Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 62

Sponsored Links

Page 62

Tun jiya da ya kirata yace mata gobe zasu taho da hajiya,tayi murna sosai saboda zaman kadaicin ya isheta amma bata kawo wai ta tanadi komai ba,ta dauki littafinta taci gaba da karatunta,tana tsaka da karatun taga inda jarumar littafin ke shirye shiryen dawowar mijinta daga tafiya,abun sai ya burgeta sosai,ta idar da sallah azahar tana saman abun sallah abun ya sake fado mata,saita dauki wayarta ta kira anty deena tana labarta mata

“Kema irin hakan zakiyi, bakiga abincin da aka kiya jiya ba a group?” Kai ta gyada

“To haka zakiyi,ki shirya shi kamar yadda aka koyar ana shirya abincin mutum” daga kan abun sallar kuwa bata koma yin komai ba ta fara practicing abincin,datayi kuma yayi mata yadda takeso,suna da komai ba abinda zata buqata,saita fara shirya komai tun a ranar.

Washegari gari yana yin haske ta gyara gidan,dama ta saba wannan ya fara zame mata jiki,saidai yau har dakinsa ta gyara kamar yadda anty deena tace mata,tana yi tana kiran anty deena ita kuma tana qara mata haske,tana aikin suna video call da anty deena ta watsapp,sannu sannan sai gashi har girkin ta gamashi tsaf,ta kuma zuba a warmer,ta jera,anty deena ta kalla ta cikin wayar,cikin farinciki tace

“Well done qanwata,yanzu saura abu daya” langabe kai widad tayi

“Allah anty na gaji sosai”

“Aikin gama,sauranki wanka,ki dauko kayanki na zuwa gidan biki ki saka,yau duka kayan kwalliyarki ki juyesu a fuskarki” ido widad ta zaro tana dariya

“Kai anty….suna da yawa fa” dariya itama tayi

“Ai wai ina nufin ayi kwalliya da kyau,a saka turaren gida dana jiki ako ina” dan turbune fuska tayi

“Wai anty duk uncle akewa haka?”

“Kai,ai yafi gaban haka ma,ba kinje min litattafai kika samu kina karantawa ba?,bakiga yadda akeyi bane?” Batason tacewa anty deena din eh,saboda wasu guraren cikin litattafan kunya suke bata(tsarkakakkun litattafai wadanda babu batsa a ciki sai qaruwa),kai ta gyada mata a kunyace

“Good,maza kije ki shirya to” cewar anty deena,daga haka suka katse kiran,ta dauki wayar ta wuce bedroom dinta,tana tafe tana hangen dining din kamar wani zai bata mata aikinta,saidai murmushi kawai takeyi najin dadin yau ta qure adaka tayi abinci,gidan kansa yadda yau ta gyarashi ita da kanta yana bata mamaki.

Sai data bata lokaci a daki tana zaben kayan da zata saka,anty deena dai tace mata atamfa,ita kuma babu abinda tafiso irin doguwar riga abaya,don kusan kullum itace shigarta,kamar kuma sunsan zabinta sun sakota da yawa sosai a lefenta,tana kallon abayar ta haqura,ta ciro atamfa riga da skert,blue black mai adon maroon,sannan ta shige bandakin ta hada ruwan wanka ta fara wanke jikinta.

Tana wankan tana ‘yan waqe waqenta qasa qasa,saboda yau din nishadi takeji cikin ranta,ta gama cuda jikinta ta shige asan shower ruwan yana ratsata,saita tuna gida,ummu na hanata shiga shower saboda wasa takeyi da ruwa, kuma tana jiqewa har kanta ne,sumarta nada tshao da yawa,yawancin lokaci saidai a saka hand Drayer a busar mata da ita,saita saki murmushi,tana jin ba dadi cikin ranta,ko sai yaushe zata ga ummu?,bata tabq zato a rayuwarta zatayi nesa da ummu har haka ba ta kuma haqura ba.

°°°°”alhamdulillahi” hajiya ta fada tana fitowa daga motar bayan tsaiwar motar tasu a farfajiyar gidan,murmushi abbas yayi

“Yau gaki a kaduna dai” sai tayi murmushi

“Eh nufin Allah kenan” yana janye da trolly dinta, muneera na dauke da jakar hannunta suka doshi sashensu.

“Assalamualaikum mutan gida” hajiya ta fada tana murmushi idanunta cikin falon,wani boyayyen ajiyar zuciya abbas din ya sauke,saboda hango warmers da yayi saman dining din,uwa uba yadda fakon yake a tsaftace ya qawatar dashi,duk da dama bai tana ganin wani abu na qazanta ko qanqani a tattare da ita ba,hasalima yana mamakin yadda bata son taji ta taka datti

“Ki zauna hajiya,inajin tana daki” ya fada yana janye mata pillow din kujerar,tayi bismillah ta zauna,haka kawai taji ranta yana mata dadi,ya juya ya dubi muneera

“Ki samo muku ruwa da lemo”

“Aah,bari dai matar gidan ta fiti tukunna ta shaida xuwanmu ko?” Murmushi abbas yayi

“Peace maker” shine sunan da sau tari yake kiran hajiyarsa,bata qaunar tashin hankali ko kuma husuma ko kadan.

Kayan daya gani baje saman gado yasa hankalinsa yadan tashi,bai kuma ji motsinta ba,ba tare da tunanin komai ba ya murda handle na bandakin ya tura ya sanya kansa.

Dai dai lokacin da take tsaye babu komai a jikinta,sai towel a hannunta tana tsane gashin kanta,mugun zabura tayi ta kuma tsorata matuqa,saidai data waiwayo suka hada ido sai taji kamar zata narke a wajen,saboda tsorata saita jefar da towel din,ta kuma sulale a wajen ta duqe tana cure jikinta waje daya,ko ina na jikinta rawa yakeyi,take ta fash da kuka.

Shi din ma kamar an jona masa lantarki haka yaji,ganinta a hakan ba qaramin al’amari bane a zuciyarsa da kuma gangar jikinsa,ya rintae idanunsa ya koma baya days saut yana mayar da qofar yadda ya ganta,saidai ya kasa sakin hannun qofar,yayi tsaye riqe da handle din yana maida mumfashi.

A hankali yaci gaba da sauke jumfashun nasa ta baki data hanci,ya bude idanunsa a hankali yana jiyo sautin kukanta,yasan yau kam ya taro match,sai ya matsa jikin qofar cikin kasala yace

“Am sorry” shuru bata amsa masa ba,sai ya sake daga murya

“Am very sorry” cakin muryar kuka tace

“Kana sane ka budeni,ai kasan wanka nakeyi” murmushi ya saki tsigar jikinsa na sake zuba a,daga dawowarsa ta masa wani irin kunnawa da yasan bashi da maganinta

“I swear bansan kina ciki ba…..am sorry…. please kiyi shuru mana”

“Allah tunda ka ganni tsirara bazan yadda ba” ta fada bayan ta miqe tana daura towel dinta da sauri,tana tsoron kada ya dawo.

Murmushi mai kama da dariya ne ya kubce masa,shagwabarta tana kasheshi ainun

“To shikenan,let me come inside,sai na cire kayana kema ki rama,kinga shikenan anyi one one”

“Wayyo ummuna….Allah karka shigo,idan ka shigo saina gayawa ummu” ta fada tana gunjin kuka jin yana taba qofar kama zai bude,dariya sosai ta kamashi har sai daya dan sunkuya

“Alright…..alright,shikenan,khalas…..ya isa,am sorry,ki qarasa ki fito,hajiya na falo tana jiranki” ya danja da baya har yanzu fuskarsa murmushi ne kwance akai ya baro dakin,gaba daya bacin ran daya taho dashi babu kaso hamsin cikin dari.

Da sauri ta miqe ta qarasa wankan jin cewa hajiya ta qaraso,ta shirya a gurguje,bata saka komai kan fuskarta ba,saisai jikinta ya wadata da turare,sanon turare ne ta bude cikin kayan lefenta.

Rungume hajiyan tayi abinta tana jin dadi,sai take ganin kamar ummunta ce tazo,ta ma mance dashi a wajen,suna gama gaisawa ta gabatar mata da lemuka da ruwa

“Hajiya na kawo miki abinci?,ni na girka da kaina” ta fadi tana murmushi,ta qagu taci taji me zata ce,dariya tayi

“Bari nayi sallah tukunna widad,nunan bandaki”

Dakinta ta kaita ita da muneera duka harda kayansu,sukayi sallah sannan suka dawo falon ta fara zuba musu abincin,a sannan abbas daya fita salla masallaci bai dawo ba.

Hankali kwance suke cin abincin suna hira,duk yau sai widad takejinta free kamar a gida,babu wanna kadaicin ba komai,har suka gama bai dawo ba,sukaci gaba da hirarsu hajiya na jinsu,yanayin da taga widad yayi mata dadi sosai,saboda ta qara wani irin haske akan wanda take dashi,hakanan ta murje sosai,duk da ba qiba tayi ba,amma fatarta tayi kyau.

Yamma liqis ta sake shiga kitchen ya gwada yin tuwo miyar kubewa,tanata taraddadi kada tayi kwaba,cikin ikon Allah sai gashi tayi shi fes,abinda ya faranta mata ranta,ta gama suka gyara kitchen din,muneera tayi mata wanke wanke sannan ta gabatarwa da hajiya bayan sunyi sallar magariba.

Farincikin da hajiyar ta tsinci kanta a ciki ba dan kadan bane,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba cin.abincin gidan abbas din ba sai wannan karon,karamcin da yarinyar ta nuna mata ya qara dad’ad’a abincin a bakinta,ya kuma qara mata qaunar widad din a zuciyarta.

Tana ta so tayi wanka amma kuma sai takejin nauyin hajiyan, saboda ba zata iya tube kayanya cikin dakin ta shirya ba,sai ta basar kawai sukaci gaba da hira abinsu.

Ana idar da sallar isha’i dukka suna falo,a sannan yayi sallama ya shigo,hannunsa dauke da leda,dukkan alamun gajiya sun bayyana a tare dashi.

Kusan a tare sukayi masa sannu da zuwa,ya amsa yana zubewa gaban hajiyan yana mata barka da dare

“Ina ka shiga haka?,tun dazu nake taraddadi”

“Wallahi na leqa office ne,akwai ayyukan da nakeso na rufe file dinsu kafin mu wuce,kuma zan dauki excuse ma.na tafiyar tamu”.kai ta jinjina

“To Allah yayi.jagora ya dafa”

“Ameen ameen hajiya,kunci abincin dare?” Sai da tayi murmushi sannan ta amsa

“Munci abinci kuwa,tuwo ma,mun qoshi kuma alhmdlh”

“To ma sha Allah” ya fada ransa na masa fari,bai taba zaton zai tadda hakan ba,ya saci.kallonta kanta yana a qasa tana wasa da zaren dankwalinta,har yanzu haushinsa takeji,kunyarsa kuwa kamar ta bace a wajen,musamman idan ta tuno a yadda ya ganta,ko ummu bata zaton ta taba ganinta a haka da wayonta.

“Na gaji fa sosai,inajin kwanciya zan shiga nayi” hajiyan ta fada tana miqewa,sai muneera itama ta miqe,don itama a gajiyen take

“Ya kamata”

“To Allah ya bamu alkhairi,sai da safe” tayi musu sallama suka wuce dakin ita da muneera.

A hankali ya tattaro dukka.hankalinsa a kanta,ya xuba mata idanuwansa yana kallon ta,da gaske ba zata kalleshi ba,har yanzu baku dankwalinta yana hannunta tana ta murzasu,cikin sakanni jikinta ya bata saqon cewa ana kallonta, tasan kuma shine,saboda rashin wanzuwar motsinsa kadai ya isa amsa.

Dan daga kai tayi,sai suka hada idanu, karon farki taji ba zata iya jurewa ba,ta saki gefan mayafin ta yunqurq zata miqe

“Ina zuwa?” Ya jefa mata tambayar,qeya ta juya masa,ya kuma tura baki gaba

“Zanje na kwanta,nima baccin nakeji” yadda tayin ya bashi dariya,amma ya maze

“Haka zaki tafi ki barni,ni baki bani abincin ba yuwa nakeji” ya fada yana karyar da wuya kamar qaramin yaro,shi kansa baisan yayi hakan ba.

Dan jim tayi,sai maganar anty deena ta dawo mata

“Idan ummu taga yayi miki ba dai dai ba ko nuna rashin kulawa,kinsan zataji babu dadi ko?,to kema idan kika masa hakan hajiyarsa ba zataji dadi ba” da wannan tunanin ta juya zuwa dining area don kwaso masa abincin,yabi bayanta da kallo,sosai skert din ya zauna mata das das,ya fidda qugunta dake juyawa sanda duk tayi taku,kamar da gayya takeyin hakan,ya janye gajiyayyun idanuwansa a hankali ya lumshesu yana furta kiran sunan Allah.
[3/13, 12:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button