Gidan Aunty Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 45-46

Sponsored Links

BOOK 1📕

Page 45_46 💖

Shigowa dakin da akai ne yasa ta saurin share hawayenta ,Sabida kamshin turarensa daya cika mata hanci, da sauri sauri zuciyarta take bugawa ,har yanxu kuma ta ki yadda ta bude idanuwan nata,ta gefan ido ya dan kalleta,be ce mata komai ba sai wayarsa da ya dauka ya fita daga dakin, kara turo kofar da akai akaro na biyu ne yasata saurin dagowa kamar me shirin yin magana ,wacce ta gani ce yasa ta saurin sunkuyar da kanta kasa wata iriyar kunya na kamata,karasa shigowa ciki mahma tayi tana sakar mata murmushi,”daughter ya jikin naki”, cikin jin kunya ta amsa mata “da sauri”tana dan wasa da yatsun hannunta,wani murmushin mahma ta sakar mata”nasan kin gaji ko,abeey zai tanbaya king ko zamu koma gida ,Inyaso sai ki fi hutawa acan kinji”,yanxu ma wasa take da yan yatsun hannunta kafun ta amsa mata da “toh”,suna cikin wannan zaman ummey ta shigo dakin,kallan ta mahma tayi” Ta karaso kuwa” girgiza mata kai ummey tayi “tace zata zauna a Abuja zuwa jibi sai ta karaso” gyada mata kai mahma tayi “Allah ya kawo ta lapiya “, Ameen suka amsa gabaki dayansu kafun ummey ta kalli tahee da tunda ta sunkuyar da kanta taki dago dashi har yanxu “ah ah yau kuma ni ake jin kunya naga kin sunkuyar da kai”wata masifaffiyar kunyace ta kamata kamar ta tsaga kasa ta shige musamman yadda taji alamun idanuwansu na yawo a jikinta, ta bude baki da niyar yin magana abeey da sha’aban suke shigo dakin,”sannu daughter,ya jikin “ da Sauki ta amsa masa har yanxu kanta a duke,kallan su mahma abeey yayi “ yanxu za a sallame ta, in yaso se a cigaba da treatment dinta a gida”,mahma ce ta amsa masa da toh kafun ta tanbayeshi ina dada take,”nasaka saleem ya mayar da ita gida kunsan haryanxu ciwon kafar nata be gama sakin ta ba”, jinjina masa kai sukai cikin gamsuwa, kallansu abeey ya karayi “ya kamata mu koma gida yanxu ,dada tana bukatar hutu,nasan bazata taba hutawa ba in ba gani tayi mun dawo gida ba”,yanxu ma,mahma ce ta basa amsa amma akeey ai naga akwai ragowar ruwan da aka sa mata be kare ba”,gyada mata kai abeey yayi,”idan ya kare zasu dawo tare da mijinta”yana gama fadar hakan ya kama hanyar fita, tunda aka anbaci mijinta jijiyoyin jikinta suka tsaya ko kwakwa kwaran motsi ta kasa,mimmikewa su ummey sukai itama sallama tayi musu suka fita ita da mahma bayan ko wacce ta sakar mara peck a goshinta. Sha’aban ma sai yanzu ya samu damar yi mata yajiki” amaryar mu Allah ya kara sauki” yana gama fadar hakan ya bar dakin gabaki d’aya yayi saura se ita kadai a dakin, gwiwowinta ta hada waje daya tare da fashewa da wani saban kukan da batasan na Menene ba. A hankali ya turo kofar dakin da take, tsayawa kallan yadda ta hade gwiwa tana kuka yayi kusan minti d’aya yana tsaye a bakin kofar kafun ya tako cikin dakin,hannunsa daya yasa tare da shafa kanta, a zabure ta dago kanta har tana kokarin bige bandegin da aka sa mata akai,sosai ta tsorata da ganinsa dan batayi tunanin ganin kowa ba, suna hada ido dashi tayi saurin janye natan tana kokarin sunkuyar da kanta ya rige habar ta da hannu daya tare da dago da fuskar tata, kin kallansa tayi sai ma kokarin lumshe idanuwan datayi “ don’t you dare, bude idanuwanki”, sosai taji shakkarsa musamman da taji yayi mata magana kamar lokacin da ta barar masa da coffee dinsa a part din ammey,bude idanuwan nata tayi yanzu amma har yanxu taki yarda su hada ido dashi”kalleni” ya kara furtawa,ba musu kuwa ta dago ta kalleshi kafun tayi kasa da idanuwanta,”me akai miki kike kuka “, girgiza masa kai tayi alamun babu”amsa “ ya furta, cikin sanyin jiki tace masa “babu”, dan ta bile bakin sa yayi kafun ya saki fuskar tata, kallan ruwan da aka sa mata yayi ganin ya kare,hannu yakai tare da cire mata abun ruwan,dan kara ta saki kadan tana lumshe idanuwanta, kallanta yayi kadan ba tare da yace komai ba, scarf din kanta ya gyara mata tare da mayafin jikinta,”stand up” ba musu kuwa ta mike da niyar takawa,jirin da ya dibeta ne yasata saurin dafe jikin gadon ,kallanta yayi na yan second kafun ya miko mata hannunsa,bin farin zara zaran yan yatsun tayi da kallo,ga nails dinsa dake faman shining kamar Wanda aka sawa abu kararan kun bansa fari tas dasu kamar ba a anfani da hannun”kina batan lokaci”, be karasa zancan nasaba tayi saurin saka hannun nata , kallan yanda fuskarta ba walwala yayi kafun su soma tafiya a hankali, ta bayan hospital inda ba kowa suka nufa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya kara cewa koda uffan ne, shi yana danna wayarsa ne ita kuma gabaki d’aya ta maida hankalinta kan titi dake tafiya, tunda suka shiga motar yake kula da yanda take takure jikinta,yanxu ma kara takure jikin nata tayi sabida yanda sanyin AC ke ratsa mata kashi da jijiya, bata Ankara ba sai ji tayi ya janyota jikinsa,ko kakarin mikewa ta sakeyi ya kara jungumeta a jikin nasa,Daidai saitin kun nanta ya rada mata “I will warm your body “, daga nan be kara cewa komai ba, itama jin sautin muryarsa a kunnanta yasa tsikar jikinta tashi,yanda ya rungumeta yasa bata da wani zabi bayan ta lafe a jikinsa tana shakar daddadan kamshin jikinsa,gyara mata kwanciya yayi kafun ya kara rufeta da faffadan kirjinsa, duk Wanda abun da ke faru zaki be sani ba sabida yanda labule ya raba tsakaninsu har aka karaso gida suna manne da juna musamman yanda sukai body contact suna jin dumin junansu. Direct part Dinsu zaki yayi parking,sai lokacin tahee ta ankara,da Sauri ta kwace jikinta tana hade ranta,ganin antsaya a part dinsa ne yasa tayi saurin kallansa, bece mata komai ba sai fita da yayi daga motar ya nufi cikin part din, tsayawa kallansa bayansa tayi cikin ta kaici ta rasa inama zata sa kanta, part din ammey ta zata wuce ko part dinsa ko na dada, itama fitowa tayi daga motar ,tsayawa tunanin inda zata nufa tayi ganin dare na karayi ne yasa tai shahada kawai ta nufa cikin part dinsa.tsayawa bin falon tayi da kallo ganin yadda kamshi ke faman tashi a ciki,sosai falan ya karayi mata kyau,duk abunda ya faru a falon yana kara dawo mata cikin kai,dubanta takai kan dinning tana tuna lokacin da yake bata abinci a baki, kwallar da ta fara fito matane yasa tayi saurin sharewa a fili ta furta “tunda baya sona banga anfanin tuna komai ba”ganin tsayuwar tata bame anfani bace yasa batare da wani dogon tunani ba ta nufi asalin dakin da ya fara kaita.tana shiga cikin dakin veil da scarf dinta ta cire, tana kokarin cire doguwar rigarta kenan ya fito daga wata kofa sanye da towel iya kugunsa, farar fatar jikinsa tafito shar sai kyalli take , karar da ta saki ne ya daga kar dashi daga goge kan nasa da yake, be kula da ita ba sai yanxu,ganin yanda ta juya masa bayane yasashi sakin wani dan iskan murmushi da be kai ko wuyansa ba kafun ya fara nufo inda take …

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰➰➰

ABUJA

CEDARCREST HOSPITAL LTD

Tare suka dawo da doctor din, yana ganinsa ya saki murmushin nasara kafun ya soma yi masa tanbayoyi game da jikinsa yana amsawa,kallan Matar doctor yayi cikin girmamawa yace mata “congratulations mah, anyi nasara a aikin da akai masa ,sai dai bazamu iya sallamar saba sabida akwai maganin da zamu dorashi akai na tsawan 2 weeks ,and karayar kafarsama tana bukatar kulawa sosai”, shiru matar nan tayi kafun ta girgiza masa kai” ba matsala” tana gama fadar hakan tayi shiru da bakinta,cikin girmamawa doctor din ya kara gaisheta kafun ya bar dakin. Kallan taheer dake hawaye tayi kafin ta zauna akan kujerar dake gefansa ,”tafiya zakiyi kema ko, nasan dama sai sun biyo ni yanxu ma,mugayene su”,girgizamasa kai tayi cikin hausarta da bata gama kwarewa ba har yanxu” ba barin ka zanyi ba,kaji doctor yace za a Dora ka under medication,and your leg shima kaga be warkeba, zanyi tafiya ne kafun na dawo nasan sun gama baka medication dinka sai mutafi tare zansa a dunga kula da kai kaji”, kallan ta yayi kafin ya miko mata dan karamin yatsansa kamar yanda suka saba shida tahee”kin mun alkawari”murmushi ta sakar masa kafun ta rike masa hannun,”I promise you!” Yanxu tell me ya sunanka,”Taheer”, jinjina masa kai tayi, you have a nice name, ka kwanta ka huta zuwa gobe zan dawo ,ok” kamar yanda ta umarceshi kwantawa yayi yana binta sa kallo, gashin kansa ta shafa kafun tace masa good night” shima good night yace mata kafun ta bar dakin, wasu hawaye ya share ,”oumma !! Tahee, nasan kunyi kewata, Nima nayi kewar ku sosai”, tunda ya kwanta tunanin oummansa da tahee yake, yana turo yanda sukai rayuwar su cikin wahala bayan mutuwar mahaifinsu amma duk da hakan sun kaunace junansu sosai , a haka bacci ya dauke sa me cike da mafarkai kala kala “.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Damshin kirjinsa da ya taba tane yasa ta kara sakin wata karar, a tsorace ta rufe idanuwanta zata bar wajan ya rike hannunta,a kausashe ya furta bude idanuwanki, ba musu kuwa ta bude idanuwan batare da ta kalle saba “ me yasa zaki mun ihu a kunne”, ba komai ta amsa masa,guntun tsaki ya saki iya mako gwaro “ kalleni ki bani amsa kafun ranki ya baci”, a hankali ta dago da kanta kafun tayi saurin kulle wa sabida arba da kakkarfan jikinsa da tayi,cikin rawar murya ta furta “bazan iya ba”, gira ya dage guda daya kafun ya furta me yasa , da sauri ta furta “ba..babu kaya ajikinka “,murmushine yake kokarin subuce masa a fuska amma ya dake batare da yyi murmushin ba,”naji bude idanuwanki “, kara girgiza masa kai tayi “ Allah bazan iya ba”, jinjina mata kai yayi “okay tunda bazaki iya ba, amma kin iya ganin abinda ke cikin towel ko”, bata san lokacin da tayi saurin toshe masa baki ba ,wani masifaffen kunyarsa na kara kamata tuno abunda bata mafarki kara gani ,kamar zatayi kuka ta furta “dan Allah kayi hakuri”,hannunta da ta dora akan bakin ya sumbata, da Sauri ta janye hannunta tana kokarin barin wajan, janyo ta jikinsa yayi kafun ya soma kokarin cire mata rigar jikinsa , hannun nasa tayi saurin rikewa tana zaro ido waje wasu kwalla ne yasoma taruwa a idanuwanta,kallanta yayi alamun menene, sun kuyar da kanta tayi kasa ganin taki maganane yasa ya kwace hannunsa da zai mayar kan rigarta, ringing din da wayarsa tayi ne yasa ya jiyo slowly kafin ya nufi d’aya daga ciki, kamar yanda yayi zato abeey ne yake kiransa ganin tana kokarin tsinkewa ne yasa yadaga wayan, a hankali yayi sallama , shima a bangaran abeey amsa masa sallamar tasa yayi yana kallan ammey da sai faman sakin murmushi take tun lokacin da taji warkewar tahee dukda taji zafin abunda basma tayi sai bata nuna ba,tasa abeey da yace king ya saki yarinyar tunda wacce aka jiwa raunin ta samu sauki,tanbayar me jiki abeey yayi,kallan bayanta yayi lokacin da take kokarin shigewa cikin kofar dressing room dinsa yayi ,kafun ya masa da “Alhmdllh “a takaice,”TAHNOON “ abeey ya kira sunan sa kai tsaye, dan waro eyes dinsa yayi jin yadda abeey ya kira ainahin sunansa yau ,”na’am abeey” ya amsa masa cikin yar kasalar da ya faraji “inaso ka saki yarinyarsan, hukuncin da kayi mata ma ya isa haka ba sai ka kulle taba”, da mamaki king yace “wace yarinya abeey”,basma “ abeey ya kara furtawa , shi sam ya manta ma da ya kulle wata ma , tuno abunda tayi dazun yasa ransa soma bashi” abeey “ dakatar dashi abeey yayi, “umarni na baka “ yana kammala zancansa ya kashe wayar, bin wayar king yayi da kallo kafun y zura hannunsa guda daya akan sumar kansa yana ya mutsata . Dakin dressing dinsa ya shiga ,ganin bata ciki ya gane ta shiga toilet ne , a nutse ya shirya cikin white din kaya me shegen laushi, sumar kansa kawai ya taje da ta kara yawa kafun ya feshe ilahirin jikinsa da daddadan turaransa me sanyaya zuciya , yana gama shiryawa ya fito daga dakin, dakin da ya kulle ta a ciki ya nufa bayan yasaka turn print dinsa,
Ba’a ganin komai na dakin sabida yan da wajan yayi duhu sosai , light din dakin ya kunna,kwance ya hangota a sume kan carpet din dake cikin dakin , babu komai a ciki sai wasu cushions da aka kawata dakin sai ya zama kamar na hutawa , a hankali ya tako inda take ganin bata motsine yasashi nufar fridge din dakin, wani ruwa ya dauka me shegen sanyi da ya fara kankara yana zuwa inda take ya bude ruwan tare da zazzaga maga shi, a matukar firgice ta farka daga suman da tayi tana faman zare ido, ganin har yanxu ruwan be dena zuba bane yasata sakin kara cikin firgita, tsawar da ya daka matane yasata shiga taitayinta,a mugun tsorace take kallansa da bakinta daya kunbura, nuni da yayi mata tayi mishi shirune yasa tayi saurin kame bakinta hawaye na tsiyaya da sauri sauri a fuskarta,dan ran kwafowa yayi kallo daya yayi wa fuskarta ya dauke kansa, a kausashe ya soma magana “Daga yau, ko me kama dake na kara gani a kusa da matata, sai na la’antasa ballantana ke da ko matsayin dan kwalin kanta baki taka ba” yana kai karshen zan cansa ya nuna kofa da hannunsa ,”kafun na irga uku ki bace mun anan idan ba haka ba sai dai a sauki kasusuwanki “ be rufe bakinsa ba ta arta a guje dukda yadda kafarta da fuskarta tane zugi, ba ciwon da yaji matane ya fi bakanta mata ba, matarsa da ya kira shine ya fi komai tsaya mata a rai,koda ya Fito daga dakin,lifter ya hau direct ta kaishi hawa saman sa, koda yashiga ne shiga daki ba, dakin da ya taba shiga nan ya shiga ,me aku a ciki kallan sararin samaniya yayi ganin yadda stars suka fiffito ga duhu da Garin yayi, sosai yanayin yayi masa dadi, kan wasu chairs ya samu ya zauna yana kara bin stars din da kallo har wajan karshe shabiyu kafun ya sakko down stairs , dakin da take ya nufa, koda yashi a cikin bargo ya sameta duk ta takure jikinta, sanyin Ac din ya rage sosai kafin ya taba goshinta, temperature dinta ya fara dawowa normal, dan goshinta da akai wa dressing ya bi da kallo kafun ya gyara mata abun lullubar tata,alwala yayi tare da kabbara sallah kamar yadda ya saba, bayan ya idarma karatun alkurani me girma yayi kafin ya kashe light din dakin gabaki d’aya yana janyota jikinsa.

ASUBA TA GARI ….

🫧🫧🫧🫧
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

ABUJA

CEDARCREST HOSPITAL LTD

Karfe 8:30am ta shigo dakin da yake , ganin ya rakube ne yasa jikinta yin sanyi, yana ganinta yayi saurin kokarin tashi, dakatar dashi tayi tare da karasowa inda yake,kallan abubuwan da tasa akawo masa tayi ganin babu abunda ya taba, “me yasa bakaci abunda nasa a kawo mata ba”, jiki a sanyaye ya furta na dauka bazaki dawo bane ,kwallar dataji tana kokarin zuwar mata tayi saurin hadiye kafun ta ja plate daya serving dinshi”me yasa kake tunanin zan tafi in barka, as I promise bazan tafi na barka ba , da zaran na dawo daga tafiya na zan zo na d’auke mubar musu ganin gabaki d’aya kaji “girgiza mata kai yayi tare da saurin bude bakinsa ta saka masa chicken din daga debo, da kanta ta dunga serving dinta, bayan ta gama shima ya karba ya bata,wata irin kaunarsa yaron ne taji ya shigar mata zuciya farat daya. A asibitin ta zauna har yamma tana tare dashi,sosai ya bata labarin su oumma da tahee har ta soma kwadayin san ganin su, taji dadin hirar tasu ko ba komai ya debe mata kewa , wata kafceciyar waya ta dakko a cikin Jakarta kafun ta mika masa,”idan na tafi zamu dinga yin waya da kai kaji”, zaro idanuwansa yayi hawaye na zubar masa “dagaske zamu dunga yin waya “ gyada masa kai tayi “kwarai ma kuwa”,kara mika masa wayar tayi ganin yayi shiru be karba bane ta kallesa”me yasa bazaka karba ba” oumma zata mun fada ita da taheer ,kallansa tayi tana nazarin kalamansa tabbas mahaifiyarsa ta bashi tarbiya “bakaso ka dunga gaisawa dani kenan”girgiza mata kai yayi “inaso” ok karba , hannu bibbiyu yasaka ya karba, hawaye na zubo masa ya dunga yi mata addua har saida ta tsayar dashi kafun ta nuna masa yanda ake anfani da wayar bayan ta fito masa da games da yawa a ciki. Ba ita tabar hospital din ba sai 9 bayan ta masa alkawarin dawowa gobe da safe suyi sallama.

➰➰➰➰➰➰
➰➰➰➰➰➰➰➰

8:30am tsaye tahee take gaban mirrorn dakin tana faman taje uban tulun gashinta ,gaban goshinta duk ya jike da ruwa har ya fara taba dressing din da akai mata,dan guntun tsaki ta saki lokacin da take kokarin tufke kan, kamar ta saki kuka haka take ji,ganin ta kasa sakawan ne yasa cikin haushi ta jefar da ribbon din, yana tsaye jingine jikin kofa , tun lokacin da ta fara taje kan ta ya shigo cikin dakin,ribbon din data yar dar ya je ya dauka haryanxu bata Ankara dashi ba saida taji ana ta ba mata gashin kai,baki ta bude daniyar kwala ihu ,”if you dare “ ya furta kalmar a fusge, kallansa tayi sosai ta mirror ganin shidin ne da gaske yasa ta sakin ajiyar zuciya da harshi dake kusa da ita sai da yaji, gashin kan nata ya tufke kafun ya kalli dressing din da yayi mata “wa yace ki sawa ciwan naki ruwa”, in ina ta soma ganin ya zuba mata rikitattun idanuwansa kwata kwata fuskarsa ba fara, sun kuyar da Kai kawai tayi tare da furta “ina wanka ne ya dan jike”, be ce mata komai ba ya juya da niyar barin wajan yaji saukar muryarta “ ina kwana”, dan waiwayo da fuskarsa yayi kadan ya kalleta batare da ya amsa gaisuwar tata ba” karki bata mun lokaci am waiting for u now”, yana kai karshen zancenta ya fice a dakin,hararar kofar da ya fita tayi cikin kwaikwayar muryarsa ta furta ,”karki bata mun lokaci am waiting for u now “, sai kace wani baba na , cikin sauri kuma ta dauki hijab dinta gudun karya zo ya sameta a dakin, a tsaye yya tarar dashi har ta fito be kalli inda take ba sai ma kofar fita da ya nufa,ganin hakan yasa itama ta tabe bakinta tare da nufar kofar,yana fitowa zaki ya sara masa har ya bude masa kofa king ya dan girgiza masa kai tare da miko masa hannu,tsaya wa tunanin me ze basa yayi sai ji yayi king yace masa “the key” waro idanuwa zaki yayi cikin suman tsaye jin ya anbaci key,idan zea iya ranshewa karshen ganin king ya tuka mota da kansa tun lokacin da yake zuwa hutu ne,”the key” ya kara anbata, da sauri kuwa zaki ya bashi key din cikin girmamawa,wani dan karamin file king ya mikawa zaki , ba tare da yace komai ba ,shima zaki jinjina masa kai kawai yayi tare da barin wajan, motar da aka fito da ita , shiga ciki yayi tare da tayar da ita,kallansa tayi ganin be ce mata komai ba ta rasa ya zatayi,batare da ya jiyo ba ya furta “kika kuskura na kara cewa wani abu rankine zai baci”, be kara kalmar tasaba tai shahada Kawai tare da shiga front seat din motar,Kai tsaye part din dada ya nufa yana gama tana binsa a baya kamar wata jaka,dada da su abeey kawai ya tarar a falon , tana ganin tahee ta soma washe baki “oh ni yau Allah ya kawo ni lokacin da zanga tahura batare da ta buya ba” sun kuyar da kai tayi kasa tare da gaishe ta , amsawa dada tayi tana godewa Allah, su abeey ta gaisar yanxu kafun ta gaishe da su uncle Saleem da suke mata ya jiki,Shigowar mahma falon ne yasa ta gaishe da ita tama , cikin kulawa take tanbayar ta ya jikinta ,king ma gaishe da iyayan nasa yayi daga nan be kara cewa uffan ba ,shi dai abeey lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushi musamman kunyar yarinyar tana burgeshi. Ganin taki sakewa ne yasa mahma janta da hira , mikewa king yayi , kallansa abeey yayi “ina zakaje son” “ammey” ya furta wa abeey kallan tahee abeey yayi “ daughter tashi ki bishi kuje ,Allah yayi muku albarka baki daya “Ameen kowa ya ansa masa kafun subar part din, sosai take zumudin ganin aunty ta yanayin parking ta fito da Sauri ta manta ma tare da wa take, tsaye ammey take tana duba abincin kan dinning sai ji kawai tayi an rungumeta ,da Sauri ta juyo dan ganin wanene,”ammey nayi kewar ki”, tahee ta fada tana fashew da kuka,itama Ammeey hawayene ya fara zubo mata a tare suka kara rungume junansu suna yin kukan , ganin kukan nasu ba me karewa bane yasashi karasowa Inda suke hannu yasaka ya sharewa ammey hawayen nata,” tare da kallan tahee ,rikitattun idanuwansa ya sa mata be ce komai ba ya kama hannun ammey suka zauna a falo, yayi farincikin ganin wannan murmushin na ammey da ya dawo, abinci ta saka musu su duka ta hada tana bawa a baki , TAHEE kam kadan taci tace ta koshi kasantuwar king a wajan. Sun dade a part din ta kafun su nufi part din ummey, itama sosai tayi farin cikin zuwansu, zoya ma tana ganin tahee ta nufeta wai suje suyi wasa,cikin jin kunya ta saki murmushi tuno lokacin da suke wajan , hira sosai zoya ta dunga bata har saida king ya dakatar da ita, lumshe idanuwa tahee ta fara , tun shigowarta falon ta fara jin jiri jiri da wani abu kamar yana kiran sunan ta , daurewa kawai take , ynxu ma jirin da take ji ne yasa ta yin shiru, sun kara kusan mintuna 5 a part din kafun suyi mata sallama itama , tana fitowa daga part din taji wani d irin juwa ta kamata kamar wacca aka bangaja zata fadi kenan king ya rikota,itama cikin tsora ta rike hannunsa sosai kamata yayi suka shiga mota, ganin yadda take sauke ajiyar zuciya ne yasa shi taba goshinta,normal temperature dinta yake , part din mahma ya mayar da ita , zata fita ya rike hannunta ,”are you ok “ amsa masa tayi da ka kafun tace masa “eh”tana shiga ta tarar da sha’aban zai fita ,cikin girmamawa ta gaishewa, shima amsa mata yayi kafun yayi mata ya jiki , ganin kiran king yasa shi saurin yi musu sallama tare da barin part din. Hira suka fara duk da tahee tana nonnoke mata ,amma sai da tasa ta sake da ita, wani boil babba mahma ta miko mata tare da umartarta ta cinye komai da ke ci, ba musu ta karba kuwa ,loma daya tahee tayi kamar me shirin yin amai, cikin narai narai da ido ta kalli mahma, fahimtar haka yasa mahma hade ranta batare da ta bata damar yin korafi ba.

🫧

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

 

Mss Lee 💖
💖💖GIDAN AUNTY💖💖
( a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

PAID BOOK
MAIBUKAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.

Leave a Reply

Back to top button