Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 65

Sponsored Links

Page 65

“Tom…..zamu tafi” abbas ya fada yana duban qwayar idanun widad din,hannunsa zube a aljihun wandon lallausan yadinsa da aka yiwa wani irin dinkin girma.

Daga kai tayi da nufin kallonsa,duk yadda taso ya hadiye abinda takeji a qasan ranta amma ta kasa,dole haka ta saka qwayar idanunta a tasa,dai dai sanda hawayen da take riqewa ya sulmiyo daga idanunta,maganar da zatayi ta riqe mata a maqoshi,sai ta saki kuka sosai,abind aya tilasta mata saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu.

Duka idanunsa ya fiddo,ya ciro hannayensa yana matsowa inda take tsaye

“What’s happening weedad?” Kai ta girgiza masa,saidai kukan take har yanxu

“Noo….noo,kada muyi haka dake mana uhnnn?” Ya fadi a tausashe,sai ya sake matsawa gabanta,ya saka duka hannuwansa ya zare nata tafukan hannayen daga fuskar tata yana kallonta

“I will be back in sha Allah…..ki daina kukan nan,yana qona ni,zuciyata tana zafi…..ko kinaso nima nayi kukan?” Ya fadi yana jin wani irin rauni da bai taba jin kamarsa ba,kanta ta girgiza amma ta gaza tsaida hawayen

“It’s okay,i promise you bazamu dade ba,shikenan?”saita sake jinjina masa kai,haka kawai takeji wani tashin hankali da rashin sukuni a tattare da ita,sai takejin kamar zai tafi ya barta,kamar bazai dawo ba,tana jin kamar an dauke wani muhimmin sashe ne a jikinta,batasan wanne irin feeling bane wannan,tsahon rayuwarta bata taba fuskantar irinsa ba.

Tas yasa soft handkerchief dinsa ya goge mata hawayen,sannan ya bude tafin hannunta ya saka mata shi,ya maida ya dunqule hannun nata cikin nasa,sai yaja da baya kadan yana gyara zaman rigarsa data cukuikuye yana kallonta,cikin ransa yakejin wani shauqi yana saukar masa,ganin wani yana kewarka…..ya shiga damuwa saboda zaiyi rashinka a kusa dashi……wani irin dadi kima da daraja gareshi a zuciya,wani irin yanayi da bazaice ga lokaci na qarshe daya ganshi tattare da matarsa ba,sai ya buda dukkanin hannayensa yana kallonta da idanunsa masu girma da zuwa yanzu suka rusuna,girmansu ya ragu

“Oya…. give me a hug” jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,qaramin miskilin murmushinta ya subuce zuwa saman labbanta,a yau din sai taji bata shakkar yin hakan,ta fara takawa a hankali kamar wadda aka sakawa wani kida na musamman,yayin da idanunsa yaji sun fara narkewa a kallonta,cat walking takeyi,irin tafiyar da sai wance da wance cikin isassun mata,bai taba lura da hakan ba sai yau,ya qaraso gareshi a hankali,ta shige jikinsa kuwa gaba daya,harda qoqarin saka hannuwanta ta zagayo dasu ta bayansa,sai ya tallafa mata,ya durquso ya sakata sosai a jikin nasa,yana jin kamar ya maidata cikinsa.

Sun jima sosai a haka kafin ta fara janye jikinta,ya danyi baya jikinsa a mugun mace yana maida numfashi,kusan minti hudu kafin ya dai daita kansa

“Ayimin rakiya mana” kai ta girgiza tana murmushi,duka idanunsa ya bude a kanta

“Why?”

“Hajiya fa…..so kake ta gane ka rungume ni,sannan tun dazu muka shigo daki ni dakai fa,nidai kunya nakeji” ta qarasa maganar tana turo baki,bai shirya ba bai kuma zata ba dariya ta kubce masa,yasa hannunsa saman bakinsa ya dara kadan sannan ya janye

“Ok, come closer” ya fada yana daga mata hannu,bata musa ba tasake matsowa,ya sukuya a hankali ya bata wani irin hot and deep kisses saman goshi da kuncinta,sannan yaja baya yana cewa

“Na bawa Allah amanarku,ki kula da kanki” ta gyada kai a hankali,sannan ta motsa bakinta

“A dawo lafiya,Allah ya kiyaye yasa ku dawo lafiya” lumshe idanu yayi har ya fice,ji yayi a duniya kamar ba’a taba masa addu’a ba, siririyar muryarta ta dinga masa amsa kuwwa a kunne,har suka isa airport yana wassafa wasu abubuwa da yawa a kanta.

Kafin jirginsu yakai ga tashi yayi kiran hafsat,ko ba komai yana son ya sauke nauyin dake kansa,yanason kuma yayi magana da yaranshi,sai daya kira sau uku,ana hudu yaci sa’a aka daga,saidai muryar yaran ce,ya biye musu sukayi surutu sosai har sai da yaji ya siqe

“Ku bawa mommynku” ya fadawa mimi,shuru na sakanni ya ratsa,sannan yaji mimi tace

“Tace bacci takeyi” idonsa ya rufe sannan ya budesu lokaci guda, irin yadda yakanyi wajen hadiya fushi idan ransa ya baci,baya so tana saka yaransa a ire iren wadan nan abubuwan nasu,yanzu ko ba komai ta koyawa yarinyar qarya

“Alright….idan ta tashi kuce nace ta kula daku,daddynku zaiyi kewarku”

“A dawo lafiya daddy,ka siyo mana jirgi” murmushi ya kufce masa,yana fatan wataran dukkansu ya kaisu umara ko aikin hajjin suma

“In sha Allah mimi na,i love you”

“I love you too daddy” ta amsa masa,dai dai lokacin hafsat da haushi ya cikata tayi fam ta warce wayar,ta jefi yarinyar da harara

“Uwar kinibibin tsiya,i love you too daddy” tayi maganar tana kwata muryar yarinyar

“Koni ban fada ba sai ke,saikibishi ai uwar son uba” taja tsaki tana jefa wayar gefe,harta koma zata kwanta sai kuma taji ta fasa,ta miqe ta fada bandaki ta watsa kwaskwarima,ta fito ta fara shirin fita,su mimi kuwa kaya kawai ta fidda musu tace su debo wasu ta saka musu,gida zasu,idan sun qarasa can a samu wani yayi musu wankan, yaro ba hankali,da murnarta ta shiga dakinsu ta debo musu kayan,uwar ba tare data tsaya wani dubawa ba ta karba ta saka musu,ta hado kansu ta sanyasu a motarta suka fice daga gidan,gidan kamar mazaunin bola,saidai hankalinta a kwance yake,tasan me sanya damuwar saita gyara din baya qasar ma gaba daya,duk sanda ta samu chance ta gyara din,hankalinta yayi gidan,tana son su hadu da anty ummee taji sabbin shawarwari,tana jin kamar tafiyar ta ta fara baudewa.

A daren ranar daya sauka ya sake kiran hafsat din don ya gaya mata sun sauka lafiya,amma harta qaraci ringing dinta bata daga ba,har a lokacin ma tana gida bata koma ba,mamarta ta sake cewa da ita

“Shareshi,wani abunma duk laifinki ne,ace mijinka baya shakkarka me akayi kenan” .

Yasan dai ba yadda za’a yi ya mata irin wanna kiran tace bata gani ba,kuma koda a daxun baccin take da gaske ai yaci ace tayi kiransa bayan ta farka,ransa yakai qololuwar baci,yaji kuma a ransa bazai sake kiranta ba indai shine,sai ya maida akalar kiran nasa ga widad.

Dukkaninsu wata irin sakewa sukayi shida ita,sunyi hira mai tsaho,duk abinda tayi a yau din sai data zayyane masa shi kuma yana kwance saman gadon hotel din da suka sauka yana biye mata,a nan take bashi labarin taga tallan wajen wani koyar da girki a kaduna tanaso

“Iyeee …. dole wai so take ta fini iya girki…… alright,zansa Samuel ya yiwa rose magana” da murnarta sosai ta shiga masa godiya,har yaga godiyar kamar tayi yawa,ita kuwa a wajenta normal ne,kamar yadda aka horeta kenan a gida.

Kwana daya da zancan kuwa saiga rose tazo har gida samuel ya kawota,haduwar farko jininsu ya hadu da rose din,saboda tana da matuqar kirki da kuma ban dariya,wannan ya sanya saurin sabo a tsakaninsu duk da rashin saurin sabon da widad ke dashi,shiryawa sukayi ita da muneera da aka bar mata suka wuce wajen sukayi register da komai da komai sannan suka dawo gida,tun daga ranar rose ce ke zuwa ta kaita ta kuma dawo da ita gida,cikin lokaci qalilan sukayi sabo,itama tana son widad saboda kirkinta,don idan sun dawo din sai ta tsare rose ta zauna taci abinci,harma suyi hira da ita,sau tari ma idan ta gwada abinda ta koya saita ajema rose din,komai tabgwada din kuwa sai yayi kyau exactly kamar yadda ta koyo,abun yayita bawa rose mamaki da sha’awa,wata irin gifted ce weedad din.

Ganin yadda widad din keda sha’awa girke girke,sai rose din ta ware wasu ranaku take koya mata irin girkin nasu qabilar,idan sukayi wasu daga ciki takance

“Oga yanaso wannan” tsaf widad ta dauke wadanda tace yafiso din,ta dinga practicing nasu da kyau,har suka zauna mata,ita a karan kanta dadi takeji,tana jin dadin yadda a yanzun ta fara iya kalolin girke girke da dama, yadda ta maida hankali a kitchen yanzun bata maida haka kan karatunta ba,gefe guda ta matsawa anty deena, kullum saita qara mata bayani akan abincin ainihin qasarsu,duk da wannan dama tana ganin ummu tana yinsu sosai,saidai bata taba cewa zatayi da kanta ba.

Cikin wata daya ta koya abubuwa da yawa ta fannin girki,ansha barna,don kullum da abinda za’a girka,saidai ta samu experience sosai.

Tun saura kwana uku su dawo take ta practicing abinda zata dafa musu shida hajiya,sunyi hira da anty deena da anty madeena sosai,sun kuma bata shawarwari cikin hikima,ana ya jibi zasu dawo muneera ta taimaka mata suka gyare gidan tas,sukayi goge goge sosai,washegari kuma rose tace mata

“Madam ko za’a kaiki saloon?” Fadin da rose din tayi sai ya zama kamar tuni a wajenta,tace ta kaita.

Waje ne mai kyau da zaka yiwa kallo daya kasan sun iya aikinsu,cikin yarensu sukayi magana da rose bayan sun gama gaisawa,mutum biyu aka gamawa sannan aka kama kanta.

Sosai matar tayi mamakin yanayin kan widad din,da kanta matar mai suna ada tace bata buqatar relaxer.

Wani irin gyaran kai akayi mata,wanda ita kanta widad din sai data tsaya ta kalla kanta da kyau a madubi bayan sun koma gida,muneera tace

“Wallahi matar nan ta iya gyara matar uncle,inama idan bikina ya taso nan zanzo tayimin”

“Kizo wallahi,saina rakaki” ta fada tana sake kallon kanta dadi yana cikata.

Isowar yammaci sukayi a washegari,kafin isowar tasu komai ya kammala kamar wata babbar mace,cikin atamfa ta shirya dinkin riga da skert,saidai ta gaza daura dankwalin sai yafashi tayi saman kanta,tana maqale jikin window din falonta har zuwa sanda motar data daukosu ta sako kai harabar gidan.

Bin motar tayi da kallo,tana zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,farincikin da batasan dalilinsa ba takeji yana ratsa zuciyarta,taci gaba da kallon motar har ta shige parking lot

“Sun iso,bakiji shigowar motarsu ba?,kizo muje mu taraso” muneera dake sanya hijab dinta ta fada tana kallon widad, waiwayo tayi tana duban muneera,sai takejin kamar qafafunta ba zasu iya kaita wajen ba,ta girgiza kai

“Kije yanzu ai zasu shigo” kai ta kada tana dariya

“Oh,wai kunyar hajiya kenan kikeyi,to nidai nayi nan” ta fadi tana yin gaba da sauri,ta bude qofaf ta fice.

Sanda ya shigo ta dauka zata iya dakewa,sai tsintar kanta tayi a gabansa,shima yayi tsammanin zai iya jurewa amma sai ya kasa, hannuwansa gaba daya ya bude mata,batayi wata wata ba ta fada ciki,ya maida ya rufeta gam a cki yana sauke wata wawiyar ajiyar zuciya,yayin da ita kuma ta fashe da kuka sosai cike da wani tune na shagwaba,sai ya gaza jurewa tsaiwar,ya sulale ya zauna a wajen,hakan ya bata damar zama sosai a jikinsa.*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Leave a Reply

Back to top button