Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 17

Sponsored Links

Waminal Hoob_* 17

PAID BOOK
_Asmy b Aliyu_

Halin da taga Aliyu waxeer ya shiga duk ya daga Mata hankali.”Kasan baka da lafia meyasa ka fito damu cikin wannan daren??”tayi Maganar da karaya a muryarta,shi dai baice komai ba har suka kawo gidan Khalil waxeer ,maigadin gidan Wanda ya kasance bature shi ya bude masu get din gidan,ya samu wuri cikin rumfar adana motoci yyi parking,
Ahankali kidan taushi ke tashi,Kusan tare suka fito daga motar
Booth din motar ya bude ya fiddo da gifts din da xai baiwa Dan uwan sa da shi da Noory tun acan yasa akayi wrapping dinsa,
Da Kuma kyawawan flower’s mikawa Noory gift din yyi shi Kuma ya rike flowers ,Idan muka shiga sai ki baiwa Yah Khalil yau Yake birthday daga haka ya lalubi hannunta ya rike Cikin nasa duk da tsikar jikinsa yarda take tashi dauriya kawai Yake haka suka jera suka nufi Entrance din shiga gidan xuciyar kowane na bugawa da wani irin yanayi……..Khalil waxeer ne da Layla tsaye a bakin kofar cikin shiga ta alfarma sunyi kyau har sun gaji ,sune ke taron duk bakon da ya shigo wurin haka ga gifts din da suka samu Nan daga gefe cikin wani katon basket da baxan iya kwatanta girman sa ba,,Khalil ya wara idonsa Yana yiwa Noory din Sannu da xuwa hugging din Aliyu yyi ,cike da ladabi Noory ta gaisheda Layla wacce ta saki Baki tana kallon yarda nooryn ta goge lokaci daya tayi wani irin fresh na ban mamaki ,dan kwakwalo murmushi tayi tana yiwa nooryn Sannu da xuwa,da haka suka Mika masu gifts Aliyu ya Rika hannunta suka nufi cikin katon parlorn nasu da akayiwa wani irin decorating ga turawa Nan a wajen da Kuma business partner dinsu hausawa da matansu ,kowane cikin shiga ta alfarma.
Wasu na rike da matansu suna rawa wasu Kuma na xaune suna ciye-ciye sosai wurin ya kayatar da Nooriyah,haka Aliyu yabisu suna gaisawa Anan wajen Yabar Nooriyah gefe ya koma ya xauna cikin soofas Yana dafe kansa dake mugun yimasa ciwo ga Kuma gefen marar sa da Yake Jin tamkar ana soka masa wani Abu a wajen,A hankali Nooriyah ta hngo wani kyakkyawan bature Yana xuwa ta wurinta. ya tsaya gabanta Yana gabatar mata da kansa ,cikin turancinsa da take fahimta kadan ,xai riko hannunta da sauri ta xaro ido gamida jada baya gabanta na faduwa ta shiga jada baya tana tunanin ta inda xata hango Aliyu baturen ya nace Mata sai magiya Yake yimata ,
Can take hango Aliyu dafe da Kai da sauri ta Isa garesa still baturen Bai daina binta ba ,Wanda shekarun sa baxasu wuce Ashirin da biyar ba……..Jin an tsaya agabansa yasa ya dago jajjayen idanunsa ganinta yasa gabansa ya Kara faduwa,Kuma ya hango wani a bayanta.
da mamaki Yake tambayarta ya akayi ne.”cikin harshen hausa take fada masa ga Wanda ke biyar ta Nan,,wani mugun kallo Aliyu waxeer yake masa tsoro yasa baturen ya juya da sauri ko waiwaye hakan ya Kusan saka nooriyah Daria,Aliyu ya dakune Fuska Yana kallonta yake fadin”Na sakaki ki tsaya cikin maxane?”ta wara ido tana fadin”ni ban shiga cikin maxa ba,ina tsaye ya sameni ae.”Aliyu na girgixa Kai Yake fadin”wannan shaidanin turaren da kika saka ba dole duk inda kikayi maxa subi ki ba.”Yayi Maganar Yana wani hade Rai,
Turarenta na Kara dagula lissafin sa.bata wani fahimci Maganar sa ba ,xatayi magana sai ga laylah waxeer da Waiter a bayanta dauke da tray ,ta dauki dayan cup glass Mai dauke da juice aciki ta mikawa Aliyu tana murmushi take fadin komai baka Sha ba,haka ta mikawa Nooriyah dayan ,kafa Kai Aliyu yyi batareda tunanin komai ba yasha Kusan Rabi ya aje itakuma Nooriyah Bata Sha ba,Layla ta Dan hade Rai tana fadin”sai kace wata bakuwa ke baxaki Sha ba.”Nooriyah na murmushi take fadin”bana Jin ddin cikina Amma xan Sha xuwa anjima.”Haushi laylah waxeer yasa tabar wurin……….Dafe kansa yyi dake mugun ciwo tamkar Yabar jikinsa haka Yana jin wani Abu na yawo acikin jikinsa har cikin tafin kafarsa dauriya kawai Yake ,Noor na kula da yanayinsa.”A gaggauce ya mike tsaye laylah waxeer na gefe tana sakin wani irin murmushi tana Jin hirar da sukayi da aminiyarta a waya ,na dawo mata
“Baki da hankali Areefa Mansoor kina da tabbacin Bai taba kama Koda hannun yarinyyar Nan ba,kinga yarda ta xama lokaci daya tayi wani irin cikowa.”Daria Areefa din tayi nasan waye Aliyu laylah bafa sonta yakeyi ba Auren su na Dan wani lokacine budurwar Farhaan Shagari ce taimakonta kawai yyi sabida gidan su xaa yiwa yarinyyar Auren dole kafin Farhaan ya gama karatu.”wani irin murmushi Laylah waxeer ta saki anxo wurin da ya kamata taji gaskiyyar lamarin”shine Ammah ke wani rawar Kai ,Ashe karya Aliyu yayi masu ??”Amma ya xama a tsakanin mu sirrine daga ni sai Aliyu sai farhaan muka San da wannan xancen?””Aran laylah waxeer ke fadin Amma kin cika wawuya shasha da kika Bari akayi wannan Auren??”xan tabbatar maki da namiji ko baya son macce akwai Abunda xai sa ya kama hannunta har yakai ga jikinta,Da wannan dalilin ta sakawa Aliyu kwaya acikin drink daga shi har Nooriyah din Amma ita batasha ba,
duk da haka ta samu Evidence din turawa Areefa Mansoor,ta dau Alwashin Kota balai Kota masifa sai ta kuntata xuciyar Ammah kamar yarda ta saka Mata ido da Aurenta,sai ta tarwatsa dukkan farin cikinta ta hanyar shiga cikin Auren Aliyu waxeer da Nooriiyah,
Ta riga tasan da Ammah ba sonta take ba ,xaman dole kawai ne take daita karama hawan jinin nata ya tashi Idan taji Auren Aliyu waxeer contract ne…….”Idan yaso xuciyarta ta buga ta mutu kowa ma ya huta,wani irin fisgo hannun Nooryn yyi Yana wani hadata da jikinsa Yana shinshinar Wuyanta Nan take ya wani irin haukace,A tsorace take kallonsa kallo daya tayi masa xuciyarta ta shiga bugawa Bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba,Laylah waxeer tayi saurin shiga tsakanin su tana masa wani irin kallo take fadin”meye Haka Aliyu??”meke damunka.?””tambayar da ta masa yyi balain Bata masa Rai,komai xakayi matarka ce Amma Bai kamata kayi acikin mutane ba.
Ta kama hannun Nooriyah da jikinta yyi balain sanyi gabanta na mugun faduwa ta nufi stairs daita tana ma Aliyu Alama da ido akan ya biyota ,dama tamkar ana basa umurni haka ya bita jikinsa na mugun rawa duk sanyi
Ac.dake makale da kowane kussuwa na cikin parlorn ya jike shakaf ko gabansa baya gani ,laylah waxeer ta bude dakin barcinta tayi Dan murmushi tana kallon Nooriyah wacce duk ta gama daburcewa daganinn yanayin Aliyu waxeer ,ki xauna Anan yanxu Aliyu xai sameki da haka ta juya tana Rufo Mata kofar Kusan cin karo sukayi da Aliyu Wanda take kallo a daburceta ka shiga tana cikin dakina……….”da haka ta wuce Aliyu tana sakin wani murmushin mugunta ,Yana turo kofar dakin ta Mike a tsorace gabanta na mugun faduwa ,tana ganin yarda jikinsa ke wani irin kadawa.Jawota yayi ta fado kansa Yana wani irin shakar kamshinta Yana sakin ajiyar xuciya ,Yana lalubar Wuyanta Yana saka kansa cikin Wuyanta wani irin Abu takeji tamkar Mai Jin fitsari,kokarin turesa take ya riketa sosae tana kallon cikin kwayar idanunsa wacce ta canja kala har kwalla kake hangowa acikin su,cikin rawar Murya take fadin”meye haka Aliyu me kake yi haka pls ka dawo natsuwarka.”Kara manna ta yyi ga jikinsa ,ko Maganar nata wani irin shauki take sakar masa,xata turesa ya wani fisge veil din da tayi Rolling kanta dashi ,sai ga gashinta ya bayyana da ta tufke da ribbon sai walwali Yake Haka wani kamshi na musamman na tashi acikin sa,wani irin shinshinar gashin Yake a haukace ya shiga subbatarta ta koina har xuwa cikin Wuyanta,hawaye taji suna cika mata ido tuno farhaan kurum,
Xip din rigar ya soma kokarin ja kasa lokaci daya ta fashe masa da wani irin kuka tana girgixa masa Kai…Hade fuskarsa yayi da Tata Yana gogar hancinta da wata irin Murya Yake fadin”I try Am very try Noory.”U belong to some one else,,ya fada muryarsa na karyewa a hankali kafin ya samu ya hade bakinsa da nata ,wani irin Rawa kafafunta suka farayi tunda take a rayuwarta Bata taba sanin haka kiss yake ba sai yanxu da Aliyu waxeer keyi Mata,sai dai ta karanta a novels
Ko ta gani a Tv……Xuciyarsa taji tana wani irin bugawa tamkar xata fito daga kirjinsa ,Ahankali ya saketa ya shiga Jan wani irin numfashi,wani irin amai yaji Yana taho masa da gudu ya nufi kofar toilet,Amai Yake xubawa tamkar xai fiddo da hanjin cikinsa duka,tana jinsa Yana Aman da ya daga Mata hankali sai dai Bata da natsuwar tunkarar sa barantana takai masa taimako,
Xip din rigarta take laluba Wanda har ya kaisa karshe dakyar tajasa sama,ta Mike ta nufi toilet din da wani irin yanayi haka lokaci daya xuciyarta na wani irin bugawa….Ya dde kwance akan bed kansa tamkar xai fice sabida ciwo, Nooriyah ta koma karshen bed ta xauna tana kallonsa,lokaci daya ya bude idanunsa da suka gama canja kala.tuno moment dinsu na daxu yasa yyi saurin rufe idon bayason tunosa ko kadan,bani wayana.”Ya fada da muryarsa da Bata gama dawowa dai-dai ba,kan mirror dressing ta nufa ta dauko wayar ta Mika masa itama kallonsa kurum Yana sakata Jin kunya da wani iri.Bata san waya Kira a wayar ba taji dai Yana fadin yaxo yanxu.”Baifi minti biyu da gama wyar ba aka turo kofar…….Khaleel waxeer ne Layla na biye dashi a baya ganin sun hada ido da Aliyu tayi saurin dauke Kai gabanta na mugun faduwa ,shi Kuma ya kasa dauke idonsa akanta kallonta Yake tamkar Mai son ya gano gaskiyyar Abunda ya faru cikin fuskarta,kallonsa ya maida kan Khaleel da ya ishesa da tambayar ko bayada lfy ne.”Ya hade Rai sosai tamkar shine babba ba Khaleel waxeer ba,
“Wace irin kwayace xaku sakawa mutane haka acikin drinks Yaya.”Idan mutum Bai da Aure Kuna so yayi xina ne??”Yana Maganar ne cikin sanyi Murya Kuma cikin harshen turanci,
da mamaki Khaleel ke fadin acikin Abun shanka ne aka saka kwaya”Kallonsa ya maida kan laylah waxeer wacce ta hade Rai,da sauri ta daga masa hannu cike da balai da masifa take fadin”karka yimin sharri plz Ban San anyi ba Kuma bbu wani Abu da aka saka ,da Haka ta juya cikin fushi tabar room din gamida bugo masu kofar duk sun Bata Mata plan,shima Aliyu mikewa tsaye yayi jikinsa duka bbu kwari Yake fadawa Khaleel xasu wuce,
“Dama bada Shirin kwana kaxo ba.??”Aliyu na girgixa Kai Yake fadin”bana tunanin haka ,har mota Khaleel din ya rakasu sai tambayar Aliyu Yake Yana iya driving kuwa.”sai da ya ga fitarsu ya juya cikin gidan,ya samu laylah a dakinsa sai cika take tana batsewa,cikin ihu da fada take fadin”Saboda ya rainaka ya shirya maka karya shine xaka yarda dama ae a dole yaxo baiyi niya ba ,tamkar baka San rainin wayon Aliyu da wulakancin sa ba,dama ai Kaine ke rawar kafa akansa shi ya damu da Kaine,Hannunta ya riko tana fisgewa sai famar hakuri Yake Bata da lallashinta.

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#

Team#NooryAliForever#

_ko kalma daya Kika karanta Baki Biya ba na barki da Allah.!”_
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: _

Back to top button