Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 72

Sponsored Links

Page 72

“Umman walidi…..amma abinda mommy hafsat take fadamin ba gaskiya bane kenan?,naga itama babba ce kamar ku,amma bata taba gayan abinda kika gayamin yanzu ba”

“Me take ce miki?” Anty madeena ta tambayi widad din tana kallonta,cikun fargabar kada ta koya mata dabi’ar banza

“Ta gayamin abinda ummu ta jima tana gayamin har nabar gidan nan,tace idan ya kama hannuna Allah zai qona ni,idan na yarda ko kusa dani ya zauna sabon Allah ne,kuma Allah zai iya qonani,kuma koda wasa ya tabanin tana ganewa,har waya take tana tambayata”

“Ke kuma idan ta tambayekin sai kike gaya mata?” Anty madina tayi hanzarim tambayar widad tana datsar numfashinta,kai widad din ta gyada,haushi da takaici ya saka anty madina sakin salati,sai yau ta yarda kaf gidan babu wanda yakai widad din rashin wayo,da gaske ne,ada da ake fada tana ganin ba haka bane,kawao miskilanci ne yayi mata yawa,ashe harda rashin wayon

“Yaushe duka ta gaya miki hakan akan uncle din”

“Kullum saita kirani,ta tambayeni dame dame nayi,dame dame yayimin” wanu malolo ya tsayawa anty madina,sai yanzu ta gane…..hafsat din tayi amfani da rashin wayon widad,da kuma tarbiyya me kyau data samu na girmama na gaba da kai da bin umarninsa ta kitsa mata wannaj baragurbin tunanin,tayi kuma sara akan gaba,suma sun manta basu fayyace mata irin rayuwar da ake nufi da rayuwar aure ba.

Zama na dirshan anty madeena tayi ta fara dora mata bayani akan matsayin hafsat din a wajenta,ta fayyace mata wace kishiya fes,sannan ta rufe da cewa

“Ba cewa akayi ki rainata ko kiqi yi mata biyayya ba,amma babu ruwanta da ko mene tsakaninki da uncle dinki,matsayinku daya a wajensa ke dashi,ki rufe sirrinki,karki yarda ki sake gaya mata komai dake tsakaninku”.

Sai kusan sha biyu na dare sannan anty madeena tabar dakin ta wuce dakin mijinta,tabar widad a zaune tanata saqa da warwara,komai ya yiwa kanta girma,tana ta jujjuya maganganun da sukayi da anty madina,tun daga farko har zuwa qarshe, yanzun itama data tafi dakin kawu abinda sukeyi kenan?,abinda ya fado.mata a rai kenan,kunya ta kamata ita kadao cikin dakin,saita cusa kanta a cikin filo tana sake hasashen abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninta da abbas din.

Bayan sallar asuba anty madeena ta zayyanewa daddynsu walidi yadda sukayi da widad din,tana dariya dariya tace masa

“Kaga babu sauran batun zuw wajen ruqiyya,a gayawa yaaya abba yayi haquri” kai ya jinjina yana murmushi

“Na yarda widad din muguwar sakaliya ce,ku daman baku fada mata komai ba?”

“Wallahi sam ban kawo haka a kaina ba,saboda naga yawanci yaran yanzun ma kafin a gaya musu sunsan komai,amma ita din shekarun nata sunyi qanana da yawa a sanda akayi auren,kuma dai dama widad din gaskiya ko cikin yaran gidan nan tana cikin ‘yan ba ruwa na,gatan da qaunar dake tsakaninta da ummu ne kadai yasa ake ganin ta sangarce da yawa,amma tana da dadin zama ainun”

“Shikenan,bari gari ya qara haske,zan shiga na yiwa ummu bayani,sai a shaidawa yaayan kafin yakai.ga fitowa,don nasan da abun ya kwana,da wuri zaki ganshi ya shigo” anty madeena dai tana dariya ta fice daga dakin.

Tare suka shiga kitchen da anty madeena din,saidai yadda taga widad din tana hada breakfast din cikin qwarewa yasa ta tsaya tana kallonta,sosai abun ya daure mata kai ya kuma bata mamaki,widad dince da iya sarrafa abinci haka?

“Me ya faru anty naga kina kallona” murmushi tayi tana sakin habarta

“Hmmmm,ba dole ba,irin wannan delicious haka da ake hada mana yau,lallai aure me gyara mutum,su Aafiya suzo suyi kallo,yau widad din da ummu ke hanawa dosar kitchen yau itace da hada breakfast tsaf mai rai da motsi” dariya tayi kawai,ita kanta a yanzun shiga kitchen na daya daga cikin hobbies dinta.

Kamar yadda daddynsu walid ya fada kuwa da wuri abban nata ya shigo da shirinsa,yana parlor yana breakfast ummu na ciki tana gyara dakin alhaji da ya tafi umra daddyn walid din ya gayawa abban komai.

Kofin hannunsa ya ajjiye yana girgiza kai

“Ashsha…..ashsha” sai yaja tsaki

“Zataci qaniyarta,wanne irin shirmen banza ne wannan?,dama wannan shirmen da shashancin tazo yi mana?”

“Har yanzu quruciya ke damunta yaaya,sai anyi a hankali” abban bai tanka masa ba,illa wayarsa daya ciro yayi kiran uncle muhsin.

Widad kuwa batasan me akeyi ba,tana can tare da anty madeena tanta karanta mata abubuwa,da azahar saiga anty deena,kamar tayi kuka haka ta dinga yiwa widad fada

“Me yasa kika taho,bance komai ya shige miki duhu ki gayamin ba?” Haduwa sukayi suka dinga wayar mata da kai,anty deena bata bar gidan ba sai bayan sallar magariba.

Washegari dai taga an hau mata shirye shirye,sai da azahar anty madeena ke gaya mata gobe zasu maidata kaduna,hawaye fal a idanunta take qorafi

“Tunda na tafi fa anty banzo ba ba’a jemin ba,kuma yanzu kwana hudu kawai sai ace na koma?ko alhaji ban gani ba”

“Eh ai wannan zuwan da kikayi mu ba irinsa mukeso ba,ki bari kizo cikin dadin rai da yardar mijinki,babu me cewa ki koma sai idan ranki yaso” dole tana ji tana gani taja bakinta tayi shuru,sai cika kawai da take tana batsewa.

Washegari samuel ya iso,tana ta kukanta kamar ranar za’a fitar da ita zuwa gidan miji,ita umma batulu,anty halima da anty madeena,anty deena ma taso zuwa,amma kuma a ranar mai gidanta zai dawo daga tafiya.

*_BAYAN WATANNI HUDU_*

*********A nutse motar ta cusa kai cikin gidan,bata saurara ba har sai data dangane da muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,ya dai daita tsaiwarta sosai sannan ya kasheta,ya zare key din daga jiki yana fadin
“Alhamdulillah”.

Waiwayawa yayi gefansa,tana kwance,ta lafe sosai cikin kujerar tana baccinta hankali kwance, murmushi ya subuce masa,bai dauka da tace baccin zatayi da gaske shi din zatayi ba,a hankali ya sanya hannu ya zare littafin dake kife saman cikinta wanda ya fadi bayan bacci ya dauketa,yadan duba page din da take ya saka mata alama sannan ya rufe ya dorashi a gaban motar.

Idonsa ya sake mayarwa kanta,ya zubawa baby face dinta ido,baccin da alama yayi mata dadi,ya saki murmushi,koda yaushe idan ya kalleta saiya tunata da wata wauta da quruciya data tafka,kome tayi ganinta take dai dai ne,har suyita rikici idan yace ba haka bane.

Hannu ya saka yadan bubbuga seat din,a hankali ta bude idanunta,ta zubesu fes cikin nasa,ta kafeshi dasu tana dubansa,he look gorgeous,kaftan din da ya saka sun bala’in amsarsa,ta gani tun daga gida kafin su fito,harma ta yaba,a yanzun kuma sai ta sake gani ya mata fresh sosai

“Yadai….” Ya fada yana dage mata girarsa cikin salon tsokana,murmushi ya subuce mata, kunyarsa ta kamata wanda a ‘yan kwanakin nan haka take ji a kansa

“Ba komai……”sai ta saka hannu ta bude murfin motar ta fito zuwa harabar gidan.

Iska ta shaqa tana duban harabar gidan,daga tafiyarsu last two weeks harabar gidan har ta canza,akwai datti da qura sosai,ita ke sawa a gyara duk sanda sukazo din,bayan ta karba hidimar sassan hafsat data tabbatar ko a yanzun akwai aiki jingim yana jiranta,a yanzun zuwa bauchin ya fara fita mata a ka saboda wannan dan uban aikin bautar da hafsat ke hadata dashi.

Waiwayawa tayi zuwa inda yake tsaye,ya fitar musu da kayansu daga booth

“Shikenan?,i have done?” Ya fada yana dubanta,narke fuska tayi sannan ta marairaice masa

“Uncle taimako please,ka qarasa min da luggage din mana” yadda tayi maganar a mugun shagwabe yayi masifar taba ransa,tun daga wancan ranar data dawo daga gudun hijirar da tayi,ba abinda ya sake bari ya hadasu,ko riqe hannunta,wannan yasa ta sake abinta sukaci gaba da mu’amalarsu,amma ya zuwa yanzun yadda kullum taketa canzawa da koyar abubuwa masu yawa ya sanya yaji ta fara taba zuciyarsa.

Kansa ya gyada,ya kama hannun jakar zuwa sassanta tana biye dashi tana masa hira.

Sai daya bude mata ya saka.mata jakar yana duban sashen nata da.har abada badai kaga datti ba saidai qura

“Can you help me?”

“Dame uncle?”

“Idan kin gama gyara sassanki please” murmushi ta saki,ko bai qarasa ba tasan me.yake nufi,kuma tana da wannan nufin a wannan karon,saboda magana da hajjaaa tayi mata tun wancan zuwa sun tsaka da waya

“Za’a yi in sha Allah uncle”

“Thank you” murmushi ya subuce mata,komai.qanqantar abu idan kayi masa sai ya gode maka,tana kallonsa ya juya a hankali ya fice,yabar mata sauran qamshin turarensa data zuqa da kyau ta fesar tana sake sakin murmushi,sannan ta taka zuwa cikin falon nata tana kallon ko ina,tare da tsara yadda zata fara aikin.

Sassan hafsat din ya wuce kai tsaye,yana son saur nauyin alqawarin sweet daya daukarma su mimi.

Yana dosar sashen yana jin dan tashin hayaniya,sai abun ya daure masa kai,saboda iya saninsa ita din bamai sakewa mutane bace,bata da fuskar da za’a zo gidanta a zauna ana hira haka,suma mutanen kowa ya gane don haka zaiyi wuya kaga tayi baqo.

Yana sake dosar sashen yana fahimtar tashin sautin maganganun ba na arziqi bane,yanayinsa yadan canza kadan da fargabar abinda yake faruwa,a haka ya isa qofar falon,ya tura ya shiga da sallama,dai dai lokacin da matar dake tsaye take cewa

“Yanzu dai ki fito da shinkafa kawai,tunda ke waye yazo gidanki ma bare ya dauka” ta buda baki zata bata amsa maganar tata ta maqale a maqoshi,tana tsaye tsakar falon,fuskarta har maiqo takeyi,kayan jikinta wari da wari ne na rigar wani lace nata da har ya fara tashi tashi saboda dadewa,sai zanin atamfa,ta yane jikinta da wani tsohon mayafinta milk color

“Sannu da zuwa” ta fada muryarta tana dan rawa,itama matar dake tsaye dauke da wata babbar roba blue ta miqa masa tata sannu da zuwan,duka ya hada ya amsa musu,sai ya wuce zuwa dakin hafsat din kai tsaye.
[3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button