Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 73

Sponsored Links

Page 73

A dan tsorace ta kalli matar,ganin kuma ita take kalla saita dake,don ita bata yarda ta fadi ba ako menene

“Bazan bayar bafa,ladan wahalar aikin da mukayi mata,nima idan tawa haihuwar tazo duka biyun haka takeyimin” dubanta matar ta sakeyi sosai,cikin bacin rai da daga harshe tace

“Haka ake taya aiki a kwashe maka abincin suna?,cooler guda saboda dan ke kafadai akayi girkin?,ku haka kukeyi?,don kun taya aiki sai kowa yace anan zaici abincin rana?”

“Sai kuma kiyita yi,don Allah ki fita kiban waje,mijina ya dawo”

“Au haka kika ce?,to wallahi saikin fito da abincin nan kuwa” nan sa’insa ta barke a tsakaninsu,tun sunayi iyasu har hayaniyarsu ta kaiwa abbas dake tsaye yana nazartar dakin hafsat din,yadda likkafara qazantarta taci gaba,ko ina pampers din nawwara da aka cire an kasa kirashi dust bin,ga zanin gadon dake saman gadonta a iya saninsa sanda ya siyoshi milk color ne mai kyau,amma yanzun ya tasamma zama ash color,naira dub ashirin da biyar ya siyeshi,kyansa da taushinsa ne ma ya burgeshi ya siya din,amma bazai iya tuna wani amfanarsa da yayi ba.

Jin hayaniyar tana yawa ya sanya dole ya ajjiye bag din hannunsa dake dauke da sweet din,ya juya zai fita a dakin yaga me yake faruwa,sai cabal qafarsa ya taka wani abu,yaja baya da sauri tsigar jikinsa tana tashi ya duba meye a qasan, kashi ne harda fitsari,yaja tsaki yana girgiza kai,dole ya juya akalarsa zuwa vabdakinta saboda ya wanke qafar tasa.

Da qyar ya samu ya hadiye yawu a bandakin,saboda urun bidirin daya gani,zarni tako ina,ga uban kashi cike cikin toilet din ba’ayi flushing ba, zuciyarsa ta fara tashi,yaji nadamae shiga bandakin,saboda qazantar bandaki tana daya daga cikin qazantar dake damunsa,baya qaunarta sam,haka ya wanke qafar ya fito yana qoqarin controlling kansa saboda sosai zuciyarsa take tashi.

Dif hafsat din ta dauke wuta sanda suka hada idanu bayan ya fito,baibi ta kanta ba,ya maida dubansa ga matar

“Me yake faruwa ne?”

“Yallabai,shinkafar suna ce,bayan sun gama aiki ta kwasota da yawa ta taho da ita,mutane nata zuwa babu,shine na biyota nace tadan rage a samu a sallami wasu, shikenan fa…….”

“Okay,shikenan” ya dakatar da matar daga rattabo masa bayanin da takeyi,shi kadai yasan abinda ya tsaye masa a wuya,bacin ran ya nuna har idanunsa

“Ina abincin?” Ya jefa mata tambayar murya a kausashe cike fal da bacin rai,muryarta a cushe tana ayyana irin rashin mutuncin da zata yiwa maqociyar tata tace

“Yana kitchen” baice komai ba ya juya akalarsa zuwa kitchen din.

Nan ma uban wanke wanke ne jibge a sink dinta,har wani tsami sukeyi,ya laluba da qyar ya gano wata warmer,ya janyo ya budeta saiga qudundunanniyar shinkafar a cuccure irin ta gidan suna tayi fuska abinta,ya daga warmer din ya juyashi,nasa ne da ake zuba masa abinci,wato tana nufin shi ta dibarwa?,shi zaici?,abincin gidan wani?,abincin da wani ya nemo a gidansa?,ba zata iya zama ta girka masa ba kenan saboda tsabar qwarewa a qyuya da kuma iya cin fuska?,ransa ya baci sosai,waye yasan tun yaushe take haka?,waye yasan irin b’arar masa da mutuncin da tayi,haka maqota suke kallonsa kenan tsirara?,ya jawo warmer din ya fito da ita.

A tsaye ya samesu matar na riqe da qugu,wani bacin rai ya sake tokareshi,shinkafar da ko masu aiki cikin gidansa sunfi qarfinta yau saboda ita aka shigo masa cikin gidan ake wanna tijarar

“Gashi” ya miqa.mata gaba daya,ta karba tana qoqarin juyewa ya daga mata hannu

“Jeki kawai”

“Flask din naku ba”

“Tafi dashi” sai ta saka flask din cikin robar ta juya tana bari wajen.

Ganin da gaske tafi mata zatayi da warmer dinta me tsada saita yunqura zatayi mata magana kan ta dakata ta juye ta bata abarta,wani kallo ya watsa mata wanda ya sakata dawowa da baya,ta kuma yi laqwas babu shiri

“Ina yarana?”

“Naga fa warmer din nan me tsada ne,sai kacw tatafi da ita?,idan kuma taje ta bata fa,kasan gidan suna” ta shigar masa da qorafinta a maimakon amsa masa tambayarsa

“Ina yarana nace?” Ya sake tambayarta wannan karon a kaurare

“Suna……a gidan sunan sukace na barsu”

“Kika barwa wa su?” Saita dan sosa kai

“Mai aikin gidan maman husna,tace zata kawosu idan……”

“Idan sun gama cin abincin gidan sunan suma?,saboda yunwacw fal a gidan ubansu?,maza maza kirata a dawomin da yara na,na baki minti biyar” yayi maganar yana murza yatsunsa,sannan ya juya yayi gaba yana barin mata sassan.

Da harara ta bishi,ai kuma shikenan ya dawo babu zaman lafiya ba sakewa,dole ya suri wayarta ta laluba number talatu tace ta dawo dasu abbansu ya dawo,tace tahe bayan layinsu da yaran amma gata nan

“Kiyi sauri don Allah”

“To” ta amsa mata,saita cire wayar daga kunnenta tana jan tsaki sannan ta wuce dakinta.

Sai data taka kashin daya taka ta tuna ma yadda dakin nata yake,ta dauki salati,tasan ya gani,kwata kwata ta manta a haka tabar dakin,harta fara gyarawa ta tuna qila da widad sukazo,sai ta yanke tayi kiranta

“Tazo ta kama aikinta,nima na samu na tsugunna na huta” daga haka ta figi mayafinta ta nufi sashen widad din.

Ta gama kintsa ko ina,sai fidda qamshi yakeyi,tsumman towel ne a hannunta tana goge nayan kallo da sauran glasses da abubuwan da suke. Daukan qura a falon,hafsat din ta turo qofar da dan qarfi,dama.ba kasafai ta fiya sallama ba har sai ta shigo falon, saboda tsabar zargi da ranta ke raya mata ko zata kama abbas a wajen(kamar wani kwarto ba matarsa ba).

Kamshin data shaqa ya riqe maya maqoshi da irin kishi ta gaza sallamar,widad ta daga kai tana dubanta,karon farko da taji ranta ya baci na yadda ta shigo mata ba sallama,ta riga ta saba,duk yawansu a gidansu,duk kuma yadda suke da ummu bata isa ta shiga waje kai tsaye ba sallama ba.

A yau itama saita riqe gaisuwarta,tana kallon yadda hafsat din kebin sassan da kallo kafin ta sauke dubanta ga widad,hatta sassan ya sauya mata,bare widad din dake qara wani irin girma da haske

“Sannu isassa, shigowar da kike nasan kinzo yau ban isa ba kenan,shine kikazo nan kika kama.naki aikin ni kin barni da tulin aiki,to ki gayamin waye zaiyi miki aikin?” Maganar ta dan baiwa widad din haushi,sai kace ita ta hada mata dattin ko tace ta dinga barinsa,ci gaba tayi da goge gogenta sannan tace

“Gani nan zuwa” tsaki hafsat din taja,ganin yadda taketa qalqale komai na wajen,ta danyi jim sai kuma ta juya ta fita,ta tsani ta shigo sassanta taga tana wannan qaqale qaqalen

“Wannan dole na sake matsa miki lamba tare da sanya idanu sosai a kanki,idan ba haka ba fin qarfina gaba zakiyi” ta raya haka a ranta.

Haka kawai yau saita samu kanta da jujjuya abinda mommy hafsat din tayi mata a rai,sai taji bataji dadin abinda tayi mata ba,amma sai ta danganta hakan da rashin sallamar da batayi mata bane yafi bata ranta.

Koda ta gama saita wuce bedroom dinta,ta canza kayan jikinta zuwa wata smocked gown me skinny straight skert da yasha tsaga ta baya,ta daure sumarta mai tsaho da santsi cikin dankwalin kayan.

Sassan abbas ta wuce,don bata manta ba sunyi dashi zata gyara masa,zuwa yanzun kuma tasan umarninsa da aikinsa sama yake dana hafsat din,kamar yadda ta taba yiwa anty madeena tambaya,ba kamar a baya ba,da takejin umarnin mummun hafsat din sama yake dana abbas dama kowa dake cikin rayuwarta.

Sanda ta shiga yana zaune saman kujerar parlor yana amsa waya,ya kasa dauke idanunsa daga kanta,saboda taja hankalinsa sosai,ta sakar masa murmushi ganin waya yakeyi,ta kuma masa nuni da hannunta kamar maganar kurame akan ta ina zata fara?.

Idonsa ya lumshe sannan ya budesu a kanta,ya mata nuni da falon,he wants to keep his eyes on her,saita tako zuwa ciki a hankali ta soma kintsa wajen.

Duk inda ta motsa idanuwansa suka biye da ita,kamar yadda duk sanda ta gifta saita bar masa qamshinta,wani irin yanayi ya dinga sauka a jikinsa,da qyar ya samu ya kammala wayar,sai ya ajjiyeta daga gefansa yayi folding hannayensa a qirjinsa yana kallonta sanda mopping parlor din da mopping mist dinta data taho dashi,lallausan qamshin daya saba ji a sassanta ya fara game nasa falon,yana sin qamshi yana son qamshi har baisan iyaka ba,tsafta na daya daga cikin abubuwan dake bashi nutsuwa a rayuwarsa,sai ya samu kansa da miqewa a hankali,ya isa gareta,ya kama mop stick din ya riqe,hakan ya sanya hannayensu gamuwa waje daya,ta daga manyan fararen idanuwnata suka sarqe da nashi waje daya.

Har cikin jikinta taji wani abu ya tsarga mata,sai ta sakar masa sandan taja da baya tana murmushi

“So kake ka tsoratani?,banji tahowarka ba Allah” tayi maganar tana yarfe hannunta kamar wadda ta riqe wani abu me zafi

“So nake na samu ladan sunnan taya matata aiki” kalmar tasa ta bata kunya,saita sunne kai cikin dankwalinta,ya daga kai yana murmushi,yana son yaha reaction na fuskarta da yadda ta karba maganar.

Tana biye dashi yana mopping din,kuma shine yace ta dinga binsa din,wajen da bai gogu ba ta gaya masa,yayi hakanne kawai saboda nutsuwar da zuciyarsa ke samu kasancewarta a kusa dashi.

Tare suka gama aikin,har cikin bedroom da toilet dinsa,ta kwashe zanin gadon kai ta sauya masa da wani bayan ta turarashi a kabbasa,ta maida komai muhallinsa,sai ya dinga jin zuciyarsa wasai,gyaran yayi masa fiye da yadda ma yake so.

“Ga tukuici” ya fada yana miqa mata wani siririn agogon silver da aka masa ado da dan wani dige digen gold a jiki,yana da tsada sosai,hafsat ya taba siyawa gift dinsa,amma har yau ya kasa bata,saboda ta kasa bada kyakkyawan yanayin da zai gabatar mata da kyautarsa,duk sanda yazo da niyyar bata sai wani bacin rai ya gifta da zai sashi ma mantawa da hakan.

Ido ta fidda sanda ta ciro agogon,yayi masifar burgeta

“Uncle…..duka nawa ne?” Ta fada da wani irin accent dake nuni da zallar quruciya,kai ya jinjina yana murmushi

“Yes,kin manta abincin da kikayimin last three days?,dama nace miki akwai gift,na hada miki harda na ranan” dan tsalle tayi,ta isa gabanshi ta riqeshi tana cewa

“Thank you uncle,na gode sosai” ajiyar zuciya ya saki saboda riqon data yi masan yasan yanzun zai bada reaction a jikinsa

“Is okay” yana kallonta tana ficewa a sassan riqe da agogon,fara’ar fuskarta ta gaza daukewa.

Da baya ya koma ya zauna saman gadon,tana ci gaba da haifar da wani yanayi mai girma da nauyi a zuciyarsa,how can he continue looking at her a mazaunin matarsa?.

Sai data koma sassanta ta ajiye agogon sanann ta wuce part din hafsat,tana hanya tana tunanin inasu mimin da bataji motsinsu cikin gidan ba.

Dai dai lokacin da hafsat ta cika ta batse rashin zuwan widad din,zuciyarta ta fara mata saqe saqe,lallai tayi sake,har ankai matsayin da zata taka ta kirata ammaa ta bata kusan awa guda batazo ta fara mata aikin data sakata ba?,anya kuwa bai aikata wani abu da yarinyar ba wanda ya sanya ta fara rainata ko qoqarin yi mata gani gani?,baiko daidaita matsayinsu ba a shimfida?,amma tana tantamar hakan,tasan abbas tasan lalurarsa tass…..ko dai itace ta fara sanyi da saken daya fara kawo wannan canjin daga yarinyar?.[3/16, 10:18 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: huguma*

Leave a Reply

Back to top button