Hausa NovelsHausa NovelsKannan Mijina Complete

Kannan Mijina Complete

Sponsored Links

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)

WHATSAPP NO:+2349030159301
[2:47 pm,2017]

*®TALENTED WRITER’S ASSOCATION*_(TWA_)

_*****KANNAN MIJINA_*****👩‍👩‍👧‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

=Dedicated 2 Talented writers=

_Dasunan Allah mai rahama mai jin k’ai,Rabbirarshiril Karen_

_jinjina da godiya ga kanwata ummi aisha Allah yabar zumunci._

_Kuna raina kannena na kaina_

_Nafisa I uba_
_Zee smile i uba_
_Umyma umcy_
_Rukayya i uba_

_Allah yabar zumunci_

*1*

~~~~ Ahankali matashin yake tuka motarsa, tunani yake tayadda zaigano gidan da yake nema,

Wata matashiyar yarinya,yahango, tana dososhi, dahanzari yabude murfin motar tasa yafito,karasowa tayi.

Dahanzari yaimata sallama,”assalamualaikum

Kamar bazata kulashiba cankuma metatuna sai taamsa

“Waalaika salam”

“Dan Allah kanwata tambaya nake”

“Inajinka”

“Gidan alhj Ibrahim mai turare,nake nema.

Shiru tayi tana tuna nazarin saurayin,

“Kana dan mikewa kadan zakaga wata makarantar islamiya , gefe zakaga wani gida mai bakin gate”

Murmushi yayi,”yace nagode kanwata , dan Allah ko zansan sunanki?

Shiru taimasa kamar batajishiba, can taamsa masa da “sunana safiyya”

Murmushi yayi har sai da kumatunsa ya lotsa,yashafi sumar kansa,kana yace ” nice name”, nikuma suna na,assadiq..

Inbadamuwa ko zansan gidanku?.

“Gidanmmu kuma?

“Eh zanzo inyimiki godiya har gida,da irin karamcin da kikai min.

“Hmm ni a ganina basai kabini gida ba”

Cikin kwantar da kai yake mata magana,

“Kiyi hakuri safiyya,ina son kulla zumuci da kyakkyawa irinki

Kwatanta masa gidansu tayi,tunda tafara magana yake kallon dan karamin bakinta,godiya yayi mata yashiga motarsa yaja yatafi,yana mai farincikin samun mata,can kuma yatuna da maganar mahaifiyarsa,nasan auramasa yar kanwarta, dankaramin tsaki yaja.

Dasassarfa take tafiya danson karasawa gida,

Da sallama ta shiga gidannasu, mahaifiyarta tatar a kitchen,tana kokarin dafa abincin dare,

“Ummina sannu da aiki”

“Yauwa safiyya,antaso?

“Eh” ummi ina yaya amina da najiba?”

“Sunje gidan yayarku rukayya..”

“Ummi danasan zasu dabanje makarantaba.

“Suma basu san zasuba,waya tai suje batajin dadi.

“Ayya Allah yasawake”

“Ameen,kije kicire uniform kizo kitaimakamin”

“To ummi”

*********

Hajiya karima ce zaune,akatafaran falonta, tacaba ado kamar mai shirin zuwa biki,yanmatanta sunzagayeta, tana nuna musu wasu materials daaka kawo mata talla.

Assadiq ne yaisallama,yashigo falon.

Afifa ce tai caraf taamsa masa sallamar…..

“Yaya sannu da zuwa cewar rushida”

“Yauwa yanmatan momy,”momy sannu da gida”

“Sannu assadiq,kadawo ?”

“Eh momy”

“Kasamu gidan?”

“Nasamu,yanason yabata labarin budurwar da yahadu da ita,yanafargabar abinda momyn zatace,dole yaja bakinsa yaishiru.

Farhana ce tafara magana cikin shagwaba,..

“Yaya sadiq”

“Naam”
Dan Allah kasiya mana materials dinnan kaji”.

“Nawane” yatambayeta ?

“Momy kifadamasa kudin,dan Allah”

“To, masu wa,cewar momy 8 thousand ne.”

“Ko wacce tadau daya momy na kidau biyu adaukarwa, ya hannatu 2.”ihun murna sukasa,wanda yayi dai dai da shigowar faruq cikin daga murya yafara magana,

“Kai kai haba,dalla malamai meye haka?”

Shiru sukayi suna kunkuni mussamman farhana datafi sauran fitsara,fada yahau yimusu,karshe suka kwashe kayansu sukai daki……

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
_®TWA_
[6:13Am,2017.]

*TALENTED WRITER’S FORUM*_©(TWF_)

*KANNAN MIJINA….*
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

_Godiya ta mussamman ga talented group fans,nagode da adduo’inku gareni mussamman,_

_Dahara nura_
_Sunhera_
_Neenoh yakubu_
_Fatima auwal_
_Halima_.
_Allah yabar kauna_

_Kuna raina_
_Kiyaya group_
_Munemi aljanna group_

_Hausa novel group_.

_Wannan shafin nakune_,
_Yaya hassan H bature_
_Aunt umma aymana_

 

*2*

_____Sai yanzu momy tadago takalli faruq,”sannu faruq da kokari,wai me yarannan suka tarema baka daaiki sai fadacefadace,wlh kashiga hankalinka,ranka zaiyi mummunan baci,kacigaba”

“Haba momy meyasa kike biyewa yarannan ne?” badamar aimusu magana,sai kihauni da fada”

Sai yanzu assadiq yasa baki,cikin karaji yadagawa kanin nasa tsawa,

“Faruq!, kana haukane momy kakefadawa haka?”,ka kama kanka inbahaka wlh zamu sa kafar wando dayadakai,stupid,kawuce kabawa mutane guri malam”

Cikin fushi yakwashi wayoyinsa yabi hanyar dazata sadashi da dakinsa.

“Rabu dashi assadiq,Allah yashirya min faruq,amma yanada wahalar shaani wlh”

Sunacikin maida zancan ne,alhaji muhammad mai nasara,yai sallama,faruq ne,yamike daazamarsa, yanaiwa mahaifinnasa sannu da zuwa,

“Dady barka da yamma,hannu uban yamika masa,yanoke,dama sautari haka sukeyi,assadiq baya iya mikawa dadyn sa hannu sugaisa,amma banda faruq.

“Kaje gidan alhj Ibrahim din Kuwa?”

“Eh naje”,bansha wata wahalaba wajen gano gidan”

“To madallah”

Sai yanzu hajiya kareema tayiwa maigidan nata sannu da zuwa”

“Alhj sannu da zuwa yaaiki?”

“Yauwa hajiya,angode Allah,yagidan da yaran?”

“Lafiya lau”

“Ina yaran?”

“Suna dakinsu,faruq ne yasa sukai daki”

“Kai faruq,sai abarshi yana ina?”

“Yana dakinsa”

Hanyar dazata sada shi da falonsa yabi.yayinda hajiya kareema ta mike dan bin maigidan nata,faruq ne yadakatar da tafiyar data fara.

“Momy”

“Naam assadiq afito min da materials dinnan bayan magariba zanje gidan yaya hannatu”

“To,daga nan kabiya gidan mamanka aisha,kugaisa da muwadda zanbaka nawa,materials din ka kaiwa muwadda”

“Momy kenasaiwa fa,yazaki bayar”

“Karkadamu,inada wasu”
Shiru yayi yawuce yana mamakin wannan alamari dayake shirin samusa,nason auramasa yarinyar da bedauketa maceba.

*********

Ummi gaskiya su yaya amina sundade,cewar safiyya kenan”

“Kuma najaddada mata karsuyi magariba acan,baffanku bayaso yadawo yaga bakwa gida”
Sallamar najibace tatsayar da maganar da maganar da safiyya zatayi.”waalaiki salam,sai yanzu?”

‘Eh wallahi,yaya rukayya tanajin jiki”

“Subahanallahi,yajikin nata”

“Dasauki ummi”

“Najiba ina yaya aminar?”

Tatsayakantin bala,zata siyawa suhyla alawa”

“Najiba daita kukataho?”

“Eh,yaya rukayyace tace mutaho daita”

“Cab,zamu sha surutu yau”.dagudu suhyla tashigo gidan.

“Cayamu alaikum”
Dariya tabasu,musamman ummi da dadi yakamata,naganin tilon jikar tata.safiyyace taamsa mata sallamar tanadariya,

“Alaiki calamu”

“Aunt cafiyya,ummin aunt najiba ina kwana?”

“Ummice taamsa da kode ina yini”

“To ina yini”

“Lafiya lau,ummata tace tanagaisheku,tace inzo inkwana bata da lafiyaba,abbana yace baby zata haifamana,kuma bazamu bawa aunt cafiyya ba tunda batazo gidanmmuba.

Amina takatseta,”au kinmanta fadan da ummanki taimiki ko?” bari inmata waya ince kinfara”

“Dan Allah aunt amina kiyi hakuri karkifadamata wayyayi dukana zatayi”

“To,bani hakuri”

“Corry”

Dariya tabasu wai sorry,suhyla yarinya mai shiga rai daban dariya.can kuma tadubi ummi tace,

“Ummin aunt najiba mekika dafa?”

“Tuwo”

“Kai wayyayi bazanci tuwo ba”
Najiba ce tatambayeta
“To mazaki ci?”

“Ni ummata indomie take dafamin da kwai”

Malam kabiru ne yashigo shida matashin dansa,dagudu tamike tanai musu oyoyo

“Oyoyo baffan aunt najima,rungumeta yayi
“Suhyla saukar yaushe ?”
“Dazo,Kawu almuccafa ina yini?”

“Bazan amsaba sai kince almustapha”

Dariya tayi dan sunsaba haka da kawun nata.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO ✍🏻
[6:11Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

***_KANNAN MIJINA_*
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

=Dedicated 2 my adorable friend *sadiya smart*=

_I whish 2 my sweet sister 2 getwell soon_
*zee smile*😊

*3*

~~~~Assadiq ne yafito,cikin blue din shadda,dinkin boda,kansa sanye da hula kalar kayansa,yana kokari sanya agogo atsintsiyar hannusa,kirar rolex,mai aikin mami yahango,tana fitowa daga kitchen, dauke dawasu lafiyayyun kuloli ahannunta,tana kokarin shinfida ledar cin abinci akan kafet,

“Saa,zonan”

Da hanzari taajiye abinda take takaraso gurinsa,gaida shi tayi,yaamsa da sakin fuska,kasancewar sa mutum mai sanin darajar dan adam,

“Meyasa kike jera abincin anan?”

“Momy ce tace ajera anan,dady zai sakko yaci abinci anan”

“Ok,mekika dafa ?”

Jollof din shinkafa, da farfesun kaji,sai coslow,sai tuwon alkama daakayiwa dady”

“Ok,momy fa?”

“Tana saman dady”

“Shiga dakin su afifa kikramin farhana”

Amsawa tayi da “to”,tamike tana fargabar shiga dakin yanmatan saboda rashin kirkinsu,ahankali tatura kofar dakin tare da sallama,aikuwa abinda take gudune yafaru afifa ce,tadaka mata tsawa,

“Aa haba malama yazaki shigowa mutane daki kai tsaye?”

“Aunt afifa wlh nayi sallama”

“Dalla yimana shiru,”cewar farhana,jalila ce tatambayeta,dalilin shigowar ta dakinnasu,kasancewarta,mara son hayaniya miskila ita dai tafi ga karance karance,yanzuma sanye take da farin glass a idonta tana duba wani littafi,

“Dama yaya assadiq ne yace inkira masa aunt farhana”

“Jeki dalla ganinan ”

Tashi tayi taja musu kofar ta fita tana jinjina halin irin na yaran da agirme ta girmesu,afalon tasameshi shida faruq suna kallon mbc max,

“Yaya assadiq gatana,yaya faruq barka da hutawa”

“Yauwa saa”

Farhana ce ta fito sanye da kananun kaya ajikinta kalar purple kanta ba dankwali,takama gashinta da ribon kalar kayan,tana hango faruq azaune ta koma ta dakko mayafi tayafa,saboda tasan jarabar fadan yayannasu,

“Yaya sadiq gani ”
Faruq ne yadago ya kalleta,malama
sallama fa?”shiru tayi tana mamakin fadan yayannasu,katsemata tunanin nata yayi tahanyar dakamata tsawa,

“Koma kiyiwa mutane sallama”

Komawa tayi tayi sallama,sannan tace yaya assadiq gani”

“Naganki farhana,ina materials din dazu?”

“Suna daki”

“Oya,jeki dakko min na yaya hannatu,kihado min dana momy,

“To”

Tafiya tayi ta dakko masa,tare sukafito,da jalila,

“Ya sadiq gashi”

Karba yayi,yamike zai fita,da sauri jalila tabishi,

“Yaya assadiq dan Allah,ingidan yaya hannatu zaka zanbika”

Can zani,amma bazani da kowaba,hanya ce bakusaniba ko me?”

Yasakai yafita,gurin faruq tadawo ta zauna kusa dashi,yaya faruq sannu”

“Yauwa, jalila,zuba min abinci kadan”

“To, yayana, faruq da jalila tasu tazo daya saboda halinsu kusan iri daya ne.

Tunda assadiq yahau titi,yake tunanin zuwa gidan su muwadda,bayason iyayin yarinyar,gidan yayarsa yafara zuwa,dan yamatsu yaje yabata labarin sabuwar budurwar da yayi ,yasan zata fahimce shi,

A dai dai gate din gidan yahadu da mijin yayartasa,habib.

“Wanake gani kamar assadiq”

Dariya sadiq yayi,nine habib,
Musabaha sukayi suka gaisa,yatambaye shi su momy,yabashi amsa da “lpy lau”

“Yaya tana nan?”

“Eh,tana ciki assadiq,nima zandanje gidane,gurin hajiya”

“Ok,adawo lpy,agaisheta dan Allah,

“Zataji”

Motarsa yaja yatafi,shikuma assadiq yayi horn maigadi ya leko dan ganin waye,yanaganin habib ya wangale masa,gate din yashiga,yana dagamasa hannu,tsayawa yayi suka gaisa,yazaro dubu biyu yabashi,yanata zubamasa godiya,idi mai gadin su habib yanaso yaga assadiq yazo,saboda alherinsa.

 

Dasallama yashiga falon, dagudu yaran suka taso,suka kankame shi suna yimasa,oyoyo, daukan karamin yayi ya cillashi sama,

“Uncle oyoyo,cewar nabil,nima daukeni”

Sauke ashiraf yayi ya dau nabil,sunata da dariya,hayaniyar da yaran sukeyi ne yafito da mahaifiyar kyawawan yaran,dan ganin hayaniyar da yaran keyi,tozali tayi da kanin nata,dariya tayi .

“Lala assadiq,kai ne a gidan,sannu da zuwa.

“Yauwa yaya”

Alawa yarabawa yaran sukaita murna,yaya hannatu ce ta kwallawa mai aikinta kira tazo,taja yaran daki.

 

“Yaya ina yini”

“Lpy kalau kanina,ya momy na dasu afifa?”

“Duk lpy lau yanzuma sai da sukace zasu biyoni”

“Daka sani kuntaho,ya faruq?”yadauke kafa a gidan na kamar baya nan,

“Yana nan”

“Ya labarin muwadda?”
Murmushi yayi yace,

“Yaya abinda yakawoni kenan”

Nan yabata labarin haduwar sa da Safiyya,

Shiru tayi tana jinjina kalamansa,can tanisa tace,

“Bakomai assadiq inshaallah zan yi kokarin ganin kasami abinda kake so,

“Kaje kasami yarinyar kuyi magana tukunna”

“To, shikenan yaya zanje,kayan dayazo dasu yabata,taita murna tare da godiya kanin nata,yanuna mata Wanda momy tabayar yakaiwa muwadda,murmushi tayi,karshe yaimata sallama yatafi.

Agurguje yakarasa gidan su muwadda,yasameta kwance akan cinyar mamanta,dasauri tatashi tanai masa sannu da zuwa,nan yagaida mama suka dan taba hira,ya bata material yace,abawa muwadda inji mama,godiya tayi,yatashi dan yatafi,muwadda ce ta taso danyi masa rakiya.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO ✍🏻*
[9:14pm,2017.]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*>💦

**_KANNAN MIJINA**_
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

Godiya ta musamman gareku.

_Ummi B uba_

_Nafisa abas Nasidi_
_Safiya musa sopy💅🏻_
_Kawata kulthum_

=Dedicated 2 Alhj uba’s *Gawo*family=

*4*

~~~ yau takama lahadi alhj muhammad mai nasara yana gida,dan zama da iyalansa,yanzuma suna tare suna danyin break fast dukkansu,suna tare banda faruq,momy ce tatambayi assadiq ina faruq,

“Momy na leka dakinsa yana wanka”

“OK”,farhana jeki kirashi yafiya batawa mutane lokaci,yai sauri”

Tashi tayi dan kiran yayan nata,kwankwasa kofar sa tayi yatambayeta waye, nan.

“Yaya assadiq farhana ce”

“Shigo”,shiga tayi dan isar da aiken daakaimata,

“Ya faruq,the break is ready we are waiting 4 u”

“Ok ,sis dibar min wayoyina kimin gaba dasu,ganinan”

Diba tayi tafita,bata dade da fitaba,yajawo kofarsa yabi bayanta,sanye da 3quater baki,da farar riga armless baka,gashinsa kwance luf,
Sallama yayi yashiga falon,yagaida iyayen nasa yamikawa yayansa da dady hannu suka gaisa,kannansa ma suka gaidashi,yaja kujera yazauna dady ne yace da sadiq,

“Sadauki aimana addua”

Nan yaimusu addua kamar yadda suka saba,jalila ce tazuba wa kowa nasa abincin,

“Assadiq nagaji da zaman ka haka,yakamata kasamo mata kayi aure ,inba hakaba zanshiga rugar fulani insamo maka mata,

Dariya suka sa,mussamman faruq da yaji abinda dadyn yacewa yayannasa,afifa ce tai caraf tace,

“Dadyna yaya fa yanada matar dazai aura,

Wai haka sadauki”
Momy ce tai murmushi domin antabo masa inda yake mata kaikayi,

“Dady zamuyi maganar daga baya akwai abinda nake son kamallawa innagama,zanfadamaka,
[9:59pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FOURM*💦💦💦

💦 *T<W>F*💦

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

_Wannan shafinnaka ne_..
*Abdullahi Mina*
(Acida man👌🏻)

*5*

Momy ce talabartawa,dady san da muwadda,takewa assadiq,shiru yayi yana juya zancan daka karshe yai fatan alkhairi yakuma jaddadawa dannasa lallai yazo masa da magana mai karfi yaamsa da

“To,jiya naje gidan yaya hannatu tana gaidaku”

“Muna amsawa,cewar momy tana lpy”

“Lpy lau”
Dady ne yatambaye shi,
“Ina abokai na?”

“Lafiyar su kalau dady suna gaida abokinsu”

Dariyar jindadi dady yayi saboda irin san dayakewa jikokin nasa.tashi assadiq yayi,domin yiwa abokinsa waya.

Dakinsa yakoma yazauna,asaman gadonsa,yana neman layin abokinnasa,bugu 2 yadauka,

Hello acida man”

“Ya akayine chairman,akwai labari ne?”

“Kwarai kuwa,”

“Gurin muwadda zamuje”

“Bansaniba,kajirani da yamma mallam,zaka rakani unguwa,

“Ok,sai kazo”

Sallama sukayi,yafara tunanin irin shigar dazaiyi kamar wanda aka tsikara yatashi yabude kwabar kayansa,yafara Mazarin kayan dazai sa,dakyar yazabi wani farin tsadaddan yadi,ya dakko bakar zanna bukar,da bakin takalmi.

Yamma nayi yashiryo dan fita,dakin momy yashiga yatarar bata ciki,sai jalila kwance da littafi a hannuta,tambayarta yayi,

“Jalila,momy fa ”

Dagowa tayi dan bazaci shibane,

“Wow yayana kayi kyau,momy tana kitchen”

Dariya yayi yafita,zuwa kitchen,acan yasameta,tana nunawa saa kayan daaka kawo naamfanin girki,

“Momy sannu da aiki”yauwa asssdiq”

“Sai ina kenan”

“Momy zanje gurin abdullahi acida”😜

“Ok” balaifi,Allah ya kiyaye”

“Ameen momyna”

Fita yayi da hanzari dan zuwa gurin abokinnasa,yana mai adduar samun nasara,yanazuwa ya dau abikinnasa su kama hanya,yana kallon shigar abokin nasa yafara yimasa tsiya,

“Chairman ina zamuje Neman auran?”
Dariya yayi,kana yace,

“Janbulu”

“Aa,nazaci zoo road zamu”

rai yabata kafin yace,
“Bacan zamuba”

“,au”kawai yace masa.
Suna isa yayi parking dai dai kofar gidan su Safiyya,yaro yasamu yatambaya nan ne gidan su safiyya,yace masa,

“Eh”

“Shiga kace ana sallama daita,

Suna zaune ita da yanuwanta,tana yankewa suhyla farce,yaron yashigo da sallama.

Amsawa sukayi,kana yagaida umminsu,ta amsa da faraarta,

“Ummin su najiba wai safiyya tazo”

“Injiwa sabiu”

“Wasune a waje”

“Jeka kace gatanan”

“To”

Tashi tayi takara gyara fuskarta,taja hannun suhyla suka fita,tana karasawa tayi tozaly da assadiq mamaki ne ya cikata,sallama tayi musu kana ta gaidasu,tunda acida,yaga safiyya yayaba da zabin abokinnasa,

“Safiyya nazo har gida inkuma jadda da godiyata agareki,inkuma miko kokon barata gareki,kamar yadda nafada miki suna na assadiq muhammad mai nasara, wannan kuma abokina ne,sunansa Abdullahi mina,amma ina kiransa da acida”,

Jinjina kai tayi tace ,

Nafahimta,to amma mekakeso inmmaka?”

Acida nai yakarbe maganar,nan yayi mata bayanin abinda yake tafe dasu,tafahimta,karshe tabashi number wayarta zata fadsmasa abinda yanke,

“Allah yasa acikin Daren nan zaki fadan ,inbahaka ba,acida inzuciyata ta buga to,fa safiyyace sila dariya suka sa dukansu,

Sai yanzu ssadiq ya kula da suhyla makale abyan suhyla,

“Aa safiyya wannan beautiful dinfa?”

“Yar yayata ce”

“Yasunanki?”

“Cahyla”

Dariya yayi yatambayi safiyya sunanta tafadamasa”

Dazasu tafi yafakko kudin yabata,tana karba taga yan dubu dubu ne mikamasa tayi,

“Karbi kudinka banason kudin manya ni cai kudin,yara”

Dariya tabasu sai yadakko 20 yabata yace,

“Toga naki,wannan Kuma,kibawa auntinki,”

“To, nagode uncle

Sallama sukaimusu sukatafi, suma suka shiga,gida.

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:36Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

_Ina bawa masu karatu hakuri sakamakon matsalolin daaka samu,a page4&5,dafatan zaaimin uzuri kasancewa ta yar koyo,a harkar rubutu_.
*Nagode*🤦🏻‍♀

 

_Gaisuwa ta mussaman gareku_

_Fatima abdu bulawis_
_Bushira sani_
_Aisha (hiran)_
_Hajara yar Madara_.

 

=Dedicated 2 aunt majida & aunt sadiqa
*TWINS*

 

*6*

 

~~~Suna shiga gida,tafadawa umminta, wanda yazo gurinta,Amina ce tazaro ido waje,tadubi yar uwar tata,kana tace,

“Safiyya dagaske kike”

“Au yaya amina,kema kinsan karya bata cikin tsarina”

Ummin suce takatse,su ta hanyar tambayar su waye shi,

“Ummi bakisan alhaji muhammad mai nasaraba?”
Cewar amina,tana mai jinjina irin kamun da yaruwar tata tayi,

“Inajin samana a gidan radio,ba tsohon kwamishan ilimi ba”

“Shi ummi,to dansa assadiq ne yazo,wai yana sona”

“Kayya safiyya,yaudarar ki zaiyi,tayaya kamar wadannan mutanan suzo neman aure gidannan,to,tsayama a Ina kuka hadu?”

Nan tabasu labarin haduwarta da assadiq,tadora da

“Wlh ummi yace aurena zaiyi”

“To kedin me kikace masa?”

“Ummi cewa nayi yadanjira tukunna”

“Shi kenan safiyya,Allah yai zabin alkairi,amma ina jinjina lamarin”

“Bakomai ummi kitayata da addua”

“Shikenan amina”

Nan safiyya tabasu dramar da suhyla tayi,sukaita dariya.

 

 

Tunda assadiq yasauke abokinsa,yake,
zumudin yakoma gida,yakira safiyya,sanda,yashiga falon ba kowa duk suna daki,dakin faruq yashiga yatarar dashi a zaune yanadanne danne waya, dago da kansa yayi dan dama yasan bawanda zai shigo masa,daki dai dai wannan lokaci inba yayan nasaba,

“A bross barka da shigowa”

“Yauwa umarul faruq,yaakayi yau bakowa a falon?”

“Eh,kasan gobe monday,akwai school,shiyasa nakora yaran can daki su kwanta,sunfiya kallon tsiya,kaga shegiyar yarinyar nan farhana bata da aiki sai sa tv agaba”

“Sannu faruq da kokari yarannan kamar yayanka,to amma sai gashi kai baka kwantaba,bansaniba,
ko kai lectures ce baka daita,goban?”

Kansa yadan shafa kana yadubi yayannasa yace,

“Bross yazaka hadani da yarancan,ina browsing din wani assignment ne”

“Yayi kyau kawai yace dashi yaja masa,kofar yafita,dakinsa ya shiga yarage kayan jikinsa yafada toilet ya watso ruwa yafito,bayan yagama shirin sa tsaf,yakoma saman gadonsa,yakwanta,wayar sa ya dauka,ya shiga,neman layin safiyya sai da takusa tsinkewa sannan ta dauka,

“Hello,sopy”
Jin muryar tasa tayi har cikin kwanyarta,

“Naam”

Nan suka kuma gaisawa taimasa ya yaje gida,

“Lafiya lau,ina amsata ta dazu ?”

Shiru tadanyi dakabaya kuma ta furta a hankali kamar yana ganinta,

“Na amince ”

Farin cikine ya kamashi,tana gama fada takashe wayar,wayar yacire,saga kunnan sa,
yazubawa ido,kamar sahibar tasa yake kallo,dahaka yaja lafiyayan bargwansa,ya kwanta,da tunanin sopy aransa.

~~Washe gari da karfin gwiwarsa ya haura saman dadyn nasu,da sallama yashiga,falon hajiya kareema,zaune a gefan mai gidannata tacaba ado,da hadaddiyar shadda combination da paper lace,coffee da orange,dinkin sanigal,

“Momy ina kwana ”

Lpy lau,assadiq,jiya Baka dawo da wuriba ko?”

“Eh momy acida ne yarikeni da hira’

“Dady barka da asuba”

“Yauwa sadauki,wannan sammakon fa?”
Allah,yasa office kayiwa”

Kansa yasunkuyar kasa kana yace “Eh, dady da office dinmma,kuma da maganarmu tajiya”

“Inajinka sadauki”

“Am,dama wata yarinya nagani shine nakeso,a nema min auranta”

“Mashaallah, a ina kasami yarinyar?”

“A janbulu take dady”

Momy ce ta harzuka tafara fada kamar tari baki,dady ne yadakatar da ita,

“Hajiya kareema! ya isa ,da Allah,meye haka,kina zaton zanyiwa yarana dole ne,to,banyardaba,shiru tayi tana sakesaken yadda zata bullowa lamarin,

“Tashi kaje sadaiki zanyi bincike akan yarinyar”

“To dady”

Kan sadiq yatashi,hajiya kareema tafice cikin fushi.

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

*💦T<W>F*💦
[1:30pm,2017.]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

**_KANNAN MIJINA_**
����‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_=Dedicated 2 my lovely brother_

*Alhaji karami ismail uba*💖

_Allah yadawo mana da kai lpy yabaka nasara a karatunka_.

 

*7*

 

~~~Tana barin dakin,dakinta tashiga,farhana ta tarar aciki,bacin ran uwar tagani tabar abinda take,tabari ta tataho gurin uwar,

“Momy me yasameki?”

“Hmm,farhana yanzu abinda assadiq zai min kenan”

“Momy meyayi miki haka”

“Duk tsawan lokacin dana dauka ina nuna masa burina nasan aura masa muwadda,yaron nan yasa kafa yai fatali dashi,

Nan ta kwashe komai tafada mata,nan take tafara zuga uwar kan karta bari yaauri wata mace inba muwadda ba,

“Haba momy wallahi karki barshi,akan me zai auro mana bare,to wai ma momy wacece,yariyar dayake son ya aura,a ina take,waye ubanta a kano?”

“To wayasani,farhana,yade ce a jambulo yarinyar take”

“Momy kira yaya hannatu kifadamata,tunkafin azo aji kunya,itama aunt muwaddar duk daita,kanason mutum amma baka bibiyarsa,haba meakayi kenan”

Wayarta ta dakko,tafara neman layin yar tata,tanata kira ba tadagaba,tsaki tayi,

“Tace bata daukaba”

Ana haka sai gashi takirata,dauka tayi takara wayar akunnanta,

“Hello”

“Momy antashi lpy ”

“Lpy lau hannatu,yagida,yasu nabil?”

“Lpys kalau momy”

Nan takwashe komai tafadamata,jinjina kai hannatu tayi,tare da zaro ido,kamar uwar na kallonta,

“Momy zancan nan bazai yu awayaba,kibari zanzo anjima”

“Shikenan hannatu sai kinzo”

*********

Ummin su safiyya ce takebawa baffa labarin saurayin da safiyya tayi jiya,shiru yayi yana jinjina lamarin,can yanisa yace,

“Wato nafisa shi lamarin aure na Allah ne,in yakaddarawa,safiyya auran yaron nan tofa,bamu da jaa danhaka mubarwa Allah”

“Hakane baffan najiba”.

Abangaran dady kuwa
yanafita,yakira assadiq a waya dan ya kwatanta masa,gidan su safiyya,abokinsa,
yadauka,alhj salihi suka tafi,basu sha wahalaba,wajen gano gidan,suna Isa,suka aika yaro,yai musu sallama da maigidan,
Akai saa yana gida befitaba,yanafitowa,
Yaga bakin fuska,

 

Sitroom din gidan yabude musu,iso,shiga sukayi suka gaisa,a mutunce,duk da basu san junaba,

“Ni sunana alhj muhammad mai nasara,

“Aa to,to, mahaifin yaron dayazo jiya?”

“Eh,wannan kuma,abokina nane alhaji salihi”

“Mashaallah sannuku
dazuwa”nan suka sabuwar gaisuwa,suka gabatar da abinda yakawo su,yayi murna sosai yakuma yaba da karamci irin na dadyn assadiq,

“amma alhaji da wuri haka,nazaci jiya yafara zuwa wurin yarinyar”

“Eh ai nazo nema masa izinin zuwa gurinta zance ne kafin mudawo,neman aure”

“Hakane,to ni anawa bangaran nabawa assadiq safiyya”

Dadi ne yakama dady,yakuma tabbatar masa zasu dawo,nan kusa danyin maganar aure,sallama sukayi suka tafi,yana komawa gida ya sanarwa, matar sa nafisa yadda sukayi,

“Baffa wannan wani irin alamari ne,jiya fa yaron nan yafara zuuwa,amma ace har mahaifinsa yazo,shi kansa yaron bamu saniba,

“To shine me?”nafisa,
Ai magana takare tunda gashi mahaifin yaron nan yazo, koh”

“Hakane baffa,Allah yasanya alheri,

“Ameen”

 

Dady ne yakira assadiq awaya ya shaida masa,yadda sukayi da mahaifin safiyya,godiya yayi sosai,sukai sallama.

Assadiq ne yakira safiyya a waya,

“Hello,matar assadiq”

Dariya yabata,

“haba AB daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaki”

“Sopy meye maanar AB,”

“Abubakar”

Dariya ta bashi,

“Kitambaya a gida,kice waye mijin sopy kiji”

“Allah yasawake,bazan iyaba,

Sallama yayi mata yakuma shaida mata,zai zo yagaida,su baffanta.

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

*💦T<W>F*💦
[9:55pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

***_KANNAN MIJINA_***

👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

*8*

 

~~~Abangaran hannatu kuwa,sauri tayi takamalla abinda take,tashirya yaranta maigidanta yajasu sukatafi,a hanya take dada bawa mijinnata labari,shiru yayi kana yace”

“Bekamata ayiwa assadiq doleba,duba da yanayin da muke ciki na sauyin zamani”

“To ai shine”

Ahaka har suka karasa gidan sunayin parking nabil yabude murfin motar yashiga cikin gidan da gudu,

“Uncle assadiq,uncle faruq kuna ina”

Bakowa a gidan duk sunfita,saa yagani a falon tana goge goge, sakin tsumman tayi ta karaso gurin yaron,

“Oyoyo,ga nabil,

“Ina su aunties?”

“Basanan,suntafi makaranta”

“Momy fa?”

“Tana dakinta”

Karasawa yayi dakin nata,sanda ya shiga tana bandaki,tana fitowa taganshi,

“Aa wanake gani”

“Nabil habib rano”

“Hmmm,kai dawa?”

Nida mamma”

Suna haka sai ga hannatu tashigo dakin

“Salamualaikum

“alaiki salam ”

Momyna Ina kwana”

“lpy lau hannatu,ya habib din”

“Yana falo,yanajiranki ku gaisa”

Mayafi tadauka,tafito dan su gaisa,da sirikin nata,yana ganin tafito,yazame daga kan kujrar,yatsuguna

“Momy ina kwana?”

“Lafiya lau habib,yasu hajya?”

“Lafiyas kalau”

Sunagama gaisawa yatashi zaitafi,yazaro kudi a aljihunsa ya ajiyewa momy,godiya taimasa,ashiraf ne yasa kuka zaibi abbansa,rakashi sukayi shida hannatu suka dawo,

“Momyna meyake faruwa ?”

“Nan tabata labarin abinda yafaru,

“Momy dan Allah kiyi hakuri kibar assadiq yaauri wacce yakeso,bawai banason auransa da muwadda bane,aa zaa duba masalaha ne,momy yanzufa zamani yacanja ga yadda aure yazama alallaba

_sabon littafina_*alallaba auran zamani*

“Yaisa haka hannatu rufemin baki,mekikeso kice min,kinason kice kina goyan bayan assadiq yaauro wata ba muwaddaba?”

Nandai momy taitafada karshe dai hannatu hakuri tabata tashaida mata zasuyi maganar da assadiq inyadawo,

Da yamma Kowa yadawo suna falo dukkansu sunata hirarsu gwanin shaawa su ashiraf sai tsalle suke akan faruq,duk da halin fadansa, yana son yara,

Dadyne yashigo da gudu yaran suka je suka rungumeshi,cikin doki yake tambayar su

“Abokan dady,saukar yaushe”

“Dazu abbanmmu yakawo mu,dady banje school bafa yau,bani da lpy”cewar nabil,

.faruq ne yai caraf,yace

“Baka da lpy kake tsalle a Kaina”

Dariya sukayi dukansu,zama yayi dadyn suka gaisa da yayan nasa,mussamman hannatu dayaji dadin ganinta,anan yakebasu labarin yadda sukayi da mahaifin safiyya,

Nan momy tai tsalle ta dire,bata yardaba

“Hmm hajiya kareema kenan kamar kinmantani koh,to ai ba laifi kiyi,babbar rigarsa yakade yaja hannun jikokin sa yai sama,nanfa faruq da hannatu sukaitabawa momy baki

“To ku yanzu mezancewa aisha,kunaso ince mata kafasa auran muwadda?to ni baruwana da auranka inko bazakajanye ba,to,sai dai kahadsu biyun kaura,dukkansu sun razana dazancan momyn tasu banda farhana da afifa,

“Shikenan momy naamince,amma zanfara auran safiyya tunda ita muwadda bata karasa makarantar ta ba”

“Duk yadda kayi dai dai ne,zanje da Karina infadawa Aisha yadda mukayi”

Hannatu ce tai musu sallama tatafi da kyar nabil ya yarda yabita shi dai kwana zaiyi gurin aunt jalila,

Faruq ne yakoma daki yasha hirar sa da rabin ransa,karshe yace tarufe idonta yai musu adduar bacci kasancewar dare yayi.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

💦 *T<W>F*💦
[1:48 pm,2017.]

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_ Ina mika godiya ta mussamman ga masoyan kannan mijina novel
*Nagode*

*9*

~~~ Baffa ne,zaune shi da matarsa,suna taba hira,saiga dansu Dr almustapha ya shigo,

Gaida iyayannasa yayi,
Sai yadora da,

“Baffa ance jiya anzo neman auran safiyya,gashi ko yaron bamu saniba”

“Hakane,mustapha,ai abunda mahaifin yaron yayi,ni naji dadi dakansa yazo yanemawa dansa izinin zuwa zance gurin safiyya”

“Hakane”
Cewar ummi ai shine dai dai dama,dazu ma tace zaizo da yamma yagaida mu”

“To ba laifi yayi kyau,zanyi kokari indawo da wuri,inshaallah ,yakamata kaima almustapha kasamo mata,kai aure,zaman haka bashi da amfani”

“Baffa zanyi inshaallahu,nafiso inkammala gini nane,tukunna”

“Eh hakanmma yana da kyau,Allah yabada nasara”

Ameen baffa,bari inzo inkaika,kasuwar”

“Aikinka fa,ko babu?”

“Da akwai,baffa amma sai dare,yau inada call ne”

“To balaifi,Kenyan inkatafi acan zaka kwana?”

“Eh,baffa”

Fita sukayi ummi tai musu fatan dawowa lpy.

Basu dade da fitaba,rukayya tashigo,

“Assalamu alaikum”

Waalaiki salam,aa rukayya sannu da zuwa”

“Yauwa ummi,ina kwana”

“Lpy lau,yajikin naki?”

” da sauki,yanzuma daga asibiti nake,nacewa yusif yasaukeni a nan”

“Allah sarki”

“Ummi,nagaji ga yunwa”

“To mezakici?”

“Yimin danwake”

“To”

Tashi tayi tadoramata danwaken sunataba hirarsu,anan take bata labarin saurayin Rukayya,tai farin ciki sosai,

“Ummi suna ina ne gidan shiru”

“Zainab tatafi,B U K.
Najiba tana makaranta,kasancewarta yar secondary, safiyya kuma naiketa gidan aunty bara ita da suhyla”

“Ummi yazancan makarantar Safiyya?”

“Jamb zata canja tunda bata samu taciba”

Daki rukayya,takoma tadan kwanta,su Safiyya ne sukadawo,suhyla tana ganin takalmin ummanta,tashige dakin,

“Ummata! Ummata!”

Afirgice rukayya ta tashi dan har tafara bacci abinka da mai ciki,nan tafara mata Dada,

“Suhyla kina haukane?”,meye haka,zaki fado kainane?”

“Aa,umma kiyi hakuri,na dena”

“Karma ki dena,kicigaba da shashanci”

“umma ina abbana?”

“ya wuce kasuwa,yana gaidaki”

Safiyyace tashigo da sallama,dauke da plate din danwake,nan suka gaisa da yayar tata taimata yajiki,taajiye mata danwaken agabanta,
tsokanar ta farayi.

 

“Safi amarya 2 be”

“Kai yaya rukayya”

Danwaken tabude zata fara ci,taga har da dafaffan kwai,

“Kai ummi data sani bata dafamin kwaiba,banaci,karni yakemin”

“Mu zamuci ko suly”?

“Aa,wlh aunty safiyya bazanciba,tunda ummata bata ci”

Dariya tabasu dukkansu,ana haka su zainab sukadawo,nan suka hadu sunata hira gwanin shaawa.

°°°°°°°°°°°°°°
Abangaren assadiq tun a office yake Allah Allah yamma tayi yaje gidansu safiyya,wayar sa yadakko,yaddana lambar abokinsa,

“Hello”acida man”

“Chairman,barka da rana”

“Yauwa,acida,zanshigo anjima zaka rakani gidan su mutuniyar”

“Muwadda?”

“Bansaniba mara mutunci”

Dariya yayi kana yadora da,

“Wlh bana gari naje mina,amma why not kakira dan shuwa”

“Wai Ebet”

“Eh”

“Ok,sallama sukayi,

Yafara neman layin abokinnasu wato,Abdullahi dan shuwa.Ebet

“Hello,Ebet,kana gida ne anjima,zanzo ,karakani uguwa”

“Eh chairman ina gida,

“Kashirya anjima zanzo karakani,gidan surukaina,ammafa kasanya manyan kaya”

“Dariya yabashi,”dagirman kujerarka,chairman ”
Sukai sallama.

Assadiq yana barin office, gida yawuce yashirya cikin dakakkiyar shadda multi colour yasanya hula kalar kayan,sai kamshi yake ,yafice daga gidan,be yarda sunhadu da momy ba.

Yana isa gidan abokin nasa yaimasa waya yafito,sutafi kiyayi yace lallai sai ya shigo sungaisa da matarsa,dole yafito daga mota,yarufe yashiga ciki,sallama yayi,tana zaune ta katon cikinta,agaba,fara tas daita daka ganta kaga shuwa,

“Amarya ya gida?”

“Lpy,ya kake?”

“Lpy lau aran angonki zakibani”

Dariya tayi,tace”gashi nan”

Godiya yayimata yazaro kudi yabata taimasa godiya

“Shukuran”
Mijinnata ne yamatsa kusa daita yakira sunata

“Khadimalla bari inraka shi indawo kinji bejira amsartabawa ya sumbaci cikin jikinta yafita.

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA I GAWO*✍🏻
[6:01Am,2017.]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

💦 *T<W>F*💦

**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA. I UBA*💐

 

*10*

 

 

~~~Su assadiq suna fita,yatsaya a wani babban mall,yayiwa safiyya siyayya,ciki kuwa har da wayar hannu mai tsadar gaske,suna isa kofar gidansu,yakirata awaya yashaida mata karasowar su,lokacin duk suna zaune har da yayansu,Dr almustapha,fadamusu tayi,atake yayannasu yafita yaahigo dasu,

“Salamualaikum”

Nan yabasu hannu suka gaisa,ni suna na
Almustapha kabeer,”

“Nikuma assadiq Muhammad mai nasara,wannan aboki nane,abbdullahi(Ebet)”

“Mashaallahu bisimillah ku shigo”

Nan suka sa kai suka shiga aka saukesu afalon baffa,suka gaisa,da kowa,agirmame,baffa ma yashigo,suka gaisheshi,kasancewar yadan fita,bayan yadawo daga kasuwa,nan kowa,yafita,yabarsu,
Sai suhyla tanata musu surutu,

Safiyyace tashigo cikin wani material mai fulawowi,green da orange,tunda ta shigo ya zuba mata,ido yana dada yabawa da zabin da yayi ,

“Inayinin ku”

lafiya lau amarya ta”

Kunya yabata,tagaida ebet yaamsa cikin sakin fuska,nan assadiq yagabatar mata da abokinnasa,ya kuma shaida mata,acida yana gaidata”

Nan dai abokin yaimata sallama yabasu guri su za ta,

“Safiyya naga Dr almustapha a ina yake aiki?”

“Aminu kano”

“Wacece mai kama da ke,nazacifa kece”

Aa autarmu ce najiba”

Kaga daga yaya almustapha,sai yaya rukayya,sai yaya zainab,sai ni,sai najiba”

“Ok yaya rukayya itace maman suhyla?”

“Eh”

Assadiq yana so yaga safiyya tana magana tana motsa dankaramin bakinta,

Nan dai suka taba hira karshe yai mata sallama yafito,yaiwa su ummi ma yafita, sabiu yagani zai shiga gidan yabashi kayan dayakawo mata ya kai ciki,yaja motarsa sukatafi,ahanya ebet yake yaba zabin abokinnasa.

°°°°°°°°°°°°°°°

Farhana ce kwance kancinyar momy suna kallon dubai 1,can ta dago takalli momyn tasu

“Momy yakamata ki kira aunt aisha kifadamata halin daake ciki”

“Yi shirunki farhana gobe insha allahu zanje da kaina muyi maganar”

“Yauwa momy,zanbiki ma,wlh tunkafin inga yarinyar da ya assadiq zai aura naji na tsaneta”

“Nima raina be kwanta da itaba farhana”

 

Faruq ne yashigo yana ganin farhana a cinyar momy yafara mata halinnasa na fada,

“Ke meye haka, dalla dagata

Baki ta turo gaba,tatashi,

“Faruq ina ruwanka daita ne”?
Meyasa baka san zaman lpy ne dan Allah,

Tasowa yayi yakwantar da farhana kancinyar momy,

Kwanta farhana Allah ya huci zuciyar momy na,nidai gyara nake”

Assadiq ne yashigo falon da sallama,

“Momyna sannu da gida”

“Yauwa assadiq,daga ina haka?”

Naje gidan ebet ne”

“Allah sarki ya matar tasa,tahaihu koh?”

“Aa ta kusa dai”

Faruq ne ya kalli yayan nasa yace ,

“Wow bross gaskiya kayi kyau,ko de ….. .,

Dariya yayi yace,

I will talk 2 u later”

“Ok”

Washe gari da yamma momy suka je gidan yar urwata aisha,nan take shaida mata abinda yafaru shiru tayi kana ta nisa tace ,

“Yaya ai shikenan bakomai ,amma assadiq yabatawa muwadda lokaci,gaskiya

“Haba aisha ai aure ba fashi sai anyi”

“Aa yaya muwadda bazata iya zama da kishiyaba”

Da kyar dai taamince zata aurawa assadiq muwadda,shi gogan mma besan wainar daake toyawaba.momy ta umarci muwadda data dinga kiransa suna gaisawa.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*11*

Shakuwa,mai karfi ce ta kullu tsakanin asaadiq da safiyya,yakaita gidan yayarsa hannatu sungaisa,tayaba da zabin kanin nata,a lokacin su jalila suna gidanta,safiyya ta tsorata da irin kallon da kannan assadiq sukai mata,bata kawo komaiba,

°°°°°°°°°
Ayau alhaji muhammad mai nasara,yaje nemawa dansa auran safiyya,shida yayansa,alhaji munir mai nasara,sunkai kudin aure,dubu100k tare da sanya rana,anyi komai cikin mutunci,

Assadiq ne kwance a luntsunme men gadonsa,yakira layin safiyya,

“Hello”

“Matar assadiq”

“Au har nazama matarka?”

“Kwarai kuwa,me yarage,shafa fatiha”

“Haka dai kace,ya momy,da su afifa?”

“Suna lpy,suna gaidaki”

“Safiyya”

“Naam A B”

Wace irin kulawa zakibani inmunyi aure”

“Hmm AB kenan sai munyi auran tukunna ko?”

“Banyarda ba gaskiya sai kinfada min”

“Naki,wayon”

“To ni bari infada miki irin kulawar da zanbaki kinga ni zandiga baki abinci abaki,inmiki tausa,ke har wanka dakaina zanmiki”

Dariya yabata dif takashe wayar tana dariya,

 

Almustapha ne suke tattaunawa da baffansa kan auran safiyya,

“Wato,mustapha naso ace,yaron nan khalifa yadawo daga tafiyar nan da yayi,da sai ahada auran safiyya dana zainab”

“Eh wallahi baffa,amma tunda bekamalla karatunsa ba dole ajira shi ai,inyadawo ayi”

“Haka zaai,mustapha,sonake afara siyayyar kayan daki ko?”

“Eh baffaa hakane,ai inshaallahu baabinda zai gagara,zanyi iya yina danganin baaji kunyaba”

“Allah ya nufa mustapha,yanuna mana lokacin”

“Ameen baffa”

°°°°°°°°°°°°°°
Alhaji Muhammad mai nasara ne,zaune tare da iyalinsa,suna tattaunawa kan bikin assadiq,

“Wato, hajiya kareema sonake ayi bikin da bazaaji kunyaba,saboda haka ina ganin zanbaki kudi kuje dubai kuhado lefe,sannan gidan nan nakusa damu angama sai kazauna aciki”

“Dady pls dani zaaje”

“Kinji afifa,dawata magana,to dani zaa”

“Yaisa haka farhana”

“Ai alhaji ina ganin basai anje dubaiba, anan ma hada lefe zaai”

“Hmm hajiya Kareema kenan,nafahinci bakyason auran nan,to ba laifi,abinda zaai kai faruq kaje gidan yayarku hannatu kace tazo ina nemanta”

“To,dady”

“Inyaso ita
sai suje dasu jalila”

Sai yanxu assadiq yasa baki,

Dady na nagode madalla allah yaja kwana,yakara girma,

“Ameen sadauki”

Assadiq beji dadin abinda momynsa tayi masaba,amma bayyada zaiyi yaji ya gani,

 

A haka lokaci yaja,su hannatu suntafi dubai siyayyar kayan lefe,datasu siyayar,momy cetaiwa hannatu waya lallai asiyowa muwadda kayan fitar biki,bayadda taiya haka tashiga yiwa muwadda siyayya .

 

Muwadda ce zaune a garden din gidansu tana ta kiran layin assadiq tana ta ringing bai dagaba,sai daga baya yadaga,

“Hello,ya assadiq,ina yini”

“Muwadda,kina lpy,ya mama?”

“Lpy lau,ya assadiq sometimes innakiraka,baka amsawa,meyasa?”

“Am,kingane ne,muwadda wani lokacin ina aikine,bancika amsa wayaba”

“To,shikenan,yanzu yaushe zakazo”

“Muwadda kenan da inzanzo ke kike sani”?

“Aa”

“To kizuba ido,duksanda nasami time,zanzo”

zatakara magana yakatse wayar,ransa a bace,safiyya ya kira suka sha soyayarsu,karshe yace tafadawa ummi nan da sati 2 zaakawo lefe,gabanta ne yafadi,data tuno kannan assadiq.

su yaya hannatu,sundawo,tayo kaya masu yawa da kyau,momy taga kaya nan tasa yartata a gaba da fada,

“Hannatu wannan uban kayanfa,kina da hankali Kuwa?”

“Haba momy yanzu ba girman mubane,ace assadiq yakai wadannan kayan”

“Rufe min baki,hannatu,ai nafahimci inda kika sa gaba”

Afiface tasa baki,

“Wlh momy tun acan,naceewa yaya,kayan sunyi yawa”

Azafafe yayar tasu tadauke,kanwar tata da mari,

“Afifa har kinyi girman da muna magana,kisa baki,to kici gaba”

Tundaga wannan lokacin afifa tadada tsanar safiyya.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[11;29 pm,2017.]

 

*💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

_godiya tamussamman gareku mosayana nagode Allah yabar kauna_
_ina maraba da duk wanda yaga gyara acikin labarina ko a rubutuna,kofa abude take dan karbar gyara daga gareku masoyana_

*NAGODE*👌🏻

 

 

*12*

Safiya nagama waya da assadiq,takira zainab tafadamata dan tafadawa umminsu,tanagama fadamata tafita tasami ummin tasu a kitchen,

“Ummi sannu da aiki”

“Yauwa zainab,bani kulolin can

“To ummi,yauwa wai nan da sati biyu su assadiq zasu kawo lefe”

“Oh!ni nafisa abun yazo,to Allah yakaimu”

“Ameen ummi,yazu meyakamata ashirya?”

“To sai dai ayiwa Rukayya waya,aji meyakamata ayi ko?”

“Hakane ummi”

“Yauwa Allah ya kaimu yasa ayi damu”

“Ameen ummi”

 

Assadiq ne sukaje gidan yayarsu shida faruq dan tattaunawa akan bikin,nan take basu labarin yadda sukai da momy da afifa,faruq be yai kwafa,kana yace,

“Wlh yaya shiyasa banason shiga sabgar yarannan basu da kunya”

“Kabarsu faruq zasuci ubansu,wlh”

“Yaya pls Mubar zancan nan,nida shawarar danayake itace,mezaihana su dandy sukai lefan nan,ko kuwa?”

“Yayi daidai,bross gwanda mukai wlh

“Au faruq har da kai?”

“A yaya hardani zaa”

“To shikenan assadiq yayi,but u should talk 2 dady ”

“OK yaya I will”

Su nabil me suka shigo falon da gudu,

“Uncle faruq oyoyo”

“Uncle A,ina dady?”

“Lpys kalau my boy”

Nan dai sukaitai masa sharrrinmansu,yaraba musu alawa,karshe sukaiwa yayartasu sallama sukatafi,

 

Hajiya kareemace zaune ita da maigidan nata,tana yanka masa fruit, assadiq yai sallama yashigo,nan yagaidar da iyayensa,

“Dady barka da dare”

“Yauwa sadauki”

“Momy na sannu da gida”

Sannu,assadiq”

“Dady dama wata shawara ce nazo daita”

“Inajinka sadauki”

“Dady me zaihana kasa su baba salhi da abba munir sukai kayan lefan na”

“Tunaninmmu yazama daya sadauki,haka zaai zan musu magana inshaallahu”

Momy tanjinsu bata tofaba,

“Hajiya kareema bakice komaiba”

“To mezance alhaji,ai tunda assadiq yagama shawara da yaruwarsa hannatu aishikenan kuma”

Dariya yayi yadubi dannasa,

“Sadauki tashi katafi Allah yabada alhr”

Tashi yayi yafita yaimusu sai da safe,

Nanfa dady yarufe momy da fada,daga karshe yaimata nasiha,dole ta hakura ta karbi safiyya a matsayin surukar fari,

Su farhana kuwa sun ci burin wulakanta safiyya,da muzguna mata,

 

 

A yau aka kai kayan lefan safiyya kamar yadda assadiq yaso mazane suka kai akwaati saiti 2 cike da
Kaya na afarama ,ansa biki wata guda,sunsallamesu da kayan arziki,da tukwaicin 100k Dr almustapha yabayar,

Hakika lefan Safiyya yaja hankula anata turuwar zuwa kallo,mussamman kawayanta…….

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
*[2:09pm,2017]*

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*13*

 

~~~Tunda aka Kai lefen Assadeeq ya kasa zaune ya kasa tsaye farin ciki ya mamaye zuciyarsa yanzu haka ma tunanin gimbiyar tashi yake a karshe ya yanke shawarar kiranta bugu biyu ta dauka cikin salon muryarta mai kashe masa jiki tace
“Assalamu Alaika”

Cikin wata kasalalliyar ya kishingida a jikin kujerar office en nashi ya amsa mata da
“waalaikissalam Amaryar Sadeeq ya kike? Yasu umma da kowa

“Tace lafiyar su kalou ya aiki”

“Yace Alhamdulillah ya ake ciki hope kinga kayan nan kuma ena fatan komi yayi miki idan akwai abinda bai miki bah ki sanar dani kinji babyn Sadeeq.

Tayi murmushi hade da rufe fuskarta da tafikan hannunta kamar yana ganinta cike da kunya tace komi yayi min Allah ya saka da alkhairi Allah ya maida abinda aka 6atar.

“Yace Ameen baby nah Allah ya nuna mana lokacin da zaa kawo min ke dakina😀”

“Tace Hmmnn 🙈

“Yace kinga malama nifa bana son hmmnn en nan kice Ameen kawai kina so kina kaiwa kasuwa kinga dan saurayi kin rikice ya karashen zancen yana fashewa da dariya don yasan halin kayarsa baza ta tanka masa ba

“Tayi murmushi tace to malam na dena cewa hmmnn en tunda baka so”

“Yace yawwa my dear 😘 yace me zan samu neh yana mai Shafa cikinsa

“Tace name fah?”

“Yace naci mana yunwa nakeji na gaji jiya duk ban huta ba wallahi

“Tace to ae dole ka gaji ka tashi daga office en nan haka kaje gida kaci abincin Momy kaji uncle A nima na dana tasu Nabil.

“Yace toh Aunty S yace toh byee luv you”

“Tace ok 👌byeeee ”

Yace ki amsa min mana

Ta rufe fuskarta tace luv you too❤

“Assadeeq ya miqe ya tattare files en gaban shi ya kullo office en ya fito yana qwalawa sectary en shi kira yace mishi ni na tashi duk wanda yazo kace na tashi ya shiga office en Abdullahi yace Achida man👨 ya meye labari neh yace normal mutumina wai kana nufin har ka tashi.

“Yace wallahi yunwa nakeji kuma kasan inba girkin sweet mother naci bah bana ganewa ya fada yana ficewa”

“Achida ya daga murya yace kuma nan da few days zaka fara cin na gimbiya safiyya bah”

“Assadeeq yace Dan iska kawae ya wuce parking space ya bude motar shi Fara qirar Ferrari”

“kae tsaye gida ya wuce bai samu kowa a palour bah ya kwalawa Saa kira ta amsa yace hada min abinci yunwa nake ji”
Bayan ta kawo mishi abincin yace ena Momy tace Sun fita dasu jalila,faruq neh ya shigo palourn yace ah bros ka shigo kenan yace wallahi cikina neh ya kira ciroma nadawo kawai zama yayi kusa dashi ya dauki cokalin yafara cin abincin gaban shi suna dan ta6a hira can bros ya nisa yace bros me Kake ganin zamu shirya neh na bikin nan saboda ena so muyi gagarumin bikin da baa ta6a yi bah

“Assadeeq ya numfasa yace faruq ae duk wani shiri yana wurinku nidai dan tayi neh”

“Sallamar su Momy ce ta katse musu hirar suka amsa suna mata sannu da shigowa Emmatan neh suka qaraso hannunsu riqe da ledoji manya gaba dayan su suka xube a kan kujeru suna wash-wash Sadeeq ya dubesu yace ragwaye kawae kamar kun dakko dala Afifah ce tayi magana cike da shagwa6a tace wallahi yaya mun gaji yace toh sannunku emmatan momy suka amsa da yawwa faruq neh yaja wani dogon tsaki yace rufe mana baki malama kona makeki suka yi masa shiru saboda sanin halinsa.

“Momy ce ta kira Saa tazo tace ki kwashe kayan nan ki kaisu sama tace Momy sannun da shigowa ya hanya tace lafiya lau ta kwashi kayan tayi sama

“Assadeeq yace Momy nah kin gaji naji kinyi shiru”

“Tace wallahi kuwa toh ya zamuyi abu yana ta matsowa ai banga ta zama tunda Ina shirin aurar dakai”

“Murmushi yayi kawai ya sunkuyar da Kai”

“Momy ce ta numfasa tace amma fa duk da haka karka manta da sharadi nah”

“Gabansa neh ya yanke ya fadi cikin zuciyarsa yace dama momy bata bar wannan maganar bah wanna fah shine ga _ga qoshi ga kwanan yunwa_😬❗.

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

*💦T<W>F*💦
[6:14Am,2017.]

 

*💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

💦*T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**

👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_> Gaisuwa ta mussamman ga yaruwata,Aunt umma aymana_
_da irin shawarwarin dakikebani Allah yabar zumunci_

*Ameen*👏🏻

 

 

*14*

 

~~~~ Biki yarage saura sati daya,shirye shirye sunyi nisa,safiyya ce zaune kusa da umminsu,tanai mata nasiha da shawarwari yadda zata zauna da mijinta lpy da *kannan mijinta*kuka tasawa ummin tata,musamman data tuna da *kannan mijinnata*
ummi taimata nasiha mai ratsa zuciya,

“Safiyya kiyi hakuri rayuwar aure kinji shi aure da kike gani bakomai cikinsa face hakuri,haka dai taitaiwa,diyarta ta.

Abangaren angwaye kuwa,shirye shirye yai nisa,sun tsara zasu gudanar da kamu,da dinner,sai walimar daurin aure,ita dai safiyya bata da tacewa duk yadda assadiq yafadamata,binsa take da to,domin jikinta yagama yin sanyi,

Abangaran su safiyya kuwa,yayanta yayi rawar gani dan yayi mata,kayan daki na alfarma,baffa ma yaimata nasa,gaskiya iyayan safiyya sunyi mata kaya nafitar kunya,yau ne akafara rabon iv card,amma yaya rukayya tahana safiyya zuwa,saboda takaita gurin hajiya aunt gyaran jiki,

A gidan su assadiq ma shiri ake banawasaba,dady yadada gyara gidan,yacanjawa momy kayan daki,dai dai da maaikatan gidan sunsan zaai bikin dangata,domin dady sai da yaimusu kayan biki suma,

Assadiq ne yaje gidan yayarsa hannatu dancigaba da shirye shirye,wasu kaya ta dakko masu tsananin kyau. Da tsada,

“Ango ga wadannan kayan ka kaiwa Safiyya tasa ranar dinner,kaima kasaka kadar su”

“Angama yayata da girmar kujerar ki”

Dariya yabata,” yaushe zasuzo,kafi?”

“Tace jibi ne”

“To badamuwa zanyi kokari inzo da wuri,dan ataresu”

“To yaya”

Sallama yayi mata yatafi gidansu safiyya,tunda ya hagota,yaji wani irin so da kaunarta acikin zuciyarsa,

Sallama tai masa,be iya amsawa ba,yaja hannuta,suka koma cikin mota,

“Baby kinganki kuwa,kinajin kamshin da yake tashi a jikinki kuwa”
Shiru tai masa saboda ta tsorata da yanayin assadiq yau,tafiskanci fitina yakeji,

“AB,pls kabari banaso”
Kwaikwayarta yayi da salon muryarta,

“Ni inaso,baby,kibarni inshaki kamshin tattausar jikinki”

Rugumota yayi jikinsa atake yasauke wata nannayar ajiyar zuciya,ita kuwa safiyya jikintane ya hau rawa,ahankali tazame jikinta,

“Baby guduna kike ko?”,badamuwa,ai saura kiris,tafin hannunta tasa ta rufe fuakarta,

“Ka kayan dinner inji yaya”

“Nagode uncle A,ayimin godiya”

“Sannu,nizanmiki godiyar ma,bari inkirata dai kiyi mata da bakinki”

“Aa bazaniya ba”

“Aikuwa sai kinyi”

“Dan Allah kabari,wallahi kunya nakeji”

“Shikenan zanbari amma sai kinmin alkawarin abu daya”

“Nayarda”

“Tunkafin kiji abun har kinyarda,lalle matar assadiq bata da wayo”

Kanta ankara yamanne bakinsa anata yanata tsotsa kamar alawa,

Kuka tasamasa,dakyar yacikata,idonsa yakada yayi ja,murfin motar takama zata fita,yai saurin riko hannunta ya kafeta idanusa,yashafa lifiyayar sumar kansa

“Sweet baby kiyi hakuri bazan kumaba”kunnuwansa yakama,

Murmushi tayi,batace komaiba,

“Oya share hawayenki amarya bata kuka,ko kinaso ummi taga kinyi kuka?”
Kai ta girgiza masa,ta sharen fuskarta,taimasa sallama tashiga gida,yadade betafiba,yana maida numdashi, daga baya yaja motars yatafi.

 

Tundaga wannan rana,Safiyya taki yarda suhadu da assadiq,faruq ya turo yakaisu kunshi da salon,

“Auntina barka da fitowa,ya shirye shirye”?

“Yauwa sannu faruq,angode ma Allah ya momy?”

“Tana gaida surukarta”
Murmushi tayi yajasu sukatafi,tunda sukatafi yake tsokanar najiba,

 

Gidan su safiyya yafara cika da yanbiki,mussamman yanuwan baffa,da suke a katsina,

Su yaya rukayya ne sukatafi kafi ita da yanuwan umminsu,sunyaba da gidan safiyya sosai,katon gida mai dauke da part 2,suna cikinn jeran ne su afifa,suka shigo suna yatsine fuska,kanwar ummi ce kallesu,

“Kukumafa?

“yayan albarka”

Farhanace tabata amsa

*kannan mijinta*

Tirkashi,muje zuwa..
.
*[9:54 AM,2017.]*

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM💦💦💦*

 

*💦T<W>F💦*

 

**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Ina miqa godiya gami da jinjina👍🏻 gareki qanwata abar alfahari nah UMAIMAH_💋❤😍

*15*

 

~~~Gaba dayansu suka yi saroro, Ruqayya ce ta dubesu tace toh sannunku

“A ciki suka amsa da yawwa suka ja guri suka zauna suna kallon yadda suke gudanar da jeren nasu,Afifah ta dubi hajir cousin en su da suka xo dg kaduna er qanwa daddy ,tace tace don Allah Hajir dubi gida har gida amma ba wasu kayan azo a gani”

“Farhana ce tayi caraf tace nima dae abinda na gani kenan duk yadda ya Assadeeq ya gama kashe kudinsa akan gidan nan amma bah Furnitures en kirki ta qarasa zancen ta yatsina fuska”

“Ruqayya ce ta yunquro ta miqe da kyar da niyyar yi musu magana da hanzari Aunty Asma’u ta dakatar da eta suka cigaba da aikin gaban su kowa cikinsu na mamakin hali irin na *kannan mijin*safiyya kowa da abinda yake saqawa a ransa

“sallamar wata mace doguwa fara tas neh ya katse musu zancen zucin da kowanne yake yi a ransa fuskarta dauke da murmushi da kaganta kasan yayar emmatan dake zaune ce saboda kamar dasuka yi bayan ta kuma yan aiki neh hannu su riqe kuloli da Tray wanda aka nade shi da foil paper sannan kuma ga yara maza su kuma sun dakko kwalin ruwa da lemo tayi magana cikin bada izini ,tace ku ajiye anan suka ajiye suka fice,ta fadada murmushinta tana mai qarasowa cikin parlour,tace sannunku da aiki suka amsa da yawwa nan suka gaggaisa ta gabatar musu da kanta A matsayin yayar Angon”

“Ruqayya ma ta gabatar mata da kanta da kuma Aunty Asma,u,da Aunty zahriyya a matsayin qannen ummin su sae kuma Gwaggo saude qanwar baffan su da kuma yakumbo bilki matsayin matar wan baffan su Wanda suke kira da (baffa babba)”

“Ya Hannatu ce ta dago ta dubi su farhana tace ku dama kuna nan neh?”

“Suka amsa da Eh, nan suka shiga gaishe ta, hajir tace ya Hannah ena su nabil”

“Tace suna gidan Momy hajir, tace ae jiya da mukayi waya da Momy Take cemin kun iso

“Hajir tace eh wlh amma nida ya beelal muka zo mamy sai xuwa yau xata qaraso”

“Tace toh Allah ya kawota lafiya”

“Gaba daya palourn suka Amsa da Ameen”

“Nan su Aunty zahriyya suka zuba abinci suka ci sukayi sallah suka cigaba da aikinsu

“Nan ya hannatu tayi musu sallama ta dubi emmatan,tace ku taso malam sule yana jiran mu nace masa zai kaimu kunshi kar lokaci ya qure sukayi sallama suka fice Suka shiga gida hannatu tace Momy kinga dakin amarya kuwa mashallah sunyi qoqari”

“Momy ba tace komai sai baki data ta6e”

 

******
Farfajiyar gidan Ruqayya neh cike da emmata da Manya dangin amarya dana ango gefe km DJ breka ya Saki waqar (shimfidar fuska) bayan dangin ango sun Kama amarya, qawayenta neh suka cigaba da cashewa can sai na hango 💦Talented writters sun shigo filin rawar da kumaYan Naseeba Gawo fans ✍🏻suna cewa muma bazaa barmu a baya bah💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

 

“Washegari ta kama ranar dinner tun misalin karfe hudu su safiyya suka tafi wurin Make up dake ribado Road Achida neh ya saukesu ya leqa shagon yace Aunty faty ga amaryan mu nan ki mata Make Up en da zamu kasa ganeta

“make up artist din ce ta dago tace baka da damuwa sir da yake qanwa ce wurin wani abokin su,nan su safiyya Suka gaisa da aunty Faty, tafara aikinta wajen qalqale fuskar safiyya da cancada Mata ado na ban mamaki nan da nan sai gashi ta Chanja dama abinka da mai kyau wayarta dake hannun qawarta wato Sadeeya Smart ce ta fara qara ta taso ta miqawa safiyya, tana dubawa taga ba kowa ke kiran illa angon nata a ranta tace to meye kuma dan rigima ta kara wayar a kunnenta tana mai yimasa sallama,ya amsa yace an kusa gamawa, tace eh, yace ena fatan baki manta da kayan dana kawo miki na wurin ya hannatu ba koh?,Tace ban manta bah,yace toh sai mun qaraso”

“Cikin qanqani lokaci aka gama komi sae ga amarya cikin wani tsadadden laces Light purple da adon silver wanda yasha dinki riga da skirt irin na amare rigar ta Kama mata jiki haka ma skirts din sae kuma dark purple Ashoke da mayafinsa wuyanta da kunnenta kuma dauke suke da silver sarqa da Yari ga kuma warwaro da zobuna tamkar diamond ta fito kamar ba safiyyan ummi bah nan sadiya Smart ta dinga zuzuta kyan da qawarta tayi nan ta fara daukan ta hoto a wayarta tana cewa Wow qawata”

“Ringing din wayar safiyya neh ya Katse su ta daga tace toh gamu nan fitowa, sukayi sallama da aunty faty dama can angwaye Sun riga Sun biyata kudinta fitowa sukai tun daga nesa Assadeeq ya kafeta da mayatattun idanuwansa masu bata kunya da tsoro wani zubin, mashallah yace a ransa ya qaraso yana mai bude mata gidan baya sanye yake cikin wata dakakkiyar getzner eta ba fara ba eta ba silver amma tafi kama da silver kansa sanye da silver hula zanna bukar tsintsiyar hannunsa kuma daure take da silver agogo qirar Rolex watch sae kuma danqwaleliyar azurfar sa data qara wani qyalli na musamman suka hada Ido lokacin da take zama ya bita da wani sihirtaccen kallo ta sunkuyar da Kai ya shigo ya kullo musu qofar Sadeeya ce ta shiga gaba Abdullahi yaja motar suma sunyi kamar saurayi da budurwa, Angon neh ya dago ya dubeta yana qasa da muryarsa yace kinyi kyau baby, tayi murmushi tace kaima haka,yace bari in dan matso kona fin jin qamshin nan da kike zubawa ya fada yana qoqarin qaqubowa jikinta tayi qasa da muryarta tare da marairaicewa tace don Allah ka bari bana so yayi dariya ya matsa yace zama ki so neh yarinya cikin abinda baifi mintina bah suka karosa katafaren wurin bikin wato (murna event center )da ya cika ya tumbatsa da Manyan motoci sai kuma kida da yake tashi sama-sama wayarsa ya zaro a aljihu ya kira hannatu yace sun qaraso tace to gata nan zuwa ta qarasa wurin MC ta sanar masa da zuwan amarya da ango nan ta tattaro su jalila, Afifah, farhana, hajir, muwadda sai kuma najiba da suka jero da faruq sai kuma sadeeya Smart da Abdullahi da ragowar abokan ango ya hannatu ta qarasa wurin ango da amarya tace gaskiya neh perfect match kunyi kyau sosai nan suka jera emmata da samarin suka fara taku dai-dai suna qarasawa cikin Hall en nan da nan camera ta fara aiki ji kake kyas kyararas DJ ya sakar musu waqar Amarya da ango suka qarasa wurin zamansu nan aka bude taro da addua Achida ya fito ya bada tarihin ango sadiya ma ta fito ta bada na amarya nan aka cigaba da gudanar da dinner inda samari da emmata suke ta shagalin su a haka amarya da ango suka tashi suka zazzaga suka gaida iyaye daga nan aka fara ciye-ciye bayan an kamalla aka buqaci amarya da ango su fito nan momy da qawayenta suka fito sukai musu liqi haka ma aka buqaci dangin amarya nan fa su ya Ruqayya,najiba,zainab da ya almustafa da sauran family dinsu suka fito suma sukayi liqi aka umarci kowa ya koma ya zauna zaa yanka cake nan MC ya shiga kiran najiba da faruq da suzo su taya yayyensu yanka cake suka fito suka yanka cake din ya ciyar da eta, itama tasa masa a baki ta mai dan sunkuyawa gwanin ban Shaawa nan aka shiga daukan hotuna duk wannan shagalin da ake muwadda na gefe tana baqin cikin wannan aure sai Bin safiyya take da harare2 ”

“Nan taro ya tashi kowa ya watse amarya da ango neh tafe cikin mota yana ta tsokarnarta tayi masa shiru yace ya dai? Tace bakomi kawai dai na gaji neh yace da kuma yunwa bah nan suka biya tawani wurin suya yace acida ya siyo musu gasassun kaji da drinks, Abdullahi yace baka wuri kawae malam Assadeeq yayi murmushi ya janyo sofy jikinsa yana mata rada a kunne naga ta rufe fuskarta tana janye jikinta,yace au rowa zaki min tamasa shiru, yace bakomi gobe kya bani ryt? Shigowar su achida ce ta katsesu nan suka wuce saukesu.
[11:6PM,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

💦 *T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Wannan shafin nakine kyauta na gode da kulawarki gareni_
*Khausar*_ma rubuciyar gida biyu_🔥

 

 

*16*

 

Washegari akatashi da hidumar daurin aure,tunkafin adaura safiyya take gursheken kuka,anyi rarrashin har angaji ankyaleta,bakimai kesata kuka ba face *kannan mijina*inta tuno da irin kallon da sukemata,musamman kallon da muwadda take mata,tana ta tambayar kanta ko wacece ita,bata da wannan amsar,

 

 

Assadiq kuwa tun asuba yatashi yakasa komawa bacci saboda zumudi,dak in faruq yashiga ya tarar yanata baccin da alama ya gaji,tashinsa yafarayi

“faruq faruq,tashi mana”

“Yaya pls leave me a lone”

“Faruq tashi mana munkusa makara fa”

Da sauri yatashi yana salati,faruq kenan ingarmar namiji mai jini ajika,

“Yaya an daura ko?”

Dariya yayi,” tayaya zaa daura auran assadiq faruq bejeba”

“Wlh yaya nagaji dayawa,gaskiya bross kayi saar mata,wlh kaiya zabi,abu daya ke damuna,auranka da yarinyar nan muwadda,banaso,
Kama kuwa fadawa anty safiyyan?”

“Haba faruq tayaya zan iya fadamata maganar nan,abinda nakeso da kai shine katayani da addua kaji”

“Inshaallahu”

Dady ne yaturo kofar dakin ahankali,gaba dayansu suka maida dubansu gareshi,assadiq ne yai saurin karasawa gabansa,

“Dady barka da asuba”

“Yauwa sadauki,ya gjyr biki,to Allah yabada alhr,yabaku zaman lpy”

Shiru yayi be iya amsawaba,faruq ne ya amsa da ameen dadyn mu”

Mai da dubansa yayi gareshi,yace faruqu,mekake baka fita kaga yadda su sale suka gyaran gurincan ba,kana nan kana baccin naka na tsiya ko?”

Tasowa yayi daga inda yake,yamikawa uban hannun,

“Dady barka da asuba,wlh nagajine shiyasa,amma bari inje,ingani

“Aa barshi kawai kude kuyi kushirya,lokaci yakaratu”

“To dady”

Shiri sukafara yi tun fitar assadiq daga dakinsa,achida yakemasa waya,ebet kuwa gidan yazo dantaya ango shiri,angofa yafito cikin farar shadda getzner wacce tasha adon golden din aiki babbar riga,yasanya hularsa zanna bukar kalar aikin,da agogansa mai tsananin tsada,Ebet ne yadakko turare yafesa masa,suna haka sai ga achida ya shigo cikin tasa shigar dasukayi da abokansu ebet ma shaddar ce ajikinsa,nan dai suka gama shirinsu sukafito,fitowarsu tayi dai dai da sakkowar dady da faruq cikin irin shigar assadiq,wucewa dadyn yayi,bayan sungaisa da su Ebet,dakin momy yashiga yagaida ta da yanuwanta da suka cika dakin,guda suka sa,sunaitai masa fatan alhr,nabil da ashraf ne suka shigo dakin suma,

“Uncle A kaga muma munsa irin kayanku,dadyn kune yaimana”

“Wow yarana sunyi kyau,oya kushige mutafi”

“Uncle A dagaske daurin auranka zamuje?”

“Eh ashiraff”

Kama hannun yaran yayi suka fita,basu hadu da yaya hannatu ba,sunacan suna aiki,suna fita sukaga harabar gidan nasu dinke da Jamaa,kowa kuma sai hankalinsa yayo kan ango musamman duba da irin shigar da iyalan sukayi abin gwanin. Burgewa ,nan aka dunguma akatafi gurin daurin aure,

 

°°°°°°°°°°°°°°°

Kofar gidan wan baffan su safiyya ne dinke da jamaa,yan daurin aure,baffa yasha shadda blue yayi kyau,Dr almustapha nahango cikin tasa shigar da taron likitoci abokansa,

Misalin karfe 10:30Am
Aka shaida daurin auran assadiq da safiyya,akan sadaki 100k,kamar yadda waliyainsa yabayar yayan dady wato Alhj munir mai nasara,daurin auran da yahada,manyan masu kudi,da manyan yan siyasa,antashi saga gurin daurin aure, dady da jamaarsa sunwuce gurin reception din da yahada da abokansa,su assadiq kuwa gidan su safiyya suka koma dan gaida iyayanta,dakuma gabatar da hotuna,

Suna shiga gida yakacame,nan kakannin safiyya sukaita tskanarsa,shi Kuwa,hankalinsa yana kan gimbiyar tasa,yana kallon tainda zata bullo,najeeba ya kira datasha hadadiyar farar shadda,da pink din aiki,yace taje tafito da Safiyya,daki tashiga tatar da yaya rukayya tasata gaba tana aikin rarrashi,itama cikin tata farar shadda mai dauke da blue din surfani,dakyar Safiyya tataso zainab tadada gyaramata fuska,taja hannunta sukafito itama tata shaddar fara da bakin surfani,tunda assadiq yaga Safiyya yadada rikicewa dan tayi kyau sosai,tasa tata shaddar fara da jan surfani mayafinta ja takalmi jaka,sarka da agogo ma ja,nan aka fara hotuna,ansha kyau ,bayan angamane yajata mota,kallonta yake da fitinannun idanunsa,kana yajata jikinsa,yadora da,

“Sweet baby kinyi kyau,kina nema kitarwatsa kirjin Assad,matso kiji begun da zuciyata keyi,inasonki safiyya,inason kiyi hakuri da yadda zakisameni,ina jerin maza masu tsananin shaawa,kuka tasamasa,yadada,

Janta jikinsa yana sharemata hawayen fuskarta sai dayayi wasa daita sosai,Ebet ne ya kwankwasa masa,kofa,

“Chairman lokaci fa yanatafiya”

Sakinta yayi ahankali yace ,

“Matar assadiq kishirya tarbar mijinki hannu tasa tarufe fuskarta wanda yasha janlalle da baki,dakansa yafito,yabudemata kofa,tafito,akunnanta yaradamata

“I love u baby”💖

Sukajaa motarsu suka wuce gurin walimar da abokan aikinsa suka hadamasa,biki ya kayatar kamar yadda akatsara.

Karfe 5 dai dai su yaya hannatu da kanwar momy sai yayar dady suka zo daukar amarya,lokacin kanwar
Momy tanashiryata,wata koriyar atamfa tasaka dinkin riga da zani ansamata sarkar gold wanda ummi tasai mata na aure anyafamata mayafi kalar atamfar abinka da mai kyau ga amarci dazaashiga,

Dakin baffa ummi takaita,tanata gursheken kuka,

“Safiyya yaisa haka kukan,kinji domain wannan ranar itace burin kowane iyaye ,nidai baabinda zance miki sai shine kiyi hakuri kibi mijinki sau da kafa,kibi mahaifiyarsa dan yanzu uwace agareki,mijnki yana da kanne kizauna da *kannan mijinki*lpy kanji Allah yayi miki albarka yasa kishiga a saa kinji”

Ummi ce taamsa da, ameen”
Kikula da tsafta safiyya kizama mai rufe sirrinki,kisani *mijinki sirrinki*ne,
_littafin kanwata ummy aisha_

Allah yayi miki albarka”

Kamata ummi tayi suka fito,
Ya hannatu ce takamata takaita mota,nata kuka mai ban tausayi,

 

 

 

*NASEEBA I UBA*✍🏻

07037732029💐
[11:44Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

💦 *T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Gidiya ta musamman gareku kawayena kiyaya 2009_🎓🎓

_Suwaiba saleh bala Maisalla_
_Rukayya Ashir_
_Aliya sani shehu Maihula_
_Rabiatu Ismail_
_Rabiatu Ismail_
_sadiya bala_
_Shafaatu abdulhamid_
_Nafeesa nasir_
_Hauwa munir_
_Atika Tijjani_

*Allah yabar Kauna*

 

 

 

*17*

 

~~~~Tunda suka tafi take kuka,harsuka karaso kai tsaye,gidan su assadiq aka wuce,daita agaban momy aka ajiyeta nan taimata nasiha mai ratsa jiki kamar ba komai aranta, su afifa ne sukai magana,

“Amarya bude fuskarki kiga *kannan mijinki*

Yaya hannatu ce tadaka musu tsawa sukai shiru,ragowar yan bikinne palon momy ne sukatashi danraka amarya,momy tabata dubu ashirin da kwalayan cigam da turare,nan aka dauketa aka kaita gidanta gida mai kyaun gaske, kowa nayaba kyawun gidan safiyya,bedroom aka shigar daita dakin sai kamshin turaran wuta yake wanda aka jona a bona,

Yankai amarya sunwatse sai yanuwan safiyya ne suka rage,

Suhyla ce tadafa cinyar safiyya tace,

Aunt cafiyya wayasa ki kuka?”inrama miki,

“Rukayya ce tabata amsa’

“Bulalar aure ce tadaketa suhyla”

“Ummata ina auren yake inrama mata”

“Bansaniba”
Suzainab kuwa dariya tabasu,janhannun yar tata tayi taimusu sallama mai gidanta yazo yadauketa tagaji da yawa ga ciki,

Yanmatan ne suka dada gyara dakin,suna cikin gyaran angwayan sukai sallama,dasauri safeena tataresu abakin kofa,sai sunbasu kudin siyan baki,
Wani abokin assadiq ne mai suna B malik yazaro kudi dubu ashirin yabasu,kinkarba tayi ,sai Ankara musu,assadiq ne yakara musu goma akai,sannan sukabasu hanya,shiga sukayi dakin sukai adduaa dan yan nasihohi suka mike dan tafiya yanmatanma tashi sukai dan binsu sukaisu gida,safiyya ce takamo hannun zainab tana kuka,itama kukan take tajanye hannunta tafita,
Abokinsa Ebet ne yajashi gafe yafara masa magana,

“Chairman kabi yarinyar nan ahankali kar kaimata illa”

Duka yakaimasa yace,

“Daniska,anfadama kowa irinka ne maifasa madara takarfin tuwo”

Dariya sukayi yarakasu yakullo kofofin,dakin yakoma yatura kofar ahankali,
Tanan zaune inda yabarta ta cure guri guda,kangadon yakarasa ya kira sunanta,ahankali

“Sopy dago fuskarki ki kalli mijiki,mayafin ya yayemata,ahankali tadago da kanta,takalleahi,sanye yake cikin green din boyel yayi mata kyau,

Kajin dasuka zo dashi da yagwat
“Taso kirakani kitchen mudakko plate ko”

Girgiza kai tayi alamar aa murmushi yayi yatashi yaje ya dakko yadawo yabude yazuba a plate yayanka da wuka,yadago yakalleta
“Oya,sakko kici”

“Nakoshi”

“Cab Ashe xanyiwa yarinya dura,sakko kici,nasan cikin nan beci komaiba,yana shafa cikinta,

Bashiri tasakko ta zauna a gefansa,yafara bata a baki,nan sukaci suka gama,ya kwashe kayan yakai kitchen kishiga toilet kiyi alwala inazuwa,bandakin tashiga,toilet din yahadu komai naciki blue tayo alwala tafito,

Shigowa yayi shima yashiga toilet din yayo alwala yafito sallaya yashinfida sukatayar da salla.

 

 

 

*NASEEBA I UBA*💐
[9:06Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA* 💐

 

_Inabawa makaranta littafin kannan mijina_ _hakuri sakomakon akasi daaka samu a page 17_

 

 

 

*18*

 

~~~ Salla yajasu bayan sun idar ne yadafa kanta yayi adduar da maaiki yakoyar damu,mikewa yayi yadubeta yace,

“Sopy inazuwa kicanja kayanki kisa nabacci”

Bata amsaba,yasa kai yafita,dakinsa yakoma wanka yashiga,bayan yafito,yasa kayan bacci masu kyau farare,turare yafesa masu tsada,yaja kofarsa yafito,dakinta yakoma,tana nan inda yabarta,murmushi yayi yawuce gurin akwatinta yadakko wata yaloluwar riga mai fulawowi ja,yakaraso gurinta yamikar daita,kokarin kwance zanin jikinta yake tarike hannunsa,dagowa yayi yakalleta hade da girgiza mata kai,sakin hannunsa tayi,yakwance zanin sannu ahankali,yasauya mata rigar baccin,tunda assadiq yaga gashin safiyya yadada kidimewa,hannunta ya ja yakaita kangado ya kwantar daita,yaje yakashe kwan fitila ya kunna AC,sai bed lamp
Kawai yabari ,yadawo yakwanta bejitaba,matsawa yakuma yi,yaganta ta dukunkune,can kasan makoshi, yakira sunanta,

“Sopy,nasan ba bacci kikeba,kibude idonki kitarbi mijinki,ahankali yafara aikamata da sakonni kuka tafara

“Assadiq dan Allah kabarni,wlh bazaniyaba”

“Zakiiya sopy ahankali zanbidake kinutsu kanji”

 

Nikam tundaga nan naja yanmatan kafafuna narufo musu kofar a hankali nakoma palo nai likimo 🤣

 

Kuka safiyya take tafaman yi assadiq yarikice yanata rarrashi take wani mugun zazzabi yarufeta jikinsa yajawota yanatafaman rarrashi ahaka har yasamu bacci ya dauketa,shikuwa yakasa rintsawa gani yake kamar zaazo adauke masa matarsa

 

Asuba nayi yazareta ahankali daga jikinsa yagyara mata kwanciya tare da lullibeta yasakar mata kiss agoshi,toilet yafada yayi wanka tare da doro alwala yafito yazo yazura sabuwar jallabiyarsa yatayar da salla,

Ahankali sopy tabude ido wani radadi taji yaziyarci ajikinta,wata kara tasaki,dahanzari assadiq yataso yazo gunta,

“Sopy menene?”

“Kaine,wayyo zanmutu”

Rarrashinta yashiga yi dakyar yasamu tayi shiru,bandaki yashiga yahadamata ruwan zafi yafito yazo yadagata ahankali yarakata toilet yajawo mata kofar,tagama abinda take tafito,tasaka doguwar riga tatayar da sallah bayan ta idarne,tajuyo tagaida shi,

“Ina kwana”

“Lpy lau matar assadiq jiya nayi laifi ko anmanta suna na,tuba nake,bazankumaba”

Murmushi tayi kawai

Fita yayi daga dakin itakuma tasami dama tashirya cikin wata purple din atamfa super riga da sikert dinkin yaimata kyau,shigowa yayi shima cikin tasa shigar brown din shadda yanaganinta yakaraso

“Wow matar assadiq kinyi kyau”

Turare yadakko yafesa mata,takalleshi tace

“Nagode”

“Karki kumayimin godiya”

Palo suka koma yakunna musu kallo,

Bugun kofa yaji yatashi yatambaya

“Waye”

“Su farhana ne”

Budemusu yayi suka shigo,hannunsu dauke da kuloli masu kyau,

“Yaya antashi lpy ”

“Lpy lau yanmatan momy,ya gida”

Kan yaji amsarsu yamike yashiga daki dakko waya,

Safiyya ce tadubesu tace,

“Sannunku”

Kezaiwa sannu ai amaya”,cewar afifa,

Murmushi tayi tadora da,

Ya momy”

,”tana lpy,ammafa kinyi kyau,zanzo kibani aran dinkin nan,amatsayina na *kannan mijinki*tanagama fada tace sutaso su tafi bazama zasuyiba,

Safiyya ce taishiru tana jinjina halin *kannan mijinta*

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

,07037732029💐
[6:35Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM 💦💦💦*

💦 *T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*19*

~~~Assadiq ne yafito daga daki yatarar har kannan sa suntafi,tambayar safiyya yayi,

“Sopy inasu farhana?”

“Suntafi”

“OK,tashi kidakko mana plates da cups muyi break ko”

Ahankali ta you nkura zata tashi taji bazata iyaba,narai narai tai da ido,tadubeshi tace,

“Dee dan Allah taimakamin intashi”

Ido yazuba mata kana yace,

“Wow nice name my sopy,naji dadin Sunan nan,zauna inje indakko kinji my sweet sopy”

Hannu tasa tarufe fuskar ta,Wanda yaaha zanan bakin lalle da ja,
Yadakko plate din yazo yazuba musu doya da kwai,da roman kayan ciki,da na kifi,sai tea,dakansa yadinga bata abaki bayan sungama ne,yakwashe kayan yadakko paracetamol yabata tasha,bata jima dasha ba bacci yadauketa,

Dada gyaramata kwanciya yayi,yalallaba yaja mata kofar palon yafita zuwa gaida iyayansa,

 

°°°°°°°°°°°°°°°°
Faruq yatarar a palon,dasauri yataso ya rungume,yayannasa,suka gaisa,yafara tsokanarsa,

Wlh yayana kayi kyau,lallai aure akwai niima cikinsa,jira nake azahar tayi inshigo ingaida auntynmmu,dankar inyimuku sammako”

“Kai faruq wannan zantuka duk kai kadai a lokaci daya”

Dariya yayi,nan suka zauna,yana
tambayarsa momy,

“Momy fa”

“Tana saman dady”

“Bross ya aunty Safiyya?”

“Lpy lau”

Afifa ce tafito daga kitchen dauke da plates din indomie ahannunta,takawo wa faruq,Assadiq ne yadubeta yace,

“Afifa shine kukatafi bansaniba ko”

“Wlh yaya sauri muke”

Faruq ne yadubeta yace,

“Ke tashi kije ki kiramin ragowar duk kuzo”

“To”

Zuwa tayi takirasu,lokacin duk suna gado,farhana na game jalila na sanaar tata karatu,
Fitowa sukayi sukasami guri suka zauna,

“Yaya assadiq barka da shigoqa,ya amarya?”

“Yauwa jalila,lpy lau,meyasa baki biyo su afifa ba?

“Yaya lokacin bantashiba,”

“OK”

Faruq ne yadago yakallesu,

“Afifa,farhana,jalila,
abinda nakeso daku shine,kuxauna lpy da amaryar yaya,babu rashin kunya baraini,wlh innaji labari kunmata abu mara dadi sai kunci ubanku,kunde ji ko,

“Munji”

Assadiq ne yadora da kuzauna lpy daita,banmmu iyaka da gidanaba,kuji yanmmatan momy,

“Inshaallahu yaya assadiq bazamu zama fitsararrun *kannan mij*marasa jiba,ai munzama daya”cewar farhana,

“Yauwa”

Tashi yayi yahau saman dadynnasu da sallama,akaamsa masa dady ne yafara magana,

“Wa nakeji Kamar sadauki”

“Nine dady”

“Dady barka da asuba”

“Yauwa sadauki antashi lpy,ya kwanan iyali?”

Akunyace “yace lpy kalau dady”

“Badai matsala ko?

Sumar kansa yashafa yace,”babu dady”

“To madalla”

Juyawa yayi yadubi momyntasu yace,

“Momyna ina kwana”

“Lpy lau assadiq ya Safiyyan?

“Lpy kalau,tana gaisheki,munga sako angode momy”

“Badamuwa kace kartafara girki saitayi sati daya”

“To zanfadamata

Dady ne yaitaimasa nashi,akan hakuri da mata,da kuma jajircewa,

Godiya yayimasa yai musu sallama yatashi

Faruq ne yabishi dan zuwa gaida safiyya sanda sukaje gidan tana daki tana bacci,

“Faruq zauna bari inkirata”

“Ok ,bross”

Dakin yashiga tanata baccinta gashin kanta yabazu akan pilo,ahankali yatattara gashin nata,yadaure da ribon,cikin kunnanta yafara mata magana,,

“Sweet sopy,kitashi ga kaninki faruq yazo kugaisa,”

Ahankali tafara bude idonta suka hada ido,take tasakar masa murmushi,

“Dee”

“Naam” my sweet Sopy

“Kadawo,ya momyna”

“Lpy lau tana gaisheki,dady ma haka,momy tace karki fara girki sai nan da sati daya”

“Ina amsawa angode,ina faruq?”

“Yana palo”

Dahanzari ta mike,tamanta da ciwon dajikinta yake,da sauri ta koma ta zauna,

“Wash”

“Yasalam sannu sopy assadiq be kyautaba,

Sunkuyar da kanta tayi,yakamata a hankali,sukafito,sunkusa karasowa gurin faruq ne tace yacikata ta tako dakanta,

“Karamin ango nayi fushi,sai yanzu,kazo ganina”

“Afuwan amaryar mu,ayi hakuri”

“Nahakura”

“Nagode,aunty”

Dariya yabata,nan suka gaisa,yadora da,

“Aunty dan Allah duk yarinyar datai miki,iskanci kifadamin”

“Haba,faruq mezasuyi min”

Sallamar su najibace takatsesu.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3:54Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALEENTED WRITTR’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJNA_**

👩‍👩‍👧

 

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*20*

 

~~~Najibace tataho dagudu tarungume safiyya,assadiq ne yayaimata magana cikin raha,

“Aa najiba zaki karyamin mata ne”

“La yaya assadiq bakaryata zanyiba”

Dariya sukayi gaba dayansu,faruq ne yatsokani najiba,

“Matar rabu dasu kinji,tayaya zaki karya masa mata”

“Nima dai haka nagani nakarfen”

Au faruq dinne nakarfan kinyi baki ko”cewar safiyya,nandai suka gama yininsu,dazasu tafi safiyya tatubure batasan zanceba tare zasutafi, dakyar assadiq ya lallabata,tahakura sukai musu sallama sukatafi,

Farhanace takawo musu abincin dare,lokacin assadiq yana wanka,safiyya ce takarba,takalleta tace

“Farhana ya gida ya momyna”

“Hmm gida lpy momyn mu de ko”

“Farhana momynku batawa bace?

“Gaskiya kam,tamuce wlh”

Dariya safiyya tayi,shikenan farhana badamuwa”

“Ina yayan”

“Yana wanna”

“Gobe zamuzo anan zamuyini”

“Kai amma naji dadi,Allah yakaimu”

“Ameen “tajuya tatafi,kitchen safiyya taje tadakko musu plates da cokula,tazo tajera musu kayan abincin kitchen din yatsaru komai green da orange,me

Assadiq ne yafito daga shi sai gajeran wando sai vest,yakaraso gunta,

“Sweet sopy wayakawo abinci”

“Farhanace,nace tatsaya kafito taki”

“OK”,zuba mana abincin,kuma abaki zaki bani”

“Dee dan Allah kaci da kanka”

“Cab ashe zaamaimaita abun jiya kenan”

“Dee,dan Allah kayi hakuri,naji zanbaka”

“Matsoraciya,to bani ”

Haka tadinga bashi abinci abaki shima yanabata,suka kammala,takwashe kwanikan takai kitchen, nan sukacigaba da kallo suna hira,jiknsa yajata,yana shafa gashin kanta,tunowa tayi da muwadda tace,

“Dee akwai wata sister ku wata fara doguwa,namanta sunanta” nafiskanci kamar bata sona, wacece ita”

Tanagama kwatanta masa ita gabansa yafadi,yace

“Oh muwadda ce yar kanwar momy ce,
amma karki damu kanki akanta kinji babyn assadiq”

“To,Dee”

Baccine yafara daukar safiyya,assadiq yatasheta suje su kwanta,nantafara masa kuka,

“Sweet sopy kuka fa?”
Meyafaru?

“Dee dan Allah karkai min abunjiya,wlh dazafi”

Dariya tabashi,yace

“Yaisa to,bakyaso”

Kai tadaga masa,”to bazaakuma ba,muje ki kwanta”

 

Washegari su afifa sukazo lokacin assadiq yana nan,

Safiyya taita murna suka gaida su,

“Yaya assadiq inayini”

“Lpy lau yanmatan momy”

Ya momy?”

“Tana lpy,tace bakazoba,lpy

“Lpy lau zanzo ne”

Safiyya ce taimusu magana,

“Jalila ya gida,bakizoba sai yau”

“Umm”nagaji ne ”

Lemo takawo musu da cincin,assadiq yajata daki,

“Sopy zanje gidan momy may be inbiya gurin achida”

“To,sai kadawo”

“Aa haka zaki barni,janyota yayi jikinsa yashiga tsotsar bakinta sai da yashanye janbakinta tas sannan yacikata,

“Dee kaga kashanye min janbaki”?

“Sorry, sweet sopy bari inkuma samiki,wani

Kuma shafamata yayi,ita kuma tadakko turare tafesa masa,

“Kuma,wallahi banda kallon mata”

“Cab aikuwa sai na kallesu tunda ke raguwace”

“Dee,karka kulasu zanzama,jaruma,

“Dagaske,kenan yau inshirya”

“Eh,ammafa. Karka kallesu”

“Angama ranki yadade”

Fitowa sukayi tarakashi,tadawo gurin su afifa,

“Kuyi hakuri kannena ”

*”kannan mijinki*de”

Inji farhana,dariya kawai tayi,haka sukaitazama,suna dan taba hira sama sama,tadafamusu abinci mai rai da lpy,sukai kaca kaca da palon,jalila,ce tace

“Farhana share gurin”

“Wlh yaya jalila,bazan shareba”

Ita da gidanta,basai tashereba,inji afifa”

Faruq ne yashigo,yatarar da inda sukaci abincin,

“Aunty na barka da yau”

“Yauwa small Ango”

Kallonsu afifa yayi,yadaka musu harara,

“Uban waye zai gyara gurin nan”

“Yaya nace,su share sunki”

“Malamai kutashi kugyar gurin,sunagamawa,sukafigi mayafansu zasutafi,kayan kwalliya tahado musu,sukaki karba,faruq yace kyalesu aunty kuwuce dalla.

 

_tirkashi_😳

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[11:41Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

 

_**KANNAN MIJINA_**

👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Dedicated 2 sajida novel world group_🐪

_Get well soon my friend_ * Maryam Sahabi*😘

 

 

 

 

*21*

 

~~~Haba faruq yazakai musu haka,gaskiya banji dadiba”

“Hmm, aunty safiyya bakisan iskancin yarannanba”

“To,meye basai inshareba”

“Bazaiyu ba kuwa”

Tashi yayi yafita,gida yabisu,

Suna zuwa gida dakin momy suka nufa,lokacin tana gyaran wardrobe,suka tura kofa,jiyowa tayi takallesu,

“Aa,jalila jarkunyi me?”

“Mundawo momy”

“Da wuri haka”

Afifa ce ta turo baki,tafara magana cikin shagwaba,

“Ba yaya faruq dinnan bane,wai yanazuwa ya hau mutane da masifa”

“Akan wane dalili”?

Farhana ce taja tsaki tadora da,

“Wai sai munmata shara danmunci abimci munbata gurin”

“To in banda halin faruq dan kunbata mata palo,sai akace sai kungyara”

“To ai nima haka nagani”inji jalila,

“Ku kyaleni dashi,zai zo yasameni ai”

Shigowarsa dakinne yasa sukai tsuru tsru,

hararar su yayi,yafara magana cikin fada

“Wallahi kushiga hankalinku inbanda iskanci ba jiya nagama yimuku fada kan banda rashin mutunci tsakaninku da ita girmamawaba,shine zakuje kufara iakanci ko?”

“Faruq meye hakane,zakazo kasamin yara agaba kanai musu fada,faruq intambayeka mana,

Kai ka haifa min yarannan ne?”

“Aa,momy”

“To baruwanka dasu,kajini ko”?

“Naji momy,gamma nibawai sansune banayiba,halinsune banaso”

“Nagama magana faruq baruwanka dasu”

“Shikenan momy”

Yatashi yabar dakin ,yana mai daura dammarar tsawatar kannan nasa.

 

^^^^^^^^^^^^^^
Tunbayan fitar faruq safiyya take mamakin halin *kannan mijinta*
Nasihar umminta ta tuno,takawar da damuwarta,wayarta ta dauka,takira ummintata,bugu biyu tadauka,

“Assalamu alaikum,ummina”

“Waalaikisalam Safiyya”

“Naam ummina yagida yasu yaya zainab da Baffa,

“Lpys kalau,safiyya”

“Ummi yaushe zanzo,inganki”

“Aa safiyya ba yanxuba,kinji yaushe aka kaiki ki kwantar da hankalinki kinji”

“To ummi,ina yaya almustapha?”

“Yana gurin aiki”

“Shima fa bezoba ummi”

“Hmm,safiyya kenan zaizo kinji”

“To,Ummi,sai anjima,agaida baffa”

Zaiji safiyya”

Sunagama wayar tatashi tadada gyara gidan takunna turaran wuta,tashiga kitchen tashirya girkinta mai rai da lpy,tanacikin wanke kwanikan data bata ne assadiq yashigo bataji shigowarsaba kawai sai jin mutum tayi yarufe mata fuska,nan ta kwalla kara,

“Wayyo,Allah na”

Ke matsoraciya,bude idonki kigani,ninefa”

Ahankali tabude idonta taga assadi ne,

Jikansa tafada tarukunkume shi tana maida numfashi,

“Dee,wlh kabani tsoro,pls karka kuma ba kyaufa”

“I am really sorry sweet sopy”

Nan yakwabe ya tayata karasa aikin datake sunayi yana tsokanarta,anan tabashi labarin yadda sukayi dasu afifa amma batafadamasa rashin kunyar dasukai mataba,

“Mugama aikin muje muyi wanka inraka ki kikaimusu daga nan kugaisa da dady”

“To, Dee”

Wanka suka shiga da kyar safiyya,ta yadda sukayi wanka tare,

Suka shirya cikin wata marron din shadda,tanade gashinta da Robin
Assadiq ne yakalleta yace,

“Wow sweet Sopy kinyi kyau karki sa dankwalin bari inmana pics,

“Dee dan Allah kabari mudawo”

“Naki,yauwa ina alkawarina”

“Hmm yanana Dee”

“Good,girl”

Nan suka gama shiriritar su suka kulle gidan sukatafi gidan momy.

_ko yaya safiyya zata karke da_*kannan mijinta*?

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[1:21PM,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Jinjina ta mussamman gareku kawayena ina mika sakon gaisuwata gareku_ 🎓🎓

 

_Rabiatu jibiril_
_Rukayya muhammad Haske_
_Hafsa Jamilu_
_Khadija Ali wada_
_Sadiya Sabiu_
_Aisha sale bala mai Salla_
_Sameera muhammad adakawa_

*Nagode da kulawarku*👌🏻

 

 

 

 

*24*

 

~~~~Bugun kofar daakeyine yasashi yin shiru,

“sweet sopy kamar bugu ake”

“Eh Dee,naji nima”

“Dagani inje inga waye”

“tsayani muje tare,amma gaskiya sai dai ka goyani”

“kai sopy kwana 2 kina wahalar da assadiq da goyo nauyi ne dake fa”

“Wlh Dee bani da nauyi dagani kaji”

kinga hau ingoyaki muje”

“yauwa,mijin sweet sopy”

goyata yayi suka karasa bakin gate din,

“waye?”

“yaya,assadiq farhana ce”

“sopy sakko”

“To,Dee”

kofar yabude tashigo,

“Farhana”

“Naam yaya assadiq,ina kwana”

“farhana kina lpy,ya su momy”?

“lpys kalau tace kazo takira. wayarka akashe”

“Dee kashe wayar kayi naga yanxu kagama waya”

“Bankasheba sopy may be matsalar network ne”

“Aunty Safiyya antashi lpy”

“lpy lau farhana,yasu afifa,da momy,kishigo mana”

“lpys lau,aa bazanshigoba sauri nake inada lectures 11:30,amma zamuzo anjima da kawayanmmu”

“To badamuwa sai kunzo”

tajiya tatafi,suka koma ciki,

“sopy zo muje daki kiji”

“Aa Dee,momy fa kiranka take”

“pls sopy kizo kiji mana,Allah kona fita sai nadawo”

“to daukeni”

“Da girman kujerarki,yasureta sai kan gado,nan yashiga lugwi gwitata,harshanta yakama yana tsotsa kamar yasami loli pop,
ahankali salon yacanja,kuka tasamasa,da kasalalliyar murya yafara magana,

“sweet sopy kiyi shiru a hankali zanmiki,tsoro yahanaki kifahimcin karatun”

“Nidai banaso,Dee”

sweet sopy assadiq yanaso”

sai da komai yalafa,sannan suka shiga toilet sukai wanka yanata tsokanarta,

“Dee,banaso”😄

tanarke fuskar zatai kuka, “tunda kake tsokanata,bazankuma kulakaba”

kunnansa yakama natutuba baby”

suka dauro towel suka fito,kaya kwabar kayansa ta bude tadakko masa wani boyel milk da hula tashiga shirya shi,zata balle masa maballi tsayinta bekaiba,nan yashiga yimata dariya kujerar mudubi yajanyo,ta taka taballe masa,tasa masa hula kalar kayan,sauka tayi tadakko turare mai tsadar gaske,tafesa masa,

“Dee kayi kyau”

“10q,👌sopy,haka zanfita, ba abinda zakibani”

“Dee pls kayi katafi kiran momy”

“Ni wallahi sai kinbani kiss”

“kai Dee,to rufe idonka”

“kema kirufe”

atare suka rufe idonsu tashiga manna masa,kiss,towel din jikinta ya kwance yashiga kissing dinta shima,

dakyar sukarabu kinrakashi tayi,dan kar yakuma bata lokaci,yanafita yadau sabuwar motarsa,yatafi.

 

^^^^^^^^^^^^
Farhana kuwa tana zuwa tafadawa momy,safiyya tahanashi fitowa,kuma ita takashe wayar assadiq din,faruq ne yadaka mata tsawa,

“farhana karya ko,dan ubanki a ina kika koyi sharri”

“faruq kar ka kuma zagar min yarinya kaji ko”

“haba momy yanzu kinyarda da maganar banzar yarinyar nan”

“To ai sai abinda kace ubana,farhana shige kiyi shirin makarantarki”

Dakin su tashige tanabawa su afifa labari,afifa ce tajinjina mata
“ga taki sis👍🏻

jalila kuwa baki kawai ta tabe,

Assadiq ne yai sallama yashigo,wani kallo,sai da gabansa yafadi.

Tirkashi!!!! *KANNAN MIJIN SOPY*

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA I UBA*✍🏻
[6:29PM,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Sakon gaisuwa gareki_
*Ummu aymana*_munemi aljanarmu mata_
_nagode da tunasarwarki garenibisa gajarta page da nake_ nagode _sosai inshaallahu zankara_👏🏻😍

 

*27*

 

~~Kintashi tayi,dakansa,yashiga toilet yahadamata,ruwan wanka,yafito,towel yamikamata,

“Ni kadai zanyi wankan, Dee”

“Sweet sopy,ya kikeso ayi”?

“Gaskiya nidai kazo muyi tare”

“Angama ranki yadade,yau nizanmiki komai”

wankan suka shiga sukayi,bayan sungama ya dakko matarsa yadireta kangado,yadakko lotion yashafa mata,yabude kwabar kayanta yadakko mata wata doguwar rigar material yadakko mai adon pink da stone akiki yashiga samata dinkin yaamshi jikinta,yadakko yari da sarka fashion kalar kayan yasawa matartasa,tayi kyau ainun,sai bayan angama sa kaya tadubeshi da shagwaba,

“Dee,bakatajemin kainaba”

“inasane sopy nafiso shine karshe,daga shi sai shafa hoda,da janbaki”

“cab banyardaba gaskiya,ni zanyi kwalliyata”

“To nayarda amma ni zangyara miki gashi ko?”

“Nayarda”

Nan yagyara mata gashinta gwaninn shaawa,tayi kwalliyarta,itama tazabomasa yadi mai tsadar gaske,kalar kayanta tamikamasa yasaka,sunyi kyau ainun suka feshi jikinsu da turare masu kamshin gaske sukafito,a harabar gidan suka tsaya sukai hotuna sannan yabudemata motar tashiga,yarufe,
_Assadiq kenan yanason matarsa_😘

gidansu sukafara zuwa tagaida momy,sanda suka shiga bakowa,a parlon,sai saa tanata goge,dasauri tataresu tatsuguna tagaishesu,

“Yaya assadiq inayini”

“saa,kina lpy,yaiki”

“lpy,lau,aunt safiyya inayini”

“lpy kalau saa”

“momy fa”?

“yanxu tashiga daki”

“jeki kikirata,yi sauri da Allah”

tafiya tayi takira momy tadawo tafadamusu gatanan,fitowa tayi farhana nabiye daita,abaya

“safiyya daga ina haka”

“momy daga gida muke,inayini”

“lpy lau,yanxu unguwarma sai kunje tare,daga auran zakutsiri yawo”

“momy tunda safiyya tazo sau biyu tafita,yanzunmma gidan yaya hannatu zankaita”

“Balaifi ai,sai ku hanzarta ai kutafi”

farhanace tai caraf ta sabaki

“yaya assadiq zanbiku”

“aa farhana bangyyace kiba”

“ai kuwa sai taje maza,kidakko mayafinki kutafi”
daki tashiga tadakko mayafinta tafito,assadiq baya saba umarnin momy,sukai mata sallama sukafita,abakin mota suka hadu da faruq,suka gaisa,

“auntyna kwana 2”

“faruq ai kaki zuwa,mun bata”

“natuba,aunty na”

farhana yakalla,”kekumafa,ina zuwa”?

“rakasu zanyi yaya faruq”

“ina Kenan?

“unguwa”

“to koma,bainda zaki wallahi,ko inci ubanki”

biyota yayi dagudu zai daketata takwasa aguje,assadiq ne yaimasa magana,

“faruq meye haka,yazaka koreta”

“Haba yaya,ina zatabiku yadda,kukai kyau haka bakwa bukatar dan rakiya”

“gaskiya faruq baka kyautaba,zafa muyi fada akan yarannan”

“aikuwa aunty sai dai muyi,danbazanbar banzayan yarannan su shiga rayuwar masoyaba”

assadiq ne yayi dariya kawai yaja motarsa sukatafi,tun ahanya Safiyya take korafin abinda faruq yayiwa farhana,shiru yayimata,sukabiya tawani katafaran super market yashiga lodarwa Safiyya siyayya mai tarin yawa
sukaiwa yaya hannatu ma dayaranta,sukagama yabiya aka kai musu mota suka tafi,gidan yaya hannatu suka dosa tatiya mai nisace takaisu,sukai horn maigadi yabude musu gate suka shiga,kofar parlon suka kwankwasa,maaikinta tazo tabude musu,tai musu sannu da zuwa tagaishesu,

“kiramana yaya ,kice tayi baki”

“To”

zuwa tayi tafadamata saigata tafito cikin shiga ta alfarma,

“lala wanake gani Safiyya amma assadiq ka kyauta

“aibazata naimiki,inayini yaya”

“lpy lau,kanina ya gida ya amarci”

“duk lpy lau”

Safiyya ce tagaisheta taamsa cikin sakin fuska,da kulawa,yaranne suka fito daga dakinsu sunaiwa uncle dinnasu,

“oyoyo,uncle A”

rungumesu yayi yana missing dinsu,

“oya kuje kugaida auntynku”

“auntynmmu ina yini”

“lpy lau yarana ya school”

“lpy lay,aunty zamuzo gidanki”

“to sai kunzo”

nan sukayi salla sukaci abinci sukabata kayan dasuka zo dashi sukatafi kai tsaye gidansu muwadda suka nufa lokacin dasuka je tana parlor tana kallo ,kallon kallo akafara tsakanin Safiyya da muwadda.

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[7:21 Am,2017.]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦����💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

*NASEEBA I UBA*💐

 

*28*

~~~Safiyyace tai mamakin ganin su a gidan su muwadda, mamakine yacikata aranta take tambayar kanta,me yakawo su gidansu yarinyar data ke ganin zata zame mata matsala a gidan auranta,katsemata tunani tayi tahanyar karasowa gabansu tadubi yayan nata tace

“yaya assadiq sannu da zuwa,ga guri zauna

“Ni kadai idonki,yagani
bakiga matata ba ne”

“Oh i am sorry naganta
banganetaba,sannu”

“kema sannunki”

“yayi kyau ina mama?”

“Tana sama,yaya assadiq dama inason ganinka”

“pls kiramana ita,a hanya muke”

kantajuya kiran mama ta sakko daga wata hadaddiyar matattaka
la,cikin taku na kasaita dakaga maman muwadda kaga hansa
kiyar mace mai ji da izza,kasancewar muwadda mahaifinta hanshakin mai kudi ga
ta ita kadai suka haifa
karasowa tayi dafararta,tanaganin safiyya tahade rai,

“Assadiq yau kune a gidan namu,har da amarya”

“Eh mama,inayini”

“lpy lau,ya su momyn taku”?

“lpy kalau,tana gaidaki

safiyya ce tazamo daga kankujerar datake,cikin faduwar gaba,tagaidata,a dakile taamsa,ta kwallawa mai aikinta,kira takawo musu,lemo,

“Aa mama mungode muna saurine”

“Ai daman bakaso kazaunaba assadiq tunda kataho da matar
ka,yaruwarka kullum cikin zancanka take”

“mama zandawo inna
sami,time”

mikewa sukayi ya sakalo hannun matarsa sukaimata sallama sukabar parlon,muwadda ce tabi bayansu da hanzari tasha gabansu tana harar safiyya,kana tace,

“yayana inason ganin
ka,pls”

da kamar bazashiba safiyyace tasaki hannunsa takalleshi da ido,alamar yatsaya tai gaba,tsayawa cikin bacin rai,

“inajinki,sauri muke”

“yaya assadiq yanzu dan abinda kakemin ka kyauta min kenan”

“menayi miki,muwadda kinason
kina son shiga rayuwata pls live me alone”

“yaya inan akan bakata,i can’t do with out u 💕”

tanagama fada tajuya da gudu tashige tana hawaye,kancinyar mama tafada,tasaki kuka mai tsuma rai,nan mama tashiga rarrashinta,yartata,tare
da alwashin sai ta aura mata assadiq,

cikin bacin rai assadiq yafigi motarsa tunda suka kama hanya bawanda yace kala,kowa da abinda yake sakawa,ahaka suka karasa gida,kai tsaye safiyya tai shigewarta ciki,shi kuwa sai da yatsaya ya kulle ko ina,yakwaso,siyayyar da sukayi sannan yashiga daki bata parlor yazube kayan akan kujera yabita ciki nan ma bata nan,karar zubar ruwa yajiyo a toilet ya rage kayan jikinsa yabude toilet din yashiga,cikin karaji tafara masa magana,

“Assadiq! pls kafita kabarni banason ganinka”

“sopy menayi miki,wane gagarimin laifin nayi miki da har kike kokarin hukuntani”

“tambayata kake, yakake nema kamaidani karamar yarinya ne assadiq”

karasawa yayi gabanta yarungumeta yashiga aikin rarrashi luf tayi ajikinsa tana hawaye,

“Sopy kiyi hakuri wallahi inasonki bazan iya rayuwa bakeba,karki damu kanki da yarinyar nan,zanmiki bayanin komai”

“Dee nafara tsorata da yarinyar ne”

“karki damu sweet Sopy”

nan suka shirya abunsu sukai wankansu suka fito,tadakko musu kayan bacci masu kyau sukasa,suka kwanta,rungumeta yayi ajikansa,kamar wani zai kwacemasa ita,

Washe gari da wuri tatashi tahada musu break fast tadawo tashiga wanka tafito,tashirya cikin atamfa super blue da yellow, tazauna a gaban mudubi tana kwaliyya,tacikin mudubi ta hango assadiq yazubamata ido,murmushi tasakar masa yataso ya rungumeta,

“sweet sopy kinyi kyau amma kinmin wayo baki tasheniba”

“Dee kayi hakuri,muje inrakaka kayi kaima”

“Gaskiya sai dai kimin”

“To,muje tunda sokake
injika kayana”

“Aa barshi shiga yayi yai wankansa yafito,yashirya cikin kananun kaya masu kyau,suka fito sukayi break fast sukagama yatayata kwashe kwaninkan suka kai kitten, yashirya yafita office tarakashi har gurin mota,tare da bashi kiss.yaja motarsa yatafi,

afiface tazo suka gaisa
taga kayan dasuka siyo jiya nan tafara diba waitana so,Safiyya,bata hanataba.

faruq ne yai sallama yashigo,yaga afifa tana zuba kaya a leda.

kallo yabita dshi yana tuhumarta.tayi tsuru tsuru.tana kallonsa

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[7:00Pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

_Dedicated 2_💦 *Talented writter’s forum*💦 💙 _love u my adorable friend_

 

*29*

~~~Guri yasamu yazauna,yagaida safiyya,da girmamawa
dasakin fuska taamsa
maida dubansa yayi ga afifa,yace,

“ke wadannan kayanfa

“umm,aunty safiyyace tabani”

“aunty wai haka”?

“Eh,haba faruq meyasa kake hakane,daka zuwanka,zakafara tuhu
marta,dan Allah ka dena”

“Aunt bazaki gane nufina ba”

tashi tayi tashiga kitchen takawi masa
meatpie,da lemo,afifa kuwa tunda taga faruq yazo batagama abinda
takeba,ta gudu,amma bahaka tasoba sotayi tai taiwa safiyya rashin kunya,faruq ne yakebawa Safiyya hakuri akan abinda yaran sukaimata,

“Aunt safiyya ya Assadiq yagayamin su
afifa,sunzo da kawaya
nsu,sunmiki rashin Mu
tunci,kiyi hakuri”

“Haba,faruq nazaci zance yawuce,dan Allah karakuma daga
zancan nan”

“Ai kuwa sai sunci ubansu,dan bazan kyalesuba”

“Tobada yawunaba,
faruq”

Nan sukacigaba da hirarsu,

Abangaran afifa kuwa
tanakomawa gida ta zazzage kayan data debowa safiyya agaban su jalila ,tamabayarta sukayi

“sister wadannan kayanfa”

“Hmm na Aunt Safiyya ne naje naga tawani ba
Jesu akan kujera,inajin
jiya yaya yasaimata”

farhanace ta jinjinawa
yaruwar tata,kana tadora da,

“yayi dai dai afifa,haka
zamudinga yimata,Ku
dubafa kugani,tunda yaya ya aureta,yadena
saimana komai”

jalilace tasa baki,tana kokarin cire glass din idonta,

“afifa baki kyautaba gsky me aunty Safiyya
taisa tataremana”

“yo dama ai ke haka zakice yaya jalila,to wallahi bataisaba”

“rabu daita farhana,kin
san yazai da kayannan

kai ta girgiza,alamar aa,

“Ajiyewa zamuyi dan mude baabinda,zamuyi dasu

“Haka zaai farhana”

ido jalila tabisu dashi
kawai,momy ce ta turo kofar dakinnasu tashigo,tadubi yanmatan nata,tace,

“afifa wadannan kayanfa”

“momy aunt safiyya ce
tabamu”

“yayi kyau,kushirya Ku
zo,kuje gidan maman
Ku,aisha kudubo min muwadda”

“to,momy,wai sai yaushe zaai bikin su
da yaya assadiq ne”

“farhana kenan ankusa
ai nafiku san ayi auran
nan,ko dan tazo ta hai
fa min jikoki”

“yauwa momy,nifa da
man matarsa bataimin
ba wallahi”

Nan suka hau shirin fita

 

Assadiq ne yadawo daga office yatarar da
Safiyya tayi kwalliya ta
yi kyau,tambayar ta yayi,

“sopy yabaki sa sarkar
damuka siyo jiyaba”

“Dee afifa,nabarwa”

“saboda me,kika bata sopy,dan kimin kwalliya ingani fa nasi
ya,miki”

“yanzu danbawa afifa
sarka zakai min fada”

“Bafada naimikiba sopy,shikenan zankoma insiyo miki wata”

“To Dee nagode”

ta sumbaci goshinsa,
yajata jikinsa,yana shakar kamshin jikinta

 

^^^^^^^^^^^^
Najiba ce take ta shirin zuwa gidan Safiyya,
ummice ta dubeta tace

“Najiba kiyi kigama shirn nan kije kidawo da wuri”

“To Ummi”
kammala shirinta tayi taiwa ummintasu sallama tatafi,tanafita
ta tari napep tahau tatafi,sanda takarasa gidan assadiq yana gida,kallonta yayi yafara magana,

“Wlh munyi fushi,
najiba,sai yau”

Dariya tayi tace,”yaya
assadiq ayi hakuri makaranta ke hanani
zuwa”

nansuka gaisa,tagaida
yayar tata,yaimusu sallama,yafita kafin yafita,yadubi najiba yace,

“Najiba ga amanar matata nan ki kulamin
da matata”

“yaya,assadiq da banzobafa”

“Nade fadamiki”

Dariya sukai gaba dayansu safiyya taraka shi gurin motarsa,yaja yatafi,gurin yaruwar tata ta koma,nan suka
shiga,hirarsu suka shiga kitchen suka dora girki,alala sukayi
da farfesun kifi,suka
kammala sukadawo parlor suka zauna,sunfara ci kenan
saiga farhana tashigo
safiyyace tafara yimata magana,

“Farhana sannu da zuwa,bisimilla ga abinci”

“Nakoshi,bazanciba ballanta kiji dadin cewa nazo nacinye miki abincin miji”

“farhana me yakawo wannan zancan kuma”

“oho”

najibace tasa baki tace

“Haba farhana,meye haka zakizo har gidan
mata,kifara mata,
rashin kunya”

“ke rufe min baki kekuma wacece,da harzakisa min baki”

“Bansaniba,mara mutunci kawai”

Safiyya ce tadakatar da najiba,

“Najiba yaisa kiyi shiru

“Farhana,Allah yabaki
hakuri”

“kibatta tacigaba wallahi dasai tagane kuranta, banza kawai”

tasa kai tafita,nan najiba tashiga mamakin rashin mutuncin kanan assadiq, Safiyya kuwa guri tasamu ta kwanta
sai najibace tagyaramata gidan taimata abincin dare,sakamakon ciwan kai da yadameta,kasancewar ta mara son hayaniya,sallama najiba taimata tatafi.

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[8:32Am,2017.]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧.

 

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

_*Sakon fatan alkhairi gareku yanuwa musulmai Allah yabamu albarkacin wanga rana ta jumaa kar mu manta da yiwa annabinmmu salati*_📿

 

.

*30*

 

~~~ Tun bayan fitar najiba,safiyya take aikin kuka,ahaka assadiq yadawo ya
Tatar daita,kwance da mamaki ya shiga parlorn bata ciki,yaga batazo,taimasa oyoyo
ba,kitchen yafara dubawa bata ciki sai
ya nufi bedroom, nan yahangota,dukunkune,
da bargo,da hanzari yakarasa kangadon,ya
yaye bargon yajata jikins,araxane yafara magana,

“sweet sopy,meke damunki”

shiru taimasa,sai kankame shi data dada yi,hawaye nata ambaliya a idonta dada kidimewa yayi ya
shiga tambayar ta,

“Ina najiba”

“Ta tafi,Dee kaina,zai cire,mutuwa zanyi”

“Sopy,meyasa baki min wayaba,tashi mu
tafi asibiti”

“kaya yacanja mata ya
dakko mata,mayafi ya
yafamata, dakyar take iya takawa,saboda jiri
daukar ta yayi,yasata a mota,suka nufi asibitin Annury special
hospital, da kyar yake
tukin motar,gaba data
hankalinsa nakanta,
suna isa yaje aka bude
mata file,suka Shiga
ganin likita,nan kikitan
yashiga,dubata,yakira
nurse taje taimata test din fitsari,basu jimaba
suka dawo,tabashi result din tafita,karba yayi yaduba,nan take
yagano safiyya na dauke da ciki,na wata daya da sati biyu,
hannu yamikawa,
assadiq,

“congratulation,ur wife
was pregnant”

ido assadiq yazaro😳
saboda abun yaimasa
bazata,likitan yarungu
me,nan take yazube ya
yi sujjada ga Allah ya
dawo gaban safiyya ya
kamo hannunta,yazuba mata
ido,

“sweet sopy,kinji abinda doctor yace,
nakusa zama dady”

shiru taimasa ita duk
kunya takamata,kudi
yadakko yabawa doctor, din wai tukwici
sukai masa,sallama
suka tafi,tun a hanya yake tambayarta mezataci,ashe tayi bacci,dariya,yayi,suka
karasa,gida ya dakkota yakaita har kangado,
yaciremata,kayan jikinta,wani sanyi taji ya ratsa jikinta,tafarka

“Wash Dee sanyi nakeji
pls rufeni,yaushe nashigo daki”

“Tun a hanya kikai bacci maman baby”
yafada,yana shafa cikinta”

“Dee,banaso,Allah zan
sa ma kuka”

“I am sorry sweet wife,
yanzu dai mezakici”

“Banacin komai”

“cab kin isama,ku kwana da yunwa”

“Nida wa kuma Dee”

“ke da babyna mana”

“To bani tea”

“angama madam”

Tashi yayi yashiga kitchen yadafo mata,tea kan yadawo
har tayi bacci,mamaki
yayi,ahankali yafara ta
shinta,yana shafa gashin kanta mai laushi da sheki,a hankali,ta bude idonta

“Sopy tashi kisha”

“Dee na koshi,bacci nakeji”

“Daure kisha ko kadanne”

dagata,yayi yafara bata ahankali tasha rabin kofin,kenan ta
sheko amai gaba daya tabata musu jikinsu da
bed sheet din kidimewa assadiq yayi

“sannu sopy,bakyason
tea din”

“To bakaine kasa min
madarar ruwaba”

“Ayya bazankumaba”

daukarta yayi,yakaita
toilet yagyaramata jikinta,yadawo ya cire bed sheet din yasa wani,ya kwanar daita ya rufeta da bargo,ya koma toilet yayi wanka
ya sa kayan bacci yafesa turare yazo ya kwanta,a bacci Safiyya taji kamshin turaran assadiq,tafarka agigice

“Dee wana irin turare kasa”

“Wanda muke sawa ne

“Banason sa Dee, pls kacire rigar nan”

“Angama dear,fitama zanyi dashi gobe”

Washe gari assadiq ne
yashiga,kitchen yadafawa sopy farar shinkafa da manja,suka zauna sukafara ci sunkusa cinyewa ta dauke plate
din,

“Gaskiya Dee,kabarmin
haka,bakoshi zanyiba fa”

“Nabar miki maman baby”

“Banaso,Dee pls kakaini gida yau kaji”

“Sopy gida kuma,keda baki da lpy”

“Dan Allah ,ka kaini,kaji”

“To shirya bari inje ingaida momy,zanturo
miki farhana ta gyara gidan”

“To, Dee”

fita yayi yaje gidansu yagaida momy nan yake fadamata Sopy bata da lpy

“Meyasameta”?

“ciwan kai da zazzabi”

“Allah yasawake,maman muwadda tace min kunje,kai da matarka”

“Eh,momy”

“To kasami lokaci ka koma”

“To momy,farhana kije
kidan taimakawa Sopy”

“To yaya”

“momy dady yana nan”?

“Eh”

Tashi yayi yahau saman dadyn yagaida shi,tambayar sa yayi safiyya,

“lpyt kalau,dady batajin dadima”

“subahanallah,kakaita asibiti dai ko?

“Eh dady”

Nan dadyn yake gayamasa zai tura faruq Dubai yakaro karatunsa scan,fatan alkhairi yayiwa kanin nasa,

farhana tana zuwa gidan assadiq tatar da safiyya naci fara da manja ko gaisheta batayiba,tasa mata hannu,tadakko yaji ta gunbuda mata,tanaji tana gani tabarmata,batason yaji

Tatashi tashiga wanka
farhana nagama cin abincin ta wanke kwanikan ammafa duk tajika mata kitchen bata gogeba,tafito tashiga dakin safiyya turaran da Safiyya bataso ta dauka tashiga fesawa Safiyya na bandaki tajiyo kamshin turare
nan tafito a gigice tozali tayi da farhana da turare a hannu,nanfa tafara sheka a mai,assadiq ne yashigo ya tarar da Safiyya nata a mai,da hanzari yakarasa gabanta,yataimaka mata,wata uwar harara yazabgawa farhana ganin turare a hannunta
yaja hannun Safiyya ya kaita dakinsa,

Tsawa yadakawa farhana,

“Dalla malama wuce kibawa mutane guri”

fita tayi yadakatar daita turaran ya mikamata tatatafi
tanazuwa gida tasa kuka safiyyace ta mareta.ido momy tazaro😳

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:25PM,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

💦 *T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

_*Ina gaisheku masoyan kannan mijina dafatan munyi jumaa lpy Allah yabamu albarkacin ranar*_ ~Ameen~👏🏻

 

*31*

 

~~~ Momy ce tadau waya tashiga neman layin assadiq tanata ringing baadagaba lokacin yana can yana gyara gurin da safiyya tasheka amai,yabar wayartasa a parlor, sai
bayan dayagama yadaukko wayar yana
dubawa yaga missed
calls din momy,kiranta
yayi tana dagawa,tace
yazo yanzunnan,
dakinsa yakoma yatarar da safiya kwance,karasawa yayi gabanta yatallafota yashiga tambayarta,

“sweet sopy meyake damunki,ina ne kemiki
ciwo”

“Dee,yunwa nakeji”

“Mezakici,insamo miki

“kayi ka shirya ka kaini
gida ummina tai min tuwo”

“To,Sopy inazuwa momy ce take kirana”

“Dee Allah yasa, bakai
wa afifa komaiba”

“Baabinda naimata,
bari inje indawo”

Bejira amsartaba yafita kai tsaye gidan
yawuce yatarar da momy a parlor ta hade
rai,yasami guri ya zauna,

Momy gani Allah yasa
lafiya”

“Assadiq me afifa taiwa matarka ta
mareta”?

“Momy yazaai safiyya
tamari afifa”

nan yabata labarin abinda yafaru,shiru ta
yi,danta fahimci safiyya ciki ne daita,
ta numfasa,tace

“Abinda zanfadama ba
shine ba matarka ba
yayana,tafita harkarsu
inbahaka zanbata mata wallahi”

“wallahi momy safiyya
bata,da matsala,
hasalima hakuri take da yarannan”

“nadai fadama,kuma kacigaba da fifita matarka,tashi kabani guru”

tashi yayi yafita,a bakin
gate suka hadu da faruq, yanayin fuskar
yayan nasa ya kalla yaga bacin rai a fuskar
sa,tambayar sa yayi,

“Bross me yasameka,
naga damuwa a fuskarka”

“Hmm,bari kai dai faruq,afifa ce tazo tacewa momy wai Sopy ta mareta,shine
momy take ta fada”

“kai wadannan anyi yanbanzan yara,wallahi nasan karya take”

“Hmm kabari kawai suna nema su haddasa min fitina agidana”

“kabarni dasu zasu ci
ubansu wallahi”

“Aa faruq kyalesu ai
suma matane gidan
wani zasu ko”

“kansuje zanfara saisaita musu zama”

“Allah ya kyauta”

wucewa yayi yakarasa
gidansa,boye damuwar sa yayi,suka shirya cikin shiga ta alfarma,suka fito,have

“sweet sopy kinyi kyau
zo muyi photo”

“Aa Dee dan Allah mutafi yunwa fa nakeji

“To,muje maman baby”

“Dee,wallahi kabari
banaso fa”😫

“Nadena sopy”

mota ya budemata tashiga,ya maida kofar yarufe,yazagaya mazauninsa ya zauna yaja su suka fita,a wani super market suka tsaya sukaiwa su umminta siyayya wata
chocolate, safiyya ta dauka kwali biyu,dama ragowar ta kenan a gurin suka biya kudin suka fito,kayan aka biyo su dasu aka zuba
musu abayan motar suka ja motarsu suka tafi, run a hanya Safiya
take shan chocolate din data siya assadiq ne yasa hannu yadau daya,cikin shagwaba tace

“Dee dan Allah kasha kadan kaji,jinta nake
kamar indauwama inasha”

“inkin shanye zan siyo
miki wata yanzu dai
samin abaki”

bakinsa yabude tasamasa yahada har da hannunta ya tsotse,

“Wash Dee zaka cijeni fa”

ahaka suka karasa gidan su safiyya,ummi
tana zaune sai gani tayi ana shigo da kaya

zatai magana kenan sai ganin safiyya tayi
tashigo,da gudu ta je ta rungume ummintata

“Haba,safiyya,har yanzu baki girmaba”

“ummina nayi kewarki”

“To ina kikabar assadiq din yana waje”

“Maza kije kishigo da shi”

fita tayi suka jero tare
gwanin shaawa,yadurkusa yagaida ummin cikin girmamawa

“Assadiq ya momyn taku”?

“Lpy lau ummi tana gaidaku, Baffa baya nan ne?”

“muna amsawa,yafita”

nan tayi musu nasiha
takuma godemasa da irin rikon da yayiwa safiyya nan yayimata
godiya yatashi zai tafi
kudi ya ajiywmata yatashi,yafita,godiya taimasa,safiyya ce tarakoshi waje yakalleta yace,

“sopy yaushe zanzo mutafi”

“Dee da daddare”

“cab nikuma,inzauna
a ina,da yamma zanzo
mutatafi”

“To,Dee,badamuwa”

kici abincifa”

“OK sir”

yaja motarsa yatafi takoma ciki nan suka sha yinin su da yanuwanta ummice
takula da yanayin yartata,tayi shiru tabarwa ranta,tuwo tace aimata,nan da nan ummi taimata taci
sosai ,baffane yadawo
yaga safiyya yaji dadin
ganinta,suka gaisa
yadada yimata nasiha
daga karshe assadiq yazo suka gaisa da baffan sukaimusu sallama suka tafi,

washe gari jalilace tashogo gidan Safiyya
taga chocolate dinta
a parlor, taddauka tashanye tas,tafito ta tarar tashanye ido kawai ta zuba mata kawai.

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:9Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

*32*

~~~ Dakyar taiya bude
baki taimata magana
saboda yadda takejin
jiki,ga wata yunwa data keji takasa cin komai daman chocolate din take iya
sha,sai ga jalila tazo
tashanye mata kallon
ta,tayi tace

“Haba jalila,ya zakiga abu bakisan kona
wayeba kawai kidauka

“Oh yi hakuri aunty ai
danaji yaya assadiq
yace mana bemana iyaka da gidansaba shi
yasa na dauka”

“Hakane to,amma ai inzaka dau abu yana
da kyau kafara tambayar mai shi ko”?

“kai dan Allah,yi hakuri
akan wata chocolate
zakitasa ni magana,
dama zuwa nayi infada miki anjima zan
zo da saurayina,pls kimana boga da stick meat”

“Allah yakaimu yabani
ikon yimuku”

“Aa aunt kamar yaya
banganeba”?

“Jalila baki ga bani da
koshin lpy ba”

“Bansaniba ni kam,
Allah yabaki lpy,sai munzo”

Batajira amsartaba tasa kai tafita,tagumi
safiyya tayi tashiga tunanin yadda zatai ta
sami wata chocolate din ga wata mahaukaciyar yunwa
datakeji,jikinta har yafara rawa,tadan kwanta,ta rufe idonta batasan sanda idonta
yafara zubar da hawayeba,faruq ne yai
sallama ya shigo,ahankali ta goge
fuskarta,tayunkura tatashi,Zaune tace,

“Faruq sannu da zuwa

“yauwa aunty ya gida
yajiki”?

“lpy lau,jiki da sauki”

“Daman yayane yaimin waya yace inzo inga yanayin jikin naki

“Au dabazaka zo ba ke
nan ko faruq”?

“Aa auntis zanzo indubaki mana”

“Ai shi kenan,faruq dan
Allah inba damuwa irin wannan chocolate din
zakasiyo min”

“To aunty angama”

kudin tashiga tadakko
masa,kantafito har ya
tafi,taajiye kudin ta koma ta kwanta,yadan jima kafin yadawo,can sai gashi yadawo lokacin tayi bacci gashi tarufe kofa ya
jima yana knocking kafin tafarka akasalance tafarka taje tabude masa yashigo,sannu yayi mata saboda yadda ya
ga ta galabaita sai tabashi tausayi,

 

“Aunt gashi ansiyo ammafa ba waccan,ga wainar shinkafa ma nasiyo miki”

“Kai faruq nagode sosai kamar kasan yunwa nakeji,taimaka
min da plate dan Allah

Tashi yayi yadakko mata tajuye tafara cin gaya ba miyar kallonta faruq yake da tausayi
yace ,

“Aunt ya bakya sa miya”

“Aa faruq banason miya”

nan sukataba hira har
yakebata labarin tafiyar dazaiyi tai masa murna amma wani bangaran sai tadanyi fargaba saboda yadda yake takawa *kannan mijinta* birki,tashi yayi zaitafi tadakko kudinsa zatabashi tambayar yayi,

“Namenene”?

“Na chocolate din ka
mana”

“yanzu aunt danna siyamiki abu sai kinbiyani,shikenan ki ajiyewa Najiba kice kudin toshintane injini”

Dariya tayi yasa kai yafita,takammala cin wainarta kenan kiran assadiq yashigo yaduba jikinta ya fada
mata yaya hannatu zata zo anjima,

“To Dee sai tazo,pls kadawo da wuri kaji

“OK my dear,kunci abinci”?

“Dee in dawa kuma”?

“Sopy keda baby na mana”

“Hmm faruq yasiyo mana wainar shinkafa

“Yauwa to ya kyauta take care of self & my baby, love u💙

“OK Dee I will love u too”💕

 

Tashi tayi tashiga kitchen tafara aikin boga,sai da ta daure hancinta sanna ta iya
yin aikin tunda tasami
ciki,batason shiga kitchen assadiq ne yake komai,ahaka ta kwaba ta gama murzawa kenan zata soya yaya hannatu ta zo,fitowa tayi taga waye tai tozali daita kwance ahancinta tayi

takaraso ta rungume

ashiraf nabil ma yakankameta suna murna,taiwa yaya hannatu sannu da zuwa,suka sami guri

suka zauna tagaisheta

“yaya ina yini”

“lpy lau kanwata ya jiki

“Dasauki yaya,ya abbban su nabil”?

“lpy lau yanaimiki ya jiki”

“ina amsawa”

“mekike a kitchen haka har kina toshe hanci”?

“Wallahi yaya aiki nakeyi jalila ce zatai bako shine,nake mata
boga da stick meat,
kitchen dinne sai inj yanai min wari”

“Ayya sannu kinji kanwata,to ita dan ubanta bata san baki

da lafiyaba,bari inje gidan kar ki kuma shiga kitchen din ita tazo takarasa,yar banzar yarinya barima assadiq din yadawo gwanda asamo miki mai aiki”

Tashi tayi ta tafi tabar yaran a gidan Safiyya

 

Tana zuwa kai tsaye dakin yanmatan tanufa suna kwance a kan gado kowacce tana abinda taga dama ita kuwa jalilama bacci take,tadana mata duka

“Dan ubanki tashi kina nan kina bacci kinbar bewar Allah da aiki ko”

Momy. ce taji kamar maganar hannutu taleko taganta tambayar ta tayi meyafaru zata samata yara gaba tanai musu jaraba gayamata tayi abinda yafaru,tace

“Sannnu hannatu yanzu kema akan matar assadiq zaki rufe ido kiki kannanki ko to kun kyauta”

“Momy mufa bakinsu muke ba gaskiya muke fadamu su,kuma wallahi kije ki karasa aikin da kika jamata”

Fita tayi taje tashiga kitchen din takarasa tatagama ta wanke kwanikan ta jikamata kitchen bata gogeba tai tafiyarta Safiyya ce tafito daga dakinta da waya ahannunta suna magana da assadiq ta shiga kitchen din bata san da ruwaba kawai ta subale sai jin kararta assadiq yayi,akidime yadinga

“Hello! Hello! ina Safiyya ta sume😰

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[2:21Pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

*_KANNAN MIJINA_*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Wannan shafin nakune masoyana ina_
_godiya da adduoinku_
_gareni Ina kaunarku_
_aduk inda kuke_ _Allah yabar kauna_
*Hajja naseeba*_na gaidaku kyauta_👌🏻💙

 

 

*33*

 

~~~Ahargitse assadiq
yatattara takardun gabansa yarufo office
din yanufi gurin motarsa abokinsa Achida ne yaga fitowar
sa,a hargitse yabiyo bayansa kan yakaraso
har yabar harabar company, ya dinga sharara gudu,
safiyya kuwa tunda ta fadi batasan inda kanta yakeba,su nabil
ne sukajita shiru suka
shiga nemanta,sauna zuwa kitchen suka ganta kwance,cikin jini
da gudu suka tafi fadawa mamansu suna zuwa suka sa kuka, tambayarsu afifa tayi

“Menene”

“umm Aunt safiyya ce
tafadi cikinta yafashe
yanata,jini”😰

agigice suka tashi suka nufi gidan kan su karaso assadiq ya shigo gidan ko motar
be rufe ba,yashiga parlon yaduba daki bata nan yafito yaduba dakinsa yanufi kitchen
tozali yayi daita kwance cikin jini akidime yayi kanta yashiga jijjigata yaji luf
daukarta yayi yai waje
daita,yasata amota zai tayar da motar kenan su yaya hannatu suka
shigo,da hanzari sukai
wajensa,tambayar sa tayi meyafaru”

“yaya muyi sauri mukaita asibiti,tamutu

“haba assadiq wace irin mutuwa”

motar suka shiga suka
kaita asibiti faruq ma ya rufamusu baya da gudu yake jan motar idonsa yakada yai jazur suna isa akadau
keta aka shigar daita ciki likita yashiga dubata da taimakon nurses aka samu tadawo daga dogon suman datayi,sunyi iya kokarin su wajen ganin cikin bezubeba,amma
ina sai da yazube,su
assadiq suna waje ya
kasa zama sai zurga
zurga yake,likitanne yafito yake sanar dasu
tafarfado,amma sai dai suyi hakuri cikin jikinta
yazubu,
kuka assadiq yasa a wurin,

“Hana Assadiq sai kace karamin yaro,dan Allah kayi hakuri” cewar yaya hannatu
wankin ciki akaimata tasha wahala assadiq
yai kuka kamar ba namijiba,aka fito daita aka maida ita dakin hutu,assadiq ne yakarasa gadon Yakama hannunta ya kankame,tana ta bacci dago da kansa yayi,yakalli yayarta sa
yace,

“yaya dama bakije gidanba,gidan momy
kika fara zuwa”

“Gidanka nafara zuwa mana sanda naje aikima takeyi a kitchen

“yaya aiki kuma,bata
iya shiga kitchen fa”

Nan tabashi labarin abinda jalila tayi,faruq ne yai kwafa yafita kai
tsaye gidansu yawuce
yana shiga yaga jalila
da saurayinta sunata hira karasawa yayi gabansu ya dauketa da mari agigice ta dago takalleshi zai karamata tagudu cikin
gida tana ihu saurayinne yatsaya tambayar me taimasa

yadakamasa harara yabita ciki,dakinsu yabita yafara jibgarta ihunta momy taji tafito
tashigo dakinnasu,tana zuwa ta zabgawa faruq mari
kuncinsa yadafe,nan tafar masifa,

“Uban me taimaka mara mutunci kawai”

“Haba momy kitan
bayeta mana,garin iskancinsu tasa safiyya tayi bari,gata can a asibiti bata san inda kanta yakeba”

“Dalla rufe min baki
tayaya jalila zata sa
matar assadiq tayi bari
garin dai sha shancinta tai bari”

Dady ne yaji hayaniyar
tai yawa yasakko yake tambayar me yake faruwa,faruq ne yabashi labarin abinda
yafaru,shiru yayi yadago yakalli jalila cikin bacin rai

“Jalila me yafaru”?

“Ummm,Dady wanke wanke naimata sai kitchen din yajike,na
manta bangoge ba”

Nan yarufeta da fada sosai ran momy yabaci,suka dunguma
sukatafi asibitin sanda suka karasa assadiq yakifa kansa akan gadon da safiyya take
yanata kuka,su dady sukai sallama suka shigo,kasa dagowa yayi sai da dady yai magana sannan yadago,

“Haba sadauki sai kace bana mijiba,Allan da yabaka aishi zaibaka wani kayi hakuri kaji”

“Dady safiyya mutuwa
zatai tun da mukazo bata farkaba”

“karka kuma fada Zara
tashi”

Yaya hannatu ce takira
yayar Safiyya tafadamata,hankalinta
yatashi,taiwa ummi waya tasanar daita

sai yanzu assadiq yadago yaga jalilla wani mugun kallo yaimata,momy ma takarasa gaban gadon
taiwa safiyya sannu,

Assadiq ne yashiga tunanin hukuncin dazaiwa jalila.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

 

 

 

 

*3
[12:44Pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*34*

 

~~~Mikewa yayi,yazo
gaban jalila yazuba mata ido yace,

“Jalila kinga abibda kikaja min ko kinjawo
narasa babyna ”
yana magana hawaye
na ambaliya idonsa,

“yaya pls kayi hakuri
wallahi bansan haka
zatafaru ba,kayi hakuri
I will never do it again
forgive me”

shigowar su ummin safiyya ne da yayanta
Dr almustapha ne yaka
tse masa maganar da suke da jalila,
Nan suka gaisa da su
momy sukatambayi
ya maijiki,daman dady
yadade da tafiya,
gaban gadon suka karasa tanata bacci ta
rame lokaci daya,

“sannu safiyya Allah yabaki lpy” cewar Dr
almustapha,yana kokarin dubata,

Ameen ya Allah Dr” cewar assadiq,
ahankali safiyya tafara
bude idonta,da sauri
assadiq yakarasa gaban gadon, dube dube tafarayi,can taji cikinta ya murda agigice ta fara magana

“Deeeee! zanmutu kiramin ummina wayyo Allahna”

karasawa ummi tayi
gaban gadon ta rungumeta,

“Safiyya sannu kinji gani umminki ce”

“Ummi mutuwa zanyi
ina baffana,da yayana”

“baffa yana gaidaki ga
yayanki nan”

maida dubanta tayi
ga yayan nata,tace

“yaya kayafemin mutuwa zanyi”

“yaisa safiyya waye yace zaki mutu”

Allurar bacci yaimata
akasamu tayi bacci,

tashi su ummi sukayi
zasutafi,tace amina ta
zauna daita su kwana

assadiq ne yakwantar
da kai yace,

“Ummi basai ta kwanaba zankula da ita”

“To shikenan assadiq angode Allah yakara lpy”

wani banzan kallo momy taimasa,sukai
musu sallama suka tafi,jalila ce take ta satar kallon Dr almustapha, bayan tafiyar su da kadan su
momy suka tafi suma

yaya hannatu akabari
tazauna da ita kafin assadiq yadawo,gida
yakoma yadebo mata kaya yayo mata siyayya,sanda yakoma

tafarka tana zaune yaya hannatu ce take
bata tea taki sha ,

“Yauwa assadiq zo kabata ko zata sha tun
dazu nakefama daita”

karasawa yayi gaban ta yazauna kusa da ita
yashiga rarrashinta ya
dau tea din yafara bata
dagowa tayi takalleshi
tace,

“Dee nakoshi,bazaniya shaba,cikina ciwo yake

Yaya hannatu ce tai musu sallama tatafi,
zairakata tace yabarshi yakula da safiyya,yaimata godiya

Dakansa yashiga bata shayin ta sha sai da ta shanye sannan yabata
kazar da yasiyo mata
kadan taci cikinta ta tashafa taji ba tudun dayayi,ahankali tafara
magana,

“Dee meyafaru da cikina,naji kamar babu

“Sopy kiyi hakuri Allah ne yabamu yakuma kaddaramana rashinsa

“Dee mekake nufi kana
so kace min narasa shi
kenan”

kuka tasamai nanfa yashiga aikin rarrashi

“Haba sopy kiyi shiru kidena kuka da munkoma gida zamu kuma samun wani babyn sai kinhaifa min
yaya goma”

dariya tai tadada shigewa kirjinsa yashiga rarrashinta ahaka bacci yakuma daukarta,ya gyra mata
kwanciyarta yazuba mata ido ahaka shima
bacci yadauke shi,

washegari da kansa yaimata wanka yashiryata cikin doguwar riga mara nauyi yazubamata ido
tadago ta kalleshi tace

“Dee kallo kuma,mene ne”?

“Sopy inasonka ina kaunarki,kitaimamin
duk rintsi karki kujeni
karki barni❣

“Karka damu Dee inshaallah inatare dakai”
kwanatar dani kaji”

“Aa sopy kibari kiyi break fast kafin ki kwanta yanzu faruq zai kawo abincin”

“Dee dan Allah inyakawo sai ka dagani”

“To maman baby”

“Dee baby kuma,ba munrasa cikinba”

“Zamu sami wani ai”

yaya rukayya ce ta turo kofar tashigo da katon cikinta da suhyla da babanta

hannu assadiq yabashi
suka gaisa🤝yaimasa
yamai jiki

yaya rukayya ma karasawa tayi gurin safiyya taimata sannu
assadiq ne yace zaije yadawo yaimusu sallama yafita shi da baban suhyla

suhylace takalli safiyya tace,

“Aunt cafiyya cannu,wai faduwa kikayi ko”?

“Eh suly,amma naji sauki ai”

labari Safiyya tabawa yayarta rukayya dalilin barinta,shiru tayi kana tace,

“Safiyya meyake damun *kannan mijinki*ne?

“Bansaniba aunty amma basu da kirki”

faruq ne yaturo kofar yashigo da fararsa yakaraso

“Auntyna sannu da jiki

“yauwa faruq yasu momy”

“suna gaisheki”

“ina amsawa faruq”

yagaida yaya rukayya
yabasu hakuri akan abinda yafaru sukace
bakomai yawuce suhyla tana taiwa faruq surutu aka zubawa safiyya abinci taci wanda rukayya takawo

kwananta uku a asibiti
aka sallameta kai tsaye gidan su aka wuce daita,da kyar assadiq ya yarda

sai shi kadai a gidan yana kwance a parlor daga shi sai vest sai gajeran wando ya rungume wata rigar Sopy idonsa a rufe kawai sai ganin mace yayi akujera tazuba masa ido👀

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:28Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

*_KANNAN MIJINA_*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Dedicated 2 my lovely friend_
*faeexa m usman*💦
_the typer of_ *Amuntarmu*_May God live us together sis_💙

 

*35*

 

jikinsa ne yabashi kamar anshigo,ahanka
li,yabude idonsa,da
mamaki yamike yashiga bedroom yada
kko,jallabiya yasa yafito cikin fada yafara
magana,

“ke wane irin haukane
akanki,zakishigowa
mutane gida kai tsaye”

muwaddace tanarke
fuska,tace

“yaya dan Allah kayi hakuri nayi sallama
bakajiba,dama nazo
duba aunty safiyya ne”

“Dakikazo duba Sopy
sai akace kishigomana
kai tsaye,ko kuwa bakitambayi inda safiyyan takeba,kafin
kizo”

“yaya pls kayi hakuri
kasaurareni,dama da
akwai maganar danakeso muyi”

ahargitse yafara magana,

“Muwadda! u better enter ur sence, how dare u,come 2 my home and talking rubbish 2 me,pls i beg u in the name of God live me a lone”😡

“Yaya assadiq dan Allah kasaurareni”

“kifitarmin a gida,aure
ko kije naji zan aureki
amma kisani gangar jikana zaki aura,nariga
na mallakawa sweet Sopy komai nawa”

zata kuma magana yadakatar daita,
dagudu tafita kai tsaye gidansu assadiq tawuce daman tare sukazo da mamanta tana zuwa tafada jikinta tashiga rera kuka,akidime momy tashiga tambayarta,

“yata,meyasameki keda waye”?

“momy assadiq bayasona,daga gidansa nake,ya koroni”😰

mamanta ce ta kalli momy da bacin rai afuskarta tace,

“Yay Kareema inganin
ahakura da auran nan
kawai”

“Haba aisha,kan wane
dalili,ai baabinda zaihana auran assadiq
da muwadda,ni ita nakeso”

farhanace tasa baki,
“Wallahi aunty muwadda ke mukeso
kuma kar wata mace
ta tsorataki”

“Ai momy kamata yayi
kifadawa dady kawai
yasan da maganar”
cewar afifa tana kokarin mikewa,jalila
kuwa shiru tayi ita yanzu tunda taiwa assadiq sanadin rasa cikin safiyya tashiga damuwa,gashi tadamu
da yayan safiyya,ko mehakan yake nufi?”

_To aganin naseeba dai so ne yake nukurkusar zuciyar jalila_😅

faruq ne yashigo parlorn yagaida maman muwadda,muwadda tadago takalleshi tace

“Faruq ba magana ko”

“Afuwan muwadda bankula da keba ya
kike?”

“Lpy ba lau ba”

mikewa yayi yabata amsa,da “Allah yakawo lau din”yai tafiyarsa faruq bayasan muwadda,Nan dai su momy sukacigaba da
tattaunawa.

Tun bayan fitar muwadda assadiq yashirya yafita zuwa gidan su safiyya ransa abace,yana zuwa yaimata waya gashi akofar gida lokacin Dr
almustapha,yana gida
shi yafito yashigo dashi bayan sungaisa🤝

yagaida ummi yashiga
dakin da safiyya take
tana sanye cikin atamfa ja da green,doguwar riga,anmata kitso kananu,tabazo da jelar
tayi kyau gashi ta mur
mure,ido yazubamata
yakarasa yazauna gefan katifar datake yazauna yace,

“Sweet sopy kinganki
kuwa,kebaki da damuwa ko”?

“Dee meyafaru,kaima
aibaka da damuwa gashina kayi kyau”

“Eh zaki iya cewa nayi
kyau amma bakiga yadda narameba,Sopy
bana iya bacci kinsabar min dayin komai tare dake”

“Dee ai nakusa dawowa”

janta yayi jikinsa yashiga aikamata da
sakonni,gabadaya ya gigice bakinta yashiga
tsotsa yazame dankwalin kanta,zai zuge zip dinta kenan

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[9:00Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_*KANNAN MIJINA*_
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

_Inabawa masoyana hakuri sakamakon gajartar da page 35 yayi hakan tafaru ne saboda wata tangarda dana samu_ .

*Nagode*👌🏻

 

 

*36*

 

 

~~~Ahannunsa safiyya ta rike tashiga girgizamasa kai alamar aa,

“Sopy kibarni mana,
nayi kewarki nayi kewar tattausar fatar
Jikinki”

“Dee kayi hakuri kaga
baa gida mukeba,karfa
wani yashigo”

Kan yabata amsa anyi
Sallama abakin kofar
dakin shiru aukayi yai
Sauri yagyaramata
rigarta ya dai daita nutsuwarsa,yamatsa
gefe,sannan safiyya tace ashigo,Najiba ce
dauke da katon tray anjera kuloli akai takawowa assadiq

“Yaya assadiq ga abinci”

“Yauwa Najiba kamar
Kinsan yunwa nakeji,
Kun daukemin mata ko

“Yaya ai takusa komawa tunda taji sauki muma munfiso
takoma tafiya sa mutum aiki” tafada tana dariya

“Aa badole tasaki aikiba ita dabata da lpy,kicigaba da kular min daita zanbiyaki”

“Angama oga”
Gaba dayansu sukai dariya tafita mai da dubansa yayi ga Sopy
ta matso tabude kulolin tuwon semovita ne da miyar danyar kubewa yaji naman kaji da manshanu ankullashi kamar kullin alala tasa
Masa kulli biyu taturamasa gabansa

“Sopy ni zanci da kaina gaskiya kibani dakanki”

“Dee wani lokacin kafiya rikici”

“Eh naji”

Nan tadinga bashi da hannunta yanata zuba
Santi sai da yaci kulli uku yakusa cinye wa safiyya tasamasa abaki yahada da hannunta yaciza yarkara tayi yasa hannunsa yatoshemata baki da shagwaba tace

“Dee cizona fa kayi kuma Allah sai narama

Dariya yasa yace

“To kirama ummi tajiyo muna kokawa incemata hakkinki kikeso”

“Lala Dee au bayan nataho kuma sharri ka koya”

Nan dai sukasha hirarsu daga karshe yaimusu sallama da zunmar washegari zaizo yadau matarsa,
Najiba yakira yabata siyayyar da yayomata

Kai tsaye gidansu ya wuce lokacin su muwadda suntafi jalila
tanaji ya shigo ta gudu
Yasami guri yazauna yagaida momynsu tahade rai tace

Assadiq daga ina kake
?

“momy naje naduba jikin safiyya ne”

“Wato kai baka dawata magana sai ta safiyya ko,me kayiwa muwadda dazu?”

“momy mezanmata wani abun tace nayimata”

“Bansaniba assadiq to ka saurareni kaji da kyau inaso kaje kasami dadynku kaimasa zancan muwadda kuma ka nuna masa Kaine kakeso kadai jini ko”

“Naji momy”

“yaushe zata dawo matar taka?”

“gobe”

“ba laifi,katashi kaje kaci abinci”

“Nakoshi momy”

farhana ce tafito tasami guri tazauna tadubi yayannata race

“yaya aunty muwadda tace wai ka kirata”

wani mugun kallo yaimata yatashi yatafi
murmushi kawai momy tayi

yana komawa gida yai wanka yahau gado yadau wayarsa yakira sopynsa suka sha hira
sunacikin hirar tyi bacci addua yaimata yakashe wayar yana kashewa kiran muwadda yashigo tsaki yayi ya kashe wayar ya kwanta.

 

washegari tun safe aka
kirawo mai kunshi tazo taiwa ssfiyy ana cikikin kunshin yaya rukayya tazo takawowa safiyya magun gunan gyaran jik, ummi tai taimata nasiha mai ratsa jiki,tare da nunamata girman hakuri kan Rukayya ta koma tace

“Rukayya inkuma ganin kafarki agidannan inbaso kike kihaihu a hanyaba”

“Dariya sukayi gaba dayansu,Da magariba assadiq yazo yadau mtarsa Baffa yaimusu nasiha sosai yayanta yabata 20k tatafi tana kuka,assadiq ne yadubeta yace,.

“Haba amaryar assadiq meye na kuka
muda zamusami baby
adaran nan”

shiru taimasa ahaka suka karasa yanata rawar jiki,aranar assadiq yayi kwanan farinciki dan sopy takoma masa kamar amarya,washegari dakansa yashiga kitchen yahada break fast yatasheta sukai wanka suka shirya cikin wata shadda sky blue iri daya sunyi kyau sukasha hotuna🤳🏻suka koma parlor sukai break da kamar bazai fitaba dady yaimasa waya yazo zasu unnguwa haka tafita badan yasoba,ya kalli Safiyya yace,

“sweet Sopy,ki kular min dakanki”

“To Dee kaima haka”

yaja motarsa yafita,be jima da fitaba sai ga afifa tarako muwadda
kallonsu safiyya tatsaya yi tace

“Sannunku,,kushigo mana”

“Aa bazama zamuyiba
yayafa”

“yafita,yasu momy afifa?”

“Tana gaisheki,tanai miki yajiki,ai mu yanzu tsoran shigowa muke
kar muje mukuma zubar da ciki”

kantabasu amsa assadiq yashigo muwadda ce tamaida dubanta gareshi takalli kayan jikinsa takalli na safiyya .

 

 

 

 

*NASEEBA I UBA*✍🏻
[10:22Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Ina gaisheki Kawata ina miki sannu bisa zazzabin da kikayi 2days Allah ya kara sauki yasa kaffara Ameen_
*Sadiya smart*

~Talented group admin~💦

 

 

 

*37*

 

 

 

~~~Kallonsu yayi a wulakance yadada tamke fuska yace,

“Uban me yakawoku gidana”

“Ummm yaya dama aunty muwadda narako”

“Tayimana me”?

Sopy ce tariko hannunsa tace,

“Haba Dee meyasa haka,yakamata kasaurareta”

“Kibarta sweet sopy,metakeso inmatane”?

Hannun matarsa yaja suka shige daki sukabar su atsaye afiface tadubi muwadda tace,

“Aunty muwadda zo mutafi kuma wallahi zatasani munafuka kawai”

Fita sukayi suka tafi gida,safiyya kuwa suna shiga daki tafizge hannunta daga na assadiq tace,

“Dee Meye tsakaninka da yarinyar nan yau sai kafadamin tsakaninku”

Jikinsa yajata yakurawa kyakkyawar fuskarta ido yace,

“Sopy banason bacin ranki,farincikinki shine
Nawa,shiyasa naki fadamiki tsakanina da muwadda”

“Dee kafadamin mana”

“Sopy muwadda itace yarinyar da momy takeso inaura”

“Deee yaushe😳nashiga uku”

Dada rungumeta yayi yashiga shafamata bayanta ahankali cikin kwantar da murya yashiga rarrashinta da banbaki kuka take kamar ranta zaifita,

“Sopy kiyi shiru banason muwadda kenake so,kice zabina,Sopy kice rayuwata kukanki yana
kona min rai”

“Dee shikenan zamurabu ko,kadena sona,nashiga uku”

“Sopy yaisa,kinason inyi kuka ko kinason
Jefani cikin damuwa
Ko”

“Aa Dee”

“To kiyi shiru ai bayanzu zaai auranba
Kinji”

Nan dai yaita rarrashinta haryasamu takwantar da hankalinta.

Momy ce zaune akusa
da maigidanta tana bashi labarin auran da
Assadiq zaikara yai shiru can yanisa yace

“Yanzu hajiya Kareema
bazaki bar maganar yarinyar nan ba ko”?

“Aa Alhj nima bayadda
banyi da assadiq yabar maganar auran nanba yaki”

“Balaifi zamuyi maganar da shi dudu du yaushe yai auran”

“Kaima kafada Alhj to yayan yanzune insukaso abu to saifa sunyi hankalinsu zai kwanta”

“Allah yashirya”

“Ameen”

Shigowar faruq ce takatsemusu hirar da sallama yashiga suka
Amsa masa karasawa
yayi gaban dady yamika masa hannu,

“Dady barka da dare”

“Yauwa umarul faruq,dafatan kanacigaba da shirin tafiya”?

“Eh dady namagama
Shirina kawai inajiran
lokacine,to amma dady duk bayan shekara daya zandinga zuwa ganinku”

Sai yanxu momy tasa baki,”Aa kabari kagama gabadaya kazo”

“Momy dagaske dai ashe bakyasona,dady
Kaji abinda momyna
tafada”

Dariya sukayi saboda yadda yayi maganar

“Faruq tanasonka mana”

“Ka kyaleshi Alhj ai shiyasan laifin dayakemin”

Nan dai sukacigaba da hirarsu karshe yai musu sallama yasakko jalila yatarar zaune tasa littafi agaba tazuba uban tagumi yadubeta yace,

“Alhudada sarkin karatu lpy dai ko”?

Glass din fuskarta ta cire tagoge hawayan fuskarta tace,

“Yaya faruq dan Allah karakani gidan yaya assadiq indada bashi hakuri,wallahi kunyarsa nakeji”

“Jalila kenan sanda kikaimusu sanadin rasa babynsu ni narakaki,bansan kinjeba danhaka ke kadai zaki yanzunmma”

Yanagama fada yai gaba,yabarta anan

°°°°°°°°°°°°°°
Yau ne ranar da faruq zaitafi Dubai kowa yashirya dan rakiya yashiga yiwa Safiyya sallama ya tarar daita a kitchen tana karasa masa danbun kaza tagama tajuyemasa tahada masa da kilishi
tamika masa kinkarba yayi yace,

“Cab bazakirakaniba”

“Mezaihanani raka karamin maigida,yanxu zanje inshirya”

“Yauwa,ai gwanda aunty dan Allah kicigaba da hakuri da yarannan watarana zasu dena”

“Haba faruq badamuwa nagode da kokarinka gareni,Allah yabar zumunci yakaika lpy,yabada abinda akatafi nema”

“Ameen aunty nagode”

Yasakai yafita,daki takoma tatar da assadiq dukunkune a bargo karasawa tayi tayaye bargon tafara magana,

“Dee katashi mushrya
faruq zaitafi”

Wani irin hucine yafito
daga bargon,agigice tataba jikinsa,taji zafi

“Dee meyasameka,meke damunka”?

“Sopy rufeni sanyi nakeji kaina kamar zaifado”

Kuka tasa tarungumeshi ajikinta
tarasa mezatayimasa,bude idonsa yayi dayakada yai jazur yace

“Sopy kukanki baabinda zaikaramin sai ciwo dan Allah kiyi shiru,wash yafada yanadafe kansa,

Karar wayarsa ne yakatseshi safiyya ce
tadauka faruq ne tadauka tafara magana kuka yakwacemata,

“Faruq assadiq bashi da lpy”

Betambayi meyasameshiba yakaraso gidan abakin kofa yatsaya Safiyya tasa hijjabi tace yashigo shiga yayi yakarasa gabansa yai
Masa sannu yayi yayi dashi sutafi asibiti yaki
Yace karyafadawa su momy yana kwance sukai sallama yatafi😰
Safiyya tarakashi bakin gate tadawo wayarta ta dauka tashiga neman layin yayanta Dr almustapha bugu biyu
yadauka,tana kuka tafara magana,

“Yaya assadiq bashi da lpy kataimaka kazo kadubashi kar yamutu”

“Meyasameshi,kedaga
Ciwo sai mutuwa ko,ganinan”

Dakin takoma tajiko tawul tazo taciremasa
Jallabiyar jikinsa tashiga dannamasa jikinsa tana hawaye ahantkali yabude idonsa yazubamata ido kai yagirgizamata alamar tadena yakakama hannunta ya sumbata,

Dady ne yatambayi faruq ina assadiq, yakefadamasa bashi da lpy,tafiya sukayi basu dawoba sai da jirginsu yatashi✈

Assadiq ne kwance a cinyar Safiyya tanata shafa sumar kansa yaruntsi idonsa wayarta tai ringing tandagawa taga yayantane zamekan assadiq tayi tadora akan filo,taje tashigo dashi sanye yake cikin kananun kaya masu tsananin kyau idonsa sanye da farin glass,duk inda akeneman dan gayun namiji akasami almustapha angama kallonta yayi yace,

“Ina assadiq din safiyya,ke badama mutum yayi ciwo saikice mutuwa zaiyi ko”

Dariya tayi tace yaxauna tashiga tatarar dashi azaune yadafe kai takarasa tarike hannunnasa tace

“Dee sannu kataso ga yaya almustapha yazo dubaka”

“Sopy bazan iya tashiba kaina kamar yatsage,kice yashigo”

Tashi tayi taje tace yashigo shiga yayi yaimasa sannu yafara dubashi atake yagano malaria ce dakuma damuwa yarubuta masa magani yaimasa allurar bacci yana shirin tafiyane sai gasu jalila sundawo sukabiyo duba assadiq

Tunda jalila taganshi tadada gigicewa ido tazubamasa harsai da yajiyo yakallesu yace

“Yanmata sannunku ,ya maijiki”

Suka amsa da yauwa jalila ce ta dora da

“Mai jiki aikai zamutambaya Dr”

“Hakane”

“Eh mana”

Yaimusu sallama yatafi nanfa dadi Yakama jalila,su afifa kuwa haushi tabasu,suka shiga suka duba yayannasu yanata bacci sukafito sulaimata sallama sukatafi tayi tayi su zauna sukaki gurin mijinta takoma tazuba masa ido yanata bacci tashige jikinsa ta kwanta tare da sakarmasa kiss a lebansa.

Su farhana kuwa sauna zuwa gida momy tace ya suka dawo da wuri,afifa tace

“Munce zamu zauna shine tace mutafi kar mu dami mijinta”

Itawa din”?

“Momy matarsa mana”.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[4:31PM,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_*KANNAN MIJINA*_
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Dedicated 2 my lovely family_*Alhj uba gawo* 😍 _U are in my mind brothers & sisters_💔

 

 

*39*

 

~~~ Kai nake saurare
Sadauki”gabansa ne yashiga faduwa yayinda kalaman momynsa yashiga yawo a kwakwalwarsa,
Ahankali yabude baki
Yace,

“Eh dady ni nakesonta”

“To amma sadauki yaushe kayi auran,to shikenan dai ba laifi
zamuje neman auranta

“To dady nagode Allah yaja kwana”

“Ameen sadauki,Allah Yakima albarka,ka gaidamin da yartawa,
Ka rarrasheta kaji ko”

“To dady nagode”

Yaimasa sallama yasakko yana sauka yahadu da momy kallonsa tayi tace,

“Ya kukayi da dadyn naku”

Nan yabata labarin yadda sukayi murmushi tayi tasa masa albarka yaimata
Sallama yatafi,su farhana najin yadda sukayi suka hau ihun murna,waya sukaiwa muwadda sukaimata albishir,murna tayi tare da kulla aniyarsu ita da mahaifiyarta.

Assadiq yana fita gidan yayarsa ya nufa waya yaiwa safiyya kartaji shiru yaje gidan yaya hannatu,taamsa da agaidata,

Yanazuwa yatarar daita a parlor yaranta tanata wasa sunaganinsa suka taso aguje
“Uncle A oyoyo”

Rungumesu yayi yakarasa gurin yayartasa yagaidata,

“Assadiq lpyr ka meke damunka”?

Shiru yayi idonsa yakada yai jaa mai aikinta takira tazo taja yaran zuwa dakinsu,

Tamaida kallonta gareshi tace,

“Assadiq gayamin damuwarka”

“Yaya,momyce”

Sai kuma yaishiru,dakyar dai yaiyabata labarin abinda yafaru,tai shiru can tanisa tace

“Baabinda zance maka assadiq sai dai inbaka hakuri kayiwa momy biyayya assadiq nayi iya yina infahimtar da momy amma taki fahimtata”

“Yaya yazanyi da safiyya,mexance mata”?

“Karka damu zatafahimceka kaji amma karka fadamata yanxu”

Yaamsa da to,yaimata
Sallama yatafi,

Safiyyace zaune tanata jiran assadiq bedawo ba,sai ga afifa
tashigo, da ledar rake
Ahanunta,tagaida Safiyya tasami guri tazauna tadau remote tacanja tashar data tarar tana kalla,batacemata kalaba tadakko rakenta,tafara sha takalli safiyya tace,

“Aunt Safiyya ga rake ”

“Aa nagode afifa,amma Dan Allah karki bata gurin”

“Kinjiki sai kace karamar yarinya”

Taja bakinta tai shiru tacigaba da kallonta
Wayartace tahau ringing tashiga daki tadauka,yayarta ce amina,takefadamata yaya Rukayya ta haihu taita murna,takira yayartasu taimata murna tafadamata zata zo da safe,sukai sallama tafito mezata gani afifa tabatamata parlor da bawan rake,tai tafiyarta gurin tazubawa I do tadakko tsintsiya kenan assadiq yashigo,gurin yakalla yace,

“Sopy ya haka,waye yashamana rake a parlor”

“Dee afiface”

Tsintsiyar yakarba a hannunta yashare gurin yagama yashiga toilet yai wanka gaba daya sopynsa tausayi takebashi,suka fito parlor sukaci abinci tafadamasa haihuwar yayarta,yaimurna,yashafi cikinta,yace

“Saura ke,Sopy”

“Dee,tsoro nakeji”

“Sopy yau zanbaki baby kishirya”

“Deee wlh banso”

Washegari suka shirya zasu je gidan yaya rukayya biyawa sukayi gidansu assadiq zasu gaida momy suka shiga bakowa a parlor
Yace Safiyya tazauna yakira momy zama tayi bedade da shigaba farhana tafito daga kitchen da cup din zobo a hannunta tana zuwa dai dai gaban Safiyya cup din yasubuce yazube a jikinta yabata mata kayanta,hakan yayi dai dai da fitowar assadiq.

 

Ayi hakuri da dan wannan👌🏻

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[8:6Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER’S FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*40*

 

~~~ Yana karasawa yadauke farhana da mari,zaikaramata momy tadaka masa tsawa,

“Assadiq kana haukane zakasa min yarinya agaba kana marinta,akan wane dalili”?

“Momy kidubafa kiga abinda taiwa sopy”

“To zataimata da gangan ne,karka kuma dokar min yaya zakazama faruq ko”

Safiyya tana zaune tarasa ma mezatace
tagaida momy taamsa
Adakile,assadiq ne yadubeta yace tataso sutafi,farhana kuwa tana jikin momy tana guraheken kuka,afifa ce tafito daga daki tadubi momy tace,

“Momy meyasami ya farhana”

“Wai saboda tazuba wa matarsa lemo ajiki
shine yamareta”

“Cab,yi shirunki yaya farhana Allah sai na rama miki”

Momy tanajinsu batai kokarin hanasuba,su assadiq suna fita kai tsaye gida suka koma
yacirewa Safiyya kayan da farhana tabatamata,yahadamata ruwan dumi tashiga tayo wanka tana cikin wankan kuka ya kwace mata,shash shekar kukanta assadiq yaji ya tura kofar toilet din,azaune yasameta acikin barb tahada kai da gwiwa karasawa yayi gabanta yadago da kanta idonsa yazuba mata masu narkar mata da zuciya
Ahankali yakira sunanta,

“Sweet sopy,kuka fa?,pls kiyi hakuri kiyi shiru,nasan baa kyauta mikiba,amma kibarni da ita sai ranta yabaci,kitaimakamin inyiwa momy biyayya”

“Dee,kannanka basa sona,menayi musu?”

Dee nagaji bazan iyaba pls kamai dani gurin ummina”

“Sopy yazaki fadi haka
Kina tunanin zaniya rabuwa da kene”?,karki kuma fada”

Zata kuma magana kenan ya toshe bakinta danasa,assadiq kenan yasan salon mantar da matarsa damuwa,dakansa yaimata wankan suka fito yabude wardrobe dinta yadakko mata atamfa super orange da adon fulawowi yellow,dinkin have gawon,da zani,tashirya tsaf,tayi kyau hartafi shigarta ta farko,shima
Yadakko yadi light orange yasa mai tsada kana iya hango farar vest dinsa,kallonta yayi ya sumbaci goshinta yace,

“Sweet sopy kinyi kyau”

“Kaima kayi kyau Dee”

Sukagama shirunsu suka fito,aharabar gidan suka tsaya sukasha pics🤳🏻

Sukagama suka shiga mota suka tafi,tunda suka hau titi yake dada rarrashinta a daidai wani babban kanti suka tsaya anrubuta
Baby dream,dagowa tayi takalleshi,tace

“Dee yahaka mekuma zamuyi anan?

“Eh,zanfara tarin kayan baby ne”

Dariya tayi sukafito suka shiga ciki,kayan baby assadiq yashiga diba,fal sopy tana kallonsa,yagama yabiya kudin suka fito sukatafi,ido taxuba masa yayi murmushi tare da lakucemata hanci yace,

“Yade,ku mukoma gidane”?

“Dee muyi me a gida kuma”

“Aa nasani ko dankinji nace zanfara tarin kayan baby,kice mukoma kozamu samu yau”

“Lala,Dee,sharri ko,to aini banaso finkarfina kawai kakeyi”

“Kedai kigode Allah kinsami jarumin miji”

Dariya sukayi ahaka suka karasa gidan rukayya,tashiga da murnarta nan fa Suhyla ta rungumeta tana murnar ganinta

“Matsa suly ni baby zan dauka”

Kuka tasa wai aunty Safiyya bata Santa,tajata jikinta tana rarrashinta,rukayya ce tadubeta tace

“Safy ina assadiq din”?

“La,yana waje yaya”

“Dan hauka kikabarshi a waje,kije kishigo da shi”

Tashi tayi taje tasameshi a mota yana waya da faruq tajira yagama tace

“Dee afuwan nabarka ko”?

“Bakomai sopy,ai ina nan ina kallon yanmata”

Duka takaimasa ya goce,yarike hannun aikuwa tacijeshi,yasaki
Yar kara,gaba daya janbakinta yagogu a hannunsa,

“Dee kaga ko,kasa nagoge janbakina,Allah sai kabiyani”

“To badanni akasaba,to na goge abina”

Suka gama shiriritarsu
Suka jero gwanin shaawa,yagaida da yaya rukayya tare dayimata barka,Suhyla takarasa gabansa tace

“Uncle A kaga babynmmu

“Nagani Suhyla,ai dashi zamu tafi”

“Aa uncle A kuma kusiyo naku”

Akai dariya yamike zai tafi yabawa maijego 10k
Yabawa Safiyya kayan baby tabata,yaimusu sallama yatafi,
Safiyya tabawa yayarta rashin kirkin da *kannan mijinta*sukemata tadada bata hakuri tare da kwantar mata da hankali,

Abangaran muwadda kuwa shiri take tayi dan zuwa gurin assadiq taci wasu kananun kaya tayafa yalolan mayafi tafito tadau motarta tafita wayarta tadauka tashiga Neman Layin assadiq sai data kusa tsinkewa sannan yadauka,shiru yayi tafara magana,

“Sweery kana gida”

“Kamar ya ina gida wace irin tambaya kenan”

“Inason ganinka ne”

“Ina office”

“OK

Bekawo zata iya zuwa office dinsuba kawai sai jin bugu yayi yayi tunanin Achida ne,kansa a dunkufe,yace a shigo,har yafara magana,abokina yaakayine,shiru yaji anyi yadago da kansa,
da mamaki yaga muwadda tsaye tazuba masa ido dakaraji yafara magana

“Muwadda baki da hankaline meyakawoki office dina”

“Sweery kayi hakuri san ganinka nake,ko kasan jiya. baniya yin bacciba”

“Bansaniba kuma banason insani,so that get out 4rm office”

“Sweery
Kanta takarasa yabuga tebirinsa da karfi yanunamata hanyar fita,yanayin fuskarsa ta kalla taji tsoro tafita,kaitsaye gidansu assadiq tawuce,tanazuwa tafadawa momy abinda assadiq yaimata,nan momy tashiga aikin fada yayanta tanata zugata

Yau ake sunan yayar safyya rukayya tuncikin dare safiyya takefama daciwon kai taki fadawa assadiq ahaka tashirya yakaita daman taaikawa su farhana suzo suje,sukace bazasuba .assadiq yakula da yanayinta,

“Sweet sopy are u ok”

“Yap,Dee”

“OK ki kularmin da kanki”

Taamsa tashige yaja motarsa yatafi anfara shagalin suna ciwon ciki ya matsawa sopy,dakin Rukayya tashige ta kwanta nan da nan bacci yadauketa

Jalila ce tamatsawa kannanta sai sunje sunan yayar Safiyya da kyar suka yarda sukaje sanda sukaje Safiyya tanata bacci zaatasheta jalila tace akyaleta yayar Safiyya amina takawo musu kayan suna taimusu karbar mutunci nan jalia take tambayarta Dr almustapha,tace yana nan.sukaci suka koshi dazasu tafi aka basu kayan daaka raba sukatafi

Suna zuwa gida suka tarar da assadiq a gidan afifa ce take tambayar sa yabasuga aunt safiyyaba kallonta yai da mamaki yashiga kiran
Layin Safiyya tanata ringing bata dagaba.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
*[9:49AM,2017]*

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTE’S FORUM💦💦💦*

 

*💦T<W>F💦*

 

 

 

**_KANNAN MIJINA**_
👩‍👩‍👧

 

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*41*

 

 

~~~Yanke shawara yayi kawae ya miqe cikin fushi ya nufi gidan ruqayya yana isa kofar gidan ya qara gwada wayarta yanzu ma dai kamar dazu tana ta ringing amma bata daga ba wasu yara yaga sun fito daga gidan sunan ya kira su yace Ku shiga ciki kuce safiyya tazo inji mijinta

 

“Bayan fitar Assadiq Jalila ta dubi afifa cikin fushi tace haba Afifa ya zakiyi haka meyasa zaki cewa ya Assadiq bamu ga Aunty safiyya yanzu kin hada su fada kenan kina ganin yadda ya fita a zuciye”

 

Afifa tayi dariya tace baza ki gane bah ya jalila ai dama fadan nakeso na hada su saboda na dau alwashin sai na ramawa ya farhana Marin da ya Assadiq yayi mata akan wannan shegiyar Matar tasa”

Tabe baki kawai farhana tayi tace haka nake so sis”

 

Safiyya ce ta fito fuskarta a kumbure alamar bacci yanayin da taga Assadiq neh ya bata tsoro fuskar nan tasa a hade idanuwansa sun kada sunyi ja ta qaraso gabansa jikinta a sanyaye tace Dee kayi haquri nasan yunwa ce ta koro ka ko naga duk ka canja”

Banza yayi mata yace malama shiga ki hado kayanki mu tafi gida

Shagwa6e fuska tayi tace kai Dee don Allah baa gama sunan ba fah

 

“Cikin harzuqa yayi magana yace zaki dakko ko inyi tafiya ta”

A sanyaye ta juya ta shiga gidan yayar tata zuciyarta cike da saqe saqe game da chanjin da ta gani gun Assadiq, dakin yayar tata ta nufa ta shaida mata yadda suka yi da mijin nata, cikin hikima mai jego ta taushe ta sannan ta hada mata abincin sunan suka fito,

Hawaye neh ya tahowa safiyya tace to yanzu yaya mutane zasuyi ta tambayar ena nake, dariya ruqayya tayi tace sai ince kun tafi cin amarci,dariya suka sa duka sukayi sallama ta fito suka shiga motar ya tashe ta da gudu a zuciye

 

Basu tsaya ko ena sai a gida yana yin parking,yayi zamansa harda kwantar da kujera,safiyya da taga bashida niyyar ce mata qala kuma bashida niyyar fita tasa hannu da niyyar bude murfin motar ta,ta kwashi kulolin abincinta tayi cikin gida dama kanshi air freshener motarsa na barazanar sata amai Allah Allah take ta fita taci alala da dambun suna,

 

Tana shiga palour ta baje ta cika cikinta da dambun shinkafa da alala tasha kunun aya ta qoshi ta tashi tayi ciki ta tsala wankanta ta fito sanye da doguwar Riga iya gwiwa pink sai gashinta data saka ta fito palour da niyyar shan ruwa, nan taga gogan nata yana cika da batsewa ko kallon inda yake bata yi ba don ta yanke shawarar qin shiga harkarsa har sai ya sakko don kansa don bata ga dalilin dazai sa ya tsiri fushi da ita, inama laifin ya gaya mata kuskurenta ta gyara ta kuma nemi yafiyarsa amma tunda ta nan ya 6illo ita ma ta iya, ruwan ta dauka tayi hanyar dakinta binta yayi da kallo ya girgiza ka tayi shigewarta tana karkada jiki

Yana ta zaune a parlour har ya gaji ga yunwa data ke kwarzabarsa gani yayi ba sarki sai Allah ya sakko ya cinye ragowar dambun da alalan data rage yana gamawa wayarsa ta fara ruri yana dubuwa yaga muwadda ke kiran nasa

 

Dagawa yayi fuskar sa qunshe da murmushin mugunta a zuciyarsa ya raya ya samu hanyar da zai rama wulaqanci da sopy tayi masa

 

Daga can 6angaren muwadda tace “hello sweery

 

Yace naam baby ya kike yasu mama ya qarasa zancen yana qarasawa cikin dakin safiyya ya zauna gefen gado suka cigaba da hirar su

Wani qululun baqin ciki neh ya tokarewa safiyya a qirji jin yadda Sadeeq ke wani maqale murya eta kuma tana shagwa6ewa

Tashi tayi ta fice ta buga masa qofa

Qunshe dariyarsa yayi sukayi sallama da muwadda wadda farin ciki ya cikata saboda yau daya Assadiq ya bata hankalinsa

Zama tayi a parlour ta kunna karatun alqurani cikin qira,ar sudais tana ji zuciyarta na mata sanyi

Shiryawa yayi cikin kananun kaya yayi kyau sosai ya dauki mukullin motarsa ya fito ko kallonta baiyi bah yayi ficewarsa

Yana fita kuka ya kubce mata taci kukanta ta qoshi

~~Bangaren Momy kuwa yanke shawara tayi ta dunqule wasu kudadenta ta bawa dady tace gashi nan Assadiq ya kawo yace akai masa kudin aure gidan su muwadda

Dady ya kar6a ya jinjina abin a ransa amma yace Allah ya bada alheri,yace to zanyiwa su Yaya da Alhaji salihi sai suje sukai

A 6angaren Assadiq kuwa bai dawo ba sai taran dare

Safiyya tun tana jiransa har ta gaji tayi bacci bata ga dawowar sa ba

 

_Tirkashi fans yau kunji rigimar data danno tsakanin sopy da Assadiq🤔nidai naseeba nace fadan nasu ma na love neh_

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[8:55Pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

“`Ina gaisheku masoyana ina kaunarku kmr yadda kuke kaunar littafina mai taken “`

*kannan mijina*

“`karku manta da bazarku nake kwaso shoki“`🤦🏻‍♀💃🏻

 

 

_Wannan shafin nakune_*Talented writters forum*💦

_inban mantaba hadin kanmmu shine alfaharinmmu_💙

 

 

 

*42*

 

~~~Assadiq bedawo ba,sai after 10 lokacin
safiyya tadade da yin bacci dakin yanufa,safiyya ya gani tacire rigar daxu tasanya have vest da da dan karamin skin tied,tayi rub da ciki gashinta yabazu akan filo,tayi masa kyau gashi tayi kiba gwanin shaawa,wata irin soyayyar tace tafizgeshi,tare da shaawarta,ahankali ya karasa gabanta yaxubamata kyawawan idonsa, a hankali,yafara shafa gashin kanta mai taushi da baki,yashiga
Shafa mata jiki ,acikin
Bacci taji kamar ana shafa mata jiki mirginawa tayi tadada
rungumo shi,sakamakon kamshin turaren da ya bugi hancinta,mamaki ne ,yacika assadiq
Yaushe Safiyya tai kiba haka mararta yashafa yaji tadan daga,kissing dinta ya farayi a hankali ta bude ido ganinta tayi
ajikin assadiq tahade rai tace

“Ya haka mekuma nayi
maka,zaka zo kana tabani”

takarashe maganar tana kokarin tashi tare da turo masa baki,

Shi sai yagama kamar da gangan tai wannan shigar riko kugunta yayi,takuma fado jikinsa,kana yace,

“Sopy mijinki ne fa,guduna kike”

“Mezanmaka ni nazaci kana da wata matar,to
Kaje nabar mata kai,haka akeyi ni banyi fushi dakaiba sai kaine zakayi,menayi maka”

Tafada tana hawaye tare da shigewa kirjinsa turaransa ne yaimata dadi,
dariya ce taso kubce masa sopynsa tana tsiwa kuma sai dada shigewa jikinsa take,

Fuskarta yadago yaxuba mata kyawa wan idonsa yace,

“Sopy assadiq kikewa tsiwa, dan kinga nadamu dake,shine zaki tsiro min da halin da banakiba,har zanzo karbar hakkina kiyi min haka kina son in karbi hakkina ta karfi kenan to zaniya yahau kiciniyar danneta kuka tasamasa tace

“Dee dan Allah katsaya kaimin bayanin laifin danaimaka da har kake kokarin yimin fyade”

“Au hakama zakice ko
to ni bazantaba yimiki fyadeba Allah yatsreni kije kirike kayanki banaso”

Yafada yana kokarin janyeta daga cikinsa

Fita yayi yakoma dakinsa ya kwanta ransa naimasa suya,

Kuka safiyya take wiwi,ahaka bacci barawo yadauketa

Assadiq kuwa juyi kawai yake yakasa bacci tunanin sopynsa yacikamasa zuciya,ga
Shi yana tsananin bukatarta a wannan lokacin,tunani yayi ko de a gidan suna ne akasami wata mara tsoran Allah ta zuga masa mata ahaka bacci yadaukeshi,

Washegari da wuri yashrya yafita,kai tsaye gidansu ya wuce,a dining area yasami momy da kannan sa suna break fast,karasawa yayi gabanta yagaidata,
Kannansa ma suka gaisheshi,yaja kujera ya zauna momy ce tadubeshi tace,

“Aa assadiq ya haka zaka baro gidanka kazo kacimana abinci,matarka fa”

Shiru yayi kana yace

“Batajin dadine shiyasa”

“Allah yabata lpy”

Yaamsa da ameen yadau cup ya. hada tea afifa taxuba masa farfesun hanta da koda sai wainar kwai,

Yaja gabansa zaifara ci kenan momy tace

“Mabawa dadynku kudi akai maka gidansu muwadda sai kafadi wata nawa zaasa”

A raxane yadire cup din da yadauka yakai bakinsa,har yana kwarewa,yace

“Momy da wuri haka kuma ai bekamata kibada kudinkiba”

“To da kake cewa da wuri kai da sai yaushe kenan koko kafisan kaita zama da matarka dataki ta haihu,wancan cikin tace farhana ce to yanxu meyahanata haihuwa,dan haka kafadi lokacin dazaai bikin”

“Shikenan momy ai komai yana hannunki,sai yadda kikace”

Yafada yana kokarin tashi yafita,murmushin jin dadi tayi tace to madallah,dariyar mugunta farhana tayi suka tafa da afifa sannan tace

“Gaskiya momy yanxu xamuyi biki”

Farhana kuwa cewa tayi ,”ai ni momy gidanma zankoma”

“Nima burina kenan ku koma can da zama aware muku daki”

Ihun murna suka sa,jalila kuwa shiru taimusu saboda ita yanxu batason abinda akewa safiyya,sai dai miskilancinta yahana taja safiyyan a jikinta.

Safiyya kuwa tunda tai sallar asuba dakyar takoma gado ta kwanta,zazzabi mai xafine yarufeta,ga yunwa tanata kiran layin assadiq unforwad taki shiga,layin farhana takira sai da takusa tsinkewa tadaga

“Hello”

Dakyar Safiyya taamsa wayar tace tataimaka tazo dakyar taamsa can saigata tazo lokacin bacci yafara daukar Safiyya taxo saitin kanta tafara magana da karfi adan
Firgice tafarka tace

“Yauwa kanwata dan Allah taliya xaidafamin jollof da manja da attaruhu wlh banajin dadi”

“Allah yasawake amma dazakina kiranmmu da *kannan mijinki*kamar xaifi,

Daakwai komai a kitchen din”

“Da akwai”

Fita tayi tashiga kitchen din tadoramata girkin maimakon. Manja da attaruhu,sai tasamata mankuli da tattasai da kifi,tai kaca kaca da kitchen din ta hautsina parlorn har dasu ledar maggi tagama takai mata,lokacin xaxxabi yaci karfinta tajuya tai tafiyarta sai da tadanji dama dama sannan tatashi da kyar tabude abincin sabanin abinda tafadamata tagani ga karnin kifi ai fa nan tashiga amai abin tausayi

Assadiq yana dawowa yaga parlor kaca kaca,ga kitchen a bude tukunya a bakin kofa

Da bacin rai yadoshi dakin Sopy.

[1:03,PM2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Nagode da kulawar ku gareni fans nasami sauki_*Allah yakaramana lpy Ameen*👏🏻

 

 

_Dedicated 2 my family_*Alhj uba takarda gawo*💘

 

 

*43*

 

~~Tura kofar yayi ransa abace fuskarsa ba walwala,yashigadakin
Mezai gani safiyya ce kwance gefe kuma amai tayi duk tabata dakin,dahanxari yakarasa gabanta yana jijigata,

“Sopy sopy meke damunki”

“Dee mutuwa zanyi,daure min cikina,pls”

hankalinsa ne yatashi yarasa ma mexai fara
Bargon data rufa dashi ya yaye,abin mamaki bakomai jikinta,jiyayi
Wani abu yatsargamasa Dakar
ta yayi,yakaita toilet yahada ruwa mai dumi yaimata wanka yagasa mata jikinta yabarta cikin barb yafito yafara gyara dakin yakwashe gurin aman,ya gyara gadon tare da canja bed sheet din,yafesa air freeshner,sannan yakoma,ya dakkota,akan gado ya direta,ya bude wardrobe yadakko mata yar fingilar riga iya gwiwa lemon green
yasamata yadaure mata gashinta,da farin ribbon, yadakko turare,xaifesa mata,takarba sanshanawa tayi tai sauri ta mikamasa tace,

“Dee bawannan xakasaminba”

Karba yayi batare da yaimata maganaba dayan yadakko,yamika
mata tasanshana ta daga masa kai alamar ya samata,karba yayi
yasamata,yaja hannunta,yakaita parlor, yazaunar da ita kan kujera yakunna mata kallo,kitchen ya koma,yadakko mata tufa da abarba yasako a plate yakawo mata agabanta yadire mata,yakoma kitchen
din yafara gyarawa,kallon kofar kitchen din tayi,tana mamakin halin assadiq dama haka yake da fushi,tufa tadauka tafara ci,
Sai da yagyara kitchen
din tsaf ya wanke kwanikan tambayar kansa yake wa yayai Girki a kitchen bashi da wannan amsar dan bazai kula Safiyya ba,

Yana gamawa yadawo
Parlor,ya gyara tsaf kallonta yayi yaga tana lumshe ido,taimasa kyau kamar baby,yakoma bedroom yashiga toilet yai wanka,yashirya cikin riga arm lace green,da farin 3quater yafesa turaran da Safiyya takeso,yafito parlorn ganinta yayi tayi bacci da tufa ahannunta,girgiza kai yayi,yakarasa gurinta ya zare tufar,yasami kusa daita yazauna,yadora kanta
Acinyarsa,yashiga yimusu pics tanata baccin,yagama yaxubawa kijinta ido,yana bukatar safiyya amma yadau alwashin hadiye shaawarsa,kissing dinta yayi ya maida hankalinsa ga tv ahaka shima bacci yaigaba da shi.

 

Yau su Alhj salihi da yayan Alhj Muhammad mai nasara suka kai kudin auran muwadda murna gurin momy da maman muwadda,
abangaran assadiq kwa besan ankaiba,

Yau tunsafe ummin Safiyya take tunanin yartata,cewa tayi da yayarta Amina taje tagano mata lpyr ta shiryawa tayi tazo akulle taga gidan tanata bugu a rufe,takira wayarta no answer shawara data shiga gidansu assadiq ta tambaya,karasawa tayi tashiga gidan mai gadin ta tambaya masu gidan suna nan
Yaamsa da eh,

Shiga tayi farhana ta tarar a parlor suka gaisa kamar bata ganetaba,ta tambayar ta tayi su safiyya sauna nan,
Shiru tai can tacemata

“Basanan suntafi gidan su kishiyar safiyya,yau mafa aka kaimasa,kudin auransa.

Shiru Amina tayi bata fahimci zancan datakemataba,tashi tayi taimata sallama tatafi.

 

 

 

 

 

*NASEEBA. GAWO*✍🏻
[6:00PM,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Inabawa masoyana hakuri sakamakon kadan da page 43 yayi hakan yafaru ne sakamakon wata yar Marsala_ *Nagode*👌🏻

 

 

*44*

 

~~safiyya ce tabude idonta taganta akan cinyar assadiq daga kanta tayi ta zuba masa ido,ahankali tashafi sajen fuskarsa
Cikin bacci yaji anashafa masa fuska idinsa yabude,ya kalleta murmushi taimasa,yadauke kansa gefe,yajanyeta daga jikinsa,yana kokarin tashi wayarsa tai ringing momy yagani ajikin screen dagawa yayi

Momyna ina yini”

“Lpy lau kazo inason ganinka”

“To gani nan momy”

Janyeta yayi yatashi,ahankali ta kira sunansa

“Dee,
Jiyowa yayi yazuba
Mata kyawawan idon
sa,idonta ne yakawo
Kwallah yawuce yatafi

Yana fita suka hadu da
Yaya amina suka gaisa,take cemasa tazo basa nan yace suna ciki bainda sukaje tawuce shima yakarasa gida .

Sanda yashiga momy
tana kitchen tanaiwa dady tuwon alkama gaisheta yayi yaja kujerar dining din kitchen yazauna yace

Momy sannu da aiki,
tuwon akemana ne”?

“yauwa assadiq zakaci
Kenan”?

“Zamuci momy Damian sopy bazata iya yimana girkiba”

“Saboda me”?

“Momy sopy batajin dadi kwana 2”

“Allah yasawake sai kuje asibiti ai,daman kiranka nayi infadi maka ankai kudin auran nan,ansa rana wata 7”

Shiru yayi yarasa mexaice karshe kitchen din yabari,yahau saman
dady.yana shiga yatsuguna gaban dady
yagaisheshi,yamika masa furar datake gabansa

“Sadauki lpy dai ko,ko da matsala ne”?

“Aa dady bakomai,kawai dai yanayin rayuwa ne sai
ahankali”

“Sadauki ita rayuwa taka ke gani hakuri akeyi kaji dan haka dukkan abinda yatasoma kanutsu ka fuskanceshi kaji ko”?

“To dady nagode Allah yakara girma”

Ameen sadauki,ya matar taka”?

“Lpyt kalau dady”

“Dakar mata furar nan ka kaimata kayi katafi

Tashi yayi yaimasa sallama yasauka.

 

Amina nashiga tatarar da safiyya nata hawaye da sauri takarasa gabanta tadafa kafadarta tace,

“Safiyya meke damunki” kike kuka”?

Farhana tace bakwanan,kuma gashi
Nazo natarar kina kuka”?

Hawayen fuskarta ta goge,tadubi yayartata
tace,

Yaya Amina banajin dadi kwana 2 narasa mekemin dadi”

Takasa fadawa yayarta sirrinta domin
tasan *mijinta sirrintane*

Itama amina godiya taiwa Allah da yaruwarta batasan zancan kai kudin assadiq ba ta numfasa tace,

“Ysnxu safiyya dan baki da lpy sai kina yin
Kuka,har yanxu baki dena kukaba dan baki da lpy,bazaki girma ba
ko”

“Shikenan ya amina nadena,yasu ummi da baffa,?”

“Lpys kalau suna gaidaki”

Nan dai suka sha hirarsu tadada kwantar
Mata da hankali batabar gidanba sai data tabbatar ta saki ranta,sannan tabar gidan,

Tashi tayi takuma yin wanka sakamakon zafin da takeji, tanacikin wankan assadiq yashigo da kulolin abinci ahannunsa,yaduba bedroom bata ciki karar zubar ruwa yaji a toilet yasami gefan gado yaxauna,ya zubawa kofar toilet din ido,bejima,da zamaba tafito daga ita sai towel da dankarami akanta tana tsane gashinta,tataho da baya da baya,tana yanwake wakenta bata saniba tai karo da kafar assadiq kansa tafada,takwalla kara,

Garin yunkurin tatashi
towel din jikinta yakwance,da hanxari assadiq ya kuma janyota jikinsa,ahankali yace,

Shiiiiii
Shiru tai taruntse idonta kasa jurewa assadiq yayi da fushin da yake yashiga sarrafa safiyya,jikinsa har rawa yake batason abinda yakemata,tunowa da fadan dasukayine yasa

ta hakura tabarshi yai yadda ransa yakeso daita daga karshe takasa jurewa tasamasa kuka,rarrashinta yashi
ga,yi da kyar yasamu
tai shiru,sai da komai
yalafa sannan yakalleta tayi lamo ajikinsa,yace

“Sweet sopy kinmin laifi amma bakiiya bani hakuriba ko”

Ashagwabe tace Dee,wlh bansan laifin danai makaba”

Nan suka warware matsalolinsu suka shirya masoyan asali kenan💙

wanka sukayi suka shirya cikin kananun kaya rigunan ja anrubuta lovers da farin rubutu,sukasa bakin jeans sunyi kyau sosai,parlor suka koma sukaci tuwon da yataho musu dashi,sunaci suna tsokanar juna wayarsa
ce tahau kara safiyya ce tadaga batre da tasan wayeba,

“Muwadda ce tace bawa mijina wayar,mana

Wayar tamikamasa tacire hannuta daga cikin abincin takoma kan kujera ta kwanta.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:57PM,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

_Inaiwa daya daga cikin *talented writers forum*jaje bisa ga abinda yasameta wato_*maman fareeda*_mai littafin danmaliki mai ruwan nairori_ Allah yakara lpy sis Ameen👏🏻

 

 

 

 

*45*

~~~ Kashe wayar yayi yakoma kusa daita yashiga aikin rarrashi da kyar yashawo kanta ta sakko suka ja abincincinsu suka fara ci dakansa yakebata abincin suka ci suka koshi tadubeshi tace,

“Dee gaskiya momy taiya girki,dama xandinga samun tuwonnan kullum”

“Zanfadamata sopy sai adinga yimiki”

“Nagode Dee”

Tashi tayi zata kwashe kwanikan yadakatar daita dakansa yakwashe yakai kitchen binshi tayi da kallon kauna a haka yadawo yatarar ta zubawa kofar kitchen din ido kallonta yayi yace,

“Yade,matar assadiq ko mukoma ne”

“Dee ina”?

Dariya yayi yabata amsa da inawa”

Nibansan inawaba”

“Kinga tashi mushirya inkaiki asibiti dan atabbatar min da zargin danake,sopy yanayinki kamar mai ciki”

“Dee bawani ciki,malaria ce”

“To malaria, naji tashi mushirya muje”

Daki suka shiga sopy tadakko bakar abaya tasa,mai adon stones silver, assadiq kuwa dakayan jikinsa yafita,suka jera suka fita xuwa gurin mota,yabudemata tashiga,shima yazaga mazaunin driver yazauna,harzai tada motar tadubeshi ashagwabe tace,

“Dee,pls bari indakko furar da dady yabayar ka kawomin kaji”

“Dacan meyahanaki sha,kawai kinason batamin lokacine inmundawo kyasha”

Dauke kanta tayi bata kuma maganaba,yasa hancin motarsa,yafice
Tunda suka tafi hanya
Yakemata hira,taimasa
Shiru,can yajiyo yadubeta,yakira sunanta da wata irin murya,

“Sweet sopy meyafaru kinajina inata magana”

Shiru takuma yimasa ahankali yalalibi hannunta yahada cikinnasa ya matsa,kara tasaka tajiyo da fuskarta mezai gani hawaye take,gefan titi yasamu yai parking ya jiyo yafuskanceta yace,

“Matar assadiq kukafa,meyasameki,
Meye dalilin xubar hawayenki Sopy”

Rushewa tai da kuka,nan hankalinsa yatashi,da shashsheka tace,

“Bayan kaine kahanani dakko furata”

Dariyama abun yabashi yace shikenan dalilin kukan sopy”tissue yazaro yashiga goge mata hawayanta yace

“Karki kuma zubar da hawayanki akan wata fura,mufara zuwa insai miki,wata,shagwababbiya kawai,yafafada yana lakacemata hanci,

Shagon daake saida fura yanufa,yasiyamata roba biyar yamikamata
“Gashi ai tasha,kar a kuma yiwa assadiq kuka”

Karba tayi tana dariya
tabude,roba daya tafara sha tace,

“10q my handsome Dee”

Asibiti suka karasa kai tsaye, office din likita suka shiga,aka shiga duba safiyya atake likita yagano safiyya nadauke da ciki na 3 assadiq murna baa magana,yarubuta musu magani suka taho,tun ahanya yake tsokanarta da mai ciki, dariya kawai taimasa,

gidansu assadiq suka wuce,lokacin duk suna parlor suna kallon arewa 24,sukai sallama suka shigo,guri safiyya tasamu tazauna,tagaida momy
taamsa da sakin fuska
Sai abun yabawa Safiyya mamaki,jalila ce tagaisheta,taamsa,
tashi tayi ta kawo mata lemon kwa kwa,abun yabawa su farhana haushi ko kallon inda safiyya take basuyiba,sai itace
taimusu magana ba kunya suka amsa,assadiq ya kallesu kawai,momy ce tadubi dannata tace

“Assadiq inafatan kaje gidan su muwadda”

“Momy banjeba,amma
amma zanje”

“Yakamata kam”

Shiru safiyya tayi tarasa gane me momy take nufi amma tabarwa ranta,assadiq ne yace sopy tashi mutafi,sallama sukaiwa momy sukatafi,

***************

Haka rayuwa tacigaba datafiyarwa safiyya yanxu cikinta nada wata 7 ,yafito tadada kyau,**kannan mijinta*
*Readers kuyi hakuri da gibin daaka samu*👏🏻

_cigaban_*45*

*kannan mijinta*
basu fasa mata rashin kunya ba yanxu iskancin dasukemata kullum a gidanta suke yini subata mata gida sutafi subarta da gyaran gida batace musu kala,yanxu hakama tana kwance tagaji kwana 2 assadiq baya barinta tana isashshan bacci ga jikinta yanadada nauyi,kallon take bacci yadauketa kawai sai jin hayaniyar mutane tayi a parlorn ga karar TV daaka kure,farkawa tayi adan tsorace afiface da kawayenta su uku,binsu tayi da kallo,tanadaga kwance ga wani ciwon kai da yamatsamata,ahankali
tadubeta tace

“Haba afifa yazaku ahigo min gida kuna hayaniya wai baku kula da halin danake cikiba”

“Hmmm sannu mai gida tayaya zamukula kekuwa ga makafi,kedai har abada bazaa rabekiba to ki kwantar da hankalinki munkusa dena xuwanniki daki,amma bazaki hana mu zuwa gidan yayanmmuba”

Daya daga cikin kawayen ce mai suna
Basma tace

“To ma inbanda abinki aunt safiyya meye naki na magana nagafa gidan danuwansu ne,duk tsiya kan yasameki su yafara samu ko”?

“Ke dakata banason iskanci kinji ko,rufe min baki ke kuma a wa”?
Dalla kufitar min daga gida”

Fita sukayi afifa tagama harar ta sannan tawuce suna fita tadafe kanta takoma ta kwanta.

Suna fita kai tsaye gida afifa tanufa tacewa momy safiyya ce ta korota,takuma mareta a lokacin assadiq yana zaune momy tanaimasa bayani kan auransa da muwadda,sai yarasama mexaice yasan karya takewa matarsa amma beisa ya karyataba yanxu momy tahau shi da fada,ai kuwa nan tahau balai danme zataiwa yarta haka dan suna
*kannan mijinta* ai bekamata tanai musu hakaba,amma bakomai tacigaba lokacintane wata rana ko da kudi akace taiyi bazatayiba mai da dubanta tayi ga assadiq

“Kafadamata maganar auranka da muwadda”

“Aa”

“To sai yaushe kenan kana tsoran fadamata ne ko me,to ni xanfadamata da kaina”

“Momy pls kiyi hakuri xanfadamata kinga yanayin datake ciki baason abinda zai dagamata hankali”

“Hmmm yayi kyau assadiq, nan da sati 2 su hannatu zasu dubai hado lefe,nayi waya da faruq yafara siyan wasu kayan kan su karaso”

“Allah ya kaimu”

Yatashi yafita ransa ba dadi gidansa yanufa yatarar da safiya kwance tadafe kanta da sassarafa yakarasa gabanta yakira sunanta,

“Sopy sopy,meyasameki”

“Dee kaina ciwo yake”

Magani yadakko yabata tasha yaragemata kayan jikinta cikinta yakalla yaga yadada girma ga babyn sai motsawa yake ahankali,tanashan maganin tadan sami afuwa soyayi yafadamata auransa da muwadda amma yanafargabar abinda zaifaru. Rungumeta yayi yashiga bata hakuri akan abinda afifa taimata kuka tasamasa nan hankalinsa yadada tashi.

*kai wadannan kannan miji*🤦🏻‍♀

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[10:37Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐.

 

 

 

_Har yanzu inamaraba da masu yimin gyara gameda rubutuna ko kuma labarina burina bewuce fadakarwa ba tare da isar da sakon gyara a zamantakewarnu da yanuwanmmu_
“`zaaiya samuna ta wannan number“` ~07037732029~ “`Taku“` *Naseeba ismail uba*💐

 

 

 

 

*46*

 

 

~~~yunkurawa tayi tatashi da kyar yamike da hanzari zai riketa dakatar dashi tayi tahanyar dagamasa hannu tajanye jikinta ahankali taketakawa takoma daki ta kwanta
Kukane yaci karfinta tadau wayarta tashiga neman layin yayarta rukayya,

Biyota yayi dakin yazauna kusa daita wayar hannunta yakarba yanadubawa yaga yayarta take kira katse Kiran yayi,yaajiye wayar yakamo hannunta yahada danasa ahankali ya kira sunanta,

“Sweet sopy,yakamata kisaurareni kikuma fahimceni,wlh bani da yadda xanyi akan abinda yake faruwa kisa a ranki bawanda yaisa yashiga tsakani na dake”

Hawayen fuskarta ta goge,tace

“Dee nagaji da jin kalamanka kullum karatu daya kakemin nazaci sama kake dasu farhana,meyasa amatsayinka na babba baxaka tsawatarmusuba”

“Sopy darajar momy sukeci banason abibda xanjayo momy taifushi dani kitaimaka min wajen yimata biyayya
Pls”

“Naji but yau inason kafadan gaskiya make tsakaninka da muwadda ,Dee karkaboyemin komai koda hakan yana nufin mutuwata”

Shiru yayi yadada damke tafin hannunta cikinnasa tare da xubamasa kyawawan
Idonsa,yace

 

“Safiyya kiyi hakuri daabinda xanfadamiki amma kisani bani da hannu cikin lamarin kuma baason raina zanaikata hakanba,umarni ne na momyna”

Nan yabata labarin auransa da muwadda tundaga farko har karshe,ido yazubamata yana karantar yanayinta,
Shiru tayi tarasa ma mexatace jitayi dancikinta yahautsina yajuya kara ta kwalla tafara murkususu,hankalin assadiq yai masifar tashi,a gigice yadauketa yakaita asibiti yaya hannatu yaiwa waya yafadamata hankali atashe ta barwa mai aikinta su nabil tanufo asibitin assadiq ta tarar yanatafaman zirga zirga hankalinsa tashe,tambayarsa tayi

“Meyafaru da safiyyan daman watan haihuwar Yakama ne”

Girgiza kai kawai yayi saboda yadda hankalinsa yatashi,likitane yafito yace yabiyoshi office binsa yayi yasami kujera ya zauna likita yagama rubuce rubucansa yadago dafuskarsa mai dauke da farin glass yace,

“A gaskiya yarinyar tanada damuwa gsky damuwarta zata iya haifarmata da matsala
Yakamata abata kulawa ko dan babyn dayake cikinta”

“To shikenan doctor nagode inshaallah zaakiyaye ”
yarubuta mata magunguguna yai masa sallama yafita,

Dakin daaka kwantar da safiyya yanufa yaya hannatu ce zaune kusa daita yakarasa gaban gadon yazauna yashafi cikin jikinta tanata bacci numfashi take a hankali,yadubi yayarsa yace,

“Yaya narasa yadda zanyi da maganar aurannan banaso banason abinda zai jawowa Safiyya damuwa,ga iskancin yarannan”

“Assadiq wai meyakawo safiyya ta
shiga cikin wannan halin”

“Nan yabata labarin abinda yafaru nanta rufeshi da fada danme zaifadamata zancan auransa da muwadda,yai shiru kansa yaixafi yarasa dame xaiji,safiyya ce tamotsa tabude idonta tadorasu kan assadiq suka hada ido yasakarmata murmushi,dauke kanta
tayi takalli yaya hannutu tace ya hannatu zansha ruwa

Assadiq ne yadakko ruwan zaibata tadauke kanta,yayi yai tasha taki yaya hannatu ce takarba tabata tasha,bayan tagama sha,tace yaya dan Allah kikaini gurin ummina,bazaniya zamaba,tagama fadar haka tasa kuka,nan hankalin assadiq yatashi,

“Kiyi shiru safiyya kiyi zamanki adakinki kinji

Karkibari shaidan yashiga zuciyarki,mijinki yanatare da ke,nima kenake so ba muwaddaba”

I do safiyya tazubamata can tace yaya kiramin ita,

To zankira miki ita,kiran ummi akai bayan sungaisa da yaya hannatu takefadamata rashin
lpyyr Safiyya hankalin
Ummi yatashi,tabawa Safiyya wayar suka gaisa tace ta kwantar da hankalinta zasuzo anjima,sukai sallama

Ran yaya hannatu ne yabaci tace bari taje gidan,safiyyace tariketa tace

“Dan Allah yaya karki tafi kibarni”

“Safiyya ga mijinki zai zauna dake yanzu zandawo”

Shiru tayi taxame jikinta takwanta tare da runtse idonta batason ganin assadiq a halin yanxu.

Kai tsaye yaya hannatu gidansu tawuce tanazuwa tafara zazagawa kannanta balai momy ce tafito daga kitchen tadubi hannatu tace,

“To uwar fada daga Ina
Kike,daga xuwa sai ki hau yara da fada shiyasa fa basazuwa gidanki wlh”

“Momy bakisan Safiyya tana asibitiba
Kuma ciwonta nada nasaba da yaniskan yarannan.

Ran momy ne yabaci.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

 

K
[7:49Pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

_Dedicated 2 my lovely mother_😘

*May Allah protect my mother with your shade on the day of judgement and keep her far far away from jahannam* “`Ameen“`👏🏻

 

“`Ina yinku“`talented writters 💦 “`tabbas hadinkanmmu shine alfaharinmmu“`🤝

 

 

*47*

 

 

~~cikin bacin rai momy tadubi ya hannatu tace,

“Hannatu ba ruwanki da sabgar gidan assadiq akan wane dalili zakizo kisamin yara agaba da masifar fada,to ki sauraramin kinji ko”

“Haba momy yanxu abinda kikewa assadiq kinmasa adalci kenan,duk cikinmmu babu mai miki biyayyar dayake miki,amma kina kallon marasa mutuncin yarannan sunaiwa matarsa iskanci kina kallonsu momy,sumafa gidan wani xasu wataran”

“To uwata kingama yanxu hannatu zaliya iya fufita matar assadiq akan yanuwanki ko,to ba laifi,to kibude kunnanki da kyau kisaurareni dakyau kicireni hannunki a gidan assadiq nazaci dake da assadiq duk a karkashin ikona kuke,to ba ruwanki,da abinda yake tsakanin Safiyya da su farhana”

“Allah yabaki hakuri momy,amma wlh sai kunci ubanku,kukuma”

Yunkurawa tayi tatashi
Momy ce tadubeta tace,

“Ina kuma zakije daga zuwanki”

“Momy zanje mugaisa da dady inkoma asibiti,

“Asibiti gurin wa kuma”?

“Gurin Safiyya”

“Meyasameta Kuma”?

“Iskancin yarannan ne yajamata haihuwa ba shiri”

Takarashe zancan tana hararar su farhan,

“Au wannan karan kuma haihuwa zasujamata ba shiri,Allah yakyauta, kishirya nan da sati biyu zakuje dubai,hado kayan lefan muwadda,munyi waya da faruq zakuzo”

“Momy bazaniya zuwaba,kwana 2 bana da lpy”

“Yayi dai dai,hannatu bakomai ni maje da su afifa”

Tashi tayi tahau saman dady,da sallama tashiga yana kashingide,yaamsa tashiga,guri tasamu tagaisheshi yaamsa da sakin fuska,yadubeta yace,

“Hannatu ina abokan nawa”?

“Sunanan kalau,dady nabarsu a gida Safiyya ce bata da lpy tana asibiti”

“Subahanallahi,meyasameta kuma”?

“Wlh dady damuwace su farhana basu da kirki sunmatsa mata”

“To akan me,me tai musu wannan ai shashanci ne”

Nan yaita fada yakudiri niyar tsawatarwa da yaran,ransa yabaci sosai yambayrta yayi yajikin safiyyan”?

“Da sauki,dady momy tace zaaje dubai hado kayan lefan muwadda”

“Bainda zaaje inzaahada a nan ahada inbaxaahadaba sai a hakura da auran kuma daga bikin zaai sai Allah yasauki matarsa lpy,wato hannatu. Allah yasani hankalina be kwanta da aurannan ba,to amma mubarwa Allah ikonsa”

“Wlh dady muma bamaso”

Tashi kitafi Allah yai zabin Alhr kigaishe min daita kafin inzo”

“To dady xataji,su nabil zasuzo ranar jumaa”

“To Allah yakawosu”

Tana sakkowa taga momy bata parlor sai su farhana nan tarufe ido taci mutuncinsu,sukai shiru Allah yaxuba musu shakkarta,taje taiwa momy sallama,tafito jalilace tabiyota tace,

“Pls ya hannatu inasibiti zaki zanbiki”

“Oh karasata zakiyi kome,to bade nixakiba,aikinsan hanya munafuncin banza”

tai tafiyarta,ciki jalila takoma kitchen ta nufa takira saa ta tayata girki zata kaiwa Safiyya

_oh ikon Allah inji naseeba_🤔

 

Tunda hannatu tabar asibiti ta juyawa assadiq baya yai maganar duniya taki kulashi tashi yayi daga kan kujerar dayake yakoma kan gadon yakamo hannuta yakira sunanta

“Sopy kiyi hakuri,sa hannunki kiji yadda ziciyata takebugawa,Sopy wlh mutuwa zanyi,kibude idonki kidubi mijinki”

Kofar dakin akaturo akashigo besan anshigoba yana gaban sopy sai da najiba takaraso gabansu takira sunansa,sannan yadago idonsa jajur

“Ummi sannuku da zuwa”

“Yauwa assadiq ya jikin safiyyan”

“Jiki da sauki ummi”

Da sauri Safiyya ta bude idonta tace,

“Ummina umnina abinci zanci”

“To safiyya sannu kinji”

Tuwon semovita miyar zogale ummi takawowa safiyya tazubamata a plate dakanta tabata taci sosai,assadiq yaji dadi dayaga safiyya taci ta koshi ya hannatu ce tadawo suka gaisa dasu ummi

Fita assadiq yayi waje yashiga Mota tare da kwantar da kujera yakwanta tare da dafe kansa,

Jalila ce tadafowa safiyya fatan wake da wainar kwai tashirya cikin jar atamfa England tayi kyau kaitsaye asibitin tanufa xuwanta yayi dai dai da Dr almustapha dadi ne yakamata takarasa gurinsa suka gaisa cikin barkwanci yakemata take Mata wasa. Flaks din yadaukar mata suka jera suka shiga cikin asibiti,

Kamar dawasa assadiq yahango muwadda da wani matashin saurayi.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[7:41Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTRS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*my mother my every things I love her i care 4 her,infact I can’t do with her may God bless my sweet mother*💙😘

 

_Dabazarku nake rubutuna_ *Talented writers forum* _Hadinkanmnmmu shine alfaharahinnmu_🤝

 

*48*

 

~~~ Da mamaki yakuramusu ido Cikin ransa yake zancan zuci,meye yahada muwadda da da saurayin nan dankaramin tsaki yaja yamaida Kansa ya kwanta xuciyar sa namai zafi,

Ahanya jalila tadubi Dr almuatapha tace,

“Dr yajikin taunt safiyya “?

“Jalila Dasauki amma zuwana kenan nima,ya su momy”?

“Lpy kalau”

Jalila namutukar son Dr almustapha anasa bangaren sa shima yarinyar tana birgeshi ahaka suka karasa dakin daaka kwanatar da safiyya sukai sallama suka shiga jalilace tagaida ummi cikin mutuntawa mamakine Yakama safiyya tadubi yayanta tace,

“Yaya inayini”

“Safiyya ya jikinki,ki kwantar da hankalinki pls kar kijawa kanki matsala kinji ko”

“To yayana inshaallah”

Jalilace takarasa gaban gadon safiyya taimata sannu dauke kanta tayi kamar batajitaba,assadiq ne yashigo suka gaisa da almustapha daga karshe kowa yaishirin tafiya safiyyace tadubi ummi tace

“Ummi kibarmin najiba dan Allah”

Kamar assadiq yace aa sai kuma yaishiru,akabar najiba kowa yatafi jalila ce tai sauri tabi bayan almustapha tace

“Pls Dr ko zaka saukeni a gida”

“OK badamuwa kanwata”

 

Assadiq yaraka su bakin mota yakoma,yana xuwa yaji safiyya tanabawa najiba labarin su afifa yana shiga tai shiru najibace tafita tabasu guri ahankali yakarasa gabanta yazubamata ido can yanisa yace

“Matar assadiq pls kiyi hakuri na azabtu kin hukuntani rashin maganarki gareni babbar illa zaiwa xuciyata”

“Dan Allah dan annabi assadiq kabarni wlh kaina ciwo yake wlh cikinka shiya hanani barin gidanka amma wlh kajira inhaihu haba nagaji”

Tanagama fadar haka tarushe da kuka,rasa yadda zaiyi yayi kawai sai yazubamata ido sai datayi mai isarta sannan. taishiru fatan waken da jalila takawo mata yazubamata yakarasa gabanta yafara bata dafari kinkarba tayi sai dataga ransa yaimugun baci sannan tasha kadan yabata magani sannan takwanta kayan jikinta yacanja mata yazubawa cikin jikinta ido yadda yaga babyn na motsawa ykai bakinsa yasumbaci cikin ture shi tayi yayi murmushi kawai kwanciya tayi aikuwa bacci yadauketa,yarufeta da bargo tare da sumbatar goshinta najiba yakira yace,

“Najiba ga amanar matata nan kikulamin dasu”

“Angama,yaya assadiq yazaro kudi yabata yace tarike a hannunta,yaimata sallama yatafi.

 

Dady ne yasa momy agaba yaitai mata fada sai dayaimata kacakaca kuma yace bainda zasu dasunan hada lefe taiyi shiru tsanar Safiyya tanunku a zuciyarta yakuma shaidamata aure zaiwa su afifa, tatashi tafita cikin bacin rai,

Muwaddace kwance acinyar mamanta tanata kiran layin assadiq yaki dagawa cikin shagwaba tadubi mahaifiyarta ta tace,

“Mama assadiq yana wahalar dani yanabani ciwon kai wlh,nafara gjy nifa gsky zanhakura dama ga muktar yadamu sai naaureshi”

“Muwadda kina haukane kina tunanin zanjanye kudirina kan yaya kareema da yayanta to wlh kishiga hankalinki ni baruwana da matar assadiq amma da sannu zancisu da yaki”

Dariya muwadda tayi tarungume uwar tata.

 

Assadiq ne kwance kan makeken gadonsa abin duniya yaimasa yawa wayarsa yadauka yashiga neman layin faruq bugu biyu yadauka suka gaisa nan yabashi labarin komai yai shiru can yai kwafa yace zai kira yaran saiyaci ubansu,yakwantarwa da yayannasa hankali

Sukai sallama yakashe wayar yakoma ya kwanta da tunanin matarsa aransa.🤦🏻‍♀

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[10:31pm,2017]

 

*💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

 

*Wannan shafinnakune masoyan kannan mijina kusani Ina sanku ina kaunarku kmr yadda kuke kaunar littafina*💙

“`Akarshe inabaku hakurin kuskuran daakasamu gurin rubutu domin masu iya magana nacewa hannun mai rubutu makahone saboda haka ina neman uzuri“`

_*NAGODE*_👌🏻

 

 

 

*49*

 

 

~~~ Kwanan safiyya biyu a asubiti aka sallameta da kyar tayarda tabi assadiq amma har yanxu taki fadawa umminta matsalarta kullum gani take *mijinta sirrinta*ne,tunda suka koma gida tadaukewa assadiq wuta taki kulashi yauma kamar kullum tana zaune a parlor akan carpet tamike kafafunta dasuka dan kumbura ga cikinta da yakara girma tasa kankana agabanta tana cakarta da fork kmr batasan sha saboda yadda take yatsine fuska,sanye take da doguwar rigar material baki da yellow dinkin bubu,assadiq ne yafito daga daki saga shi sai farar vest da dogon wando blue tusa dankaramin pilo acikinsa yarufe da vest din jikinsa yazauna das kamar cikin gaske yafito yana tafiya ahankali tare da yatsine fuska kamar mai cikin gaske da sauri Safiyya tadago takalleshi wata dariyace tasubuce mata tace

“Deee meye haka kuma nashigesu”

Gabanta yakaraso yaxauna da kyar yadubteta yace,

“Sweet sopy tayaki dakon cikin zanyi ko kyadena fushi da assadiq”

“Hmm to naji dan Allah cire pilon nahakura,komai yawuce amma dan Allah Dee kayi adalci tsakaninmmu kaji tsoran Allah ka rike amanar kaina danabaka”

Wani farin cikine yacika masa zuciya yarungumeta yace,

“Nagode sopy Allah yaalbarkaci rayuwarki yarabaki da babyna lpy kuma kisa aranki kenake so kuma kezancigaba da so harkarshan rayuwata”

“Nagode Dee”

“Sopy kinji abinda babyna yace,sai naji kamar yana kiran sunana”

Yakasa kunnansa acikin tashifi lallausar sumarsa tace,

“Kai dan Allah wlh tsoratani xakai wlh ,nidai bantaba jin baby yayi maganaba”

“Cab na assadiq yanayi, sopy pls yau abarni ingaisa da babyna mana”

“Gsky Dee bazaniyaba dan Allah kabarni”

“Sopy bakisan halin danashigaba ko da baki kulani kwana 2 kinason ciwon cikin dayamatsa min yakasheni ko,shi kenan nahakura”

Yafada yana kokarin tashi kawai sai yazube yafara murkususu yana kiran cikinsa zanmutu Safiyya kiramin momyna,agigice tayinkura takaraso gabansa tadafa hartafara kuka tace,

“Dee dan Allah karka mutu wlh inkamutu nima mutuwa zanyi,mekakeso”

Ahankali yafara magana yace,

“Sopy,sppy kece maganina amma kinhanani hakkina,gwanda inmutu konasami saukin abinda nakeji”

“Dee nayarda pls katashi kaji taso muje”

Ahankali yamike ya dan dafata sukai daki,

_nide naseeba zama nayi a parlor dan shan ragowar kankanar Sopy_😋

Sai da komai yalafa sannan assadiq yadubeta yace

“Sweet Sopy nagode Allah yarabaki da babyn assadiq lpy”

“Ameen Dee”

Tafada tana lumahe ido,tashi yayi yahadamusu ruwa sukai wanka suka fito,yadubi kafrta yaga tadaga alamar kumbiri yatsuguna yalatsa kafar yaga tadotsa,yace

“Matar assadiq shirya mufita ammafa akafa kidan zaga ko kafarki tasabe”

“Dee bazaniya fitaba nagaji wlh”

“Mekikayi dazki gaji,Allah sai munfita”

Yafada yana karasawa gaban wardrobe yabude yadakko mata wata doguwar Riga irin wacce tacire amma wannan purple ne material din yazura mata yadakkomata mayafi kalar kayan tayafa shima yadi yadakko kalar kayannata yasa yadakkomata flat shoe tasaka sunyi kyau gacikin jikinta yaimata kyau,wayars yadakko yashiga yimusu pics,sukagama sukafita kallonsa tayi tace,

“Mijin sopy ina muka nufa”

“Mufita titi mudawo ko muje gidansu Achida kinga ma kya gaida mamansa”

Taamsa da to,sukakama hanya sunatafe tanahutawa ahaka sukakarasa waya yaimasa yafito yashiga dasu sukagaisa da Safiyya tare da. yimata sannu kai tsaye gurin hajiyarsa yakaisu suka gaisa tai taiwa Safiyya sannu takwo mata kilishi da danbun nama fita su assadiq sukayi acida ne yadubi assadiq yace ,

“Chairman baka da matsala wlh kasami sweet 16 sai morewa kake”

Kade zauna
Zauna dan iska katsufa a gaban hjy
gashinan har nakusa
xama dady

Ina nan tafe sonake kabani daya daga cikin sisters dinka

Aa kaimusu tsufa Malam

Dariya yayi yabugi kafadarsa yace

Chairman baka da dama wlh

A naji sai hagu ni zo kamaida mu gida

Karkace a napep kukazo

Tracking mukayo kafar matata ce ta kumbura

Ayya Allah yaraba lpy

Ameen.indagaske lake

Dariya kawai
Yayi saboda Sanin
halin abokinnasa harxasu.shiga ciki
Yadalatar dashi nan yabashi labarin muwadda shiru yayi can yanisa yace

Abokina.kayi hakuri kaiwa momy biyayya
Inshaallahu zakaci riba aga a

Nagode abokina Allah yabar zumunci xanzo karakani gidansu

OK

Gurin Hjy suka karasa assadiq yace safiyya ta taso sutafi sukaiwa hjy sallama tabawa safiyya alawar madara
Cikin farin bokiti sukaimata godiya sukatafi

A hanya.assadiq yaketa tarairayar
Safyya Achida yaita dariya a kofar gidan su
Assadiq yasaukesu sukaimasa godiya sukawuce ciki suka gaisa da baba mai gadi suka wuce ciki lokacin magariba tayi
Saa kawai sukasamu tana jera kayan abinci

Ta tsuguna tagaishesu

Suka amsa.assadiq ne
yatambayeta

Momy fa

Sunaciki bari a kirasu

Jalila ce tafara fitowa
Da murna ta karaso tazauna kusa da Safiyya tace

Aunty Safiyya sannu da xuwa yajikinki

Naji sauki jalila

Assadiq ne yakalli jalila yace

Sis kiraka sopy tai salla bari Nina inje inyi indawo ki kularmin da kanki sopy

OK Dee

Fita yayi sukuma suka shiga dakin dan yin sallah su farhana ne kwance a gado ganin Safiyya a dakinsu ne yasa su yin saroro.

 

 

 

 

 

NASEEBA GWO✍🏻
2⃣0⃣1⃣7⃣

 

 

💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM💦💦💦

💦T.W.F💦

 

KANNAN MIJINA
👩‍👩‍👧

 

NA

NASEEBA I UBA💐

 

Inabawa makaranta littafina hakuri zaadinga ganin sanje sanje a rubutuna haka yafarune adalilin phone dita data sami matsala dafatan xaai min uxuri nagode👌🏻

 

Sakon fatan alkhairi gareku masoyana dafatan munyi jumaa lpy Allah yasadamu da annabinmmu ameen👏🏻

 

Kuna raina talented writters forum💦 hadinkanmmu shine alfaharinmmu🤝

 

 

 

 

 

 

5⃣0⃣

 

 

Karasawa tayi gabansu tasami guri ta zauna tace

Farhana da afifa ba magana

Oh sannunki yakike

Lpy lau

Jalila ce tafito daga.toilet tace

Aunty safiyya taso kishiga

To jalila
Tatashi da kyar tashiga toilet din afiface tadubi jalila tace

Yaya jalila ya haka xakisa tashigo mana daki

Bansaniba mara kunya yakamata kushiga hankalinku malamai

Hmm yaya jalila kenan
To ai anyi walkiya munganki amma muje zuwa intai wari maji

Sunagama fadar haka sukabar dakin safiyya ce tabude kofar toilet din tafito sallaya jalila tashinfidamata tasa hijjab ta tayar da sallah data idar sai
ta dan kwanta

Assadiq ne yadawo daga salla yatarar dasu jalila a parlo yamaida dubansa ga jalila yace

Sis ina matar assadiq

Yaya tana daki bari indubata
Tamike tashiga dakin akwance tasameta takarasa gabanta tace

Aunty safiyya kixo inji yaya

Ta yunkura tatashi fitowarta tayi dai dai da fitowar momy daga saman dady tadubeta taga tayi kiba da kyau tace

Ku kuma saukar yaushe kidinga yawo ko safiyya keda kikai nauyi sai kinhaihu a hanya

Assadiq ne yaamshe xancan yace

Momy wlh gani nayi kafarta tadaga shiyasa muka danfita tadan xaga

Ba laifi ai

Tsugunawa Safiyya tayi tagaida momy taamsa ba yabo ba fallasa

Tashi sukayi gabadayansu suka nufi dining area dan yin dinner

Safiyya tana xaune bata tashiba assadiq ne yaimata rada saitasa dariya

Mikewa yayi yakrasa gurin cin abincin yace

Momyna Allah yasa tuwo kikaimana

Nayi tuwo amma na dadynku

Abashi yaci cewar dady yafada yana sakkowa daga bene toxali yayi da Safiyya ccikin sakin fuska yadubeta yace

Aa yata tare kuke tafe sannu kinji

Yauwa dady tafada tana kokarin gaidashi yaamsa da walwala yaimata yajiki

Taamsa akunyace

Maida da dubansa yayi ga assadiq yace

Sadauki tuwon kakeso momy yakalla yarufeta da fada sunbar Safiyya basukirata cin abinciba assadiq ne yace

Dady kunya takeji kuma tafison tuwo

Axubamata tuwon taci
Abata du nakoshi

Yanagama fada yai sama momy kuwa haushi ne yakamata taturawa assadiq kulartuwon yace

Yauwa momy angode ke farhana dakkomana kibiyomu dashi

Momy ce tace bainda
Zata kakira saa tadaukarmuku

Hakuri yabata yadau daya yabawa Safiyya daya jalilace tace

Yayana dakanka kawo indaukar muku

Mikamata yayi tahada
Har ta safiyya ta dauka sukaimata sallama sukatafi

Afiface tadubi momy tace
Wlh momy sai kintashi tsaye akan yaya nifa nafara tsorata da makirar matarsa

Hmm ai wlh momy laifin kine kina kallon yadda yaya yakewa banzar matar nan kin kasa daukar mataki
Cewar farhana tafada tana yatsine fuska

Can momy tanisa tace
Kubarta da makircinta da muwadda taxo xata gane kuskurenta

Afiface takuma jan tsaki tace

Ni wlh yaya jalilace takebani mamaki taita wani shugemata

Eh mana.aikin banxaba
Wai ita mai ciki ina ganin botikin alawar madarar nan nasan tatace wlh baxata shaba shanyewa zamuyi

Dariya kawai momy tayi ai kuwa sukasa alawa gaba sukaita sha

Oh ni naseeba 🤔Allah yashiryi kannan mijin Sopy

Jalila tanakaiwa su safiyya tuwo tajuyo bayan assadiq yagama yimata nasiha kan tazauna lpy da matarsa ba musu taamsa takuma
bawa safiyya hakuri tai musu sallama tatafi

Wanka sukayi sukai sallar ishai wata figigiyar riga Safiyya tasa iya gwiwa fara kal tasaki gashinta abayanta assadiq kuwa jallabiya yasa sukafito sakale da junta yanata tsokanarta mai ciki eye ganina tafe

Dee banaso.kabari
tafada cikin shagwaba

Nadena Sopy

Karasawa sukayi parlon yataimaka mata ta zauna plate yaje yadakko yazuba musu sukaci suka koshi yakwashe kwanikan yamayar kitchen
Yatahomata da kankana a plate

Tanaganinsa tashagwabe fusku tace

Gsky Dee baxanshaba daxufa nasha nide dakko min alawar madarata kuma guda uku xanbaka

Au kinbani ajiya alawarki daman kinbarta a gidan momy

Yafada yanaimata dariya kuka zataimasa
Yajata jikunsa yaxaro
Wayarsa yashiga neman layin jalila farhana ce ta dauka yanajin muryarta yace

Ke ina. Jalila bata wayarta Malama

Mikawa jalila wayar tayi tana wani tabe Baki

Hello yayana

Jalila mubar alawar madara ko

Eh amma su farhana sun shanye

Safiyya yakalla takuramasa ido kawai
Sai yace

OK
Yakashe wayar dasauri tace

Dee nabarta ko

Eh xaakawo miki

Dada gyara.kwanciyar ta tayi ajikinsa yanata kallon yadda cikinta yake motsawa

Sopy inkinhaifi namiji wane suna like so

Assadiq zakasamin

Hmm sopyn assadiq Kennan

Macefa umm sunan momy ko na ummina

To Allah yarabaku lpy matar assadiq

Ameen

xxxxxxxxxxxx

Cikin safiyya yaisa haihuwa tuncikin dare takedan jin ciwo ahaka
tadaure takifadawa assadiq hargarai yawaye tandanji kula assadiq yayi da yanayinta yace yade ko haihuwarce tace aa

Shiryawa yayi yace Sopy bari inje office indawo daga nan zanbiya gurin abokin faruq inkarbo kayan baby faruq naaikawa da kudin yasiyo min

Sai kadawo karka dade.

To dakinji ciwo kikirani

Zankiraka Dee

Yafita ai kuwa yanafita ciwo yakama Safiyya gadan gadan ta kira layin assadiq taki shiga layin momy takira wayar tana hannun afifa taki dagawa tafara neman layin umminta kenan mararta tamurda tare da bayanta wullar da wayar tayi tadurkushe a gurin.

2⃣0⃣1⃣7⃣

 

 

💎💎TALENTED💎💎 WRITTERS FOROM💎💎
💎💎

 

����T W F💎

 

Hadinkanmmu💎 shine💎 alfaharinmmu🤝

 

KANNAN MIJINA
. 👩‍👩‍👦

 

 

NA

NASEEBA I UBA🐠💐

Wannan shafin kine
Xeee smile😇 inatayaku murnar cika shekara daya da aure
Allah yakara xaman lpy yakawo xuria tagari Hmm masoyan juna🌹 Zainab I uba
And
Abdulbasid I isa🌷

Allah yakaro shekaru bila adadin💃🏻masoyan naseeba I uba kuce ameen👏🏻

 

 

Muje xuwa fans 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

 

5⃣1⃣

 

Cikin tsiwa sukafara magana zuwa mukayi daukar baby

Kamar yaya bamuganeba wai ku wasu irin mutanene
Kundinga abu kamar yara

Cewar najiba kenan tafada tana daukar babyn

Inna jamila ce tace
Haba yayan nan meyasa zakuyi haka

Aa baba mufa yanaike ne dady ne xaiganta ko kunganmmu a gidan nan ne tunda akai haihwar ni kalar yarma banganiba

Cewar afifa farhana ce taamshe xancan

To mexai kawoka haka kawai aimaka sharri

Najiba ce tadubesu tace to munji dan Allah
Kuje xaakawota

Inna jamilace tace abasu sukaita

Safiyya dai tarasama mexatace saboda cikinta dayake ciwo ko magana batason yi amma ranta yabaci

Aka dada gyra babyn cikin wasu kaya pink da fari aka nade ta cikin farin shawul sai kamshi take

Suka dauketa sukatafi

Najibace tace
Wlh ya safiyya sai nai maganin mutanan nan
Wlh

Shiru taimata sai inna jameela ce tace.

Aa najiba ba ruwanki dasu dan Allah suma ai matane gidan wasu
xasu ko haba basu da kunya wlh amma yaruwarsu baruwanta
yarinyar kirki

Hmm itama dai denewa tayi cewar safiyya kenan

Cikinta ne ya murdamata tahau murkususu😰

Su farhana nafita suka karasa gida suna zuwa suka mikawa momy babyn sukafara banbamin masifa wai kanwar safiyya taxagesu safiyyan tanajinta bata hanata ba

Hmm dakyar fa sukabada babyn

Au da baxasu bada itaba kenan ai xasu aikata amma suyi lokacinsu ne daan auro
Muwadda ai shikenan

Daman ai jira ake tahaihu ayi bikin

Ai gwanda cewar afifa kenan

Tashi momy tayi tanufi saman dady dan kaimasa babyn

Yana bedroom sanda tashiga takarasa tamika masa babyn

Mashaallah tabarakhallah Allah yaraya mana mekama da faruq yafada yana kokarin yimata addua

Momyce tace aa alhj karfa kaga sabuwar mata kamanta dani

Au hjy Kareema kina zaune daman

Hmmm ai kuwa azo amayar daita gida

Sukai dariya assadiq ne yai sallama yashigo
Yasami guri yazauna yagaida iyayannasa suka amsa cikin sakin fuska dady ne yadubi dannasa yace

Sadauki matarka taiya haihuwa tahaifawa faruq mai kama dashi Allah yasa kar tai halinsa nafada

Yai murmushi yace

Dady dama xuwa nayi inji wane suna zaasamata

To ai sadauki zabi nagareka ko fatanmmu dai Allah yaalbarkaceta

Ameen dady to ni da sunan momy xansa mata

To ai yayi balaifi sadauki to hjy Kareema kinsami takwara

Hmm ina ganin karka asamata sunana

Ko meye dalilin ki

Haka kawai Alhj nadgode asamata wani sunan

To kaji abinda mahaifiyyarka tace

Eh naji dady bakomai sai asamata sunan ummin Safiyya

To balaifi sadauki Allah yarayamana ita

Ameen dady

Yamikawa momy ita yatashi yabude wata akwati yadakko wasu takardu da wata sarka ta gwal yamiwa assadiq yace

Sadauki gashi takardun filine da sarkar gold namallakawa amaryata

Dady angode Allah yakara.girma momy gashi kigani

Nagani assadiq angode Alhj

To madalla atafi amayar daita

Tashi sukai suka sakko tare guri yasamu yaxauna yace

Momy yaxaai da taron suna dakuma kayan barka

Kaje kuyi magana da yayarka

Yaamsa da to yatashi yafita su farhana ne suka fito daga dakinsu suka dauki babyn afifa tace

Momy amma sunanki zaasamata ko

Aa ai muwaddace xatahaifi me sunana

Wlh kuwa momy to Sunan wa zaasamata

Babarta mana

Wlh dama asamata fadila

Aikuwa sunan da dadi shikenan asamata

Yauwa momyna

Kutashi kukaita

Jalila ce tashigo sanye da bakar abaya tayi rolling da farin glass dinta afuskarta tana ganin babynsu takarbeta tarungumeta
tace momy sannu da gida amayar daita nasan anata xuwa ganinta

Kaita jalila ya makarantar

Lpy lau momy

Su farhana kuwa.sai hararta suke

Assadiq yana xuwa gida yatar sopy ba lpy hankalinsa yatashi yajata dakinsa yabata maltina tasha yabata

Magani tadan kwanta fara shafamata jiki yayi tasamasa kuka

hakura yayi yabata sakon dady tai ta godiya yashaidamata sunan umminta xaasa
Tayi murna

Jalila ce tai kacibus da
Dr almustapha yazo ganin baby suka tsaya suka sha hirarsu karshe sukai musayan number

Suka shigaciki yaduba safiyya hade da rubuta mata magani daxai tafi yabata dubu hamsin
Yabawa jalila goma

Ranar suna Safiyya tashirya cikin swiss lace tayi kyau anata hidimar suna kawai saijin maroki tayi yana Allah yaraya fadila memakon sunan Ummi

 

 

Ayi hakuri bayawa
🤗🤗🤗

 

 

 

NASEEBA GAWO✍🏻
2⃣0⃣1⃣7⃣

 

💎💎💎TALENTED WRITTERS FORUM💎💎💎

💎T.W.F💎

 

 

KANNAN MIJINA
👩‍👩‍👧

 

NA

NASEEBA I UBA💐

 

Dedicated to my group fans may Allah live us together💙

 

5⃣1⃣

 

Hankalin assadiq ne yakasa kwanciya gaba daya tunanin sopy ne aransa wayarsa yaxaro daga aljihunsa yashiga naman layinta tanata ringing bata dagaba hankalinsa yai masifar tashi sai yashiga neman layin momy akai saa tadauka arikice yafara magana

Momy dan Allah kitura agano sopy nafita nabarta batajin dadi inata kiran layinta akashe

To mai mata ai dai kabari mugaisa ko meyasameta

Afuwan momyna ina kwana may be haihuwar ce

Lpy lau Allah yaraba lpy xan aika

To momy nima gani nan

Shiru tayi takashe wayar dady ne yadubeta.yace meyaaami safiyyan

Wai batajin dadi shine dan iyayi wai aje agano masa ita wlh assadiq yafiya son Matar nan tasa

Hmm hajiya Kareema kenan to ai yayi dai dai meye laifin matar sadauki

Babu kam

Kitashi kije da kanki ki ganota inhaihuwarce kutafi asibiti

Aa alhj infara tura yara dai ko in haihuwarce sai suzo sufadamin mutafi

Balaifi ai

Tashi tayi takira farhana tace taje tagano jikin matar assadiq sai data gama nuku nukunta sannan tatafi

Safiyya kuwa tarasa inda zatasa kanta dan axabar ciwo tuntana salati har tai shiru anahaka sai ga assadiq yadawo da hanxari yai parking ya fito ya nufi gidan tundaga parlor yafara jiyo nishin sopy da axama yamurda kofar yashiga mexai gani

Sopy ce kwance ciwo yaci karfinta rikicewa
yayi yarasa kankame shi tayi takasa magana kawai Dee take iya fadi

Yadauketa yasata amota kenan sai ga farhana wani banzan.kallo yaimata yadubeta yace

Fitar min a gida xanrufe

Yaya momy ce taaikoni inga jikin aunt safiyya

To naji jeki

Yafada yana dakamata tsawa bashiri tafita tana kunkuni

Yarufe gate din gidan
Yaja motarsa yanufi asibiti yanatafaman yimata sannu kanta kawai take iya dagawa

Yaya hannatu yaiwa waya aikuwa takidime bata bata lokaciba tanufi asibitin kusan atare sukai parking takaraso gurinsu dabino tabawa Safiyya taci guda bakwa aka kawo whole chair aka dauki sopy

Assadiq jiyake kamar yabita labour room din yakasa zaune yakasa tsaye yanajiyo yadda take salati da karfi kawai sai yasawa yayarsa kuka ita saitarasa ma mezatace masa ta lallabashi yatafi yadaklowa safiyya kaya dana baby

Dakyar yatafi yacemata kayan babyn yana mota tabishi takarbo yace a kira ummin safiyya tace aa abari ta haihu yace to yaja motarsa yatafi idonsa yai jazur takoma ciki Safiyya.tarasa inda zata sa kanta saboda axaba duk agaji anbata amma haihuwa shiru hankalin yaya hannatu ne yai masifar tashi takira yayar safiyya wato ya rukayya tafadamata hankali tashe tanufo asibitin da dan babynta

Assadiq yanafita gidansu yawuce kai tsaye dakin momy ya nufa yana xuwa yaxube agabanta yashiga rera kuka

Hmm assadiq kenan akan sopy bayajin kunyar kuka sai kace ba namijiba🤔

Cikin tashin hankali take tambayarsa meyafaru

Momy sopy mutuwa zatai tana asibiti

Au shine kazo kasani gaba kakemin kuka
Amma de Allah yasawakamaka wlh

Yanzu tana wane asibitin

Annury momy

Ai saikatashi mutafi tafada tana kokarin tashi tare da mitar yakoromata farhana

Gidansa yashiga yahadowa safiyya kaya
Sannan yazo sukatafi da momy su afifa suna kallonsu suka tafi ko Allah yasawake jalila kuwa tana makaranta

Suna zuwa Allah yasauki safiyya lpy amma tasha fama kukan babyn ne yacika gurin assadiq murna kamar me wata nurse
ce tafito tana faraa
da sauri assadiq yatareta yanatambayar ta

Nurse ya matata

Lpyt kalau yallabai yanxu zaafito daita

Momy ce taja tsaki tace ai katambayi abinda Allah yabaka ko
Me akasamu nurse

Hjy mace akasamu

Mashaallah Allah yaraya

Assadiq ne yadakko kudi yabawa nurse din taita murna

Anahaka akafito da baby momy ce takarbeta kamarsu daya da faruq take kaunar yar taratsa ta badan komaiba sai dan tayi kama da danta

Tamikawa ya hannatu
Taxubawa yar ido katuwa farinta irin na safiyya rungumeta tayi ajikinta

Yaya rukayyace ta dauketa akarshe tamikawa assadiq babyn

Tafita takira ummi tafadamata sukaita murna tace gasu nan
Tai mata sallama tanata mamakin uwar mijin Safiyya

Safiyya aka turo akan gado anshiryata tsaf tanata bacci aka kaita dakin hutu gabadayansu suka nufi dakin

Mikawa yaya rukayya babyn yayi yanufi gurin matarsa haushine yakama momy bata jira farkawar Safiyya ba tatafi

Ummi ce taxo ita da su amina.nan sukai ta murna suka dau babyn ya amina ta kankameta najibace tace

Haba yaya amina nima bani ita bangaji da ganintaba

Akasa dariya ummi takawowa Safiyya farfesun naman kaji da tuwo tare da yajin daddawa

Fita assadiq yayi yafara kiran abokansa
Yakira dady yafadamasa

Dady yau anyiwa momy takwara

Aa mashaallah sadauki Allah yaraya kace dai nayi amarya

Hakane kam dady

To Allah yaimata albarka yabata halin urwata

Ameen dady nagode

Sukai sallama yakira faruq wani ihun murna yasa musamman daakace kamarsu daya

Ahankali safiyya tafara bude idonta jinta tayi sakayo tamaida dubanta ga umminta tace

Ummi dagani inzauna tadagata tare dajeramata sannu

Kukan babyn ne ya sata dagowa tadubi hannun najiba ummi
Ce takarbeta tabawa Safiyya ita nokewa tayi wai kunya akai ta mata dariya da kyar takarbeta batajimaba tamikawa ya hannatu ita akaxubamata farfesun tafaraci kenan assadiq yashigo dauke da ledoji ahannunsa gabadaya sukafita ummi kuwa sallama tai musu tatafi

Kangadon yahau yadau babyn yadubi Safiyya yace maman baby sannu da kokari nagode yafada yana daukar cokalin abincin yashiga bata abaki

Babyn ce tafara kuka alamar yunwa yace

Sopy bata tasha

Nashiga.uku wlh Dee
baniyaba

Ninaiya ai yafada yana
matsawa yadaga rigarta yakaramata babyn aikuwa.takama tanata tsotsa

Kara Safiyya tasa tace wlh Dee dazafi

Dariya yasamata yacigaba dabata nata abincin

Kwanansu daya akasallamosu najibace a gidan da wata kanwar ummi mai suna inna jameela jalilama tadawo gidan saboda kaunar datakewa babyn assadiq yaji dadin hakan

Su afifane sukaxo daukar babyn cikin gadara da isa.

 

 

 

 

Readers kuyi hakuri bazaku dinga ganin posting dinaba sakamakon wayata datasami matsala😫

 

 

 

NASEEBA GAWO✍🏻
2⃣0⃣1⃣7⃣

 

💎TALENTED 💎
💎💎WRITTERS💎💎
💎FORUM💎💎💎

💎T W F💎

 

 

KANNAN MIJINA
👩‍👩‍👧

 

NA

 

NASEEBA I UBA💐

 

Wannan shafin nakine ke kadi
Kawana kyauta nabaki👌🏻sadiya smart

Naseeba💐natayaki murnar birthday dinki🎈Allah yakaro shekaru masu albarka👏🏻 TALENTED dole mukwaso shoki💃🏻💃🏻💃🏻🤦🏻‍♀

HAPPYBIRTHEY DEAR🎂🎂🎈🎈

 

 

 

 

5⃣3⃣

 

Najiba ce tashiga daki tasami safiyya zaune tanabawa baby nono tace

Yaya safiyya sai naji kamar fadila akasawa babyn nan ko

Haka nima naji bari inje gurin assadiq din

Kece masa me kuma safiyya

Cewar yayarta amina
tafadawa tana kokarin zama

Inade uwa tafada tanakokarin fita tadau babynta kai tsaye dakin assadiq tanufa ahankali tatura kofar yanatsaye gaban madubi yanataje sumar kansa daga shi sai towel yakaraso yataresu rungumesu yayi tsam akirjinsa yasakarmata kiss yakarbi babyn yace

Fadilaty bintee

Dee fadilafa kenan

Eh sopy sunanta kenan

Amma Dee bahaka mukaiba kace sunan ummina xakasamin

Kiyi hakuri sopy abinda yasa nasamata sunan tunda aka haifeta nakesamun budi kinga nafrko ankaramin girma a office kullum arxikina karuwa yake kinga kuwa tacancanta asamata sunan

Shikenan Dee Allah yarayamana ita

Yauwa ameen matar assadiq dada rungumeta yayi tsam akirjinsa yace

Nayi missing dinki sopy yakamata akawowa assadiq agaji

Dee pls kabari kaga fa da mutane agidan tadada tana janye jikinta

To muje kitaimakamin
Inshirya

Kwantar da babyn yayi tadakko masa shadda gexina milk da brwon din aiki yasa tasamasa hula zanna kalar kayan yayi kyau

Itama less dinta milk ne da brown din fulawowi sunhadu mukulli naga yadakko yadankamata tace

Dee wannafa

Sopy mukulin motane nabaki tukwaicin haifamin fadylaty

Rasa ma mexatace tayi tace

Dee nagode Allah yakara budi

Cab bankarbi wannan godiyarba acanja wata

To rufe idonka

Narufe yafada yana kokarin rufewa

Stol din mudubi tajanyo.ta tahau tasakar masa kiss💋

kankameta yayi yashiga kissing dinta sai da yashanye janbakinta tas sanna
yabarta takarasa gaban madubi taga ya ggemata janbaki cikin.shagwaba tace

Dee kagogen janbaki

Kunnansa yakama yace

I am sorry sweet Sopy

Gyarawa tayi tadau fadila yashiga yimusu pics sunsha kyau

Sukagama yakarbi babyn suka fito gwanin shaawaa fitowarsu tayi dai da shigowar yaya hannatu taxuba musu ido tace

Kai kannena kunyi kyau mashaAllah safiyya Allah yakara lpy

Tasa hannu takarbi babyn assadiq ne yace yaya kixo muje kiga motar danasaiwa Sopy

Fita sukayi sukaga motar safiyya taimata murna sukawuce gidansu safiyya Kuma
Takoma ciki tasamu yaya rukayya ma taxo

Nansuka gaisa tatambayeta ina takwara ummin take

Hmm takwara ummi
Kuma yaya rukayya aibaasamata ba fadila akasamata

Fadila kuma lallai wlh nasan momy ce tahana ko shegun kannansa Cewar ya amina

Ai wlh basu da mutunci yaniska

Yaisa dai haka mude fatanmu Allah yarayata

Cewar yaya rukayya kenan tafada tana kwantar da mashkur

Mukulin motarta tanuna musu sukaita murna suhyla ce tashigo tadugudu tafada kan safiyya tace

Aunty cafiyya ina babynki

Tana gidan momy suly

Inkikaje sai nadokeki uwar magana kawai
Cewar yaya rukayya

A bangaran gidansu assadiq kuwa hidima aketayi kaitsaye saman dady su assadiq suka nufa da sallama suka shiga suka gaisheshi yaamsa da kulawa ya
hannatu tamika masa fadila yakarbeta yasamata albarka yadubi dannasa yace

Sadauki Allah yaraya mana ita yaimata albarka

Ameen dady

Sukaimasa sallama suka suka sakko farhana ce takarbi fadila tai dakinsu daita nabil ne yakalli babyn
Yace

Aunt farhana nasami matar aure

Dallacan yimana shiru mukuma akansu xamu
Kare
cewar afifa kenan make kafada yayi yace

Ni wlh sai naaureta bari uncle A.yadawo

Kantabashi amsa ya hannatu tashigo takarbi babyn nabil ne yabiyota suka fita tare

Maman muwadda takaiwa babyn takarbeta taji son yar aranta

Gidan Safiyya yacika dayan suna assadiq yakashe kudi anyi hidima sosai sa assadiq yayankawa fadila safiyya tayi shiga taalfarma tayi kyau

Su jalila sai hidima suke ita da najiba sunyi anko iri daya

Sai..dayamma su farhana sukaxo da kawayansu suka karbi babyn basmace tatambayi farhana sunan babyn tace

Fadila dafa wani suna xaasamata mukabawa momy shawara asamata
Fadila karaf a kunnan Safiyya da najiba data kawomusu abici zatai magana safiyya tahanata sukabarmusu parlorn

Assadiq ne yaimata waya ga yaronsana office me suna ashiru spider yakarbar masa abinci tanaxuwa.dauka taga babu tanfito kawai taga su farhana sunaci😳

Najiba tagansu nantahau yimusu masifa kankace me sunkacame da fada Safiyya ce tafara kuka jiri yadebeta xatafi akakaita daki

 

 

Kai kai.🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

 

 

 

NASEEBA GAWO✍🏻
[4:37Pm,2017]

 

*®💦����💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W>F*

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*sakon taaziya gareku iyayena bisa rashi damukayi na babban yayanku amadadin yan uwana Munai muku gaisuwa Allah yakara hakuri yaimasa rahama hakurin rashinsa*Ameen_😰

*Godiya tamusamman gareku masoyan NASEEBA ngode da adduoinku bisa rashin da mukayi angode Allah yakara zumunci*😘

 

 

 

*54*

~~~kwantar da ita su ya rukayya sukai akabata magani tasha cikin ikon Allah bacci yai gaba daita abangaran su farhana sunnanta xuba rashin mutunci najiba natai musu masifa ya hannatu ce tashigo ta tatar da su farhana nata rashin mutunci cikin sauri takarasa tana xuwa ta dasuke farhana da mari takuma kawata ta kan afifa tanufa tafara jibgar ta da kyar aka kwaceta ba shiri suka gudu gida tambaya tayi ina safiyya akafadamata tana daki
kai tsaye dakin tanufa
ta tasami bacci fadila ta karba a hannun ya rukayya tadubeta cikin jin kunya tace

“Dan Allah rukayya kuyi hakuri da abinda yayan Nan sukai muku wlh sai sunci ubansu ”

” Bakomai ya hannatu, ya wuce Allah ya shiryesu”

Amma gaskiya basa kyautawa safiyya wlh laifin me tai musu”?

Cewar ya amina tafada cikin bacin rai ya rukayya ce takatseta cikin fada

“Amina meye haka nazaci magana ta wuce yakamata abar zancan haka, haba”

Kiran Assadiq ne yakatse musu maganar da sukeyi ya hannatu ce tadaga

“Hello sopy”

“Assadiq baitabace”

“yaya ina safiyya dafatan dai lpy?

Lpy kalau kanta ne kemata ciwo tasha magani ta kwanta”

“yaya ko asibiti zanzo mutafi”?

“Aa tasami bacci ka barta”

“shikenan yaya naaiko spider yakarbar mana abinci yazo”

“yazo amma kai muku take away in kazo mayi maganar”

“yaya akwai matsala kenan”

“kabari dai kadawo”

“ok”

Sukai sallama ta kashe wayar fadila ce tafara kuka akatashi safiyya tabata nono ta kurawa fadila ido ya hannatu tadada bata hakuri takuma tabbatar mata sai sunci uban su. tai musu sallama tafita su ka dada kwantar mata da hankali amma ta shirya tunkarar Assadiq da dalilin da yasa akasawa yarta sunan da kannansa suka zaba.

Taro yawatse kowa yaci yasha amma *kannan miji*sun tafka rashin mutunci

Abangaran su farhana kuwa suna zuwa suka sawa momy kuka kannan safiyya sun zageta sun kuma maresu nanfa ta hau fada jalila ce tadubesu tace

“wlh afifa kuji tsoran Allah nazaci kune kukai musu laifi”

“rufemin baki jalila yaushe kikafara kin kannanki zasuyi musu karyane to ki iya bakinki kuma kishiga hankalinki”

“Gsky momy kidena haka tsakani da Allah bakya kyautawa yanzu meye laifin safiyya”

“au tambayata kike hannatu to yayi kyau xanfada miki amma sai naji duka tukunna uwana.

“Allah ya baki hakuri ya huci zuciyarki”

“Ameen”

Tafada tana kokarin tashi ta nufi saman dady Assadiq ne yai sallama ya shigo guri ya samu ya zsuna yadubi ya hannatu yace

“yaya ya gajiyar taron suna dafatan anyi lpy?

“lpy kalau Assadiq sai yan iskan yarannan da sukai halin nasu na tsiya”

“meyafaru, ke afifa me kukayi a gidan sunan ?

“ya Assadiq sune wai

“wai me, dallacan rufewa mutane baki mara kunya fitsararru”

Nan takwashe komai tafadamasa wani banzan kallo ya watsa musu yai musu kaca kaca kuma yai musu iyaka da gidansa yana cikin yimusu fada kenan dady ya sakko yadubi yayan nasa yace

“Sadauki lpy dai ko naga kunyi carko carko”

Dady wlh su farhana basa ji sunje sun dagawa mutane hankali a gidan suna”

“afifa meyasa bakwaji kunfiso kutajawa mutane magana ko, me sukayi?

Yaya hannatu ce tafadamasa yadubesu cikin bacin rai yace

Kun kyauta farhana to kubude kunnanku da kyau kuji ba ku ba matar Sadauki kufita harkarta kuma ko wacce tafito da miji ai mata aure in ba hakaba wlh zanbaku mamaki shasha shan banza”

Yafada yana maida dubansa ga Assadiq yace,

“Sadauki kibawa safiyya hakuri kaji”

“shikenan dady xanfadamata inshaallah ”

yasa kai yafita sukacigaba da tattaunawa da ya hannatu nabil ne ya shigo parlon yakarasa
gaban Assadiq yarungume shi yace

” uncle A matata?

“nabil wacce matarka?

“fadila mana wai aunty afifa tace banzan auretaba wai akansu zamu kare, hakafa tace

“rabu dasu nabil dina basu da kirki zanbaka auran fadilaty kai dai kacewa abbanka yatanadi kudin auran queen”

Dariya ya hannatu tayi
Momy ce tasakko tadubi Assadiq tace

“yauwa gwanda daka shigo abinda nakeso dakai Assadiq shine ba ruwan matarka da yayana takama kanta inbahakaba wlh xan shayar da ita mamaki ”

” to amma momy

“rufemin baki wanda bayason laifin matarsa kuma kafara shirin auranka da muwadda ”

Rasama abinda zai ce yayi kawai ya mike yaimata sallama yatafi

Kai tsaye gidansa ya nufa yana shiga yatarar da inna jamila a parlon ya gaisheta taimasa da kulawa ya tashi ya nufi dakin safiyya tana sanye da wata doguwar riga pink gashinta kwance a gadon bayanta gefenta

Fadila ce kwance tanata wutsil tsila kafa yakarasa yadau fadila yace

Fadilaty binty ga papa
Yadawo”

Maida dubansa yayi ga safiyya cikin muryar rarrashi ya kira sunnanta dauke kanta tayi tai masa banza karshema ta juyamasa baya tai kwanciyarta bayanta ya zubawa ido

 

 

 

Alhmdulillah 2morrow is my birthday 🎂🎂💃🏻💃🏻 I need ur wishes sisters 👏🏻

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:47Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*Godiya tamusamman gareku masoyan NASEEBA a gaskiya bani da bakin dazan gode muku bisa fatan alkhairin da kukai min a ranar birthday na sai dai ince Allah yakara zumunci yabar kauna Assadiq da sopy suna gaidaku kyauta👌🏻ina sanku masoyana a duk inda kuke*🙅🏻😍😘

*Banmanta da kuba TALENTED WRITTERS domin kuwa hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*wannan shafin nakune kyauta👌🏻 makaranta kannan mijina*👩‍👩‍👧

 

 

*55*

 

 

~~~tashi yayi yazagaya daya barin data juya ya zuba mata ido yakira sunnanta da wata iriyar murya

“sopy yakamata ki saurareni kiji abinda zanfada miki mana

Shiru taimasa fadila ce tafara kuka ya kuma yimata magana da ta karbeta ko motsi bataiba ransa ne yabaci cikin daga murya yace

“safiyya ya inatai miki magana kinmin banza ko tunda kikaga naxo aikinsan maganar data kawoni ko amma meye laifin Fadila da har zaki ki karbarta”

Cikin karaji tadago tadubeshi tace

“Assadiq dan Allah kabarni haka dame zanji meyasa kukeson bani ciwon kai ne banson magana nazaci fadila yakara ce ko kuma ince yar kannanka ce tunda har suna da ikon zaba mata suna to ai ina ganin ka kaimusu ita haba wace irin rayuwa ce wannan nagaji wlh ”

Tanagama fada tasa kuka tsayawa yayi kawai yana kallonta ya kuma mikamata babyn ko kallonsa bataiba gashi tanata kuka ransa ne yabaci ya dau fidarta ya fita dakinsa yanufa da ita yashiga aikin rarrashi ya bata ruwanta na zam zam tasha tadanyi shiru can takuma tsanyarewa da kuka lebansa yasamata abaki tai ta tsotsa can xuwa anjima tai bacci a hankali yaxare kallonta yake da wata irin soyayya ya lallaba ya kwantar da ita a gadon sa ya tashi ya shiga toilet yayi wanka sai yanxu yatuna beci abinciba maltina da madara yafssa yasha duk wannan abinda ake su najiba nata baccin gajiya sai da yagama komai sannan yadau fadila yafita da ita kai tsaye dakin safiyya ya nufa ya tura kofar a hankali bacci take tafaman yi yakarasa ya kwantar da fadila a gefenta taba jikin safiyya yayi yaji xafi alamar xaxxabi har zaitasheta tasha magani sai kuma yafasa kiss yasakar mata yaja bargo yarufe su ya kashe musu kwan fitila yaja kofar yafita dakinsa ya koma yanashiga kiran muwadda yashigo da kamar yashare sai kuma yadaga cikin farin ciki tace

“Hello sweery”

“muwadda kina lpy ya mama”?

“lpy kalau ya diyata da mamanta”?

“suna lpy”

“Am sweery pls yaushe zaka zo kagafa lokaci yana neman ya kure mana bamu shirya komaiba”

“kinga muwadda kibari xankiraki da safe yanxu bacci nakeji”

“ok, Sweet dreams love u💙

“me too”

Ya kashe wayar abangaran muwadda wani farin ciki ne yasamata tafara samun kan Assadiq wani shuumin murmushi naga tayi ko mekenan can daya wayar ta tafara ringing kirar I phone 6 cikin hanzari tadaga tare da farin ciki muktar ne shine saurayin da muwadda take so dan ajin sune mahaifinsa yarasu daga shi sai mamansa da kanwarsa rushida suka sha wayarsu

 

Washegari su najiba da ya amina sai inna jamila suka tashi da aikin suyar nama Assadiq bafito daga dakinsaba sai 11:30 yasanya farin yadi da bakar hula dakin safiyya ya shiga yatarar da fadila kwance cikin gadonta mai kyan gaske ansamata wasu kaya purple sai kamshi take ya dakko ta yafara yimata wasa kmr ba baby ba

Fadilaty binty kintashi lpy

Safiyya kuwa tana xaune tasa wata atamfa super yaluwa da green tanada dan kwalinta kamar gwaggwaro tayi kyau tanata break yasaci kallonta a ransa ya godewa Allah da yabashi safiyya a matsayin mata kwantar da fadila yayi cikin gadon ta yakaraso gabanta ya xauna ya tankwashe kafarsa yaja kofin shayin nata gabansa da farantin dankali da farfesun kayan ciki gabansa dagowa tayi suka hada ido taganshi kamar randa yafara xuwa gurinta xance ahankali tace

“ina kwana ”

” kintashi lpy”

“lpy kalau ”

Daga haka basu kuma maganaba yayi break dinsa ya gama mikewa yayi yanufi gurin fadila yasakar mata kiss ya fita kallo safiyya tabishi da shi yana fita su ka gaisa dasu ya amina najiba tace Yaya Assadiq ga abincin ka can

” kinmakara najiba naci na matata”

“shikenan ya Assadiq ”

” ga amanar mata ta Nan da Fadilaty a hannunki ”

” baka da damuwa yaya”

Yaimusu sallama yafita kai tsaye gidansu ya nufa

Safiyya kuwa wani haushi ne yakamata wayar tace tafara ringing tana dubawa taga umminta suka gaisa tai mata ya jiki tadada bata hakuri akan shaanin rayuwa da muhimmancin hakuri tace rukayya zata zo araba naman akaiwa momy zubawa sabiu atamfofi guda 5 a hadawa su momy taamsa da to taimata Godiya sukai sallama

Assadiq yana shiga parlon ya tatar da jalila kwance cikin bakar abaya da farin glass dinta manne a fuskarta tanata waya daka ganta kasan tana cikin farin ciki tana ganinsa tace

“Dr i will call u later”

Daga daya bangaran aka amsa da ok

Ta kashe wayar tadubeshi tace

“ya Assadiq sannu da shigowa ina queen”?

“yauwa jalila lpy kalau momy fa”?

“tana dakinta

“ok dawa kike waya”?

“Dr Almustapha ne”

“ba laifi”

farhana ce tafito cikin wasu kananun kaya riga da wando blue sun matseta ta gaisheshi yadaga mata harara yace koma kicanja kaya sha sha sha kawai daki takoma tana zunburar baki afifa ce tace ya farhana ya kika dawo

“ya Assadiq ne wai indawo incanja kaya ”

” mijin sopy zakice dalla rabu da shi in yafita kya tafi

“au afifa ke da kina zaton zaniya sa riga da zani ne baxan iyaba”

Dakin momy yashiga tana zaune tana hade wasu kaya yasami guri yaxauna

“momy na antashi lpy

“lpy kalau Assadiq ya kwanan kawartawa

“lpyt kalau momy tana nan sai kuka

Ayya to karde kusaba mata da kuka, yauwa ga kayan lefe nan nafara siya yakamata kabada kudi a hado akai dan na fuskanci faruq baze siyoba”

“To momy kamar nawa zanbayar”?

Kabada miliyan 1

“momy lefan muwadda ne har miliyan”

“Eh tafima haka

Shikenan momy ba damuwa innadawo xanbada

Yafada yana kokarin tashi yaimata sallama yafita wayar sa ya dauka yaiwa safiyya text ya wuce office

Safiyya na zaune suna hira da ya rukayya text din Assadiq yashigo tana dubawa taga sakon kmr haka

“kinyi kyau sopy ki kularmin da Fadilaty binty

Shareshi tayi ya rukayya da inna jamila suka raba naman kmr yadda umminsu tace aka hada musu da atamfofin akabawa najiba takai musu tana xuwa ta tatar da farhana a parlon ta dubeta tace

“momy fa”

Lpy dai ko ”

” gashi kibata inji ya safiyya ”

Kimayar kice tabarshi mungode”

Ke farhana meye haka!
Cikin sauri tajuya waza tagani. 😳

07037732029 👈🏻

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
{2:30Pm,2017}

 

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
����‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

 

*Dedicated 2 my Sweet mom*😘😘

 

*kunaraina fa TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine. alfaharinmmu*🤝🤝

 

*56*

 

~~~Dady ne yashigo yatarar da najiba da kaya a hannu cikin ladabi ta tsuguna tagai sheshi da sakin fuska yaamsa yace

“Daga ina kike tafe”

“ya safiyya ce ta aikoni shine farhana tace inmayar basa so ”

Maida dubansa yayi ga farhana yace

” farhana gurinki aka aikota dama”

“aa Dady”

“to dan meyasa xakice a mayar saboda raini da wulakanci ko

Shiru tayi nan yaimata kaca kaca kuma yadora da

“Tunda bakyaji farhana zanbaki mamaki wlh ki saurareni”

Momy ce tafito daga dakinta duban mai gidannata tayi tace

“Alhj lpy”

“Nida wannan sha sha shar yarinyar nan ne mana”

Nan yafadamata abinda tayi da irin hukuncin dazai yankemata tunda bataji baki momy ta tabe tace

Allah yabaka hakuri Alhj”

Ita de najiba gaida momy tayi tabata sakon data kawo karba tayi momyn tace kice angode dady ne yabata dubu biyu taki karba sai da ya matsamata sannan ta karba tai masa godiya ta tafi kai tsaye dakin sa yanufa farhana ce tabude kayan atamfofine musu kyau ta momy engla tasu ma mai kyau ga nama fal afifa ce tashigo tadubesu tace

“momy wadannan kayan fa?

“aunty safiyya ce tabawa mara mutuncin
kanwarta ta kawo mana”
Cewar farhana kenan tafada tana daukar tsokar nama

“wlh matar nan makira ce munafuka kawai”

Sai yanzu momy tasa baki”

“Hmmm tayi tagama ai

“aa to Allah na tsanesu

“To marasa mutunci wa kuka tsana”? juyawa sukayi dan ganin mai magana

Jalila ce tafito tasami guri tazauna momy ce tabata amsa

“matar Assadiq ko xaki dau matakine jalila na fiskanci inda kika dosa to wlh muxuba”

“Allah ya baki hakuri momy, yanzu dai daga ina aka sami kayan nan”?

“Matar Assadiq ce takawo ki dau daya, kidau ta hannatu”

“kai amma angode madalla Allah yarayamana queen”

Farhana ce ta harareta tace nikam banaso wlh”

Cab ina so ai raba arne da makami ibada ne, ya farhana”

Cewar afifa tafada tana kokarin daukar tata

Momy ce tace sai kibawa saa ai

Kiranta tayi tana kitchen tana aiki tafito ta tsuguna tace

“gani aunty farhana”

“To, azakwai naganki dauki atamfar nan kije kidinka”

“Nagode madalla”

“Dallacan godiyar taisa haka wuce kibamu guri
Kai yaisa haka farhana Cewar momy

Jalila ce ta kwashe nasu kayan tanufi daki

Najiba tana koma tafadawa su safiyya yadda sukayi da farhana inna jamila ce tace

“Allah ya shirya amma yarannan ban san irin su ba

Wlh inna sunfi hakama basu da mutunci yan iska kawai

Cewar ya rukayya yaya amina ce tadora da

Dama ni naje wlh Allah da sai sunci ubansu

Safiyya de batace kalaba saboda gaba daya sunfitar mata akanta

Assadiq bedawoba sai dare lokacin ya rukayya da ya amina suntafi sai najiba da inna a parlon safiyya kuwa tana toilet ya gaida inna najiba ma ta gaida shi yawuce dakinsa wayar sa ya dauka yakira layin safiyya sai da ta kusan tsinkewa sannan ta daga atakaice yace

“kizo ina dakina kitahomin da Fadilaty ”

” To”

Kayan bacci tasa tafesa turare tayafa mayafinta ta dau fadila ta fita

Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga yana daure da tawul yafito daga wanka hannu yasa yakarbi fadila ya dubi safiyya yace

“abincina fa”

“yana kitchen”

“dakko min shi nan”

Fita tayi taje ta dakko masa takawo taajiye a gabansa bata ce masa kala ba dubanta yayi yace

“safiyya ni zanzuba da kaina kenan “?

Zuba masa tayi tafara bashi abaki kamar yadda tasaba yaci ya koshi fadila ce tafara neman nono yadubeta yace

” kibata tasha mana”

Yafada yana kafeta da ido karbarta tayi tasata cikin mayafinta tafara bata nono dariya tabashi yace

“to ke me kike boyewa meye naki bansaniba yarinya yakamata kizama free”

Yanagama fada ya yaye mayafin yakura musu ido saboda yadda safiyya take shayar da fadila a hankali ya kira sunnanta

Sweet sopy pls ki saurareni mufahimci juna nagaji da shariyar da akemin yanxu kifadamin abinda yake ranki kinji

“mekakeso ince maka alhalin kasan komai”

Hmmm to shikenan akaddara nasan komai Allah ya baki hakuri abisa abubuwan da suka faru ayafewa juna baxaniya jure fushinki ba”

“Ai kaiya dadin baki shikenan ta wuce”

“yauwa matar Assadiq yanxu mexan samu

Kmr me kenan “?

Wani shuumin kallo yaimata Nan take tafahimceshi girgiza kai tayi tace

” Gsky aa Dee bayanxuba

Janta yayi jikinsa yashiga aikamata da sakonni gaba daya ya kidime karbar fadila yayi ya kwantar daita a gado yakuma kankameta gani tayi xai wuce iyaka tazare jikinta tadau fadila ta gudu dakinta lokacin najiba tai bacci xubewa yayi akan gadon yana Maida numfashi toilet yashiga yai wanka ya fito yasa kayan baccinsa ya kwanta da kyar yasamu bacci ya dauke shi tuna nin matarsa fal ransa

 

“kwanaki sunja yau safiyya tai arbain sun shirya tsaf zasuje gida inna jamila ma tahada kayanta ita da najiba Assadiq yaimusu kyautar girma sunnanta godiya safiyya ma haka gidan su Assadiq sukafara shiga suka gaisa da momy takarbi fadila suka tashi zasu tafi afifa takarbi fadila tace momy subarta anan zankaita anjima jalila ce tace

Haba afifa nawa fadila take da xakice abarta

Momy ce tace to meye aciki dan anbarta sai kace xaagutsireta

Su safiyya de na tsaye suna kallon ikon Allah. 🤔

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:6Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Ina biye da ku TALENTED WRITTERS FORUM a kullum hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

 

*Na sadaukar da wanga shafi ga kawuna da yarasu rana irin ta yau dafatan Allah yaimasa rahama yasa can yafi nan mu kuma Allah yasa muyi kyak kyawan karshe AMEEN*😰����🏻

 

 

 

*57*

 

 

~~~Assadiq ne yajisu shiru basu fitoba rufe motarsa yayi ya biyo bayansu yana shiga yatarar da su a tsaye cikin kosawa ya dubi safiyya yace

“Haba safiyya me kuke yine baku fitoba”

“afifa ce wai abar fadila zata kawo ta ”

” ina kenan”?

“ya Assadiq xankaimata ita anjima”

Dalla malama kawota saboda hauka sai a bar jaririya uwarta tana can wai me yasa baku da hankali ne”

“yaisa haka Assadiq nazaci anbaku yarku to kuje ba sai ka zagar min yaya ba”

“momy meyasa bakyason laifin yarannan ba dama ai musu magana sai kice ba haka ba ”

” Assadiq ku shige kutafi ya isa haka haba”

Safiyya ce ta dan rusuna tace “momy sai mundawo”

“Allah ya kiyaye hanya”

Suka sa kai suka fita jalila ta rako su bakin gate anan suka hadu da dady suka gaisa jalila tabashi fadila ya karbeta da farin ciki ya Maida da dubansa ga safiyya yace

“yata ya jiki?

“Da sauki dady”

“To madalla yanxu ina zasuje sadauki”?

Dady yau sukayi arbain shine zasuje gida akaiwa baafa fadila yayanta”

“to to yayi kyau kun kyauta, amma ita kanwar taku zata dawo ko”?

Safiyya ce tabashi amsa a kun yace “aa dady bazata dawoba”

To, balaifi angode kinjini Allah yai muku albarka”

Suka amsa da ameen kudi yazaro yabawa najiba sukai masa Godiya suka tafi jalila taja najiba gefe tabata wasu kaya a leda fal tai mata Godiya kai tsaye gida suka nufa bayan sun tsaya a wani super market sunyiwa su ummi siyayya tunda suka tafi ran Assadiq yake abace saboda abinda momy taimasa safiyya ta kula da yanayinsa kawai sai tai masa shiru har suka karasa gidan yana yin parking najiba ta fita bayan ta karbi fadila ko kayanta bata diba ba murmushi Assadiq yayi safiyya ce tamaida dubanta ga Assadiq takama hannunsa tahada da nata ahankali ta kira sunansa,

“Dee meyafaru naga kmr damuwa ta mamaye kyar kyawar fuskar ka mai cike da annri”

“karki damu sopy ba komai”

“Haba Dee yazakace haka bayan bahaka muka fito ba karfa kamanta damuwarka tawace ko kana zaton zansamu nutsuwa alhalin mijina natare da damuwa ”

Ajiyar zuciya yayi kana yace,” sopy ina takaicin halin da kannena suke miki na rasa dalilinsu nayin haka, bama wannanba kunyar ummi nakeji intaji zan kara aure baason raina zanyiba sopy”

“Dee pls kabar maganar nan yanzu saboda farin ciki na sai kasaba umarnin momy, to banyardaba saboda haka kadena damun kanka kaji mijin sopy”

“Nadena matar Assadiq yafada yana sakar mata kiss najiba ce tadawo diban kayanta ta kwan kwasa glass din Assadiq ne ya bude yace

“yar gidan ummi anje anga ummin “?

” Naganta ya Assadiq har yanxu baku shigoba ga queen can tafara kuka”

Da sauri safiyya tafita tai cikin gidansu tana shiga ta rungume umminta tana dariya ya amina ta dubanta tace

“safiyya xaki karyamana ummi fa”

“kai ya amina nawa nake ummi baffa fa

” yana ciki karshanta bacci yake”

Assadiq ne xai shigo su gaisa”

“To bari atasheshi kice ya shigo”

Fita tayi tashigo da shi ya tsuguna ya gaida ummi a ladabce yashiga dakin baffa suka gaisa suka dan taba hira yaimasa sallama yafito a tsakar gida ya tatar da su ummi yaimata sallama hade da godiya yafita bin bayansa safiyya tayi suka tsaya a waje yadubeta yace

“sopy xanwuce office xan dawo da magariba mutafi dan yau nafi ma ango xumudi dafatan xaabiyani bashina”

Dariya yabata tace, “Dee baka da damuwa zan kuma mallaka maka komai nawa a karo na biyu”

“Nagode Sweet sopy, sai na dawo a kulamin da Fadilaty”

“ok, ka kula da kanka”

Yawuce ya tafi yabawa yara kayan da ya siyo aka shiga dasu ciki dakin baffa tashiga ta gaida shi fadila tana hannunsa yaimata addua yace

Sannu safiyya Allah yakara lpy kinji”

Ameen baafa, dady yana gaisheka”

“ina amsawa kuna lpy dai ko”?

“lpy kalau baffa sai dai matsalar kannansa gashi momy ta matsa sai ya auri yar kanwarta”

“subahanalla to shikenan ba komai Allah yayi jagora ke de kiyi hakuri kinji ki rike mijinki da amana nayaba da hankalinsa nasan bazai wulakanta min ke ba”

“To baffa nagode”

Ummi ce tashigo ta tatar da fadila agurin baffa tace

“kigama xama a cinyar mijina yafi karfinki suhyla ma tayi ta gama”

Dariya sukayi yace “aa nafeesatu kedai kishi ne ke damunki suhyla matsoraciya ce, wannan kuwa wayo zatayi”

Su ka kuma yin dariya Dr almustapha ne yai sallama ya shigo safiyya yagani yai dariya yace

“safy saukar yaushe”?

“bamu jimaba Dr, ina kwana ya aiki?

“lpy kalau ya baby fadila”?

“lpy kalau”

Karbarta yayi ya gaida iyayansa yashaida musu yasami aiki a wani asibiti a garin abuja baffa ne yace

Masa Allah to yaxakai da nan garin kuma ko shikenan”

“aa baffa innaxo weekend xandinga xuwa”

“To, madalla Allah ya sanya alkhairi to, ya maganar aure kuma”?

“baffa na kusa nasami yarinya

“kamar gaske kullum xancan kenan”

Cewar ummi safiyya ce tai dariya tace,

“ummi dagaske Dr yasami matar aure”

“au ni nafada miki, xandai nemeki safiyya zamuyi maganar ”

” to Dr ”

” kar kabari inkuma yima maganar aure mustapha”

“aa to gwanda kafada masa da kanka ko yafi ji ”

” wlh ummina na kusa aikin gidan ma yayi nisa”

Allah yabada alkhairi” Cewar baffa
Suka amsa da ameen

Tashi yayi yafita aiki suma suka koma dakin ummi suka hadu sukaita hira ummi ma tai taimata nasiha najiba takiramata mai kunshi tai mata da kitso fadila tasha gata a gurin su ummi da magariba Assadiq yaxo suka tafi bayan tadan xaga danginsu

Tunda suka dau hanya Assadiq yaketa tsokanar ta ita dai murmushi kawai take a haka suka karasa gida suka baje a parlon sukaci abinci suka kammala ta kwashe kwanikan takai kitchen fadila ta dauka tai daki shima dakinsa yanufa yai wanka yashirya ya fito sai kamshi yake ya dawo dakin safiyya tana wanka sai fadila kwance a gadon ansamata kaya marasa nauyi anshafeta da powder yakarasa yadau keta rigingine yayi ya dorata a cikinsa yana taimata wasa tana dariya a haka bacci ya dauketa safiyya ce tafito daga ita sai tawul a hankali ya kwantar da fadila a gadon ta yakarasa gabanta hannunta yaja ya kaita gaban mu ya shafa mata mai da turare wani fitinan nan kallo ya kemata jikinta ne ya hau bari tace

“Dee dan Allah kabarni

“Ni tsoro nakeji kar inkuma samun ciki”

“baxaki samuba sopy ”

Janta yayi kan gadon yafara aika mata da sakon nni kuka tasamasa bema san tanayiba ya kidime kamar ranar yafara saninta a ranar safiyya ta wahala saboda sai da Assadiq ya fanshe kwana 40 dinsa da kyar yabata tasamu bacci fadila ce tafarka ya tashi ya dakko ta xuwa yayi yakarata jikin safiyya tasha nono ta koshi ya lallabata takoma bacci ya mayar da ita gadon ta Yadawo nasu gadon yaja sopy jikin sa bacci yai gaba dasu.

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[2:24Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*wannan shafin nakine ke kadai yar uwata hjy umma aymana*
*(aunty momy)*

*Nagode da shawarwarin ki gareni Allah yabar kauna na gaidaki kyauta*👌🏻

 

*TALENTED kuna wuta ina binku da fetir*🔥
*Hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

 

*58*

 

Da asuba safiyya tafarka taganta manne a jikin Assadiq zubawa kyak kyawar fuskarsa ido tayi ta ga kamar sa da fadila ta bayyana kamar kuma faruq har baccinsa irin na fadila ne dan karamin bakinsa ta sumbata ta zare jikinta a hankali ta karasa gadon fadila ta gyaramata kwanciyar ta tanufi toilet tai wanka ta doro alwala tafito Assadiq tagani a zaune a gefan gado kallon ta yayi da lumsas sun idonsa yace

“sopy ya baki tasheniba”

“Dee gani nayi kanata baccin gjy”

“Hmm to ai ke kika jamin gjyr ko”?

“Haka dai kace Dee”

Tafada tana kokarin saka doguwar riga da hijjabinta ta tayar da salla wanka yayi shima yafito yasaka jallabiya fara kal ya fita masallaci ta idar tafara axkar kenan fadila tafarka tun tana salla taji kushun kushun dinta tashi tayi tadakkota ta koma kan gado tafara bata nono kofa Assadiq ya turo ya tatar da su jallabiyar ya cire ya koma kusa dasu ya xauna leka fuskar fadila yayi yace

“Fadilaty binty, har kin tashi”

Nonon tacika ta dago ta kalleshi tasa dariya safiyya ce ta dauketa zata mika masa ita ta sa kuka cikin sauri Assadiq yace

“haba sopy itama rowar zaaimata kmr yadda akewa papanta ”
Pls ki bata tasha ta koshi”

“umm wlh Dee da zafi dan bakasan tso tso bane shiyasa kake fadar haka”

“eh naji bansan tsotson ba nidai abawa Fadilaty tasha ta koshi”

Sai da ta koshi sannan ta cireta karbar ta yayi yashiga mata wasa tanata dariya mai da dubansa yayi ga safiyya cikin murya kasa kasa yace

“Sweet sopy yazaai ne Assadiq fa yana neman second round”

“Dee pls kabarni haka kuna neman kuyi min rub dugu fa”

“Nidai gsky kibani kinji yafada kamar wani karamin yaro ido taxuba masa saboda yadda yake shagwaba tace

“ok karka damu mijin sopy ina zuwa jirani in zo ”

Tafada tana kokarin fita daga dakin kitchen ta nufa shikuwa komawa yayi ya kwanta ya kwantar da fadila a kirjinsa yanai tai mata wasa ahaka bacci yai gaba dasu safiyya kuwa tana kitchen tadora girki dankali ta feraye ta fara soyawa ta dakko kaji ta gyara ta tana na sannan tasamata hadaddan kuli kuli dayaji kayan kamshi da curry tasa mai tasaka a oven tagasa ta yanka albasa cyilize ta xuba ta dama kunun gyada hadadde tajuye a flaks da karami da babba tadafa shayi cikin awa guda ta kammala ta xuxxuba a flaks musu kyau tafito ta jera nasu a dining tabar ragowar a kitchen dakin ta koma ta tatar dasu sunata bacci sai suka birgeta toilet tashige tai wanka tafito ta tsaya gaban mudubi ta fara shafa mai ta fesa turare fadila ce tafarka da sauri takarasa tadauketa daga jikin Assadiq tasa masa pillow bandaki takoma tai mata wanka tafito tashafamata mai da powder tasamata kaya masu kyau green da fari tasamata farar safa tasamata farar yar karamar hula ta kayan ga gashinta yashsa mai antaje ta fesa mata turare ta kwantar daita takoma takarasa shiryawa wata shadda ta dakko marron colour tasa doguwar riga tasa yari da sarka kalar kayan tanada dankwalinta kmr gwaggwaro tayi kyau fadila ta dauka suka koma parlo ta kunna kallo wayar ta tadauka ta Kira layin jalila bugu daya tadaga tace

“Hello jalila kuntashi lpy

“lpy kalau aunty safiyya ina queen”

“lpy kalau saa tana nan

“Eh tana nan”

“ok kituromin ita zata karbar wa dady sako”

“ok tohm gata nan

Sallama sukayi baajimaba saa tazo tagaida safiyya taamsa da kulawa tasa hannu tadau fadila mikewa safiyya tayi tashiga kitchen ta hado kulolin a kwando ta mika mata ta dakko dari biyar tabata tace

“kice abawa dady, kudin kuma nakine ”

” Nagode aunty Allah yasaka da alkhairin, intafi da fadila ”

” aa babanta zai kawota”

“To, aunty ”

Fita tayi ta tafi Assadiq ne yafarka me makon ya ga fadila sai ya ga pillow murmushi yayi ya tashi ya nufi parlon anan ya gansu sunyi kyau ahankali yakarasa gabanta tsugunawa ya yi yace

” sopy san kai ko ki ka shirya keda yarki kika barni ko”?

“Dee kai ko daga rigima sai kai sai rufe kofa ”

” Ni din ko ”

” Eh”

“Fadilaty kinji mamanki ko ”

” yanxu dai muje inhada ma ruwan wanka kayi ”

” sopy inyi fa kikace au dama xancan daake fada gaskiya ne mata dakun haihu sai kudena bawa mazanjanku kula ”

Oh ni safiyya Allah yabaka hakuri muje intayaka”

Fadila ya dauka suka koma dakin ta hada masa ruwan wanka ta fito takarbi fadila ta kwantar da ita taja hannunsa suka yi bandaki yana shiga tafito ta rufo masa kofar dariya yayi yafara wankansa ita kuwa safiyya dakin ta gyara tsaf tadakko masa kaya masu kyau murda kofar yayi yafito karaswa ta yi ta mika masa karamin towel ya goge kansa suka karasa gaban mudubi tashafa masa mai ta taje masa gashinsa yasa kayan data dakko masa yasa suka koma parlo kulolin abincin ya bude ya dago ya Kalleta yace

Sopy ina inakikai wadannan girkin ”

” kana bacci mana Dee
Taxuba musu sukaci Assadiq yaita santi kammala wa sukayi ya tashi zai fita fadila ya dauka yatafi da ita gidansu bakin mota safiyya ta rarrashi tana ta xuba masa shagwaba ya lallabata ya fita

 

Saa ce tashigo dauke da kwando da kuloli momy takaiwa ta ce

“gashi momy abawa dady inji aunty safiyya ”

” meye aciki, bude mugani”

Budewa tayi tagani cewa tayi ta rufe ta karba momyn takaiwa dadyn yaita godiya tazubamasa yafara ci yana sawa safiyya albarka

Assadiq ne yashigo da fadila a hannun sa suka gaisa da mai gadi yaiwa fadila wasa Assadiq yaxaro dubu daya yabashi ciki ya shiga afifa ya tarar ta fito daga kitchen da sauri ta karaso ta karbi fadila ta gaida shi ya amsa ba walwala tambayarta yayi

“momy fa “?

” tana saman dady, ya Assadiq dan Allah kudi nakeso kabani”

“nawa kenan”

10k

A aljihunsa yaxaro yabata tasa hannu ta karba tai masa Godiya

Saman dady yanufa yai Sallama aka amsa ya shiga guri yasamu ya xauna ya gaida dady ya juya yagida momy taamsa da kulawa dady ne yatambayi fadila yace tana gurin afifa waya yaimata ta kawota

Muwadda ce tashigo cikin shiga ta alfarma da jalila ta hadu dauke kanta tayi tayi kamar bata gantaba sai abun yabata mamaki.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:35Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Ina bayanku TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine fa alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Dedicated 2 my Sweet sister ummy aisha* 👌🏻
*MIJINA sirrina*🌹

 

 

*59*

 

 

Cikin isa da takama ta dubi jalila tace

“jalila nafiskanci kmr raini yana kokarin shiga tsakani na da ke, ko zansan dalili”

“aa aunty Muwadda kmr yaya kawai de mamaki kika bani dana ganki dai dai wannan lokacin”

“Meye damuwarki da zuwa na”

“oho bansaniba gaskiya”

Afifa ce tafito da fadila a hannun ta tozali tayi da Muwadda tasaki faraa takarasa gabanta tagaidata dubanta tayi tace

“afifa babyn nan kmr yar faruq babyn waye”

“kai aunty Muwadda fadila ce fa yar ya Assadiq”

“wow kawota ai bantaba ganintaba”

“kuma ahaka kike ikirarin auran babanta”

Cewar jalila tafada tana gyara zaman farin glass dinta

“jalila kenan har yanxu bakisan Muwadda ba amma kiyi hakuri xaki sanni”

“ok ai gwanda kisanar dani ko nafahimta”

Wayar afifa ce takuma yin ringing tana dubawa taga ya Assadiq da sauri ta ta dubi Muwadda tace

“aunty Muwadda bari inkaita gurin dady”

“kafin kitafi ina momy take?

“tana saman dady, ya Assadiq ma yana can ”

” ok kice nazo”

“ok”

Tana hawa tamikawa dady fadila Assadiq ne yadubeta yace

“sannu afifa sai yanxu ko yayi kyau ”

” ya Assadiq aunty Muwadda ce taxo shiyasa nadan tsaya”

Rai ya hade kamar tana gabansa momy kuwa farin ciki ne yakamata tace

“tana ina Muwaddan “?

” tana kasa momy ”

” kice taxo ta gaida dady ”

” tohm momy ”

Sauka tayi ta ganta da farhana su nata hirarar bakinta takarasa gabanta tace

” aunty Muwadda momy tace kizo ki gaida dady ”

” ok muje ”

Tashi sukayi suka rakata ta gaida dady yaamsa da kulawa ya tambayeta abbanta

” lpy kalau dady ”

Momy antashi lpy”

“lpy kalau yata ina mama aisha”?

“lpy kalau momy tana gaidaki ”

” ina amsawa”

“ya Assadiq antashi lpy
“lpy kalau Muwadda”

Tashi sukayi suka sakko baajimaba momy ma ta sakko da fadila a hannun ta tayi bacci dakin ta takaita ta kwantar da ita tadawo parlon gurin su farhana ta dubi Muwadda dafatan dai bawata matsala ko

“eh to momy amma har yanxu narasa gane kan ya Assadiq ”

” kar ki damu yata da sannu komai zai dai dai ta”

“shikenan momy ba damuwa”

Hmmm aunty Muwadda mufa ke mukeso wlh kuma xamuyi alfahari da auranki”

Cewar farhana dariya Muwadda tayi tace

“haka ne farhana, to nagode da kaunar ku gareni ”

Dady ne yadubi Assadiq bayan ya kurbi kunun gyada yace

Sadauki kasami mata yar albarka wacce tasan darajar iyayenka bansan dalilin dayasa kukeson kara aure ba”

“Dady katayani da addua ita kawai nafi bukata a yanxu ”

” shikenan sadauki Allah yabada alheri, yaushe ne bakin kenan”?

“saura wata biyu dady”

“shikenan Allah ya kaimu ka kula da matarka inkasaba mata sadauki to fa kai da Allah”

“inshaallah dady xan kikayaye dady inason xuwa gurin faruq ”

” yakamata kam to sai kafara shiri ”

” to dady xannemi visa ayau dinnan dan yanata mita anmanta dashi ”

” Hmmm sarkin rikici kenan ”

Tashi yayi yaimasa Sallama yadakko shima dadyn shirin fita yafara yi Assadiq yana sakkowa yai tozali dasu Muwadda ido taxuba masa saboda yadda yai kyau tanason Assadiq amma tafison muktar momy ya kalla yace

” momy xanwuce office
“Assadiq bakaga Muwadda ba “?

Momy ai naga mungaisa sauri nake wlh”

“momy nima wucewa xanyi”

“tun yanxu yata, to kasauketa a gida ”

” shikenan momy sai na dawo ”

” Allah ya kiyaye hanya tura rurruka momy tabawa Muwadda su farhana suka rakata gurin mota sai da sukaga tafiyarsu sannan suka koma jalila kuwa saman dady ta hau ta dakko ragowar abincin da safiyya ta kawowa dady ta sakko dashi tabaje tafara ci farhana ne tafara shigowa taganta tace

“ya jalila wannan kayan dadinfa daga ina “?

” inzakici kawai xauna malama banson yawan magana”

Xama tayi afifa ma haka sukaita santi afifa ce tace

Gsky momy taiya gasa kaza ”

” momy ko aunty safiyya ”

Cewar jalila da sauri farhana ta dubeta tace
” mtsww wai ita ta kawo saboda makirci ”

To mara kunya ki iya bakinki inba hakaba kuma xai kai ki yabaro ki”

Tana gama fada tai gaba dariya sukasa rada afifa taiwa farhana suka tafa

Tun ahanya Muwadda taketa kokarin Assadiq bayason zuwa gurinta

“Muwadda bani da lokacine amma innasamu xanxo ”

” kullum haka kakecemin sweery, yanxu wane shiri kakewa bikinmmu sonake ayi bikin yayan gata ”

” Hmmm ko to ai kin makara tunda ni dai bayaro bane kinga kuwa dole intakaita ”

Wayar safiyya ce tashigo bugu daya yadaga

” Hello Sweet sopy, yanabarki dafatan bamatsala ko “?

” Dee sai kewarka data sakoni a gaba, yanxu kana ina “?

Maida dubansa yayi ga Muwadda yaga ta kafeshi da ido cikin wata iriyar murya yace

Ina hanyar office”

“ok Dee ka kularmin da kanka kaji ”

” To matar Assadiq angama kema ki kula da kanki da Fadilaty ”

” Tohm”

Sukai Sallama yakashe wayar Muwadda ce takulu xatai magana kenan yadaga mata hannu

“pls Muwadda karki bani ciwon kai da safannan dole sai kinyi hakuri”

Shiru tayi tamaida kanta gefe a dai dai gate dinsu yayi parking dubansa tayi ”

” sweery baxaka shiga ka gaida mama ba “?

” Muwadda sauri nake ki gaisheta karki damu xan dawo ”

” ok badamuwa sai najika ”

Taballe murfin motar ta fita tausayi tabashi yadda ta damu da shi amma har yanxu ba sonta a ranshi motarsa yaja yatafi be jimaba ya karasa office da abokinsa yaci karo Abdullahi achida ta fawa suka yi ya dubeshi yace

” kaga mijin safiyya da Muwadda baba ga fadila ”

” to karamin dan iska fadi kakara fada kade xauna ka mutu bakai aureba ”

” chairman laifin kane ai nace kabani daya daga cikin kannanka kaki ”

Kai musu tanufa malam”

Dariya yayi suka shiga office din kaitsaye,

Tun fitar Assadiq daga gidansu afifa tashirya ta fita gidan safiyya ta nufa tana xuwa ta tatar da ita a parlon tana kallon mbc drama remote ta dauka tacanja tasha bata kulataba can ta dubeta tace

Amm aron motarki xakibani xanbawa saurayina xamu fita tasa ce tasami matsala ”

Da yaushe xaki fita”?

” da yamma ”

” ok mukulin yana gurin Assadiq sai dai Yadawo ”

” Badamuwa ”

Fadila aka kawo tanata ihun kuka a gigice safiyya ta tashi taleka farhana tagani da fadilan a hannu.

 

 

 

 

 

07037732029 👈🏻

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:33Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W>F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*wannan shafin nanakune KANNAN* *MIJINA GROUP* *NASEEBA*
*NAGAIDAKU*🙋🏻

 

*TALENTED WRITTERS hadin* *kanmmu shine* *alfaharinmmu a*
*Kullum*🤝🤝

 

*6o*

 

Cikin sauri safiyya ta dubi farhana hannu ta sa takarbi fadila tace

“farhana kukan me take haka me yaasameta”

“Aa ya zaai insani kawai rigimar tace, keku bakiji ma kunyar tambayata ba sai kace ba yarki ta fari ba haba ai kara nada dadi”

“ke farhana ni kike fadawa haka saboda natambayeki meyasameta to intambayeki mana,duk cikin ku akwai wanda ya haifa min fadila da zakiyimin rashin kunya ”

” Hmmm babu to ai yayana nane ya haifeta ko zaki haifeta ke kadai ”

Cikin zafin nama safiyya ta dauketa da mari tace Dan kunga ina kyaleku shine xaku dinga yimin cin kashi ko to wlh ba xaku taba min ya kuci bulus ba mara mutunci kawai”

Tana gama fada tai gaba tabar farhana dafe da kunci kuka tasa afifa tafito daga parlon taga farhana na hawaye tambayarta tayi

“ya farhana me yafaru me taimiki aunty safiyyan?

“marina tayi kuma wlh baxan yardaba”

“lallai wlh kije kkfadawa momy”

Fita sukayi suka je suka shirya karya da gaskiya momy tai ta uban fada saa ta kwadawa kira da hanzari takaraso ta tsuguna tace

” momy gani ”

” kije gidan Assadiq kicewa matarsa meye dalilinta na dokarmin ya ”

Tashi saa tayi ta tafi tana mamakin halin momy tana karasawa ta jiyo kukan fadila har a lokacin safiyya tanata faman rarrashi Sallama tayi tashiga ta gaida safiyya taamsa ta gabatar mata da sakon da aka aikota safiyya ce ta dubeta da mamaki tafadamata yadda sukayi da farhana saa ce tace

“wlh aunty akan kujera ta kwantar da ita tafado”

Cikin raxana safiyya ta zaro ido 😳tace to saboda Allah ta kyauta kenan shi kenan to momyn tasan tafadi”?

“tasani aunty ”

” to kice tayi hakuri”

“aa aunty safiyya kefa aka cuta kuma kice abasu hakuri”

“To saa mexance”

“aunty safiyya kiyi hakuri da halin kannan mijinki nasan kinayi”

“bakomai saadatu ai suma matane xasu dandana ji inda dadi”

“Hakane aunty bari intafi kar momy tajini shiru”

Safiyya ce ta Maida hankalinta ga fadila tai mata tik tana duba jikinta tana taba hannun ta ta dada tsanyara kuka safiyya tarasma mexataimata can ta dakko missileta ta shafamata ta samu ta bata nono takarba tafara sha da taki karba cikin ikon Allah bacci yai gaba daita goyata tayi ranta yai masifar baci tunani tashiga yi wai metayi wa *KANNAN MIJINTA*ne bata da wannan amsar

Saa tana komawa tafadi sakon safiyya na cewar tayi hakuri cikin fushi tace

Abani hakuri kenan tana sane ta dakar min ya, to yayi kyau”

“wlh momy sai tasan ta mareni sai nabata mamaki”

Cewar farhana tafada tana dada kwanciya jikin momy afifa ce

“wlh matar nan ta mike kafa kawai dan yar ta tayi kuka sai ta mareki ”

” daga kan kujera fa ta fado cewar farhana karaf akunnan jalila cikin sauri ta dubi farhana tace

“farhana badai fadila ce tafadi ba ”

Ita ce mana daga kwantar da ita akujera inje kitchen indawo garin mutsu mutsunta tafado”

“garin dai sha shancin ki dai banza inke kika haifeta xakibarta tafado ne ”

” yaisa haka jalila xatai dagan ganne ko kinfimu santane eye to abar maganar”

Cewar momy tafada tana kokarin tashi daki jalila ta wuce domin amsa wayar daake mata

Dr almustapha ne yake fada mata cewar xai xo da yamma shiru tayi can tace

“Dr amma a gidan aunty safiyya”

“acan kikeso muhadu”?
“Eh”

“ok sai naxo”

Sallama sukayi littafi ta dauka tafara dubawa ahaka bacci yai gaba daita

Abangaran safiyya kuwa hankalinta ne yatashi yadda taji xaxxabi ya rufe fadila kwantar da ita tayi ta lullibeta takoma kitchen tafara hada girkin dare tuwon shinkafa tayi miyar agushi tahada lemon kwa kwa ta kamalla tajera a dining ta gyara a kitchen har lokacin fadila bacci take wanka tayi tashirya cikin wani bakin material doguwar riga tadanyi kwalliya kadan dakin Assadiq ta koma tafara gyarawa Assadiq ne Yadawo kai tsaye dakin safiyya yanufa yana shiga yai gun fadila tafarka tanata kalle kalle da sauri Ya dauketa jiyayi jikinta zazzabi da sauri ya shiga kwadawa safiyya kira

A parlon sukai kacibus cikin kidima ya tambayata

“safiyya meyasami Fadilaty naji jikinta xafi ”

” sannu da xuwa Dee”

“yauwa inajinki”

“tunda aka kawo ta daga gidan momy take kuka in antaba hannuta xata sa kuka”

“safiyya karfa yarinyar nan faduwa tayi ”

Shiru taimasa hannun ya taba ai kuwa sai kuka, shiru yayi can yace

” samata kaya mutafi asibiti”

Kaya ta samata masu dumi tafesheta da turare kuka take ta faman yi kallon ta yayi

“sopy bata tasha kafin mutafi”

“Dee taki sha da kyar ma nasamu tasha daxu”

“kide bata mugani”

bata ta kuma yi kin karba tayi karbarta yayi suka fita safiyya ce ta rufe kofa a mota tasamesu karbarta tayi yajasu suka nufi asibiti likita yadubata ya tabbatar musu faduwa tayi Assadiq ne ya maida dubansa ga safiyya yace

“safiyya ya akai tafadi”

“Dee bansaniba nima haka aka kawota”

Magani aka rubuta musu suka je suka siya suka koma gida dakansa yabata maganin yarungumeta take tai bacci yayan safiyya ne yaimata waya yana waje Assadiq tafadawa yamikamata fadila yafita yashigo da shi da cewa yayi baxai shigo ba xance yazo gurin jalila dariya Assadiq yayi yace

“Dr ai gwanda kashigo mu gaisa”

Shiga yayi suka gaisa safiyya ma ta gaidashi yakarbi fadila jiyayi jikinta xafi yadubi safiyya yace

“safy yanaji jikinta da fever anbata magani”

“Eh ya yanxu muka dawo daga asibiti”

“ok”

Maida dubansa yayi ga Assadiq yace

“Assadiq naxo da kokon bara ta dafatan zaabani auran jalila”

“Aa me xai hana Dr amma naji dadi sosai Allah ya tabbatar da alkhairi”

Suka amsa da ameen safiyya taje ta kawo masa lemo yadan sha kadan yafita xuwa bakin gate waya yaimata baajimaba ta karaso tacaba kwalliya tayi kyau nan suka sha hirarsu suka kulla alkawarin aure yaimata Sallama yatafi yabata kudi da kyar ta Karba yaiwa su safiyya ma Sallama ciki jalila ta koma suka gaisa da safiyya ta bata hakuri akan faduwar da fadila tayi karaf akunnan Assadiq take ransa yabaci kai tsaye gidansu yanufa yana xuwa yasamesu a Parlo marin farhana yayi nan ta fasa ihu da sauri momy tafito tana xuwa ta daga Assadiq yanata faman masifa nan ta daka masa tsawa ta rufe shi da fada take tsanar safiyya ta nunku aran farhana cikin fushi yabar gidan kai tsaye gidansa yawuce yasami jalila nacin abinci fadila ya dauka yai dakansa jalila nagamawa taiwa safiyya Sallama ta tafi kayan abincin safiyya ta dauka takai masa daki cikin bacin rai taganshi da kyar tasamu yaci abincin sukai salla sukai shirn bacci can cikin dare xaxxabi ya rufe safiyya saboda yadda fadila taki shan nono yaciko yadameta gashi kwana fadila tayi tana kuka Assadiq Hankalinsa yakasu biyu sai gefin asuba yasamu fadila tai bacci.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[9:38Pm,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*TALENTED WRITTERS kuna kamshi ana binku da humra cewar kamshin TALENTED*🤣

*Hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*masoyana ina godiya da adduoinku gareni nagode sosai da kulawar ku gareni Allah yabar kauna ina sonku Fadilaty binty na gaidaku kyauta*👌🏻😘

 

 

*61*

 

 

 

~~~Bayan kwana biyu fadila tasami sauki haka safiyya ma amma ta rage kaita gidan su Assadiq yarinyar tayi wayo ta girma ga kyau gwanin shaawa yau Assadiq ya shirya dan tafiya kasar dubai tun safe safiyya ta tashi tai masa danbun kaxa da yawa tadibarwa momy tabayar aka kaimata daki ta koma ta tatar da Assadiq na hada jakarsa ta kaya cikin shagwaba ta dubeshi tace

“Dee baxaka bari in xo in hadama kayan ba”

“I am so sorry Sweet sopy naga kina aiki ne shi yasa”

“Dee gsky xamuyi kewarka da yawa ni baxantaba iya bacci ba inba a faffadan kirjinkaba”

Tafada tana shigewa kirjinsa bazato tafara rera kuka kidimewa Assadiq yayi dada matseta yayi a kirjinsa yafara kissing dinta mayar masa tafara yi cikin kwarewa xip din rigarta ya xuge nan ya dada gigice wa akan gado suka xube Assadiq yagama ki dimewa nan suka shiga farantawa junansu sun barje kmr sababbin aure basa taba gjy da junansu domin safiyya jaruma ce tana jure bukatar mijinta shiyasa yake dada sonta sai da komai ya lafa sannan ta hada musu ruwa sukai wanka nan ma sai da suka kuma shan soyayyar su kukan fadila ne yasa Assadiq saurin daura towel yafito ya xo yadauketa yana daukarta tafara yimasa dariya shima dariyar yaimata yafara mata wasa safiyya ce tafito itama daure da towel ta dubeshi tace

“Dee kawota aimata wanka”

“papanta ne xai mata ko Fadilaty binty”

Kmr taji shi tai dariya

“Dee karfa kasamata yaji a ido tom”

“lallai ma sopy bari kiga yadda uba xai wanke yarsa”

Ban dakin yanufa ya hada ruwan xafinsa ya tsoma fadila ya shiga yimata wanka tana tai masa dariya ahaka ya kammalamata tsaf yanadota a towel dinta yana fitowa ya tarar safiyya ta shirya tsaf cikin wata ash din atamfa riga da siket rigar ta kamata ido kawai Assadiq ya xuba mata yace

“matar Assadiq kinyi kyau anyawa kuwa bafasa tafiyar nan xanyiba”

Lala Dee baruwana kace xaka sa faruq dan karamin hauka”

“to yaxanyi nariga nafadamasa ina tafe amma xanyi kewar fadilaty ”

Dariya kawai safiyya tayi yashiga shafa mai ya Shirya cikin brwon din shadda safiyya ta shirya fadila cikin wasu riga da siket pink tasamata safa tagyarata tsaf kuka tafara Assadiq ne yadubi safiyya yace

” sopy kular min daita mana”

“Dee rigar ce ta matseni narasa yadda xanyi inbata tasha”

“cab ashe kuwa xan yaga rigar”

“pls xugemin zip din kaji”

Zuge mata yayi ya kuwa xuba mata ido tashiga shayar da fadila suka bashi shaawa can ya nisa yace

“Sweet sopy nima xansha”

Yafada yana kashemata ido ido taxaro tace

“Dee ka girma fa

dariya yayi yakarasa shryawa fadila ce tai ta kallon sa daukar ta yayi safiyya tai musu hoto aka gama yamikawa safiyya ita taki xuwa dariya sukasa yace

“Fadilaty binty ta gane papanta bari intafi da ita gidan momy daga nan xanje ingaida baffa tunda sai dare jirginmmu xai tashi ”

” Dee pls in shrya mutafi tare ”

” Aa”

Fita yayi ya nufi gidansu yasamu momy tana cin danbun kaxar da safiyya ta ai kamata ya mikamata fadila ta karbeta suka gaisa duban dan nata tayi tace

“badai tafiyar ta zoba ”

” aa momy sai dare xan je gidansu Muwadda ne ”

” kai amma ka kyauta Assadiq Allah yaima albarka ”

” Ameen momy na, dady fa “?

” ya fita wani bako yayi daga sokoto suka xo shi da dansa babban dan ixala ne a can a unguwa uku suka sauka ”

” ok ko malam mudassir ne ”

” tabbas shine ”

” momy bari inje sai na dawo”

“to, Assadiq Allah ya kiyaye”

Yana mike wa fadila ta fara kuka juyawa yayi yace

“Haba Fadilaty binty momy kuma xakiwa kiwa”

“tafara wayo ai”, cewar momy jalila ce ta dauketa akai Saa ta hakura yasa kai yafita gidan su safiyya yafara xuwa ya gaida iyayenta yace najiba tazo ta taya safiyya kwana xaiyi tafiya ummi tace

“najiba bata nan Assadiq taje rano gidan kanwar baffansu ”

Yaamsa da to yabata kudi takarba da kyar yaimata Sallama yatafi gidan ya hannatu ya nufa taita murna su nabil suka kankameshi yana tambayarsa

 

uncle A ina Mata ta”?

” tana nan kalau nabil ”

Assadiq ashe dubai xaka yau she ne tafiyar”

“yaya anjima ne ”

” xaka hado lefan amma ”

” aa gsky ”

” ok Allah ya kiyaye agaida faruq ”

Xaiji”

Ta bada kilishi da yawa akaimasa yaxaro kudi yabata taimasa godiya sukai Sallama yatafi

Be xame ko inaba sai gidan su Muwadda yai Sallama yashiga tana kwance a cinyar mamanta cikin shiga ta kananun kaya da sauri ta tashi ya gaida mamanta murna fal ransu tasa aka kawo masa lemo ta tashi tabasu guri suka gaisa suka dan taba hira yafada mata tafiya xaiyi tace

“kasiyo min kit din kayan kwalliya kaji sweery ”

Hmmm ok”

Ya tashi xai tafi mama tafito sukai Sallama ya xaro kudi yabata a bakin gate yahadu da abban Muwadda suka gaisa yaja motarsa yatafi

Yana xuwa gida wanka yayi yaci abinci yafara shiri fadila kmr tasan tafiya xai yi ta makale masa achida yai wa waya yaxo ya kaishi airport baajimaba yakaraso nan fa suka kule adaki shi da safiyya suka rungume juna safiyya sai kuka yadagota yana sharemata hawaye yabar mata kudi masu yawa yace su farhana xasu xo sutayata kwana gabanta ne yafadi suka fito xuwa gurin mota achida ya karbi fadila suka gaisa da safiyya ya mikawa Assadiq ita yadaga ta sama Fadilaty binty papa xai yi missing dinki yabawa safiyya ita suka ja motarsu suka tafi yana daga musu hannun safiyya tana ta share hawaye haka fadila kuka

Gidansa ya tsaya yaimusu Sallama yaiwa dady ma yarabawa kannansa kudi da masu aikin momy yafadawa su farhana suje su dinga taya safiyya kwana sunajin haka suka fara murna xasu sami damar musgunawa safiyya

 

Karfe tara jirginsu Assadiq ya tashi ✈

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
. [6:42Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd Allah yakabamu alkhairin da yake cikin wannan gwala gwalan ranaku ameen*👏🏻👏🏻

 

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

*Ina rokon Allah yakara miki lpy kawata faeex talented kina raina naseeba talented na miki sannu Allah yasa kaffarane ameen*😘

 

 

*62*

 

 

~~~Safiyya na shiga daki ta kira umminta bayan sungaisa take tambayarta fadila tace

lpy kalau ummi, ummi Assadiq ne yaitafiya shine kannan sa xasu sutayani kwana wlh ummi fargaba nake nasan baxamu wanye lpy ba ”

” eh daxu yaxo safiyya da cewa yayi najiba tazo ta kwana to ta tafi rano gidan innarku amma abinda nakeso da ke shine kiyi kokarin kyauta ta musu kinji ki dauke kai kiyi ta hakuri safiyya wataran sai labari ”

” to, ummina nagode agaida baffa da ya amina xanxo cikin satin nan ma”

“xasuji keda mijinki baya gari ina xaki fita”

“kai ummi ai xanmasa waya ai ”

” To Allah yakawoki ”

” Ameen ummina ”

Sukai Sallama ta kashe wayar waya taiwa jalila sutaho dan Allah hakuri tabata cewar bata da lpy amma gasu farhana nan tai mata sannu baajimaba suka xo cikin faraa safiyya ta taresu sai cika suke suna batsewa farhana ce tamika hannu xata dau fadila tasa kuka dunguremata kai tayi tace

“au ni xakiyiwa kiwa lalle to bari kiji yarinya ni uwar ki ce dolen ki kuma”

“aa to fadamata ya farhana kinsan fa su yaya sunfison dangin uwarsu alhalin dangin uba sune suka fi karfi ”

Cewar afifa kenan safiyya dai yarta ta dauke xatai daki farhana tadubeta tace

” Aa aunty safiyya yunwa fa mukeji”

“Gsky bani da abinci sai dai danbun kaxa da yagot inxakuci in kawo muku ”

” to muda mukejin yunwa ina mu ina cin wani danbun kaxa da yagot kayan kwadayi, gsky kimana girki ”

” yi hakuri mana farhana ai kitchen din ba bakonku bane xaku iya shiga ku dafa ”

Tai tafiyarta daki tafara shirin bacci tashi sukayi suka dora indomie sukai kaca kaca da kitchen din har da fasamata cups suka juyo ta parlo suka dawo suka ci kadan suka barta anan dakin suka shiga sukai wanka lokacin safiyya tayi bacci rungume da fadila afifa ce tace

“ya farhana a ina xamu kwanta mu dan wannan gadon yaimana kadan ”

” au afifa xamu kwana akasa ne ai wlh tashinta xamuyi ”

Aikuwa tashinta sukayi wai dole sai tabar musu gadon ido kawai ta xuba musu ta dau yarta ta fita ba kunya suka kwanta dakin Assadiq takoma ta kwanta kewar mijinta tadawo mata karatun kuraani ta kunna take bacci ya dauketa

Bata farka ba sai asuba ta tashi tai salla tayi axkhar fadila ce tafarka goyata tayi tanufi kitchen kaca kaca taga sun mata da shi tarasama taina xata fara cikin kankanin lokaci ta gyara komai ta dora musu break daya da kwai tayi sai farfesun kifi ta dafa tea ta kammala tajera a dining tafito ta gyara parlon takunna turaran wuta dakin Assadiq takoma tagyara tai wanka taiwa fadila taje dakinta tadebo musu kaya har lokacin bacci sukeyi ta tashesu sukai mata banza tafiyarta tayi ta shirya tsaf tashirya fadila ruwan tea tafito tasha takoma daki suka koma bacci su afifa basu farkaba sai wajen 10 wanka sukayi sukai salla wardrobe din safiyya suka bude suka dau sababbin atamfofinta suka sa sukai kwalliya parlo suka fito xama sukayi sukai break fast suka barmata doya guda uku miyar kuwa du suka shanye tashi sukayi suka kunna kallo safiyya ce tafito dan yin break mexata gani kayanta ne a jikin su sababbi ma sharewa tayi tadubesu tace

“kuntashi lpy ”

” mungode Allah, ina sarkin kiwa ”

” bacci take dafatan kun karya ”

” ummm mun karya ”

Karasawa tayi da xummar karya wa ba komai sai ragowa haushi ne yakamata tace

” ya baku cinyeba ”

” munkoshi ne ”

Kwanikan ta kwashe takai kitchen kunun gyada tadama tasha haka suka kadai jikinsu suka tafi

 

Abangaran Assadiq kuwa yasauka a dubai faruq ne yaxo daukar Assadiq shi da abokinsa fahad yana ganin Assadiq ya rungume shi yana murna tambayar sa yayi

” yaya Assadiq ina yata fadila ”

” lafiyar ta kalau faruq, duk suna gaidaka”

Fahad ya gaida Assadiq suka rankaya suka tafi hotel din dasukai masa buking suna isa faruq ya karbi wayar Assadiq yafara ganin hotunan fadila yaga takara girma tun daga ranar faruq ya tattaro kayan sa daga school Yadawo gurin Assadiq da xama

Assadiq ya kira safiyya yafadamata yasauka cewa yayi takarawa fadila wayar magana yafara yimata

“Hello Fadilaty binty ya kike ya kewar papa haka dai yai taimata magana karshe sukai Sallama

Haka dai safiyya tai tafama da su farhana

Yau shiryawa tayi ta tafi gidan su Assadiq kwai tasiya takai musu tasaiwa dady turare masu tsada dady yai farin ciki sosai da ganinsu momy kuwa ba yabo ba fallasa su farhana ne suka bata kayan dasuka sa nata tace su barshi tabar musu can xuwa anjima ya hannatu ma tazo gidan gwanin shaawa momy tarasa inda xata sa jikokinta ya hannatu takarbi fadila ta rungume ta nabil yanata murna yaga matarsa nan suka yini da yamma tai musu Sallama takoma gida ta aikowa dasu nabil kayan wasa nan su momy suka fara tattaunawa kan bikin Muwadda

 

Yau satin Assadiq biyu a dubai tun safe safiyya take shirin tarbar sa tanata girki girke Assadiq kuwa da kyar faruq yabar shi suka rabu cikin kewar juna yace da yagama karatunsa nan da shekara daya xai taho

 

Safiyya ta gyara ko ina tayi kunshi da kitso ta gyarawa fadila kai da ribons masu kyau kitchen ta koma tana xuwa taga farhana ta saukemata girki ta dora nata girkin wai danbu xata yi gashi jirgin su Assadiq ya sauka.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:26Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*wannan shafin nakine kanwata umyma inai miki fafan alkhairi Allah yakaiku lpy yabaku arfa mai sauki baxan iya misilta irin kewar dazanyi ba sai dai fatan Allah yabani juriya*😰💕

*Hajiya 2 bee*🕋

 

 

*63*

 

 

~~~cikin bacin rai tadubeta tace

“farhana meye haka xaki saukemin girki bayan gas dinna ba daya bane”?

“to ai gani nayi daya barin ba ya ci sosai ni kuma sauri nake baki xanyi ”

Wani baxan kallo safiyya ta watsa mata ta sauke ta maida nata girkin ta dora mata a daya barin rashin kunya tafara yimata tai mata banza karshe ko danbun bata kula ba tai tafiyar ta safiyya kuwa ta kammala aikin ta tsaf ta jera a dining takarasa mata danbun ta juye a kula taiwa jalila waya ta turo mata Saa data xo tabata takai mata.

Karfe 3:00 achida Yadawo Assadiq gida cikin sauri ya shiga parlon yana tozali da safiyya ya ware hannusa cikin farin ciki tafada jikinsa ya rungume ta yana shakar kamshin turaranta cikin kewar juna yace

“Sweet sopy ina Fadilaty binty ”

” ta gaji da jiran papa tayi bacci”

Sakinta yayi ya nufi dakin tana cikin gadonta tana bacci daukanta yayi ya rungumeta cikin farin ciki ya kira sunnanta

“Fadilaty binty wake up ur papa was return”

Mika yaimata ai kuwa ta bude idonta ta kuramasa ido kuwa sai kuma tai dariya mai da dubansa yayi ga safiyya yace

“sopy mekike bawa Fadilaty ta girma ga wayo ”

” Dee ba komai, amma ina ganin ankusa fara bata abinci”

“banyarda ba abata nono kawai ”

” Dee wlh yanxu baya isarta ”

” shike nan sopy ”

Sai yanxu ya tuna yabar abokinsa a waje fita yayi da fadila a hannun sa acikin mota yasame shi yana ta danna wayarsa ya dubeshi yace

” afuwan abokina nabarka kasan in ina gaban sopy manta komai nake”

“Gskyr magana abokina aure xanyi saboda nima inhuta inhade jikina guri daya”

Ya karashe xancan yana karbar fadila a hannun Assadiq

Dariya Assadiq yai taimasa sai da yayi mai isarsa sannan yace

“abokina kaji maxa waya fadama xaman goranci abu ne mai dadi”

“chairman mubar maganar wasa pls kabani afifa in aura ”

” Dagaske kake achida nasan sharrin ka fa ”

” I am serious chairman ”

” ok xamuyi maganar da momy, yanxu dai taso mushiga ciki kaci abinci ”

” wlh kmr kasan yunwa ce fal cikina dama hajiya bata nan”

“to gauro, bude min but inkwashe tsarabar mata ta data binty”

“chairman kenan nima ankusa xama baba”

Yafada yana kokarin fita daga motar taimaka masa yayi suka shigar da wasu akwatuna musu kyau har guda shida sai wasu guda biyu daban

Safiyya ce tafito sanye da mayafi suka gaisa da achida ta zuba musu abinci fadila ta karba ta koma daki nan suka fara cin abinci dukkansu sunji dadin abincin achida kuwa sai zuba santi yake suka kammala ya mike dan tafiya turaruruka Assadiq yabashi yaiwa safiyya Sallama yatafi ciki Assadiq ya koma safiyya xata hada masa Ruwan wanka kenan yajata jikinsa dubansa tayi tace

“Dee wanka fa?

“Bashi xanfara ba sopy ke nake bukata baki san daurewa kawai nake ba”

Kunya yabata ta sinne kanta a kirjinsa rada yaimata a kunne tasa dariya ta shige daki da gudu binta yayi a ciki ya cimmata ya kankameta a gado suka zube yashiga sarrafa ta cikin kwarewa

_nikam dakin sopy na koma na kula da Fadilaty_🤣

 

Sai da komai yalafa sukai wanka kmr yadda suka saba yashirya cikin kananun kaya yayi kyau kmr saurayi ya kwashi tsarabar su momy yafita bayan yabawa safiyya tata nan yabarta tanata duba kayan dana fadila akwati guda da tarkacan kayan wasa

Yana fita kai tsaye gidansu ya wuce abakin gate suka gaisa da malam sule mai gadi yaimasa sannu da xuwa ya wuce ciki a parlo yasami momy afifa na matsa mata kafa Sallama yai musu yasami guri ya xauna dadi ya cika momy ya gaida ta taamsa da kulawa ta tambayar tayi faruq

“lpy kalau momy yana gaida ki ”

” ina amsawa, ina yar rigima tunda katafi sau daya aka kawota ”

Lpy kalau take momy

Yafito da tsarabar su yabasu lesina ne musu kyau kyau da takalma sukai masa Godiya maida dubansa yayi ga momy yace

” momy daman abokina ne yakeson afifa da aure shine nace yajira infara tuntubar ki tukunna”

“waye kenan”?

“Abdullahi ne momy ”

” to ai gata nan inta amince shikenan ai yana da kirki ”

” Gsky momy banason sa ina da wanda nakeso wlh ”

” afifa ki dubi kwayar idona kice bakya son abokina ”

Yayi kyau afifa nagode ”

“abar maganar Assadiq tunda bata sopy, anhada lefan Muwadda sati mai xuwa zaa kai befi asa sati hudu ba”

“Allah yakaimu momy ”

” Ameen bari a dakko ma kayan kagani ”

” aa basai naganiba momy, bari inje mugaisa da dady ”

Mikewa yayi yanufi dakin dady yana kashin gide da kayan fruits agsbansa da Sallama yashiga yasami guri yazauna hade da tankwashe kafarsa ya gaida shi cikin girmamawa hannu ya mika masa kmr kullum ya noke yace

” sadauki andawo lpy ya kabaro faruqu ”

” lpy kalau dady yana gaida ku ”

Muna amsawa ina kabar matar tawa”

“bacci take shiyasa bamu taho tare ba ”

” to madalla momyn ku tafada min cewar nan da sati biyu xaa kai lefan Muwadda ko ”

” eh dady yanxu nima tafada min ”

” to Allah yabada alkhairi sadauki kazama jarumi a gidanka kaji ”

Ameen inshaallah dady, nagode”

Ya bashi turaruruka masu kyau da tsada yai masa Godiya Sallama yaimasa ya tashi yatafi

 

°°°°°°°°°°°°°°°

 

Yau tun safe aketa aikin girke girke a gidan su Assadiq saboda bakin da dady xaiyi malam mudassir ne xai kawo wa dady xiyara 12 dai dai suka iso da murna dady yataresu a sit room ya saukesu nan suka gaisa cikin girmamawa matashin dansa ya gaida dady momy tashigo suka gaisa su farhana ne suka dau kayan abincin suka tafi kai musu da Sallama suka shiga jalila ce tafara shiga sai afifa farhana ce karshe tunda tashiga matashin saurayin yake kallon ta suka tsuguna suka gaisa da malam mudassir ya amsa da sakin fuska dady ne ya dubesu yace

Baku gaisar da yayan ku ba ”

Gaida shi sukayi suka hada ido da farhana take gabanta yafadi murmushi ya sakar mata suka tashi suka fita suna fita malam mudassir ya dubi dady yace

” alhj muhammad mexaihana abawa ibraheem auran daya daga cikin yanmata nan kaga dangantakar mu tadada kulluwa addua ibraheem ya ke aransa Allah yasa abashi ta ukun nan dady ne yadubi abokanansa yace

“amma naji dadi sosai ina ganin sai ahada shi da farhana ”

” wacce ce farhana “?

” tabayan mai doguwar riga ”

” to Alhmdulillah naji dadi sosai Allah yatabbatar da alkhairi

“Ameen ”

Inshaallah kafin mutafi xaai komai agama”

Nan suka cigaba da tattaunawa karshe sukai masa Sallama suka tafi amma ibraheem yaso yakuma toxali da farhana.

 

 

 

 

 

*_readers meye raayinku game da wannan novel din na KANNAN MIJINA_*

*Ina sauraranku ta wannan number 07037732029*👈🏻

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:04Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W>F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*TALENTED💦 💦WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

*masoyana naji raayinku raayoyinku game da wannan novel din na KANNAN MIJINA nagode sosai kuma inshaallah xakujini da raayoyinku farin cikin ku shine nawa kune ni da bazarku nake rawa*🤝

 

*kuna raina kawayan kwarai*💙

*Nana Fiddausi umar*
*zainab maigalura*
*Najaatu gusau*
*Reeda boss*

*sirinmmu make up & novel group*

*Duk ina gaida ku kyauta*👌🏻

 

 

*64*

 

 

Abangaran su Muwadda shirin biki suke bana wasa ba yanxu haka ma zaune suka a parlo suna tsara yadda bikin xai kasance Muwadda ce ta dubi abbanta tace

“abbana amma dani xaaje siyayyar kayan ko”?

“Muwadda da alhj rufai zanbawa sautu tunda yana can kasar dama”

“To abba pls kacanja min motata kaji ”

” Haba Muwadda me xai hanani canja miki mota ni de fatana ki xauna lpy kinji kar inji kar ingani ”

” to abbana inshaallah ”

Mai da dubansa yayi ga hjy aisha yace

” hjy yaushe suka ce xasu kawo lefan ”

” jibi ne alhj ”

” to mashaallah sai ai min list din abinda xaa bukata in nadawo sai Abani ”

Yafada yana kokarin fita taamsa da to tare da yaimasa adawo lpy mai da dubanta tayi ga diyar ta ta tace

” Muwadda ki bude kannanki da kyau kiji abinda xanfada miki ”

” to mama na ina jiki ”

” kin san munfar auranki da Assadiq “?

” Aa ”

” Tohm bari kiji, sonake ke kishiga jikin hjy kareema sosai ki tarwatsa farin cikin ta ki kunsa mata bakin cikin da ta dan dana min a baya haka kaxalika kamallaki dukiyar danta Assadiq ”

” momy me dukiyar Assadiq xataimin bayan abbana ya mallaki abinda Assadiq be mallaka ba”

“Hmmm ta yaro kyau take bata karko, Muwadda hjy kareema tai min abinda bazan manta da shi ba wato lokacin da mijinta yai kwamishina sai ta manta alaka ta daita giyar mulki ta dubeta ko kallo ban isheta ba Muwadda gashi lokacin muna tsananin bukatar taimako abban ki bashi da komai in har munsami tai mako to daga mijinta ne hjy kareema ta wahalr dani mutuka ko dan ubanmmu daya gashi mu biyu ne mata amma tun ina karama nake fuskan tar matsi daga gareta ”

” Hmmm momy nafahimce ki to amma momy meye laifin Assadiq da xan mamaye dukiyar sa ”

Ai in aka taba Assadiq to kmr ita aka taba tana son Assadiq”

“shi kenan mama to nifa har yanxu ina son muktar ”

” kibar maganar yaron nan Muwadda kinji ”

” Gsky mama bazan iya rabuwa da shi ba ”

” to ba ruwana kuwa”

 

Iyalan alhj muhammad mai nasara ne zaune a parlon sa sai yan jiko kinsa guda uku nabil ashraf sai fadila data girma tafara rarrafe yanxu haka ma tana ta xagaye atsaka nin iyayan nata gyaran murya dady yayi bayan addua da Assadiq yayi yafara da kmr haka

“bawani abu ne yasa nataraku anan ba sai dan in shaida muku sakamakon xiyarar da malam mudassir ya kawo min jiya yanemi da muhada aura tayya tsananin daya daga cikin yanmata nan da dansa ibraheem to mun yanke shawarar hada shi da farhana in Allah ya kaimu zai zo anjima dan su dai daita atsakaninsu ”

Ai farhana angama jin jawabin dady ta zunduma uban ihu sai da ta razana fadila taxo ta kankame ya hannatu tana kuka

Ita batason sa wlh yan ixala ne kuma baance a sokoto sukeba”

Dady ne yadaka mata tsawa cikin bacin rai yace

Farhana kinfara haukane da xaki fasa wannan uban ihun sai kace wacce uwarta ta mutu har kina razana fadila ko to kirubuta ki ajiye baki da miji sai ibraheem”

“Haba alhj kaifa kace bazaka taba yaiwa yayanka auran dole ba ”

” yaisa haka hjy kareema kina zaton malam mudassir xai nemi abu aguna inki yaimasa shi mutukar inada iko, to kar akuma daga xancannan inba hakaba rai xai baci ku ma kuyi kokarin fito da maxajan aure ”

Sai yanxu Assadiq yasa baki cikin ladabi yace

” Dady dama inason xuwa infadama tun tuni ita jalila yayan safiyya ne yake sonata”

“yayan matarka kenan “?

” shi dady Dr almustapha ba likita ne a asibitin malam aminu kano amma yanxu wani asibiti xai koma a abuja”

Momy ce take ta xabgawa Assadiq uwar harara bema san tanayiba dady ne yadubi jalila yace

“jalila abinda naji hakane”?

Cikin kunya ta kada kai

“to Alhmdulillah abinda zaai shine ka turomin shi sadauki ”

” to dady ”

” amma alhj saboda Allah

“dakata hjy kareema nagama magana bana son kwan gaba kwan baya, yaushe xaa kai lefan sadauki “?

” jibi xaa kai amma mata ne xasu kai ba kmr aransa nafariba da maxa suka kai ba”

“Hmmm hjy kareema kenan shikenan ai sai abinda kikace saboda nafiskanci bikin nakine Allah ya bada alkhairi, afifa kema ki fito da mijin aure kar inkuma yimiki maganar ”

” to dady ”

Nabil ne yace dadyn su aunty afifa nima auran xanyi kasan wa xan aura?

Fadilan uncle A”

Dariya sukasa Assadiq yace

“nabil auran Fadilaty binty sai anshirya kafadawa abbanka yafara tanadi”

“baabinda zai gagara ko nabil “?

” wlh kuwa ummata”

Dady dai murmushi kawai yake ya mai da dubansa ga hannatu yace

Dukkan ku baku da kara, hannatu kar ki tafi ki tabbata kinga xuwan ibraheem”

“to dady ”

Kowa tashi yayi suka fita ran momy abace musamma da dady yayarda auran jalila da yayan safiyya.

 

 

Safiyya ce xaune adaki tana gyarawa fadila wardrobe Assadiq yai Sallama yashigo da fadila a hannusa tana ganin safiyya tafara kokarin sakkowa tana ta kiran

“mamma”

“lala ki kafara iya sunan mamanki kafin nawa ko nagode Fadilaty ”

” wlh Dee wani sain kafiya ban dariya to bani nasha wahalr nakuda ba

“au hakama xakice to bani nai……….

“kayi me fadi mana ”

“. adai bar maganar ”

Dariya tayi ya tashi ya janyo akwatinan da ya xo dasu binsa kawai take da kallo agabanta ya ajiye su cikin sanyi yakira sunnanta

” Sweet sopy ina dada baki hakuri bisa kaddarar data samemu na karin auran da xanyi bansan da wane yare xan fahimtar da ke ba, sai dai ince kiyi hakuri kiyi hakuri safiyya ”

” Dee nafahimceka ni dai yanxu abu daya nake so daga gareka ”

” ina inki sopy ”

” kabarni inkoma makaranta kaji ”

” Angama madam kuma daga yau xanfara koya miki mota kinga sai ki dinga tafiya dakanki, ga kayan fadar kishiya nan ki duba in daakwai abinda babu sai kifadamin ”

” ni da kabarsu ma nagode ”

Takarashe xancan tana rushewa da kuka fadila ta mika masa tabar dakin binta yayi da kallo ya mike yabi bayanta a parlo ya sameta nan yajata jikinsa yafara aikin rarrashi da salon soyayyarsa ya mantar da ita yajata sukai daki suka kwanta cikin dare safiyya ta tashi tayo alwala tafara salloli data idar tashiga kwararo adduoi tana fadawa Allah damuwarta dafatan Allah yakareta daga sharrin mai sharri yakuma bawa mijinta ikon yin adalci tashafa anan bacci yai gaba daita data tashi da safe sai taji ranta yai sanyi da irin abinda takeji jiya da azumi ta tashi a ranar

 

Yau aka kai kayan lefan Muwadda kaya na alfarma momy tahada kmr yadda tafada mata ne suka kai aka sa biki sati biyu su farhana sunata murna nan suka fara shirin biki yaya hannatu ce taje gidan safiyya tai ta bata hakuri da ban baki kimar matar ta nunku a idonta.

 

Safiyya ce tashirya taje gidan yayar ta rukayya tafada mata auran Assadiq shiru tayi can tanisa tace

“hakika safiyya Allah ya jarabceki agidan aure amma kiyi hakuri xakici riba nan gaba”

“shikenan yaya nagode, amma ina fargaba wlh ”

Nan tai tabata shawarwari yadda xata dada kula da mijinta suhyla ce take tafaman shara ala dole ta girma sai masifa takewa kaninta yana dawo mata da shara baya cikin fushi tace

” aunty safiyya kiwa musadiq magana ”

 

” lallai suly angirma andena cewa cafiyya ”

 

Da daddare Assadiq yaxo ya dauketa suka tafi wani katafaran shago yakaita ta xabi kayan gado da kujeru musu kyau da tsada tai masa Godiya suka biya kudin suka tafi gida washe gari aka fitar da tsofafun kayanta aka xuba mata sababbi komai purle da fari.

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:44Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*TALENTED WRITTERS 💦hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

*sakon gaisuwa gareki xainab Abdullahi blouse uwa ga Fadilaty binty wannan shafin nakine ke kadai*😍

 

 

*65*

 

 

~~~Shirye shirye ya kankama ta ko wane bangare amma banda ango Assadiq momy kuwa ji take yanxu ne xatai biki haka su farhana anata shiri anfir fitar da anko safiyya kuwa ganin abun take kmr almara gashi kullum gidan ta cike yake da masu aiki anata fenti andada gyara bangaran da Muwadda xata xauna gaba daya atakure take Assadiq ne Yadawo da wuri daga office tana can kuryar daki fadila na gefenta tanata wasa ahankali yatura kofar dakin yashiga idonta ta rufe saboda yadda takejin xafinsa ko san ganinsa batayi da hanzari fadila ta mike ta nufi gunsa

“papa papa ”

” oyoyo Fadilaty inye yaushe aka fara tsaiwa ”

Safiyya tana jinsa taimasa shiru guri yasamu ya xauna kusa da ita ahankali yafara kiran sunnanta yana shafa lallausar gashin kanta

” sopy, sopy nasan ba bacci kike ba pls ki bude idonki”

Tafiyar tsutsa yafara mata akafar ta ba shiri ta bude idonta tashi tayi ta zsuna ya xuba mata ido taimasa kyau wata guntuwar riga ce ajikinta ta zubo da gashinta baya

“matar Assadiq kina rikita mijinki fa kullum kyau kike karawa kmr budurwa meye sirrin ”

” Dee sannu da xuwa ya office ”

” lpy kalau ina tambayar ki kinyi shiru ”

” mexance maka to”

Maida dubanta tayi ga fadila tace

“shine kika hana ni bacci ko fadila ke bakiyi ba ni baki barni nayiba”

“wai haka Fadilaty kin hana mamma bacci ”

Gwalanto tafara yaimasa ala dole magana xata fara

” sopy bani abinci inci innagama mufita kifara koyan motar ko ”

” To Dee ammafa cous cous nadafa bansan xaka dawo yanxuba gashi basonsa kake ba ”

” Badamuwa kawo min kadan kinxubawa masu aikin can ko ”

” eh”

Fita tayi taje ta dakko masa abincin fadila tana ganinta da kuloli tafara murna ajiyewa tayi tashiga zuba masa a plate ta tura masa gabansa kallon ta ya tsaya yi yace

“sopy kinfara gajiya dani ko acikin sauyin da kike min har da horan cin abinci da kaina pls safiyya kar kimin haka ki taimaka kici gaba da kula dani kinji ”

” Haba Dee yanxu wane canji kagani daga gareni me andena yima amma dai shikenan inshaallah xan nunka abinda nake akan da shi kenan ”

” shikenan matar Assadiq nagode Allah yai miki albarka ”

” Ameen”

Basu saniba fadila tasa hannu tana ta ci sai yanxu suka ankare safiyya tasa tissue ta goge mata hannun ta da bakinta kuka tasa danme xaa matsar da abincin safiyya tadau cokali tafara bawa Assadiq abincin inta bashi sai tabawa fadila ahaka suka koshi dubansa tayi tace

“Dee inason yaye fadila tunda takama abinci komai ci take ”

” safiyya tun yanxu da dai kibarta ta dan kara sha kmr xaifi ”

” Dee wlh taisa kaga kuma ga makaranta xankoma gwanda a yayeta tun yanxu ”

” shikenan sopy amma kibari sai bayan biki ko kuma banyarda akai min ita ko inaba ”

” ni da akaita gurin ummi ”

” Hmmm sopy kina son hana Assadiq nutsuwa kenan, hada min ruwan wanka”

“tashi tayi ta fita dakinsa ta koma tahada masa ruwan wanka yana nan inda tabar shi fadila nata wasa ajikinsa tadubeshi tace

“Dee nahada ma kawota kaje kayi ”

” kishirya kema ki dibi kayan da xaki kai dinki mubiya mukai ”

” Ok”

Yasa kai yafita Kwanikan tafara debewa takai kitchen fadila na bayanta ta goyata ta wanke Kwanikan ta gyara kitchen din daki ta koma ta gyara inda fadila ta xubar da abinci tagama tafesa air freshner tahada ruwan wanka taiwa fadila tafito ta xaunar daita itama ta shiga tayo wankan kan tafito fadila ta dafa gado ta mike ta dakko mai tayi wasa dashi tabata gurin da jikinta safiyya tana fitowa taga aika aikar datai mata cikin sauri takarasa ta karbe man dan haushi sai da tadaketa ai kuwa tafashe da kuka Assadiq yana dakinsa yajiyo kukanta ya shirya riga kawai xai xura yaji kukan tilon yartasa yaajiye rigar yafito dakin yanufa yana shiga yaganta kaca kaca da mai yadubi safiyya yace

“sopy me yasameta haka “?

” wlh sabagar fadila sai ita Dee kaduba fa kaga yadda tai wasa da mai ”

” to kukan me take “?

” Dukanta nayi daga mata wanka sai ta tsiri wasan mai shikenan bazata barni in hutaba ”

” yaisa haka safiyya gaskiya kar ki kuma dokar min ya nawa fadila take da xaki daketa ”

” Allah yabaka hakuri ”

” Ameen “yafada yana kokarin daukar ta bandaki yashiga yakuma yimata wanka da ruwan dumi safiyya tana kallon sa aranta tace

_in tayi mura ai tazo tahanaka bacci mai ya Allah intayi ba dai dai ba sai na daketa_

Ashe afili tayi maganar karaf akunnan sa

” shikenan safiyya ki daketa kar ki fasa bani kayanta insamata ”

Wasu riga da wando ta mika masa jajaye wandon dan gajere iya kaurinta yake xuwa rigar mai hannun vest da farin rubutu agaban anrubuta

*my parents my every thing*

Yakarba yakamata yasamata farar safa da jan takalmi akaxo gyaran gashi yakasa cikin fushi yacewa safiyya

“kibar abinda kike kigyaramata kai ”

Yana gama fada yafita gida uku taraba mata gashinta tasa jan ribon a gefe da gefe tasamata fari abaya ta shafa mata powder da turare tayi kyau yarinyar gashi dai ba fara bace amma kalar ta mai kyau 😘

Dawo wa yayi dakin tana ganinsa tata fi ta rungume shi daukar yayi ya cillata sama yace

“wow binty kinyi kyau”

Maida dubansa yayi ga safiyya yace

“inkingama shiryawa kisamemu a mota, kar ki manta da kayan dinkin ”

” Dee pls kayi hakuri kaji ”

” shikenan sopy ya wuce ”

Yasa kai yafita gurin maaikatan ya nufa sunata aikinsu suka gaisa ya dudduba aikin suna taiwa fadila wasa yarinyar badai farin jiniba yai musu Sallama ya nufi mota yana shiga kiran Muwadda yashigo dagawa yayi

” Hello sweery ”

” Muwadda kina lpy ya shirye shirye ”

” Alhmdulillah sweery yakamata kasami lokaci kazo kaji ”

” xanxo Muwadda kijirani gobe ”

” sweery yaufa ”

” yau ba lokaci Muwadda ”

” shikenan sweery ina fadila ”

Lpy kalau gata tana jinki”

“agaida min da ita ”

” ok ki gaida mama ”

Safiyya ce ta karaso cikin wani wani lace na alfarma blue rigar have gwon tayi kyau ta bude kofar motar ta bude tashiga kamshin turaran ta ne yabigi hancinsa ya dubeta yace sopy wane turare kika sawa kayanki

” Dee gaffas nayiwa kayan ”

” meye kaffas sopy “?

” Dee bafa wani abu bane akan wani dan abu nakaba zaka sa kayan sai kasa turaran wuta akasa hayakin zai dinga ratsa kayan ”

” au shine baaiwa Fadilaty ko ”

Dariya tayi yajasu suka fita tun daga nan tamaida hankali taga yadda yake tuki

 

Farhana ce kwance anatafama daita ta tashi ta shirya ibraheem yaxo da kyar tatashi wanka tayi tashirya cikin wasu english wears riga da sikert ta shafa powder ta feshe jikinta da turare dankara min mayafi tayafa tafita yana sit room sanye cikin shadda fara kal da hula ash fari ne amma ba tas ba da dan madai dai cin gemu ahabarsa Sallama tayi tashiga tunda ya kalleta sau daya yadauke idonsa saboda yadda ta matse jikinta shiru sukayi can yanisa yace

“Amm malama farhana idan badamuwa ko xakije kicanja koda mayafi ne

“ko me naji kina yayi ”

” wato ainihin be kamata kina irin wannan shigar ba duba ga yadda shigar taki tayi ba dai dai ba ”

Banxa taimasa nan yaitai mata waazi damunta yayi ta kira afifa awaya ta kawo mata mayafi baajimaba ta kawo mata ta gaida shi tafita yafawa tayi ya dubeta yace

” mashaallah kinga yanxu kinfi kyau ”

Nan yagabatar da kansa gareta yakuma jadda da irin son dayake mata gaba daya haushi yabata tai masa banza ya karbi wayar ta yasa number sa yakira yai saving din tata tashi yayi yaimata Sallama yatafi yana fita ta rushe da kuka sai da tayi mai isarta sannan ta koma ciki tundaga ranar ya tsiri yimata waya wataran ta kula shi wataran tai masa banza

 

Yau almustapha yaxo amsa kiran dady suka gaisa cikin mutunci take dady ya yaba da hankalinsa yakuma ce ya turo magabatansa yai masa Godiya yatafi jalila yakira ya fadawa yadda sukayi da dady tai murna

 

Yana zuwa gida yasami baffa yafada masa zancan auransa da jalila yai murna yakuma tabbatar masa xai tura baffan ninsa ummi dai bata ce komaiba amma tana ganin momy bazata so wannan auran ba mai da dubansa yayi ga ummin tasu yace

“ummi na yanaji kinyi shiru ”

” Allah ya sanya albarka mustapha ”

” Ameen ”

Washe gari Assadiq yaje gidan su Muwadda nan fa tashiga lissafa masa partyn da xatayi shiru yai sai data gama sannan ya dubeta yace

” Muwadda duk najiki amma fa kisani baxan iya xuwa wadannan events ba ”

” Haba sweery meyasa ”

” raayina kenan dan haka kifadi nawa kike bukata kawai inbaki ”

” kabar kudinka ”

” ok”

Yai mata Sallama yatafi binsa tayi da kallo tasaki wani murmushi.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:28Am 2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

*Dedicated 2 billy ladan fans group thanx 4 ur suport*💙

 

🔛🔝👈

 

*66*

 

~~~~Assadiq yana tafiya Muwadda ta kira number momy bugu biyu ta daga

“Hello ‘yata ”

” Naam momy Ina yini”

“Lpy kalau ya maman taki ya shirye shirye “?

” Lpy kalau momy ”

” Badai matsala ko “?

” eh to dama Assadiq ne yazo daxu nafada masa events din da xanyi da kuma kudin danake bukata shine yahau ni da fada kuma wai ba inda xaije ”

Tana gama fada ta rushe da kuka akidime momy tafara magana

” yaisa yata share hawayanki kinji ai ni na haife shi bashi ya haifi kansa ba saboda haka kar ki kuma asarar hawayanki kinji kuma maganar kudi da kansa xai xo ya kawo miki”

“to momy nagode Allah yakara girma ”

” Ameen Muwadda ki gaida mama kinji ”

” zataji momy ”

 

Sukai Sallama ta kashe wayar tana dariyar mugunta

Assadiq kuwa yana barin gidan su Muwadda kai tsaye gidan su ya wuce a parlo ya tatar da momy tana waya da faruq tun da yashiga take hararar sa tagama wayar ta dubeshi tace

” sannu Assadiq wato har yanxu baxaka Maida hankali kan auran Muwadda ba ko kudin da ake bawa amarya kai kafurje baxaka bata ko har ikirari kake wai baxaka halacci bikin ba to kar kaje kaga yadda xansaba maka kuma wlh kaje da kanka ka kaimata kudin nan kaji dai nafadama ”

Tana gama fada ta mike tabar gurin kansa yadafe yarasa ma mexai ce shi dai yasan bahaka sukai da Muwadda ba to amma me momy take nufi jalila yakira tana kitchen tafito da glass dinta manne a fuskar ta guri tasamu ta xauna

” ya Assadiq gani ”

” jalila Muwadda ta bugowa momy waya ne “?

” eh yaya sunyi waya amma bansan me tacewa momyn ba but naji tana bata hakuri ”

” shikenan badamuwa, dady fa?

“dady be shigoba”

“ok, jeki bari in wuce kicewa momy natafi ”

” to ”

Fita yayi ransa a mutukar bace yana xuwa gida kai tsaye dakin sa ya wave kayan jikin sa ya cire yafada toilet ruwan sanyi yasakarwa kansa saboda yadda yakejin xyciyar sa na zafi ya dade yana wanka sannan ya fito yashirya cikin 3quater da riga armlace ko mai be shafaba ya kwanta bsyan ya kashe kwan fitila

Safiyya kuwa tana dakinta tana lallaba fadila tai bacci dayake ba baccin xatai ba sai tabar safiyya da baccin nan ta tsiri wasa ta tabo wannan ta taba wancan sai da ta hautsina dakin sannan ta dawo jikin safiyya ta kwanta bacci yai gaba daita

Safiyya bata farkaba sai wajen 10 taga aikin da fadila tai mata murmushi kawai tayi aranta tace

_yarinya sai kirinkin tsiya adaketa babanta ya hau sababbi Allah yashiryi fadila_

Mai da dubanta tayi ga agogon dayake manne a jikin bango mai dauke da hoton fadila taga karfe 10 mamaki tayi to ina Assadiq yau be dawo da wuri ba wayarsa takira tanata ringing baadauka ba dakin ta gyara tamaida fadila cikin gadon ta tai mata addua tashiga wanka bata jimaba ta fito tashirya cikin wata rigar bacci lemon green iya gwiwa tafeshe jikinta da turare ta gyara gashinta hula tasa fara kal parlon tafito ta ga baya nan kai tsaye dakin tanufa sai taga kwai akashe sai kuma tajiyo kmr nishin Assadiq tsorata tayi tafara addua kwan ta kunna Assadiq ta hango kwance cikin bargo da sauri ta karasa ta hau gadon ta yaye bargon jitayi jikinsa da mugun xafi cikin sauri takira sunansa

“Dee, Dee meyasameka nashiga uku”

“sopy rufe ni sanyi nakeji xaxxabi ne ajikina ”

” sannu kasha magani “?

” Aa baxan iya shaba kawo bakin shayi kadan ”

Fita tayi ta dafa masa tahado masa da abinci takawo da kyar ta taimaka masa ya tashi yajingina da pillow ya karbi shayin yafara sha da kyar yasha rabi abincin tafara bashi yadan ci shima dan ta matsa masa ta bashi magani yasha dubanta yayi yace

” sopy ina Fadilaty binty “?

“tayi bacci, Dee meyafaru kadawo bansaniba kuma kayi wanka da ruwan sanyi ko?

” raina ne abace safiyya shine nai wanka da ruwan sanyi ”

” Haba Dee dan ranka yabaci sai kasawa jikinka ruwan sanyi bayan kasan illar da yakewa jikinka ”

” bazan kumaba sopy, dakko Fadilaty mu kwana anan ”

” ok”

Fita tayi ta dakko ta tadawo karbar ta yayi ya kwantar da ita kusa da shi ya juya ya rungume matarsa take yaji damuwarsa ta gushe lallai ya yarda safiyya itace rayuwarsa a haka bacci ya dauke shi cikin dare safiyya tazame jikinta ta tashi tayo alwala tazura hijjabinta ta fara sallolin nafila

Washe gari Assadiq yashirya yaje gidan yaya hannatu yafada mata yadda sukayi da momy haushi ne yakamata ta dube shi tace

“wlh Assadiq bana son abinda momy takeyi nifa hankalina har yanxu be kwanta da auran Muwadda ba ”

” wlh kuwa yaya bani da matsala da mata ta banasan abinda xai bani ciwon kai to nafahimci yarinyar tana da damuwa ”

” bakomai Allah ya tabbatar da alkhairi, yanxu kaje ka kaimata kudin karbarta da halinta ”

” Gsky yaya baxanje ba amma abokina B malik yana gari innaje office xanbashi kudin yakai mata ”

” shikenan Assadiq yanxu yaushe xaa fara bikin ”

” oho musu, nifa bansan komai ba nasan dai ranar lahadi daurin aure ”

” oh ni hannatu wannan wane irin ango kenan ”

” ai nagama biki yaya tunda na auri Sweet sopy ”

” Assadiq mijin sopy, ina ‘yata fadila?

“Lpy kalau sai sabga tunda tafara tafiya shikenan aka banu bata xama ”

” ai dama, yakamata a yayeta tunda safiyya xata koma makaranta ”

” ni tausayinta nakeji wlh kawai acireta daga nono ”

” au to abarta Assadiq kar ka bari ayayeta yarinya ta girma to me yarage ”

” zaai yaya ina su ashraf “?

” suna school ”

Sallama yai mata yatafi yana xuwa office yabawa B malik kudi musu yauwa yakaiwa Muwadda bayan yaimasa kwatance
Haka yabawa safiyya itama tayi hidimar biki

 

Yau takama laraba yau aka fara bikin Muwadda da Assadiq yau kamu tun safe su farhana suke shiri gidan su Muwadda suka tafi ita da afifa jalila kuwa kin binsu tayi

Muwadda kuwa tana gurin salon ita da kawarta naeema da kanwar saurayin ta rushida muktar dinne yakaisu a motar ta

_to Muwadda basu rabu da muktar ba kenan_🤔

Suka gama yamaida su gida nan akafara shirin tafiya kamu su farhana sun rasa wacece rushida tambayar Muwadda sukayi tace yar kanwar abban ta ce

Amarya anfito ansha kyau gashin nan yaci atach wayarta ta dauka tashiga neman layin Assadiq akashe gurin mamanta tanufa kmr xatai kuka tace

“mama inata kiran layin Assadiq akashe ”

” bari inkira ya kareema

“bugu biyu ta daga nan ta tambayeta ina Assadiq ya shiga momy tace bari ta nemi wayarsa neman duniya baasami Assadiq ba haka akai kamu ba ango kmr yadda aka tsara sai da aka kusa tashi Sannan Dr almustapha yakawo jalila abin yabatawa Muwadda rai

Ana gama kamu momy tanufi gidan Assadiq tana xuwa ta tatarar da safiyya a kitchen fadila tanata ta wasanta Sallama tayi tasami guri ta zauna safiyya taji kmr muryar momy tana fitowa taganta takarasa tai mata sannu da xuwa taamsa a takaici dubanta tayi tace

“bawani abune yakawo ni ba xuwa nayi infada miki kifita a idona in rufe kin hana Assadiq sakat kibarshi yai biki kmr yadda yai naki nasan makircin ki ne yahana shi xuwa kamu to wlh kishiga hankalinki kuma bake ba Muwadda kinji dai nafada miki ”

” wlh momy rabona da Assadiq tun safe inata kiran wayarsa akashe ”

” ke tashafa nade fada miki ”

Tana gama fada tai gaba ko fadila bata kulaba idonta yarufe safiyya tai kuka kmr ranta xai fita karatun kurani ta kunna take tasami saukin damuwarta

 

Washe gari diner Assadiq ya furje bazashi sai da safiyya tai da gaske tace

” wlh Dee mutukar bakajeba to gida xantafi ”

” sopy saboda abinda be shafeki ba xaki ce xaki tafi gida to baxanjeba ki tafin inkin tashi tafiya ki ajiye min ‘yata ”

 

” shikenan Assadiq ”

 

Kayanta tafara hadawa a akwati tagama tsaf tamika masa fadila taja akwatin ta tanufi kofar parlo. 🙆🏻

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻✍🏻
[9:32Pm, 2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

*67*

 

~~~cikin sauri ya sha gabanta akwatin ya rike yaxuba mata sexy eyes dinsa dauke kanta tayi cikin sanyi ya kira sunnanta,

“Sweet sopy akan wata can daban xaki tafi kibar ni yanxu xaki iya rabuwa dani da tilon yarmu kinsan baxantaba iya rayuwa bake ba ”

” Assadiq sakar min jaka nagaji yakake so inyi da raina da me xanji ”

Takarashe maganar da kuka mai tsuma xuciya tausayi tabashi hannun ta yaja suka koma gefan gado suka xauna dubanta yayi yace

” sopy pls kiyi hakuri ki dena kukan haka bazan iya jure jin ki kina kuka ba yanxu me kike so inyi miki ”

Shiru taimasa sai da yai ta aikin rarrashi sannan ta dago ta dubeshi tace

” in har kaga na zsuna to wlh kaje diner din bikin nan ”

” shikenan inde naje hakan xai faranta miki rai ”

” ummm ”

” shikenan safiyya xanje amma su waye suka xo gidannan tsakanin jiya da yau ”

” ba kowa”

“karya ba halinki bane saboda haka fadamin gaskiya ”

” momy ce tazo ”

” shikenan tashi ki taimaka min inshirya Allah ya huci zuciyarki mata ta ”

Fadila ya mika mata tanata bacci kwantar da ita tayi tahada masa ruwan xafi yashiga yai wanka ta bude wardrobe ta dakko masa hadaddiyar shadda milk mai babbar riga da takalmi batozi sai silver din agogon axurfar sa mai kyau da tsada be jimaba yafito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare yafito a angonsa
Shiru yayi can yanisa yace

“Allah ya albarkaci rayuwar ki matar Assadiq nagode wa Allah da yabani mace mai hakuri da kawaici ”

” Hmmm dawa zaku tafi wajen diner “?

” ke zaki kaini bazan iya tafiya ni kadai ba”

“bazan iya tukin dare ba ka kira B malik ya kaika ko achida ”

” achida baya gari yaje mina 😜but bari in kira B malik ”

Wayarsa ya dauka yakira layin sa bugu daya yadaga bayan sungaisa yace yaxo gida yadauke shi yakai shi mina event center

Be jimaba ya karaso Sallama yaiwa safiyya ya fita yana fita takoma gado ta shiga rusa kuka 😭

_gsky auran Assadiq da Muwadda yataba xuciyar naseeba saboda ji nake kmr gaske duba da yadda safiyya takeji aranta Allah ka sauka kawa yanuwana mata radadin kishi_😭👏🏻

 

 

Sai da tayi mai isarta sannan ta goge fuskar ta wayar ta ta dauka takira layin umminta tanata riging sai data kusa tsinkewa sannan ta daga

 

“Hello ummina kin manta dani ko “?

” haba safiyya ya xaai kice na manta da ke kar ki kuma fada ”

 

” ummi kimin addua xuciyata xata fushe”

Tana gama fada takuma rushewa da kuka kyaleta tayi mai isarta sannan ta shiga rarrashinta da nasiha da shawarwari

“safiyya kiyi hakuri kinji kar ki duba ni ko yayar ki kowa da yadda Allah ya shiryamasa rayuwa kuma Allah yasan xaki iya shi yasa ya dora miki saboda haka ki daure kici jarabawar da Allah ya jarrabceki kinji ina nan inai miki addua

“to ummi nagode acewa najiba da yaya amina suxo gobe dan Allah su kwana saboda gobe xasuxo kafi ”

” to shi kenan safiyya xasu xo kinji ki cigaba da addua Allah yakara hakuri ”

“Ameen ummi nagode agaida baffa”

“zaiji agaida min da fadila ”

” to ummina ”

Sukai Sallama ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta tai lamo tunani fal ranta

 

Tunda Assadiq ya fita kiran Muwadda yake shigowa da kmr bazai daga can ya daure ya daga

 

” ya Assadiq ”

” naam ina jinki ”

 

” I am waiting 4 u ”

” I am on the way”

Yana gama fada yakashe wayar ya mai da hankalinsa ga abokinsa yace

 

“Hakika abokina in banda iyaye iyaye ne wlh banga dalilin da xai sa inkara aureba ”

 

” to ya xaai chairman dole muyi yadda suke so fatanmmu dai Allah yaraba mu dasu lpy ”

” Ameen B malik ”

 

Suna Karasawa suka tatar gurin cike da kawayan amarya sunsha anko waya yaimata yace yakaraso farhana ce ta karaso ta bude masa murfin motar harara ya watsamata yafito Muwadda ma tafito daga cikin mota cikin shigar amare tayi kyau suka jera atare hannun ta tasa cikin nata binta yayi da kallo kawai kawayanta na biye dasu suna shiga yanuwa sukai musu caa yayin da DJ yasaki wakar ango da amarya momy ta shiga yaimusu liki maman Muwadda kuwa farin ciki fal ranta su ya hannatu kuwa suna gefe ita da jalila amarya da ango suka zauna a mazauninsu akaita hotuna biki yayi biki anci ansha anyi barin nera burin Muwadda yacika anyi bikin yar gata Assadiq Ya kagara atashi hankalinsa yana kan safiyya karfe 11aka tashi ko tsayawa beyiba yatafi sai neman ango akai aka rasa yatafi

Sanda yaisa gida safiyya tayi bacci kayan jikinsa yacire yashiga wanka yana fitowa yasa kayan baccinsa yakaraso gadon yadauke fadila daga jikinta ya mai data gadonta Yadawo ya kwanta jikinsa yajata ya rungume ta yana shakar kamshin jikinta yashiga sarrafa ta cikin kwarewa da kewa sai da yagama wasa da ita sannan ya sami bacci tana jinsa tai shiru

 

Washe gari aka tashi da daurin aure da kanta ta shirya shi cikin farin boyel babbar riga yayi kyau da kyar yatafi daurin auran shi da abokansa Ita ma tashirya cikin atamfa super purle tai mata kyau ta shirya fadila cikin kananun kaya masu kyan gaske su najiba kuwa tun safe suka xo yaya rukayya ce tai yo girki sai data gama sannan ta xo

 

Karfe 10 :30 aka daura auran Assadiq da Muwadda kan sadaki 100k nan sukai ta gaisawa da jamaa dady ma yana ta gaisawa da abokansa yar walima abokansa suka hada masa

 

“momy ma anata fama da jamaa gidan yacika da jamaa

Gidan safiyya ma yafara cika da jamaa anata hidima tasaki ranta ana gama daurin aure Assadiq Yadawo gida kai tsaye dakin sa ya wuce yamaida kofa ya rufe kwanciya yayi yana tunanin yadda xai kwana da wata ba safiyya ba

 

Karfe 4 yanuwan abban Muwadda suka xo gyara dakin amarya suka shiga dakin safiyya suka gaisa suka nufi dakin Muwadda yasha kayan alatu
Tun sannan gaban safiyya yaketa faduwa

Karfe bakwai aka kawo amarya kai tsaye gidansu Assadiq aka wuce daita mumy murna kmr ta goyata akwati guda tabata shake da kaya amatsayin siyan baki

 

Aka kaita gidan ta sai da aka kaita dakin safiyya inbanda kamshi ba abinda yake tacaba kwalliyar ta cikin hadaddiyar shadda combination da paper cofee da yellow tasha sakar gwal nan akai musu nasiha tabata rafar yan dari biyu da kwalin cingam suka dauketa xuwa bangaranta

 

Yan uwan safiyya kuwa Sallama sukai mata suka tafi tayi jugum ta rungume fadila

Assadiq kuwa yana daki akulle yakashe wayarsa.

 

 

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:45Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

 

*sako zuwa ga wasu daga cikin marubuta hakika banji dadin yadda wata marubuciya taxage ta faffadi maganganu game da masoya littafinta ba ni aganina kaunace yasa suke bibiya be kamata ace kiyi amfani da wannan damar kifadamus maganganu marasa dadin jiba dan Allah mu gyara, shawara ce 👌🏻gyara kayanka baya taba xama sauke muraba*🙅🏻

*Ina yinku masoya online writters farin cikin ku shine burin naseeba*💙

 

 

 

*69*

 

~~~mamaki ne yakama su suka shiga tambayar kansu me Muwadda take nufi kenan basu da wannan amsar cikin isa tadubesu tace

“afifa kina haukane da zakixo ki canja min tasha ina cikin kallo ko kuma kawai iskanci ne to wlh tallahi kar ki kuma yimin irin wannan dan bazan jure ba ”

” Haba aunty Muwadda be kamata ace kina fada akan dan wannan dalilin ba ”

” au farhana wannan iskancin datai min shine dan, ok yayi kyau Allah yabata Saa tayi gagarimi tagani ”

Waje suka samu suka xauna suka gaidata taamsa a takaice ta maida hankalinta ga tv can farhana tace

” aunty na ina kaxar amarcin abamu mudan taba ”

” Hmmm farhana kenan ai kaxar amarci layi ce dan haka sai kujira tazo kanku ”

” kai aunty Muwadda dan Allah ki bamu, to shi kenan dafa mana ko indomie ce kinji ”

” kut wacece xatai muku girkin wai ni, Hmmm ku tunda kuka sanni kuntaba ganina nayi girki to bari kuji girkina yana wuyanku dan kuwa ko xaku dinga yimin wlh ”

” angama auntyn mmu, yanxu dai bari mudafa indomie ”

” ku ta shafa fitsararru kawai ”

Takoma ta kwanta kitchen din suka shiga ya hadu komai blue da fari suka kunna gas suka hau dafa indomie da kwai basu dadeba suka kammala suka juyota a plates suka dakko lemo suka fito tana xaune ta dora kafa daya kan daya ta dube su tace

” guda nawa kuka dafa “?

” guda uku ce aunty ”

” Hmmm sai kubani inci inrage muku ai ”

” kixo dai muci tare ko ”

” saboda raini xanci abinci da ku dalla malamai kubani ”

Bashiri suka mika mata taci rabi tabasu rabi suka karba suka ci abinda taje musu suka maida plate din kitchen suka dawo suka xauna dubansa tayi tace

” inafatan kun gyara min kitchen din ”

” Eh angyara ”

Sallamar kawar tace takatse mata maganar da xatayi ita da kanwar muktar suka xo ta tashi ta rungume su tana murna ta shiga kitchen ta dakko musu kaxar da suka ci da daddare da lemo ta hado musu da katuwar fresh milk ta kawo musu su afifa suna xaune suna kallon ikon Allah ta dubi kawar tata tace

“kawata bisimilla rushuda ya muktar da umma “?

” Lpy kalau aunt Muwadda suna gaisheki ”

Ina amsawa”

Rushida ce tamai da dubanta ga su farhana tace

“afifa kuxo muci mana ”

Caraf Muwadda tayi tace” kirabu dasu yanzu suma sukaci nasu ku de kuci ”

Mamaki tabasu sukai mata shiru safiyya ce tai Sallama tashigo cikin mutunci suka amsa banda su farhana abinci ta kawo musu Muwadda tace

” farhana ko afifa ku karbeta mana kun tsaya kuna kallon ta, aunty sannu da aiki ”

” yauwa sannunku ”

” ina fadila ”

Dee yakaita gidan momy”

Tana gama fadar haka tafita tana yaba haduwar dakin Muwadda aranta take mamakin yadda su farhana sukewa Muwadda biyayya safiyya na fita Muwadda ta maida dubanta garesu tace

Afifa dakko mana plates a kitchen ”

” kai aunty Muwadda wlh nagaji ”

” oh ni xan dakko ko me dallacan jeki dakko mana banza kawai ”

Tashi tayi ta dakko ta kawo tace farhana taxuba musu xubawa tayi tamikawa kowa taxuba nata da na afifa
Suka kammala tace su kwashe Kwanikan su wanke ba musu suka wanke Kwanikan suka gyara kitchen din tsaf cewa tayi su gyara parlon taja su rushida suka koma bedroom farhana ce ta dau mayafinta tai tafiyarta afifa ce ta gyara parlon takunna turaran wuta dakin tashiga ta taga tabaje musu kayan lefan ta suna xabar atamfofi da kayan kwalliya Muwadda ce ta dubeta tace

“yadai menene?

“aunty Muwadda mungama xan je gida ”

” farhana fa?

“ta tafi tun dazu ”

” au batai aikin ba, lallai yayi mata kyau ”

Janbaki tabata da hoda sai jagira da body spray tace tagaida gida fita tayi tana mamakin halin Muwadda tana xuwa gida ta tatar da su farhana a parlo kayan ta zazzage a kasa momy ce ta dubeta tace

” afifa wannan kayan fa Saa tace abawa ”

” Hmmm nawa ne aunty Muwadda tabani ”

” kai kai dan wannan kayan tabaki cab ”

Cewar jalila tana kokarin sauke fadila daga bayanta momy ce taamshe xancan tace

” to ina lefi abinda xaa rabawa dangi shiyasa nasa aka xuba mata su da yawa ”

” kunga kayan data ke hadawa kawarta da yar kanwar abbansu da yawa wlh ”

” bayason korafi afifa ku xauna lpy da Muwadda kunga dai burinmmu yacika ”

Sai yanxu farhana tasa baki ta dubi momy tace

” amma fa wlh mutukar xata dinga sa mu aiki wlh bazamu zauna lpy ba ”

” to meye dan tasaku aikin ba yayanku bace ”

Jalila dai dariya kawai take kunshewa ta dau fadila tafita dan kaita gida

Da yamma Assadiq ya dawo gida kai tsaye dakin safiyya yafara shiga tana kitchen ta xaunar da fadila a kujera tana ta cin biskit yashiga tana ganinsa ta tashi ta rungume shi

Oyoyo papa ”

Oyoyo Fadilaty binty”

Safiyya ko juyowa batai ba tai masa sannu da xuwa rungume ta yayi ta bayanta ahankali yace

I miss u Sweet sopy ”

” Hmmm Dee kenan kai da kake da sabuwar amarya pls cika ni inkarasa aikina ”

” sopy Assadiq yayi laifi ko “?

Kunnansa yakama yace

” natuba matar Assadiq ayi hakuri nadena ”

Dariya tayi kuma rungume ta yayi yafara kokarin zura hannunsa a rigar ta rike hannunsa tayi ta girgixa masa kai alamar yabari hakura yayi ya sakar mata kiss yafita da fadila bangaran Muwadda yanufa tana xaune tana kallo tacaba kwalliya cikin english wears

Cikin sauri takarasa ta rungume shi

“welcome honey I miss u ”

Thanx Muwadda I miss u too”

Hannu ta mika da niyar karbar fadila taki yarda
Assadiq ne yace

“Muwadda bari inje Inyi wanka ”

” aa nide tare xamu tafi gsky honey ”

” ok muje ”

Fita sukayi yafara kai fadila gurin safiyya da kyar ta yarda tana ta kuka

” papa ”

Safiyya ce ta rungume ta yarinyar tabata tausayi da dane Assadiq bazai rabu da fadila ba amma gashi saboda yayi amarya sai rawar kafa yake

Suna shiga dakinsa Muwadda ta dubeshi tace

” honey inxo intayaka wankan ”

Aa nagode baby”

Bandaki yashiga yai wanka yagama yafito daure da towel yakaraso gabanta yace

“baby baki fito min da kayan da zansaba ”

” honey ai bansan wanda xaka sa ba ”

” ok yayi kyau ”

Jallabiya ya dakko fara tas yasa yasami gefenta ya xauna amma hankalinsa yana gun safiyya tashi yayi yafita kacibus sukayi da ita xata kawo musu abinci fadila na biye da ita Assadiq ne xai dauketa tamake kafada tayi fushi surar ta yayi suka sa dariya shi da safiyya ahaka suka shiga Muwadda tana ganinsu taraina kanta yadda taga safiyya ta caba kwalliya cikin dandatse tsan lace dinta taiwa fadila ma kwalliya gashi sun shigo suna dariya kayan abincin taajiye cikin yauki tacewa safiyya

“sannu da aiki aunty ”

” yauwa amaryar Assadiq ”

Wani kallo Assadiq yaimata tai dariya kasa kasa taxuba musu abincin a plate daya suka fara ci Assadiq yana ta santi yanai taiwa safiyya hira ga fadila tanata tsalle a jikinsa du haushi yahanata cin abincin bayan sungama yace su shirya suje sugai sa da dady yadubi Muwadda yace

 

“Muwadda kitai makawa sopy ku fitar da Kwanikan daga nan ki canja kaya ”

Bata amsaba ta kwashe Kwanikan haduwar dakin safiyya yabata mamaki kitchen dinmma ya tsaru dakinta ta koma ta dora abaya tafito abakin kofar Assadiq suka hadu suka rankaya suka tafi

Parlon ba kowa sai jalila da hanzari ta karaso ta taresu fadila na ganinta tafara murna momy naganin Muwadda ta Washe baki ita kuwa haushi ma momyn tabata.

 

 

07037732029 👈🏻

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[4:41Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*

 

*sakon fatan alkhairi ga daukacin musulman duniya musamman alhazan mmu ina rokon Allah yabasu arfa mai sauki yakarbi ibadunsu damu baki daya ubangiji yabamu alkhairin wadannan gwala gwalan ranaku Dafatan xamuyi shagulgulan babbar salla lpy AamEEN*👏🏻

*littafin KANNAN MIJINA daga wannan page din yatafi hutun salla babba Allah yasa ayi lpy agama lpy*💕

 

 

 

*70*

 

 

~~~~cikin ranar jiki momy takaraso ta rungume Muwadda guri safiyya tasamu ta zauna gefenta Assadiq yazauna momy a kujera mai cin xaman mutum uku momy da Muwadda suka xauna safiyya ce taxamo daga kan kujera tace

“momy barka da dare ”

” yauwa yagida”

“Alhmdulillah momy”

Ran Assadiq ne ya sosu da irin yadda momy taamsa wa safiyya shima ya gaisheta ya tashi ya hau saman dady yabarsu
Muwadda ce ta maida dubanta ga momy tace

“momy na ina yini ”

” Lpy kalau ‘yata, dafatan ba wata matsala ko ”

” eh momy ”

” yauwa duk wanda yabata miki rai kimin waya kafada min kinji ko ”

” to momy na, su afifa fa?

“suna dakinsu basu san kinxo ba ”

Kwalla musu kira tayi suka amsa can sai gasu nan sun fito safiyya tana xaune ita da jalila suke hirarsu suna fitowa suka ga su Muwadda da murnar su suka rungume ta

” oyoyo ga amaryarmu ga amaryarmu ”

Dariya ta sakar musu tare da rungume su ajikinta tace

” yanmatan kanne na kuna lpy ko dayake ma nayi fushi wlh, wai momy yarannan suka tafi daxu ko Sallama nahada musu kayan kwalliya suka ki tsayawa su karba ”

” amma baku kyauta ba farhana ku da yayarku xaku tafi bakuyi mata Sallama ba ”

” kai momy

“yimin shiru afifa banyarda wani yasabawa Muwadda ba daman inason jadda da miki ke safiyya kiji tsoran Allah kixauna da abokiyar xaman ki lpy ban yarda ki cutar min da ‘ya ba inba haka ba xanbaki mamaki”

“to momy inshaallah xan kiyaye ”

Wani irin tafasa xuciyar safiyya takeyi saboda yadda momy take nuna mata kiyayya jalila ce tace

” amma momy ai bekamata kiyiwa aunty safiyya fada ita kadai ba sai kihada da ita aunty Muwadda ki musu ”

” jalila ni kike fadawa haka saboda rashin kunya oho saboda kin likewa yayanta shine xaki sa min baki ina magana ko, yayi miki kyau ”

” momy kiyi hakuri amma na kula jalila bata farin ciki da aurena ashe kanwar saurayinta take tayawa kishi ”

” haba aunty Muwadda ai mu muna sonki kuma muna yinki ”

Cewar afifa safiyya sai tarasa ma me xatace fadila ce fara kuka ta karbeta a hannu jalila tafara bata nono momy ce ta dubeta tace

” wai sai yaushe xaku yaye yarinyar nan abinda bata xuwa ba kuma abinda bataci amma kinki yaye ta haba ”

” ke kuwa momy ba yar so bace yaushe xaa rabata da nono ”

Cewar farhana kenan takarashe maganar tana kokarin daga wayar ibraheem cikin bacin rai Assadiq ne yasakko daga saman dady yadubi safiyya yace

” sopy kuxo muje kugaisa da dady”

Muryar sa fadila taji tasaki nono tafara kiransa

“papa”

“Fadilaty binty kindena fushin dani ”

Daukar ta yayi yahau saman su safiyya suka bi bayansa da Sallama suka shiga cikin sakin fuska dadyn yaamsa sallamar su guri suka samu suka xauna safiyya ce tafara gaida shi

” dady barka da dare ”

” yauwa ‘yata kuna nan kalau ya matar tawa sarkin hada hada tazo tai tai min yaran da bana ganewa ”

” Lpy kalau dady ai wai dole sai tayi magana ”

” mashaallah”

“ina yini dady ”

“Muwadda kina lpy ya bakunta”

“Alhmdulillah ”

” naji dadin xuwanku badan komai ba sai dan intunasar daku xaman tare musamman ma kai sadauki kaine shugaba ka kula kabawa ko wacce hakkinta in matanka sun hada kai sun xauna lpy to daga gareka ne in aka samu matsala to daga gareka ne sadauki ku kuma

Kuhada kanku ku xauna lpy banda tashin hankali musamman ke Muwadda kace karama dole sai kin girmama safiyya dan gaba take da ke haka kema safiyya kibata hakkinta na kanwarki kunji Allah yaimuku albarka yabaku xaman lpy ”

Suka amsa da ameen kimar dattijon tanunku a idon safiyya fadila ce ta dau huular dadyn tasa masa suka sa dariya dady yace

” lallai fadila ana auran da dady to ke da momy ba ruwana ”

” dady ai kaimata tsufa dama ”

Cewar Assadiq suka kuma yin dariya ran Muwadda ne yabaci yadda ta kula dady nason safiyya sai ta kosa su tashi su tafi Assadiq ne yace

“dady bari muwuce”

“to ba laifi sadauki madalla gashi kabawa ko wacce dubu goma goma ”

” Dady angode amma kabawa yayanka ayi tuya anmanta da albasa ni baka bani ba ”

” Allah ystsareni dabawa ma gidanci kudina, kuje sai da safe ”

Dariya Assadiq yayi suka fita suna sakkowa momy tabawa Muwadda wasu turaruruka masu tsada aleda safiyya ce tamikawa momyn wasu mayafe a wata yar jaka masu shegen kyau karba momyn tayi tace

” ke bakya gjy da hidima to angode fadila sai da safe sarkin kirinki Muwadda kigaida gida kinji ”

” gida xaiji momy na nagode ”

Assadiq yaimata Sallama shima bayan yabata kudi jalila ce tarakasu tadan jera da safiyya tana ta bata hakuri Muwadda kuwa sai nanewa Assadiq take ita ga me miji

Suna komawa gida kowacce tai bangaranta Assadiq kuwa bayan safiyya yabi da fadila a hannun sa tana shiga daki tiolet tashiga tahada ruwan xafi tafito hannu tasa xata dauki fadila yarike hannun nata ido yaxuba mata take yafahimci bacin rai afuskar ta cikin kwantar da murya yace

“matar Assadiq meyabata miki ranki haka na kula tunda muka taho baki magana ba ”

Pls kabarni bacci nakeji bani ita wanka xanmata mu kwanta”

“barshi ni xanmata wankan ai bake kike mata wankan dare ba ”

Matsawa tayi bata kula shi ba tafara kokarin cire nata kayan ta daura towel ta bude wardrobe din fadila ta dakko mata kayan bacci Assadiq kuwa tiolet din yashiga yaiwa dadilansa wanka yafito yana fitowa safiyya tai shigewar gaba daya Hankalinsa na kanta adaddafe yashirya fadila ya kwantar daita ban dakin yabi safiyya tana cikin wanke fuska taji shigowar sa cikin fushi tace

“waye ne?

Shiru yayi dauraye fuskar ta tayi taganshi dada daure fuska tayi tace

“Lpy dai ko dama baka gamaba na shigo sai infita ”

” Karasawa yayi gab da ita ya hada bakin sa danata yafara tsotsa kuka tasa masa shi kuwa bemasan tanayi ba saboda yadda yai kewar ta karfi tasa ta tureshi ta daura towel dinta tafito kan gado ta hau tai ta kuka biyota yayi ya tsuguna gabanta cikin da kushashshiyar murya yakira sunnanta

Sweet sopy dan Allah kifadamin damuwarki in nine wlh baxan kumaba kiyi hakuri pls wlh sopy duk abinda kika ga inayi kafin hali nake na matsu in dawo gareki mata ta ”

” ni ba abinda kai min kawai katafi kabarni kana shiga hakkin matarka ”

” shikenan sopy xantafi amma kibarni inji dumin jikin ki pls ”

Kan tayi magana ya rungume ta atare suka saki wata ajiyar xuciya xamewa tayi ta kwanta ta rungume fadila ba yadda ya iya sumbatar fadila yayi ya tashi kwan fitila yaja musu kofar yafita

Yana zuwa dakinsa wanka yayi yasa kayan bacci yakoma kan gadonsa ya kwanta tuna nin safiyya fal ransa jiyayi Muwadda shiru tashi yayi yabita dakinta kofar yatura yashiga bata parlo bedroom din yashiga hangota yayi can kuryar gadon cikin wata bingilar rigar bacci tanata shashshekar kuka da sauri yakarasa kan gadon yakira sunan ta

“baby kuka kuma meyafaru haka “?

Shiru taimasa tacigaba da kukanta yai ta magana damunta yayi ta tashi xaune tace

” pls katafi kabarni haka ka koma gurin matarka ”

Kansa ne yadau xafi yarasa dame zaiji jikinsa yajata yafara rarrashinta tayi shiru yayi yai daita ta taso su koma dakinsa taki yahakhra ya kwanta adakinnata ahankali yafara aikamata da sakonni tanajin hannunsa ajikinta ta suka daga gadon takoma kasa ta kwanta biyo ta yayi ta kuma guduwa yarasa yadda xaiyi da ita haushi ne yakama shi yaja mata kofar yafita xuwa dakinsa asaman gadonsa ya kwanta yarasa meyake masa dadi.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:8Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝

 

 

*Sakon barka da salla gareku yanuwana mata dafatan anyi salla lpy ya gjyr aiki ubangiji Allah yamaimaita mana ya Allah ya huta gjy ya nuna mana badin badada AMEEN*👏🏻

*Allah kadawo mana da alhaxanmmu gida lpy yasa sunyi hajji mubarak*🕋

 

*wannan shafin nakine kawata shaawa ibraheem inai miki barka da salla dafatan kinyi salla lpy naseeba nagaida ki kyauta*👌🏻😘

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*71*

 

 

~~~Abangaran Muwadda kuwa Assadiq yana fita ta tashi ta kulle kofarta da mukulli saman gadon takoma ta dau wayarta takira layin muktar kmr jira yake takirashi bugu biyu ya daga

“Hello baby lpy a wannan daren, bakiyi bacci ba ”

” muktar kewar ka tahana ni sukuni gsky danasan haka auran yake wlh da banyi ba”

“baby me kike so kice min, banfahimci inda zancan ki yadosa ba, yanxu ina mijin naki “?

” yana dakinsa nema yake ya takuramin ni wlh bazan iya ba nifa kai naiwa tanadin kaina amma nema yake ya dagula mana lissafi ”

” baby kenan kinajina ko ki bada kai bori ya hau kingane ko sai kin saki jikinki sannan zamu sami biyan bukata, kinji ya kike shiru baby ”

” to amma muktar nifa gangar jikina kai nakewa tanadi in nadawo gareka me xan mallaka maka kenan?

“baby kenan kar ki damu ai ni ke nake so dan haka kar kiji komai ”

” shi kenan dear nagode sai kajini inna huta daga gjyr biki zanxo muhadu kaji ”

” shikenan baby sai kinxo ki kula da kanki ”

Sallama sukayi ta kashe wayar ta gyara kwanciyarta ta kwanta.

 

Washegari da wuri safiyya ta tashi tahada break fast tai wanka ta shirya fadila daki takoma ta dau wayarta takira layin umminta Bugu uku tadaga

” Hello ummina, ina kwana ”

” Lpy kalau safiyya, ya fadila da babanta ya abokiyar xaman taki dafatan ba matsala “?

” Lpy kalau ummi Alhmdulillah ba matsala, ummi dama fadila na yaye yau shine nakeso najiba tazo ta dauketa ”

” oh ni nafeesa, safiyya haka ake yayan sama taka ko dan rubutu baai mataba ”

” wlh ummi momy ce take ta fada wai naki in yayeta shiyasa nagaji nayi yau ”

” shikenan safiyya Allah yarayata zata zo anjima kice baffa nada sabuwar amarya ”

” ai kuwa dai ummi ki sha zamanki kinsami mai tayaki aiki ”

” ai fa, sai anjima to agaida Assadiq din ”

” zaiji ummi ”

A jiye wayar tayi fadila ta zuba mata ido kamar tasan zancan da ake yi tashi safiyya tayi tahada mata kayanta a akwati da kayan wasanta dana ciye ciye tagama tsaf ta dauketa suka koma parlor kallo ta kunna tahada wa fadila tea tafara bata kenan Assadiq ya shigo fadila tana ganinsa ta tashi ta rungume shi daukar ta yayi yacillata sama tanata dariya cikin gwarancin ta take masa magana

“Fadilaty kintashi lpy ya surutu “?

Gaida shi safiyya tayi tadauke kanta guri yasamu ya xauna ya dubeta yace

” sopy break fast dina fa?

“yana nan yana jiranku tun dazu ”

” ni dawa kuma?

“kamar ya kai da wa, kai dawa ka kwana oh dankazo gurina xaka manta da wacce ka kwana ”

” yasalam sopy pls kar ki bani ciwon kai da safan nan, kicire kishi aranki, ni jeki kawo min tea ”

 

Fita yayi yakoma part din sa safiyya ta kwashi kayan abincin takai masa sanda tashiga tazaci zata ga Muwadda sai shi kadai akwance yadora fadila akan ruwan cikin sa tanata wasa kallonsu tayi suka bata shaawa cikin nutsuwa tace

” Dee gashi amma ina Muwadda?

“sannu da aiki sopy kimata magana tana dakinta ”

 

Shiru taimasa tai kamar bataji shi ba sai kuma ta juya tafita zuwa part din Muwadda akulle tasami kofar ahankali ta fara bugawa daga ciki aka tambaya

 

” waye anan”?

“safiyya ce ki fito muyi break fast ”

“ok ina xuwa aunty”

Tafiya safiyya tayi takoma dakin Assadiq yana nan yadda tabar shi idinsa arufe Karasawa tayi kusa da shi ta kira sunansa

 

“Dee kalau kake kuwa ko bakajin dadi “?

Bude idonsa yayi wanda suka rine suka xama jajaye yana daga kwancen yace

 

” samo min kanwa kijika min kadan ki kawo min cikina ke ciwo, fara xuba min ruwan tea kadan kar ki sa madara ”

 

” ok, sannu Allah yasawake Dee tun yaushe kake ciwon cikin “?

” koma yaushe ne ai baku da damuwa dan haka kawai ki kawo min kanwar inxansamu inkuma baxan samu ba in hakura ”

” oh Allah yabaka hakuri Dee bani nakar zomanba ratayar ma baabaniba”

 

Ruwan tea ta zuba masa tafita samo masa kanwar tana fita Muwadda ta shiga ta sami kusa dashi ta zsuna bayan tadau fadila dauke Kansa yayi cikin kwantar da murya ta gaidashi atakaice ya amsa matsawa tayi jikinsa cikin fushi yadaga mata hannu yace

 

“Muwadda meye haka kuma?

*sweery pls kayi hakuri kaji wlh,

Kantakarasa yadakatar da ita

“pls kibarni inji da abinda yake damuna kar ki kara min damuwa, amma kisani ni ba saurayi bane da aurena kika ganni dan haka ki rike kayan ki banaso ”

 

Shigowar safiyya ne yasata yin shiru takawo masa kanwa a cup yakarba yasha Muwadda ce tagaida safiyya taamsa a mutunce suka xuba tea da doya da kwai sai farfesun kaji suka fara ci safiyya ce tamaida dubanta ga Assadiq tace

” Dee axuba ma doyar “?

” baxan iya cin doyar nan ba safiyya kude kuci ”

Tashi yayi yashiga dakinsa sai gashi yafito cikin shirin fita safiyya tadubeshi da kulawa tace

” Dee fita kuma xakayi kai da bakajin dadi ”

 

” ummm, fita xanyi ana jirana a office ne ”

 

Muwadda de na kallonsa sai taji yabata tausayi guri yasamu ya xauna saboda yadda cikin sa yake murdawa sannu sukai masa safiyya ta kwashe Kwanikan tafita dasu dakinta ta koma Assadiq ma tashi yayi xai fita yadubi Muwadda da fadila a hannunta yace

 

” inkingama xaman kirufe min daki ”

” aa fita nima xanyi, sannu sweery Allah yakara sauki ”

Banza yayi mata tafita yabita abaya yarufe dakinsa part din ta ta nufa da fadila shi kuma yakoma part din safiyya tana daki a kwance yashiga ido yaxubawa bayanta bacci ne yafara dibar ta sai jin mutum tayi a bayanta yana tasauke ajiyar xuciya ahankali ta juyo ta kalleshi rikici tagani fal idonsa magana xatayi ya toshemata bakinta dana sa bakin ahankali yake tso tsa sarrafa ta yafara yi biye masa tayi saboda yadda tafuskanci dalilin ciwon cikin sa sai da taga yana kokarin wuce gona da iri ne sannan tazame jikinta takoma gefe ahankali yafara sauke ajiyar xuciya cikin kasalalliyar murya yace,

 

“Sweet sopy yaushe xaki karbi girki nagaji wlh da rashinki kusa dani ”

 

” Dee da sauran kwanaki fa kai da kake da sabuwar amarya ”

 

Ido yaxubamata ya mare rece fuska dariya yabata tashi yayi yashiga toilet dinta yai wanka yafito yadan sami saukin ciwon tana kwance inda yabarta dubansa tayi tace

 

” Dee yau Fadila xata tafi gidan ummi yaye ”

 

Cikin sauri yajuyo ya kalleta” sopy bayan ciwon cikin da kuka haddasa min be isheki ba sai kin haddasa min hawan jini ”

 

” Dee hawan jini kuma, dan ankai fadila yaye shine xan samaka hawan jini ”

 

” Hmmm rabani da Fadilaty kamar raba ni da lpy tane sopy ”

 

” to gashi na fadawa ummi axo a dauketa yanxu ya zaai kenan Dee ”

” to ai kin gama magana sopy tunda kin riga kin fadawa ummi xatazo, mexance yanxu me xaa siyo mata kenan ”

” asiyo mata kayan da tafi so na hadamata
wasu dai ”

” sunyi kadan sopy, zandawo anjima xanyo mata shping ”

” Dee kenan shikenan Allah Yadawo da kai lpy ”

Ya amsa da ameen, yafita tashi tayi tashiga toilet

Assadiq yana fita kai tsaye motar sa yanufa yafita Muwadda na kallonsa dakinta ta koma tasami fadila tayi bacci kwantar da ita tayi a kan gadonta tashiga kitchen ta dakko juice ta dawo daki muktar ta kira suka sha hirarsu

 

 

******

Yau malam mudassir suka kawo kudin auran farhana shi da abokinsa, dubu 100k hade da sa rana wata takwas

 

Farhana najin labarin kawo kudinta ta kurma ihu sai da dady yaimata kaca kaca sannan tai shiru momy ma ranta yagama baci dan bata son auran farhana da ibraheem amma ba yadda taiya

Najiba ce tazo daukar fadila da Sallama tashiga dakin safiyya a kitchen tasameta tana girki jin muryar najiba tayi yasa tafito ganin najiba tayi ta rungume ta nan suka koma parlor suka gaisa kitchen din suka koma suka cigaba da aiki tare sai da suka kusa kammalawa sannan Muwadda takawo fadila nan suka gaisa da najiba cikin mutunci xama tayi suka ci abinci tare suna taba hira alaka suka kammala dakinta ta koma ta na zuwa taga farhana na kallo dubanta tayi tace

“ke kuma yaushe kika zo ”

 

” Tun dazu, inata jiranki kina ina ne?

“kmr yaya ina dakin aunty safiyya mana kinji wata banzar tambaya ”

 

” lallai ma aunty Muwadda ke har wani dakinta kike xuwa sai kace baki da wayo ”

Fada Muwadda ta rufe farhana dashi taimata kaca kaca haushi farhana taji tai tafiyarta gida tana xuwa ta sa kuka Muwadda ta zagi momy

Sai yamma Assadiq Yadawo da kaya niki niki na yayan fadila har da sababbin kaya dakansa yakai su ita da najiba dasu ka je da kyar yarabu da fadila suka wuce ciki yaja motarsa yatafi

 

Momy ce take tafaman kiran wayar Muwadda taki dagawa karshe taaiki Saa lokacin Muwadda suna tare da safiyya wacce zazzabi yafara rufewa saboda yaye Saa tai Sallama tashiga ta gaida su kana tadubi Muwadda tace

Aunty Muwadda momy ce taaiko ni wai me farhana tai miki “?

” kmr yaya metaimin ki koma kice ta tambayata ita me taimin, ke nifa bazan jure iskancin *KANNAN MIJINA*ba wlh ”

Safiyya najinsu tai musu shiru tashi Saa tayi ta tafi fadawa momy sakon Muwadda.

 

 

💦💦
*HAPPY SALLAH KABEERU*💦

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:42Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W>F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

*subahanallahi wabihamdihi subahanallahil azim*

 

*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝

 

*Ina gaisheki @faty Abdullahi blouse dafatan kinyi salla lpy nagode da kulawar ki gareni Allah yabar kauna wannan shafin nakine ke kadai uwa ga Fadilaty binty*😘

 

 

 

*72

 

Sanda Saa ta koma gida a parlor ta tatar da su momy har da Assadiq da Sallama tashiga ta gaida Assadiq kana tadubi momy tace

“momy wai tace ki tambayi aunty farhana ai tasan abinda tai mata ”

” haka tace miki, wai me yasa Muwadda take son bani kunya ne

Assadiq yana jinta yayi mata shiru yana chart da faruq, jalila kuwa inbanda dariya ba abinda take momy ce tadubi Assadiq tace.

Assadiq kanajina da matarka ko “?

” wace matar momy?

“au kai duk abinda aka fada yanzu baka ji ba ”

” hankalina yana gun faruq momy, meyafaru?

“Muwadda ce mana daka zuwanta zata tsiro da muna nan halaye ni da nake so su zauna lpy da kannanta ”

” ayya bata kyautaba gsky momy Allah ya kyauta ”

Yana gama fada ya tashi ya nufi saman dady nan yabar momy dasu afifa nata faman fada.

Dakin dady yashiga da Sallama cikin muryar masu mura dady ya amsa guri yasamu ya xauna ya gaida shi

” Dady na barka da hutawa ”

” yauwa sadauki ya office ina matar tawa?

“office Alhmdulillah dady, matarka angirma anmata bulala yau ”

” mashaallah tana can tana rigima kace ”

” Eh to dayake tana gidan su safiyya, dady baka jin dadi amma?

“wlh sadauki mura in akace shekaru sunja sai hakuri yau nan ciwo gobe can ”

Subahanallah sannu dady Allah yakara sauki yajamana kwanan ka”

“Hmmm ameen sadauki, faruq yace nan da wata guda zai kammala karatunsa zai taho gida haka ne?

“eh dady haka ne yanxu ma mukai magana da shi ”

” to yayi kyau Allah yakawo shi lpy ”

” Ameen dady ”

Sallama yaimasa yafita yaiwa momy sai da safe yana fita suka hadu da Dr almustapha yaxo gurin jalila hannu yabashi suka gaisa Assadiq ne yadora da

” Dr ina amanar dana bawa najiba?

“Hmmm Assadiq kenan tana nan kalau nabarota a gida tanata wasanta ”

” Allah sarki Fadilaty binty wlh dan dai sopy tariga tasanar da ummi zaakawo ta da dakaina zanya ye Fadilaty ”

Dariya Dr yayi nan suka taba hira karasowar jalila ne yasa yai masa Sallama yatafi ahankali ta karaso gabansa tasami daya daga cikin fararan kujerun gurin ta zauna binta yayi da kallo ahankali yace

” matar Dr kinyi kyau yakamata inyi inturo ayi komai agama indau keki sai abuja, dan bazan iya zama a gidan da aka bani ba mata ba ”

Cikin shagwaba tace,” Gsky ni bazan iya tafiya abuja inbar fadila ba ”

” cab jalila kina tunanin Assadiq zai baki fadila ne, muma da munyi aure zamu sami baby ”

Kunya yabata ta rufe fuskarta da tafin hannun ta nan suka sha hirar su da zai tafi yashiga ya gaida momy taamsa bayabo ba fallasa su farhana suka zuba masa ido aranta ta yaba haduwar sa amma kasancewar sa yayan safiyya ko kallon sa basu yi ba da zai tafi ya ajiye wa momy kudi ya tafi

 

Sanda Assadiq ya koma gida safiyya tana can cikin dakinta a kwance xaxxabi ya rufeta ruf part din ta yafara shiga bata parlor yaduba kitchen nan ma bata ciki kai tsaye dakin ta ya nufa nan ya hangota kwance da sauri yakarasa kan gadon bargon ya yaye nan yaji hucin zazzabi tabata yayi yaji xafi rau jikinta ahankali yafara tashinta bayan yajata jikinsa

“sopy, meyasameki haka “?

Ahankali ta bude idonta can kuma ta runtse su kidimewa Assadiq yayi yashiga tambayar ta

” sopy rabuwa da Fadilaty ne ko “?

” Dee nono ne yake min ciwo saboda yayen danayi shi yasa min zazzabi”

“sopy daga yaye sai ciwo mugani ”

Rigar ta yadaga nan yai toxali da su sun ciko dam shi sai suka bashi shaawa nan yashiga murxasu kara tasa tadubeshi tace

” wash wlh Dee da zafi dan kabari banaso ”

” ayya sannu matar Assadiq sau daya zankuma tabawa kinji ”

Nan yacigaba da jagwal gwalata sai da tasa masa kuka sannan yakyaleta tashi yayi yazubo musu abinci a kitchen Yadawo tana kwance sai kuka take da hanzari yakarasa gabanta yakira sunnanta

” sopy tashi kici abinci kisha magani pls kibar kukan haka nadena kinji ”

Tashi tayi tazauna dakansa yadinga bata tanaci taci kadan yakarashe ragowar magani yaballo zai bata girgiza masa kai tayi alamar aa yaduba mata ido can yanisa yace

” sopy antaba ciwo ba magani kisha xaki ji dadin jikinki ”

” Dee ummi tace kar insha magani ”

” sopy ai paracetamol xaki sha, to wai meyasa baa shan magani?

“Dee in ansha magani fa motsewa yake ”

” me din?

“nonon mana ”

” aa to karki sha sopy, nide ko fasa yayen nan zaai bari inyiwa najiba waya zanzo In dauki Fadilaty ”

” Dee pls karbarta ni dai katafi gurin Muwadda tana jiranka

“sopy bazan iya tafiya inbarki ba ”

” Dan Allah katafi zankula da kaina ”

” shikenan sopy zantafi tunda korata kike nasan tsoran da kike ”

” ummm nayarda tsoran nakeji ”

Kwanikan abincin ya dauka yafita dashi a kitchen ya ajiye yakoma part din Muwadda tana kwance a kujera tana waya da mamanta guri yasamu ya xauna ya maida dubansa ga tv bata bi ta Kansa ba tacigaba da wayarta

” wlh mama yaran basu da mutunci ni bazan zuba musu ido ba da sunmin zan mayar musu ”

” nagoyi bayanki yata duk wanda yaimiki kimasa kinji ”

Sallama sukayi ta kashe wayar mai da dubansa yayi gareta yace

” ko zansan me yahadaki da farhana “?

” wai akan me zaa dameni da zancan farhana ne, ita yarinyar bata fadi rashin mutuncin datai minba ”

” ke Muwadda kishiga hankalinki kinji ko kisan da wa kike magana bana son raini ”

” kmr yaya wai meyasa bakwason gaskiya ne ”

Mamaki ne yakama Assadiq yarasa ma me xaice kawai ya tashi ya fita

Masifa Muwadda tai tayi ita kadai

Dakinsa yakoma yai wanka yakira najiba ta hada shi da fadila yai tai mata hira bacci ne ya dauketa ya kashe wayar ya kwanta

 

 

 

Yau Muwadda ta cika kwana bakwai adaddafe Assadiq sukai kwana 7 nan yau da farin ciki ya tashi xai koma gurin safiyya kullum sai yaje yaga fadila ummi tagaji da sintirin da yake musu ta dawo masa da yarsa

Afifa ce taja kawayanta kai tsaye dakin Muwadda suka nufa tayi girkinta zatayi baki tagama ta jera a dining xama sukayi afifa tashiga kitchen ta dakko musu juice da kofuna abincin ta dakko musu nan suka baje suka fara ci
Motsi taji da hayaniya a parlon tafito mezata gani su afifa suncinye mata abincin dataiwa bakinta wani mugun kallo tafara yaimusu.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

 

 

 

.
[6:06Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillah azim*👏🏻
.

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

 

*wannan shafin nakine ummata a gaskiya bani da bakin da zan gode miki bisa goyon bayan da kike bani wajen kyawawan manufofina sai dai fatan Allah yasaka miki da gidan aljanna haka ina mika Godiya tamusamman gareku kannena bisa ziyarar da muka kai gidan marayu dafatan kun koma gida lpy gsky nayi farin ciki bisa yadda nasami gidan marayun cikin walwala da nishadi sakamon partyn da wani layin waya suka hada musu Allah yasaka musu da alkhairi AMEEN*😘

 

 

 

*73*

 

 

~~~cikin masifa da bacin rai Muwadda ta karaso gaban su afifa dubansu tayi a wulakance tace

“kut afifa kina hauka ne ko kuma tsabar iskanci ne da gadara, wadannan banzayan fa?

Cikin tsiwa afifa ta dubeta tace, “haba aunty Muwadda wai me yasa kike irin haka ne mu da gidan yayanmmu to gsky bahaka aunty safiyya take mana ba, ko kimanta mu *kannan mijinki*ne?

” ke! ni kike fadawa haka dan kasancewar ku *kannan mijina*sai akace anbaku damar yin duk abinda ranku yakeso, dalla malamai kutashi ku fitar min a daki yan iska kawai”

Bashiri suka dibi mayafan su suka fita afifa nata zage zage adai dai part din safiyya suka ganta zaune ita da fadila ko kallon su batayi ba amma tanajinsu da Muwadda kawayan afifa ne suka gaisheta taamsa suka fita sunaiwa afifa dariya sun sami dai dai su saboda sun san rashin mutuncin da sukewa safiyya

Kai tsaye gida tawuce tana xuwa ta tatar da momy ita da yaya hannatu tazo ko gaida yayar ta su batai ba tafada kan momy tasaki kuka tambayarta momy tashiga yi

“ke afifa lpyr ki kike kuka waya tabamin ke ince ko matar Assadiq ce “?

” momy aunty Muwadda ce ta cimin mutunci agaban kawayena shine sukai ta min dariya ”

” cab narasa gane manufar yarinyar nan wlh tun da tazo gidan Assadiq nafiskanci akwai fitina aranta wlh,

Su yaya hannatu suna jinta sukai mata shiru jalila kuwa dama in irin haka tafaru dariya kawai takeyi jin basu ce mata komai ba yasa tadubesu tace

” hannatu, jalila kunaji na inata magana kinmin shiru ko ina farhana take ne nasan xata tayani fadan ai ”

” momy me zamuce ke da yarki, waxai shiga fadan ‘ya da uwa ”

” haka ne hannatu, amma wata kusar ai tafi kusa ko, ni banyarda atabamin’ yaya ba ”

 

Farhana ce tashigo cikin shigatar ta data saba wato kananun kaya sai magan ganu takeyi yaya hannatu ce ta dubeta tace

” ke kuma fa zaki shigo kina yaiwa mutane kunkuni me akai miki “?

” Gsky nide yaya banason ibraheem din can wlh, kullum yazo sai yace shiga ta batai ba sai na saka hijjabi ni bazan iya ba ”

” Dallacan yiwa mutane shiru ai shine dai dai ke sha sha kawai ”

” hannatu meyasa kike haka ne memakon ki rarrasheta sai ki kuma sata a damuwa to kija bakinki kiyi shiru banason jin bakinki, wlh har ga Allah banason auran nan na farhana da ibraheem ”

” momy me akaiwa afifa take kuka?

“ita da Muwadda ne ”

” aunty Muwadda kuma me yasa bata da mutunci wai sai nafara gwada mata rashin mutunci ko, ina zuwa wlh sai naje gidan yanxun nan ”

” Gidan wa zakije?

Gaba dayansu suka juya suna kallon mai maganar dady ne yashigo parlon

“tambayar ki nake farhana gidan wa zakije”

“Dady aunty Muwadda ce ta daki afifa”

“shine me, dan andaki afifa kinsan me taimata da zaki kwashi jiki kitafi ke mara kunya ko, to in naga kafarki awaje sai ranki yabaci,

Yanxu hajiya kareema kina kallon yarannan suna abinda be daceba me makon ki musu fada, aa sai ki biye musu ko, nazaci ita Muwadda ba yarki bace, amma har kunfara samun sabani daita, to yayi kyau ”

Shiru sukayi suna sauraran sa yagama fadansa yaya hannatu tagaida shi ya hau sama nan ran momy yakuma baci

 

Abangaran Muwadda kuwa su afifa suna fita ko parlon bata gyara ba taja motar ta tafita

Sanda Assadiq Yadawo gidan be ga motar Muwadda ba kai tsaye part din safiyya ya nufa tana kitchen tana girki kamshi ya cika kitchen din sai fadila a parlon tana kallon tom and jerry tana ganinsa ta rugo aguje ta rungume shi

“papa, oyoyo ”

” oyoyo Fadilaty, ya kike ”

” Lpy kalau papa ina Sweet dina ”

” lala nayi lefi ban siyowa Fadilaty Sweet ba yau ”

” sauka tayi daga jikinsa tanufi kitchen gurin safiyya abakin kofa ta tsaya tahade fuska ala dole tayi fushi bayanta Assadiq yabiyo tana ganinsa takoma gurin safiyya, juyowa safiyya tayi tadubesu tace

“Dee sannu da xuwa ”

” yauwa sopy, ya gida ”

” gida lpy kalau, fadila bakiga papa ba ”

” naganshi mamma, munbata andena kula shi ”

” lala, wannan ai fadan ku ne na manya waxai shiga, me yai miki ”

” yace zai siyo min Sweet kuma be kawo min ba”

Karasowa yayi ya tsuguna agaban ta yakamo hannunta yahada da nasa yace

“binty, kiyi hakuri yanxu inmuka ci abinci mukai salla sai muje tare in siya miki Sweet ko?

Mai da dubanta tayi ga safiyya tace,

” mamma, zaki bimu kema papa yasiya maki Sweet ”

” aa fadila bazaniba kuyi tafiyar ku ”

” papa bazaniba tunda mamma na bazata ba ”

Dariya sukasa suna cike da mamakin saurin girman fadila ga dan karan surutu taimaka wa safiyya yayi ta kammala girkinta suka jera a dining dubanta yayi ashagwwbe kmr karamin yaro yace

” Sweet sopy gsky yau sai anbawa Assadiq kulawa ta musamman hade da agajin gaggawa ”

Fadila ce tazuba musu ido tana kallon su safiyya ce ta kula daita kasa kasa tace

” Dee yarka kai take kallo fa kana shagwaba ”

” Dariya yayi yalakace mata hanci yace

“Fadilaty me papa yace “?

Shiru taimasa tacigaba da kallon ta mai da dubansa yayi ga safiyya yace

” sopy yata bani take kallo ba kawai de kice jamin aji zakiyi, yanzu kiraka Fadilaty gurin Muwadda muje ki taimaka min inyi wanka ”

” Dee Muwadda ai bata nan tafita tun yamma ”

” kmr yaya tafita, kina so kice min tafita bada izini na ba shiyasa banga motar ta ba “?

” aa haba Dee yazaai kaimin wannan tambayar yazaai insan bata tambayeka ba wannan ai tsakanin ku ne ko “?

Ransa ne yabaci yafita yakoma part din sa, abinci safiyya ta zubawa fadila taajiye mata a gabanta tace

” oya maza kici abinci yanxu zandawo kinji ko

“mamma nakoshi, nide kidima min madara insha”

“aa fadila kici abinci tukunna kinji ko ”

” innaci sai ki dama min insha ”

” eh ”

Tana gama fada tafita part din Assadiq ta nufa yana kwance daga shi sai gajeran wando da vest ahankali ta karasa gabansa kusa dashi ta zauna yana ganinta ya ya tashi dora Kansa yayi akan cinyar ta yadubeta yace

” sopy Muwadda tana yawan bani ciwon kai, yarinyar nada damuwa ”

” dan Allah Dee kayi hakuri kacire damuwa may be uxuri ne yasa ta tafita ”

” yaisa haka sopy, wane uzuri ne zai fitar da mace batare da izinin mijinta ba, dan Allah mubar maganar raina dada baci yake ”

” shikenan Dee Allah ya huci zuciyarka”

“Ameen, ina Fadilaty binty ”

” nabarta a parlor tana cin abinci da kyar ma tayadda taci, wai ita madara zata sha ”

” madara kuma sopy, makaranta yakamata insata wayon ta yaisa ”

Yafada yana kokarin zuge mata zip din rigarta bakinsa yasa yafara sarrafasu biye masa tayi dan faranta masa rai safiyya ta kware wajen kula da mijinta zame mata yayi kmr zakin da yadade beci abinciba sai da komai yalafa sannan tahada musu ruwan wanka tare sukayi kmr yadda suka saba

 

Muwadda kuwa tana fita gurin muktar ta wuce suka sha hirarsu da zata tafi tabashi kudi tare da yaimasa alkawarin zata kawo masa wasu inta karba gurin Assadiq sukai Sallama ta wuce gidansu nan ma tai zamanta tabawa mamanta labarin abinda afifa taimata cikin fushi mamanta tace

“Muwadda duk wacce tai miki ki zage kici ubansu kar ki dau raini kinji nafada miki ”

” naji mama ”

Nan sukaita hirarsu da kulle kullansu sai wajen 8sanan ta ta tafi

Afifa ce taje wani super market siyan mayuka tunda tashiga matashin saurayin yake kallon ta sai da tagama dibar kayan tsaf taje biya matashin yabita kudin yazaro yabiya dubansa tayi tace

“ko me hakan yake nufi kazaci bani da kudin biyan ne ko me “?

” ko daya gimbiyata kauna ce, ni suna haisam ambasador kabeer mahaifina shine ambasador na kasar england yanxu haka ma munxo hutune dafatan zansami karbuwa ”

” hmm baka da damuwa ”

Nan sukai musayan number sukai Sallama ta tafi ranta fari tas tasami irin saurayin data keso

 

To waye haisam ne 🤔

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:43Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Lahaula wala kuwata illa billahil azim*👏🏻

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

 

💙
*Ina godiya gareku masoyan littafin kannan mijina inajin dadin yadda kuke biye da ni inayinku kmr yadda kuke yina Allah yabar kauna taku NASEEBA GAWO*💙

 

 

*74*

 

~~~Tun da afifa suka rabu da haisam take ta faman murna tana xuwa gida ta bawa momy labarin sa, murna gurin momy baa magana jalila kuwa haushi ma afifa ta bata momy ce ta dubi afifa tace

“lallai kincika mai Saa afifa tun tuni naso kusamo irinsu Allah beyiba gashi ke Allah ya baki ”

” wlh kuwa momy na kinsan yace england xamu tafi in yaaureni wlh kuma baki ganshi ba yaro ”

” to munji banza, zaki cikawa mutane kunne ”

Cewar farhana tafada tana dada kwanciya a kujera

” Aa farhana ki rabu da ita tabani labari, ina ruwanki inajinki afifa ”

Kan tayi magana kiransa yashigo wayarta da sauri tadaga suka gaisa yaimata ya taje gida tare da naman kwatancan gidan su ba musu taimasa sukai Sallama tare da alkawarin zaizo

Sanda Muwadda ta koma gida su Assadiq basa nan sunfita tana xuwa ta ga gidan ba kowa shiru tsoro ne yakamata motar ta taajiye ta nufi gidan su Assadiq

Da jalila ta ci karo suna zance da Dr almustapha ko kallonta batai ba ita kuwa Muwadda tsayawa tayi takarewa Dr kallo take ta gano kmr sa da safiyya wuce su tayi tashiga ciki kallon jalila yayi yace

“habibty ya kina ganin bakuwa baki gaida ta ba ”

” ba bakuwa bace, aunty Muwadda ce amaryar ya Assadiq, karbarta bata da kirki wlh ”

” ummm, duk rashin kirkinta ai bekamata kiki yimata magana ba ko ”

” shikenan zan gyara, ya ummi na?

“Lpy kalau, tana gaida surukarta ”

Muwadda tana shiga parlon ba kowa aciki sai farhana a kitchen jin motsi yasa ta fitowa kallon kallo aka tsaya yi can Muwadda ta dauke kanta tace

” momy fa?

“kmr ya momy fa, uban me zatai miki “?

” Hmm farhana kenan, tambayata ma kike, to ubanki zatai min shikenan ”

” kut ke kin isa ma kizo har gidan mu ki zagi ubana”?

Momy ce taji kmr hayaniya a parlon tafito ganin Muwadda tayi tana share hawaye kallonta tayi takarasa gabanta tace

“yata kukan me kike waya taba ki? Ince ko matar Assadiq ce, dan ba kirki ne daita ba?

“aa momy daman tun rannan nace ya Assadiq yabani kudi zanyi siyayya yahana ni shine yau natafi gurin mama zankarba bayan nadawo natarar dasu basa nan shine nataho nan, ina zuwa farhana tafara zagina ”

” farhana zagi kuma “?

” wlh momy bazaginta nayiba itace ma tazageni ”

” rufemin baki farhana Muwadda ba yayar ki bace dazaki mata rashin kunya eyi, banaso ki dena ”

” momy gsky………

“banason jin komai kimin shiru, kinci abinci Muwadda?

“aa momy, banyiba?

“to yanzu kici abinci, tukunna zan nemi Assadiq din yanzu awaya kinji yata ”

Saa ta kwallawa kira da sauri ta karaso dubanta tayi tace takawo wa Muwadda abinci

************

Su Assadiq suna fita kai tsaye wani babban kanti suka nufa, nan yasaiwa fadila kayan kwadayi na yara yaiwa momy ma siyayyar duk wanda yagansu sai sun bashi shaawa yabiya kudin suka fito abakin kantin yaga wani matashin saurayi da wata budrwa manne da juna sunata tabarar su suka zo suka gifta ta gabansu matashin sai kallon fadila yake taburgeshi tana sanye da wata doguwar riga blue mai hannun vest iya gwiwarta da yar tsana a hannunta, mika mata hannu yayi saurayin

Beauty mugaisa ”

Assadiq ne yajanye ta ya kalleshi yace”

“meya ruwanka da yata malam “?

” oh, yi hakuri mai ya taburgeni ne babyn, bansan baa kulataba ”

Tsaki Assadiq yaja yadauki yarsa suka wuce mota sai bayan sun shiga motar ne safiyya ta dube shi tace

” Dee banji dadin abinda kaiwa saurayin can ba ”

” ni naji sopy, baki kula da yadda suke ba ko “?

Shiru taimasa yaja motarsa suka wuce gidan ya hannatu sanda suka isa suna parlor ita da mijinta da su ashraf suna ganinsu yaran Suka taso suka rungume fadila musamman nabil

” ga mata ta, ga mata ta, abbana kaga fadila ta ta girma ”

” naganta nabil, dadyn ta zai baka kuwa, naji ance sai muntara kudi ”

Dariya sukayi suka gaisa ya hannatu taja fadila jikinta duban safiyya tayi tace.

” safiyya yarinyar nan ta girma me kuke bata haka ”

Caraf fadila tayi tace” kinsan me nake sha “?

” aa binty, sai kin fada ”

” papa,infada mata “?

” fadamata mana Fadilaty, nima bansan abinda mamma take baki ba ”

Karasawa tayi kusa da kunnan ya hannatu tai mata rada dariya ya hannatu tayi nabil ne yace

” Fadila mijinki beji ba, zoki fada min kinji ”

” naki bazan fada maka ba ”

Wayar Assadiq ce tafara ruri yana dubawa yaga momy ce dagawa yayi

” kana ina Assadiq “?

” momy muna gidan yaya hannatu ”

” to, kazo ina son ganinka yanxu ”

” to momy ganinan”

Tashi sukayi zasu tafi ya hannatu ta ja fadila dakinta tabata tarkacan kayan wasa tai ta murna abban su nabil kuma yabata kudi mika masa kudinsa tayi tace

“abban ashraf karbi kudin ka sunyi yawa gsky karage”

Dariya tabasu, yace “ki rike du nabaki”

“papa wai in karba ”

” karbi mana Fadilaty ai kyauta yabaki, kice kin gode ”

” nagode abban ashraf ”

Nabil ne ya dubeta yace,

” matar nabil sai yaushe, ko sai nazo zance

 

“mamma kinji shi ko ai bakyau kula maza ko?

“Fadila nabil ai yayanki ne ”

Sallama sukai musu suka tafi tun ahanya Assadiq yake kallon safiyya da sexy eyes dinsa hannunta yakama yace,

” Sweet sopy yazaai ne Assadiq fa……..

“Dee dan Allah kabari wlh yarka tana kallon ka fa kabari muje gida duk abinda zaayi sai ayi ”

” shikenan sopy, Fadilaty binty ko tayi bacci ne ”

” aa papa gurin dady xaka kaini inbashi kudina yaboyemin ”

” angama Fadilaty ”

Suna Karasawa yafara kai safiyya gida sannan yadau fadila suka wuce suna shiga fadila ta hau saman dady Assadiq kuwa guri yasamu ya xauna ko kallon Muwadda beba ya gaida momy dubansa tayi tace

” Assadiq me yahada ka da Muwadda “?

” momy banfahimce kiba ”

” eh tace kabata kudi kaki, inbaka bataba wa zakabawa, matarka ko? wacce kafi so fiye da kowa ”

” momy bata fada miki abinda tayi ba ko daman ita atsarinta baa tambayar miji inzaa fita “?

” abar wannan magana bazata kuma fita bata tambaya ba ”

” Gsky momy ni fa bazai dinga kulleniba wlh akan me?

“Muwadda agabana kike fadar haka ”

” aa momy gsky nafada ai yanzu dai kice masa yabani kudin kawai ”

” wlh ko sisi bazan baki ba mara kunyar banza ”

” yaisa haka, nawa kike so?

50k,nake so ”

” shikenan naji ni zanbayar shikenan kutashi katafi ”

” to ai baki bani ba tayaya zantafi ”

Tashi momy tayi ta dakko mata kudin tabata dan haushi Assadiq ko tsayawa beyiba yatafi Momy ce tace

” Muwadda inkin fara gurki kema ki dinga kawo wa dady kinga safiyya duk jumaa take kawo masa ”

” karya haramun, wlh bazan iya ba momy ”

Tana gama fada tai gaba mamaki ya cika momy, fadila kuwa tana can saman dady tanata surutu kudin tabashi tace

” dady kajiyemin kudina kar kabawa kowa kaji papa zanbawa yasiyo min kani ”

” Fadila kenan daman siyo kani akeyi “?

” nima aunty farhana tace siyo ni akeyi ”

” inji farhana nan?

“eh ”

” to ba laifi fadila Allah ya taimaka ”

” dady yanxu mezaka bani “?

” alawa ce gata ”

Karba tayi tasakko tana sauka taga bata ga Assadiq ba ihu tasa ina papa, farhana ce tadaka mata tsawa afifa kuwa dungure mata kai tayi

” Dallacan yimana shiru uban waye yace kihau kiki sakkowa, wlh ba wanda zai kaiki ”

Momy ce tajata jikinta tana rarrashinta shiru tayi taruntse idonta tsoran su farhana yakamata kukan ta jalila taji tafito tana xuwa ta dauketa sukai daki kwantar da ita tayi tafara rarrashinta dubanta tayi tace

” aunty madara xansha

“madara kuma fadila “?

” eh ”

Fita tayi tadamo mata madara a kofi tabata tasha farhana ce tashigo dakin takalleta tace

” uwar iyaye wai kullum inzata kwanta sai tasha madara ”

” wai ita yar madara ba
Cewar afifa jalila ce takwalla musu harara
Tana gama sha bacci yai gaba daita

 

Assadiq kuwa suna xuwa gida yabi Muwadda dakinta yai mata kaca kaca yaja mata kunne kan kar ta kuma fita bada ixinin sa ba banza taimasa

Dakinsa yawuce yai wanka yasa kayan bacci ya nufi dakin safiyya tana bandaki lokacin binta yayi toilet din yasamu jikin bango ya tsaya yana kallonta murmushi taimasa yamayar mata karbar soson yayi yakarsa mata suka gama tadaura towel suka fito

Dakansa yadakko mata rigar bacci fara kal yasamata yajata jikinsa dubansa tayi tace

“Dee fadila fa?

“anbarta gidan momy ”

Hankalinta be kwanta ba amma ba yadda taiya jikinsa ta kuma shigewa cikin kasa lalliyar murya yace

” Sweet sopy kishiryar karbar baby adarannan ”

Cikin shagwaba tace,

” Dee gsky aa bayanxuba ”

mbakinta yakama yashiga tso tsa kmr yasami alawa

 

Washe gari jalila taiwa fadila wanka tashirya cikin wata riga purle anrubuta *fine girl*ajiki da farin mini skirt tasa mata farin ribon tana zaune a parlon ita kadai da kofin madara a hannunta matashin saurayin yashigo cikin wasu kananun kaya masu tsananin kyau da tsada da jaka rataye akafadar sa yahadu sosai tozali yayi da kyakyawar yarinya kallonsa take shima ita yake kallo gabanta yakarsa ya tsuguna hannunta yakama ya dago habarta da daya hannun yace

“mashaallah fine girl, kinsanni “?

Kai ta girgixa alamar aa

” ya sunanki?

“Fadila Assadiq muhammad mai nasara, kasan me papa yake cemin?

“Fadilaty binty ”

Kai mezaka dinga cemin?

” ni kuma zan dinga ce miki fine girl ”

Jalila ce ta fito taga mutum tsugune agaban fadila tambayar kanta take waye wannan kamshin turaran sa yacika parlon.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻

 

 

 

 

 

 

*74
[5 :48Am, 2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Hasbunallahu waniimal wakil*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

 

*💙Dedicated 2 TALENTED GROUP FANS*. 💙

 

 

 

*75*

 

 

~~~Ahankali jalila takara so gurin su fadila tana duba fuskar saurayin nan taga faruq wani ihun murna tasa ta rungume shi su farhana ne suka jiyo ta tana yaya faruq oyoyo gaba dayansu suka fito nan sukai ta murna afifa ce taruga saman dady tasanar dasu zuwan faruq din momy kin yarda tayi sai gashi yayi Sallama yashigo dauke da fadila mamaki ne yacika kusa da dady yaje ya rungume shi tare da mika masa hannu sugaisa sannan ya gaida momy farin cikin yacika momy dady ne ya dubeshi yace

“umarul faruq, kenan wato zuwan bazata ko?, to dakuma kazo katarar bama nan fa “?

” wayyo dady, ai da bansan me xanyi ba, momy na nayi kewar ki wlh ”

” Hmmm, faruq kenan nima haka, ya karatun dafatan angama kpy”?

“Alhmdulillah, momy lpy kalau, yanmatan momy ya kuke? ya rashin kunya kuma?

“Haba ya faruq wace irin rashin kunya kuma ”

Cewar afifa, fadila ce tadubi dady tace

” dady wannan waye ko shima papa na ne?

“kwarai kuwa fadila shima babanki ne kinsan sunan sa?

“eh banaji kace faruq ba ”

” aa fadila uncle dai ko “, cewar jalila momy ce ta dubi yanmatan nata tace

” yakamata ahada masa abinci ko ”

” aa momy baa nan zanci abinci ba gidan ya Assadiq xanje ko fine girl ”

” eh uncle kazo muje in nuna maka papa na inbaka madara kashi, yauwa dady bani kudin dana baka ajiya inbawa uncle dina ya boye min ”

” au daga zuwan babanki zaki karbe ajiyar ki, to ai ba laifi ga kudin ki nan ”

Dariya sukasa farhana kuwa hararar ta tayi suka hada ido jikin faruq takoma ta takwanta dady ne ya ya cewa faruq

” umaru meyasa baka fada mana kataho ba, kar ka kuma irin wannan tafiyar kaji ko ”

” to dady inshaallah bazaa kuma ba, bari inje gidan yayan”

“to agaida su “afifa ce tace

” yaya faruq Allah yasa kasiyo mana waya ”

” bissimillahi, shegiya zata fara, to bansiyo ba ”

Yana gama fada yafita momy ce ta dubi dady tace

To shi kenan kuma sarkin dada ya dawo,’ya’yana sun shiga uku”

Dariya dady yayi yace, ai shine dai dai su ”

Wayar ta dauka tashiga naman layin Muwadda sai da ta Kusa tsinkewa sannan ta daga

” Hello yata”

“naam momy antashi lpy ”

” Lpy kalau, kinajina ko ga faruq nan yataho nan gidanku kimasa abinci kinji ”

” abinci kuma momy, to ai ko ya Assadiq banfara yiwa girki ba bare faruq, gaskiya bazan iya ba wlh ”

Tana gama fada takashe wayar bin wayar momy tayi da kallo afifa tace.

” momy metace?

“Hmm halin Muwadda sai ita, wai bazata iya ba ”

Murmushi kawai dady yayi farhana takuma kullatar Muwadda aranta

 

Assadiq ne kwance agado yana bacci yayin da safiyya ke gaban mudubi tana kwalliya fadila tashigo dakin tana kwadawa Assadiq kira

” papa, papa ”

Bata kula da safiyya ba kan gadon tahaye yayi rub da ciki ta hau bayan sa tafara tshinsa safiyya ce ta dubeta tace

” haba fadila yazaki shigo ba Sallama bana hanaki ba, gashi kinxo kinatshinsa, mezai miki ”

” mamma, kiyi hakuri namanta banyi Sallama ba, sonake yatashi yaga uncle dina ”

Shiru safiyya tai mata taci gaba da shiryawa fadila kuwa ahankali ta ciji Assadiq akunne ba shiri ya bude ido yaganta murmushi ya sakar mata yace

” Fadilaty yaushe kika dawo, waye ma yakawo ki ”

” papa shine katafi kabarni agidan momy ko, munbata ni yanzu uncle ne papa na”

“binty, waye kuma uncle “?

” taso muje parlor kaganshi yace ma fa kamar mu daya ”

Maida dubansa yayi ga safiyya cikin muryar bacci yace

” sopy riketa kuje parlon kiduba kiga ita da waye ne ”

” “to Dee ”

Rike ta tayi suka fita parlon yana tsugune agaban tv yabada baya yana kunna kayan kallo gabanta ne yafadi yayin da fadila ta kwace hannunta daga na safiyya taje ta dane bayan faruq safiyya ce tace

” bawan Allah waye kai ne “?

Juyowa yayi wazata gani, faruq! tafada cikin mamaki dariya yayi yace

” Naam aunty, nasameku lpy, ya hakuri damu ”

Lpy kalau faruq saukar yaushe, shine kai mana bazata ko”

“wlh kuwa aunty surprise nai muku, yaya fa?

“yana ciki bari inkirashi ”

” ok ”

Dakin takoma ta ta tatar da Assadiq yana toilet kwankwasa kofar tayi

” yes sopy, shigo ”

” aa Dee kayi sauri kafito faruq Yadawo ”

” waye faruq Kuma?

“faruq dinka mana ”

” Dagaske kike sopy ”

” Dee kenan kayi sauri ”

Sauri yayi yagama yafito jallabiya yasaka yafita yana ganin faruq ya rungume shi nan suka sami guri suka xauna suka shiga hirar yaushe gamo fadila ta dubi Assadiq tace

” papa kaga uncle dina ”

” naganshi Fadilaty ”

Safiyya ce ta kawo musu abinci cikin sauri faruq yasakko ya zuba yafara ci mai da dubansa yayi ga safiyya yace

” aunty wlh nayi missing din girkinki ”

” ayya kanina yanxu zandinga yimaka mai dadi ”

Fadila ce tafita zuwa part din Muwadda tana xuwa ta ga kofa arufe bugawa tafara yi

” aunty kibude kikga uncle dina ”

Zuwa tayi ta bude mata hannunta taja zuwa ciki kallon ta tayi tace

” Fadila ta a ina kika kwana?

“a gidan momy, naimusu kuka da banga papa ba shine aunty farhana ta dakeni ”

” kut farhana ce ta dakeki, kibarni da ita sai na rama miki kinji baby na ”

” to aunty, zo muje kiga uncle dina ”

” uncle kuma fadila ”

” eh wlh ”

” ok shiga dakina ki dakko min hijjab ”

Zuwa tayi ta kawo mata tasa ta zura takalmanta suka tafi

Yana zaune suna cin abinci da Assadiq suka shiga tana xuwa ta fada kan faruq cikin wasa yace

” wayyo fine girl xata karya uncle dinta ”

” lala papa wlh uncle dina bashi da karfi, yauwa aunty kinganshi ”

Daga da Kansa yayi yaga wacce a ka kira da aunty Muwadda yagani sai yanzu ya tuna ashe fa Muwadda matar Assadiq ce kallon sa tayi tace

” faruq saukar yaushe ”

” Daxu da safe, nasameku lpy?

“Gamu nan dai ya karatun ”

” Lpy ”

Maida dubanta tayi ga Assadiq tace

” Sweery katashi lpy ”

” Lpy, ya kika tashi?

“fine, but i miss u ”

” murmushi kawai yayi tagaida safiyya taamsa a mutunce tai mata tayin abinci ta zuba kadan taci

Assadiq ne yaja faruq suka fita

 

*******

Yau haisam yazo gidan su afifa tacaba kwalliya ta fito zuwa gurinsa yana tsaye jikin lafiyayyar motarsa takarasa cikin yauki kmr bazata taka kasaba murmushi ya sakar mata suka gaisa cikin so da kauna suka sha hira su Assadiq ne suka shigo hango afifa yayi da saurayin da suka hadu a super market cikin bacin rai yakara sa gurin su kallon kallo aka fara tsakanin Assadiq da haisam.

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:27Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*

 

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad*

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

 

*76*

 

 

~~~cikin mamakin ganin saurayin a wajen afifa Assadiq ya dubeta yace

“Afifa waye wannan?

“ya Assadiq haisam sunan sa, shine wanda nake son aure ”

” shut up, afifa, ni kike fadawa shi zaki aura, kin san shi din waye “?

” ya Assadiq dan Allah….

Kan takarasa abinda zata fada faruq yadaka mata tsawa ya kora ta ciki Assadiq ne yamaida dubansa ga haisam yace

“Kai, bakaine yaron da muka hadu dashi a super market ba?

“Eh nine yaya ”

” dakyau, me yakawo ka gurin kanwata?

“auranta zanyi yaya Assadiq ”

” Hmmm kana maganar aure ko?, to da Allah wuce katafi bazamu baka ba, kunaji na ko kar Inkuma ganin ka a gidan nan ”

” yaya wlh….

Faruq ne yakatse shi da cewar, “am abokina dan Allah wuce katafi kar kabari musami sabani da kai”

Juyawa yayi yashiga motar sa sai da suka ga fitar sa sannan suka shiga ciki faruq ne yadubi Assadiq yace

“ya Assadiq waye shi din daka koreshi ”

“. mushiga ciki faruq agaban momyn zanfadi abinda nagani game da yaron,

Suna shiga suka tarar da afifa na kuka momy sai faman rarrashinta takeyi ai kuwa suna shiga ta dubi faruq tace

“kadawo ko faruq zakafara matsawa yayana, to wlh baxan lamunta ba ”

” yasalam momy nifa baruwana akan me zan korota sanin sa nayi ma ita da ya Assadiq ne ”

” momy nasan yaron nan momy ”

Nan ya basu labarin haisam momy ce ta dubi Assadiq tace

” naji Assadiq amma yazama dole abar afifa da zabin ranta dan bazaai mata irin ta farhana ba ”

Tana gama fada taja hannun afifa sukai daki
Assadiq ne yadubi faruq yace,” faruq kaji fa abinda momy tace ”

” naji yaya, bari zamuy

maganar da dady, ashe yaran nan suna nan da halin su ”

” Hmmm me hali ai baya fasa halinsa faruq ”

Tashi Assadiq yayi yatafi office faruq kuwa dakinsa yanufa yai wanka ya kwanta”

 

*********

Makarantar safiyya ta kankama angama yimata komai game da rigistration yau monday itace ranar da zata fara zuwa tunanin inda zata bar fadila bayan tagama shirin ta tsaf tazauna jiran Assadiq kasancewar girkin Muwadda ne jinsa tayi shiru taimasa waya cikin bacci yadauka

“Hello Sweet sopy, yaakayi “?

” Dee, I am waiting 4 u ”

Tafada kmr zatayi kuka dariya yayi yace,” ayya sopyn Assadiq kar ki kuka gani nan ”

Duk abin nan da akeyi. Muwadda na bacci jallabiyar sa yasa yafito tana parlor suna break fast ita da fadila yana shiga fadila ta taso ta rungume shi daukar ta yayi ya karasa da ita gaban safiyya yasami gefenta ya zauna tana sanye da doguwar riga pink ta material ta kamata kallon ta yayi yace

“matar Assadiq kinyi kyau yafafada yana kashe mata ido tare da daukar kofin shayinta yakai bakinsa yana sha yaji zafi da sauri ya hadiye tare da sakin kara

Dariya fadila tasa safiyya ma dariya take masa duban fadila yayi yace

“Fadilaty binty, papan ki yakone kimasa dariya ko shikenan nagode binty ”

” papa kayi hakuri nadena kaji, to rama ”

” bazan ramaba amma bazan sa ki a school ba ”

” wayyo Allah, mamma kibawa Dee dinki hakuri ya kaini school ”

Dariya tabasu sosai Assadiq ya dubeta yace

” Fadilaty waye Dee ”

” bahaka naji mamma na nafada maka ba, nima haka xandiga cemaka wlh ”

” Fadila uwaki amina, kar ki kuma kiransa da Dee, inba hakaba sai na zane bakin ”

” lala papa kaji wai uwata aunty amina fa tazaga ta gidan su aunty najiba, kuma zagi ba kyau ”

” sopy kar ki kuma zagin aunty amina ko Fadilaty ”

” eh papa ”

Safiyya ce ta dubi Assadiq tace,” Dee time fa na tafiya yazaai ne “?

” ya zaai kuwa sopy kawai mushiga daga ciki abawa Assadiq agajin gaggawa inbaso kike ciwon cikina ya motsa ba ”

” Dee wai intambayeka mana?

“inajinki sopy ”

” baadakin Muwadda ka kwana ba yau?

“acan na kwana mana, ke, Muwadda fa lazy ce sam……

“Yaisa haka Dee kabar maganar tsakanin ka ne da matarka wannan, yanzu dai inason wuce wa school yazaai da fadila?

“emmm, akaita gidan momy yanxu inna shirya zanzo in dauketa sai inkaita school ”

Murna fadila tafara yi zaasata a school, kudi yadakko yabawa safiyya ta kwashe Kwanikan takai kitchen tashirya tsaf suka fito sai da Assadiq yafara tura fadila gurin mota sannan yaja safiyya suka koma ciki jikinsa yajata yakama bakinta ya shiga tsotsa sai da yashanye janbakinta tsaf sannan yasaketa, magana zatai yaktseta yace

“inkika kuma sa janbaki inzaki fita to nikuma sai na shanye shi tsaf

Fita sukayi zuwa gurin motar ta fadila na tsaye da kofi mai murfi a hannunta duban safiyya tayi tace

“mamma shine kika goge janbakinki bayan yayi kyau ”

Safiyya ce ta kalli Assadiq shima ita yake kallo murmushi sukai hannun fadila yakama yace

Fadilaty bakyau saka janbaki a fita shiyasa ta goge”

“to papa, tadena sakawa tunda ba kyau ”

A mota yasata ya mayar da murfin ya rufe tare da sakar mata kiss hannu safiyya tadaga masa taja motar tafita ciki yakoma

Ya tarar da Muwadda ta tashi tahada cornflakes tana sha daga ita sai vest da skin tied guri yasamu ya xauna ya dubeta yace

” Muwadda break fast dina fa?

“banyiba, nima bakaga abinda nake sha ba ”

” ina ruwana da abinda kike sha, malama kitashi kimin abinda zanci infita ”

” cab wlh sai dai kayi hakuri haba dame zanji jiya gaba daya hana ni bacci kayi gaba daya jikina ciwo yake min wlh, nifa bazan jure ba ”

” Muwadda ni kike fadawa haka saboda raini ko “?

” Hmmm bazancan raini ya Assadiq, iya gaskiya ta nafada maka ”

Tashi yayi ya nufi part din sa yashiga wanka ya shirya yafita

 

 

Safiyya na zuwa gidan su Assadiq tasauke fadila kin shiga tayi dole tarakata suna shiga ciki suna zuwa suka tarar da su momy a parlor suna break fast guri tasamu ta tsuguna tagaida momy taamsa ba yabo ba fallasa su farhana kuwa ko kallonta bsuyiba jalila ce tagaida ta taja fadila jikinta momy ce tace

“ina zaku je da safan nan haka?

“momy zanfara zuwa school ne ”

” ba laifi, ina Muwadda “?

” Lpy kalau take momy ”

” am, kibani aran motar ki mana zandanje unguwa anjima ”

” to ai kinga zanje school ne yanxu kibari indawo mana afifa ”

” har sai tajira kindawo wayasan dawor ki, kibata ke kihau na pep ”

 

” to momy”

Mukulin tabata ta tashi ta fita tana fita fadila tasa kuka farhana ce ta daka mata tsawa sai da ta saki kofin hanunta madarar ta ta zube hakan yayi dai dai da Shigowar faruq.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:27Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*

 

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad*

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

 

*76*

 

 

~~~cikin mamakin ganin saurayin a wajen afifa Assadiq ya dubeta yace

“Afifa waye wannan?

“ya Assadiq haisam sunan sa, shine wanda nake son aure ”

” shut up, afifa, ni kike fadawa shi zaki aura, kin san shi din waye “?

” ya Assadiq dan Allah….

Kan takarasa abinda zata fada faruq yadaka mata tsawa ya kora ta ciki Assadiq ne yamaida dubansa ga haisam yace

“Kai, bakaine yaron da muka hadu dashi a super market ba?

“Eh nine yaya ”

” dakyau, me yakawo ka gurin kanwata?

“auranta zanyi yaya Assadiq ”

” Hmmm kana maganar aure ko?, to da Allah wuce katafi bazamu baka ba, kunaji na ko kar Inkuma ganin ka a gidan nan ”

” yaya wlh….

Faruq ne yakatse shi da cewar, “am abokina dan Allah wuce katafi kar kabari musami sabani da kai”

Juyawa yayi yashiga motar sa sai da suka ga fitar sa sannan suka shiga ciki faruq ne yadubi Assadiq yace

“ya Assadiq waye shi din daka koreshi ”

“. mushiga ciki faruq agaban momyn zanfadi abinda nagani game da yaron,

Suna shiga suka tarar da afifa na kuka momy sai faman rarrashinta takeyi ai kuwa suna shiga ta dubi faruq tace

“kadawo ko faruq zakafara matsawa yayana, to wlh baxan lamunta ba ”

” yasalam momy nifa baruwana akan me zan korota sanin sa nayi ma ita da ya Assadiq ne ”

” momy nasan yaron nan momy ”

Nan ya basu labarin haisam momy ce ta dubi Assadiq tace

” naji Assadiq amma yazama dole abar afifa da zabin ranta dan bazaai mata irin ta farhana ba ”

Tana gama fada taja hannun afifa sukai daki
Assadiq ne yadubi faruq yace,” faruq kaji fa abinda momy tace ”

” naji yaya, bari zamuy

maganar da dady, ashe yaran nan suna nan da halin su ”

” Hmmm me hali ai baya fasa halinsa faruq ”

Tashi Assadiq yayi yatafi office faruq kuwa dakinsa yanufa yai wanka ya kwanta”

 

*********

Makarantar safiyya ta kankama angama yimata komai game da rigistration yau monday itace ranar da zata fara zuwa tunanin inda zata bar fadila bayan tagama shirin ta tsaf tazauna jiran Assadiq kasancewar girkin Muwadda ne jinsa tayi shiru taimasa waya cikin bacci yadauka

“Hello Sweet sopy, yaakayi “?

” Dee, I am waiting 4 u ”

Tafada kmr zatayi kuka dariya yayi yace,” ayya sopyn Assadiq kar ki kuka gani nan ”

Duk abin nan da akeyi. Muwadda na bacci jallabiyar sa yasa yafito tana parlor suna break fast ita da fadila yana shiga fadila ta taso ta rungume shi daukar ta yayi ya karasa da ita gaban safiyya yasami gefenta ya zauna tana sanye da doguwar riga pink ta material ta kamata kallon ta yayi yace

“matar Assadiq kinyi kyau yafafada yana kashe mata ido tare da daukar kofin shayinta yakai bakinsa yana sha yaji zafi da sauri ya hadiye tare da sakin kara

Dariya fadila tasa safiyya ma dariya take masa duban fadila yayi yace

“Fadilaty binty, papan ki yakone kimasa dariya ko shikenan nagode binty ”

” papa kayi hakuri nadena kaji, to rama ”

” bazan ramaba amma bazan sa ki a school ba ”

” wayyo Allah, mamma kibawa Dee dinki hakuri ya kaini school ”

Dariya tabasu sosai Assadiq ya dubeta yace

” Fadilaty waye Dee ”

” bahaka naji mamma na nafada maka ba, nima haka xandiga cemaka wlh ”

” Fadila uwaki amina, kar ki kuma kiransa da Dee, inba hakaba sai na zane bakin ”

” lala papa kaji wai uwata aunty amina fa tazaga ta gidan su aunty najiba, kuma zagi ba kyau ”

” sopy kar ki kuma zagin aunty amina ko Fadilaty ”

” eh papa ”

Safiyya ce ta dubi Assadiq tace,” Dee time fa na tafiya yazaai ne “?

” ya zaai kuwa sopy kawai mushiga daga ciki abawa Assadiq agajin gaggawa inbaso kike ciwon cikina ya motsa ba ”

” Dee wai intambayeka mana?

“inajinki sopy ”

” baadakin Muwadda ka kwana ba yau?

“acan na kwana mana, ke, Muwadda fa lazy ce sam……

“Yaisa haka Dee kabar maganar tsakanin ka ne da matarka wannan, yanzu dai inason wuce wa school yazaai da fadila?

“emmm, akaita gidan momy yanxu inna shirya zanzo in dauketa sai inkaita school ”

Murna fadila tafara yi zaasata a school, kudi yadakko yabawa safiyya ta kwashe Kwanikan takai kitchen tashirya tsaf suka fito sai da Assadiq yafara tura fadila gurin mota sannan yaja safiyya suka koma ciki jikinsa yajata yakama bakinta ya shiga tsotsa sai da yashanye janbakinta tsaf sannan yasaketa, magana zatai yaktseta yace

“inkika kuma sa janbaki inzaki fita to nikuma sai na shanye shi tsaf

Fita sukayi zuwa gurin motar ta fadila na tsaye da kofi mai murfi a hannunta duban safiyya tayi tace

“mamma shine kika goge janbakinki bayan yayi kyau ”

Safiyya ce ta kalli Assadiq shima ita yake kallo murmushi sukai hannun fadila yakama yace

Fadilaty bakyau saka janbaki a fita shiyasa ta goge”

“to papa, tadena sakawa tunda ba kyau ”

A mota yasata ya mayar da murfin ya rufe tare da sakar mata kiss hannu safiyya tadaga masa taja motar tafita ciki yakoma

Ya tarar da Muwadda ta tashi tahada cornflakes tana sha daga ita sai vest da skin tied guri yasamu ya xauna ya dubeta yace

” Muwadda break fast dina fa?

“banyiba, nima bakaga abinda nake sha ba ”

” ina ruwana da abinda kike sha, malama kitashi kimin abinda zanci infita ”

” cab wlh sai dai kayi hakuri haba dame zanji jiya gaba daya hana ni bacci kayi gaba daya jikina ciwo yake min wlh, nifa bazan jure ba ”

” Muwadda ni kike fadawa haka saboda raini ko “?

” Hmmm bazancan raini ya Assadiq, iya gaskiya ta nafada maka ”

Tashi yayi ya nufi part din sa yashiga wanka ya shirya yafita

 

 

Safiyya na zuwa gidan su Assadiq tasauke fadila kin shiga tayi dole tarakata suna shiga ciki suna zuwa suka tarar da su momy a parlor suna break fast guri tasamu ta tsuguna tagaida momy taamsa ba yabo ba fallasa su farhana kuwa ko kallonta bsuyiba jalila ce tagaida ta taja fadila jikinta momy ce tace

“ina zaku je da safan nan haka?

“momy zanfara zuwa school ne ”

” ba laifi, ina Muwadda “?

” Lpy kalau take momy ”

” am, kibani aran motar ki mana zandanje unguwa anjima ”

” to ai kinga zanje school ne yanxu kibari indawo mana afifa ”

” har sai tajira kindawo wayasan dawor ki, kibata ke kihau na pep ”

 

” to momy”

Mukulin tabata ta tashi ta fita tana fita fadila tasa kuka farhana ce ta daka mata tsawa sai da ta saki kofin hanunta madarar ta ta zube hakan yayi dai dai da Shigowar faruq.

 

 

C

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:54Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*

 

*Bissimillahil lazi la yaburru maa ismihi shaiun fil arbi wala fissamau wa huwa samiul alim*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦🤝

 

 

*💙Dedicated 2 my lovely friend mufida muazu the writter of auran dole 😰thanx 4 ur care mufy*💙

 

*77*

 

~~~faruq na shiga parlon yaga fadila na kuka ga madarar ta tazube akasa yana kula da irin kallon da farhana take mata tana ganinsa ta bar gurin jalila ta tafi gurinsa ta rungume shi tana sauke ajiyar xuciya dago da kanta yayi yashiga tambayarta

“Fine girl, wayasa min ke kuka fada min ”

” uncle, mamma na ce ta tafi tabar ni shine nafara kuka sai aunty farhana ta daka min tsawa madara ta tazube ”

Tana gama fada takuma rushe da kuka mai da dubansa yayi ga farhana yace

” farhana, akan me zaki sata kuka? me tai miki zaku fara ko halin ku yana nan ko “?

” Dakata faruq kar ka soma takura wa yayana, au ita bazaai mata fada ba kenan, inbanda shegantaka in ta zauna nan zamu gutsiri namanta ne? haba yarinya sai shegiyar shagwabar tsiya ga wani sabon banza da akaimata na shan madara saboda sangarta ”

” Haba momy yanzu nawa fadila take da xakice ana sangarta ta ”

” bansaniba jalila, ai duk bakinku daya ”

Shiru sukai mata faruq ya cigaba da wurgawa farhana harara, jalila ce ta kwallawa Saa kira tazo ta gyara gurin da madarar ta zube ta kuma hadowa fadila wata

Assadiq ne yashigo gidan a parking space yaci karo da motar safiyya mamaki ne yakama shi yakarasa zuwa ciki a parlon ya tarar da su fadila tana ganinsa ta tazo ta rungume shi

“papa, ga mamma na ta tafi tabarni ko, kar ka kuma yadda tace ma Dee kaji ”

” ayya sorry Fadilaty bazan kuma amsawa ba ko tace ”

dariya faruq da jalila sukayi sai momy datai murmushi farhana da afifa kuwa haushi ta basu aranta suke cewa _yarinya sai kace aljana ga kyau ga iyayi dama ita ta haifeta_

Hannun ta yaja suka karasa gaban momy ya gaida ta faruq ya mika masa hannu suka gaisa kannan sa ma suka gaida shi mai da dubansa yayi ga jalila yace

“sister, sopy fa, naga motar ta anan bata tafi ba ne?

“wlh ya Assadiq afifa ce takarbi mukulin motar wai zata unguwa anjima shine ita ta hau napep ”

Shiru yayi yarasa ma me zaice mata faruq ne ya dubeta yace

” kawo min mukullin nan, wlh bazaki hau ba, mara mutunci saboda iskanci sai ki karbar mata mota gidan uban wa zaki to?

Nan yaimata tas sukai shiru dan sun san halinsa yanxu zai wa yarinya duka. Momy de rasa ma abinda zata ce tayi dan ita faruq tsoro ma yake bata

Assadiq ne yadubi farhana yace, “jeki kawo min tea ki soya min kwai”

Momy ce ta dubeshi tace,

“kamar ya akawo maka tea yanxu mutum mai mata 2 yakasa karyawa agidan sa sai kazo nan ”

” momy, Muwadda ce zata bani abinci ita ke da girki, to tace bazata iyaba tagaji ”

Shiru tayi saboda kar taja zancan faruq yafahimci halin da ake ciki amma ta kudire yau zata je tasami mamanta suyi magana game da abinda Muwadda keyi, ai kuwa sai da faruq din yasa baki bayan yadago da Kansa daga kan screen din wayar sa

” Au wai yarinyar nan irin rashin mutuncin datake yi dama kenan, Hmmm ai nasan zaai haka shiyasa wlh ni banso auran nan ba, ai kuwa zan gyara mata zama, inba taiwa mijinta girki ba uban wa zatai mawa”

“yaisa haka faruq, haba ina ruwan ka ko kaine mijin iyi, dan haka ba ruwanka ”

” Haba momy……..

“yimin shiru faruq, haba ”

Shi kam Assadiq farantin kayan tea dinsa yaja gabansa yafara sha fadilan sa na gefansa

Dady ne ya shigo parlon yasami guri yazauna cikin so da kauna yayan suka gaishe shi faruq kuwa sai da yakarasa kusa da shi yabashi hannu suka gaisa dady ne ya dubi Assadiq yace

“sadauki mezangani kabaro gidan ka kataho mana gida shan shayi anyawa kuwa sadauki…

“dady ayi hakuri yau na momy na nakeson sha ”

Yafada yana sosa kai dariya kawai dady yayi fadila ce ta dubi dadyn tace

” dady ranta min ashirin isaiwa uncle dina Sweet ”

Gaba daya parlon sai da akai dariya ba musu yazaro 20 yabata can dady yanisa yace

” am yanxu malam mudassir yaimin waya nan da sati biyu zaakawo kayan lefan farhana dan haka biki nan da wata guda, da naso ahada da na jalila
amma abinda zaai kai sadauki kace shi almustaphan yazo ina nemansa

“to dady inshaallah zaa fada masa ”

” tunda dady yafara magana momy bata ce kala ba saboda takaici farhana kam tashi tayi tabar parlon Assadiq kuwa fadila ya dauka dan kaita school ahanya take ce masa

“papa, meyasa su aunty farhana basa sona “?

 

Mamaki Kalaman yarinyar suka bashi hannunta ya rike cikin nasa yace

” binty kar ki kuma cewa wani bayason ki kinji ko ba kyau dukkansu suna sonki ”

” to papa nadena bazan kuma fada ba ”

” ehemmm, that is my good girl ”

Yafada yana kissing dinta.

Abangaran safiyya kuwa sai da tai tafiya mai dan nisa sannan tasamu abin hawa tagama gjy ga bacin rai ahaka taisa zuwa school sanda ta isa har anfara lecture tasamu tashiga malamin be jimaba yafita anan tahadu da wata kawa mai suna khadija kusan tare suka taho gida suna tafe suna taba hira kai tsaye safiyya gidan su ta wuce tana xuwa ta fada jikin umminta tasa kuka cikin kidima tafara tambayarta

“ke safiyya lpyr ki kuwa zakixo kisani agaba kina kuka ”

Sai da tayi mai isarta sannan ta fara fadawa umminta abinda yafaru

rufeta tayi da fada tace

” amma dadi yaimiki yauwa safiyya abu nawa sukai miki wanda yafi wannan baki zo kinfada minba sai su amina sufada min amma kikasa hadiye wannan haba safiyya ”

” Hmmm ummi bakisan halin su ba ne wlh aunty safiyya fa tana hakuri ”

” nasani najiba, ai bance bata yiba kawai dai tadaga min hankali ne wlh ”

Nan tai ta rarrashinta tare da nasihohi da nuna mata girman hakuri da irin ribar dazata samu anan gaba.

Take taji sanyi aranta tasami nutsuwa da kalaman umminta bata jimaba tai mata Sallama ta tafi bayan taimata alheri

 

Abangaran Muwadda kuwa Assadiq yana fita sukai waya da muktar yana son ganinta saboda bashi da kudi kuma tayo masa girki sukai Sallama ta kashe wayar kitchen tashiga tahada masa girki dai dai iyawar ta ko kitchen din bata gyara ba tashiga wanka tafito wasu riga da wando tasa masu kyau ta dora abaya tafito mukulin motar ta ta dauka bayan ta dau kulolin abincin tasa amota

Kai tsaye gidan su Assadiq ta wuce tana xuwa ta tatar da jalila a parlon dubanta tayi tace

 

“ke, jalila momy fa?

Banza tai mata tacigaba da karatunta bayan ta gyara zaman glass dinta a kyakyawar fuskarta afifa ce tafito daga kitchen tana ganinta ta ta sakar mata murmushi mayar mata tayi ta tambayata momy

“bari inkirata yauwa aunty na pls kibani aran motarki zanje unguwa kinji ”

” kut ni zan baki aran mota cab kin dade baki je unguwar ba wlh ”

Karf akunnan momy karaso wa tayi tadubi Muwadda tace

” Haba Muwadda ke da kanwarki yazaki fada mata haka, meyasa kike haka ne?

 

“Haba dan Allah momy ni yaakeso nayi ne?

“shikenan yaisa haka yanxu ina zaki?

 

“zanje gurin mamana nakarbo wasu kudi ne, shine nakawo mukulli farhana ko afifa suje suyi min gyaran daki da wanke wanke ”

 

” ke suwaye zasuyimiki wanke wanken, ke baza kiyi ba eye wacce bata iya kula da mijinta ba ”

Gaba daya suka juya dan ganin mai maganar faruq ne karasowa yayi ciki bayan ya wurga mata wani mugun kallo dubansa tayi tace

 

” Haba kanin mijina ai bankasa da kai ba ballanta ka dauka ko kabarni inyi magana da mata ”

Hannu yadaga zai mareta momy tarike hannun nasa murmushi Muwadda tayi bayan ta mikawa momy mukullin tasa kai tafita duk abin nan daakeyi akan idon ya hannatu yafaru tana tsaye tana kallonsu.

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6 :19,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Auzu bikalimatullahi tamat minsharri makalaka*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

*💙wannan shafin nanakune ga dukkan mai suna safiyya sopyn Assadiq na gaidaku kyauta ba da kudi ba*💙😃

 

 

*78*

 

 

~~~Guri momy tasamu ta zauna ta dafe kanta wanda yake barazanar fashewa zuciyar ta kuwa jitake tana tafasa ahankali take iya magana

“Gsky yarinyar nan tabani kunya, wlh ai bansan haka take ba da banhada auran nan ba ”

Ya hannatu ce takarasa Kusa daita ta zauna dubanta tayi tace

” momy ai aikin gama yariga yagama kawai yanzu sai dai fatan Allah yabamu hakurin jure halinta ”

Faruq kuwa dan takaici rasa ma abinda zaice yayi, jalila kam taji dadin abinda Muwadda tayi ko bakomai momy ta sakar wa safiyya mara ta sarara, haka dai sukai ta tattaunawa farhana ce ta dubi afifa tace

” malama, kitashi kije ki gyara mata dakin mana ko sai ta dawo tazo taiwa mutane tujara ”

” cab, wlh bazaniba tadawo tayi abinda zatayi din ”

” faruq ne ya dubeta yace,

“ai wlh afifa sai kinje, dan ubanku baku kuke sonta, dallacan tashi ”

Momy dai ba bakin magana, tashi afifa tayi tafita, yaya hannatu kam banda takaici ba abinda take yi,

 

Muwadda tana fita ta nufi gurin da suka saba haduwa da muktar yana nan yana jiranta tasami guri tai parking din motar ta takarasa gurin sa tasami gefansa ta zauna dubansa tayi tace

“Dear I am so sorry, i have westing ur time ”

” nvr mind baby, yanzu dai ina abincin yunwa nakeji ga shi bani isassun kudi fa, Allah yasa kinzo min da kudi ”

” yasalam wlh namanta bankarbi kudinba gaba daya yan iskan yarannan sun mantar dani ”

” su wa kenan baby”?

*”kannan mijina*mana, marasa mutunci ”

” shikenan baby yanzu meye labari dafatan baki da ciki, saboda banason ki haihu da wannan mijin naki nafison kihaifa min”

“Dear nifa bana ma yadda dashi kwata kwata ”

” ayya shiyasa har yanzu kika kasa samun abinda muke bukata a hannunsa, kisaki jikinki dashi baby ni dai kar ki ciki ”

” shikenan dear abinda kakeso shi zanyi, yauwa ina rushida, inason tazo ta kwanan min ko sati ne ”

” Hmmm baby kenan, to in mijinki ya tambayeki wacece kice masa wa?

 

“aa mekuwa zance, ince masa kanwar saurayina mana ”

” dawasa kike, zanfada mata inshaallah zaki ganta ”

Nan sukai ta hira karshe taimasa Sallama ta wuce gidansu tana xuwa tai parking din motar ta ta shiga ciki mamanta bata parlo sai mai aikinsu tanata gyaran parlon ta tsuguna ta gaida ta taamsa a wulakance tabi kofar dazata sadata da bedroom din mamanta

Tana shiga tafada kanta dubanta tayi tace

 

“Haba Muwadda, sai kinji wa kanki ciwo ko kijiwa babyn da yake jikinki, dan Allah kidinga kula ”

” mama baby kuma, aina?

“au bakisan kina da cikin ba, Yanayin ki kadai yaisa ya nuna haka, naji dadin faruwar hakan Allah yasa kihaifo namiji Muwadda ”

Muwadda rasa ma me zatace tayi kuka tasa wa mamanta ita bataso zubarwa zatayi, can tadago ta dubi mamanta tace

” mama naga ke ba likitaba tayaya daga zuwa na zakice wani ciki ne dani ”

” bansaniba Muwadda kuma wlh kika sake kika zubar da cikin nan sai nabaki mamaki, ke tashima muje asibiti ma ”

Bamusu Muwadda ta tashi suka nufi asibiti suna zuwa suka ga likita akai mata test take aka gano shigar ciki na wata biyu, hankalinta in yayi dubu yatashi magan ganun muktar ne suke mata yawo, tashi sukai sukaiwa likitan Sallama suka tafi.

Har gida mama takai Muwadda lokacin Assadiq yajima da dawowa suna parking space shi da safiyya da fadila sun shimfida dadduma suna shan fruit, binsu kawai Assadiq yayi da kallo tashi yayi yakarasa gurin su domin ya gaida mama amma aransa bakin ciki ne fal ransa tsuguna wa yayi ya gaisheta safiyya ma tagaida ta fadila ce ta taso ta rungume Muwadda amma bata kulataba saboda tashin hankalin datake ciki

Part din ta suka nufa Assadiq har zai koma ya zauna mama takirashi ba musu yabi bayanta har fadila tayunkura zata bishi safiyya ta rike ta komawa tayi tazauna

Assadiq yana shiga yasami guri yazauna mama ce tadubeshi tace

“Assadiq muwadda nakai asibiti ankuma tabbatar min tana dauke da ciki saboda haka ka nika kulawar ka gareta banda yawan fitar nan datake dan Allah ku kula kaji ko ”

” naji mama, to amma maganar fita muwadda bata taba tambayata unguwa ba sai dai tai fitar ta kawai, sai nake ganin ita zaki jaddadawa hakan ”

” shikenan dai koma meye dai abarshi nide ka kular min da ita, yauwa ”

” shikenan mama, zaakula inshaallah ”

Yana gama fada yatashi yafita sanda yakoma inda suke zaune da safiyya bata gurin sun koma daki kai tsaye binsu yayi yana zuwa yatarar fadila tanata aikin kuka sai safiyya ta goyata

 

” wlh fadila bazan goya kiba, bakya tausayina ko ”

” nide Allah ki goyani, nima fa gajiya nayi”

 

Assadiq ne yadubi safiyya yace, “Haba sopy dan Allah ki goya ta nawa Fadilaty take balle kice nauyi ne daita”

“Wlh Dee bazaniyaba, to kai ka goyata mana ”

 

” shikenan, binty zo kihau ba irin nata ba ma ni har zani zansa miki ”

 

” yauwa papa na, inason ka ”

 

” nima haka Fadilaty ”

Goyata yayi, tayi luf jinta yayi shiru yakira sunanta Bata amsaba zuwa yayi yakaita daki ya kwantar daita safiyya ce tafito daga toilet daure da towel tanata yarfe gashinta wanda ruwa yajika shi dubanta yayi Karasawa yayi gabanta ya dau karamin towel yafara goge mata yanayi yana tsokanar ta

“matar Assadiq yakamata inbaki baby acikin daren nan “yafada yana shafa cikin ta juyowa tayi ta shafi lallausar sajensa tace

 

” Gsky Dee bayanzuba, sai nadada hutawa ”

 

” nide yanzu zaki haifa min baby ”

Nare nare tayi da ido zatai kuka jikinsa yajata yafara rarrashinta bakinsa yahada danata yashiga tso tsa hade da jan towel din jikinta hannunsa ta rike ta girgixa masa kai alamar aa murya can kasa yace

 

” sopy meyasa, dawasa nake bazan bari ciki ya shigaba pls help me ”

 

” Dee, kamanta Muwadda ke da girki, bakyau fa, pls katafi gurinta ”

Kansa yadafe saboda inyana gaban safiyya manta komai da kowa yake, sai da yagama jin dumin jikinta sannan yasaketa hade da sakar wa kirjinta kiss yaja mata kofar yafita

 

Part din Muwadda yanufa tana kwance a kujera da wata yar fingilar riga a jikinta wacce tabayysna cikar kirjinta ido yazuba mata yanayinta yatabbatar masa da cikin datake dashi ahankali yakarasa gabanta yahaye kanta idonta arufe sai jin mutum tayi a kanta arazane ta bude idonta suka hada ido, kanta tadauke kissing dinta yafara tureshi tashiga yi tasamu ta yunkura ta tashi dakinta ta gudu, binta yayi saboda bazai iya hakura ba sai da yagwada mata karfi sannan yasamu biyan bukatar sa yana gamawa yabar mata dakin

 

 

 

Yau aka kawo kayan lefan farhana kaya masu kyau da tsada sai hijjabai da nikaf tunda taga kayan take kuka gashi ibraheem ya tabbatar mata a gidansu zasu zauna ga kannan sa maza da mata

 

Haisam ne zaune da matar sa yana cin abinci gefansa kuma yara ne guda biyu maza kiran afifa yashigo sai da yasaci kallon matar sannan yadaga

“zankira anjima “kawai yace dubansa tayi tace

” dawa kake waya?

Kame Kame yafara yi

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6 :19,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Auzu bikalimatullahi tamat minsharri makalaka*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

*💙wannan shafin nanakune ga dukkan mai suna safiyya sopyn Assadiq na gaidaku kyauta ba da kudi ba*💙😃

 

 

*78*

 

 

~~~Guri momy tasamu ta zauna ta dafe kanta wanda yake barazanar fashewa zuciyar ta kuwa jitake tana tafasa ahankali take iya magana

“Gsky yarinyar nan tabani kunya, wlh ai bansan haka take ba da banhada auran nan ba ”

Ya hannatu ce takarasa Kusa daita ta zauna dubanta tayi tace

” momy ai aikin gama yariga yagama kawai yanzu sai dai fatan Allah yabamu hakurin jure halinta ”

Faruq kuwa dan takaici rasa ma abinda zaice yayi, jalila kam taji dadin abinda Muwadda tayi ko bakomai momy ta sakar wa safiyya mara ta sarara, haka dai sukai ta tattaunawa farhana ce ta dubi afifa tace

” malama, kitashi kije ki gyara mata dakin mana ko sai ta dawo tazo taiwa mutane tujara ”

” cab, wlh bazaniba tadawo tayi abinda zatayi din ”

” faruq ne ya dubeta yace,

“ai wlh afifa sai kinje, dan ubanku baku kuke sonta, dallacan tashi ”

Momy dai ba bakin magana, tashi afifa tayi tafita, yaya hannatu kam banda takaici ba abinda take yi,

 

Muwadda tana fita ta nufi gurin da suka saba haduwa da muktar yana nan yana jiranta tasami guri tai parking din motar ta takarasa gurin sa tasami gefansa ta zauna dubansa tayi tace

“Dear I am so sorry, i have westing ur time ”

” nvr mind baby, yanzu dai ina abincin yunwa nakeji ga shi bani isassun kudi fa, Allah yasa kinzo min da kudi ”

” yasalam wlh namanta bankarbi kudinba gaba daya yan iskan yarannan sun mantar dani ”

” su wa kenan baby”?

*”kannan mijina*mana, marasa mutunci ”

” shikenan baby yanzu meye labari dafatan baki da ciki, saboda banason ki haihu da wannan mijin naki nafison kihaifa min”

“Dear nifa bana ma yadda dashi kwata kwata ”

” ayya shiyasa har yanzu kika kasa samun abinda muke bukata a hannunsa, kisaki jikinki dashi baby ni dai kar ki ciki ”

” shikenan dear abinda kakeso shi zanyi, yauwa ina rushida, inason tazo ta kwanan min ko sati ne ”

” Hmmm baby kenan, to in mijinki ya tambayeki wacece kice masa wa?

 

“aa mekuwa zance, ince masa kanwar saurayina mana ”

” dawasa kike, zanfada mata inshaallah zaki ganta ”

Nan sukai ta hira karshe taimasa Sallama ta wuce gidansu tana xuwa tai parking din motar ta ta shiga ciki mamanta bata parlo sai mai aikinsu tanata gyaran parlon ta tsuguna ta gaida ta taamsa a wulakance tabi kofar dazata sadata da bedroom din mamanta

Tana shiga tafada kanta dubanta tayi tace

 

“Haba Muwadda, sai kinji wa kanki ciwo ko kijiwa babyn da yake jikinki, dan Allah kidinga kula ”

” mama baby kuma, aina?

“au bakisan kina da cikin ba, Yanayin ki kadai yaisa ya nuna haka, naji dadin faruwar hakan Allah yasa kihaifo namiji Muwadda ”

Muwadda rasa ma me zatace tayi kuka tasa wa mamanta ita bataso zubarwa zatayi, can tadago ta dubi mamanta tace

” mama naga ke ba likitaba tayaya daga zuwa na zakice wani ciki ne dani ”

” bansaniba Muwadda kuma wlh kika sake kika zubar da cikin nan sai nabaki mamaki, ke tashima muje asibiti ma ”

Bamusu Muwadda ta tashi suka nufi asibiti suna zuwa suka ga likita akai mata test take aka gano shigar ciki na wata biyu, hankalinta in yayi dubu yatashi magan ganun muktar ne suke mata yawo, tashi sukai sukaiwa likitan Sallama suka tafi.

Har gida mama takai Muwadda lokacin Assadiq yajima da dawowa suna parking space shi da safiyya da fadila sun shimfida dadduma suna shan fruit, binsu kawai Assadiq yayi da kallo tashi yayi yakarasa gurin su domin ya gaida mama amma aransa bakin ciki ne fal ransa tsuguna wa yayi ya gaisheta safiyya ma tagaida ta fadila ce ta taso ta rungume Muwadda amma bata kulataba saboda tashin hankalin datake ciki

Part din ta suka nufa Assadiq har zai koma ya zauna mama takirashi ba musu yabi bayanta har fadila tayunkura zata bishi safiyya ta rike ta komawa tayi tazauna

Assadiq yana shiga yasami guri yazauna mama ce tadubeshi tace

“Assadiq muwadda nakai asibiti ankuma tabbatar min tana dauke da ciki saboda haka ka nika kulawar ka gareta banda yawan fitar nan datake dan Allah ku kula kaji ko ”

” naji mama, to amma maganar fita muwadda bata taba tambayata unguwa ba sai dai tai fitar ta kawai, sai nake ganin ita zaki jaddadawa hakan ”

” shikenan dai koma meye dai abarshi nide ka kular min da ita, yauwa ”

” shikenan mama, zaakula inshaallah ”

Yana gama fada yatashi yafita sanda yakoma inda suke zaune da safiyya bata gurin sun koma daki kai tsaye binsu yayi yana zuwa yatarar fadila tanata aikin kuka sai safiyya ta goyata

 

” wlh fadila bazan goya kiba, bakya tausayina ko ”

” nide Allah ki goyani, nima fa gajiya nayi”

 

Assadiq ne yadubi safiyya yace, “Haba sopy dan Allah ki goya ta nawa Fadilaty take balle kice nauyi ne daita”

“Wlh Dee bazaniyaba, to kai ka goyata mana ”

 

” shikenan, binty zo kihau ba irin nata ba ma ni har zani zansa miki ”

 

” yauwa papa na, inason ka ”

 

” nima haka Fadilaty ”

Goyata yayi, tayi luf jinta yayi shiru yakira sunanta Bata amsaba zuwa yayi yakaita daki ya kwantar daita safiyya ce tafito daga toilet daure da towel tanata yarfe gashinta wanda ruwa yajika shi dubanta yayi Karasawa yayi gabanta ya dau karamin towel yafara goge mata yanayi yana tsokanar ta

“matar Assadiq yakamata inbaki baby acikin daren nan “yafada yana shafa cikin ta juyowa tayi ta shafi lallausar sajensa tace

 

” Gsky Dee bayanzuba, sai nadada hutawa ”

 

” nide yanzu zaki haifa min baby ”

Nare nare tayi da ido zatai kuka jikinsa yajata yafara rarrashinta bakinsa yahada danata yashiga tso tsa hade da jan towel din jikinta hannunsa ta rike ta girgixa masa kai alamar aa murya can kasa yace

 

” sopy meyasa, dawasa nake bazan bari ciki ya shigaba pls help me ”

 

” Dee, kamanta Muwadda ke da girki, bakyau fa, pls katafi gurinta ”

Kansa yadafe saboda inyana gaban safiyya manta komai da kowa yake, sai da yagama jin dumin jikinta sannan yasaketa hade da sakar wa kirjinta kiss yaja mata kofar yafita

 

Part din Muwadda yanufa tana kwance a kujera da wata yar fingilar riga a jikinta wacce tabayysna cikar kirjinta ido yazuba mata yanayinta yatabbatar masa da cikin datake dashi ahankali yakarasa gabanta yahaye kanta idonta arufe sai jin mutum tayi a kanta arazane ta bude idonta suka hada ido, kanta tadauke kissing dinta yafara tureshi tashiga yi tasamu ta yunkura ta tashi dakinta ta gudu, binta yayi saboda bazai iya hakura ba sai da yagwada mata karfi sannan yasamu biyan bukatar sa yana gamawa yabar mata dakin

 

 

 

Yau aka kawo kayan lefan farhana kaya masu kyau da tsada sai hijjabai da nikaf tunda taga kayan take kuka gashi ibraheem ya tabbatar mata a gidansu zasu zauna ga kannan sa maza da mata

 

Haisam ne zaune da matar sa yana cin abinci gefansa kuma yara ne guda biyu maza kiran afifa yashigo sai da yasaci kallon matar sannan yadaga

“zankira anjima “kawai yace dubansa tayi tace

” dawa kake waya?

Kame Kame yafara yi

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:33Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

 

*NA*
*NASEEBA I UBA*💐

 

 

 

*wallahu galibun ala amri wala kinna aksarin nasi la yaalamun*👏🏻

 

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦🤝

 

 

💙
*Inaiwa kawata rukayya taaziya bisa rashi da tayi na yarta naseeba ubangiji Allah yai mata rahama yasa ta huta yabaki wata naseeba AMEEN💙*

 

 

💙
*Wannan shafin nanakune munemi aljannar mu mata group ku kadai banhada ku da kowane group ba ina yinku wlh*🙅🏻

 

 

 

 

*79*

 

 

~~~cikin masifa da tsantsar kishi shukura takewa haisam magana yayi shiru saboda sanin bakin kishinta da masifa

“haisam ya zaka maida ni wata yar iska inai maka magana kai min shiru “?

” to me kike so ince miki shukura, yanxu saboda Allah daga yimin waya baki san waye ba sai ki hau masifar fada, haba mata ta sanin kanki ne kinsan daga ke ba kai, ni yanzu ko cewa akai zaai min aure kyauta ai bazan yarda ba yadda nake fama yanxu kasuwar bawani cikin kirki akeba”

“oho matsalar kace wlh duk sanda kasake kayi aure wlh daga kai har matar sai kun gane kuka kuranku, haba baka da aiki sai bin yanmata gidanka ana fama da matsi to kayi Allah yabaka Saa ”

Tana gama fada ta dau karamin danta me suna salman tayi daki haisam kuwa rasa ma mezaice yayi tashi yayi yashuri takalmansa yafita

Kai tsaye gidan su abokinsa ya wuce yai Saa yana nan, suka gaisa duban abokin nasa yayi yace

” abokina yazaai ne, tai makon daakasaba zaai min ”

” wai me, kana nufin kaya da mota?

“yauwa dangari sufa, wlh kayana duk sun dan sha jiki, nadan sami kudi nasai wasu to har yanzu baa dinka ba ”

 

” amma abokina me zai hana ka dena wannan dabiar taka ta yaudara da karya ba kyau fa ”

” Hmmm usman kenan bazaka gane ba, yanxu nasamo matar aure wacce zanhuta ta ko ina, sonake na aureta nan da dan kan kanin lokaci, soma nake nazo insami alhajin ku, ya taimaka yanema min aurenta wlh ”

 

” ita wa kenan?

“Hmmm, afifa muhammad mai nasara ”

 

” Kai, kar kace min yar gidan tsohon kwamishina ce yarinyar “?

 

” kanuba, au babanta har kwamishina yayi,hmm abokina bani kaya masu zafi dan Allah intafi ”

tashi usman yayi ya dakko masa wata hadaddiyar shadda milk sai daukar ido takeyi ya shirya tsaf taimasa kyau ainun kasancwar sa farin bafulatani yakarbi mukullin motar yafita

 

*Waye haisam ne??*
🤔

Sunan sa na gaskiya shuaibu asalinsa dan adamawa ne shine kusan auta a gidansu duk yayyansa manya ne daga masu mata biyu sai uku ga tarin yaya kmr me mahaifinsa yakawo shi gurin abokinsa wato mahaifin matar sa shukura karatun boko yasamu yai secondary yafantsama kasuwa ahaka yahadu da mahaifin abokinsa usman yadauke shi amatsayin yaron kanti ba laifi yana samu amma hangen nasama dashi yasa baya godewa Allah, ahaka aka hada shi aure da shukura badan yaso ba saboda shi burinsa yafantama da yanmata ga karyar tsiya yau kaganshi da waccan budurwar gobe da waccan ahaka ya hadu da afifa ya kuma kudirce wa ransa sai ya aureta tunda yai aure yaki zuwa garinsu saboda yanxu jiyake yafi karfin zaman garinsu su.

 

**********

Yana isa yaimata waya gashi yana waje cemasa tayi bata gida tana gidan yayanta gida mai kallon nasu parking din motar yayi yafito cikin katsaita yakarasa ciki yana shiga yaci karo da fadila akan dan karamin lilonta gurinta yakarasa saboda tunda suka hadu da yarinyar take burgeshi tsugunawa yayi agabanta yarike lilon yadago habarta yace

“fine girl, ya kike?

“la kaima uncle ne, uncle dina ne yake kirana da fine girl ”

” ayya, nima uncle dinki ne, to fadamin sunanki ”

” Fadilaty binty ”

” nice name, to yanzu mezan baki “?

Bakomai, papana yace kar indinga karbar abun mutane”

“har dana uncle “?

” aa, kudi yazaro yan dari biyu yabata ta karba sauka tayi daga kan lilon tanufi ciki tana ta kwallawa safiyya kira tana kwance a kujera mai cin mutum uku tana duba wani littafi fadawa fadila tayi kanta tana kiran

“mamma na kinga uncle yabani kudi ”

” Haba fadila meyasa bakya abu da nutsuwa ne, bakisan kaina ke ciwo ba ga gjyr school ”

” sorry mamma na nadena, nidai bari papa na Yadawo muyi shawarara infada masa kidena zuwa school tunda ciwon kai kike yi ko?

” to ai sai abinda kikace fadila, yanzu de wayabaki kudin nan?

“uncle ne yabani, zo muje kiganshi ”

” to inazuwa bari nadan sami saukin ciwon kan”

 

 

 

Afifa kuwa tana bangaran Muwadda tanai mata meat pie tagama tsaf ta dibarwar haisam tahada masa da drinks dakin Muwadda tashiga ta tatar da ita tanata bacci ahankali ta bude wardrobe dinta ta dakko wani hadaddan lace blue da pink tasa tayi kwalliya tanada dankwalin kamar gwaggwaro tayi kyau ai nun ta fesa turare tafita yana zaune saman motarsa takarasa dirowa yayi ya karbi tray din hannun ta suka sami guri inda aka zuba fararan kujeru suka zauna dubanta yayi da fararan idonsa yace

 

“queen kinyi kyau dama daga nan gida na zamu wuce ”

” hmm king kenan, kar ka damu kamar yau ne ai, pls kana da aure ne?

“Haba Queen wani irin aure kuma, bani da aure ke nake ta jira kullum ke nake gani a mafarkina sai gashi Allah yahada mu ”

 

” Hmmm ”

Cikin bacci Muwadda taji turare yadameta da kamshi farkawa tayi taji dakin yacika da kamshi take taji kanta yafara juyawa hijjabainta ta zura tanufi kitchen meat pie din taje dauka taga saura uku mamaki ne yakamata tashiga kwadawa afifa kira bata gantaba ragowar ukun ta dauka tanufi part din safiyya su afifa sunga shigar ta amma ita batagansu ba haisam ne yadubi afifa yace

Queen waccan ce maman Fadilaty “?

” aa waccan aunty Muwadda ce, au kaima Fadilaty kake cemata?

“aa ba sunnanta ta bane ”

Sunan ta fadila babanta ke kiranta Fadilaty”

“Queen inason yarinyar dama inmunyi aure abamu ita ”

 

” cab wannan me shegen surutun tsiyar”

 

Fadila ce ta dami safiyya ta taso taga uncle dinta, tashi tayi ta leka hangosu tayi da afifa tana juye masa abu a leda jitayi yaron be kwanta mata ba.

Shigowar Muwadda ne yasata sakin labulan takoma ta zauna guri Muwadda tasamu itama tazauna tagaida safiyya taamsa a mutunce fadila ce tadubi Muwadda tace

 

Aunty kinga nasami kudi ”

 

” nagani fadila waye yabaki “?

 

” uncle dina ne yabani ”

” to angode masa, yauwa aunty safiyya afifa bata shigo nan ba ”

” bata shigo ba Muwadda, yaushe rabon afifa da nan, har na manta, amma ai ita ke zance a waje ”

” ok zata zo tasameni zataci ubanta wlh ”

 

Ita dai safiyya shiru tai mata, tai mata tayin meat pie taki karba, Sallama haisam yayiwa afifa bayan yabata sababbin kudi tai ta murna part din safiyya tanufa dan tasan acan zata hadu da Muwadda ai kuwa tana shiga Muwadda taga kayan ta ajikin afifa wata uwar ashar ta lailayo mata hade da dauketa da mari ta dora da

“afifa kinfara shaye shaye ko, da har zaki dau kayana kisa, ko ni saar ki ce haba shiyasa naji dakina Yacika da kamshin turaran danafi tsana a yanzu, tsaya ma tukunna ina ragowar meat pie din yake?

 

“bansaniba, muguwa azzalima nabawa wanda ya isa keda kina tunanin zanmiki wahala ne, to dan saurayina nayi ”

 

Tana gama fada tai gaba safiyya kam tana tsaye tana kallonsu bin bayanta Muwadda tayi har gurin momy suna parlor gaba dayansu har da Assadiq da yaya hannatu suna tsara bikin farhana afifa tashigo tana kuka, can kuma sai ga Muwadda cikin masifa gaba daya suka zuba mata ido

 

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[8:06Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

 

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad*📿

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

💦
*Ina tayaki murnar kammala littafinki kawata maman farida mai suna DANMALIK MAI HADARIN NERORI allah yasa muamfana da abinda muka karanta*💦

*haka kazakika ina taya kawayena faeex usman da fatima auwal fara littafinsu dafatan Allah yasa sufara asaa readers kar ku sake abaku labarin wadannan littafe*

*💦FEENAT*

*&*
*RASHIN SANI*💦

 

 

*80*

 

~~~cikin masifa da rashin kunya muwadda takewa afifa masifa gaba daya idonta yarufe bata ma kula da wadanda suke wajenba momy ce ta dubeta tace

“Haba Muwadda, yazaki shigo ba Sallama kina zage zage, me afifa tai miki haka?

“wlh momy tambayar ki tana bani mamaki, to ki tambayata mana ita tafada miki abinda taimin ”

Yaya hannatu ce tadubeta tace

” ke, bamason hauka da iskanci kinji ko, ke wacce irin sha sha ce, wacce bata san me take ba, to wlh kishiga hankalinki tun wuri ”

Juyi tayi agaban su tare da yatsine fuska tace

” yaya hannatu, kenan, dan Allah intambayeki mana, meyasa bakwason yiwa mutum adalci ne, oh dama laifine mutum acutar dashi yaja bakinsa yai shiru, to gaskiya ni Muwadda banyarda da wannan tsarin ba, saboda haka sai kuyi hakuri da halina ”

Assadiq ne ya dauketa da mari, take ta fasa kara tafara ihu, tafita kai tsaye gida ta wuce tadau motar ta tayi gidansu

Faruq ne yadubi afifa yace

” ke zonan dan uwanki, me yahadaki da ita ki jawo tazo taiwa mutane rashin mutunci ”

” yaya faruq, wlh ba abinda nai mata, wai dan nasa kayanta ne, fa kawai ”

” oh ashe fa baki da kaya ko?

“ina dasu yaya, aiki nayi shine najikina suka baci ”

” afifa, meyasa kuke haka ne, Muwadda fa ba kamar safiyya ba ce, ni kaina hakuri nake da ita amma kude burinku kuja abinda zaai rikici ko? yayi kyau

“Dakata Assadiq meye da safiyya da har zakace Muwadda ba kamar safiyya ba, to ai inbaka saniba kasani duk naka yafi bare,

Dan haka, abar Zancan haka, kuma wlh kar ka kuma dukanta, kaji nafada maka ”

Gaba dayansu mamaki kalaman momy yabasu musamman yaya hannatu, haushi ne yakamata tadau jakar ta da mayafinta ta tafe ko Sallama batai musu ba, Assadiq ma fita yayi ya nufi gidansa ransa a mutukar bace, faruq kuwa kwaciya yayi a kujera yashiga latsa wayarsa

Assadiq yana zuwa gida ya tatar da part din Muwadda arufe ga motar ta bata nan, part din sa ya wace kwanciya yayi saboda yadda Kansa yake sarawa bayason hayaniya ko kadan,

Safiyya bata san ya shigoba saboda baccin da yakwashe su ita da fadila, cikin bacci taji wayar ta na ringing ahankali ta bude idonta tadubi sunan *Dee*tagani ajikin screen din dagawa tayi

“sopy, ina dakina, banajin dadi pls kizo ”

Yanagama fada yakashe wayar tashi tayi tagyarwa fadila kwanciyarta sannan tafita part din sa tanufa yana kwance a kujera yadafe Kansa da sauri takarasa gabansa tadafa kafadarsa tare da cire hannunsa da ga Kansa tace

” Dee, meyasa meka haka?

“sopy, muwadda kashe ni, takeson yi, tana yawan bani ciwon kai, bata da kirki ko kadan yarinyar ”

” yaisa haka Dee, kayi hakuri yanzu mezan kawo maka kaci, ko kuma katshi ka tashi kafara yin wanka ko?

“sopy, bazan iya ba, jinake kamar kaina zai fado, kihada ruwan wanka ki taimaka min inyi ”

Ba musu tashiga toilet din ta hada masa Ruwan wanka tafito taimaka masa tayi yacire kayansa tarike hannun sa suka nufi toilet din tare sukai wankan suka fito daure da towel yasami gefan gado ya zauna dubanta yayi yace

” bani kaya marasa nauyi sopy, ki dafa min tea zansha magani ”

” to Dee, sannu ”

3quater ta dakko masa sai riga armlace ya karba yasaka mayafi ta yafa tafita batare da tasa kaya ba kitchen tanufa ta dafa masa lipton dakinta ta koma ta dubi fadila baccin ta take tayi ahankali ta rufo mata kofar tafita farantin data jera flaks da cup din ta dauka tanufi dakin Assadiq yana nan inda tabar shi karasawa tayi taaje farantin, dubanta yayi yace,

“sopy, ya bakisa kaya ba kike yawo da towel ”

 

” Dee banasan intaba wardrobe din ne fadila ta tashi nasamu tayi bacci ”

” shikenan sopy nima nafison jin dumin jikinki ahaka ”

Zuba masa tea din tayi ta mika masa dauke Kansa yayi yaki karba murmushi tayi ta koma gefansa ta zauna tafara bashi yana sha yadora Kansa a kafadar ta yafara lumshe ido, magani ta dakko taballa tasa masa abaki ta bashi ruwa ya sha jikinsa yajata ya matse ta tsam ya koma ya kwanta, nan yashiga wasa da ita tare da kissing din wuyanta itama dada rungume shi tayi tashiga yimasa susa a Kansa da hura masa iska akunne take yafara lumshe ido, bacci yai gaba dashi ahankali ta zare jikinta ta jera masa filo a kusa dashi taja bargo ta rufeshi tabar dakin

 

Abangaran Muwadda kuwa tana xuwa gidan su kai tsaye dakin abbanta tanufa yana zaune da wasu takardu a gabansa tashiga tasaki wani kuka mai tsuma zuciya cikin kidima yashiga tambayarta

“Muwadda, lpyrki kike kuka, meyasameki, waya taba min ke?

“abba, nagaji da aurannan, wlh bazan koma ba,

“haba yar gidan abba, kifadamin meyasameki

Nan takwashe komai tafadamasa ransa yabaci sosai yashiga kwallawa mama kira a kidime tashigo dakin tozali tayi da Muwadda mamaki ne yakama tashiga tambayarta meakai mata

Cikin bacin rai abban muwadda yafara magana

“naji abinda *kannan mijinta*sukai mata to bari kiji, banyarda dan suna yanuwanta ba su shiga wulakanta min ya ba baze yuba kuma yanzun nan zankira alhj muhammad din dan bazan yi magana da mijinta, kuma bainda zata koma, yar tawa guda daya bazai yaba,

Maman Muwadda dai tarasa ma me xatace jikinta taja Muwadda tafara rarrashinta wayarsa ya dauka yafara neman layin dady bugu biyu ya dauka

Nan suka ya kwashe komai yafada masa, hakuri yai tabashi ya sanar da shi besan anyi ba, amma zai tsawatar musu sukai Sallama yaajiye wayar mama taja Muwadda dakinta tashiga rarrashinta

“Haba muwadda kar kibari arabaki da mijinki kinga hakar mu takusa cimma ruwa, dan haka kibarni dasu, da sannu zanyi maganinsu ”

” gaskiya mama, ina takura fa, kamar yadda kike da buri haka nima ina da nawa burin yanzu gashi kinsa ni adamuwa ”

 

” Haba Muwadda, kiyi hakuri mana, yanzu ki kwanta ki huta kuma wlh sai na rama miki marin da afifa tasa Assadiq yaimiki ”

 

Tana gama fada tai tashi ta fita Muwadda kuwa wayar ta ta dauka takira layin muktar suka sha hira ya kuma jadda da mata kar tabari tasa ciki da Assadiq take gabanta yabada dam ta tabbatar masa bazata bari ba, sukai Sallama tare da alkawarin tura masa kudi

***********

Dady ne yatara yayansa yai tai musu fada akan abinda sukaiwa muwadda momy ce tadubeshi tace,

“Haba alhj yarinyar nan fa bata da kirki dan baka tsiyar da takewa mutane ba ”

” yaisa hajiya kareema sai dai inke ce baki da kirki bazeyu ace surikanki biyu ace duk basu da kirki ba dan haka wallahi ku kiyayeni ”

Yanagama fada yatashi yabar parlon faruq ne yadubi momy yace

 

” momy kinga irin ta ko wlh shiyasa natsani auran nan tun farko irin haka na guda, amma gwanda ma da hakan tafaru kwa fahimci halin kirki na aunty safiyya ”

” dakata faruq rufemin baki, kai tashi kabani guri sarkin iya tsara magana kawai ”

 

Fita yayi yakoma dakinsa su farhana kuwa take suka kira Muwadda awaya sukai mata tasas bata kyalesu ba sai da taci mutuncin su

 

 

Yau aka kawo kudin auran jalila da afifa Dr almustapha yakawo 50k yayin da haisam yakawo 200k murna gurin momy baa magana tanata kushe na jalila tace,

“afifa kinyi goshi, jalila kuwa nasan bazai abun arziki ba, yo wani wan safiyya ne zayi abin azo agani, dan albashi ne fa ”

Jalila dai bata tanka mata haka farhana wacce jikinta yafara sanyi sakamakon jibi zaa fara biki, gashi ibraheem ya hanata fita ko ina duk partyn da xatayi yace bazai zo kuma inde da maza zatayi to kar taje, gashi bata iya yimasa musu taci burin bakinta ga yadda yakasance

 

Muwadda ta dawo dakinta bayan kwanakin da tayi maman ta har gida taje taiwa momy rashin mutunci bayan taramawa yarta marin da Assadiq yai mata akan afifa momy tai ta kuka tai mamakin abinda kanwar tata taimata sai kace ba yayar taba

 

Tunda Muwadda ta dawo Assadiq be bi takantaba yau takarbi girki ta daure taimasa girki saboda wata bukata ta dakinsa tanufa yana kwance da fadila abayansa ta kwanta sunata dariya yana ganinta ya hade rai yamike yadau yarsa zai fita hannunsa takama yadago suka hada ido wani malalacin murmushi taimasa wanda yakasa gane manufarsa🤔

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:33Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W>F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*Rabbana atina fidduniya hassanah wafil akhirati hassanah wakinna azabar nar*👏🏻

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

💙💦
*Ina gaisheku TALENTED WRITTERS gsky kunaji da naseeba nagode sosai da Dedicating din da kukai min Allah yabar LOVE gaba dai gaba dai ina biye da ku sisters muje xuwa*💙💦

 

🍇
*Ina tayaki murnar fara sabon novel dinki kawata garkuwar fulani mai suna RUBUTACCN ALAMARI Allah yasa kinfara a saa, Assadiq din sopy yana gaida hamma umar kyauta ba da kudi ba*🤝🍇
😃😃
😂

 

 

 

 

*81*

 

 

~~~wani banzan kallo Assadiq ya watsawa muwadda ba shiri tasaki hannunsa amma bata bashi hanya ba fadila ce tadubi Assadiq tace

“papa, me aunty na tai maka? dan Allah kayi hakuri tadena, kaga fa tana bani Sweet kuma ita bata dukana kmr yadda su aunty farhana suke dukana ”

Shiru yayi yaxubawa dan karamin bakinta ido irin na safiyya can yanisa yace

” shikenan Fadilaty na hakura komai ya wuce ”

Ran muwadda ne yadan sosu amma sai ta dake , tashafi cikin jikinta da yafara fitowa tace

” nagode sweery, kazo muje ga abinci can nahada ma, baby fadila nagode kinji ”

Tafada tana kokarin jan hannun fadila, Assadiq ne ya janyeta yace

” aa, kibar abincin ki nagode, munkoshi ”

Narai narai tayi da ido kmr zatayi kuka, tausayi tabashi yabi bayan ta suka wuce part din ta ta gyara parlon tsaf, guri yasamu ya xauna dubansa tayi tace

” sweery ka karaso dining din mana ”

” aa ki kawo min nan, annabin mu betaba cin abinci a kan abu madaukaki ba, haka dan bancika son hawa dining ba ”

Gajiya tayi dan batason motsa jikinta, haka ta daure ta kwaso kayan abincin tare da taimakon fadila, ta zuba masa jollofe din taliya tayi sai coslow da soyayyar kaza taliyar tafara narkewa dan tadahu luguf kazar kuwa tauri tun a ido ya raina abincin, wani plate din ta dakko zata zubawa fadila, hannu Assadiq yadaga mata yadora da

“No, kibarshi zumuci tare, ya isa haka ”

” ok, tafada takoma gefansa ta zauna sai faman wash takeyi ahankali ya furta

“sannu ”

Yai bissimillah yafara cin abincin lomar farko da kyar ya hadiyeta yadiba yabawa fadila dubansa tayi tace

” papa ”

” naam binty ”

Gsky nakoshi abincin ba irin na mamma na bane, nide madara zansha”

Hmmm, muwadda kinji fa abinda yarki tace, kidamo mata madara, da Allah ”

” Bani da madara, takare ”

” amma baki fadanba”

“to ina naganka, amma dai shikenan, yanzu nafada maka ”

Shiru yayi yadan tsakuri abincin yaci, tashi yayi zai kai fadila, dubansa muwadda tayi tace

” sweery, pls ina son magana da kai kaji ”

Ok, kijirani, inje masallaci indawo , nazaci tare zamu kwana, karewa”

Goya fadila yayi ya fita zuwa part din safiyya tana kitchen tagama tuwon alkama da miyar kubewa danya tun da yadoso part din kamshi yadaki hancinsa, kitchen din yanufa tana sanye da doguwar riga ta mterial dinkin buba, a kofar kitchen din yatsaya fadila ce tace

“mamman fadilan Dee, zumunci abinci ”

Da sauri safiyya ta juyo ta dubi Assadiq tace

” Dee, kanajin yarinyar nan ko,?

“Hmm, inajinta sopy, ai batai laifi ba ko?

“au tambayata kake, to ai kafini sanin amsar tambayar ka ”

Ciki yakarasa bayan ya sauke fadila yadora Kansa a gadon bayanta yana shakar kamshin turaran ta ahankali ya furta

” matar Assadiq *QAMSHIN*ki daban yake, wai wane turare ne wannan “?

” Dee, dafarko dai kadagani, kaga fa hankalin yarka yana kanmmu ”

” naki sopy, inbanji dumin jikinki ba fada min nawa zanji ”

Ai kuwa fadila ta zuba musu ido can ta tafa hannunta tace

” la, mamma na zata goya papa na, cab wlh mamma na tanada karfi ”

Sauri Assadiq yayi yajanye jikinsa daga na safiyya yanata dariya can yace

” sopyn Assadiq, tuwo kike mana, lallai zamuci dadi yau ”

” aa, Dee tuwo na dady ne, sai nawa guda biyu ”

” “cab kice yau akwai rikici “, yafada yana dakko kofiin fadila na madara yahada mata mika mata yayi ta karba tana sha ta mika masa tace

” karba, gaskiya bana sha, sugar bejiba ”

” Kai Fadilaty, meyasa kike son wahalar dani ne, kawo inkara miki sugar ”

” Dee, wlh kai kake shagwaba yarinyar nan shiyasa take ji har yanzu bata girma ba ”

” to girman tayi sopy, ki kyalemu ko Fadilaty ”

” eh mana papa na ni kadai ”

” Ok yayi kyau fadila,
Dee ko zaka mikawa dady tuwon nan ”

” me zaihana sopy, ai ba wani abu dan mata ta aiki mijinta ”

” lala, rufa min asiri Dee nikam ba aikenka nayi ba ”

” papa na zanbika gidan momy gurin aunty jalila ”

” ok Fadilaty mutafi ”

Kwandon kayan abincin ya dauka suka fita safiyya tayi tai fadila ta ajiye kofin madarar ta taki suna zuwa suka hadu da dady da faruq zasu masallaci jalila yaiwa magana tafito ta karbi abincin ta shiga da shi ciki da fadila yai alwala yabisu masallacin

Farhana naganin fadila ta kira ta

“ke dan uwarki zo nan, wai ke yar madara ko, kyaci ubanki randa kika wayi gari ba madarar ”

” Hmm ai su rainon madara sukai mata, ni kuwa yayana cab bansan rainon ma me zanyi musu ba wlh ko da yake muda zamu tafi england ai sai Allah ”

Cewar afifa tafada tana fari da ido jalila ce
tadubesu tace gaskiya bakwa kyautawa wlh yanxu me yakawo wanga zancan haka yakamata ace kun kaunaci yarinyar nan ko dan kasancewar ta jinin mu ko”

“aa aunty jalila yi hakuri mana, kibar mu muyi abinda muke so ”

” nabarku afifa, to amma kusani zakuga abinda bakwaso anan gaba, ajuri zuwa rafi wata ran tulun zai fashe ”

Karar wayar ta ne yakatseta tana dubawa taga *Dr almusty*murmushi tayi tasami guri ta zauna taja fadila jikinta tadaga kiran

” Hello, *Doktar*”

“naam habibty, kina lpy ”

” Lpy kalau, ya aiki ya ummina “?

” aiki gashina nan yaimin katanga da mata ta ummi kuma tana kano ”

” Hmmm, *doktar*kenan, yaushe zaka baro abujan?

“ummm, wajen jibi zandawo dan namatsu inyi tozali da kyak kyawar fuskar mata ta ”
” shikenan Allah yakawo min kai lpy, ga fadila ku gaisa ”

” Hello uncle *Dr*, ina yini, ina umminku “?

” Lpy kalau aku, ina surutu?

“nadena sai dan kadan fa nakeyi yanzu ”

” to yayi kyau ki ce ina gaida maman ki ”

” to uncle zan fadamata, ina allura, kazo kaiwa su aunty farhana tunda basa sona ”

” shiiii, fadila kar ki kuma cewa wani bayason ki kinji ko ”

” uncle *Dr*”

“naam fadila ”

” dukana fa sukeyi ”

Zasu dena kinji ko, kibawa aunty wayar”

Jalila ce ta karbi wayar suka taba hira karshe sukai Sallama ta kashe wayar su farhana kuwa tunda tafara wayar suka bar mata wajen dan sun raina auran jalila gani sukeyi ba wani abu zata tsinta ba

Dady ne ya shigo da zaratan yayan sa abayansa lokacin momy tana zauna a kujera fadila na kwance a cinyar ta, Assadiq yaji dadin hakan aransa yake tunanin momy tafara kaunar fadilan sa karasawa sukai suka zauna fadila ta taso ta rungume faruq shima rungume ta yayi yana fadin

“fine girl, kwana 2, ina mamma ”

” Lpy kalau uncle, ga tuwo can na kawo maka ai zaka ci ”

” bana cin tuwo fine girl amma zanci naki ”

” Kai, uncle bani ce nayi ba fa, mamma na ce tayi ”

Assadiq ne yadubesu yace Fadilaty tuwo fa na dady ne da zakiyiwa uncle kyautar sa”

“Rabu daita sadauki, ai andena bata rancan kudina ”

Sakin faruq tayi ta tafi gurin da dady yake zaune ta rike kunnuwanta tace

” kayi hakuri dady tuwon ka ne ”

Gaba daya suka sa dariya Assadiq ne yagaida momy, jalila ta dakko plate ta zuba wa dady tuwon safiyya suma suka zuba sai sa mata albarka yake, haushi ne yakama momy aranta take fadin ina ma Muwadda ce tayo girkin nan

 

Assadiq be koma gida ba sai wajen 10 suna ta tsara bikin farhana, lokacin safiyya har tafara bacci suka shiga
Fadila ce tafada jikinta atsorace ta farka, tsawa ta daka mata

“wai dan wace irin yarinya ce ke fadila, bakya abu da nutsuwa ko, wlh jikinki, zai fara gaya miki”

“mamma na kiyi hakuri nadena ”

” ai banaso ki dena kici gaba, Dee sannu da xuwa, ya su momy”

“yauwa sopy, lpy kalau, amma naji kamar kina cin alwashin dokar min ya ko to kar ki fara”

” Haba Dee yanzu baka ga me tayi min ba ”

” nade fada miki ”

Hannun fadila yaja suka nufi bandaki yai mata wanka ya sa mata kayan bacci masu kyau ya kaita kan gado ya kwantar da ita tare da yimata addua safiyya ce tashigo dakin ko kallansa batayi ba tasa kayan bacci ta kwanta sai da fadila tai bacci sannan Yadawo gefan safiyya ya shiga balle mata maballin rigar ta ahankali yashafi kirjinta ya ce

“Sweet sopy kidena kwana da bra zata hanaki bacci mai dadi”

“sai gashi kuma ni inaso, ya kenan ”

” to banyarda ba sopy ”

“yafada yana kokarin kai bakinsa ga kirjinta ture shi tayi tare da rufe kirjinta ahankali yace

” kar ki kuma rufe min ai banaki bane ke kadai, kuma ai mallaki na ne, sai da yagama jagwal gwaleta sannan yagyra mata rigar ta

Yasakar mata kiss sannan yaja musu kofa part dinsa yanufa yai wanka sannan yanufi part din Muwadda tana zaune da wata yar bingilar riga ajikinta wacce ta fito da cikinta tana ta shan agwalima gefanta yazauna ta kwanto da kanta aciyarsa tace

“sweery kadade, meyasa “?

” muna tare da su dady ne ”

Yafada yana shafar cikin jikinta, dan dago da kanta tayi tace

” sweery yakamata bani kudi infara yo siyayyar baby ”

” ok, yanzu dai zanbaku kudin hidimar biki ”

Shiru taimasa saboda bikin baya gabanta

 

Biki yazo anata hidima haisam yazo ya kawo wa afifa kaya a akwati da kudi saboda hidimar bikin farhana

Dr almustapha ma yazo yaiwa jalila kyautar kudi yabawa momy ma gudun mawa

Farhana ce take ta faman shirin zuwa kunshi ita da kawayanta yan gayu kuma yan karya kiran ibraheem ya shigo wayar ta tana dagawa kawai tasaki kuka tare dayin cilli da wayar.

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[3:46pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

 

*💦T <W>F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐

 

*mashaallahu la kuwata illa billahil azim*👏🏻

 

💦*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝💦

 

 

💙
*wannan shafin naka ne yaron kirki hakika yau rana ce ta* *musamman a gareni da kai kanka ummin ka tana tayaka murnar cika shekara 5 dakayi* *ayau 16 september ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka yasa kazama abin alfahari ga alummar* *musulmi Allah yasa kaza memin hasken idaniya ta Ameen Allah sarki Assadiq kenan tun kana karami kakewa ummin ka waka*💙

*_sannu gimbiyar mata ummi sarauniyar mata_*💃🏻

🎈
*HAPPY BIRTHDAY Assadiq muazu yusif🎈*🎂🎂
🎂

 

 

 

*83*

 

~~~Ahankali farhana take bin yanmatan nan da ido su dinmma ita suke kallo tare da karewa dakinta kallo bayansu kuma wasu samari ne guda biyu dauke da akwatina shigowa sukai suka zube akwatin a parlon

Gaisheta sukayi taamsa a wulakance basu kulaba daya a cikin suce ta dubi farhana tace,

“amaryar ya khalil bakya magana ne, ai de kya bamu dama mu gabatar da kanmmu ko duk da de da sannu zamu saba tunda zamu zauna a muhalli daya ”

Wata farar yarinya ce tafada, shiru farhana tai musu can tanisa tace

” bandamu da sanin ko kudin suwaye ba,amma badamuwa ina sauraran ku ”

Gaba dayansu mamaki kalamanta yabasu sukai mata shiru can yarinyar da tafara magana ta kuma yin Caraf tace,

” amaryar mu kenan, to dafari de, ni suna na fareeda, wannan kuma
fatisa ga faixa ga bilkisu sai kanwar hajiyar mu zainab masari”

“ok sannun ku, ko ya kuke?

Wacce aka kira da masari ce tabata amsa

“kamar yadda kike, haka muke”

Ibraheem ne yai Sallama ya shigo suka amsa kannan nasa ne suka shiga yi masa sannu da xuwa ya amsa da kulawa, farhana kam ko kallon sa batai ba yasami gefenta ya zauna ya dubeta da kulawa yace

“farhana ya baki kawo musu komai ba?

“ni bansan kitchen din ba ”

” Hmm ko, ok zan nuna miki kafin nan zan gabatar miki da yan uwa na, nan ya kuma yimata bayani game da su ya dora da

“farhana, zamu zauna tare da fatisa da zainab anan bangaran na mu saboda haka ku zauna lpy, ki dauke su kamar kannan ki banasan ki dauke su amatsayin *kannan mijinki*”

Wani kallo tai masa, amma fargaba ce fal ranta, saboda yadda taga zagada zagadan yanmata nan ace tare zasu zauna, ahankali ta furta

“Allah ya bani ikon zama lpy ”

” Ameen, ke bilkisu shigar musu da kayan su dakin su, ku kuma ku tashi kushiga kitchen ku dora mana girki ”

Yana gama fada yaja matar sa sukai daki tashi sukayi suka shiga kitchen suka fara girki

Farhana kuwa, suna shiga daki tafara kuka, ita bazata iya zama da *kannan mijin ta*ba, tun ibraheem yana rarrashinta har yagaji ya fara yimata fada karshe yabar mata dakin

 

Sanda su fatisa suka kammala girkin su farhana tana daki suka ci suka koshi, ko takanta basu bi ba su bilkisu sukai tafiyar su

Ibraheem be shigo ba sai bayan sallar ishai lokacin su masari ne kawai a parlon sukai masa sannu da xuwa suka koma dakinsu zama yayi yana jiran farhana shiru bata fito ba gajiya yayi ya nufi dakin tana xaune ta idar da salla dubanta yayi yace

“farhana tashi muyi salla ko”

“ni bana salla ”

” Hmmm baki san waye ibraheem ba farhana, to bari nadan baki kadan daga cikin halayena, bana son karya haka kazalika bana son raini, ya inzo in tatar da ke kina salla amma saboda wulakance kice ba kya salla ”

” to naji ina salla, karabu dani bazan iya ba, fakat ”

 

Sai da yaimata da gaske sannan ta tashi sukai salla rakaa biyu dafa kanta yayi yaimata addua sannan ya dakko ledojin da yashigo dasu guda biyu ya dau daya yafita da ita dakin su zainab ya nufa ya kwankwasa budewa sukayi ya mika musu ledar kazar tuna ni tashiga yi me ibraheem ya fita yi shigowar sa ce ta katse mata tuna nin data ke nan ya zauna suka ci kazar tambayarta yayi

“farhana kinci abinci amma?

“banciba ”

” meyasa?

Shiru taimasa ahaka suka kammala cin kazar tashi tayi tashiga toilet tai wanka tana fitowa shima yashiga yayi, kan yafito ta haye gado ta kwanta tunanin gida tafara sai kuma kuka ahaka ya hau gadon ya jata jikinsa, da kyar farhana ta yarda da ibraheem komai ya kwana tasha azaba da kyar tasamu bacci

Washegari da asuba ibraheem ya tasheta taimaka mata yayi tayi wanka har ta koma ta kwanta ya dubeta yace

“farhana be kamata ki kwanta ba, kitashi ki shiga kitchen ki hada mana break fast, kinga su fatisa zasu makaranta ”

” a gaskiya ni bazan iya ba…..

 

“dakata farhana ki daure ki tashi bana son yarannan su makara ”

 

Tashi tayi tafita zuwa kitchen tana zuwa taga wasu cups dinta afashe ga Kwanikan da sukai girki duk abace haka ta daure ta dafa tea ta soya dankali ta kammala takai parlon ta zubawa su zainab nasu ta barshi a kitchen ta koma daki ta kwanta

Karfe 8 su fatisa suka fito daga dakinsu a lokacin ibraheem da farhana suna parlon suna break, karasawa sukayi suka gaisa da yayan su, fatisa ce kawai tagaida farhana ta amsa a sanyaye zainab ce ta dubeta tace

“amarya break dinmmu fa?

“yana kitchen mana ”

Tashi tayi tashiga kitchen ta dakko musu flaks din tea da dankali ta dawo fatisa ce ta bude dankali ta gani mai da dubanta tayi ga zainab tace

“yaya zainab kinmanta bana cin dankali”

“to ya zakiyi amarya shi tayi ”

Ibraheem ne ya dubesu yace

Wai me kuke fada ne?

” yaya khalil bana cin dankali, nafison indomie ”

 

Maida dubansa yayi ga farhana yace

” farhana daure ki dafa mata indomie ”

Dagowa tayi ta zuba masa ido tarasa ma me xatace ce,

Bayadda ta iya haka ta tashi ta dafa mata indomie tana yi tana hawaye

Bayan ta kammala ta shirya cikin wata atamfa green da ja tayi kyau ibraheem ne yadubeta

” kisa hijjabinki kizo muje ki gaida su hajiya

Kallonsa tayi tana jinjina sa hijjab, haka ta dakko hijjab din tasa suka nufi bangaran su hajiyar ibraheem kannan sa ne maza zaune a kujera nan farhana tagaida hajiya taamsa da kulawa nan tashiga yimata nasiha

Kannan sa ne suka dubi farhana suka ce

 

“amarya kwanan abincin mmu yana gurinki ”

” dariya ibraheem yayi yace

“jafar kenan, to ai badamuwa ko farhana ”

Shiru farhana tayi tadan zauna jim sannan ta koma part dinta tana shiga taga parlon kaca kaca kamshi tajiyo a kitchen
Ahankali ta shiga kitchen din bilkisu tagani tana soya doya shiru taimata tanufi dakinta tana shiga tafashe da kuka wayar ta ta dauka tashiga neman layin momy

 

 

 

*NASEEBA GAWO*✍🏻
[5:56Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
����‍👩‍👧

 

*NA*

*NASEEBA I UBA 💐

 

 

 

*Allahumma ya mukallabil kulubi sabbit kalbi ala dinika AMEEN*👏🏻

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

💙
*wannan shafin nakine sumayya sumy Allah yaraya mana nana khadija ya albarkaci rayuwar ta ameen*💙

 

 

💘
*sakon gaisuwa gareku mutanan nijar maradi zindar da mali sakon ku ya iskeni dafatan duk kuna lpy ina gaisheku da babbar murya Allah yabar kauna AMEEN*💘

 

 

 

*85*

 

 

~~~Mamaki ne yakama safiyya, tare da tambayar kanta me zaisa farhana ta kira ta tana kuka cikin kidima tafara tambayarta

Hello, farhana lpy kike kuka “?

” aunty safiyya, wlh nagaji, bazan iya ba *kannan mijina* basu da tausayi bare afuwa kullum agurina suke tarewa banda guda biyu da muke tare da su ga maza kullum ni ke basu abinci, wlh nagaji momy tace zaa kawo min mai aiki ibraheem ya ce be yardda ba ”

” aa subahanallah, to abinda nake so da ke farhana, kayi hakuri ita rayuwa da kike ganin ta hakuri ake musamman rayuwar aure kinji ko, yanzu me kike so ayi ”

” aunty so nake ki fadawa ya Assadiq ko zaiyiwa ibraheem magana akawo mai aikin dan Allah ”

” to shi kenan farhana zan fada masa inshaallah, amma fa kikara hakuri ”

” tohm shikenan, ina fadila bata mu gaisa ”

Safiyya tana mikawa fadila wayar ta gudu bayan yaya rukayya ta buya ita bazata gaisa da ita ba sai da safiyya tai da gaske sannan ta karbi wayar, farhana nata magana tai mata shiru hakura tayi ta kashe wayar

Safiyya ce ta mai da dubanta ga yan uwanta tabasu labarin yadda sukayi da farhana, najiba ce tai Caraf tace

“Hmm dadina da gobe saurin zuwa, har anyi daren gari kuma ya waye, kijifa ummi wai yaya safiyya take bawa labarin *kannan mijinta* wlh bata ma da kunya ”

” aa to ba rayuwar kenan ba, najiba shiyasa kayi da kyau ko dan gaba ”

Cewar ummi, amina ce ta dora da

” ni ba abinda yafi bani haushi ma wai abata fadila su gaisa, yarinyar da ta dau karan tsana ta dora mawa ”

” to ni de zanyi iya bakin kokari na wajen ganin ankai mata mai aikin ”

” Allah ya nufe ki safy ”

Cewar yayar su rukayya, sallsmar yayan su ce ta katse musu hirar nan suka gaisa da shi suka zauna hira gwanin shaawa ummin su dadi yakamata ganin yaran nata cikin walwala da nishadi sai dare Assadiq yazo daukar safiyya ya shiga suka gaisa da
Su baffa yai musu
Alhr suka tafi tun a hanya fadila tabawa Assadiq labari

“papa, kasan me?

“aa Fadilaty sai kin fada ”

” Dazu aunty farhana tai wa mamma na waya
Wai abani mugaisa
Nikuwa naki mata magana ”

 

Safiyya ce ta daka mata tsawa ta dora da,” wlh fadila akan
banzan surutun ki ko wataran sai na zane miki jikin ki ”

” amm sopy, kullum kina ikirarin dokar min ‘ya wlh kinji na rantse kar ki fara zaki ga mugun bacin rai na, kinji dai nafada miki ”

” Haba dan Allah Dee………

“yaisa bana son mai maita magana baya ya juya yakalli fadila da take tsaye abayan kujerar sa yace

“binty, kinajina ”

” A, papa”

“Good, kar inkuma ji kince anbaki farhana awaya ku gaisa kin ki, itama auntyn ki ce kinji ko ”

” To papa na, nadena bazan kuma ”

” dakyau Fadilaty binty ”

Safiyya kam shiru taimasa, ahaka suka karasa gida suna shiga ta balle murfin motar ta nufi part dinta, sai da yarufe kofa sannan ya budewa fadila kofar motar ta fito ya riko hannunta suka nufi part din Muwadda tana daki sai rushida a parlon tana cin abinci, da sauri tai masa sannu da zuwa ya
amsa a takaice saboda shi dai yarin
yar, bata kwanta masa ba, kai tsaye dakin Muwadda yanufa tana kwance agado tana waya da muktar tana ganinsa ta katse wayar dubansa tayi
Shi din ma ita yake kallo, kan gadon ya karasa ya dubeta yace

“ya jikin naki “?

” Da sauki sweery, sai ciwon baya kadan kadan haka ”

” Allah yasawake, yaushe zaki koma asibiti “?

” sati na sama inkuma na haihu ne ma shikenan ”

” haka muke fata Allah yaraba lpy ”

” Ameen sweery, fine girl ba magana ko ”

” to ai kema baki yiwa uncle dina magana ba shiyasa nima nai miki shiru ”

” Kai fadila lamarin ki yana da ban mamaki, tashi muje ki kwanta,Muwadda sai da safe ki kular min da baby ”

” ok sweery, baka da damuwa, sai da safe ”

Yasa kai yafita dama so take yayi yafita tace gaba da wayar ta

 

Kai tsaye part din safiyya yanufa fitowar ta kenan daga wanka yashiga dauke kanta tayi sai da ta shirya sannan ta dubi fadila tace

” kiwuce muje inmiki wanka ”

” kibar shi zanmata, kije ki dafa min lipton ”

Bata amsaba ta fita shikuma yashiga toilet din yaiwa fadila wanka yasa mata kayan bacci wasu farar riga da gajeran wando ja yasa mata turare dubanta yayi yace

” saura kuma me?

Kunan sa takama tarada masa magana murmushi
Yayi ya ja hannunta suka fita kai tsaye kitchen suka nufa safiyya tana kallon su taci gaba da abinda take cup ya dauka ya dama mata madara yabata suka koma parlo tasha tana gama sha tai bacci safiyya ce takawo masa lipton din data dafa masa ta zuba masa a cup mika masa tayi yadauke Kansa dole tashiga bashi yana sha can ya dubeta yace

 

“matar Assadiq, fushi ko??

“Dee to ai kai dinne wlh kafiya sangarta yarinyar nan ”

 

” to ai kece kullum baki da zance sai na duka, shifa duka da kike gani baya gyara sai kangarar wa ”

 

” shikenan Dee xan kiyaye ”

” yauwa sopyn Assadiq yafada yana janta jikin sa ahankali ta kira sunan sa

 

“Dee, dazu munyi waya da farhana, nan tabashi labarin yadda sukayi da farhana murmushi yayi kana ya dubeta yace

 

“sopy kenan, to ke kintaba ganin wani yashiga hurumin gidan wani to in kira ibraheem ince masa me, baa haka tayi hakuri tabi umarnin mijinta kawai ”

 

” Amma Dee….

Kan takarasa ya toshe bakinta dana sa bayadda ta iya haka takyaleshi yashiga sarrafa ta yadda yake so

 

Abangaran farhana kuwa har tasaba da dawainiyar *kannan mijinta* yanzu haka zaune take a parlor tana kallo masari ce tafito da wani plate cd a hannunta kai tsaye gurin tv ta nufa tasa, cikin bacin rai farhana ta

Dubeta tace, “ke, masari kike ko wa?, wani irin iskanci kenan ina kallo zaki zo ki sa min wani abun daban”

 

“Hmmm, amarya kenan, A baki bata ba masari suna na ko kice zee, inbanda abinki wayaki waazi ke mufa baa cika kallo a gidan nan ba gwanda ma ki sani ”

Cikin zafin nama farhana takaiwa masari mari da azama fatisa ta rike hannuta mamaki ne yacika farhana ta kwace hannunta nan sukai mata tatas daki ta shige tai ta kuka ranar ko girki batai ba

Ibraheem yana shigowa su fatisa suka sa kuka wai farhana ta xagi malam, ransa ne yabaci cikin sauri ya nufi dakin tana kwance a gado yafara mata masifa

 

“farhana me yakai ki zagin mahaifin mu, akan wane dalili ”

” ibraheem wlh karya suke min ta yaya zan zagi mahaifin ku bari kaji fa yadda akai……..

 

“yimin shiru farhana baki da abinda zaki cemin karya ba halin mmu bace dan haka kijira hukuncin da zai biyo baya dan ina sonki bashi zai baki damar cin mutuncin yan uwana ba ”

Yanagama fada yafita kai tsaye part din hajiyar sa ya nufa muryar fatisa yaji tana fadawa hajiya abinda farhana tayi gaban sa ne yafadi saboda yasan zafin hajiyar tasu intaji be san matakin da zata dauka ba

Haisam ne zaune acikin mota afifa na gefansa taci kwalliya sunata tsara bikin su wayar sa tana hannunta kiran shukura ya shigo kallon sa tayi tace

“Darling shukura fa?

“Dan Allah manta da ita kanwa tace, bazai wuce zancan biki zatai min ba kinsan tunda bikin nan yakarato bata da aiki sai tsare tsare ”

” Allah sarki ai daka daga ”

” manta da ita muci gaba da hirar mu, yauwa dady fa yace da anyi bikin mmu zamu wuce england ”

” Kai amma naji dadi sosai Allah ya kaimu

“Ameen tawan ”

Jalila ce zaune tana karatun wani littafi wayar ta fara ringing tana dubawa taga *Doktar*nan tadaga suka gaisa tambayarta yayi

” habibty me kike shiryawa game da bikin mmu ”

” Gsky sai kazo tukunna ”

” to shikenan ba damuwa, amma fa maganar gaskiya ni ba me kudi bane ”

” Haba dokar dan Allah nifa bandamu da kudi ba kai nake so ”

 

Dariya yayi sukai Sallama ta kashe wayar, yau tun safe Muwadda ta tashi da nakuda tun da aka fadawa momy takasa zaune takasa tsaye asibiti aka kaita sai ihu take hankalin Assadiq ne yatashi haka mamanta har yamma bata haihu ba dole Assadiq yasa hannu zaai mata cs

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[5:55Am,2017]

*®💦����💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*ya hayyu ya kayyumu bi rahamatika astagisu aslihil shaani kullahu wala takilni ila nafsi darfati ainin* 👏🏻

 

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

*🎈Hip hip hurry*🎈

*💙2day is a worndafull day 4 u suhyla mustapha khalid whish u plenty years a head*💙

*Happy birthday 2 my dear suly*😘

 

 

 

*86*

 

 

~~~Dab da zaa shigar da Muwadda dakin tiyata ne Allah ya sauke ta lpy ta haifo yarta mace amma tasha jiki sosai murna gurin Assadiq baa magana haka momy sai murna take anhaifa mata takwara maman Muwadda kuwa hankalinta yana kan yarta ita so tayi ta haifo namiji sai gashi hakan bata samu ba aka kintsa mejego da baby kai tsaye dakin hutu aka kaita kan kace kwabo asibiti ya cika ya hannatu ma tazo tare da nabil da ashraf yaran sun zama manya Muwadda kuwa hankalinta yana kan babyn ta sai da magariba safiyya ta zo dauke da abinci fadila tana ganin baby ta karasa sai murna take aunty ta sai baby safiyya ta gaida su momy tare da yimusu barka mai da dubanta tayi ga Muwadda

“sannu Muwadda, ya jiki”

“Alhmdulillah, aunty da sauki ”

” mashaallah, Allah yaraya baby ”

” Ameen nagode ”

Safiyya ce ta ja ya hannatu suka fita waje, domin tattaunawa akan matsalar farhana

” ya hannatu, dan Allah ayi wani abu game da matsalar farhana ”

” maman fadila kenan ke har kin manta iskancin da yaran nan sukai miki, to me zaai mata kowa ai da haka yasaba rayuwar aure saboda haka ki kyaleta ta dan dana”

“haka ne yaya amma…….

“safiyya mubar maganar farhana mushiga wata ”

” shikenan yaya ”

 

Kwanan muwadda 2 a asibiti aka sallamota mamanta taso tafiya da ita gida Assadiq yaki yarda dole suka hakura aka kaita gidan momy daki guda aka bata nan dinma dole akai masa afifa sai murna take ansami takwarar momy shiru kawai take musu amma ita sunan mamanta zaasamata kullum safiyya zata shigo ta ga baby sannan ta wuce school momy zata kulata ba yabo ba fallasa

Faruq ne zaune a parlo bayan Yadawo daga kai fadila jalila ya kwallawa kira da sauri tafito

“yaya faruq gani ”

” alhuda huda, karatun ake yi ne “?

” yaya faruq alhuda huda kuma nazama ”

” sunan da yadace da ke kenan, yauwa jeki dakko min babyn nan inganta ”

” to, yaya ”

Tana shiga ta tatar da Muwadda na bata nono, karasawa tayi kan gadon ta dubeta tace

” aunty Muwadda ya faruq ne yace abada baby zai ganta ”

Shiru tai mata sai can ta nisa tace

” to, yanzu zanrabata da nono ne ko kuma yazaai?

“kmr yaya, kawai kibada ita shine zaki tsaya kinaimin dogon turanci ”

” inya matsu ya shigo mana yaganta, ko kuwa zai gwada min iko irin na *kannan miji* ne”

“me abin iko anan daga ki bada baby sai kice wani zaagwada miki iko to angwada ikon yar ke kika haifeta ke kadai ne ”

” oho miki jalila, amma wlh ba inda zaaje min da baby ”

 

Fita tayi tasameshi zaune inda tabar shi dubanta yayi yace

” jalila ina babyn?

Nan tabashi labarin yadda sukayi da Muwadda shiru yayi can yanisa yace

 

“lallai yarinyar nan rashin mutuncinta ya isa, dan ta haifi ya shine zata ninka rashin mutunci, tabar ‘yarta nafasa ganin yar ”

Momy ce tafito daga dakinta ta dubi faruq tace

” to, sarkin rikici me yafaru kake sababbi ”

” momy ni da mara mutuncin yarinyar nan ne mana ”

” safiyya ko?

“safiyya kuma, aunty safiyya zankira da mara mutunci, wa ccan de ”

Nan yabata labarin abinda tai masa yanzu, shiru tayi ta tashi dakin Muwadda ta nufa tana rungume da babyn dubanta tayi

tace,” Muwadda meyasa kike haka ne?

“momy me nayi kuma?

“ya faruq zai aiko abashi baby yagani kice aa akan wane dalili “?

” Haba momy, shi faruq din wa yafi da bazai yaganta ba zai wani aiko ”

” yaisa yanzu dai ki kawo ta akaita gurin alhaji yaganta ko shima bazaki bada akaita ba ”

” aa akaita mana ”

Daukar ta momy tayi tafita faruq tafara mikawa kin karbar ta yayi ya leka yaganta a hannun momy

” gata nan kuwa kamar su daya da uwarta, Allah yasaba hali ”

” Ameen ya faruq ”

Cewar jalila tafada tana gyra xaman glass din fuskar ta momy de dariya tayi ta wuce saman dady

Kiran farhana ne yashigo wayar afifa wacce tashigo parlon yanzu

” Hello, aunty farhana ya kike ya ibraheem ”

” Lpy kalau afifa, Hmmm ustaz zakice ”

” aa kice da matar malam nake magana ”

” ke de bari afifa ai abin baa cewa komai, ya aunty muwadda da baby “?

” Lpy kalau, ashe kinji haihuwar ”

” naji kinsan kusan kullum sai ustaz sunyi waya da yaya Assadiq to shi yafa da masa ”

” ok, ya *kannan mijinki* kuwa?

“yan iska de zakice shegu, kinga ki turo min pics din baby ingani kafin muzo suna ”

” tohm shikenan aunty farhana ”

Sallama sukayi ta kashe wayar take ta tura mata pics din

 

Sanda momy takewa dady baby yana toilet sai da tajira shi yafito sannan ta bashi yar yaganta yasa mata albarka tare da mata addua dagowa yayi ya dubi momy yace

” ita kuma wannan ya sunnanta “?

” Hmm alhj kenan ai takwara ce ”

” to ba laifi Allah yaraya, ina sarkin surutu kwana 2 bata zo karbar kudin alawa ba ”

” Fadila ta shiga makaranta shi yasa take wuyar gani

 

Ina ruwan fadila ”

Karamar sarka ya dakko ta gwal yabawa baby, sai dai bata kai girman ta fadila ba

Momy tai masa godiya ta sakko lokacin maman Muwadda tazo suna daki ita da yar
tata suna shirye shiryen suna momy ta turo kofar tashigo

Nan suka gaisa da yar uwar tata ta bada sarkar da dady yabawa baby sukai godiya haka momy ta hado kayan barka wai ai takwarar ta ce dole taimata Muwadda ce tadago ta dubeta tace

 

“momy takwarar ki kuma, gaskiya sunan mama zaasamata ”

” Muwadda kiri kiri kike cewa sunan mahaifiyar ki zaasa miki, baki ji kunyata ba ”

” aa mama kijifa ingama shan wahalar sannan sunan ma sai anzaba min, gsky nide………..

“yi shirunki Muwadda, haba yaya kareema kibar yarinyar nan tazabi sunan da take so asawa yar nan mana ”

” shikenan aisha nabari asa mata wanda take so din Allah yaraya mana baby ”

 

” Ameen yaya ”

 

 

Farhana ce taje gaida hajiyar su ibraheem tana shiga tasami guri ta zauna tagaida ta taamsa a takaice can tanisa tace

” farhana naji abinda kikayi mungode madsllah to amma bari kiji daga yau kar ki sake kunna mana kallo a gidan nan, kuma kullum kar ki bari karatu ya wuce ki kidinga fitowa da zarar kingama aiki, ki zauna lpy da kannan ki kidena kallon su a matsayin *kannan mijinki* dafatan kin fahimce ni banason musami matsala da ke farhana ”

” wlh hajiya yanzun ma bani da laifi sune suka fara takalata musamman zainab tafi yimin wulakanci ”

Nide banason maimaita magana, ke bilkisu tashi ki rakata ta gaida malam”

Tashi sukayi suka fita zuwa bangarsnsa yana parlon sa da tulin littattafai a gabansa suka tsuguna suka gai dashi ya amsa da sakin fuska yadora da

 

“yata kina lpy dafatan dai ba matsala ”

” ba komai malam, andawo lpy ”

” Lpy kalau, anfada miki ana karatu da asuba ko?

“eh anfada min ”

” to madalla, Allah yai muku albarka ”

” Ameen ”

Tashi sukayi suka fita bilkisu yakira taamsa

” bilkisu ki turo min jaafar da malam karami ”

” to ”

 

Suna fitowa farhana tai bangaran ta su fatisa ne a parlon sun baje littattafai suna karatu parlon kaca kaca ga shi sun bude mata showglass dubansu tayi tace

 

” zainab ya kuka bar min showglass a bude ”

” eh kamshi muke ahaka ko munyi lefi ”

” oh tambaya ta kike to bansaniba ”

Dariya suka sa mata suka ci gaba da abinda suke shiru tai musu ta nufi kitchen ta dora girki, tagama ta zubawa kowa nasa ta dauke na ibraheem inbahaka jaafar da yagani zai dauka tayi magana ibraheem ya rufeta da fada

 

Karfe 8 ibraheem ya dawo gidan tayi wanka tacaba adonta cikin kananun kaya tayi kyau yana shigowa yai tozali da ita rungume ta yayi tare da sakar mata kiss

“mashaallah, matar ustaz kinyi kyau ”

” nagode ustaz dina, muje kayi wanka kazo kaci abinci ”

Daki suka shiga yayi wanka yasa jallabiya duk abinda sukayi akan idon su fatisa ne masari ce mai kwaikwayar farhana suka tuntsire da dariya

Parlon suka fito tazuba masa abinci yafara ci dubansa tayi tace

” ustaz jibi sunan aunty Muwadda dan Allah zanje ”

” aa farhana gaskiya ki hakura kinga bikin su jalila ya kusa sai kuje tare da su bilkisu ”

” Dan Allah ustaz ”

” dakata farhana banason magiya dan haka mubar zancan haka ”

Fitowar su fatisa ne yasa ta koma cikin dakinta tasa kuka sukuwa zaman su suka yi suka taba hirar su da yayan nasu

Ahankali ya tura kofar dakin yashiga tana xaune tana cin farfesun kajin da momy tai mata kan gadon yanufa yasa hannu ya dau babyn
Ahankali ya furta,

“uwata ta kaina, Allah yaraya ki ”

” sweery wane suna kenan “?

” wace irin tambaya ce wannan ”

” eh munyi magana da momy tace sunan mama na zaasa ”

” to ni banyarda ba ke yakamata ki sa mata suna ko ni, dan haka sunan momy zansa ”

Yana gama fada ya ajiye babyn yafita kai tsaye dakin momy ya nufa tana xaune ita da yaya hannatu suna tattaunawa kan taron sunan da zaai
yai Sallama ya shiga ya gaida su duban yayar tasu yayi yace

” yaya saukar yaushe?

“tun dazu nazo Assadiq ”

Momy ce tadubeshi tace

” Assadiq wane suna zaa sa wa babyn?

” momy nida sunanki zaa sawa yarinyar nan ”

” Hmmm Assadiq Muwadda taki wai sunan maman ta zaa sa mata”

“eh yanxuma haka tace ni dai nace aa ”

” aa bakomai asa mata ai dani da aisha abu daya ne bakomai ”

” amma momy…

 

“ya isa hannatu abar maganar haka ”

 

 

Assadiq rai bace ya koma gida safiyya na kitchen taji shigowar sa guri yasamu ya xauna ya nata kada kafa fitowa tayi tasameshi

” Dee lafiya kuwa?

” bakomai bani ruwan sanyi insha ”

Kawo masa tayi yasha ya kwanta bata matsa masa taci gaba da aikin ta sai da tagama ta shirya taje kaiwa Muwadda kayan barka fal tai ta godiya nan take fadamata sunan mama aka sa tai mata Allah yaraya ta dawo gida a parlon ta tatar da su shi da fadila suna cin abinci tasami guri ta zauna suka ci tare da kyar tasamu ya dena fushin da yake,

Ranar suna yarinya aka sa mata aisha afifa tace sai adinga ce mata humyra
Cikin yatsine fuska Muwadda tace

“aa bawani humyra *hamra*zaa kirata ”

Bayadda suka iya haka suka hakura ansha suna ankashe kudi safiyya kam a gidanta tayi nata taron da yanuwanta taro yatashi lpy dan Muwadda kin sakarwa su afifa tayi kawayanta ne akan komai

 

.muktar ne zaune a dakinsa Yana ta gwada layin Muwadda yaki shiga tsaki yaja ya cillar da wayar gashi rushida bata nan ballantana yaji labarin halin da Muwadda take ciki abokinsa ne yai Sallama ya shigo

“abokina lpy dai ko, kai da zanga ka kana murna budurwar ka ta haihu sai Inganka a hargitse ”

” nazifi meyasa wani lokacin kafiya soki burutsu ne wacece budurwa ta ”

” Muwadda mana ”

” karya kake nazifi ”

” wlh abokina ba wasa nake ba ”

” kut ashe kuwa akwai balai, amma shegiyar yarinyar nan bata fadan ba ”

” wa kenan “?

” rushida mana ai kuwa sai taci ubanta ”
Can kuma me ya tuna yasaki wani malalacin murmushi

 

*NASEEBA GAWO*

✍🏻
[6:21Am,2017]

 

*®💦💦����TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

*Alhmdulillah Alhmdulillah hakika Allah kaine abin godiya ayau muka shiga sabuwar shekarar musulunci alkhairin da yake cikin ta Allah kasada mu da shi sharrin da ke ciki Allah ka nisanta mu da ga shi Allah ka albarkaci rayuwar mu kacika kowa burinsa na alkhairi ka karemu daga sharrin mai sharri AMEEN*👏🏻

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wasallim*📿

 

*wannan shafin nakine sadnaf💅🏻 ina 💞tayaki murnar kammala novel din ki DAGA TAIMAKO🙆🏻 a gaskiya kin nishadantar kin waazantar Allah yakara basira yasa kifi haka naseeba💐 na biye da ke*

 

*87*

 

~~~sallamar rushida ce ta katsewa muktar tunanin da yake cikin sauri yafito daga dakinsa tare da yimata wani mugun kallo yadora

“ke, dan uwarki zo nan shegiya mai suffar munafukai ”

” aa haba yaya muktar me nai maka daga dawo wa ta ”

” uwarki kikaimin tunda tambayata ma kike, dama Muwadda ciki ne da ita har ta haihu, saboda ke manafuka ce baki taba fadamin ba ”

” Hmmm yaya muktar kenan to meye alakar ka da cikinta, tabbas nasani itace tace kar inbari kaji ”

” yayi kyau, to naji amma abinda nake so dake shine kar ki fada mata nasan ta haihu mutafi a bansaniba daga nan zuwa sanda burina zai cika ”

” yaya buri kuma, wani irin buri kenan “?

” to yar jarida ke de kiyi yadda nace, kema zaki shana wlh ”

Tohm shikenan yaya na, kuma fa munyi waya da ita bata fadan ta haihu ba”

“to ba munafuka bace, kibarni da ita zan koyamata hankali ”

” yaya muktar umma fa “?

” tafita aiki ”

” ok bari inshiga ciki in huta sai inje gidan nata ”

 

 

Muwadda sunyi arbain ansha fama dan kullum cikin rashin mutunci take momy kam ta kosa ta koma gidanta yau tun safe take shirin komawa gidanta Assadiq ne yai Sallama ya shigo

Guri yasamu ya xauna ya dubeta bayan ya dau hamra dubansa tayi tace

Papan hamra dama tun dazu kai nake jira ”

” ina jinki, ya kwanan baby ta ”

” afuwan ina kwana ”

” Hmmm lpy ”

” dama ina son zuwa gida ne in kwana 2 saboda arbain din da nayi ”

” aa ba kwana 2 zakiyi ba shekara biyu zakiyi, to ban yarda ba ki shirya in saukeki ki yini zuwa dare zanzo in dauke ku ”

” gaskiya sweery ni dai…..

“dakata muwadda nariga nagama magana inkin yarda ki shirya in baki yarda ba ki hakura ina parlo ina jiranki ”

Daukar hamra yayi ya fita parlon su faruq suna zaune suna break fast yasami guri ya zauna momy ce ta dube shi tace

” Assadiq Muwadda tace maka zata gida ta kwana 2 ko ”

” tafada min momy nace aa ”

” yauwa yaya kar ka barta wlh saboda shiririta kawai sai ta wani tafi gida ta kwana ”

” faruq me yashafeka da zakasa mana baki, ina ruwanka ”

” Allah ya baki hakuri momy na, sai na dawo ”

Yafada yana kokarin tashi bayan ya kurbi tea yaajiye kofin hannunsa yafita

Fitowar Muwadda ne yakatse musu zancan da sukeyi tacaba ado tayi kyau sosai tasami gefan Assadiq ta zauna momy ce ta dubeta tace

” Muwadda kin shiryo, saa takai miki break fast ko ”

” takai min amma banci ba in naje gida naci acan ”

” to ai shikenan, Allah ya kiyaye hanya ”

” aunty Muwadda pls inzo inraka ki ”

” bangyyace ki ba afifa dan haka kisha zamanki ”

Karbar hamra tayi a hannun Assadiq tai waje Sallama yaiwa momy ya rufa mata baya suka nufi gurin mota suka shiga yajasu suka tafi

 

Abangaran haisam kuwa burinsa ya cika yagama shirin sa tsaf yaje gidan su abokinsa yanemi alfarmar zaa kawo amaryar sa nan amatsayin su na iyayen sa suka amsa da bakomai ai shima dansu ne tunda abokin dansu ne

Shukura kam yau takai bango jiransa take ya dawo ya fita ysbarsu ba abincin kirki cikin ikon Allah sai gashi yashigo tana parlon su dan madaidaici

“Shukura uwar gidan haisam uwar gida ran gida ”

” banfahimce ka haisam baka taba yimin irin wannan kirarin ba ko meye hakan yake nufi ”

” to shikenan bazan kodaki ba sai yazama laifi, Allah to ya huci zuciyarki mata ta, kawo min abinci ”

” ba abinci zankawo maka kasuwar dawano zankawo ma ”

” to, yadabakar bagana kuma, me yayi xafi shukaran haisam ”

” kafini sani ai, tunda kasa kafa kafita baka sake bi takanmmu ba sai yanzu zaka kwaso yanmatan kafafunka kazo kace abinci ”

” shikenan ya isa tawan, yanzu bari infita indawo ”

” Kai kasani kuma ”

Fita yayi yanufi kasuwa acikin kudin bikin sa ya diba yaimata siyayyar kayan abinci yakaimata tai ta murna tadora musu girki suka ci dubanta yayi yace

” Shukura zanyi tafiya zuwa adamawa a kalla zanyi sati uku ”

” tare zamu tafi amma ko “?

” aa, kibari inje indawo tukunna ”

” shikenan haisam Allah yakaimu ”

” Ameen, ina su hafiz “?

” suna gidan mu ”

 

Safiyya ce kwance a jikin Assadiq suna hira cikin so da kauna can tadago
dakanta ta dubeshi bayan ta shafi sajen fuskar sa

” Dee kasan me?

“sai kin fada sopy ”

” wlh hankalina be kwanta da saurayin nan na afifa ba ”

” Hmmm, to ai ita taji tagani ko, dan haka sai akyale ta ”

Hayaniyar fadila suka jiyo tai saurin barin jikinsa rike ta yayi tsam ajikinsa dagowa tayi tace

” Dee bakaji fadila zata shigo ba sai tazo taganni a jikin ka ko ”

” and so what ”

” to badaniba, gaskiya ”
.
Da gudu ta shigo parlon tana xuwa ta fada kan Assadiq

” oyoyo papa, inata jiranka kazo ka daukeni a school baka zo, na dena kula ka ”

” ho, Fadilaty bakisan uzurin da ya rike ni ba, yanzu wa ya dakko ki ”

” uncle dina ”

” to bashi kenan ba, wuce kije kicire unifoam dinki ”

” Kai wlh ban iya ba mamma ”

” zo incire miki binty ”

” yauwa papa na gurin hamra zani aunty ta goya min ita”

“kide yar da ita, wa zai baki yarsa ”

Safiyya tafada tana kokarin tashi bayanta fadila tabi suka nufi daki

Abangaran farhana kuwa tun dare take fama da zazzabi da amai hankalin ibraheem ya tashi da sassafe suka shirya Suka nufi asibiti sai da tasa katon hijjab da nikaf sannan suka fita gwajin farko aka gano tana da ciki na wata 2 murna gurin ibraheem baa magana suka dawo gida suna zuwa ta kwanta be jimaba yai shirin fita kasuwa dubanta yayi yace

“farhana in kinji dadin jikinki ki dafa abinci kinga su fatisa sunkusa dawo wa daga makaranta ”

Da mamaki tadago ta zuba masa ido, tarasa ma me xatace masa shiru kawai taimasa yasa kai yafita

 

Yau aka kawo kayan lefan afifa kaya bana wasa ba akwati saiti 2 shake da kaya momy sai murna take afifa tayi goshi

Washe gari aka kawo na jalila saitin akwati daya kayanta masu kyau da tsada nan afifa tai ta dariya aka sa biki sati uku

Bangaran gidan su safiyya ma ankawo na yaya amina da angonta khalifa shirye shirye kawai ake

Muwadda ce zaune ita da Assadiq kiran muktar yashigo wayar ta Assadiq ne yadau wayar yana dubawa yaga sunan *muktar*

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[8:57Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*Allahumma la sahala illa ma jaaltuhu sahala waanta tajalu haznah iza shi itu sahala*👏🏻

 

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

*Ina taya kiyaya group murnar karuwa da muka samu na babies hauwa munir da suwaiba sale bala mai salla Allah yaraya mana kiyaya🎓 2009 munzama mamas😂Allah ka sauki mama aliya sani shehu mai hula lpy ameen*

 

 

 

*88*

 

~~~cikin tuhuma yake kallon ta dakewa tayi ta karbi wayar kan ta daga kiran ya katse cikin shakewar murya yace

“Muwadda waye muktar “?

” Oh yayan rushida ne fa, kuma nafada maka alakar mu tun tuni ”

” Muwadda yaakayi bansan su ba ne “?

” eh bazaka san su ba gsky, ba a garin nan suka fara zama ba ”

Shiru yaimata badan ya yarda da ita ba yagama shirinsa ya fita zuwa office

Yana fita ta kira layin muktar bugu biyu ya daga

” Hello baby kina son soyayyar ki ta kashe muktar ko ”

” Hmmm haba dear kana tuna nin zan iya rayuwa ba kai ne, kwana 2 ina tare da kewar ka banajin dadi ne shiyasa ”

” ayya I am so sorry baby, yanzu ya jikin naki ”

” Da sauki zaace ”

” baby ina tsoran fa ciki yashiga jikin ki fa ”

Mai da dubanta tayi ga hamra kana tace

” kar ka damu dear yanzu dai ya labari ”

” Hmmm bari ke dai baby wlh kasa ta rikici gari yaci wuta ”

” ayya ok, badamuwa zan bawa rushida ta kawo ma 200k amma dan Allah dear kafara mana tanadi kaji dan saura kiris burinmmu yacika ”

” baki da damuwa baby ke de kici gaba da zube kayan aiki, wata harka zan fara matsalar sai da kudi masu nauyi ne wlh ”

” Hmmm ba damuwa zan iya mallaka maka duk abinda na mallaka, yanzu zanyiwa abbana magana zai bani ko nawa nake so shima kuma Assadiq zan karba a hannun sa dan haka kar kaji komai ”

” Allah sarki baby shiyasa nake masifar son ki wlh nagode, sai na jiki ki kular min da kanki ”

” ok kai ma haka, ka gaida min da umma ta

” zataji baby na ”

Sukai Sallama ta kashe wayar tare da fargabar yadda zasu karke da muktar kukan da hamra take ne Yadawo da ita daga tunanin da take shikuwa zaginta yake tare da kulla muguwar aniyar sa

Biki yarage saura kwana 5 kowa yana ta shiri musamman safiyya wacce bikin yazamar mata gaba da baya haisam kuwa kullum sai yazo dan shirye shiryen bikin safiyya ce ta dau nauyin gyaran amare da su turaran wuta da humra Assadiq ysbasu kudi masu yawa dan hidimar biki Muwadda kam 20k taiya bawa momy shima sai da maman ta tai da gaske ragowar tabawa muktar da kudin da ta karba gurin abban ta

Momy kam sai shiri ake tana murna yanzu zatai biki dady dai yazuba mata ido amma shima hankalin sa be yarda da haisam ba yafi son auran jalila da *Dr*almustapha

Yaya hannatu ce tazo dan shirin tafiya kafi ita da kannan momy guda biyu sai kanwar dady sai Muwadda da Assadiq ya matsawa sai taje gidan jalila zaafara yi Washe gari ayi na afifa

Sunje gidan ta ma dai dai ci mai kyau da tsari kmr ganin turawa irin ganin tsakiya gefe kuma dan karamin lambu ne katon parlo sai bedromm guda 2 da toilet ga kitchen sai dining area nan suka yaba tsaruwar gidan sukai kafin su cikin kwanciyar hankali suna cikin kafin su safiyya suka zo kawo musu abinci da kayan da aka saba bayar wa na alada sukai wasa da dariya zuka tafi Muwadda kam sai kebe baki take ta raina gidan jalila

Dady yayi kokari anmusu kaya masu kyau da tsada

Tunda Suka koma momy take tambayar hannatu

“hannatu ya gidan jalila kuwa dan nasan ba abin arziki zasuyi ba musai kaya masu tsada karshe gidan bana arziki bane ”

” Gsky momy kidena haka wlh duk yar da tasa mi gidan jalila hakika ta caba ”

” aa aunty hannatu meye abin burgewa agidan jalila cab ”

” yauwa Muwadda ni nasan zaki fadan gsky ”

Wani banzan kallo yaya hannatu ta watsawa Muwadda ta taja tsaki ta mike ta yi kitchen

Sanda Muwadda ta koma gida su jalila suna gidan gurin safiyya ta shiga lokacin safiyya tana daki afifa ce ta dubeta tace

” aunty Muwadda kun dawo ya gidan amaryar”?

“Hmmm, su jalila dai anfado wlh duk girman kan yakare a dan wannan gidan ande ji kunya ”

” Alhmdulillah bandamu da gida ko yawan arziki ba farin ciki nake nema da kwanciyar hankali, inshaallah sai anyi koyi da irin *ZAMAN AURENA*”

 

Fitowar safiyya ne yaktse maganar da Muwadda zatayi da murna safiyya ta dauki hamra tana son yar itama yarinyar tafara ganeta

“Muwadda sannunku sai yanxu “?

” eh to, nadade gidan momy ne ”

” ok wlh nima kaina ke ciwo shiyasa na taho da wuri ”

” Allah sarki Allah yasa wake ”

” Ameen ”

Tashi tayi tafita afifa ta karbi hamra ta bita jalila kam waya ta dauka suka sha hira da angonta

Washe gari aka je gidan afifa katon gida mai azabar kyau nan fa yan kafi suka gigice haisam da ksnsa ya kawo musu abinci na restueant da katan katan na lemo da ruwa sukayi suka gama ba wanda yazo da sunan dangin ango

 

Farhana tun ana saura kwana 5 biki taketa shiri ibraheem nadaga tafiyar Saboda kannan sa suna exam kuma tare zasu sai yau ana gobe kamu sannan suka taho da bilkisu da fatisa sai masari tun agida yace tasa nikaf da katon hijjabi kuma kar tasake taje party mutukar da maza taamsa da to amma badan ta yarda ba driver ne yakaisu suma zasu taho ana gobe daurin aure yabata kudi mai yawa tayi biki tabawa momy kuma akan idon masari

 

Suna daukar hanya ta dubi farhana tac

“amarya ina kudin da yaya khalil ya baki ki bamu

 

“kmr yaya ban fahimce ki ba zainab

“fatisa bilki kunji mu da mata

“ai wlh sai kinbamu haka ake yi dan zamu garin ku biki sai kifara wulakanta mu”

Banza tai musu saboda yadda zuciyar ta ke tashi ahaka har suka gaji sukai shiru ita ma bacci ya dauketa

Sai yamma suka isa faruq yana bakin gate suka shigo yan mata ne guda uku suka fara Fitowa sai wata da katon hijjabi da nikaf tana ta doso inda yake zaune yarasa wacece da murna ta kira sunan sa

 

“yaya faruq ”

” naam baiwar Allah sannunku da zuwa ”

Daga nikaf din tayi tana dariya da mamaki yace

 

” Kai farhana, na you lallai matar malam ”

” su fatisa suka gaida shi ya amsa da sakin fuska ciki suka shiga nan farhana ta rungume momy dakin su tashiga su afifa na ganinta suka rungume juna suna murna

Su masari kuwa sai kebe baki suke momy da kanta takai su daki sukai wanka suka ci abinci

Farhana kam ana tare da yanuwa anata da labari sunata tsokanar ta mai ciki tana ta basu labarin *kannan mijinta* afifa ce tace

“Kai kuma kika barsu baki ci ubansu ba ”

” ke aure maisa mutum yai laushi afifa ai infada miki *ZAMAN AURE* sai a hankali ”

” jalila kuwa mamakin farhana ya hanata magana tashi tayi ta nufi saman dady suka gaisa yai mata ya jiki suka sha hira su zainab ma sunzo sun gaisa

 

Da daddare ta nufi gidan Assadiq suna kitchen shi da fadila wai alawar madara zai mata safiyya kam tana parlor tai musu banza fitowa yayi yana mata magana

 

“sopy dan Allah zo ki gani tayi ”

 

” Dee nifa ban iya ba, shiyasa nace kar ka biyewa fadila ”

” mamma na dan Allah ki koyawa Dee kinji ”

 

Dariya yarinyar tabasu Sallamar farhana ce ta katse musu dariyar da suke fadila na ganinta ta kwasa aguje tai daki

 

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[7:5Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

 

*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillah azim*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

💙
*Ina taya Fiddausi sodangi da zara Surbajo kammala novels din su dafatan munfadaku da abinda muka karanta ameen NASEEBA na biye da ku sisters*💙

 

 

*89*

 

 

Da mamaki safiyya ta karasa gurin farhana tajata zuwa kan kujera Assadiq ma karasawa yayi ya zauna suka gaisa da kulawa

“farhana saukar yaushe, ya mai gidan naki “?

” dazu yaya, lpys kalau yana gaida ka zasu zo sai ana gobe daurin aure ”

” ina amsawa yaron kirki kenan, Allah yakaimu, safiyya kawo mata abinci ”

” aa wlh yaya nakoshi, ya baby ina fadila banganta gidan momy ba ”

Sai lokacin suka kula ba fadila a parlon Assadiq ne ya dubi safiyya yace

” sopy duba kitchen ko bata fito ba ”

Dubawa tayi bata nan daki tanufa tana can kuryar gado karaswa safiyya tayi tace

” Fadila lpyr ki kika zo nan kika zauna ”

” wlh mamma ko, inajin tsoran aunty farhana ne fa ”

” Kai, fadila to mezata miki ta dena duka taso muje ku gaisa ”

Hannunta ta riko suka fita farhana naganin fadila ta rungume ta a jikin ta

” I miss u Fadilaty ”

Shiru tai mata sai daga baya ta gaida ta tare suka fita gurin Muwadda bayan ta dubi safiyya tace

” aunty zan dawo akwai hira may be anan zan kwana ma ”

” tohm shikenan farhana ina maraba da ke ”

Assadiq ne ya dubi safiyya yace

” sopy nagode da kulawar ki ga yanuwana Allah ya albarkaci rayuwar ki ”
” Ameen Dee ”

 

Kai tsaye farhana gurin Muwadda ta nufa tana parlor hamra sai kuka take suka shiga tana shiga ta dauki yar tafara rarrashinta Muwadda kam kallon ta kawai take yadda taga farhana ta canja tade yi kyau amma tayi sanyi sosai guri suka samu suka gaisa

” cab musulumatun farhana kece ”

” kinji ki to da wace, ke kam kifiya abin haushi wlh ”

Dariya tai tai mata karshe ko gaisuwar kirki basuyi ba ta tafi zata tafi da hamra ta karbi yarta

 

*********

Yau takama alhms yaune zaafara kamuun su jalila safiyya kam tun safe ta tafi gidan su anata shirin biki amare sunyi kyau sosai anyi kamu a gidan ya hannatu Washe gari diner tun safe haisam yadada jaddada dawa farhana kar tasake taje tanaji tana gani aka shirya aka tafi su fatisa ma sunje sai kawai tace bazata iya zuwa ba ba tajin dadi

Angwaye da amare sunyi kyau kayan su iri daya haisam yayi barin nera Dr almustapha kam sai tarai rayar jalila ya ke anci ansha su safiyya ma sunyi kyau cikin ankon su na lace faruq ma yazubar da kudi sosai haka Assadiq Muwadda kam tunda tabawa yaya hannatu hamra ta silale ta nufi gurin muktar har aka kusa tashi bata dawo ba ga yarinyar nata kuka ran Assadiq yabaci ankira wayar ta akashe haka akatashi haisam da afifa suka shiga wata lafiyayyar motarsa abokinsa yajasu suka tafi sai kissing dinta yake a mota ita kam ta narke sai zuba shagwaba take kiran shukura ne ya shigo dagawa yayi

“Hello, zankiraki “kawai yace ya kashe wayar yana dada shigewa jikin ta

Sanda Muwadda ta koma gurin dinner antashi kai tsaye gida ta wuce ta tatar da hamra nata bacci a gurin safiyya Assadiq na zaune a kujera ahankali ta shiga ko kallon ta be ba tasa hannu ta dauketa tare da yiwa safiyya Godiya satar kallon sa tayi taga ya hade rai yana tunanin matakin da zai dauka akanta

Washegari aka shurya aka tafi dinner din da haisam ya shirya jalila taje amma ba Dr su safiyya ma ranar sukayi ta yaya amina duk budirina daake banda farhana saboda *kannan mijinta* sunhanata sakat dabasu tazo da baabinda zai hanata zuwa dinner din daakeyi gashi su ibraheem sunzo har da su jaafar ibraheem ne yazo ya dauketa suka tafi mamakin su saboda yadda yayi kewar ta sai dare Yadawo da ita bayan sunsha soyayyar su

Washegari aka daura aure sdakin afifa 200k na jalila 50k akai yini da yamma aka fara shirin kai amare dady yai musu nasiha mai ratsa jiki aka debesu jalila taraka afifa gidanta mai balain girma da kyau sannan aka kai jalila sai da aka fara kaita gidan su safiyya lokacin antafi kai amina sannan aka kaita gidan ta mai kyau

Kowa ya watse aka bar amare a gidansu
Assadiq kuwa fushi yake sosai da Muwadda ko kulata baya yi washegarin gama biki ibraheem yace su farhana su shirya su tafi momy tace yabar ta takara hutawa da kyar yabar ta suka wuce dasu masari momy tai musu alhr haka ma dady

Amare anyi kwanan farin ciki kmr ko wacce amarya babu abinda babu a gidan afifa komai baja baja haisam da Kansa yaimata komai

Haka jalila hakika tayi dace da miji na gari ba karya a lamarinsa sai da taje gidan sa sannan ta fahimci lallai tayi saar miji

Kwanan farhana 5 sannan ta koma bayan tabawa safiyya labarin yanayin *ZAMAN AURANTA* tabata shawarwari tare da yimata alhr

Kwanan su jalila 5 akano suka wuce abuja bayan sunje gidan su da gidan su Dr ummi sai nan nan take da ita sunje gidan afifa ma

 

Abangaran afifa kuwa anata shan soyayya kullum tambayar haisam take yaushe zasu wuce england sai yace bayanzu ba

Yau da sassafe suna bacci taji wani mahaukacin bugu a firgice ta tashi taje bakin gate tana tambayar waye ”

” bude ki gani ”

Aranta take nanata kalmar bude ki gani, to waye wannan?

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[5:57Am, 2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W>F*💦

 

*KANNAN MIJINA*

👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wasallim*👏🏻

 

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

 

*90*

 

 

~~~haisam ne ya farka yaga bega afifa ba parlo yafito yana kiranta da muryar bacci yaji shiru sai yaji kmr tana kokarin bude kofar gate da sauri ya bude kofar parlon yafita ya kira sunnanta

“baby, lpy zaki bude kofa “?

” yauwa dear zo ka bude tun dazu ake bugu nagaza bude kofar ”

Daga murya yayi yatambayi,” waye “?

” KB ne ”

Hantar cikin sa ce ta kadada amma sai ya dake ya dubi afifa yace

” amm baby koma ciki inbude masa bana son dan iskan nan yagane min ke ”

” dear shi din waye to ”

Tai magana cikin shagwagaba kmr zatai kuka

” kar ki damu wani yaro nane a kasuwa, ki shiga ciki ki jirani zanzo in dora mana break ”

Ok, dear pls kar ka dade kaji”

Tana gama fada ta shige ciki sai da yaga shigar ta sannan ya bude kofar ido hudu sukai da kb sai cin magani yake dubansa yayi yafara magana

“KB, yaakayi ne dafatan lpy ”

” kut amma gsky ka raina min hankali tambaya ta ma kake lpy, ya mukayi da kai? kasa na debi kudin mutane na ranta ma har yanxu baka biya ba, kuma saboda rainin wayo ka wani tambayeni lpy”

“ho KB, to inbanda abinka yaushe akai daren bare gari ya waye ko sati fa baayi da auran nan ba kar ka damu zanbiyaka”

“wlh dana Sani ban dau kudin mutane nabaka ba, yanzu gashi kana kokarin Sani cikin matsala ”

” Haba KB xanbaka, nan da ranar assbar ma zanzo da kaina ”

” shikenan sai najika

Ya lallaba shi yatafi ya maida kofar ya rufe Hankalinsa yai masifar tashi musamman da yatuna mutanan da suke binsa bashi ahankali ya furta *AURAN BASHI* dai daita nutsuwar sa yayi ya koma ciki afifa tana kwance tana kallo be bari sun hada ido ba ya nufi kitchen binsa tayi ta rungume shi ta baya

“dear yatafi ”

” yatafi baby, wai sunji ni shiru banfito kasuwa ba, nace amarya ce ta rike ne ”

Dariya tayi ta taimaka masa suka hada break

 

Abangaran Muwadda kuwa tagaji da shariyar da Assadiq ke mata ya dena bata ko kwandalar sa ga muktar yamatsa mata kudi yake so shiryawa tayi ta nufi gidan su

Sanda taje maman ta tana kitchen ita da mai aikin ta sallma tayi kai tsaye kitchen din ta nufa dauke da hamra

“mama sannu da aiki ”

” aa Muwadda daga ina haka?

Tafada tana kokarin karbar hamra tanai mata wasa

“daga gida mama ”

” aunty ina yini ”

Ina gajiya saude”

Fita sukayi suka barwa saude aikin suka koma parlo suka zauna Muwadda ce ta dubi maman ta tace

“gsky mama nagaji da gidan nan wlh, yanxufa papan hamra kawata kwata baya kulani kuma ba abinda nai masa ”

” Hmmm, Muwadda ina zargin kishiyar ki fa ”

” aa mama bata da laifi wlh, kawai wulakanci ne itama momyn yanzu ba sona take ba ni dai wlh nagaji ”

” ta yaro kyau take bata karko, Muwadda ki nutsu ki bari musami cikar burinmmu mana ”

” Kai kai mama, nima fa ina da nawa burin fa ”

” ki adana naki kifara cika min nawa ”

Shiru tayi karshe ta kwallawa saude kira da sauri ta zo ta tsuguna

” gani aunty ”

” naganki saude, da Allah ki dau hamra ki goyata ki kular min da ‘ya fa ”

” to aunty ”

” mama bari inje indawo bazan dade ba, ina son ganin abba na ma ”

” ai kuwa baya gari ina kuma zaki Muwadda “?

” nai masa waya yanzu zandawo ”

Tasa kai tafita kai tsaye motar ta tanufa tashiga gurin da suka saba haduwa da muktar ta nufa yana nan yana jiranta tayi parking ta fito kusa dashi ta zauna

 

” dear yi hakuri kasha jira ”

” jira ai yakusa karewa baby yakamata ki rabu da mijin nan naki ki zo muyi auran mu ”

” kar kadamu dear saura kiris ni kaina nagaji da zama dashi ada ina masifar son Assadiq amma tunda na hadu da kai gabadaya naji bana son sa kai nake so muktar ”

” Hmmm nima ina sonki baby, sai dai muktar ba kudi ”

” kar kaka damu muktar zan tattare duk wata sarka tawa kai har da mota ta asiyar inbaka kudin kaja jari muktar ”

” wow, Allah baby ”

” kafi karfin haka dear ”

Ahankali motar tashigo gurin nacikin motar sai waige waige yake yana neman abokin sa dasukayi alkawarin haduwa a gurin karaf idanunsa ya sauka akan muwadda da muktar suna ta hira cikin mamaki Assadiq ya kuma kallon su sai dariya suke take yagane saurayin shine wanda yataba ganinsa da ita a asibiti Kansa ne yasara take ya juya yabar gurin sai waya yaiwa abokin nasa bazai sami damar zuwa ba yayi hakuri

Ko office be koma ba yanufi gida

Sukuwa basu ma kula da shi ba sai da suka sha hirar su sannan suka bar gurin da niyar zata kawo masa sarkokin ta da motar ta yasiyar

 

Sanda Assadiq yakoma gida safiyya ta dawo daga school kai tsaye bangaran sa ya nufa asaman gadonsa ya kwanta jin Shigowar mota ne safiyya yasa safiyya ta leka mamakin ganin Assadiq ya dawo a wannan lokacin ne yasa ta nufar dakinsa sanye take da doguwar riga purple ta material tasaki gashin kanta baya tayi kyau
Ahankali ta turo kofar parlon baya parlon daki ta nufa nan ta hango shi kwance akan gadon dafe da Kansa da sauri takarasa gabansa

“Dee, lafiyar ka, naga kadawo yanzu “?

” ummm”

Kawai yace mata ya juya ya kwanta shiru tayi tana nazarin sa lumhe idon sa yayi kmr mai bacci gjy tayi da zama tace

Dee, bari inje in dakko fadila a school ”

” sai kindawo dan Allah kar ki dade ”

Shiru taimasa bata ce komaiba ta fita tana fita yaji wasu hawaye masu xafi suna bin kuncin sa tunda ya auri muwdda be huta ba

 

Abangaran farhana kuwa cikin ta ya fito da kyar take iya yin aiki su fatisa basu fasa yimata rashin mutunci ba tun tana tanka musu har tadena yau tun safe tana kwance su suke aikin gidan ibraheem ya fita tana daki sai jin karar fashewar abu tayi tass suna ta dariya ahankali ta taso ta fito show glass dinta suka fasa gaba daya rasa me xatace tayi tabisu da kallo can tanisa tace

“Haba zainab garin yaya dan Allah kukai min haka?

“yi hakuri bamu kula ba ”

” ku makafi ne da zakice baku kulaba ”

” eh to wataran mukan taba makanta ”

Cewar fatisa tasaki taja ta koma ciki bata kuma fitowa ba sukuma basu share ba har ibraheem ya dawo ya tatar da gurin ahaka suna parlor ya tambayesu

” wa yafasa abun nan ”

” wlh ya khalil aunty farhana ce ta biyo fatisa zata mareta tafasa abinta da kanta ”

” akan me zata mareta ”

” haka kawai ”

Dakin ya nufa tana kwance sunnanta ya kira da karfi

” farhana me fatisa tai miki xaki mareta har kika fasa abinki kuma kika kasa kwashe wa ”

” haka suka ce maka to shikenan suje dan kansu tajuya taci gaba da kwciyar ta sai kuma hawaye fita yayi ya gyara gurin sai kuma tausayin matar tasa yakamashi

Jalila kam bata da wata matsala da mijinta kullum suna faranta ran junansu duk sati sai yakira dady sun gaisa ga aiken abin arziki da yake wa momy ita abun ma mamaki yake bata wani lokacin ma jalila bata san yayi ba yasa momata islamiyya tana xuwa kafin afara admission ta dawo kano tafara B u k yanzu haka fita zaiyi zuwa aiki sai shagwaba take yana ta yimata dariya

 

“Haba matar doctor bazan dade ba zandawo kinji bana son inganki cikin damuwa ”

” *Doktar* nide bana son yanmatan abuja su kalle min miji wlh ”

” to yanzu bani nikaf insaka shikenan ”

Dariya sukayi ya sakar mata kiss yafita ciki takoma tana murmushi hade da gode wa Allah

Muwadda tahada komai takaiwa muktar ya karba harda motar ta faruq ne yaxo wuce wa yaganta itama shi take kallo take tsoro ya kamata dauke Kansa yayi muktar kuma yimata Sallama da niyar zasu yi waya

Kai tsaye faruq gidan Assadiq ya nufa dan sanar da shi abinda yagani

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[6:00Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*Alhmdulillah ala kulli halin*👏🏻

 

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

*💦Dedicated 2 kannan mijina group*💦

 

 

 

 

*91*

 

 

~~~sanda faruq yaje gidan Assadiq baya nan sai safiyya ya tarar tana koyawa fadila home work tana ganinsa ta taso a guje ta rungume shi

“uncle oyoyo, yaushe xaki kaini gidan su yaya nabil ”

” can kike son zuwa ”

” eh wlh ”

” to zankai ki amma kwana zakiyi ”

” Kai kai, mamma kinji wai kwana zanyi gsky aa ”

” ai kuwa sai kin kwana, faruq ya aiki “?

” wlh angode ma Allah aunty, yaya Assadiq fa ”

” yana gidan momy, tun dazu ”

Fita yayi ya nufi gidan su Muwadda kam hankalin ta yagama tashi da yadda faruq yaganta da muktar tana dakin ta tayi shiru amma wani bangaran na zuciyar ta farin ciki take Allah yasa yazama silar rabuwar ta da Assadiq kenan

 

Assadiq yana zaune gaban momy yana fada mata abinda muwadda take yi, faruq yashigo guri yasamu ya xauna bayan ya mikawa yayan nasa hannu sun gaisa

“yaya ashe kana nan naje gidan ka banganka ba ”

 

” ina nan faruq Allah yasa lpy?

“eh to, lpy ba lpy ba ”

Nan yabashi labarin abinda yagani ransa Yakuma baci

Momy ce tanisa tace

” wai wacce irin yarinyar ce wannan, wlh fitinar Muwadda ta isheni fa ”

Waya ta dauka tashiga neman layin ta sai da ta Kusa tsinkewa sannan ta dauka

” Muwadda inkina gida kizo ina son ganin ki ”

” gani nan ”

Sai da ta jima sannan ta shigo guri tasamu ta zauna sai harare harare take momy ce ta dubeta tace

” ke Muwadda waye yaron da aka ganki da shi ”

” wane yaron fa momy “?

” bansaniba tambatayata ma kike ”

Assadiq ne yadago ya kalleta bayan ya watsa mata wani kallo

” ke bama son raini waye muktar “?

” aa haba papan hamra so nawa zanfada maka matsayin muktar a gurina ”

” ke yazaki rainawa mutane hankali ne da wa naganki dazu ko bake bace ”

 

” to kai kuma meye naka malam ina ruwanka kabari muyi magana da mijina ”

” Gsky nifa momy nagaji wlh shi kenan badama kayi muaamula da mutum sai ace dan me akan me?

“Muwadda momyn kike fadawa haka saboda baki da mutunci ko, to wlh zan dau mummuna mataki akan ki ”

” Hmm yaya Assadiq kenan kwantar da hankalin ka kafin ka dau mataki ni zan dauka da kaina ina dalili, yau zanfada maka waye muktar

Hakika muktar shine wanda nake so shi ne burin raina dashi nake son yin *ZAMAN AURE* wani wawan mari Assadiq ya dauketa da shi

Nan tazube tafara gunjin kuka, tana zage zage tayi waje momy kam zubewa tayi numfashin ta na sama sama gaba daya su faruq kanta suka nufa sunai mata sannu ina bata ma san suna yi ba daukar ta sukayi sai asibiti

 

Muwadda kam tana fita bangaran ta ta nufa ta hada kayan ta tsaf dana hamra tayi part din safiyya lokacin tana daki tashiga sallamar ta tajiyo ta fito tana xuwa taganta tana kuka

“aa Muwadda lpy me ke faruwa “?

” aunty safiyya wlh yau angama zaman gidan nan, dan haka ga hamra nakawo miki ita ki kula da ita nasan bazaki cutar da ita ba ”

” Muwadda kina da hankali kuwa yarinyar ki karama baki fa yaye ta ba ”

” eh nasani nariga angama yanke hukunci wlh abinda zani da ‘yar Assadiq ”

Tana gama fada tai gaba tabar safiyya da sakin baki cikin dakin ta takoma ta kwantar da hamra kusa da fadila ta zubawa yaran ido kamar su daya

Wayar ta ta dauka tashiga neman layin Assadiq tanata ringing be dauka ba gajiya tayi ta ajiye wayar

Su Assadiq suna asibiti momy tana jin jiki dan jininta ya hau sosai hankalin su yagama tashi sun yiwa dady waya ya taho

 

Muwadda kam tana xuwa parlon gidan su tasaki ihu tana kuka cikin tashin hankali mama ta tareta

“subahanallah, Muwadda lpy me yafaru ina hamra “.

” nashiga uku mama Assadiq yaimin sharri wai bin maza nake shine yai min duka ya kwace yarsa yabawa matarsa, nashiga uku ”

” cab dijan, lallai akwai dan karamin yaki wlh bari abban ki Yadawo

 

Abangaran afifa kuwa yau tun safe gas dinta ya kare haisam ya dauka zaiyo repilling tagaji da jiransa ga yunwa store tashiga dan dakko lemo mezata gani ba komai a ciki sai buhun shinkafar da suka farka sai taliya komai dai sai wanda suka fara amfani da su ne kawai mamaki ne yakama ta wayar ta ta dauka zata kira shi ba kudi please call me tayi masa yana gani yaki kira dan yana tare da shukura suna break fast wai dawowar sa kenan daga adamawa yan yaransu na gefensa

Gajiya afifa tayi da jiransa tasa kuka gidan ta rufe ta nufi gidan su ba kowa gidan Assadiq ta shiga ta tarar da safiyya nabawa hamra madara guri tasamu ta zauna da mamaki safiyya ta dubeta

“afifa lafiyar ki ina haisam din “?

” tun safe yafita be dawo ba shine hankalina ya tashi gashi nazo gida ba kowa ina momy “?

Kiran Assadiq ne ya shigo wayar ta da sauri tadaga

” sopy kar ki ji ni shiru muna asibiti momy ce ba lpy ”

” subahanallah meyasameta Dee, wai ma meke faruwa ne “?

” pls ki jirani indawo gidan tukunna ”

Kukan hamra yaji yatambayi safiyya

” sopy yanake jin Kukan hamra “?

” itace Dee ”

Shiru yayi ya kashe wayar afifa ce ta tambayeta meke faruwa gaya mata tayi sai tasa kuka safiyya ce tai ta rarrashinta ta shiga kitchen ta dakko mata abinci nan tashiga ci sai da ta cinye tas sannan ta karbi wayar safiyya ta kira haisam tafada masa tana gidansu Hankalinsa ne yatashi ba shiri ya biyota

 

Su jalila sun zo kano hutu sai da suka huta sannan suka nufi gidan su safiyya su gaida su baffa ya rukayya ma tazo haka amarya amina sukai Sallama suka shiga suhyla tana ganin jalila ta rungume ta tana murna suka gaisa da su cikin mutunci ummi kuwa tarasa inda zata sa jalila dan farin ciki suka shiga suka gaisa da baffa yasa musu albarka nan yatafi ya barta ta wuni najiba kuwa sai hira take mata sai dare yazo ya dauketa suka tafi tabawa ummi kudi najiba kuwa turaruruka ta bata

Cikin dare farhana na jikin ibraheem taji wani irin ciwon mara da baya agigice tafarka tasamasa kuka kukanta yaji ya tashi ganinta yayi tana juyi ba shiri yaje ya fadawa hajiyar sa cikin sauri ta taso kan suzo ta galabaita suka dauketa suka kaita asibiti su fatisa sai dariya suke mata zata haifi bakwaini.

Farhana kam tasha wahala abin mamaki kuwa bakwaini ta haifa na miji nan aka kaishi nursery ita kuma aka kaita dakin hutu

 

 

*NASEEBA GAWO*

✍🏻
[9:16Pm, 2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

 

 

*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillah azim*👏🏻

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦

 

 

*kawata faeeexa usman ina kika shiga ne kwana 2 bana jin ki dafatan dai lpy kike* 👌🏻

 

 

*92*

 

~~~zaman asibiti ne yakama farhana yayar ibraheem ce tazo daga katsina take zaune da ita gida ya koma nasu masari ibraheem da Kansa yaiwa Assadiq waya yafada masa haihuwar yai murna nan yake fada masa rashin lpyr momy yace kar ya fadawa farhana

Ankwantar da momy saboda yadda jininta ya hau yaya hannatu ce tazo hankalin ta ne yatashi yadda taga yadda momy take shan jiki Assadiq ne yajata gefe yabata labarin abinda muwadda tayi dubansa tayi tace

“Hmmm nasan a rina wai ansaci zanin mahaukaciya, to yanzu wane mataki ka dauka kenan ”

” ai yaya ina ganin yazama dole inrabu da muwadda atsarin rayuwata babu sakin mace saboda illar dake cikin hakan ”

” to yazakai gwanda kasaketa taje tayi *ZAMAN AURE* da wanda take so mara mutunci kawai, kuma wlh bazaka bata hamra ba ”

” aa yaya bazan raba ta da yarta ba ”

” Assadiq kenan, Allah ya kyauta kawai ”

” Ameen, bari inje in dawo

” ok badamuwa sai kadawo ”

 

Fita yayi ita kuma ta koma ciki faruq yayi tagumi yana kallon momyn tana ta bacci saboda allurar daakai mata

Sanda Assadiq yakarasa gidan sa su afifa sun fito ita da haisam zasu tafi asibiti duba momy da sauri ta karasa gurin sa

” yaya Assadiq ya jikin momyn “?

” da sauki afifa yaushe kika zo?

“dazu ”

Haisam ne yabashi hannu suka gaisa yai masa ya mai jiki tare da tambayar sa number dakin da aka kwantar da momy yafada masa Sallama sukayi suka tafi ciki yakarasa hamra na bayan safiyya tayi bacci sai fadila kwance a kujera tana kallo ya shiga da gudu fadila tazo ta rungume shi

“oyoyo papa”

“Fadilaty kina lpy, ya school ”

” Lpy lau, papa naje gurin aunty bata nan ta tafi ta bar hamra na taiwa mamma na kuka, dan Allah papa akaita gurin ta ”

Shiru yayi ya maida dubansa ga safiyya wacce ta zubawa fuskar mijin nata ido yadan fada fuskar sa ba wal wala can yanisa yace

” sopy muwadda fa “?

” Dee wai me ke faruwa ne?

“tambayar ki nayi ko, ina muwadda?

“Bata nan tazo tana kuka ta kawo min hamra wai inkula da ita, tabar min ”

” Good haka tace, ba laifi sopy ga hamra nan ni Assadiq nabaki ita ki zame mata uwa halak malak”

Yana gama fada yasaki hannun fadila ya nufin dakin sa

Kanta ne ya daure tabishi dakin yana zaune gefan gado dafe da Kansa kusa da shi tasamu ta zauna ahankali ta kira sunan sa

“Dee dan Allah kasanar dani abinda yake faruwa ”

Dago da Kansa yayi ya dubeta idon sa yakada yai jazur

Labarin abinda yafaru yayi, hankalin ta ya tashi kuka tasa masa cikin shash shekar kuka tafara magana

” Dee dan Allah kayi hakuri kar ka saki Muwadda kar ka raba uwa da yarta ”

” Dakata safiyya, inbazaki rike min yarinyar nan ba insani karfa ki manta inada masu rike min ita amma banfada miki maganar nan ba dan ki sa bakin ki ciki ba aa nafada miki ne kawai dan kin isa infada miki kin gane ko, dan haka abar zancan, kitashi ki dafawa momy abinci kar ki sa gishiri ”

” shikenan Dee, nagode ubangiji Allah yataya ni riko, ya jikin momy ”

” da sauki inkingama kishirya muje ki duba ta ”

” to ”

Fita tayi ta nufi kitchen ta dora fatan wake da farfesun hanta ta kammala ta soya wainar kwai ruwan dumi ya hada yaiwa yaran wanka itama ta shiga tayi tafito wasu riga da wando tasawa yaran iri daya purple da fari sunyi kyau hamra sai kallon Assadiq take tana daga hannu ya dauketa fadila ce tace

“papa, ko de anbarwa mamma na hamra ”

” Kai Fadilaty, anbar mata, shikenan hankalin ki ya kwanta

sopy kiyi sauri ki shirya bari inje in sa kaya ”

” tohm ”

Be jima ba ya fito suka dau abincin momy a kuloli masu kyau suka shiga mota suka tafi ahanya yake fada mata haihuwar farhana

” mashaallah, Allah yaraya yabata lpy amma Dee waye zai zauna da ita “.

” aa wa kuwa zai zauna da ita wannan wace irin magana kike ”

Yafada yana gyara mudubin gaban motar sa

” eh gaskiya gwanda atura yar dattijuwa ta zauna da ita ko adawo da ita gida ”

” Hmmm sopy kenan, shikenan zaa samo wacce zata ”

 

Karasawa yayi cikin asibitin yayi parking din motar sa suka fito daukar hamra yayi safiyya kuma ta dauki kwandon kuloli fadila na gaba da faruq suka hadu yana ganinsu ya dauki fadila tare da sakar mata kiss ya gaida safiyya dakin da momy take suka shiga tana xaune yaya hannatu na da afifa na gefenta safiyya ce takarasa gaban gadon tai mata sannu

“momy ya jiki ”

” Da sauki safiyya, nagode kinji Allah yai miki albarka ”

Kallon kallo aka shiga Assadiq kuwa mamaki ne yakama shi aransa yake fadin

*_ikon Allah momy ce ke sawa safiyya albarka lallai mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romansa_*

 

Momy ce taka tse masa zancan zucin da yake ta hanyar maganar da take masa

“Assadiq wane mataki ka dauka akan shedaniyar yarinyar nan, kuma ya naga hamra atare daku ”

” momy hukunci yana hannun ki tunda dama ke kika aura min ita ”

” Gsky ne Assadiq, to sakin ta zakai yau din nan ba sai gobe ba ”

 

” kar ki soma hjy kareema akan wane dalili zakice yasaki matar sa to ni nace aa ”

 

Gaba dayansu suka juya dan ganin me magana dady ne

Fadila ce taje ta rungume shi karaso wa yayi ciki gaba dayan su suka tsuguna suka gai da shi yaamsa momy ce tace

” Haba alhj basu fada maka abinda yarinyar nan tayi bane ”

” basu fadan ba, yanxu ke bata lafiyar ki ake ba, dan haka abar duk wata magana sai anje gida ”

Jalila ce tashigo ita da Dr almustapha kai tsaye gurin momy ta nufa hannun ta takama tashiga yimata sannu

 

Dr almustapha ne ya tsuguna ya gaida dady yabawa su Assadiq hannu suka gaisa karasawa yayi yaiwa momy sannu da jiki taamsa a mutunce

Haisam kam yana waje cikin mota yakira afifa a waya tazo

Shiga tayi tasame shi duban ta yayi yace

“baby abinda yakamata ayi shine ki zauna ki kwana da momy ”

” aa dear yaya hannatu ce fa zata kwana tare da ita ”

” eh duk da haka kema ki kwana ”

Badan taso ba taamsa da to Sallama yayi mata yatafi sai bayan ya tafi ta tuna ba kudi a hannun ta ciki ta koma lokacin su jalila na shirn tafiya da kyar dady yabarta ta kwana su safiyya ma suka tafi sai lokacin momy ta iya cin abincin safiyya

 

Haisam na zuwa gida ya kwashe kayan lefan afifa ya kulle gidan ya nufi gidan shukura tunda yau girkinta ne

 

Assadiq ne kwance yayi rub da ciki safiyya ta shigo sanye da rigar bacci fara kal gefansa tasamu ta kwanta mirginowa yayi ya jata jikinsa hade da sakarwa wuyanta kiss ahankali yafara jan rigar tata bireziyar ta yacire mata ya wurgar ahankali yace

Bana hanaki kwana da wannan abar ba ”

Cikin shagwaba tafara magana

” Dee, nide gsky kamayar min da abata

 

“to ai banaki bane abun dan haka abar min su haka ”

Kan tabashi amsa ya hade bakinsa ta nata

 

Tun da Muwadda ta je gida take kiran layin muktar akashe shiru tayi tashiga tuna nin lpy ya kashe wayar sa

 

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[9:07Pm,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

*Assatagafirillah waatubu ilehi Assatagafirillah azim*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦

 

 

*masoyan KANNAN MIJINA ina gaida ku kyauta dan Allah masu son kannan mijina daga farko kuyi hakuri na kusa gamawa document yana nan tafe*👌🏻

 

 

*93*

 

~~~gajiya tayi da neman layin wayar muktar taajiye wayar, muktar kuwa sai da yagama hade kan kudin muwadda sannan ya kunna wayar sa layin wayar ta yakira
Bugu biyu tadauka

“Hello baby ya kike kinji ni shiru ko ”

” Hmmm, wlh sweery hankakina har ya tashi, Allah yasa lpy ”

” wlh baby, ina can ina fafutikar hada kuda dan nan ni de kiyi kokari ya sakeki musamu mucika burin mu ”

” baka da damuwa sweery ai wlh bazan koma ba nifa da kai kadai zan iya *ZAMAN AURE*”

“to shikenan baby sai najiki, to ina kika bar babyn taki “?

Diriri cewa tayi cikin rawar baki tace

” Dear baby kuma, wacce kenan ban fahimce ka ba ”

” oh, rushida tace min anbaki yar kishiyar ki ko ”

” Hmmm, dear kana tunanin zan dauki yar wani bayan naki haihuwa ”

” gsky ne kuma baby, to shikenan dai sai kinji ni, zankira ki anjima ”

” ok dear, love u ”

” love u too ”

Sallama sukayi ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta tana tunanin hamra ahankali aka turo kofar dakin aka shigo saude ce ta tsuguna tace

” aunty abba na kiranki ”

” naji jeki gani nan zuwa ”

hijjabinta tasa tafita yana zaune a parlor mama na gefansa tayi Sallama tashiga guri tasamu ta zauna dubanta yayi yace

” muwadda meyafaru kuma ina hamra?

“Dady nagaji assadiq kashe ni zaiyi wlh ga sharri da yaimin wai bin maza nake”

Tana gama fadar haka ta rushe da kuka ransa ne yabaci mama zatai magana ya daga mata hannu wayar sa ya dakko ya shiga neman layin assadiq

Kwanan momy 2 aka sallamota su assadiq suna tare da ita sun zagayeta fadila na gefanta Dady ma ya shigo dakin dubata wayar assadiq ce tafara ringing dakko wa yayi yaduba abban muwadda ya gani ajikin screen dauka yayi

“salamu alaikum, abba barka da yamma ”

” dakata malam ka bude kunanka da kyau ka saurareni, ka kawo min takardar sakin muwadda nabaka nan da awa daya ”

Yana gama fada ya kashe wayar mai da dubansa yayi ga su dady su dinma shi suke kalla nan yabasu labarin yadda sukayi da abban muwadda faruq ne yazaro biro da takarda yamikawa assadiq

” bross dont wait, pls divorce her ”

” to dama me xai jira faruq ai wlh sai ya saketa ”

” hannatu meyasa haka ne eye, ku zaku yanke hukunci ko me”

“dady kayi hakuri ”

” sadauki wane laifi matarka ta aikata ma ka ina son jin me yahada ka da ita ”

Momy ce ta kwashe komai tafada masa shiru yayi can ya nisa yace

” sadauki tashi muje gidan su matarka bana son zancan banza akan me zai saki matar sa ”

” amma alhj……..

“Hajiya kareema dakata du Allah ”

Fita yayi assadiq ya bi baysnsa fadila ce tai zunbur ta mike tace

” papa zanbika dan Allah katafi dani ”

Dawowa yayi ya tsuguna agabanta tare da hada hannunsa danata yace

” binty ki zauna da su umman nabil ga uncle dinki nan zai kaiki shop rite kinji ”

” papa amma har da hamra ko ”

” har da ita mana fadilaty ”

” to shikenan, sai ka dawo papa ”

Kissing dinta yayi ya fita gurin faruq ta koma ta zauna sunan sa ta kira

” uncle, kaji abinda papa na yace ko ”

” naji fine girl dole inkai ki ”

Momy ce ta dubi yaya hannatu tace

” hannatu kiramin farhana awaya inji lafiyar su ”

” to, momy, wai wa zai je ya zauna da ita ne, nide wlh zanje da kaina in dakko ta ”

” kafin kije dakko ta, ki fara kiramin ita nide ”

Wayar ta ta dauka ta kira layin farhana bugu biyu ta dauka

Suka gaisa da yaya hannatu tai mata ya jiki tare da tambayar lafiyar baby mikawa momy wayar tayi

” Hello, farhana ya jiki ya baby dafatan ba wata matsala ko ”

Farhana najin muryar momy tasa kuka kwantar mata da hankali ta shiga yi da kyar tayi shiru

” haba farhana kar ki damu zamu zo kinji kuma gobe maijidda zata zo, ta zauna da ke ”

” shikenan momy nagode agaida dady

Sukai Sallama takashe wayar tattaunawa Suka ci gaba da yi akan farhana

 

Sanda su assadiq Suka je gidan su muwadda abban ta na sitt room Sallama sukayi Suka shiga Suka gaisa dady ne yafara magana

“alhj, banji dadin abinda yafaru ba ko kadan amma du Allah ayi hakuri adawo da yarinya dakin ta ”

” au alhj muhammad ba takardar muwadda kuka kawo min ba, to ni kam yata tagama zama da yaron nan tunda be duba *zumunci* ba ”

Dady yakada yaraya amma abban muwadda ya kafe sai ansaketa ran assadiq ne yabaci yafurta

Abban ni assadiq na saki muwadda saki daya”

“ba da baki nake son ji ba ga biro da takarda rubuta ga bani ”

Karba yayi ya rubuta yana gamawa ya mike yafita

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[12:11pm, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*Allahumma inna nasalika afiyan walafiyati fidduniya walakhairati AMEEN*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin*💦

 

 

*alhmdulillah kamar yau ne kanwata ta tafi tabarni cikin ikon Allah gashi ta dawo umymaty ukuty inai miki sannu da zuwa dafatan kindawo lpy Allah yakarbi ibada sis WELCOME BACK SWEERY*💃🏻💃🏻💃🏻

 

*94*

 

 

~~~Ran dady ne yabaci hannu ya mikawa abban muwadda suka gaisa ya fita a cikin mota ya tarar da assadiq ya kifa kansa a sitiyarin a mota be ce masa kala ba assadiq yaja motar suka tafi

 

Safiyya tana zaune a parlo tana bawa hamra firiso cream assadiq ya shigo kan 3siter yasamu ya kwanta dafe da kansa mikewa tayi tadawo kusa da shi bayan taajiye hamra ahankali ta kira sunan sa

“Dee me yasameka dafatan ba ciwon kan nan bane”

Dan karamin tsaki yaja bayan ya bude idonsa ya dora su akanta take yafara samun saukin damuwar sa ahankali yadubeta yace

“sopy kaina kamar yafashe haka nake ji pls kawo min liptone kadan ”

Mika masa hamra tayi ta nufi kitchen ta dafa masa liptone ta kawo masa tashi yayi ya karba yafara sha yana bawa hamra Safiyya kam ta zuba masu ido dago da kansa yayi ya kalleta yasakar mata murmushi itama murmushin ta mayar sa

” sopy, ina fidilaty?

“tana gidan momy, yauwa Dee muwadda shiru dan Allah kaje kadawo da ita

“Safiyya Safiyya Safiyya! sau nawa na kira sunan ki ”

” sau uku Dee ”

” Good kar ki sake yimin maganar muwadda bana so kinji dai nafada miki ko ”

” naji, kayi hakuri bazan sake ba inshallah ”

” tashi ki hada min ruwan wanka ”

Tashi tayi tashiga bedroom ta nufi toolet ta tara masa ruwan wanka

 

Afifa ce zaune tana kallo haisam ya fita sai jin bugu tayi tashi tayi tanufi bakin gate din tambaya tafara yi

” waye ne?

“bude kigani mana ”

” kai kamar yaya, bangane ba ”

” zaki gane ne to kb ne, yana nan ne “?

” bansaniba, banza kaje ka koyi yadda ake tambaya sakarai kawai ”

” kut ni kike fadawa haka wlh zaki sani aikin banza auran naki da akayi da kudin bashi banzar mace kawai ”

Shiru taimasa yai ta zage zage amma hankalinta yagama tashi tana mamakin lamarin haisam yafara bata tsoro ciki ta koma ta dau wayar ta tafara kiran layin haisam tana ta ringing be dauka ba

Ajiye wayar tayi tanufi bedroom dinta akwatinta ta jawo tafara budewa abin mamaki ba rabin kayanta duk ankwawhe tambayar kanta tashiga yi ina kayanta shiru tayi tafara tunanin meke shirin faruwa da ita ne wayar tace tafara ringing mika hannu tayi ta dakko akan bed side sunan jalila ta gani da sauri ta daga wayar

“Hello, yaya jalila ”

” Afifa gani a kofar gida zo ki bude min”

Zabura tayi tafita zuwa bude mata tana ganin ta ta rungumeta tana murna ciki suka shiga suka sami guri suka zauna kallon Afifa kawai jalila take murmushi afifa tayi tace

“yaya jalila lpy naga kina kallo na ”

” Hmm afifa, lafiyar ki kuwa kamar fa baki da nutsuwa”

Kuka tasaka mata sai da tayi mai isar ta sannan tayi shiru ta dora da

“yaya jalila, wlh nafara tsorata da halin haisam gaba daya yacanja duk bayan kwana 2 sai yace yayi tafiya ga shi dazu wani yaro yazo wai auran bashi haisam yayi nifa nafara jin tsoro gashi ya dena bani kudi

“haba Afifa me kike son fada min ki nutsu haba may be yana can yanai muku shirin tafiya england ”

” kai yaya jalila anya kuwa ”

” kinga tashi ki dora mana girki ”

” cab wlh bani da gas ”

” to yazaai kenan afifa, amma bari naiwa Doktar waya ya turo min wanda yake zuwa yakai aimin refiling ”

” yauwa dan wlh haisam bazai kai ba wai risho fa zai siyo min, yauwa yaushe zamuje gidan farhana ”

” eh ni wajen jibi da nake son muje ko ”

” to Allah ya kai mu ”

Yaron ne yazo yadau gas din afifa akai refiling aka kawo ta dora girki suka ci suka sha hira da yamma Dr almustapha yazo ya dauke ta yabawa afifa 10k tai ta murna suka tafi

 

Momy tana kwance fadila tana matsa mata kafa tadago ta dubeta tace

” *kakus* kinsan me?

“aa fadila sai kin fada ”

” aunty fa tabar mana hamra, mamana ce take mata wanka ”

Kan tabata amsa Safiyya ta shigo sallama tayi tasami guri ta zauna ta gaida momy taamsa cikin sakin fuska dubanta tayi tace

” Safiyya sannu da kokari kinji Allah yai miki albarka yabaki ikon rike hamra da amana kuma ina baki hakurin qbubuwan da suka faru abaya kinji ”

” ameen momy nagode bakomai ”

Yanzu zansa akawo miki mai aiki ta taimaka miki da rainon hamra ko tunda kina zuwa makaranta”

“to shikenan momy nagode, ga faten wake ”

” yauwa yata nakuwa gode fadila dakko plate azuba mana ko”

“yauwa momy wa zai je ya zauna da farhana ”

” antura maman su ta tafi tun jiya amma su jalila ma zasu ”

” ok thom shikenan momy ”

Nan suka zauna suna taba hira Safiyya dai mamaki ne yakamata yadda momy take mata

 

Muktar kam yahade kan dukiyar muwadda ya bar garin text yaimata ya tura mata tana zaune tana cin abinci amma hankalinta yana garin Muktar da yarta hamra wayar ta tai kara alamar shigowar text

 

 

 

*NASEEBA GAWO*

✍🏻
[6:14Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T<W>F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

*1st october*🇳🇬
*alhmdulillah 2 day it is wonderful day the day that nigeria get her independed oh freedom freedom oh freedom freedom every where*💃🏻💃🏻

 

*💙sakon gaisuwa gareki aunty na fauziya D suleman naseeba na gaidaki kyauta ina rokon allah ubangiji ya hada fuskokin mmu AMEEN*💙

 

*95*

 

~~~cikin sauri muwadda ta duba screen din wayar ta murmushi tasaki dataga sunanan *sweet muktar*barobaro duba sakon tafara yi kamar haka

 

_amincin allah agareki sahiba agurin mukatar abdullah ina mai baki hakuri bisa ga sakon dana turo miki bason raina ba kenan son zuciya tane yazama dole inbata abinda ranta ke so kamar yadda kika bawa taki abinda take so muwadda ko ince maman hamra haka ne, mukatar yai miki nisa nisa na her abada ko ince gaba da abada, kash inama zaniya auranki wlh dana aura sai dai bazan iya auran second hand ba amma inai miki fatan alkhairi ki koma gurin baban yarki hamra kinemi yafiyar sa kinji nagode naki ada mukatar abdullah_

Wani gumi ne yadinga ketowa muwadda take tasaki razananniyar kara wacce ta gigita mama tafito da sauri ganin muwadda tayi tana gurshekan kuka tambayar tashiga yi

“muwadda lafiyar ki meyasameki”

“Mama ya cuceni ya zalunceni wlh shi nakeso nashiga uku”

“ke wai dan ubanki waye ne shi meyai miki shi din”

“Mama muktar ne wayyo allah na ”

tasaki mama taja tai tafiyar ta tayi ta koma daki muwadda kam mukullin motar maman ta ta dauka tanufi gidansu muktar

 

Watan farhana 2 a asibiti aka sallamesu suka dawo gida mama maijidda tacigaba da kula daita da baby tun a asibiti farhana taso ibraheem yasa mata sunan dady yaki yarda sunan mahaifin sa aka sa masa wato mudassir ake ki ransa da *aman* tana zaune tana lallaba shi yai bacci bilkisu ta shigo

“aunty farhana ki bada aman zaakai gurin malam ”

” to, bilkisu bari acanja masa kaya ko ”

” kai wane irin kaya kuma dan allah ki kawo shi haka haba ”

” wlh ke sai nacanja masa kaya inbazaki iya jira ba jeki ankawo shi ”

Fita tayi taje tasami ibraheem yana zaune shi da hajiyar su tashiga tace

” yaya khalil wai bazata bada shi ba bacci yake bazata tasheshiba ”

” ke bilkisu kiji tsoran allah bana son karya fa “.

” ahaf hajiya ai bazan mata karya ba ai “.

Ibraheem ne yatashi cikin fushi yafita kai tsaye dakin farhana ya nufa tagama shirya aman kenan ya shigo hannu yasa kawai ya dau babyn batare da yace da ita kala ba gabansa tasha ta kafe shi da ido

” ustaz, me bilkisu taje tace maka ”

” bansaniba farhana tambaya ta ma kike, meyasa kike son raina min hankali ne ”

Tsaki yaja yafita yabarta ta zube tana kuka mama maijidda ce tashigo tasameta tace

” farhana lafiya kike kuka me ya hada ki da mijin naki ”

” mama maijidda *kannan mijina* basu da kirki wlh kullum burin su su hadani da mijina ”

” ayya kiyi hakuri farhana wataran zasu dena”

“Hmmm mama ni fa gani nake hakkin aunty safiyya ne ke bibiyata kullum ace bani da kwanciyar da hankali a gidana ”

 

” hakan zata iya kasance farhana amma ki nemi safiyya kinemi yafiyar ta kinji ”

” to shikenan mama nagode inshaallah xanyi yadda kika ce ”

 

Safiyya tana kitchen taji sallamar bakuwa fitowa tayi taga wata dattijuwa da wata yar matashiyar yarinyar dubansu tayi da kulawa tai musu sannu da zuwa tabasu gurin zama takawo musu ruwa da lemo

” sannunku baba ”

” yauwa yar kirki, hajiya ce ta turo mu nice wacce zan kawo yarinya mai aiki ”

” allah sarki sannunku ya sunanan ta ”

” sunanan ta saddiqa ”

” mashaaallah sannu saddiqa zaki dinga yimin rainon yara sai aikin da bazaa rasa ba ”

” to aunty ”

Daki safiyya ta nuna mata dan karami mai kyau taajiye kayanta suka fito safiyya tadakko dubu 3 tabawa tsohowar ta tafi tanata tai mata godiya kukan hamra ne yasa safiyya nufar dakin ta ta dakkota tabata ruwa mikawa saddiqa ita tayi nan ta sa kuka dariya safiyya tayi ta karbeta

 

“uncle kasan me zan siya in munje shop rite ”

” aa fine girl sai kin fada ”

” ko dayake sai munje ka gani ”

 

Dariya yayi yaci gaba da tukin motar da yake adai dai shop rite yayi parking suka shiga rike hannunsa tayi suka shiga suna shiga ta fizge hannunta tanufi gurin wata budurwa rungumeta tayi tace

” aunty najiba oyoyo ”
Shiru yarinyar tayi mata sai kuma tasakar mata murmushi ta tsuguna tare da dafa kafadar ta tace

” fine girl kinsanni “?

” aa aunty nazaci aunty najiba ce kiyi hakuri ”

Dariya tayi har sai da dimple dinta ya lotsa faruq yana tsaye ya harde hannunsa a kirji yana ta kallon budurwar can yanisa yace

 

” dan allah kanwata kiyi hakuri da halin fadila ”

” ayya ba damuwa ”

” ko dayake ma ai yata ta kulla alaka tsakanin uncle dinta da mai kyau ”

 

” Hmmm ko ”

” kwarai kuwa ko bazan samu gurbi ba mai kyau ”

Shiru taimasa fadila kam ta ki sakin hannun budurwar nan cikin kashe murya faruq yace

” ni suna na faruq muhammad mai nasara wannan diyar yayana ce fadila assadiq

” ni kuma suna na safeena nasir ”

 

Nan take suka saba sukai musayan numbobi sukai sallama ta tafi

” sopy, kishirya akwai bikin da zamuje na aboki na umar shuwa ”

” Dee aure zaiyi ”

” eh zai auri sister din sa abin haushin ma yarinyar bata so sopy ”

Kan tabashi amsa fadila tashigo da gudu tafada jikin assadiq tace

” papa alboshirinka ”

” goro fadilaty”

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[5:34Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*Alhmdulillahil lazi baada ma amatana wailehiln nushur*👏🏻

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦

 

*innalillahi wainna ilehir rajuun ina taya daukacin maaikatan freedom radio alhini rashin da sukayi na rasuwar TIJJANI ADO dafatan allah yaji kansa yai masa rahama yabawa iyalinsa hakurin rashin sa AMEEN*

 

*96*

 

~~~safiyya ce takafe fadila da ido tana kallonta assadiq kam kama hanyanta guda biyu yayi ya hada da nasa yana sauraranta

“uncle dina aure zaiyi munga matar fa da mukaje shop rite ”

” dagaske kike fadilaty ko da wasa ”

” wlh papa da gaske nake bari ya shigo ma ka tambayeshi ”

” wlh Dee kai kake biyewa shirman fadila shiyasa ta girma bata san ta girma ba”

“eh na biye mata din in so kike insan ta girma to ki dage ki mata kani ko binty ”

Kai tadaga masa safiyya kuwa jan bakinta tayi tai musu shiru shigowar saddiqa ne yasa fadila ta zabura ta mike daga jikin assadiq tace

” mamma wacece wannan ta daukar min hamra sai ta gudu da ita ko”

” fadila meye haka ne to tagudu da ita takaita ina ke ko tohm, sunan ta aunty saddiqa anan zata zauna tare da mu kinji ko ”

Dariya saddiqa tayi ta tsuguna ta gaida assadiq ya amsa a mutunce ta mikawa safiyya hamra ta fita assadiq ne ya dubi safiyya yace

” sopy, wannan yarinyar fa daga ina “?

Nan tabashi labarin dalilin kawo ta da wacce takawo ta din shiru yayi yatashi ya nufi dakin sa tashi safiyya tayi ta bishi tabar su hamra a gurin mai aikin

Yana tsaye yana balle maballin rigar sa tashiga da sauri ta karasa ta balle masa janta yayi zuwa jikin sa yahada fuskar sa da tata yace

“da assadiq yake dan gata a gurin sopy, amma sanadin ‘ya’ya anwatsar da shi komai da kansa yake yi ”

” Hmmm wlh Dee Inkana wani abun kamar karamin yaro yanzu yanzu me cece damuwar ka me kake so ”

 

” sopy nake so ita nake da muradin jin dumin tattausar fatar jikinta kuma inbata kyautar baby a daidai wannan lokacin ”

 

Cikin shagwaba ta kira sunan sa be iya amsawa ba saboda kasalar data saukar masa bakinsa ya hada da nata ya shiga sarrafawa kamar alawa abakin yaro zip din rigar ta yaja ta rike hannun sa da ido yaimata magana murmushi tayi tasakar masa kidimewa yayi yajata zuwa gado nan yashiga sarrarfa ta Cikin kwarewa kullum jinta yake kmr amarya tana kwance ajikinsa bayan yasami nutsuwa yana shafa lallausar gashin kanta a hankali ya kira sunan ta

“amaryar assadiq”

“Dee, amarya kuma”?

“sopy mamaki kike dan nakira ki da amarya to kidena dan kinfi amarya a gurina, bari kiji kefa
mace ce
tamkar da dubu ina alfahari da samun ki amatsayin mata uwar yaya ga assadiq ke dai fatana allah ubangiji ya barmu tare ”

Dariya tayi tamike ta nufi toilet bayan ta daura towel binta yayi da kallo yana murmushi lekowa tayi ta kira sunanan sa

” Dee, kataso muyi wanka kaji ”

” sai dai inzaki goyani ”

Dariya tayi ta maida kofa ta rufe tashi yayi ya bita Cikin toilet din sukai wanka kamar yadda suka saba

Muwadda kam tunda tafito daga gida take gwada layin muktar yaki shiga inta kira ta kanwarsa rushida itama akashe ahaka ta karasa gidan su abun mamaki arufe yake wasu samari tagani zaune takarasa gurin su tare da yi musu sallama

“dan Allah masu gidan nan fa ”

daya daga Cikin su ne yayi dariya yace

” cab hajiya ai basa nan dama haya suke kuma antashesu ”

” dan allah ina suka koma “?

” ai hajiya sai dai kiyi hakuri dan mude bamu san inda suka komaba”

Shiru tayi tashiga tunanin inda zata ga muktar take wani zazzabi yarufe ta tare da wani mugun jiri da kyar taiya karasawa gida tana zuwa ta kwanta sai rawar sanyi take yi tana kiran sunan muktar hankalin mama ya tashi Cikin azabar zazzabi take sanbatu

“muktar kai nake so yazaka tafi kabarni karaba ni da assadiq ka raba da yata wayyo allah na ”

” ke muwadda kinfara haukane me yake shirin samun kwakwalwar ki ne ”

Shiru tayi tacigaba da gursheken kuka mai tsuma rai mama dai zuba mata ido tayi akwai tana sauraran kukan yar tata

 

Shukura na zaune tana bawa abdul abinci fara da mai Kb yai sallama ya shigo dubansa tayi Cikin wulakanci da masifa tace

” malam kana haukane zaka shigo min gida kai tsaye meye haka ”

” Hmmm allah sarki yi hakuri uwar gida agidan haisam ango agurin Afifa muhammad mai nasara ”

” kai dallacan dakata bana Cikin haukanka kaji ko me yakawo ka”

“mai da wukar hajiya, zuwa nayi inshaida miki mijinki fa yayi aure yana can tare da matar sa a katon gida nasan baki sani ba ”

” kai dallacan fitar min a gida mahaukacin banza da wofi

“Hmmm dan allah kizo muje ki gani da idonki ”

Shiru tayi kamar bazata motsa ba sai kuma ta nufi daki ta dakko mayafinta ta tasa yaranta agaba ta bishi suka nufi gidan Afifa

 

Tun safe Afifa takewa haisam kuka ita tagaji gashi anata kwashe mata kaya intai magana sai ya rufeta da fada yanzu ma fada suke yi tana ta masifa yai mata banza yaki kulata bugun daakafara yi ne yasata yin Shiru tashi yayi yafita yatsmbayi waye

“bude kagani mana ”

Budewa yayi hakan yayi dai dai da fitowar Afifa ganin haisam tayi da wata mata da yaya tanaiwa haisam kallon tuhuma ido tazuba musu tana kallon su can ta nisa tace

” bewar allah ko lpy zaki shigo min gida da gayyar yayanki”

“Hmmm bi ahankali da sannu zaki ji ko ni wacece ”

” ke fita malama Afifa kar ki saurareta makaryaciya ce ”

” ko kuma kai din makaryaci ba, ke wannan da kike gani mijina ne uban yaran nan kuma ko zansan naki matsayin “?

” bansaniba, haisam ka karyata zancan banzar matar nan, kace min ba gaskiya bane ”

Tana fada tana kuka Shiru yayi yarasa me zaice kb kuwa murmushin mugunta kawai yake ana haka wani mutum yashigo gidan haisam na ganinsa ya dada zabura sallama yai yadubi haisam yace
” haisam zuwa nayi infada maka musu gida zasu dawo dan haka suna bukatar gidan su dan haka katashi kabasu gidan su ”

Daskarewa Afifa tayi shukura kuwa wani dadi ne yakamata tace

” amarya ya da gidan aro kuma, amma kinyi asara banza mai auran mijin wata ”

Wani banzan kallo Afifa taiwa shukura ta shiga parlorn ta ta dakko mayafinta ta fito ko kallon inda haisam yake batai ba ta fita

Faruq ne zaune shi da momy da dady yana basu labarin budurwar da yayi momy ce ta dubeshi tace

” faruq kunyar ka ragagiya ce wlh yanzu a ina yarinyar take ”

” kyale ta umar zan nema maka auran yarinyar kwana kwanan nan meye sunan yarinyar ”

” sunanan ta safeena dady ”

Dariya momy take shigowar Afifa ne yakatse musu hirar da suke suka zuba mata ido suna kallon ta dady ne ya dubeta yace

” ke Afifa lafiya lafiyar ki me yafaru “?

Nan ta kwashe komai ta fada musu Shiru sukayi ran momy ne yabaci mamaki yagama cika ta dady ne ya nisa yace

” ke Afifa tashi ki koma gidan ki ki turomin mijin naki ”

” aa alhj me zai hana ta zauna inyaso akira shi yazo”

“aa ta wuce ta tafi kawai ”

Yana gama fada ya tashi ya hau sama faruq ne ya dubeta yace

” oya tashi ki tafi malama allah ya kara ”

Kuka tasa momy ce ta dubeta tace

” kinga Afifa tashi ki tafi gidan yayan ku kifadawa auntyn ki kinji ”

Faruq kam dariya ce ta kufce masa ya maze tashi Afifa tayi ta nufi gidan assadiq gurin safiyya

 

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[6:34Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

 

*💦T <W >F*💦

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA💐

 

 

*INNA LILLAHI WAINNA ILEHIRRAJUUN ALLAHUMMA AJIRNA FI MUSIBATI WAAKLIFNA KHAIRAN MINHA*😰

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦

 

 

 

*97*

 

~~~su saddiqa ne a parlor ita da fadila da hamra tana basu abinci Afifa tai sallama ta shiga guri tasamu ta zauna yaran suka zuba mata ido saddiqa ce ta gaisheta

Sannu da zuwa aunty, ina yini ”

” lpy kalau, fadilaty ba magana ko, ina mammanki “?

” mamma na tana daki ”

” oya jeki ki ce mata nazo kinji ”

Tashi tayi ta shiga bedroom dan kiran safiyya hamra ce tasa kuka sai Afifa ta dauketa daukar ta tayi

Safiyya na gyran wardrobe fadila ta shigo da gudu

” mamma kizo ga aunty Afifa tazo ”

hannun ta takama ta murde mata kunne kana tace

” fadila ban hanaki gudu ba bakya ji ko, baki ganin kin girma ne ”

kuka tasa saboda zafin da taji Cikin kuka tace

” mamma dan Allah kiyi hakuri na dena”

“fita ki bani guri ”

Fita tayi tana kuka bata jima da fita basafiyya ta biyo bayanta a parlorn ta tarar da fadila nata kuka afifa nata rarrashinta Cikin sakin fuska ta dubi Afifa tace

” afifa sannu da zuwa, ya gida dafatan kina lpy ”

” aunty ba lpy ba ina Cikin tashin hankali na shiga uku ”

Safiyya ce ta dubi saddiqa tace

” saddiqa ya baki kawo mata komai ba, jije ki kawo mata lemo da abinci ki Ja yaran ku koma daki ”

” to aunty ”

Mai da dubanta tayi ga afifa tace

” afifa me yafaru fadamin inji ”

Nan ta kwashe komai ta fada mata

Shiru safiyya tayi saboda yadda abin ya bata mamaki can ta nisa tace

” yanzu afifa ina haisam din yake “?

” a gida nabar shi aunty ni wlh bazan koma ba ”

” aa farhana bahaka zaaiba, yanzu ki bari in yiwa Dee waya tukunna ”

Wayar ta ta dakko tafara kiran layin assadiq sai da ta kusa tsinkewa sannan ya dauka Cikin narkar da murya ta fara magana

” Hello Dee ya aiki ”

” lpy sopy, ya gidan da yarana “?

” lpy kalau Dee, pls zaka dawo da wuri ”

” eh to, lpy dai ko “?

” dama afifa ce tazo da wata matsala wlh, shine nake son inji sanda zaka dawo saboda asan yadda zaai ”

” ok, sopy, badamuwa sai na dawo gidan ”

Sallama sukayi ta kwashe wayar afifa kuwa kuka take tai wa safiyya tana rarrashinta

 

Abangaran jalila kuwa bata da wata matsala kullum Cikin zaman lpy suke da mijin ta yanzu haka zaune suke da mai gidan nata cikin shagwaba ta dubeshi tace

*Doktar* wai yaushe zamu haihu ne, nifa namatsu in samu baby asa mata sunan ummi na ”

Dariya yayi ya shafi fuskar ta kana ya ce

” habibty, baby kike so, bakisan na dade da baki baby ba, tun last 2 weeks na fuskanci baby na na kwance a mahaifar matar *doktor*”

Dariya tayi ta shafi Cikin ta tace

“to, amma nifa banajin ciwon komai dama ana haka ne?

“Hmmm, habibty kenan,ana yi mana amma zanmiki test dan mutabbatar ko “?

Kai ta daga masa ta rufe fuskar ta tana dariya Cikin kunnan ta yarada mata wata magana da duka takai masa ya goce yana dariya can ta shagwabe fuska tace

” pls *doktar*muje mu gaida ummi da momy ”

” sai kin min alkawari guda daya kin yarda ”

” na yarda *doktor*”

“oya shirya muje ”

Shiryawa tayi Cikin wata atamfa Ja da green mai zanan gyanye tayi kyau sosai dubanta yayi yace

” kwalkiyar ki tayi yawa gsky, muje a rage ”

” nide gsky mutafi ”

kyaleta yayi suka fita kai tsaye gidan su suka nufa

 

Abangaran farhana kuwa tafara samun saukin matsalolin ta dan malam mudassir ya tsawatar wa dasu fatisa ya yi musu fada sosai sun dena mata abinda suke yi suna zaune lpy yanzu haka tana kitchen tana girki aman yana ta kuka masari ce ta shigo ta dubi farhana tace

“aunty farhana hajiya tace kukan me aman yake yi ”

” wlh zainab rigima ce kawai wai bazaa goya shi ba ”

” ayya babana baka son mama tayi aiki, kawo shi in rike miki shi ki karasa ”

” yauwa zainab tafi ma dashi gurin hajiya dan Allah, in samu in karasa ustaz ya kusa dawo wa ”

” ok tohm ”

Karbar sa tayi tafita farhana godiya tayi wa Allah da yabata zaman lpy da *kannan mijinta*

 

Abban muwadda ne ya tsareta da tambaya akan dalilin ciwonta Shiru tayi tsawa ya daka mata Cikin kidima tafara magana

” abba dan Allah kayi hakuri, wlh muktar ne ya karbar min komai nawa shi yaraba ni da assadiq yaudara ta yayi wlh ”

Cikin tsawa yafara magana,” muwadda waye muktar, meye alakar ki dashi kina matar aure, kenan dama kece baki da gsky kika sa ni naiwa mutanan arziki rashin kirki ko sha sha, kika watsar da yarki saboda son zuciyar ki “.

” alhj dan Allah, kayi hakuri….

“Dakata min hajiya ai da sanin ki komai ya faru, dan haka kija bakin ki kimin Shiru kuma wlh zan baku mamaki, ki saurari hukuncin da zan yanke akanki muwadda ”

Yana gama fada ya fita ransa a mutukar bace kuka muwadda tasa wa maman ta tace

” mama dan Allah kibawa abba hakuri zan koma gidan ya assadiq “.

” ya isa haka muwadda yi Shiru zamuyi magana in yadawo kinji “.

 

 

Momy ce zaune da yaya hannatu suna tattaunawa game da matsalar afifa fadila ta shigo jikin momy tafada tafara magana Cikin shagwaba

” kakus, kinga mamma na tasani kuka ko ”

” kai amma bata kyauta ba fadila, kibar ni da ita ”

Dariya ya hannatu tayi kana tace

” fadila shagwabar ki tahana aga girman ki ”

Faruq ne ya shigo yasami guri ya zauna suka shiga hirar su gwanin shaawa

Assadiq be dawo ba sai yamma suna tattaunawa akan mijin Afifa kiran muwadda ya shigo dubawa yayi yaga sunan muwadda kallon safiyya yayi ita dinmma shi take kallo

 

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[5:33Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

 

 

*Alhmdulillahil lazi ahayana baada ma amatana wailehiln nushur*👏🏻

 

*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦

 

 

*💙mashaallah ina taya TALENTED WRITTERS murnar kamala littafin kawar mu wato sadiya smart mai suna MEENAL dafatan mun amfana da abinda muka karanta allah yakara basira yasa afi haka sai munji ki asabon novel kawata*💙

 

 

*98*

 

~~~kamar bazai dagaba sai kuma yaga gaba daya hankalin sopy yana kansa sai da takusa tsinkewa sannan yadaga

“Hello ”

” Hello, ya assadiq ina yini ”

” lpy, wake magana ”

” Ummi, muwadda ce, dan Allah yaya assadiq kayi hakuri da abinda yafaru, ka dawo dani dakina inshaallah bazan kuma ba ”

” Da Allah dakata malama kinajina ko, daga yau kar ki sake yimin waya inbahaka ba wlh ran ki sai yabaci, me yarage tsakanin mu “?

” shikenan amma dan Allah ina neman alfarmar kabani hamra in rike ta agurina ”

Tasaki yayi ya kashe wayar, duban safiyya yayi ya ce

” sopy ko da mahaukaciyar yarinyar nan zata zo kar ki kuskura ki bata hamra ”

” Dee, kamar yaya, ai bazaa raba ya da uwa ba ”

 

” to, ni assadiq muhammad mai nasara na raba dan haka ki kiyaye sai azauna lpy ”

Shiru tayi can ta nisa tace,” Yakamata ayi wani abun game da afifa dan Allah, ni wlh tun farko yaron nan be kwanta min ba wlh ”

” Hmmm, maganin ta kenan meye bance ba, ni ba ruwana suje can su karata ”

” dan Allah mijin sopy, kayi hakuri ku duba lamarin yarinyar nan ”

” Safiyya kenan, yanzu me kike so ayi kenan ”

” yauwa Dee ina ganin aneme shi ayi magana ta fahimta aji ina ya dosa ko ”

” shikenan naji, yanzu tana ina afifa ”

” tana daki ta dan kwanta bata jin dadi ne

Hmmm, ki kirata”

Tashi tayi ta kira ta tare suka fito ta tsuguna ta ta gaishe shi yaamsa bayan ya zuba mata ido can ya nisa yace

“ki tashi muje, zaa sami mijin naki ko ”

” wlh yaya assadiq bani da tabbas ”

Wayar sa ya zaro ya kira layin faruq, bayan ya daga ne ya ce yafito zasu gidan afifa
mikewa yayi suka fita abakin gate suka hadu da faruq din wani banzan kallo ya watsawa afifa suka shiga motar kai tsaye gidan afifa suka nufa sanda suka isa abin mama ki anfito da kayan afifa waje wani mutum yana kokarin kulle gidan da sauri suka nufi inda mutumin yake faruq ne ya fara magana

“salamu alaikum, malam, ya haka zaku fitowa da yarinya kaya waje, ina mai gidan ”

” alaika salamu, dafarko dole afito da kayan nan saboda gobe masu gida zasu dawo suna bukatar gidan su ”

Sai yanzu assadiq yasa baki saboda gaba daya kansa ya kulle Cikin mamaki yace

” yallabai bamu fahimceka ba, wai ina shi haisam din yake ”

” eh, kamar yadda nace gida aro nabashi a yanzu haka yan sanda sun tafi da shi saboda bashin daake binsa”

 

Wani ihu afifa ta kurma wanda ya janyo hankalin mutane faruq ne yadaka mata tsawa tayi Shiru can assadiq ya nisa yace

“yanzu ina zamu same shi kenan ”

” gaskiya banace ba amma kuje ku sami uwar gidan sa may be zaku sami labarin sa ”

Faruq ne ya dubi assadiq shi dinmma shi yake kallo sannan suka dubi afifa atare suka hada baki wajen magana

” ke dama yana da mata ne?

Kai kawai ta daga saboda yadda take ji kamar ta mutu ga ciwon kai ga bacin rai, assadiq ne ya dubesu yace

 

“faruq kassmo babbar mota a kwashe kayan nan, ni kuma zamu je gidan uwar gidan nasa ”

” tohm shikenan bross, sai mun hadu a gida, shegiyar yarinya ta tayar da mutane a tsaye kawai wlh gurin safeena zanje fa ”

 

Murmushi kawai assadiq yayi ya shiga mota suka tafi bayan anmusu kwatance, isar su gidan tayi dai dai da zuwan haisam wanda yayi baki ya fita hayyscinsa kunya ce takama shi yayan sa ne suka jiyo muryar sa suka fito aguje suna

” oyoyo abbba ”

Rugume su yayi yana hawaye shukura ce tafito ita ma ganin su afifa ne yasata dada hade rai assadiq ne ya gaji da kallon su yayi gyaran murya yace

” ji mana malam, yanzu kai abinda kayi ka kyauta kenan, wace irin rayuwa ce wannan ga karya ga rashin gaskiya, to mu bazamu lamunta ba dan haka kabani takardar afifa tagama zama da kai

Arazane ya dago da kansa ya zubawa afifa ido take wata soyayyar ta ta kuma mamaye shi, Shiru yayi afifa kam wani jiri ne ya debeta ta tafi luuuu zata fadi da sauri haisam ya tareta ta fada jikin sa Cikin tashin hankali assadiq ya dubeta a mota aka sata suka nufi asibiti shukura kuwa dariya tayi taja hannun yayan ta suka koma ciki

 

Suna zuwa asibiti aka shigar da ita ganin likita nan da nan aka fara dubata take likita yagano jininta ya hau ga karamin ciki allurai akai mata sannan aka sa mata ruwa duk assadiq ne ya biya kudin

waya yayi wa momy yafada mata hankalin ta yatashi kodimewa tayi takira faruq yazo ya kaita asibitin yace bashi kusa layin safiyya ta kira tafada mata lokacin tana tsaka da girki

“Hello, safiyya afifa aka kwantar a asibiti dan Allah inba abinda kike kizo muje, na kira faruq baya kusa ”

” subahanallah, to gani nan momy ”

 

Saddiqa ta kwallawa kira tazo dubanta tayi tace

” yauwa Saddiqa zan dan fita ne ga girki na dora ki karasa min ki kula da yaran nan, ina hamra?

 

“tayi bacci aunty, fadila tana gidan
momy ko?

“aa tana gidan mu,dazu bayan kinfita nasa aka kaita ”

” to shikenan aunty ”

Daki ta koma ta shirya ta fito sai da gyarawa hamra kwanciyar ta sannan ta fita

Sanda ta karasa gidan su assadiq momy sai sintiri take tana ganin safiyya ta nufeta suka gaisa mota suka nufa safiyya taja suka nufi asibitin

Sanda suka karasa afifa ta farka sai kuka take tana ganin momy ta dada fashewa da kuka wata harara momy ta watsawa haisam kasa yayi da kansa ya gaishe ta taki amsawa safiyya tai mata sannu da jiki

Kwanan ta uku a asibiti aka sallameta kai tsaye gidan su aka wace da ita dady ne ya kira haisam ya sa shi agaba yai taimasa fadan karyar da yayi musu da nasiha, momy kam ta tubure sai yasakar mata ya, yaki dady ne ya dakatar da ita ya dubi haisam akaro na biyu yace

“a hakika nin gaskiya ni kaina naso raba auranka da yata, to saar ka daya wannan Cikin da yake jikin ta shi zai sa nafasa ku dirina, dan haka ni yanzu zanbaka gida da jari dazaka rike iyalinka kuma zan hada ka da mutum 2 aje garinku dan ganin danginka, inafatan ka fahimta ”

” na fahimta dady nagode madalla, allah yakara budi yaja kwana ”

” ameen, tashi kaje nan da sati zaku tare ka kular min da afifa kaji ko kayi kuma adalci tsakanin ta da abokiyar zamanta ”

” inshaallah dad”

Momy dai tarasa bakin magana afifa kuwa banda aikin kuka ba abinda take

 

Kamar yadda dady yafada su afifa sun tare a gidan da dady yabasu gida mai kyau sama da kasa afifa asama shukura akasa kowa kitchen din ta daban amma tsakanin ta da shukura ba sauki dan zafin kishi ne da ita gashi Allah yasa mata tsoran ta kamar me

 

Haka rayuwa tai ta tafiya Cikin sauyin yanayi yau da dadi gobe ba dadi safiyya kam bata da wata matsala dan yanzu tazama abar kauna ga dangin assadiq fadila ta girma sosai hamra ma haka dan har ta shiga school safiyya takan kaita gurin muwadda amma ba tare da sanin assadiq ba

Cikin afifa ya tsufa yau gikin tane tana kwance tana fama shukura ta shigo dakin ta duban ta tayi ta yatsine fuska tace

“to uwar langwai wazai miki girkin da kika zo kika kwanta ”

 

” haba maman abdul baki ganin halin danake ciki ”

” eh bana gani baga makauniya ba matsalar ki ce fa ni de kitashi kimana girki kawai ”

Tana gama fada tai gaba abinta kuka sosai afifa tayi ta yunkura zata tashi ta dora girkin kenan haisam ya shigo da abinci wanda yasiyo a restuarent ya mikawa shukura nata yazo suka ci shi da afifa yana ta lallabata

 

Nabil ne zaune shi da maman su wato yaya hannatu dubata yayi Cikin jin kunya yace

“umma dan Allah kisa baki abani auran fadilaty in ta girma ”

 

Wata tsawa ta daka masa sannan ta dora da

” Nabil banyarda da auran zumunci ba dan wlh bazaku rabamu da junan mu ba dan haka kar na kuma ji wlh kaji dai nafada maka ”

Ashraf ne ya dubi maman tasu yace

” amma mama ai…

“Dakata Ashraf bana son zancan haka kutashi kubani guri ”

Fita sukayi ransu abace tsaki taja ta maida kanta ta kwantar a kujera

 

Anemawa faruq auran safeena ankai kudi da sa rana biki saura wata biyu yakawo ta gurin momy sun gaisa duban sa momy tayi tace

 

” faruq ka kaita gurin safiyya su gaisa ”

” to momy daman zankaita ”

Sallama tayi mata tabata turarurruka suka tafi kai tsaye gidan safiyya ya kai safeena suka gaisa take shakuwa ta kullu a tsakanin su fadila tana ganin ta ta Rugume ta tana murna assadiq ma yadawo sun gaisa ya yaba da zabin kanin nasa

 

 

Muwadda ce ta shirya tsaf tafita zuwa super market tana Cikin siyayya taga wani matashi da wata hadadiyar mata Rugume da bsby cikin sauri ta karasa gabansu dan tabbatar da abinda ta gani gaske ne, waye wannan din.

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*
✍🏻✍🏻
[5:54Am, 2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

*NA*
NASEEBA I UBA💐

 

*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*📿

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦

 

*2nd 2the last*👈🏻

 

*98*

 

~~~Cikin rawar murya muwadda takira sunan muktar basarwa yayi, yayi kamar be ji ta ba sai maryam matar sa ta tabo shi sannan ya dago da kansa ya kalleta fuskar sa ya hade sannan yace

“oh, muwadda ya kike ya maigidan naki”

“muktar wacece wannan, yanzu kai kana ganin kai min adalci kenan kaci amanata ka cutar da zuciya ta, mukatar…… ”

” dakata dan allah kar ki tara mana jamaa, wannan da kike ganinta mata ta ce, sunanan ta maryam ga babyn mmu nan, shaheed, so dan haka ki saurara min ki rabu dani ki manta da kin taba sanin wani muktar a duniya kin gane ko ”

” Allah ya isa tsakani na dakai wlh bazan taba yafemaka ba mugu azzalumi, kuma wlh sai ka biyani dukiyata ”

Maryam ce ta kosa da jin kalaman muwadda jikin muktar ta matsa ta ce

” sweet *mk* pls mu tafi mana wai meye alakar ka da ita ne nifa banason kana hurda da mata ”

Takarashe maganar Cikin shagwaba dubanta yayi yace

” ayya kar ki damu matar *mk* baki da fargaba akaina ai ko zanyi hurda da mata to bazanyi da mahaukata ba, so that muwuce kawai ”

 

Tafiyar su suka yi suka bar muwadda atsaye kuka ne ya kwace mata tayi iya yinta ko siyayyar batayi ba ta fito abakin kofa ta hadu da su safiyya sunzo shoping kamar ance ta kalli can sai ga assadiq ya sakale hannunsa Cikin na sopy sun taso yaransu agaba gwanin shaawa sunci kayan su iri daya doguwar riga ta swiss lace sunyi kyau tsayawa tayi tana kallon su safiyya ce ta kula da ita cikin murna tafara mata magana assadiq kuwa gaisawa kawai sukayi ya shige ciki fadila ce ta gaisheta ya yin da hamra ta nufi gurin papan ta ko kallon ta batayi ba sai da safiyya ta kira sunan ta sannan ta dawo

“Hamrah baki ganin maman ki ko, bazaki gaisheta ba ”

” ni ba itace mama na ba, kece mamana ”

Shiru sukayi muwadda kam kamar tace wayyo Allah saboda takaici safiyya ce ta ja hannun yarinyar ta hada dana muwadda tace

” Hamrah, itama mamanki ce kar ki kuma cewa ba mamanki bace kinji ko, ba kyau ko kina son Allah ya kona ki a wuta “?

Kai ta girgiza alamar aa,” yauwa yata to ki dena kinji ”

Kiran wayar assadiq ne ya shigo dubawa safiyya tayi taga shine Cikin sauri ta daga

” Hello, Dee ”

” wai safiyya me kike har yanzu baki taho ba, meye haka ne ko ance miki bani da aikin yi ne yanzu da zaki tsaya kina bata min lokaci in amfasa siyayyar sai ki fada min ”

Yana gama fadar haka ya kashe wayar safiyya ce ta maida dubanta ga muwadda tace

” kiyi hakuri muwadda bari mu wuce sai munyi waya ”

Rungume Hamrah tayi ajikinta sai kuma tafara zubar da kwalla safiyya taja hannun Hamrah suka shiga ciki

Sanda suka shiga assadiq yacika yai fam a hankali ta kira sunanan sa

” Dee I am so sorry”

Banza yayi mata itama basarwa tayi ta shiga daukar abinda tazo siya suka gama suka biya kudin suka fito a mota safiyya take taiwa assadiq magana yayi mata magana yayi Shiru fadila ce ta kira sunan sa

“papa, mamma na fa tana ta maka magana baka amsaba, dan Allah ka amsa ”

” ki rabu da ita fadilaty ina jinta, mun bata ne ”

” gsky banyarda ba nide, mamma na ki bashi hakuri kinji ”

Shiru safiyya tai musu karshe ma tashiga danne danne a wayar ta, Hamrah ce ta ce

” papa”

“naam kalaty”

Wai mamma ba ita tahaifeni ba, wai aunty ce mamma na ”

Kallon safiyya yayi ya tsareta ta da ido dauke kanta tayi can ya nisa yace

” aa bahaka bane, wa yafada miki haka ”

” papa auntyn ce fa tafada dazu ”

” to aa sopy ce maman ki kinji ko kar na kuma ji ”

 

Safiyya ce ta dubeshi har zatayi magana sai kuma tayi Shiru ahaka suka karaso gidan su safiyya yana yin parking fadila ta bude murfin motar ta fito ta nufi Cikin gida Hamrah ma binta tayi safiyya ma kama murfin motar tayi zata fita ya dafe hannun ta ido yakafe ta dashi ita dinmma shi take kallo fuskar ta yashafa sannan yace

“sopy fushi ko, kina fushi da assadiq ko saboda nai miki fada, shikenan sopy kiyi hakuri ”

” ni haka nace maka”

“to yane, inbahaka ba, shikenan dai yanzu kishiga ciki kifadawa ummi zan shigo mugaisa but ki kawar da fushin da ya kwanta a kyakkyawar fuskar nan taki kinji ”

Yakarasa maganar yana kashe mata ido tare da langabar da kai dariya tayi tace

” wlh Dee halinka sai kai wanda besan halinka ba ya wahala ”

Fita tayi tabarshi yana dariya kallon ta yake yana dada godewa Allah da yabashi safiyya amatsayin mata tana shiga suhyla ta Rungume ta dan suma sunzo nan suka gaisa da yaya rukayya yaya amina ma tazo ummin su dadi yacika ta ganin yayan nata sun zo tafadamata assadiq zai shigo suka gaisa yabada siyayyar dasuka yi musu aka shigo da ita nan yai musu sallama ya tafi hirar su suke Cikin so da kauna wayar safiyya ce ta hau ruri tana dubawa taga sunan momy dagawa tayi suka gaisa sannan ta dora da

“Safiyya dama zancan hado lefan faruq ne dake zaa je dan haka assadiq zakai ki ai miki pasport daga dubai zaku wuce saudi kuyi umara ”

” to shikenan momy allah ya kaimu amma yanzu bana gida muna gidan mmu sai mundawo ”

” to shikenan badamuwa bani ummin naku mu gaisa ”

Wayar ta mikawa ummi suka gaisa Cikin mutunci momy taitaiwa ummin safiyya godiya da ban hakuri bisa abubuwan dasuka faru abaya tace bakomai ai anzama daya sukai sallama ta kashe wayar

” cab mahakurci mawadaci safy momy ce me kiranki a waya lallai komai na da lokaci ”

Cewar yaya rukayya yaya amina ce ta ce gaskiya safiyya kinyi hakuri ina zan iya abinda kikayi Allah nagode maka da bani da *kannan miji*

” to yanzu bagashi komai ya wuceba ”

Cewar ummi nan tai taiwa yaran nata nasiha, sai yamma Dr almustapha ya kawo jalila su safiyya sukai ta murnar ganin su, nan suka gaisa jalila ta gaida ummi Cikin girmamawa Dr almustapha ne ya dubi najiba yace

” najiba ga amanar matata nan ki kular min da ita kimata me ma kikace habibty”

Dariya jalila tayi tace, “najiba danwake”

Dariya ummi tayi safiyya ce ta dubi najiba tace

“najiba kowa ke yake bawa amanar matar sa, haka fa da Dee yakeyi ”

” ai sun san ba wasa badai kula ba, dan haka bari ma natashi indorawa aunty jalila dan wake ”

Dariya sukayi dubansu jalila taja hamra jikinta tanai mata wasa sai da magariba baffa ya shigo suka gaisa da yayan nasa kowacce ta tafi gidan ta

Afifa ciki ya tsufa da kyar take iya aiki tana daki yanuwan shukura sukazo suncika gidan da hayaniya da shewa sun dameta amma ba yadda zata yi haka ta hakura ta kulle kofar ta ta danne kunnanta da pillow sai yamma suka tafi cikin dare tana jikin haisam tana bacci kamar an tsira mata allura tafarka agigice

 

“wayyo Allah na haisam zan mutu katashi mutuwa zanyi ”

Agigice haisam yafarka yarasa yadda zaiyi shukura yaje yataso tanajinsa tai masa Shiru hakura yayi ya koma yana zuwa tana sakin wani nishi mai karfi sai jin kukan baby yayi murna ce takama shi ganin Afifa ta haifa masa baby girl waya ya dauka ya kira momy nan tai ta murna dady ma haka ya taimaka mata ta gyara jikinta da sassafe yaya hannatu taje gidan Afifa nan aka shiga hidimar suna farhana tazo tayi kyau da kiba ga danta gwanin shaawa tunda assadiq yaga aman ya dauke shi ya rungume saboda yadda dan ya shiga ransa safiyya ce tamiko hannu zata daukeshi assadiq yace

 

“aa sopy kema ki haifo naki babyn kide ki ko shikenan aure zanyi amaryar ta haifo min mai sunan dady

 

“Dee banaso ”

” to kiyi zuciya ki haihu ”

Su farhana dai dariya suke musu jalila ma ciki ya tsufa faruq ne ya shigo nan sukai masa caa suna tsokanar sa ango ango dariya yayi yace

 

” wlh kar kuga kunyi aure ubanku zakuci ”

 

” aa faruq ya da zagi kuma, karfa ka auro yar mutane kazo kana zaginta fa ”

 

” haba dai yaya assadiq ina ni ina zagin feena cab allah ya sawake ”

 

” ameen angon safeena ”

Cewar safiyya tafada tana karbar aman ahannun assadiq

 

Ranar suna baby taci sunan babar haisam wato khadija ansha taro yanuwan sa sunzo yankauye dasu kawai kallon su Afifa take

 

Su safiyya sun kammala shirin su tsaf dan tafiya dubai da saudi anbar su fadila a gidan momy safiyya taso akai hamra gurin muwadda assadiq yaki yadda tunda suka je safiyya takwanta rashin lafiya komai sai assadiq yaimata haka tai ta fama asibiti yakaita ana gwada ta aka gano tana da ciki na wata 2 watan su daya suka dawo

 

Wani alhjn birni ne ya zo neman auran muwadda fafur ki tayi saboda yadda taganshi

 

 

 

 

 

*NASEEBA GAWO*
👌🏻
[5:29Am,2017]

 

*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T <W >F*💦

 

 

*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NA*

NASEEBA I UBA 💐

 

 

*Alhmdulillahil Alhmdulillahil tammat bi hamdillah wa shukurullah mashaallah la kuwata illa billah*👏🏻

 

💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin*💦

 

 

*hakika burina yacika a yau ssabar 7/october 2017 bazan iya musulta farin cikina ba na kammala kannan mijina ba sai dai in kuma cewa alhmdulillah abinda muka karanta Allah ya sa mu amfana wanda nai kuskure Allah ka yafeni*😍👏🏻

 

 

*🔚100🔚*

 

💙
*Dedicated 2 all kannan mijina fans all over the world*💙

 

 

~~~Alhj namadi dariya yake wa muwadda musamman yadda ya ganta yar gayu ita kuwa dada tsuke fuska tayi ahaka ta karaso gurinsa taja ta tsaya dubanta yayi yace

“ranki ya dade gimbiyar mata jarumar mata sarauniyar mata mata a gidan Alhj namadi in Allah…….

“Heee, dakata haba malam meye haka, ya kuma haka, wacce irin magana kake son furta min, nashiga uku ”

” Allah sarki baby kiyi hakuri so da kauna ce ta kawo ni gurin ki kuma auran ki zanyi ”

 

Shigowar abbanta ne yasa ta tayi Shiru karasowa yayi dan shiga parlorn sa da sauri Alhj namadi ya tsuguna ya gaida abbanta muwadda kam ciki ta shige

Abba ne ya dube shi yace,” sannu ko, meye manufarka akan yata”

“Auranta zanyi alhj”

“mashaallah, zanso jin taeihinka ”

” to badamuwa, ni sunana Alhj namadi ni dan kasuwa ne a kasuwar kwarai ina da mata 2 da yaya shida ina zaune a sharada ”

” to yayi, ba laifi, abinda nake so da kai shine ka turo magabatan ka dan ku ba yara ba ne ina fatan ka fahimta ”

 

” nafahim ta Alhj na kuma gode sosai inshaallah cikin satin nan zan turo ”

” yauwa, allah ya kaimu ”

Sukai sallama ya shiga ciki alhj namadi ya shiga motar sa ya tafi cike da farin ciki samun nasarar auran karamar yarinya

 

Tunda da abban muwadda ya shaida mata ya bawa Alhj namadi auran ta take kuka gashi yanzu son assadiq take kamar hauka maman ta ce tazage tai ta masifa yai mata kaca kaca dataji fadan yai yawa taja bakinta tai shiru

 

Abangaran safiyya kuwa tana kwance tana fama da laulayi ga final exam ta taho yau yini tayi tana amai ga assadiq ya fita tana kwance a daki taji Shigowar sa, sanda ya shigo parlorn su fadila suna zaune da saddiqa fadila na koyawa hamra homework suna ganin sa suka tashi suka rungume shi duban su yayi yace

“fadilaty binty, ina mamma, ko jikin nata ne “?

” A papa, gsky akai ta asibiti mamma na fa tana jin jiki ”

” Ayya, zan kaita inshaallah, hamra ya jikin mamma ”

” Ba sauki papa, yau fa amai tai tayi ”

Dariya suka yi saboda sun saba da shirman hamra gabuwa ce da kaganta kaga yar fari tashi yayi ya shiga dakin safiyya tana gado a kwance gaban gadon ya karasa ya zauna jikin sa yajata ya zuba mata ido ita kuwa lumshe ido tayi saboda dadin turaran sa dataji a hankali ya kira sunanta

“sweet sopy ya jikin ki fadilaty tace kina ta amai hakane ”

” Dee, dama bansami Cikin nan ba da yanzu ina nan ina harkoki na ko”

“haba sopy akan me zakice haka ni da nakeso ki haifa min yaya dozin ”

 

” Dee so kake inmutu ko, ka gaji dani ko kaduba fa kaga yadda nake shan wahala kuma kace sai nayi dozin , ni yanzu ya zanyi da Exam din da zamu fara ”

” haba sopy ta yaya assadiq zai so ki mutu ai tare zamu mutu baki san bazan iya rayuwa bake ba, maganar exam kuwa inshaallah zaki iya kinji, yanzu mezaki ci akawo miki “?

” Dee banason cin komai komai wari yake min, turaran ka kawai nake son shaka ”

Hmmm sopy kenan sarka mai rikicin gan gan, turare na kike so bani ba ko”

 

“Dee to ai kaine mai rikicin gan gan daga cewa ina son qamshin turaran ka sai ka juya min magana ”

” shikenan dai yanzu me zansamu sweet sixteen”

 

“Dee tun yau she natashi daga sweet 16 kuma ”

 

” wa yafada miki haka ai bakya tsufa a gurin assadiq, yanzu dai abani agajin gaggawa dan dab nake da shiga wani hali ”

 

Shiru tayi kamar bataji shi ba ta runtse idonta saboda yadda take tsoron haduwar ta da shi baya saurara mata amma bayadda zatayi haka ta daure tabashi hakkinsa amma tasha kuka saboda yadda ta jigata be san ma tanayi ba sai da komai yalafa sannan yaga yadda take kuka dariya yayi ya dada jan ta jikin sa yana shafa gashin kanta yace,

 

“sopy waye yasa min ke kuka bayan baby na yana wahalar min dake ”

 

Hararar sa tayi tare da turo baki tace

 

” bayan assadiq ne ya kasa yimim afuwa bisa halin danake ciki ”

 

Dariya tabashi sosai tashi yayi ya shiga toilet ya hada musu ruwan dumi yazo ya kama hannunta suka nufi toilet dan yin wanka

 

Kwanan su jalila 6 da komawa abuja Dr yana kitchen yana girki ita kuma tana parlor tana kallo taji marar ta da bayan ta sun daure ga wani azababban ciwo kara tasaki wacce ta gigita Dr yafito da sauri cikin tashin hankali ganinta yayi a durkushe nan yakama ta ya shiga yi mata sannu gumi akwai takeyi ba shiri ya dauketa ya kaita asibitin da yake aiki cikin Kan kanin lokaci aka shigar da ita dakin haihuwa da taimakon sa dana abokan aikinsa jalila ta haifo danta namiji fari tas dashi ko gyara dan baayiba Dr ya dau dan ya rungume shi har da kwallar farin ciki jalila kam tana kwance saboda yadda ta sha fama nan aka kimtsa mai jego da baby aka kaisu dakin hutu

Waya yayi wa ummin sa yafadamata haihuwar. murna tayi tace lallai yakawo ta kano gobe yaamsa da to sukai sallama. Nan yaita kiran wayar yan uwan sa yana fada musu

Washe gari da sassafe suka shirya sai kano tun da suka dau hanya take bacci tana rungume da baby hankalin Dr yarabu gida 2 yana Kan tukin da yake yi yana Kan matar sa da babyn su ahaka suka karasa kano kai tsaye gidan su yakaita momy tai ta murna nan aka shiga hidima su safiyya sunzo ganin baby najiba kuwa kullum sai tazo momy tai ta tsokanar ta sai tai ta dariya

Ranar suna yaro yaci sunan baffa suna kiransa da fahad nan momy taci gaba da kula da maijego

 

Bikin faruq yazo ankai lefe na alfarma baki yarage saura kwana 2 anata shirye shirye

Ranar alhmis safiyya ta hada masa dinner ita tayi komai anci ansha ango da amarya sunyi kyau *kannan mijin*safeena da safiyya sai jansu suke da wasa yaya hannatu sai dariya take musu akai lafiya aka gama lafiya ranar daurin aure assadiq da faruq sunci shadda iri daya sunyi kyau haka nabil da ashraf sunyi kyau sunsa shadda iri daya da su fadila gwanin shaawa

Andaura auran faruq da safeena akan sadaki 100k

Da yamma aka kawo amarya gidan ta kusa da na assadiq bayan ankawo ta ganin su assadiq

Amarya suna zaune lpy da safiyya da *kannan mijinta* faruq bayajin kunyar makalewa matar sa ko agaban waye suyi tamasa tsiya

 

Muwadda ta tare a gidan Alhj mai kudi gidan mata 2 ita ta uku gidan balai dan matan akwai kishi ga yayan nasa basu da mutunci shikuma kulle ne dashi baa fita haka dai take zaune abin tausayi

 

Safiyya ta haifi danta namiji kykkyawa murna gurin assadiq da su fadila baa magana safeena ce kullum take shiga gidan safiyya take tayata aikin gida ranar suna yaro yaci sunan dady wato muhammad suna kiransa da *little* fadila kam tana kiran sa da

*didi* tun tana fada safiyya tana hanata har ta hakura ta kyaleta

*BAYAN SHEKARA*
*3*

 

DUK wata nasara da mace take fatan samu a gidan aure safiyya tasamu domin ahalin yanzu safiyya tazama hanshakiyar mace ga kudi ga ilimi dan anbata kwamishinan ilimi suna zaune cikin kwanciyar hankali da mijinta

 

Fadila ce zaune tana duba wasu takardu nabil ya shigo Cikin shiga ta alfarma tana ganinsa gabanta yafadi saboda yadda ya matsa mata da maganar aure karasowa yayi ya tsuguna a gabanta ya kira sunan ta a hankali

“habibty fadilaty ”

” ayya nabil barka da zuwa ya ummata da ashraf”

“umman ki lpy, *kanin mijnki* kuma yana A B U zariya ”

” yaya nabil banaso fa ashiraf ne *kanin mijina* shigowar litile ne yakatse wa nabil maganar da zaiyi bayan sa ya labe yayin da hamra ta biyo shi a guje tace

 

“yaya fadila kinga litile ko, wlh sai na dakeka”

“hamra, meyai miki, wlh didi sai na zaneka akan tsokana ”

 

” wlh yaya fadila itace take tsokana ta ”

” pls hamra kidena tsokanar sa ”

Cewar nabil Shiru hamra tayi ta zunbura baki ta tafi gurin safiyya

 

Yau gidan alhj muhammad mai nasara cike yake da yaya da jikoki suna taron taya safiyya murnar bude islamiya da tayi assadiq ne yajata jikin sa akai musu hoto gaba daya gurin tafi akasa a kunyace tace “Dee rankwafowa yayi yace

” yes, sweet sopy, sopyn assadiq. Maman fadilaty da hamra da muhammad assadiq muhammad mai nasara ”

Dariya tayi taja yayan ta dana *KANNAN MIJINTA*ta rungume a hankali ta furta *ALHMDULILLAHIL*👏🏻👏🏻👏🏻

 

NASEEBA ma tace alhmdulillah dan bani da kalmar da zan furta wajen godiya gareku masoyana sai dai ince Allah yabar love 💙💙💙💙💙💙

💦💦💦
*TALENTED WRITTERS FORUM hakika kuncika yan halak domin da bazar ku naseeba ta taka rawa up up up TALENTED WRITTERS*💦💦💦💦

Godiya gareku

TALENTED group fans

KANNAN MIJINA group

Aisha garkuwa group

Sadiya smart group

Kiyaya 2009 group

Munemi aljanna group

Ummi Aisha group

Da sauran groups din da naseeba bata ambata ba 👌🏻👌🏻

 

Sai kunji ni a sharhi game da littafin *KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧

 

*NASEEBA GAWO*

 

NASEEBA GAWO✍🏻

 

“`I need ur prayer sisters I am sick“`😰🤦🏻‍

*NASEEBA GAWO*✍🏻

*NASEEBA GAWO*✍🏻
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)

WHATSAPP NO:
+2349030159301