kowannansu na zazzaune a falon , amrah da sumayya sai faman harara juna suke batare da kowa ya hankalta dasu ba, musamman amrah da lokaci zuwa lokacin takan Kure tahee da kallo, ita kadai tasan abunda take rayawa akanta. Mikewa zoya tayi , aunty tahee please cakes dina zaki dakko mun kinji,jinjina mata kai tahee tayi tare da mikewa , kama hannunta zoya tayi suka soma tafiya, kallansu abeey yayi” yarana ina zuwa kuma “ sun kuyar da Kai tahee tayi “dama zoya tace zan dakko mata abune “, hararar zoya ummey tayi, kin kallanta zoya tayi tana buya bayan tahee, batace musu komai ba shima abeey da ammi murmushi kawai suke , su mamy kuwa kowannansu murmushin ya’ke yake saki, can dining su tahee suka nufa inda cakes din suke dayawa a ajje, kallanta tahee tayi “ wanne kikeso a ciki” wani me kalar chocolate ta nuna mata, daya daga cikin kankanin plate din tahee ta dauka tare da zuba mata chocolate cake din”, har tun juya da niyar komawa kuma sai tahee ta tsaya tare da komawa, cakes din ta zuba cikin kananun plates din tare da jerasu kan babban tray a haka harta karaso falon da suke zaune kowa sai binta yake da kallo, inda su dada suke zaune ta nufa tare da ajje musu tray din, babu Wanda be yi murmushi ba ganin abinda tayi, sosai ta burgesu musamman abeey da dada dake faman sakin murmushi, murmushin jin dadi uncel salim ya saki”mun gode sosai kuwa daughter , Allah yayi albarka “sosai kowa ya nuna jin dadin musamman dada da sai faman shi mata albarka take, abeey ne ya kalleta cikin zolaya yace “an kawo mana abun turawa daughter saura abunda sha”, murmushi ta saki tana sun kuyar da kanta , “tom bari na dakko muku” ta fada tana mikewa har lokacin zoya natare da ita kowa na mamakin sakewar da tayi da ita, murmushi amrah dake zaune tayi ganin ta kara komawa wajan dimming din, bata motsawa saida taga taheee ta futo da wani tray din cikin sa cups din glass ne sai juice din data dakko a kai tazo Daidai wjan da steps dinnan cikin Sauri amrah ta tashi da niyar wucewa sai ta bugar mata kafa batare da kowa ya lurasa sai aunty dake faman sakin murmushi ganin abinda amrah tayi,tray din hannun tahee ne ya fadi kafarsa sosai ta bugu jikin stairs din da kwalba ta fashe, mikewa kowa yayi ganin abinda ke faruwa, gadan Ganda kanta ya taho da niyar Dakar glass din, cikin sauri mutanan gidan suka nufeta , kara kawai tahee ta saki, Jin zata fada ga azaba da kafarta ke mata, ta sadakar faduwa kawai zatayi taji an riketa, sosai ta rike Wanda ya riketan, sai faman sakin kuka take, kafarta harta fara kumbura ga Jinin da yake fita a jikinta..

Ba yawa please .

Comment and share.

Mss Lee 💖✍️.

 

Leave a Reply

Back to top button