Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 64

Sponsored Links

Page 64

Shi kadai yasan yadda yayi surviving wannan daren,ya azabtu da yawa,daga baya da yaga ba sarki sai Allah dole ya zareta daga jikinsa bayan yaji saukar numfashinta tayi bacci.

Ya dade yana kai komo,zuciyarsa na gaya masa ya aika abinda zai samu sassauci,to amma yana tuna abinda zaije ya dawo,har yanzu ya tabbatar bata gama sanin meye aure ba,bugu da qari rainon zuciyarta yakeyi,baida tabbacin soyayyarsa a ranta,beside ma hajiya na gidan,bai kamata haka ta kasance ba a karon farko.

Sai wajen biyu na dare ya samu kansa da qyar,da kansa ya zabi kwanciya a qasa,zuciya da ruhinsa cike fal da tunani,wannan din ba komai bane sai kasawa da gazawar hafsa,bai taba zuwa mata weekend ko tafiya irin wannan ya samu irin tarbar da yakeso ba,bai taba dawowa sun rabu lafiya lau da ita ba,duk yadda kuwa zaikai gakai zuciyarsa nesa da dauke kansa,ya tabbatar inda ya samu ko yana samun yadda yakeso daga gareta,duka hakan ba zata faru dashi ba,saidai kuma ajizanci irin na dan adam.

Kusan tare suka tashi sallar asuba shi da ita,abu na farko data fara tambaya tun batayi alwala ba shine lafiyarsa,ya jikin nasa,ya saki murmushi yana jin dadi hat xikin ransa,saboda baisan da kalar wannan kulawar ba,yana iya yin ciwo har ya warke hafsat din bata sani ba saboda tsabar rashin kulawa irin nata

“Na warware alhmdlh”

“Sannu uncle,Allah ya sawwaqe”

“Ameen” ya amsata yana murmushi,da gaske yarinyar ce,wadda aka raineta bisa tsaftataccen tarbiyyar da har batasan meye ainihin ma’anar aure ba,batasan sha’awa ko wani abu daya danganceta ba,abu kadan ta sani wanda baikai girman da zai shiga tunani ya lalata mata rayuwa ba, tashin farko da yaji rashin sanin meye aure da batayi ba bai wani dameshi sosai ba,saboda wannan shine yake basji guarantee na cewa ita din mai tsaftataccen tunani ce da batasan komai ba,zaiyi dashensa yayi shukarsa ya kuma yi girbinsa yadda yakeso kenan.

Tana kan abun salla tana tunanin me zata dafa da safen,wayarta da tayi qara ta katse mata tunaninta,ta tashi ta dauko wayar tana duba me kiran

“Mommy hafsa da safen nan?” Ta tambayi kanta gabanta yana faduwa,sai a sannan ta tuna a dakinshi fa ashe ta kwana,ko wani ya gaya mata ne?,wannan tunanin ya hanata daga wayar har ta katse.

Iska mai zafi hafsa dake tsaye cikin dakinta ta furzar,ta daura alwalar amma ta gagara tayar da sallar,ta manta gaba daya gidan daki biyu gareshi,hakan yana nufin hajiya na daki daya,ita da abbas dinta zasu kwanta daki guda shimfida guda?.

Ko yanzun data kiratata bata daga ba, zuciyarta na kissima mata qila a daren jiyan ya samu yadda yakeso ne,babu yadda take shi yasa ta gaza daukar wayarta,wannan tunanin ya tashi hankalinta,ta koma gefan gadon ta zauna ta shiga jera mata kira ba qaqqautawa.

Abin da ya sake tsorata widad kenan ta kasa daga kiran,lallai tasan a dakinsa ta kwana,kuma tambayar da zata mata kenan tunda taketa kira,sai ta ajjiye wayar tana kallonta gabanta yana ci gaba da faduwa,har zuwa sa’ar da abbas ya dawo daga sallah,ya buda qofar dakin ya shigo.

Idonsa akan wayar,don itama ita take kalla,hannunsa zube a aljihunsa ya qaraso,ya dauke idonsa daga kan wayar ya maida kan fuskarta,saita dan dauke kai tsoron kiran da ake mata,da kuma kunyarsa suka hadar mata

“Ina kwana?”
“Kin tashi lafiya?”
“Lafiya lau ya jikin naka?” Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana sakin murmushi, lallai quruciya na damunta da gaske

“Da sauqi,na warke” kai ta jinjina masa,sai ya sake duban wayar

“Ba kiranki akeyi ba ki daga” fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin

“Ina zuwa?” Waiwayowa tayi

“Xanje gaida hajiya” sai ya gyada mata kai kawai.

Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama.

Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare.

Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za’a nuna a jiki.

Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura.

Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice.

A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu’o’i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu’arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu’ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin.

Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama.

Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba’a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din.

Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna

“Bakiyi bacci ba hajiya?” Sai tayi murmushi

“Banyi ba,ina dai shiri”

“to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita”

“Komai a kammale yake”

“Ma sha Allah…..shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe”

“To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya” sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad

“Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku” dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita.

A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito.

Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka.

Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri.
[3/14, 7:17 PM] +234 816 133 8078: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button