A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 1

Sponsored Links

Book 02*

Page 01

Cikin mugun mutuwar jiki kasala da kuma fargaba ta hada kalmomin

“Wacce irin matsala kuma umma?,na shiga uku”

“Malam baiga komai akan yarinyar ba,komai ya rufe masa,bai hangi ciki ba,kamar yadda babu tabbacin babu shi”.

Goshinta hafsat ta dafe,tana jin yadda zuciyarta ke tafasa,a zahiri tayi mugun tsanar yarinyar,ta zame mata qarfen qafa sosai,tanason kuma ta zama barazana ga rayuwarta,cikin tsananin fusata tace

“Umma,yayi mata koma meye,duk abinda ya dace da ita da zai d’ai d’aita rayuwarta ayishi,banason ganinta kwata kwata cikin gidan nan,yanzu haka fa abban mimi ya biya mata hajji,aikin hajji zasu tafi” ta qarashe maganar tana barkewa da kuka,don abun yayi mata ciwo ba kadan ba.

Salati umman tata ta sake kamar tana gaban hafsat din

“Kina raye kina kallo?,lallai sai munyi da gaske,sai mun tashi tsaye akan yarinyar nan”

*A B B A S*

“Ya salam” ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki, kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare da samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad.

Ido suka hada shi da ita,ta narke fuska sosai,dab take da sakin kuka,suna hada idon kuma sai rauninta ya bayyana muraran,yasan tabbas yau akwai daru,amma koma meye a shirye yake daya shanyeshi,ciki a jikinta?,cikin da yasha yi mata wayo yana gaya mata ba tarayyarsu ce zata saka tayi ciki ba,shan ruwa a qoshi ne?,yasan lallai zai sha tuhuma.

Hannu ya miqa mata alamun ta taho har yanzu murmushi kwance bisa fuskarsa,amma sai ta kauda kai hawaye na ziraro mata,yasan za’a rina,yau saita Allahu,ya dinga danne dariyarsa sannan ya.miqe tsam ya isa gabanta,ya tsaya daga gefanta yana riqe da hannunta yana murzawa a hankali cikin nasa,idanunsa akan na dr

“Yanzu ya za’a yi?,ina fatan bazai bada matsala ba wajen tafiya”

“Bana jin gaskiya,zanyi qoqari ayi mata komai ku wuce tare,tunda bai nuna ba” ta fada ita kanta tana mamakin watannin cikin,da kuma yadda ya boye kansa da kyau,iya ganinka ba zaka hangeshi jikinta ba.

Komai da akeyi kawai tana binsa da ido ne, hankalinta gaba daya bai jikinta tunda akayi zancan ciki,tsoro da fargaba gaba daya sun hadu sun lullubeta,har suka gama komai yana riqe da hannunta,ya bude mata gaban mota ta shiga ya maida murfin ya rufe ya zagaya mazauninsa shima.

Ai yana shiga tana fashe masa da kuka,kamar wadda ke jira,ya dakata daga kunna motar ya waiwayo yana dubanta

“Ya salam ya Allah…..menene kuma?,ko wani abun na miki ciwo?”

“Wallahi idan abba yaji ka yimin ciki sai ya kashemu ni da kai” duk yadda yaso ya riqe dariyarsa amma wannan karon ya gaza,dariya ta kubce masa,har sai da yasa zara zaran yatsuntsa ya toshe bakinsa kada cibi ya zama qari,sai yaushe zata gama girma ne?,ashe har yau da sauran quruciyar nan tana nan?,ta yaya zai bullo mata,sai kawai ya juya fuskarsa zuwa kalar alhini shima yana dubanta

“Innalillahi……yanzu ya kike ganin za’a yi?” Da farko dariyarsa ta qular da ita,amma yanzun maganar da yayi saita wanke wancan

“Nima ban sani bafa….duk kaine ka jawo,saida nace banaso,kace wai idan nasha ruwa ne zaizo” ta fada yana harararsa,saiya narke fuska kalar tausayi ya langabar da kai

“To ai nima na zata hakanne,kuma ma kinsan me?” Kaita girgiza tana sharar qwalla,sai ya juyo yana fuskantarta sosai

“Sanda kika gudu kano?” Saita gyada kai tana dubansa

“Abba da kansa ya kirani yace nayi wannan abun fa da bakiso din” dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu fado tana kallonsa a tsorace,ya jijjiga mata kai

“Da gaske nake” ya sake fada yana danne dariyarsa,bai ankara ba ya takai masa duka tana sake fashewa da wani kukan a sakalce

“Allah abbana ba dan iska bane da zaice maka haka” sosai yau din take sashi dariya,ya kare dukan da daya hannun yana dariya tare da fadin

“Allah…..Allah kinji nace Allah” ta sanshi farin sani,kaifi daya ne,baya qarya,yana fadin hakan sai kunya ta kamata,ta kifa kanta a cinya tana juya yadda abban nata zaice haka,yanzu.kowa.kenan yasan abinda suke aikatawa?,tana jinsa yanata magana amma bata dago ba bare ta amsa,yana dariya qasa qasa ya tashi motar sukabar asibitin,ransa fes,zuciyarsa qal,wani farinciki daya jima rabon da yaji irinsa ya cika masa zuciya,har hakan yana bayyana kansa saman fuskarsa.

Saida sukayi nisa a tafiyar yace

“Kona ajjiyeki gidan hajiya?” Ya fadi hakanne saboda yadda yaga sam.batason zaman gidan nasu,saita girgiza kai da sauri

“Aah,nidai ka kaini gida” murmushi ya subuce masa,ya gane mai take gudu,kada hajiya ta gano tana da ciki,daga haka yabar zancan ya dauke kan motar suka nufi gida.

Sanda ya tsaida motar da kansa ya dauki hand bag dinta yana riqe da ita zuwa ciki,ta langabe kai tana kallonsa

“Ka bani,zan iya dauka” kai ya girgiza idanunsa cikin nata,yana jin wata qaunarta tana fusgarsa

“Ban yarda ba baby,dama naji a jikina,wannan rashin lafiyan akwai dalili,muje kawai,ko na daukeki?” Ya fadi shima yana langabar dakai,kunya ya bata,ta kauda kanta gefe tana gulmarsa cikin ranta,wai shi kam bayajin kunya ne ma wai?,kamar ba ciki yayi mata ba?.

Kamar yasan maganar da takeyi ya saki murmushi kadan,ya kama hannunta ya matsa kadan yana cewa

“Muje baby”.

Sanda suke shiga din akan idanun hafsat dake tsaye bakin window,tunda suka fita ta kasa zama,zuciyara nata qiyasta mata gurare daban daban da zasu iya zuwa,tana goye da shukra dake ta faman rigima,ji take kaman ta yago yarinya ta ajjiyeta,qunqunin yarinyar har tsakiyar kwanyarta,idanunta suka sauka kan handbag din widad da hannayensu dake sarqafe waje guda.

Wani matsanancin qunci zuciyarta ta shiga,duk yadda taso daurewa amma ta kasa,ta saki ashar,kasheta mutanen nan sukeson yi?,bayan abinda abbas din ya aikata mata shine zasuci gaba da sabgarsu kamar ma ba’a yi mata komai cikin gidan ba?,ba zata iya dauka ba,dole kowa yasan an tabota,sai kawai ta kunce yarinyar ta aza saman kujera ta nufi qofa da wani irin mugun sauri.

Idanunsa ya lumshe kadan,yana tsaye saman kanta yana mata wani duba dake cike da shauqinta,ko yaya ta motsa sai taja hankalinsa

“Zan dan fita,amma bazan jima ba zan dawo,me kike buqata?” Ya qarashe fada yana ritsata da idanunsa masu matuqar kwarjini da jan hankali,sai tadan rufe idanunta kadan ta girgiza kai

“Babu komai”

“Really?” Ya tambayeta yana dubanta,kai ta sake gyada masa

“Okay…..zan tafi” ya sake maimaitawa,saita sake lumshe idonta,tasna me.yakeso,amma jikinta a mace yake murus,ta gyara zamanta sosai ta nutse cikin kujerar sannan tace

“A dawo lafiya”

“Au ‘yar hakace yau?” Murmushi tayi kawai tana boye fuskarta,saiya saki wani murmushin,ya duqa kadan a tausashe yayi kissing goshinta sannan yace

“Take care of yourself” kai ta jinjina,sai daya juya sannan ta bishi da kallo,zuciyarta na gaya mata wai da gaske ba abun kunya sukayi ba,ta dora hannunta saman cikinta a hankali tana shafawa cike da mamaki da kuma tsoron cewa wai ciki ne a jikinta.

Dai dai sanda muryar hafsat ta ratso har cikin falon nata da wani irin amo,sai ta bude idonta a hankali tana saurarenta sanda take magana cikin rawar murya

“Wallahi bazan yafe wannan zaluncin ba,sai Allah yayi min sakayya” wani mugun tsaki widad din taja tana tabe baki gami da gyara kwanciyarta cikin kujerar,ita gaba daya mutuncin matar ya gama zubewa a idanunta,tunda take bata taba ganin yadda akema babba rashin kunya ba kamar yadda itadin taga tana yiwa abbansu mimin,ko babu komai aiya girmeta,kuma ko ummu da take tsohuwa ai tana ganin yadda take girmama alhaji,har tabar gidansu bata taba gani ta karba abu daga hannunsa daga tsaye ba,ko ya fada tace a’ah, miqewa tayi cak tana daukar jakarta ta wuce bedroom dinta,haka kawai taji batason jin wata hayaniya kusa da ita.

Hannu daya abbas ya sanya cikin zallar bacin rai ya fincikota,ya riqeta gam yana tafe riqe da ita,bai tsaya ko ina ba sai da yakai sassanta ya watsar mata da hannun cikin falon,da yatsa ya nunata

“Wannan ya zamana shine lokaci na qarshe da zaki qara gangancin cewa zaki shiga sashenta ko zaki tabata,daga lokacin da kikayi wannan kuskuren zaki fahimci baki da wayo,tunda na fahimci sauna ce ke shashasha wadda batasan girmanta ba” sosai maganarsa ta doketa kamar saukar mashi saman zuciyarta,ita din abbas yake cewa sauna shashasha?

“Kowanne suna kakeso ka kirani dashi,daidanka ne,amma bazan fasa neman haqqina ba”

“Idan kika fasa neman haqqinki kin raina Allah” kalmar da tasa ta bishi galala da kallo har ya fice,sai ta sake fashewa da kuka,dole tayi iya yinta taga ta tarwatsa farincikinsu,ba zata zauna ita kadai bacin rai ya hallakata ba.

Yana tafe zuciyarsa cike da bacin rai,mahaifin hafsat shi daya yake tunawa,mutumin kirki da kowa ya yaba halayyarsa kafin barinsa duniya,yana sonsa yana girmamashi,har yau yana tuna haquri na qarshe daya bashi a kanta kafin barinsa duniya da ‘yan awanni,yaja wani dogon tsaki,xuciyarsa na ayyana masa hukunci kala daban daban da zai iya dauka a kanta.

A hankali kuma yaji yana sauka musamman daya tuna kyautar da Allah yayi masa a yau daga wajen halitta mafi soyuwa cikin rayuwarsa,sai yaji dukkan haukan hafsat din wani abune mara muhimmanci da zai iya tattarasu ya watsa kwandon shara,idan ta gaji ta sauke kamar yadda ta saba.

*******Cikin kwanakin da sukayi cikin gidan kafin tashinsu saudiyya dan qaramin yaqi aka dinga gwabzawa tsakanin abbas da hafsat din,kullum cikin kuka qorafi da masifa,dai dai sanda ‘yan abun nasa suka motsa(miskilanci),yayi watsin tsiya da ita,tamkar ma ba dashi take ba.

Ta fannin widad ma sai tayi kamar batasan me ake ba,dama ita dimma ba baya bace wajen miskilancin,bare a yanzun da take mugun jin xafin mummy hafsat din haka kawai,ta tsani ta ganta tare da uncle din nata,tana dannewa ne tayi kamar bai dameta ba tunda batasan ainihin me yasa takejin hakan ba,uwa uba ko meye zatayi saidai ta jiyota daha sashensa sashenta ko.farfajiyar gidan,bata doso sassanta,wannan yasa bata dameta ba,a kullum tunaninta da zuluminta sanda kowa zaisan tana da ciki,cikin wata irin wauta dake sanya abbas din ya qunshe kansa yayita mata dariya,a fuska kuma ya tayata jimami da alhini kamar gaske.

A lokacin hafsat din ji take kamar zata mutu,yaqi kulata sannan widad din da taso rage zafi da ita ya mata shamakin da ko giyar wake tasha ba zata doshi sassanta ba,ta sanshi farin sani,yana da kawaici yana da alkunya,amma duk sanda ka sake ka turashi inda bai kamata ka turashi din ba…..to kuwa abinda zai biyo baya bashi da sauqi.

Duk haukar da hafsat din keyi hakan bai canza komai ba,don kuwa kwanakinsu biyar suka wuce kano,kai tsaye kuma sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na mallam aminu kano.

Sosai widad din tayi mamakin ganin ‘yan gidansu acan suna jiransu,tayi farinciki sosai amma kuma abinda tasan tana tattare dashi ya hanata sakewa,sai qumbiya qumbiya takeyi,duk kuwa da cewa cikin abaya sakakkiya take da hijabin daya tsaya mata iya qugu saqar qasar indonesia,wanda ya sake fitar da zallar kyanta da kuma yadda ta sake cika ta kuma sake yin kyau.

Duk wani motsinta yana kan idanun abbas har sukayi sallama da ‘yan gidan nasu,suka kuma bi ayarin tawagar mai girma governor din bauchi wadda kusan duka iyalinsa ne da manya manyan qusoshin gomnati da matayensu.

A darare take gaidasu saboda rashin sabo,uwa uba kusan duka sun girme mata,sa’annin yayyenta ne aurarru,saidai suna da tsananin kirkin daya gaza boyuwa,kallo daya zakayi musu kuma kasan wayayyun mata ne da suka goge da sanin rayuwa,idan akace wayewa bawai wayewa ta rashin kunya rashin da’a da rashin kamun kai ba,a’ah…….wayewa ta ma’ana da sanin darajar kai da kimar kai wadda ke gauraye da ilimin zamani.

Yadda yaga taqi walwala kafin tashinsu sai yaji duk ba dadi,tana tsaye batasan da isowarsa wajen ba

“Suma fa duk sunayi….. qila jiya da daddarema duk sai da sukayi kafin mu taho nan” abinda taji an fada kenan a kunnenta,da mugun hanzari fararen idanunta a waje ta waiwaya,duk da tasan duk duniya babu mai gaya mata hakan kanshi tsaye sai uncle din nata…..uncle abbas dinta,shi dinne,tsaye a bayanta dab da ita,hannayensa zube a aljihun wandon wata lafiyayyar suit da tunda ya sanyata ta gaza dauke idanunta daga kansa har suka iso nan,murmushi ne kwance saman fuskarsa yana jifanta da wani kallo da su kadai sukasan ma’anarsa,saita langabe kai a shagwabe tana dubansa gami da yi masa nuni da mutanen dake gabansu kadan tana masa alamar kada suji fa,kafadunsa duka biyu ya daga ya watsa hannayensa in i don’t care manner,ya sake matsowa kadan yana yin qasa da muryarsa

“Wannan tsoron naki xai sa kowa ya sani” ya furta yana duba agogon hannunsa

“Feel free,u are safe dear,okay?” Saita gyada a hankali,ya aika mata da wani murmushi na musamman sannan ya juya,saita sauke ajiyar zuciya ta bishi da kallo.

Batakai ga waiwayo ba taji maganar daya daga cikin matan mai suna hajiya sha’awa

“Badai har kun fara kewar juna ba?” Kunya sosai ta kamata,saita girgiza kai da sauri,kafin ta amsa mata sauran sun iso,cikin mintuna qalilan ta shige cikinsu ta kuma fara sakewa,saboda yadda suketa qoqarin janta a jiki tare da sakata a hirar su,hirar data dinga jin kamar ta girmeta,saboda hira ce ta manyan mata,amma ta qarfi da yaji haka suke sanyata a ciki.

 

 

Back to top button