Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 13

Sponsored Links

Waminal Hoob_* 13

PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_

Xagaye hannayen sa yyi akan kugunta dago kanta tayi tana fadin “Da gaske Kaine.”wani sly smile yyi Yana dage gira Yake fadin”nine Mana,Dan rage tsawon sa yyi ya subbaci bakinta tareda fadin I miss you my luv.”Kara kankame sa tayi tana Jin tamkar ta maida sa ciki,sakin sa tayi da sauri ta nufi Kitchen lemu ta dauko masa da cup glass ta tsiyaya ta Mika masa tana kallonsa da murmushi a fuskarta,
Hira suka Dan taba ya tambayeta ya karatun ta,Dan juya ido tayi tana fadin bbu ddi.kumatun ta yaja Yana sakin murmushi,Yana tare daita Amma mind dinsa gaba daya Yana kan Nooriyah Kusan 9 yyi Shirin tafia Yana fadin xai tafi.”da mamaki take fadin ba kwana xakayi ba ,Yana shafa kansa yake fadin bani kadai naxo ba Areefa.”Nan take mood dinta ya canja ,
Kaida waye??”girl friend din Farhaan ,toh meye Kuma na daga hankali badai ka sauketa masauki ba.”ta karasa Maganar da bacin Rai A muryarta ,sai Kuma nabar Yar mutane a bakon wuri.”yyi Maganar Yana kallon cikin idanunta kin cewa komai tayi ta juya xa tabar masa parlorn ya fisgota lokaci daya,Bai Bata damar magana ba ya hade bakin su wuri daya.Ya dde Yana tsotsar bakin ta sai da yaji jikinta ya saki duka sa’annan ya saketa,gobe xan fito mu fita jibi xan wuce…….”da haka ya subbaci goshinta ya juya da sassarfa Yabar parlorn gamida ja mata kofar…….sanye take cikin sleeping dress riga da wando da hula akanta tana xaune a parlor wayarta a hannunta tana famar juyata taji ana saka key a kofar,kallo daya tayi masa ta dauke Kai,shima kasa hada ido yyi daita wucewar sa yyi acikin bedroom ,kwanciyar ta tayi akan soofa batareda ta koma cikin room din ba.shima Koda ya fito wanka Shirin barci yyi,
Ya tuna baiyi waya da Ammah ba,shi Kuma Bai shirya yimata karyar suna London ba,Idan Kuma yace Yana Egypt xaya Sha tambayar meya kaisa Egypt Kuma.washe gari kamar yarda yayiwa Areefa Mansoor Alkwari suna tare har Bayan magrib shopping yayi Mata na fitar hankali,sai Kusan 10 Yabar gidanta ,haka ya samu Nooriyah a parlor a karo na biyu wannan shurun nata Yana saka sa Jin wani iri,
Shima girman Kai ya Hana yayi Mata magana.washe gari jirgin safe sukabi xuwa kasar London…..dukan su barcin gajia sukayi acikin kyakkyawan gidan Aliyu waxeer,da yamma ya tashi peter ma’aikaci Mai masa gyaran gida da girki har ya shirya masu teburin cin Abinci,xama yyi ya cika cikin sa Yana yi Yana kallon kofa yaga ta inda Yar baka xata fito sai Kuma gata cikin takunta Mai natsuwa tana cikin shigar (Allura maxi dress)kalar yellow,
Wani irin yawu Aliyu waxeer ya hade haka ya kasa dauke kansa daga gareta,kayan ba karamin kyau sukayi Mata ba,har ta karaso agabansa Bai sani ba.
“Xanyi waya da Ammah wayarta Bata xuwa ko kasan wani layi nata bayan wannan.”nima ban sani ba ,ki bari sai kin gama miskilancin ki sai ki tambaya kwana nawa bakya min magana bakya gaisheni.”Ya fada yana wani hade Rai,Baki ta bude tana kallonsa sai dai Bata ce komai ba ta juya ta koma cikin parlorn ta xauna,da ido yabita tana barin kamshinta a wajen,tana xaune taji an wani fisge wayar ya hade Rai sosai ya shiga xuba Mata lambobi a wayar,
Yana gamawa ya Mika Mata wayar .nagode ta fada cikin rawar Murya baice komai ba ya nufi master bedroom dinsa dama tunda suka iso ya nuna Mata dayan dakin da xata sauka,
Baa jima ba ya fito cikin bakin yadin filtex sai kamshi yake xubawa ya kafa hula akansa Wanda ta dace da kalan shigen nasa,
Kallonsa kawai take xuciyarta na bugawa ,Bata taba ganin Wanda traditional kaya keyiwa kyau ba irin Aliyu waxeer,kina bukatar wani Abune??”da sauri ta girgixa kai Kofa ya nufa Yana Amsa waya da sanyayyen turancin sa,haka ta saki Baki tana kallonsa har ya fice daga falon.cikin sa’a Wayar ta Ammah ta shiga ,mutanen uk na sameku lfy??”cike da ladabi ta gaisheda Ammah , Ammah ta amsa cike da Jin ddi tana tambayarta ya bakunta garin Yana Mata ddi kuwa.”Ita dai murmushi kurum tayi Wanda Ammah na Jin sautin murmushin ta cikin wayar,Ammah Batool fa??”Batool ta koma Kano sunyi resuming school ki kirata.”Hira sukayi da Ammah kafin Ammah tayi Mata Alkawarin tana Nan tana bincika Mata wacce xata koya Mata turanci da harkar Business har ma da harkar passion godia tayiwa Ammah sun dde suna waya kafin suyi sallama.Farhaan ta Kira suka taba yar Hira har Yana fada mata Koda wane lokaci xai iya xuwa ya kawo Mata xiyara,yyi missing dinta sosai……..washe gari da farin ciki ta tashi kurum farhaan ya fada Mata xai kawo Mata xiyara tana sanye cikin Jallabiyya kirar oman,
Karar Buda kofa taji da sauri ta kalli kofar
Yana cikin Asalin uniform dinsa na tukin jirgin Sama wannan karon harda hular tana ajey bisa kansa,ya fito captain dinsa,wata xuciyar tana fadawa Nooriyah karki yaba kyawun da yyi ina ruwanki da kyawunsa,
Kasa dauke idonta tayi har ya karaso wajenta,xanyi tafiar kwana biyu xuwa kasar somalis, duk Abunda kike bukata kiyi magana da peter xai kawo maki.”ta girgixa kai Cikin muryar tausayi take fadin bana gane turancin sa,ba karamin Daria ta basa ba sai dai baiyi dariar ba,Yana hararta Yana fadin”kin ga Amfanin ilimi ae yanxu xaki biyewa Ammah.”kiyi tunani kafin ki hau kan Abunda Ammah xata doraki……….”Idan xakuyi vedio call da farhaan ki tabbata kin saka hijab ba haka xaki tsaya agabansa ba,karki manta matsayinki Yanxu.”yyi Maganar Yana wani hade Rai,kallo ta bisa dashi har Yabar parlorn aranta take fadin “Allah ya kiyaye hanya masifaffe kawai.”A yinin ranar ta wuni cikin kadaici ,haka wani sashen na xuciyarta tana ta kewarsa.har dare Aliyu waxeer na makale a xuciyarta ,tana tsaye a tsakiyyar master bedroom dinsa tana karewa hadadden bed dinsa kallo kalar fari kall ,sai doguwar soofa itama fara da 1 seater guda biyu duk acikin room din sai katon hoton sa Wanda ke kallon bangon gabas,Yana sanye da kayan pilot da murmushin kasaita a kyakkayawar farar fuskarsa,shagala tayi da kallon hoton xuciyarta na amsar wani bakon yanayi ,wani irin kamshi room din keyi
Kamshin da Aliyu keyi…hayewa tayi akan bed dinsa gamida daukar favourite pillow dinsa ta manna akan kirjinta,al’amari Mai girma take ji Akan Aliyu waxeer Wanda ko farhaan shagari da take soyayya dashi Baa ta Jin haka ,Ahankali taji xuciyarta bbu burbushin son farhaan aciki sai dai akwai girmamawa Mai girma da xuciyarta keyi masa.
Kenan hauka takeyi ,ba soyayyar Aure take yiwa farhaan Shagari ba.”tana yimasa so sabida kyautatawar sa agareta ,da sauri xuciyarta take fadin”da kin cika butulu Noor ki farka da wannan mafarkin da kikeyi,tabi shawarar xuciyarta ta soma yaki da sabbin kibiyoyin da xuciyarta kebin ta dasu akan Aliyu waxeer,kwana tayi tana Addu’a Allah yasa kar xuciyarta ta kunyatata ta wulakanta ta,babban wulakanci kuwa na son Aminin farhaan Shagari Dan Bai cancanci irin wannan sakayyar ba,amma sai dai Kash xuciyarta ta riga da ta makaro kwana tayi da mafarkan Aliyu waxeer masu wuyar misiltawa na haihuwar kyawawan Yara tare dashi ,suna acikin babban lambu suna guje-guje da ya’yan su…..da tayi sallar Asubah acikin sujadar ta ta karshe tana Rokon Allah sassauci akan lamarin Aliyu waxeer maimakon ta samu sauki saima soyayyar Aliyu din ta Kara mamaye sako da kowane lungu na xuciyarta,hawaye takaici take xubarwa akan me xuciyarta xata xo mata da wannan mummunan kaddarar.”Har karfe 12 na Rana Nooriyah Bata fito daga dakin Aliyu waxeer ba tana can dunkule cikin tattausan bargonsa jikinta ya dau xafi sai kakkarwar sanyi takeyi,haka peter ya shiga xarya a parlor da kitchen Kiran da Aliyu yayi masa yakai goma,
Yana fada masa madam Bata fito daga dakinta na barci ba,
A Kiran karshe Aliyu ya umurcesa yaje ya kwankwasa kofar kusa ga dakinsa na barci ,peter yabi umurnin Mai gidansa ya nufi wurin da sassarfa ya shiga bugu kofar shuru yakeji,bugun ya tada Nooriyah daga barcin wahalar da ya kwasheta dakyar takai kofa ,da hijab ajikinta idanunta sunyi sukutum,har Peter xai juya sai gata ta bude kofar .xaro ido peter yyi Yana kallon yanayin nooriyah wacce ta fara layi ,tana dafa bango sannu madam??”ya fada cikin harshen turanci,meke damunki??”dakyar ta karaso parlorn.”dakyar ta iya hado kalmar turanci nacewar Bata da lfy.”da sauri Peter ya Kira Aliyu a wayar tamkar jira Yake ya dauka,cikin harshen turanci yake masa bayanin tamkar Bata Jin ddi Bata wayar Aliyu ya fada masa,
Muryarsa kawai ta Kara sakata cikin wani yanayi……”meke damunki??”tambayar da ya soma jefo Mata kenan,cikin rawar Murya take fada masa ciwon Kai da xaxxabi,
Ba peter wayar.mika masa wayar tayi,sun dde suna magana,
Kafin ya kashe wayar.
“Sai can Aliyu ya Kara Kira lokacin peter na a kitchen Yana kokarin hadawa Nooriyah din Tea,Bata wayar yyi
“Kiyi wanka ki Sha tea doctor xaixo gida ya dubaki ,ki tabbata da Hijab ajikin ki .”da haka ya kashe wayar,
Duk da tana cikin ciwo sai da tayi murmushi komai nasa daban ne…samun kanta tayi da bin umurnin sa wanka tayi riga ta saka marar nauyi taje parlor peter ya hada Mata wani tea,Dan wancan ya Dade da sandarewa,mintuna Kusan Ashirin sai ga kararrawar buga kofa da alamar dr.da xai dubata ya iso kyakkyawan bature,sai sannu yake Mata cikin harshen turancin haka sunyi waya da captain Aliyu waxeer ya fada masa meke damunta ,
Magani kawai yabata dama ya riga da yaxo dashi ,Yana fita tabi umurnin Dr.tasha maganin Kusan 2 ta samu barcin Rana ,Koda ta tashi Kusan 5 ciwon kan ya sauka haka xaxxabin ya rage sai dai ko kadan jikinta bayada karfi wanka ta karayi,
Ko lunch din da peter ya hada Mata kadan taci har yau Bata Saba da cimar kasar ba,sai a hankali……..Sai da dare Aliyu ya kirata ya Mata ya jiki ta fada masa ta samu sauki,
Sai da safe yayi Mata gamida kashe wayar.
Yau ko kadan Bata da sha’awar Kiran farhaan shima sai akayi sa’a Bai kiraba.a gida Nigeria Kuma ta Kira kawunta tana tambayarsa labarin Kabir fa.”Ya fada Mata Yana cikin koshin lfy Kabir ya fara samun natsuwa Aliyu na kula da lamarinsa,haka ya fada masa idan ya natsu xai tsaya masa tsayin daka yaga ya samu ilimin boko,murna tayi sosai yau a dakin ta tayi kwanciyarta.yau tun da safe da kanta ta shiga gyara gida ,ta canjawa Aliyu bedshirt ta wanke masa toilet,tana tsaye da peter acikin kitchen suna hada dinner dama peter ya fada Mata,oga mafi yawancin tafiarsa yafi dawowa da dare .suna gamawa ta shige wanka gamida dauro Alwallah.Amma har Kusan 10 bbu Aliyu bbu Alamarsa har ta gaji da duba agogo,
Haka peter ya sameta a parlorn ,Yana fada Mata oga Ba xai samu shigowa ba sai gobe da safe,ta fahimci haka acikin turancinsa.nan take fuskarta ta canja ,sai da safe yayi mata ,ya Rufo Mata kofar haushin xuciyarta taji akan me xata ma damu da dawowar mutunen da Bai wani dauketa da muhimmanci cikin Rayuwarsa ba.Har tayi Shirin barci tana Jin haushin xuciyarta sosai akan damuwa da lamarin Aliyu waxeer…..

Littafin waminal Hoob na kudine#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan Lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#

ASMY#??
WM#??
Team#NooryAli forever??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah?

Back to top button