Hausa NovelsWaminal Hoob Hausa Novel

Waminal Hoob 12

Sponsored Links

12
“Yaushe Yah Khalil xaiyi hankali Ammah??”Aliyu waxeer ya fada cikin bacin Rai,dashi har matarsa bbu Wanda ya San ciwon kansa”.lokaci yyi da xaki huta Ammah har yanxu Baki huta ba,sune ya kamata su Rika kawo maki ,sai dai su kullum suxo su cika cikin su.kar su Kara xuwar maki part cin kowane irin Abinci su tsaya gidansu su girka nasu ya karasa Maganar sounding so ped up a Muryarsa da alamar Abun ya dde Yana masa ciwo yau ne ya samu damar fitar dashi a mind dinsa,jikinsa har rawa Yake da sauri ya juya Yana fadin xanje nayi masu magana.”da sauri Ammah ta riko hannunsa,juyowa yyi Yana kallonta.yar kwallah ya gani a idanun Ammah,da sauri ya xaunar daita gefen bed dama har room dinta ya sameta ya baro Nooriyah a karamin parlorn Ammah, Addu’a kawai xaka yiwa Dan uwanka, matarsa ta riga ta gama dashi Dan haka ban taba sha’awar ka Auri Yar boko ba Aliyu Mai wayewa ,a kullum ina rokon Allah ya baka macce dai-dai da irin wacce xata dace da Rayuwarka,
Sai gashi jinkirin da nake ya xamo maka Alkhairi Aliyu Nooriyah itace ta dace da Rayuwarka ina Jin haka ajikina tun ranar da na fara ganinta,da sauri ya katse Ammah xuciyarsa na wani irin bugawa Yake fadin.”Ammah ki rage son Noory da yawa bamu San inda kaddara xata wulla da Rayuwarmu ba mu duka…”Ammah na girgixa Kai take fadin karka yimin karya Aliyu har aranka kaso Auren Nooriyah ko dai akwai wani Abu da kake boyemin,na lura ba sosai kake farin ciki da Auren Nan ba please ka fadamin.”Ammah ta fada cikin karaya a muryarta,me Kuma ya kawo wannan Maganar Ammah ,pls karki dagawa kanki hankali da bana son Nooriyah da baxan Aureta ba Ammah.”Ga Nooriyah can a parlor tana jiranki,shine kabarta tun daxu kayi tahowarka,Ammah na fada tana nufar kofa…kayatattar waleema akayi Wanda sai Kusan 3 mutane suka fara watsewa sosai take Jin gajia ajikinta,da Ammah ta lura da haka ta Kira Aliyu tana masa umurnin yaxo ya tafi da matarsa Angama ,duk mai son ganinta yaje ya sameta gidanta……….Kwana biyu da Auren Bayan ishai ya tafi da Nooriyah part din Ammah da take nemen su cikin Kiran gaggawa.dukan su suna A babban parlon Ammah ,Ammah na xaune cikin Royal chairs da hijab ajikinta. Itama Nooriyah hijab ne ajikinta har kasa.Ammah na murmushi tana fadin”Ya bakunta Jewel.”cikin Jin kunyar Ammah take fadin Alhmdullhi….Ammah ta maida hankalinta kan Aliyu waxeer tana fadin Yaushe ne tafiar ka.”Ammah xuwa jibi ne.”ban gane jibi ba kana nufin Kai kadai xaka tafi banji kana Maganar yi Mata processing visa dinta tafita UK ba.baki ya bude Yana kallon Ammah da Dan mmki,
Ammah bafa tare xamu tafi ba itama gobe xan kaita ta cika form xata fara schooling Anan taya tafiar mu xata yuyu ,ae xan rinka xuwa akai -akai da sauri Ammah ta kallesa tana fadin karatun me xatayi Aliyu??”kana duba kyawun matarka kuwa??”ko Dan ka ganta bakane shiyasa baka ganinsa sosai,
Ban yarda da wannan bokon na Nasara ba,
Hankali tashe Nooriyah ke kallon Ammah ,cikin Rawar Murya take fadin Ammah xanyi karatu xan tsaya Anan basai munje tare ba.”da sauri Ammah ta katseta cikin tashin Hankali take fadin”mekike nema A bokon iyakacin sa ki gama ki fara Aiki ki Tara dukia Ki taimaki yan uwanki Right??”ba dai kina da ilimin ki na addini ba,na maki Alkawarin a duk wata xan Rika ware maki Albashi mai tsoka haka xan sakaki acikin business Dina ,xan sa Aliyu ya nemi baturiyar da xata koya maki turanci xan saka a koya maki duk wani harkar (Economic computer)harkar passion Kuma har sai kince ya isa saboda class xaki xama super model a fadin uk kaf dama Nigeria dukanta,konawa ne xan iya kashewa inhar xaki xama hakan, Ammah ta kamo hannun Nooriyah da jikinta ya gama saki gaba daya ta xaunar daita kusa daita ,tana murmushi take fadin Bayan wannan wane irin buri gareki Nooriyah.”Bawai karatu ne bana so kiyi ba,na fison karki yi nisa da mijinki inhar Kuma kinga akwai takura a hakan xan sa A bincika maki wata makarantar a UK.da sauri Nooriyah ta girgixa Kai tana fadin
Baxa ayi hka ba Ammah inhar burinki shine na xauna innuwar Aure tareda Aliyu xan xauna dashi,
Har karshen numfashi na,bokon Kuma na hakura Ammah duk yarda kikeso haka xaayi.”kallonta kurum Aliyu Yake yarda take magana tana ji ajikinta Yana kallonta Amma Taki yarda su hada ido,xaiyi magana Ammah ta katse sa da sauri tana fadin kaje ka fara shirye-shiryen tafiar Nooriyah da wani irin yanayi ya wuce daga parlor……Ranar Ammah saboda murna tamkar xata goya Nooriyah din,
Har tayi Shirin barci ya turo kofar dakin da take .Jin tayi an fisgota an hadata da kofa,wara ido tayi tana kallonsa.A mugun hasale Yake Fadin wane game kike playing??”mekika fadawa Ammah ke yanxu Dan Rashin sanin ciwon Kai kin amince da Duk Abunda Ammah ta tsara maki kin amince kin fasa karatu kibini?””kina ji kina gani ilimin boko ya gagareki,bari na fada maki har Abada baxaki taba xama daya da wacce tayi jami’a dake da kike xaune a gida.baki ga Yarda matar Yaya Khalil take bane,bakya so ki xama kamarta.” Nooriyyah tayi murmushin da iya labbanta ya tsaya tana kallon cikin idanunsa take fadin”xanyi kokari na cika burin Ammah na shekara daya in har hakan xai sakata farin ciki idan mukayi Aure da Farhaan sai nayi karatu ,Maganar Kuma na xama kamar yarda wata take bai taso ba,,ina son kaina yarda nake Kuma ina Alfahari da yarda nake.Hade Rai yayi Yana Mata wani irin kallo Yana Jin kamshinta na sakasa wani irin shiga yanayi,
Xan kwanta.”Yaji muryarta tsakiyyar kansa,da sauri ya saketa sai dai har lokacin ya kasa cemata komai Yana kallonta ta kashe wutar dakin duka ta hayewarta kan bed gamida Jan duvert ta rufe jikinta dashi duka,
Addu’a kurum take yabar Mata dakin ko kadan Bata son kusan cin ta da Aliyu waxeer sai ta rika jinta cikin wani irin yanayin da Bata taba tsintar kanta ciki ba,Koda ya riketa dauriya kawai takeyi tana Jin ya Rufo Mata kofar tayi saurin kunna makunin fitilar dake gefen gado tana sauke numfashi ,Idan tana tareda Aliyu waxeer mance komai da kowa take”……….Da tunani kala-kala aranta tayi barci Kuma cike da mafarki duk akan Aliyu waxeer,
Mutunen da ya Raina halittar da Allah yayi mata Mai xai sata ta damu da lamarin sa haka harda su mafarkin sa,fada ta shiga yiwa xuciyarta
Washe gari tunda ta tashi Bata saka sa a ido ba har dare,Bata yi wani kadaici ba suna tareda Batool da Aysha har magrib.Bayan ishaai sukayi haramar tafia,
Cikin kalar tausayi Nooriyah ke fadin baxaku kwana ba.”gaba daya suka hada Baki suna xaro ido da fadin ki rufa Mana Asiri wurin Yah Aliyu.”Idan ya same mu a gidan Nan xai canye mu duka sabida masifa,Aysha waxeer ta amshe xancen da fadin ,ni ko xaki kwana wallahi baxan kwana ba ta fada tana daukar handbag dinta dake kan mirror dressing ,suna fita taji gidan yayi mata wani iri wanka tayi ,ta gabatar da sallar ishaai haka ta taxama a parlor har Kusan 10 bbu alamar Aliyu sai taji tana so ta gansa kafin tayi barci,wata xuciyar ta fada Mata meke damunta da lamarin Aliyu.?”goma da Kusan Rabi ya turo kofar parlorn da mamaki yake kallonta,
Metake a parlor har xuwa wannan lokacin.”cikin takunsa na kasaita ya shigo cikin parlorn ,ya Mika Mata ledar hannunsa,kallonsa tayi kafin ta karbi ledar.”waya ce aciki tana da caji xuwa da safe xan nuna maki yarda xakiyi Amfani daita.” Cikin sanyi Murya take fadin ta gode Allah ya saka da Alkhairi, ya nufi stairs ba tareda ya Amsa ba, ta bisa da ido tana shakar kamshinsa da yabari a parlorn ,itama dakinta ta shige tana juya wayar kirar iPhone 12
Addu’a tayi gamida kwanciyarta Bata dde ba tayi barci,har yyi Shirin barci wayar Areefa Mansoor ta shigo tamkar kar ya daga wayar yadai daga,Yana dagawa ta fara complain akan ya daina sonta yanxu.”Areefa muyi magana gobe yanxu barci xanyi.”cikin Murya Mai rauni take fadin”I miss you so much Aliyu Yaushe xaka kawo min xiyara.”wannan karon Areefa ta karya xuciyarsa ,xanxo acikin satin Nan Areefa kina farin ciki yanxu.”Yana Jin sautin murmushin ta da wata irin Murya take fadin”kayi Alkawari??”I promise xanxo ,haka ta rika basa labari sai da taji shuru tukuna ta kashe tasan Yyi barci…….washe gari Abuja suka wuce kwanansu ukku ya gama processing visa dinta.suka dawo kaduna ana gobe xasu wuce suka je gidan Ammah suka yini,sabida Aliyu yace gobe xasu wuce Abuja acan jirginsu xai daga,
Ya fadawa Ammah ne sabida baya bukatar Yan rakkiyya xuwa airport,Dan xai kaiwa Areefa xiyara a Egypt.bayan magrib suka nufi gidan Baffa kabir nasiha yayi masu,sai Bayan ishaai suka baro gidan.kusan tare xasuyi tafiar da Khalil waxeer Amma shi xai tsaya a Abuja na sati daya matarsa xata ga iyayenta ,kasancewar iyayen laylah suna xaune a garin Abuja.sai Kusan 11 ta kwanta sabida Shirin kayanta Kuma a ranar Bata samu yin waya da farhaan ba,a yinin ranar Bata xauna ba.
Kuma Aliyu ya gargadeta karta yarda ta Kira farhaan Shagari a gidan Ammah.washe gari sukayi sallama da Ammah suka dau hanyar Abuja ,Aliyu ne ke jansu acikin ferrari dinsa,Khalil da laylah ne A baya yayinda Noor da Aliyu ke gaban motar…..kwana su daya A Abuja suka hau jirgin Egypt Bai fadawa Areefa xaixo ba,A hurghada Apartment suka sauka dama duk yaxo Anan Yake sauka,sai da sukayi wanka ya huta,yayi Shirin fita
Lokacin Nooriyah na ramakon barcin da Bata samu tayi ba,misalin Kusan karfe 6 na yamma……..kofar ya sakawa key ,akwai Yar tafia a gidan da Areefa Mansoor take xuwa inda ya sauka sai Bayan magrib ya isa ,
Sai da ya tsaya massallaci yayi sallar magrib,waya ya fidda yayi dialling lambar Areefa Mansoor lokacin tana tsakiyyar dakinta na barci itada maheera kwalaben beer ne a tsakiyyar room din,Areefa harta tsiyaya tata acikin cup glass Kiran Aliyu waxeer ya shigo ,tamkar baxata daga ba sai Kuma ta daga tana dakune fuska,Jin tayi yace ta bude masa kofa ,Kara kallon wayar tayi ganin da gaske Aliyu waxeer ne ya kirata ,wani irin ihu ta saka .Da sauri maheera ta kalleta tana fadin Areefa xaki fasamin dodon kunne,
“Aliyu ya iso plz tattaramin wannan duka ki xubasu acikin bag dinki ki tafi dasu,
Mikewa tayi tsaye jikinta har wani shaking yake wata bingilar rigace ajikinta ,wacce da kadan ta wuce gwiwarta kalar red sai dogon gashin kanta da ta tufke a tsakiyyar kanta da katon ribbon shima kalar red,turare ta Kara fesawa ta xura plat shoe a kafarta ta nufi parlorn da gudu tana Buda kofar ya bude Mata hannayensa,da gudu ta fada kansa ta wani kankame sa ,Yana Jin yarda take sauke ajiyar xuciya…

Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN ta wannan Lambar#
09060259200
Shaidar Biya ta wannan lambar
08086207764#
WM#??
ASMY#
HWA#??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??: *_

Back to top button