Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 8

Sponsored Links

Page8️⃣
Idon sa a saitin gado, Yana kyetkyet tasu, Anasa tunanin ta saitin inda nake kenan,

**Bansan lokacin da dariya ya kamanii ba hawaye nabin fuska ta duk a tare nace”da wani idon kaga nayi kyau wama yace maka kwalliya nayi nii Koh Kaya bansa ba” na fada ina dubansa, har lokacin bakina d’auke da murmushi Wanda har hakora na masu haske, d’auke da hakoran Gwal na makka har guda biyu a gyfe da gyfe na hakoran gaba,
suka bayana, na kasa rike murmushin abin ya, bani dariya especially lokacin da ya furta Kuma idonsa na kallon wani wajen.

Sam ransa Bai baci ba da abinda nace asalima wani sanyi yaji a ransa Jin sautin dariyar ta na farko a Kan kunnensa,

Zuciya tane ya sanar dani kinye kyau

“Aiku zuciyar taka Bata fada maka daidai ba, don ni banyi kwalliya ba atoh”
Zaki iyya rantsewa?

“na rantse nayi kwalliya Amma tsakaninka da Allah ya akayi ka gane”?

Uhmm bayan kin shiga dakin nan kin zauna akan dressed mirror Ina ji ki aje Abu kamar gwangwanin Mai kinfi minutes 17 kina ajewa da dauka,hakan ya tabbatar min kwalliya kike,

in Khadija tana kwalliya haka nakejin buruntun irin yanda naji d’azun,danake cin abincin

“Lallai fa,”kawai nace nayi shuru

Zan fita me da me za’a bukata, yace mini

“No ba kome tunda kayan miyar safiya zai Mana kwana biyar Koh hudu” kaga daidai ya kare ka biyani kudina,

Ok sai na dawo”toh” nace Masa yasa kafa ya fita

*Komawa nayi na zauna Ina maijin haushin kaina Dana sake baki Ina tanka masa,

kunna TV nayi ga fanka na kadawa k’wanciya nayi Ina kallo,Tashar zee cinema ana kallon wani film Mai suna bang bang sosai film in yamin dadi,

10:00pm naji sallaman Khadija mikewa nayi Ina amsawa na fito waje itace tsaye hannunta d’auke da kulan jiya,

Ina kwana Aunty,

“Lafiya Alhamdulillah ya Goggo”?

Lafiya tace a gaidaki,

“Aiko Ina amsawa”

“Ki shigo mana”

ah ah Aunty tafiya zanyi yanzun

” Aiko baki isaba shige muje ciki yau ini zamuyi”

Ba musu ta shigo dakin Muka zauna muna kallo sai 11:00 na mike na shiga kitchen Zan fara aiki, sai ganin Khadija nayi itama ta shigo,

“Ah ah fa Khadija yau Kam zama zakiyi ki huta”
Yanzun Zan kammala ”

Ah ah Aunty wallahih bazan iyya zama kina aiki ba Zan dai tayaki,

Ba yanda na iyya haka Muka Kama aiki sai 1:30 Muka kammala tuwo da miyar kuka, nayi Tuwon da yawa harda na dare kawai, na huta d’aura sabo, zubawa yayan khadija,akula na zuba na dare a wani kulan na rufe, mukayi sallah ta Kai masa nasa,

tana dawowa na zuba Mana munaci muna Hira,

“Nikam Khadija wani school kike zuwane”?

Aunty bana zuwa makaranta ai

“Ban gane ba Khadija”

Eh na kammala junior set.

“Shine zakice kin Gama karatu”?

Eh Aunty na Gama jss 3 Amma ban daura senior set ba

“Me yasa”?

Shuru tamin Naga alama batason bani Amsa

,Nima ban takurata ba,
Na chanja zancen da, wani,

“Khadija nikam akwai Wanda kika sani ne? ta iyya kitso, budurwa haka tazo tamin a gida Koh guda shida so nake na wanke kaina”

Aunty Baga kanki a tsefe ba bazaki wanke ba sai an kitsa?

“Aii Khadija bana iyya wanke Kai a tsefe sani ciwon Kai yake”

Lallai Kam aunty bara mu kammala ci na kama Maki Kan in mun gama,

“Au kin iyya kitson kenan”?

Zandai Kama Miki, “Koh Zaki chanchara mini ba”

Hh toh na yarda.

Muna Gama cin abinci Khadija ta Kama mini kaina guda shida, na tashi naje nayi wanka na hada da Kai,

*Sai dana rike Khadija har yamma kafun na barta,ta tafi,

Sai yamma ya dawo Kamar yanda ya Saba haka yauma yayi wanka da sallah sai Isha mukaci abinci yau akwai NEPA tun na safe har yanzun Basu dauke ba dukan mu muna zaune a daki Ina kallo shima dai idonsa biyu, sai 10:25 na sa kayan bacci muka kwanta,

Misalin karfe daya na dare na farka da wani irin azababben ciwon ciki Wanda tunda nake da wayo bantaba yin irinsa ba,

Mai tsanani gaskiya tun Ina daurewa har dai na fara kuka Ina nishi duk iskan fankar da yake kadawa a dakin gumi nake,

Cikin bacci yakejin kuka-kuka, Nishi daga ji na azaba ne, cikin D’an hanzari ya mike ya sauka a kujiran cikin azama yake magana muryarsa na rawa,Jin da gaske Sumayya ce Mai kuka da Nishi

Sumayya!! Sumayya!! Lafiya kuwa ya fada Yana laluben inda nake,
nikam saban azaba nama tsullubo kasan cafet daga Kan gado Ina durkushe reke da ciki,Koh amsa na kasa basa,

Da lalube ya lalubo ni kafada ta ya dafa yana cewa, muryar sa na rawa,Sumayya lfy meke faruwa ne kimin magana mana,

“cikina ” nace Ina Kara fashewa da kuka,

Hankalin sa in yayi dubu ya tashi, hannu yasa ya dauke ni cak kamar ya dauki Yar baby da lalube ya daurani akan gado.

Nikam tashin hankali Bai barni nama San ya dauke ni ba, tsaban azaba, jikina har bari yake ,, sosai hankalinsa ya Tashi ,mikewa yayi zai fita cikin rawan jiki na kama Masa hannu na damke cikin nawa dake rawa sosai, ciki muryan ciwo yaci karfina nake cemai”D’an Allah karka tafi ka barni Zan mutu ka mikamin waya ta na Kira babana karna mutu”
Sosai zuciyarsa ta tsinke Jin tana am batar mutuwa,Amma ya daure cikin sanyi murya yake cemin Kinga yanzun dare ne Bai kamata ki kirasa a daga Masa hankali ba,

bara naje Koh Allah zaisa na samu iro ya kaimu asibiti da keke napep NASA kinji, sannu,

**Gaskiya ya fada hakan yasa na sakar Masa hannu ya fita,

Waje ya fita Yana lalube ya dauki sandar sa a dakali da lalube ya fita a kofar shashen Yana lalube harya Isa hanyan kofar gida wanda ke dauke da d’akunan samarin kusan bakwai,

a kofar dakin iro ya tsaya ya fara buga Masa kofa Yana Kiran sunan sa,

Cikin bala’i ya bude kofar ya fitoh kai don Allah lafiya Ina cikin bacci karfe daya zakazo ka bugamin kofa Dan wulakanci kome,?

Don Allah iro ka taimake matatace ba lfy sosai shine nace Koh zaka taimaka mini ka kaimu asibiti,

Buran uba a Daren nan ba shegen da ya isa yasani in fitoh wallahih Koh inno ne ba lfy ba inda zani bare wata banxa Wai matarka don Allah ware ka ban waje nikam, Yana Gama masifar ya koma daki ya banko kofar,

Haka ya juya don yasan tunda har iro yace bazai taimake Saba ba Wanda ya Isa yasa sa daukan su , waje ya fita Amma titi shuru. Ba motsin kome,yakai minutes 30 baiji motsi ba dole ya hakura haka ya juya da sanyin jiki ya koma cikin gidan,kofar ya shigo cikin hanzari ya Isa dakin har yanzun dai kukan take,gadon ya hau a hankali ya Isa gareta cikin sanyi yake ce mata, don Allah Sumayya kiye hakuri wallahih ban samu abin hawa ba,

cikin muryar kuka nace “ka dubamin wayata tana Kan dressed mirror,ka bani na Kira Abie”

Ba yanda ya iyya dole ya Bata wayar ganin irin azabar da take Sha gashi ya kasa Nemo Mata mafita ga ciwo na cinta,

Sauka yayi a gadon Yana lulube harya gane dressed mirror in, har Allah yasa ya samu wayar mikamata yayi,

Karba nayi cikin Nishi nake lalubo number Abie na na Kira yakai sau biyar baya dagawa Daman tun Randa aka kawoni gidan nan Koh na Kira sa baya dagawa sai ana biyar in nayi sa’a ya daga cikin muryar kuka nake cewa abie Zan mutu cikina ciwo kazo ka kaini asibiti,,

abinda naji abina ya fada shiya Kara hargitsamin k’wak’walwa, yau nice yau abie ke cewa Inna mutu baida asara Kuma karna sake kiransa tsakiyar dare Yana bacci,

**Anya abie nane kuwa? Mai Sona da tausayina Mai son ganin farin ciki na yake furta wannan magana gareni,shikinan shima abie yanzun baya Sona 😭 wayar na sake daurawa a kunne na Amma abie ya kashe call in ban daddara ba na sake kiransa wannan Karo Kam line busy ya Danna mini.

**Me nai Masa lfy lfy Muka rabu cikin kewan juna da Addu’a tare da fatan alkhari hade da nasiha,
bansan lokacin da wani sabon kukan ya barke,min ba

Sosai hankalin Al’ameen ya Tashi baisan lokacin da ya iso garita ba ya Kamata ya runguma cikin wani irin yanayi na tashin hankali yake lallashin ta,

**Kara rungumar sa nayi na yenyene Masa ajikinsa Ina kuka maitaba zuciya wannan kukan bana ciwo bane kadai harda na bakin ciki Abiena shima ya juyamin baya adaidai lokacin da nafi bukatar sa,

Haka nayi ta fama da ciwo daga ni harshe bamu rintsa ba sai addu’i yake tufa mini har hudu na asuba,

Yaji taja numfashi da karfe sai Kuma yaji kome nata ya sake Daman har lokacin tana jikinsa,

cikin wani irin rikice wa jinta ta Bata motse yasashi mikewa ya sabeta cak a kafada Yana lalube ya fita a dakin Koh kofar Bai rufe ba tsabar tashin hankali,fita yayi a shashen yayi hanyar kofar gida…………..

*masu Tambaya na complete in MATAR MAKAHO* ,
*A Ranan 30/8/2021 na fara Post na novel innan bani da complete*

🪀My WhatsApp number
08084453785

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
Free book🤧

*More comments* 😁
*More post* 🤕

Back to top button